Showing 6001 words to 9000 words out of 95534 words
farincikin boye masan da tayi yana saukar mata,kwata kwata kuma ko sau daya bata taba yiwa buderi kallon mutum mai hankali ba,hasalima tsoro yake bata ainun,buderi kenan,baqin bafulatani na usul,wanda ke ciie da wasu irin baudaddun halaye na wauta jahilci da hauka,irin nau'in haukan da jahilcin ne ke haifar dashi,zuciyarta cike take da mamakin me yasa shi din baya gudunta kamar yadda sauran samarin qauyen ke gaza rabarta bare su furta mata kalmar so?,me yasa shi bai gujeta ba?,ta jima tana yiwa kanta wadan nan tambayoyin.
Sai data tabbatar da cewa ya yiwa wajen nisa sannan ta fito,zuwa sannan zazzabin jikinta yayi wata irin saukar da babu shiri,sai sauran dumi,ciwon kai mai tsanani saboda razana da bayyanar buderi da kuma ciwon jikin da har yanzu tana jinsa shima,ta tako a hankali ta dawo ainihin wajen da ta fara zama da farko,tana tattare jikinta waje daya.
A nutse yake takowa yana kuma sake nazarin rigar tasu,yanayin yadda ko yaushe take bunqasa da tarin dabbobi da albarkar kiwo kusan ya zarce na kowacce ruga dake maqwabtaka dasu,ni'imar dake wajen ta banbamta daya sauran yankuna,hakan shi ya sanya yanayin wajen da rayuwarsu t bambanta data sauran sassa.
Tun daga qasan ruhinsa zuwa saman fuskarsa cike take da wani irin nishadi,tun daga daren jiya da yayi gamo da ita.....har kawo warhaka da yake takowa cikin rugar tasu daga doguwar tafiyar da yayi zuwa cikin ainihin garinsu,tunaninta,siffa da kuma kamanninta basu bace daga idanunsa ba,duk sanda siffarta zata wulqa cikin idanu da tunaninsa sai ya samu kansa da subucewar murmushi,wani lokaci hatta da haqoransa sukan bayyana,nuni da girman nishadin da zuciyar tasa take ciki.
Goye yake da baqar jaka,yana sanye da baqin wandon jeans,sai asalin rigar fulani dake jikinsa mai gajeran hannu,daga ciki kuma t.shirt ya sanya mai dogon hannu saboda hana bayyanuwar dantsen hannunsa,saman kansa ma hular fulanince,sai qafarsa dake sanye da wani rufaffen baqin takalmi na danqo.
Ba qaramin qara masa kyau da haiba kayan sukayi ba,sun kima fidda ainihin salsalarsa na bafullacen usul,duk da kana dubansa zakasan cewa ya dan banbamta da sauran matasan fulani irinsa dake rayuwa cikin rugar,akwai wani banbanci na daban da kuma haske tattare dashi.
Hakanan kawai zuciyarshi ta bashi yabi ta gefan ruwan,yana da tabbacin hakan zai qara masa nishadi,bayi wata wata ba yabi shawarar zuciyarsa,yana tafe yana kallon yadda dabbobin dake baibaye da gefannin kogin keta kaima cikinsu ruwan.
Da kallo yaci gaba da.binsu yana sake takawa izuwa gaba,babban abinda ke sake hanashi sakewa da garin kenan,had'akar ruwan sha a gurbi guda tsakanin dabbobi da kuma al'ummar yankin,daya daga cikin burin da yake dashi idan har Allah ya cika masa burinsa,banbance ruwan shan dabbobi dana mutanensa.
Dauke idanunsa yaso yi,saidai daga gefe guda dab da rafin wani abu ya dauki hankalinsa,ya rage sassarfar da yake a tafiya,ya sake qura mata idanu saboda tabbatar da hasashensa,shin itace koba ita bace,bashi da sauran zabi.bayan ya tabbatar da ita dince illa bin umarnin zuciyarsa dake azalzalarsa yakai gareta,ko zai rabauta da daddadan sautin nan da take magana dashi a koda yaushe.
"Assalamu alaikum" ta tsinkayi sallama daga gefanta,bata tsorata ba duk da bataji takun tafiya ba darajar sallamar da aka gabatar mata,sai ta cira kanta dake boye tsakanin qafafuwanta.
Fes ta zubesu a kansa,tadan tsura masa idanu na wasun gajartattun mintuna,qwaqwalwarta da zuciyarta nason tuna mata fuskar,ba tare da daukan dogon lokaci ba ta harbo mata wayeshi,mutumin da ya fara taimakonta tsahon xamanta a rugar ummaru,bai kyautu ba ace ta manta fuskarsa haka da wurwiri ba.
Dukkan jarumta da juriyarta ta tattaro,ta sake masa murmushi wanda yayi fidda wani boyayyen kyau dake kwance saman fuskarta
"Yallijam(ina yini)" ta furta da sassanyar muryarta tana sauke qafafunta dake takure cikin jikinta kai tsaye sukayi masauki cikin ruwan dake gabanta,sai daya maida mata da murtanin murmushinta,yana jin wani.abu na narka zuciyarsa sannan ya amsa mata
"Jam....alhamdlh" ya amsa mata idanunsa bisa kanta,tana wasa da qafafunta cikin ruwan
"Nobaluɗa ke`yen(ya kika kwana jiya)"
"Lafiya alhmadlh" ta amsa masa tana masa kallo daya,saita maida idanunta ga ruwan ganin ita yake kallo
"miyatti fa,na gode sosai da alkhairinka na jiya"
Karamin murmushi mai sauti ya sake sannan yace
"ko'en waɗi ken yen?(me akayi jiyan?" Dubansa ta danyi cikin mamaki,sai kuma ta kawar da kai ganin kallonta yake,shuru ne yadan ratsa a tsakaninsu,kafin ya buda bakinsa a hankali cikin nutsuwa yace da ita
"Anaunaaki nke'yan?(bakiji ciwo ba jiya?)" Hannayenta ta kalla a hankali,tana jin yadda jikinta yake mata babu dadi
"Eh" ta amsashi a hankali,sai shuru ya sake wanzuwa a tsakaninsu,jifa jiya yake satar kallonta,yana son sake mata magana ne,akwai abubuwan da yakeson sani game da ita,bazai yiwa kansa qauron baki ko ya cuci kansa ba,kansa tsaye zai iya fadima kowa cewa daga jiya zuwa yau din ta sace zuciyarsa,ta kuma tafi da hankalinsa,dan zaman nan kuma da sukayi na wasu gajerun mintuna ta sake burgeshi qwarai da yanayin tsarin dabi'arta,yawan shuru shuru da kuma alamun cikakkiyar nutsuwa,dukka sun nuna kansu tattare da ita
"No'indema surbajo(ya sunanki ne 'yammata?)" Ya fada yana kallonta,fuskarsa qunshe da murmushi,yanayin yadda ya furta maganar tasa maimunatu jin wani banbarakwai
"Inde'an maimunatu,daada ta tana cemin diyam" ta fadi maganar wani abu yana motsa zuciyarta,don har sai da hakan ya nuna a saman fuskarta,kai ya jinjina
"endema eweli (Sunanki nada dadi....ni baki tambayi nawa sunan ba" satar kallonshi kadan tayi,bataga amfanin tambayar nashi ba,saidai tana duba da alkhairinsa gareta,don haka tace
"No'indema" murmushi ya saka kadan sannan yace
"Ibrahim.....anfi kira na da himu" kai ta jinjina kawai ba tare data ce komai ba,dukkansu idanunsu kan ruwan dake wucewa ta gabansu
"Deko tata nwulo?(yaushe zaki tafi gida?)"
"joni(yanzu)" ta samu kanta da fada,duk da ainihin abinda yake cikin zuciyarta kenan,saidai tana tunanin komawar,bataso taje ta tadda bud'eri cikin gari yana jiranta,tanajin kamar taci gaba da zamanta cikin jejin,saidai kuma dole ta koma gida,ko don yadda takejin yanayin jikinta a yanzu.
"Amma kamar lokacin komawa bai qarasa yi ba ko?" Himu ya fada bayan ya gama qarewa sama kallo,wadda keda sauran rana tarwai,kai ta gyada,sai taji bata sha'awar fada masa qarya,yar kulawa daya nuna mata daga jiya zuwa yau takejin girmanta har ranta,tunda abune da bata saba ganinsa ba
"Minyauɗo(bani da lafiya)" tayi maganar kanta a qas,zuciyarta na karyewa
"Subhanallah" ya fada cikin rudewa kadan yana dubanta
"Tun yaushe?"
"Jiya" ta amsa masa a taqaice
"amma hanjun foɗi gurtoyiɗa durgul?ginɗimu?(Amma shine kika fito kiwo,me yasa?" Shuru tayi ba tare data furta komai ba,shi kuma yayi tsaye yana jiran amsarta,amsar da bata da ita,tunda batasan me zata gaya masa da zai fahimta ba.
Ganin bata da niyyar cewa komai,da alama shuru shuru da rashin sonyin magana cikin jininta da halayyarta suke,sai ya miqe yana ajjiye jakar dake goye a bayansa yana cewa
"kowanna tama?(me yake damunki?"
"Zazzabi ne"
"qila inpab ɓoje(wataqil malaria ce)" shuru tayi masa,duk da tasan cewa ba malaria din bace,har zuwa sanda ya yiwa jakar ma'ajiya
"imi wara(Ina zuwa" ya fada yana takawa zuwa wata hanya da zata fiddaka daga wajen kiwon gaba daya.
Binsa tayi da kallo,ko waye shi?,me yasa yake rabarta?,baisan wace ita ba?,maganganun 'yan rugar tasu dangane da ita bai iskeshi ba?,saita maida idanunta ta lumshe ta sake budesu kan jakarsa daya ajjiye gefanta,ta kalli jakar me kyau da ita,kuma fes take,da alama tsafta ta wadaceta,tun ganin farko data masa zuwa yanzu ta tabbatar ga banbanta da dukka sauran mazan qauyen,ta kwantar da kanta saman cinyarta tana tariyo magangun da sukayi dashi daga jiya zuwa yau.
*Arewabooks username*
*HUGUMA*
❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥
*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*
*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*
*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*
😄😄😄😄😄😄😄
*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*
*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*
INAYA(riba biyu)___mamughee
SANADIN LABARINA___Rano
BABU SO___Billynabdul
FARHATUL K'ALB___Miss xoxo
GURBIN IDO____Huguma
*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*
*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*
Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300
*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank
*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902
*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107
*_THANKS FOR CONTINUES PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
*_GURBIN IDO_*
*Arewabooks::HUGUMA*
Free page 04
Sallamarsa ta yanke mata dan qaramin bacci mai dadi data fara yi,ta daga kanta tana amsa masa,da murmushi ya bita,hannunsa dauke da baqar leda qananu guda biyu,inda ya tashi dazun ya koma ya zauna,sannan ya bude ledan yana cewa
"Ga magani kisha" idanunta ta lumshe gami da budesu lokaci guda cike da.mamaki,yau ita ake cewa ga magani?,anya kuwa ita dince......maimunatu?,bata sauka daga wannan mamakin ba ta sake jin muryarsa yana sake miko mata wata ledar
"Amma ki fara cin wani abun tukunna,na sani idan baku da lafiya bason cin abinci kuke ba,haka innata ke fama dasu zubaida idan basu da lafiya" ya qarashe maganar yana miqewa
"Bari na baki waje,amma idan bakisha maganin ba zan dawo" saiya juya yayi nesa da ita,yayin da ta rakashi da kallo har sai data daina hangoshi,sannan ta janye manyan idanunta ta mayar kan ledojin,ta sanya hannu ta jawosu tana budewa.
Ledar farko magunguna ne,qwayoyi tablet sosai,sai leda fa biyu dake dauke da gurasa mai kyau,wani yawu ta hadiya,duk da yanayi na lalurar rashin lafiya da take amma sai da tsohuwar yunwa ta taso mata,batayi qasa a gwiwa ba ta dauka ta fara ci,tana ci tana lumshe idanunta tsananin azabar yunwar data tarawa cikinta,dama don bata da lafiya ne,amma duk sanda inna ta gwada mata irin wannan rashin imanin......a nan gurin kiwo take samun daya daga cikin naggen ta tatsi nono mai dumi tasha,duk da ta sani,yawanci da safe shine lokacin tatsar,amma dole tasa wasu lokutan take hakan,idan kuma ta samu ta faki idon innar sanda take tatsar da sassafen ta ɗaɗɗaki wani,shine zata wuni nata damu ba,yunwa kuma bata addabeta ba kamar yanzun,har shan nonon ya zame mata jiki,ya koma kamar shine abincin nata,abinda yasa ko kadan bata da wani jiki kwata kwata,duk sirantaka irin ta bafullace tata ramar ta fita daban.
Bawai don ta qoshi ba ta janye hannunta,a'a,tayi hakanne saboda kunya kara da alkunya,kada yazo ya taras ta tashi da ita,ta bude ledar maganin wanda ya sanya ledar ruwan pure water guda daya,ta daga pure water din ta jujjuya shi a hannunta,ba zata iya tuna sanda tasha ruwan leda ba a rayuwarta,saita koma kan magungunan,ta balli kowanne kamar yadda taga anja sandunan layi ajiki ta kora da ruwan.
Idanunta ta mayar tana sake lumshesu,tana jin yadda numfashinta yadan fara daidaita albarkacin gurasar data ci tun kafin magani ya soma mata aiki,a hankali take zuqan iskan wajen tana kuma sauraren koke koken dabbobi dake kai kaw a wajen,jikinta yana mutuwa murus kamar wadda aka yiwa dukan tsiya.
Tun daga nesa ya kafeta da ido,idanunta dake lumshe sai suka sake qarawa fuskarta kyau,yana ganin baqonnin yanayi tattare da ita,yana son sanin wace ita sani na haqiqa,da kuma dalilin da yasa take kebance kanta take nesa da jama'a haka.
Sallamarsa ta sanyata bude idanunta
"A henyi?(Kin gama?)" Kai ta gyada masa tana kallon qasa,kunya tana cikata,tanajin yadda tayi abun kunya,na yadda zata zauna taci abinda ya futo daga hannun saurayi
"hokkoyon dunni sauro(miko min sandar can)" ya fada yana nuna sandarta dae gefe,sai data kalli sandar sannan ta maida dubanta kanshi,ya fahimci me take nufi,don haka murmushi kawai ya sakar mata,ya taka da kansa zuwa gefanta ya dauki sandar,ga bishi da kallo mamaki fal zuciyarta
"waye shi?" Tambayar da taketa nanatawa kanta kenan.
Daga nan inda take tana iya hangen yadda yake tattare mata kan dabbobin nata cike da hikima da kuma qwarewa wadda ta lunka tata,da alamu shima din gwanine wajen iya kiwo,bai dauki wasu lokuta masu dama ba ya dawo gareta,yana sabe da sandar kan kafadarsa
"indillo(Muje ko?)" Yace da ita,dubansa tayi sanna ta janye idanunta gefe daya,sam maganar batayi mata ba,ta yaya zata jera dashi har cikin gari?,akwai idanun mutane masu yawa a kanta,sannan tana da kunyar da ba zata iya aikata hakan ba
"ummadillen(Tashi mu tafi),ko ba zaki iya tashi ba?"ya sake maimaitawa a tausashe,a hankali ta girgiza masa kai
"Kaje kawai,na gode,zan qarasa kaisu gida da kaina,na gode qwarai" idanu yadan zuba mata kadan,sai ya sauke ajiyar zuciya yana sauke sandar daga kafadarsa,ya fahimci me take nufi,tabbas ga cika bafulatanar gaske.
"Shikenan,zan kora miki su,tumudilli tokkirawaya gaɗa taajan banna wala kyettaiɗo ingwandi(idan na tafi ki biyo bayana,karki damu,ba wanda zai gane tare muke)" duk da hakan yayi mata,amma kuma batason dora masa wani nauyin kuma ko dawainiyarta,saidai kafin ta sake cewa komai yayi gaba,dole ta miqe,ta dauki malfajenta ta mayar saman kanta,ta dauki jakarta ta daura tabi bayansa.
Bata sani ba ko shima ya kula,sharewa kawai yayi,ko kuma bai kula din ba.....da gaske ita daya ta lura,yadda mutane keta binsa da kallo a sanda aka ganshi yana kora shanun da ita ke da hakkin kula dasu,yayin da ita kums ke biye dasu a baya,kasan samun nutsuwa tayi kwata kwata,jinta take a daure,har sai da suka isa gida,ya miqa mata sandanta idanuwansa akanta,fuskarsa dauke da murmushi
"Sai jaaango?" Ya fada yana sake nazartar kyakkyawan fuskarta
"Miyatti" ta amsa masa a gajarce,sai ya jinjina kansa
"Alla ɗaudane jamu(Allah ya qara lafiya)kisha magungunanki da kyau"
"to Allah jaɓe" ta fada tana jin nauyin mixanin kyautatawarsa a gareta.
Ko sanda himu yake nufar gida tunaninta ne fal cikin ransa,kamar yadda murmushi yaqi barin fuska da bakinsa su huta,sosai yake ji cewa yayi gamo da Matar aure,ta kuma zo dai dai lokacin da ya kamata ace tazo din,bayajin zaiyi nauyin baki ko jinkirin shaidawa innarsa,duk da cewa babansu baya nan,amma dai yana da kyau innar ta sani,ta kuma shaidawa baban da zarar ya dawo.
Da sallama ya shiga faffadan tsakar gidan nasu,kishiyar mahaifiyarsu wadda asalin sunanta shine rahama....amma sauran dangi da 'yan rigarsu na kiranta da ramatu,su kuma yaran gidan suna kiranta da yuuma,tana duqe gaban murhu,ta kammala kwashe tuwon dare tana wanke muciyar cikin tukunyar tuwon himu ya shigo.
Fuskarta dauke da fara'a take amsa sallamar tasa,macace mai matuqar kirki haquri hagen nesa da kuma sanin ya kamata,duk da kasancewarta wadda Allah bai azurtata da haihuwar yaro ko daya ba,amma sam bata kasance mai baqin hali gabyaran mikin nata ba,mutum ce mai sauqin kai,wadda take kallonsu ibrahim tamkar ita ta haifesu,tana kulawa da kowanne daya daga cikinsu,duk da zamantowar safara'u mahaifiyar ibrahim mace mara haquri da biyema zuciyarta a wadansu lokuta,amma yuuma ta danne,suna zaman lafiyar daya sanya jama'a da dama cikin karkarar ke sha'awar zaman nasu,ba tare da sunsan cewa fiye da kashi tamanin cikin dari na zaman nasu haqurin yuuma ne ya qawatashi.
Barka da gida yayi mata ta amsa tana masa sannu da zuwa
"Inna walaɗon(inna bata nan ne?)"
"o'o immoder,one ɓayi e'ummakiɗo(A'ah tana ciki,don bata jima da tashi daga nan ba),kila barci ne ya saceta,don tacemin bata danjin dadin jikinta sosai" kai ya gyada sannan ya sake tambaya
"Yaran nan fa?,su safiya?"
"inna'onliliɓe,amma ɓeɓadake wartuki(Innar ce ta aikesu,amma suna gab da dawowa)" har ya taka zaiyi gaba sai ya sake tambayarta
"Yaushe baaba yace zai dawo ne?" Murmushi ta sake
"Yau kuma 'yan tambayar ne a kusa himu?,rana wata yau in sha Allah" kai ya gyada yana murmushi,yaji dadin jin cewa bazai jima ba zai dawo gidan,ya tafi ikko ne da wasu shanunsa zai saidasu,wanda dama.yawanci can yake kaisu,shi kansa ibarahim din yafi zama a can,mafi yawan rayuwarsa ta can ce wajen wani dan uwan baaban nasa,yanzu ma gajiya yayi da zaman can din ya dawo gida yadan huta sannan ya koma,uwa uba kuma sun samu hutun semester,don acan din bai zauna ba yana karatunsa.
Ya daga labulen dakin ya samu barcinne kuwa ya dauketa,sai ya sauke ya wuce dakinsa,yayi abinda zaiyi a ciki sannan ya fito ya fara daura alwalar magriba,bai kammala ba innar ta fito tana daura dankwalinta
"denattoi ɗa himu(yaushe ka shigo himu?)" Ta fada tana dubansa,ita din duk da bafullatsna ce amma sam ba ruwanta da wannan kunyar da kaara tadan fari
"Ban jima ba,na leqo na samu kina bacci,ya jikin naki?"
"Alhamdlh,nasha ragowar maganin nan daka taba kawomin kwanaki kafin na kwanta,kaga kuwa har ya fara sakina"
"To alhmdlh,hammiyami jula miwarta(bari nayi sallah na dawo)" ya fada yana warware hannun rigarsa,a bakin kofar shigowa gidan sukayi kacibus da qannensa,yammata masu tasowa su biyu,yace maza su shige gida an fara kiran sallah,suka amsa masa amma suna binsa da.kallo,saboda labarin da suka samu a kansa tun a hanyarsu ta isowa gida.
Bayan sallar isha'i ya shigo gidan,babu kowa tsakar gidan sai yuuma dake zaune daga bakin kofar dakinta ita daya,gabanta fitilar aci balbal ce,sai qaramar redio da bata rabo da ita saboda jin labarai,sannu da gida yayi mata,ta amsa masa tare da shaida masa abincinsa na wajen innarsa,ya amsa mata yana wucewa kai tsaye zuwa dakin innar,bayajin dadin yadda wasu lokuta safiya da zubaida ke barin yuuma ita kadai,duk da lokaci lokaci zaka samesu wajenta,yana matuqar