Showing 15001 words to 18000 words out of 95534 words
ya kafe,wai duk nigeri shine lamba daya.....kijimin qarya ramatu" anni ta qarashe fada tana yatsina fuska da tabe baki.
Murmushi yuuma ta sake tana kada kai,tana matuqar sha'awar yadda suke kula da anni,tana jin cewa dama ace itama tana da arziqin da zata ramawa anni koda dan kadanne cikin irin alkhairanta gareta
"Tunda ya fada ai hakanne anni" kashingida tayi kan lallausan katifa da bargo da yuuma tayi mata shimfida da ita
"Ke rabu da shi ramatu,bokon tasu ma ta wannan qarnin tafi qarfin hankalinka,ke bakya ce sunyi muhammadiyya ba" anni ta fada tana fadawa wani tunani can,wanda har sai da yuuma ta ankara
"Yanzu anni har yau baki bar sana'a ba?" Idanunta ta bude sosai tana kallon yuuma
"Ramatu,kome arziqin mijinki jikoki da 'ya'ya kada ki kuskura kice zaki rabu da sana'a,duk tsiya naka naka ne,koda ba'a rageka da komai ba,amma naka yana da dadi" kai yuuma ta jinjina tana gamsuwa da zancan anni,tun tale tale anni bata saba da zaman banza ba,har kawo yau da babu abinda ta nema ta rasa,ko rai tace tana so idan ana siyar dashi za'a siya mata,amma bata daina nema ba,tana da makeken gidan gona,wanda tafi ji dashi fiye da komai nata.
Tun suna hira sama sama har bacci yayi awon gaba da anni,sai a sannan yuuma ta gyara nata wajen ta kwanta itama.
*_WASHEGARI_*
K'arfe takwas na safe yuuma ke dosar dakin daada dauke da turamen atamfa gudu hudu a hannunta da shadda ta maza yadi goma,sai takalmi na maza me kyau wanda ta tabbatar zaiwa ibrahim.
Da sallama ta daga labulen dakin daadar,safiya dake zaune tana shan kunu ta amsa mata tana gaidata,dai dai lokacin daada ta fito daga uwar dakinta tana daura zani,kafadarta saqale da hijabi.
Gaisawa suka fara yi da yuuma sannan ta'ajjiye mata kayan
"Gashi inji anni"
"Too.....anni bata gajiya,to Allah ya amfana ya qara arziqi" daadan ta fada cikin farinciki,mutum ce dake matuqar son ka yiwa 'ya'yanta alkhairi,safiya dake shan kunu tataso itama tana daga atamfofin tare da fadin
"Bara na zaba tawa kafin zubaidata iso ta dauke wadda tafi kyau......gaskiya anni nada kirki,bata gajiya" murmushi yuuma tayi ta miqe,har takusa da qofa ta juyo
"Af.....niko daada nace ba,ko ibrahim ya gaya miki inda yaje ne?,tun jiya anni keta tambayarsa,kuma kamar banga shigowarsa gidan nan ba tun shekaran jiya,abincinsa ma sai da safen nan na hada a dumame" tana shirin saka hijabinta ta amsa mata
"Eh.....na turashi gidan sukaina"
"Sukaina?" Yuuma ta maimaita a ranta cike da mamaki,saidai ba kasafai take magana akan wasu abubuwan da daada ke yankewa kan yaranta ba
"Ayyah...to Allah yasa zasu hadu,don jibi annin zata koma"
"Ba lallai gaskiya,inajin sati zaiyi acan kafin ya dawo"
"To ba laifi" yuuma ta fada tana ficewa,kanta ya daure tamau,sukainan yayar furera ce,bata da kirki ko kadan,masifaffiya ce ta bugawa a jarida,tana aure ne a wani qauye dake maqotaka da rugarsu,ta yaya za'a tura saurayi kamar himu gidan yayi kusan sati?,duk da itama tana da samarin yara kamarshi,amma kuma tafiyar ai ba ta radin kansa bane,kamar wani qaramin yaro?,da wannan tunanin yuuma ta koma dakinta,inda tabar anni da kuma laila wadda ke jira a kawo mata qosai da yuuma ta bayar a siyo mata,tace shi take sha'awa,tunda suka tashi da safen take jiyo qamshinsa.
Suna tsaka da hira daada ta shigo a shiryenta tsaf,suka gaisa da anni sannan tayi mata godiya daga bisani tace
"Zanje na dawo yuuma,ba dadewa zanyi ba" kallonta yuuma tayi cike da mamaki,ina zata da safen nan,uwa uba kuma ma kusan dokar bappa ce,basa fita unguwa a gidan matuqar ya tafi kudu irin haka sai ya dawo,kamar anni tasan tunanin da yuuman take sai tace
"Labaran ya sassauta tsaurin nasa kenan?" Tayi maganar tana dariya.
Kai daada ta kada fuskarta na nuna zallar damuwa
"Ko daya anni,dole ta kama na fita ne,zanje na yiwa wata yarinya data nacewa himu gargadi,waye zaiso hada iri da irin tsiya irin jaraba",laila dake dan sauraron voice note na watsapp ta earpiece din dake kunnenta sai ta zareshi,ta miqe ta zauna sosai tana kallon daada,saboda yadda taji maganar banbarakwai,ita kanta anni dake rayuwa cikin tsakiyar birni,cikin ahali da muhallin da wayewa da kuma boko suka yiwa katutu sai data ji maganar bawai
"Tooo....ikon Allah,to....abi a sannu dai,Allah ya maganta mana"
"Ameen ameen,sai na dawo"
"Allah ya kiyaye" yuuma ta amsa mata.
Shuru yuuma tayi tana juya batun cikin ranta,me yasa daada take haka?,akan yaranta gaba daya idanunta suje rufewa?,yanzu Allah ne kadai yasan idan taje me zasu aiwatarwa da yarinyar,tunda ta riga data sani,innar laulo qawace kuma aminiya a wajenta,ita kanta banda ubangiji ya riga da ya qaddara tafi qarfinsu,da ba qaramar wuya zata bata ba ta hannun daadan.
"Wai....nace ba" laila ta fada tana duban yuuma,sai ta maida hankalinta ga laila
"Wai daada kuwa cikakkiyar bafulatana ce yuuma?" Murmushi yuuma tayi,tasan me lailan ke rayawa cikin ranta
"Gaba da baya,har gwara ni innata itama ruwa biyu ce,amma ita babu sirki"
Tun gabanin lokacin tafiyarta kiwo yayi yau din ta shirya,da wurwuri tayi wanka don kada innar laulo ta farga ta hanata yi,ta gyara jikinta sosai,ta kama jelar gashinta ta nannadesu tayi musu wata lanqwasa me qawanya me kyau,hatta da duwatsun kwalliya na kanta da hannunta sai data qara wasu,ta sake fita bufalatana zam.
Can qasan ranta takejin cewa tana yin wannan kwalliyar ne duka saboda ibrahimu,tana ji a jikinta zaiyi wuya ace yau din baizo inda take ba,saboda yaune kwanaki uku suka cika bata ganshi ba,bata saurari wani abincin safe ba,tunda ba ita zatayi ba yau,ta cika gorarta da nono wanda ta tatsa ta barwa innar laulo xatayi aikinsa za'a fiddashi kasuwar qauyen dake maqotansu wadda take ci yau.
Tun kafin innar ta tashi ta kada dabbobin kiwo,yau fes takejin zuciyarta,da wani nishadi na daban,ba kuma lallai ka fahimci haka ba,amma idan ka kalli fuskarta da kyau xakaga akwai banbancin yanayi a tattare da ita.
Wajen daya zame musu gurin zama ita da ibrahim din ta koma ta zauna bayan ta gama duk abinda ya kamata tayin,lokaci bayan lokaci tana daga kanta zuwa sama,ta wurga kallonta hagu da dama,tana ji kamar ibrahim din yana hanya,kamar yana tahowa inda take.
"Kin fara son ibrahim ne?,me yasa zuciyarki ke canzawa?" Ta yiwa kanta wannan tambayar karo kusan na uku kenan,sai ta girgiza kanta a hankali,har yanzu batace ga dalili ba,amma rashin zuwan ibrahim din a kwana uku rak sai takejin kamar tans komawa izuwa wata duhuwa ne data fita ta bari.
Duk da yadda lokaci ke qara jaa amma bata saare ba,bata rasa qwarin gwiwarta ba,taci gaba da dube dube,har daga bisani ta miqe daga wajen,ta fara kewaye cikin dabbobin,wai ko hakan zai sanya lokaci yayi gudu,ya kusantata da zuwansa wajen.
"Maimunatu na!" Kakkaurar muryar mai cike da kaushi ta doki kunnenta,ta kuma zama musaya ko ince madadi ga muryar ibrahim da take ta dako da fatan ji.
Buɗeri ne,ba shakka shine,saboda shi daya yake mata wannan kiran mafarautan,kiran dake sanya zuciyarta luguden bugu,ta sauke sandarta a hankali tana nufin juyawa zuwa gareshi,saidai kafin ta waiwaya din har ya iskota ya sha gabanta,taja baya da sauri saboda yadda kusancin dake tsakaninsu yayi qanqanta da yawa.
Fuska ya hade yana kallonta
"Meye na ja da bayan?,kin manta ke din tawa ce?" Ya fada yana nunata da yatsa,kau da kanta tayi,idanunta suka sauka ga qafarsa dake cikin huffaje,saidai shi kansa huffajen yayi daqal daqal dashi,kamar yadda sutturar jikinsa take cidin cidin,sau tari tana mamakin uban tulin qazanta irin naa buderi,abune me matuqar wuya ka sameshi fes cikin tsafta
"Amma kinyi kyau maimunatuna......ina fata babu wanda ya kallemin ke" yayi maganar yana washe baki,kanta ta daga a hankali tana duban gefe da gefanta,tana fatan kada Allah ya kawo Ibrahim a yanzu har sai buderi ya wuce,tasha jin alwashi daga bakin buderin na cewa,duk randa yaga wani ya rabi maimunatunsa,wala shakka sai ya sha jininss,tana kyautata zaton wannan na daya daga cikin dalilan daya sanya babu wanda yake mu'amala da ita
"Me kike nema kuma?" Ya fada yana hade rai,kai ta girgixa
"Babu komai" amsarta tasa ya saki fuska
"Na sani,kinfi kowa hankali cikin 'yammatan rugar nan,nasan babu wanda zaki kula,ungo wannan" yayi maganar yana miqa mata wata leda.
Babu batun ma tace ba zata karba ba,don kuwa bata baki ne,don haka ta saka hannu ta karba tana cewa
"Na gode"
"Yauwa,medillu,dan men waratam?(zan tafi,yaushe zanzo?" Mummunan faduwa gabanta yayi,kada dai xancan da innar laulo ke gaya mata ya tabbata,buderi..... Buderi ne zai fara zuwa tadi wajenta?
"Ban sani ba" sandarsa ya wulwula sama ya caketa a qasa
"Shikenan,ni xan saka rana da kaina" sai ya juya abinsa ya fara tafiya,dama can shi din ba mutum ne da ya iya yin sallama ba,da ya gama abinda ya kawoshi xai saka kai ya wuce abinsa,har ya dan bata rata sai taga ya dawo da tsaya a gabanta
"Baki taba cewa kina so ba maimunatu,ate ayyam?,ayid'iyam?(zaki aureni?,kina sona?)" Banbarakwai taji maganar tasa,ta kuma rasa amsar da zata bashi,tana matuqar tsiron buderi,batajin xai kasa maketa a wajen idan tace bata sonshi,amma kuma idan tace tana sonsa din tayi masa qarya,sannan yaudara ta shigo ciki.
Dariya ya bangare da ita
"Ja'ira,kunyar gayamin kikeji kenan.....shikenan,idan nazo saiki gayamin tunda zuwan dare ne,bana ganinki sosai" daga haka ya juya abinsa yana waqar tauri.irin ta matasan fulani yana cilla sandarsa.
Baya taja a hankali ta jingina bayanta da bishiyar dake wajen,ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tana lumshe idanunt,sannan ta saki ledar hannunta a hankali ta sulale zuwa qasa.
A matakin rayuwarta gaba daya ba zata iya dorar da komai ba,ba zata iya fadin meye ainihin rayuwa ba,kamar yadda ba zata iya fadin me rayuwa ta qunsa ba,meye manufar tata rayuwar?,me ta cimma?,me takeso ta cimma?,tabbas a karan kanta tasan cewa akwai abubuwa da dama da takeso ta cimma,tana da mafarkai da burika masu yawa irin na kowanne dan adam,saidai ita kanta batasan wadanne ne burikanta ba,me takeso ta cimma din,dukka bata sani ba,rayuwata qwaqwalwarta dama komai nata na tattare ne a waje daya,a yanzun kumma innar laulo ta dauko hanyar da zara qara ruguzata zuwa pieces gaba dayanta,aure da buderi?,me hakan yake nufi?,wanne buri ne a ran innar da takeso ta cimma?.
Ta jima a haka kafin ta iya bude idanuwanta,dukka wani fata da take dashi na ganin ibrahim ya fara zagwanyewa daga zuciyarta gaba daya,ganin yadda lokacin da ya dace tabar wajen zuwa gida ya gabato,jiki a mace ta miqe daga jikin bishiyar,saidai tana taku biyu takalminta ya katse
"Innalillahi" ta fada gabanta yana faduwa,ta duqa a hankali da zummar daukoshi,sai tayi arba da ledar da buderi ya kawo mata wadda ta jima da faduwa a wajen,ta sanya hannunta a nutse ta budeta,sai tayi arba da gasashen naman daji,cikin tashin zuciya ta dauki ledar gaba daya tayi wurgi da ita can cikin daji,sannan ta dauki takalminta ta duba da kyau,ya gama moruwa,bataga laifinsa ba,saboda yayi mata iyakar qoqari,bata da wata sauran dabara data rage mata,abu dayane a yanzu yayi mata saura shine ta cire dayan ta dauresu a qugunta,sannan taci gaba da tafiya da zallar tafin qafarta tana fara hade kan dabbobin,tanayi tana takatsantsan kada ta taka qaya.
07
Tun batayi nisa ba gaba daya qafafunta taji sun daddaure saboda tsakuyiyin da take takawa,wani gurin harda cabalbalin daya cakude da ruwa da qasa,tuni ta jima da sanin cewa ba qaramar rahama bane takalman a gareta,rashinsu a yan mintuna kadan yasa fa fara dandana kudarta,bata kuma san sanda zata sake mallakar wasu ba.
A hankali motarsu daada ke kutsawa rubibbiyar hanyar mai yawan gargada,kamar yadda sukazo a yanzunma su hudune,saidai yanzun akwai qarin saddam da zai musu rakiya,a hanyarsu ta zuwa ziyara qauyen dake kusa da rugar ummarun.
Cikin motar tattaunawa suke kan yadda gwamnati tayi banza da nuna halin ko in kula da jama'ar dake rayuwa a irin wadan nan muhallan,babu ruwa ba wuta babu hanya me kya bare azo ga maganar tsaro
"Subhanallah" salmanu driver ya fada yana taka burki sanda shanun suka fara keto burtalin xasu wuce,salmanu ya kalli agogon hannunsa yana cewa
"Aqalla sai sun kusa minti biyar ko takwas suna wucewa,shi yasa tun dazun nake sauri mu wuce kafin su iso"
"Wai daman kuna iya kula da dabbobi babu duka?" Laila ta fada cikin mamaki,idanunta nakan maimunatu dake koro shanun daga can baya
"Qalilan ne gaskiya,kiwo yana da wuya fa adda laila" maganar data ja hankalin daada,ta daga kanta zuwa ga sashen da maimunatu take.
Ido ta zuba mata sosai cike da mamaki da kuma burgewa,gaskiya sadam ya fada ba kowane ke iyawa ba,kula da dabba koda guda daya ne abune mai matuqar wahala,sai mutum me haqurin gaske da kuma tausayi,bare wadan nan da sun haura talatin,banda akuyoyi,yarinya qarama irin wannan me qananun shekaru,ita daya babu mataimaki,zata iya cewa bata taba ganin wannan ba,koda akwai din sai jarumar mace mai kamar maza,wadda taga jiya ta kuma ga yau.
Idanun maimunatu nakan motar sanda ya rage ita daya ce zata haura hanyar,idanunta cike fal da fargaba da tsoro,karo na biyu kenan da taga motar,amma sai take ga kamar abinda ya faru da ita shekarun baya zai sake faruwa da ita,sassanyar ajiyar zuciya ta saki sanda taga ta tsallaka,dai dai lokacin da anni ta sauke idanunta ga qafafuwan maimunatu,mamaki ya cikata ganin yadda take ratsa wajen da zallan qafarta ba takalmi.
Ta buda baki xatayi magana ta jiyo sautin maimaunatun
"Wayyo Allah" tayi maganar a matuqar jigace tana duqawa zuwa qasa tana duban tafin qafafunta
"Tsaya salmanu.....dubamin me ya samu yarinyar can" anni ta tsaida salmanu dake shirin tada motar,wajen suka kalla su duka,laila tayi kamar zatayi magana amma sai ta fasa kada qilu ta jawo bau,seat belt din jikinsa ya zare ya bude murfin motar ya fita,bai wuce minti daya ba ya dawo
"Kaya ce ta shige mata qafa,ta huda wajen sosai,amma naga ta zareta ma"
"Garin yaya?" Wajen da take salmanun yakalla
"Qafarta ce ba takalmi,dana tambayeta yana ina sai tace ya tsinke ne"
"Ina silifa din nan da nace a sakaminsu a mota?,daukomin daya a ciki" ta fadawa laila,daukowa laila tayi ta miqowa annin
"Bawa salmanu yakai mata ta saka" hannu salmanun ya saka ya karba ya juya yakoma indatake,zuwa sannan ta miqe tsaye bayan ta yagi wani ganye dake gefanta ta manna a wajen.
Daga kai tayi ta dubi salmanun sanda yake bata takalmin,sai taja baya kadan gami da girgiza kai alamun ba zata karba ba,abinda ya sanya salmanu dawowa inda anni ke zaune tana kallonsu
"Anni taqi karba fa,kamar bata yarda bane damu"
"Budeni" anni ta bashi umarni,sai ya zagayo ya bude mata qofar
"Anni,karkice zakiyi magana da ita,kaf fadin rugarmu babu wanda yake kulata" sadam ya fada,a mamakance anni ta kalleshi
"Saboda me?"
"Ban sani ba nima,amma tsoron mata magana akeyi" shuru anni tayi na wasu sakanni sannan ta zura qafafunta waje ba tare data sake bi ta batun saddam ba
Har maimunatun tayi taku daya biyu taji muryar anni
"Yarinya" cak ta tsaya,a tsorace ta waiwayo idanunta akan anni,tsoro ya sake kamata,don sam annin batayi zubin mutanensu ba.
"Yallijam" maimunatu ta fada a hankali ganin idanun annin har yanzu yana kanta
"Jam" anni ta maida mata tana kallonta tare da karantar yanayinta
"ya kike tafiya haka ba takalmi?" Qafarta ta kalla sannan ta kalla annin
"Sun tsinke ne daada" yadda ta kirata da girmamawa sai yasa anni ta saki murmushi
"Salmanu bata wadan nan ta saka,da hatsari wajen taka gurin nan haka" da fari kai maimunatu ta sake girgizawa kamar yadda ta yiwa salmanu,don batasan me zatacewa inna ba idan ta ganta da takalmin
"Na gode daada,zan qarasa a haka" haka kawai taji ta burgeta,akwai alamun tarbiyya da kamun kai me yawa tattare da ita
"Karki damu ki saka,idan ma kina tsoron fada ne a gida kice baquwa ce daga gidan bappa labaran ta baki" daga kai tayi sosai tana duban anni,idan ta canka dai dai fa kenam gidansu himu take nufi,ita a wa sa zata ambaci sunan gidan tace wani abu daga hannunsu ya fito zuwa gareta,a sanyaye ta karba takalman ta sakawa qafarta.
Cif da cif kuwa kamar an aunata,wasu irin slipper ne na danqo amma me garai garai dake nuna hoton flowers daga dukka jikin takalmin kaman tangaran,kallon qafar tata tayi ta sake kalla,sai ta daga kai a hankali tace
"Na gode sosai daada" duk kuwa da tana da yaqinin wannan takalmin idanunsa idanun inna ba rabonta bane,murmushi anni tayi
"Ba komai" sai ta juya maimunatun tana qara hanzari don ta taddo dabbobinta da sukayi gaba,tana kuma kiransu da wani irin salo da yasa anni ta bita da kallo.
"Anni....anni kenan,qaqale qaqalen mutane,tayiya jajibo jama'a ana zaune qalau" laila tayi 'ya qaramar mita ciki ciki,abinda yaja hankalin anni dake maida qafafunta cikin motar salmanu yana shirin rufe mata
"Me kike cewa ke kuma?"
"Bance komai ba"
"Oho miki,idan ma zagina kikayi kin zagi marwanu da Aishatu" idanu laila ta lumshe tana dafe goshinta,kafin tace wani abu wayarta dake kan cinyarta ta dauki sautin kida me dadi,saita daga wayar tana dubawa
"Ga marwanun nan" lailan ta