Showing 27001 words to 30000 words out of 33472 words

Chapter 10 - UMMI

Start ads

Unknown   

13 Aug 2025

126

Middle Ads

ta karaso wurin ta ajiye tray din akan table sanan ta kalle Sadiq tace "Bismillah, ni zan koma ciki" "thanks but ba kiyi serving dina ba" ya fada a dan shagwabe, karaf Ihsaan tace "ai ko ni zan yi serving dinka Yaya, Nana ki wuce kawai ki huta" Nana tayi murmishi tace "Noo, bari in cika lada na kawai" Ihsaan ta tabe baki. Nana ta gama serving Sadiq sanan ta koma cikin gida. Tana shigan parlor, Inna ta gani a zaune tana shan furan ta tana kallon dadin kowa. "Sannu Inna" cewar Nana "ke banason munafurci, atoh banda munafurci kin saba gaishe ni ne Iyye. Toh idan ma furar ke shige maki ido, toh ki cire tun wuri don billahilazi ba wace zan ba fura ta, koda kuwa Ummin ce da take jikata balantana ke da ban hada komai dake ba, babu dangin iya balle na uba". Ihsaan ce ta shigo ta same su, Inna na ganin ta tayi shiru ta washe baki chan tace "yar nan, ni kam ina Ummi, ni fah tunda ta shige ciki ban gan ta ba" "ai Wlh Inna dazu Yaya ya kira ta, taje ta same shi, haryanzu dai bata dawo ba" Inna ta sake baki tace "au toh haka abin ya zama, toh Allah dai ya kyauta" murmishi Ihsaan tayi ta wuce dakin su, Nana ma ta bita a baya bayan Inna ta gama bambamin ta.

9:20pm Ummi ta tashi daga bacci jin ana ja shafa mata gashin ta. A hankali ta mike tana kallon Farid tace "we slept off, what's the time"? Wayar shi yayi tapping ya nuna mata time. Zaro ido tayi tace "Na shiga uku, maiyasa ka barni nayi bacci haka, now it's late. Meye zan fada masu Ammi"? Murmishi yayi yace "sai kice you were together with your husband" hararan shi tayi ta mike tana cewa "ka maida ni plsss". Shiryawa suka yi ya maida ta gida, har bakin kofar parlor ya raka, yayi pecking dinta sanan ya juya ya nufi gate. Ummi ta bude kofar tana leka ciki, ta gan wutan parlon a kashe sanan ko ina shiru alaman kowa ya kwanta. Shiga tayi bayan ta cire takalman ta, ta rike a hannu sanan ta fara tiptoeing sabida kar aji ta. Ta kai tsakiyar parlon kenan aka kunna wutan, juyawa tayi a firgice tana kallon Nana dake kallon ta itama. Murya kasa Sosai Ummi tace "Wlh kin bani tsoro" dariya Nana tayi, ta mata alama suje sama, ta kashe wutan. Suna shigan daki Nana tace "daga kuje ki bashi abinci yaci shine kuka fita kika dade ko sis" ta karasa maganar tana turo baki, Ummi tace "ai nima abincin ce" ta kashe mata ido ta fara kokarin cire hijabi.... Nana kuwa ta sake baki tana kallon Ummi, "Heyysss why are you staring at me like that"? Cewar Ummi, Nana tace "ah ah sis ai kin fi karfi na" dariya suka yi, Ummi ta tambaye ta ya suka kare da Sadiq, Nana tace mata ta bashi abincin daga nan ta koma cikin gida. Sake baki Ummi tayi tana kallon ta kafin tace "amman Wlh ke dai sai a slow, yanzu barin shi kika yi. He came because of you ne fah" Nana ta turo baki tace "Na fah ce miki suna tare da Ihsaan" Ummi ta harare ta, tace "And so what idan suna tare, is she not his cousin, amman Wlh you can spoil show for Africa" Nana ta kara turo baki tace "Ni fah sis ba kya so ki fahimce ni ne kawai. Kuma according to Chuchu, tace Ihsaan tana son Sadiq din and besides ba son shi nake yi ba, ni nafi son Yusuf dina" Ummi taja tsaki tace "waye kuma Yusuf, muna maganar Sadiq taya zaki kawo mana wani Dan daba cikin zance" Nana bata kula ta ba, ta kwanta akan gado tace "ni dai zan taya ki kwana yau" mikewa Ummi tayi ta tace "kya ji dashi" daga haka ta wuce shirya kwanciya, sanan ta kashe wuta suka yi addu'a suka tofa, suka kwanta.

Washegari bayan sun idar da sallahn asuba, Ummi tayi wanka ta shirya cikin turquoise blue color material gown, tayi kyau sosai, daga haka Ita da Nana suka fita daga dakin. Dakin da Inna take suka shiga dan gaishe ta, zaune suka same ta akan darduma tana ta faman gyangyadi ga charbi a hannun ta. "Inna ina kwana" Ummi ta gaishe ta, a firgice Inna ta bude ido, tace "amman ke kam Aminu ya haifa jaraba" Ummi ta tabe baki, Inna ta cigaba da cewa "kina fah ganin cewa ina addu'a, kawai ki shigo min daki gatsau babu sallama ki katse min addu'a" Ummi ta kalle Nana dake ta murmishi kasa kasa tace "Ina har sau uku mukayi sallama muka ji shiru, da muka shigo kuma gyangyadi muka ga kike yi" Inna ta fara matsar kwalla tana cewa "Wlh Aminu ya haifa jaraba, yanzu Amina bakya tsoron Allah zaki kalle ni Kice ina karya, taya zaki gan ni ina lazimi kice gyangyadi nake" Ummi da ta sake baki tana kallon Inna tace "Wlh bazan bi taki ba" daga haka ta mike ta fita daga dakin Nana na biye da Ita. Daga wurin Inna, dakin da Ammi take suka wuce don gaishe ta. Ammi na zaune kan gado tare da Aunty Turai. Sallama suka yi kafin su shiga dakin, suka gaishe su cikin ladabi Ammi ta amsa musu da fara'a itama aunty Turai haka. Daga dakin suka sauka kasa dan taya yan matan gidan hada breakfast. Bangaren aunty Shatu kuwa, bayan Ita da Sajida suka isa wurin bokan, ya ba aunty Shatu wani garin magani yace "wanan garin da kike gani nan mai karfi ne Sosai. Zaki kona shi acikin kasko, idan ya fara hayaki zaki kira sunan yarinyar da ake aikin a kanta sau uku, sai ki fada abin da kike so ya faru da ita, daga nan aikin zai isa wurin ta" daga haka suka gode mai suka fita daga zauren. Tana isa gida kuwa tayi yanda tsohon ya fada mata. Bayan ta gama ne take cewa "shegiya, ke har kin isa kiji dadi, kin tashi a gidan kudi kina auren mai kudi, gashi yana son ki, families dinshi duk suna kaunar ki, ga kuma cikin shi a jikin ki, inaaaaaa, sai dai ba ni bace A'ishatu Tanko ba"
ℹ Wlh people like Aunty Shatu suna bani mamaki. And the irony is they'll always end up being destroyed if basu nemi gafara ba. Irin su, basu san meye kaddara ba. Duba da yanda take cewa Ummi na da this and that as if ita ta ba kanta all these things. Allah ne yayi blessing dinta, but no! Idanun Aunty Shatu sun rufu da envy da rashin imani forgetting that Allah yayi blessing kowa. Bangaren da yayi blessing dinki ba nan yayi blessing dina ba. Allah dai yasa mu cika da imani, ya gyara mana kurakuren mu. Masu irin halin aunty Shatu kuma Allah ya shirya, ya ganar dasu.


✏📖

Bayan su Ummi sunyi breakfast, suka shiga dakin da Nabeelah da kawayen ta suke ganin cewa gidan ya fara cika jama'a. Kasancewa sai da dadare za'ayi Arabian night din yasa basu fara shirin sa kaya ko make-up ba sai ma hiran su da suke tayi "wai kun gan yanda take Iyayi ne da ta gan shi" cewar Zeenat, duk suka kwashe da dariya harda tafi, Ummi tace "waye ya taba mana mata a gidan Sultan" shewa suka kara yi, Zeenat tace "wai sunanta Fatima ko Meye" ta karasa maganar tana rolling eyes dinta, Nana tace "ai toh ki kwantar da hankalin ki tunda har yace miki she was his class mate a secondary school and she's not his girlfriend" haka dai suka cigaba da hirar su har aka kira sallahn Asr duk suka nufi dakunan su dan yin sallah. Ummi tazo wucewa taji muryar Inna a karamin parlon da Ammi da yan uwanta da wasu manyan mata suke tana cewa "toh in takaita maku sanda baban su Aminu ya aure Kande yar uwa ta" su Ammi suka biye mata suna bata hakuri, rolling eyes dinta Ummi tayi ta wuce dakin ta tayi sallah. Ummi na zaune akan daduma bayan ta idar da sallah tana waya da Farid Inna ta shigo rike da cup a hannun ta. "Baby, let's talk later or sai ka zo, Inna is here" daga haka suka yi sallama.Ummi tana kallon Inna tace "Innasko sannu" "a'a rike sannun ki, da kin damu dani ai da baki zage ni da safe ba, amma bazan bi ta danyen halin ki ba. Ba dan Aminu yana uban ki ba meye hadi na dake" tabe baki Ummi tayi, mika mata cup din Inna tayi tana cewa "Ungo yi maza ki shanye ki bani kopi" Ummi ta leka cup din ta yamutsa fuska tace "Meye wanan kuma"? Inna ta washe hakora tace "Maganin tsaro ne, kinsan mijin kawata Larai babban malamin addini ne a ungwar su, toh shine na bata dubu biyu nace ta gaya ma Malam Isuhu(mijin Larai) ya miki addu'an tsaro da saukan Al Qur'ani mai girma. Toh kafin mu taho habuja ta kawo min wani gari tace a zuba maki a kindirmo kisha, babu maye ko makiyi da ya isa ya maki komai" Ummi tabe baki kafin tace "ni bazan sha ba, ke ki sha ki tsare kan ki kuma ai ina addu'a" dakuwa inna tayi mata tace "kin ci mai garin ku, ce maki akayi bana addu'an ne, kuji min ja'irar yarinya. Toh gaskiya baza ki sani asaran dukiya ba, dubu biyu na bada aka maki addu'a, sanan dari uku na ba Naja dazu ta sayo maki wanan kindirmon" dariya Ummi tayi tace "dubu biyu da dari uku kike kiran dukiya Inna, ni fah bazan sha abin nan ba, idan ma so kike a baki kudin ki zan baki" sake baki Inna tayi, ta fara matsar kwalla tace "amman dai Hadiza ta haifa jaraba, ke ana nema maki sauki kin ce wahala kike so. Baki san cewa auren da kika yi wasu na iya maki bakin ciki ba" Ummi ta tabe baki ta kau da kan ta. "Haba Amintako yar jikale ta, yar gaban goshin iyayen ta" a haka dai Inna ta lallaba Ummi har ta sha kindirmon tana yamutsa fuska "ko ke fah yar Albarka" cewar Inna tana washe hakora. Bayan fitar Inna, Ummi mikewa tayi, ta linke dadumar, ta hau kan gado ba dadewa bacci ya dauketa. 5:40 pm Ummi ta tashi daga bacci, wayarta ta jawo ta duba time. Ganin time yasa ta zaro ido tana cewa "Innalalahi wanan wane irin bacci ne haka" mikewa tayi, ta shiga bayi tayi alwala sanan ta fito tayi sallah. Tana idarwa su Rayyana suka shigo dakin "Sis, kin tashi kenan" cewar Nana, "Wlh har na makara sallah, ya nagan baku fara shiri ba" Rayyana dake zaune kan ottoman ta amsa cewa "sis kin manta cewa sai bayan Isha fah za'a fara event, ina ko muka gan ta shiri yanzu" Ummi tace "oh yes, haka ne fah" Chuchu tayi murmishi tace "sis an kai abinci dakin su Nabeelah, in deba in kawo miki ne"? Shiru Ummi tayi tana tunani kafin ta tambaya mai aka dafa,Chuchu ta amsa "couscous da chicken salad aka yi" yamutsa fuska Ummi tayi, Rayyana ta tambaye ta ko lafiya, tace "ba zan ci couscous ba wlh" Chuchu tace "rufa min asiri sis, kinga tun breakfast baki kara cin komai ba, kuma da Ammi ta tambaye ni ko Kinci abinci nace mata ae, dan Allah kici koda kadan ne, ko kuma da abin da kike so kici ne"? Ummi tace "ni para nake so inci, wanda akwai yaji Sosai" Rayyana da Nana suka yi dariya kasa kasa, chuchu kuwa kaman tayi kuka tace "sis ina zaki gan para yanzu fisabillilahi, Idan kuma Ammi tasan baki ci abinci ba, toh kashi na ya bushe dan ce mata nayu kin ci" turo baki Ummi tayi, haka suka dinga draman su Ita da Chuchu, Nana da Rayyana kuma suna tayi musu dariya. Karshen ta dai Ummi ta yarda taci couscous din kadan, lokacin Nabeelah tare da Zeenat da Zulaikha da kuma Ihsaan suka shigo dakin suka baje suna ta hira. Lokacin magrib nayi, kowa ya mike domin zuwa yin sallah, bayan sun idar ne make-up artist har guda hudu suka iso gidan, aka fara yiwa wasu yan matan dake gidan, daya kuma tana yiwa amarya Nabeelah, daya kuma tana wurin su Ammi da aunty Turai zatayi musu, sai kuma daya da take yiwa Rayyana. Lokacin sallahn Isha nayi, Ummi ta wuce dakin ta tayi wanka da alwala sanan tayi sallah. Tana idarwa, ta fito da lafayar da zata saka sanan ta fito da designers din takalmi da jaka na company Zara, wucewa tayi wurin dressing mirror, ta shafa face cream dinta na Oriflame Sweden, sanan ta fesa turaruka masu sanyin kamshi ta fita daga dakin ta wuce nasu Ammi. Ammi dake zaune ana yi mata make-up bayan an gama wa aunty Turai na ganin ta tayi murmishi tace "daughter ina kika shiga tun safe, kin ci abinci kuwa" Ummi tayi murmishi ta gaida Ammi da aunty Turai sanan ta amsa mata cewa taci abinci. Aunty Turai tace "toh, daughter ya na gan fuskar taki babu kwalliya" "daman nayi sallah ne, kuma ana yi ma su Rayyana idan an gama nasu, sai a min" daga nan Ammi da aunty Turai suka dinga jan ta da hira dan sun lura kunyar su take ji Sosai. Bayan kaman 30 minutes Ummi ta mike tace musu zata je ayi mata make-up, amsa mata suka yi suna yaba hankalin yarinyar a zuciyar su. Ummi tazo wucewa ta parlor ta gan Inna a zaune tare da wasu tsoffafi sun cika parlon da muryar su suna hira, Inna ta sha ado cikin riga da zani na embellish din atampar Vlisco, ga madaidaitun gold earrings dinta a kunne. Ganin Ummi tazo wucewa, Inna ta kalle daya daga cikin tsoffafin da suma sun sha ado cikin shigar alfarma, tace "toh Kinga wancan da zata shiga dakin chan, toh Ita ce jika ta, matar Faridu" duk suka ce Masha Allah, Ummi dake jin su, ta gaishe su sanan ta shiga dakin lokacin an gama yiwa Nabeelah da Rayyana make-up. Tana shiga, babu bata lokaci make-up artist din Nabeelah ce tayi mata,within 40minutes ana gamawa, cikin hanzari Ummi ta wuce daki ta saka kaya dan har mutane sun fara barin gidan zuwa event center. Daya daga cikin make-up artists din ne ta taya Ummi daura lafayar ta milk color, bayan ta saka wani dark blue body con aciki, sanan aka daura mata turban mai kyau Sosai, ta saka takalmin half covered mai tsayi sosai ta dau jakar ta sanan ta fesa bakhoor dinta da wasu turaruka masu sanyin kamshi... ba karamin kyau tayi ba. Wayar ta dauka ta kira Farid ta sanar mai ta shirya yace yana hanya, daga nan ta wuce dakin su Nabeelah, nan fah taga yan matan sun sha kwalliya, sun saka Abaya, Rayyana, chuchu, Nana da Ihsaan ne kadai suka yi ankon lafaya, duk sunyi kyau Sosai. Fita suka yi daga dakin suka sauka zuwa main parlor dake cike da mata tsofaffi da budurwaye masu jira a zo a kai su event center. Sake baki Inna tayi ganin irin kyan da Ummi tayi, tace "amman dai ina ganin bariki ni Yakwalo. Amina kiji tsoron Allah kiji tausayin abin dake cikin ki. Yanzu wannan uban takalmi mai shegen tsini kaman an feke pensir( pencil) kika saka gaki da tsohon ciki" kallon cikin ta da bama Za'a san akwai shi ba Ummi tayi ta turo baki, ta samu wuri ta zauna bata kula Inna ba, mutanen dake parlon kuwa dariya suka dinga yi, inda wasu yan mata kuma suna mamakin ashe Ummi matar aure ce harda ciki. Ihsaan, Zeenat da Zulaikha da wasu yan mata suka bi Sadiq kansancewa ya iso kafin Farid, ya rage Rayyana, Chuchu, Nana da Ummi wanda Farid zai kai, sai Inna da zata bi su Ammi da Aunty Turai sanan kuma wasu yan mata da kawayen amarya. Shigowa parlon Farid yayi da sallama sai kallo ya koma kan shi, yana sanye cikin dressing irin na larabawa tsak, ba karamin kyau Farid yayi ba kaman ka sace shi, kishi ne ya zo ma Ummi ganin yan matan parlon sai kallon shi suke yi, they can't just take their eyes off him. Karasawa yayi ya gaida Inna da ladabi, Inna tace "Faridu yanzu nake wa matar ka magana akan wanan dan iskan takalmi da ta saka sai kace an feke pensir, toh ni dai babu ruwa na" murmishi Farid yayi, ya kalla Ummi dake ta turo baki, Wowww! He couldn't just take his eyes off her, she looks so chic and cute, a ranshi yace "damn, that's my gurl". Rayyana ce ta dan yi gyaran murya ganin cewa idan ba'a yi hankali ba za'ayi abin kunya. Hararan ta Farid yayi ya mike yana sosa keya ya kalle Ummi yace "muje ko" mikewa Ummi dasu Rayyana suka yi sanan ya kalle Inna yace "muje Inna, motar da zai kai ku ya iso" mikewa Inna tayi tana salati tace "wa innahu min sulaimanu, halale mu bazama" kallon Rayyana yayi yace "shiga ki ce wa su Ammi motar su ya iso" daga haka shi da su Ummi suka fita. Lokacin da suka isa hall din Sheraton hotel, a cike yake tam da mutane. Hall yayi kyau Sosai ga haske ta ko ina, sai kamshin turaren wuta dake tashi ga kowa ya sha ado cikin kaya ta alfarma. Table din dasu Rayyana da wasu kawayen amarya suke Ummi ta zauna while Farid yaje inda su Sadiq da wasu abokan ango suke. Inna kuwa tana zaune a table daya da Ammi, aunty Turai sai wasu manyan mata. An danyi huduba da wasu games and other activities kafin aka fara raba abinci irin su( Mandi rice, Biryani rice, Arabian tea, Ram barbeque, Kheer, warm milk da sauran arabian dishes) kallon mandi rice dake gaban ta Inna tayi tace "amman wane irin shinkafa ne haka duk a tsatsaye kaman nonuwan maza" dariya su Ammi suka yi

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login