Showing 6001 words to 9000 words out of 33472 words
yau 2 weeks da Ummi ta dawo gida, sauka Ummi tayi ta tarar da Nana tana ta zagin Samirah, Ummi ta karasa wurin su tace "lafiya dai, ya haka ne" Nana tace "kiji min yar rainin hankalin nan, cewa nayi bazan ci wainan da tayi ba, ni ta soya min samosa kuma ta hada min tea, shine take gaya min maganar banza wai tana aiki yanzu baza ta iya ba" Ummi da ta gama ji ta zauna kan kujeran dining, ko kallon Nana bata yi ba balle ta bata amsa, sai tace wa samirah "Dan Allah ni ki kawo min waina in ci pls, ki kawo min da fruits" cikin sanyin murya Samirah ta amsa mata. Nana ta sake baki tana kallon Ummi wato ta mayar da Ita banza. Ummi ko sai aikin danna sabon iPhone 13 dinta take yi. Piiiii Nana ta wuce wurin Shatu ta fada mata komai, Shatu tace "ai wannan Ummin tana da nata bakin halin amman kar ki damu zanyi maganin ta" daga hakan ta sauka kasa ta bar Nana a dakin. Kitchen ta wuce tana hararan Ummi bata ma san tana yi ba. Samirah na ganin Shatu tasan cewa akwai problem "ke dan kaniyan ki, Watto ke kin isa da har yar gida zata Saki abu ki kiyi" Samirah cike da raini tace" wace yar gida kuma dai, banda aunty Ummin akwai wata yar gidan ne kuma aunty"? Shatu kaman zata fashe "ke ni zaki gaya wa bakan magana, amman Wlh anyi yar Shegiya munafuka" "ni dai ba yar Shegiya bace, tunda uwata na da uba kuma ya na nan da ransa" cikin fishi Shatu ta fita daga kitchen din ta Nufi wurin Ummi tana masifa "ke kuma kina ji kina gani wata bare mai aiki tana raina yar uwarki amman baki dau mataki ba" Ummi ta kalle Shatu for like 8 seconds Sanan tace "aunty ni dai ban ga dalilin da zai sa ku tada jijiyar wuya ba. Ai nasan dai Samirah baza tayi mata hakan babu dalili ba" "toh kaniyan ki nace, dage ke har Samiran" daga hakan ta wuce piiii. Ummi dakin ta ta wuce don ta shirya zuwa school bayan ta kamalla breakfast. Tun da aka sace ta, yau ne zata koma school. Wanka tayi, tayi sallah tayi yan shafe shafen ta Sanan ta Nufi wurin wardrobe dinta ta bude ta fito da wata ash Abaya mai kyau, ta saka bakin takalmi da jaka ta saka shade dinta ta fita daga dakin taje wurin mummy dan tayi mata sallama. "Oh harkin shirya zaki wuce" "eh mummy" mummy tace "toh dauka car key dinki daga wancan locker din ki mika wa Zakariya, daga yau he's your guard kuma shi zai dinga kai ki school" "toh mummy, amman why would you get me a bodyguard, I don't like it, I want to be comfortable ba sai kowa ya san cewa I come from a rich home ba" "Look Ummi I understand amman it's not safe for you to start going out alone after what happened, kuma daddyn ki ne yace, ki dinga fita da guard" "toh mummy, I get it, thank you Allah ya bar min ku" cewar Ummi, mummy ta amsa da "Allah ya tsare, a kula da kyau pls" Ummi tace "okay mummy" daga nan ta fita.
A school, Zakariya na ta bin Ummi duk inda zata and this was making her feel uncomfortable, daka gan shi kasan he's a bodyguard, yasaka black suit da black glass fuskan shi ba rahama. Sai kallon Ummi akeyi wasu na cewa ai Spoilt brat ce, wasu kuma na gulman cewa anyi kidnapping dinta, Ita Ummi ko kallo basu isheta. Ta shiga class still Zakariya na biye da Ita, ganin su Iftihal yasa ta nufe sits din da suke suka gaisa Zahra da Iftihal kaman su hadiye Ummi tsaban dadi. Iftihal ta daga kai taga zankalelen dake gefen ta, muryar kasa kasa tace "Ummi shi wannan kuma fah" Ummi tace "Wlh mummy ta hada ni dashi wai he's my bodyguard and driver" Zahra tace "ai hakan yayi gaskiya, mummy ta kyauta". Suna hira Ummi tayi shiru ganin cewa daddy na kiran ta, Sannan ta daga "Assalamu Alaikum, daddy ina yini" "wa'alaikum salaam my dear, hope you're doing fine" Ummi tace "Alhamdullilah, wai daddy har yanzu ba ka samu hutun bane, yaushe zaka zo" "Ummita kenan karki damu yar daddy very soon zaku gan ni. Dazu nayi magana da mum dinki and she said you went to school, komai dai dai ko"? Ummi tace "yes daddy, amman maiyasa ka hadani da guard, ana magana na kuma ana kallo na, I'm really uncomfortable" Daddy yayi dariya yace "yar daddy you'll get used to it Kinji, it's for your own safety" Bayan sun gama maganganu su, su kayi sallama. After first period, sun fita waje Zahra cike da tsokana tace" gobe ne fah event din, gashi baki da date" ummi ta turo baki bata ce komai ba, "wai baku shirya da Farid din bane" Inji Iftihal "mun shirya, har muna chat ma" suna magana, sai wani guy rike da rose flower yazo ya mika wa Ummi ya wuce ba tare da yace mata komai ba, sai wani ma yazo still with another flower ya danka mata ya wuce, haka again and again and again sun kai 7. Ummi ta zama abin kallo, ga hannun ta cike da beautiful roses pink and red. Tana cikin raba idanuwan ta, kawai sai ga Farid ya bilo rike da babban rose, Woahhhhh, yasaka designer English wear da shegen shade, yayi kyau, mata sai crushing suke suna kalon shi har ya nufe wurin da ummi take tsaye, ya cire shade din yana kallonta Yayi kneeling a gaban ta yaUmmiUmmi will you be my date"? Kunya kaman zai kashe ummi tace "yes I'll" tana juya mai ido ta amsa rose din. Yellow kuwa da take kallon komai, kaman zata fashe. Su Ummi da Farid kuwa fita suka yi daga department din Zakariya na biye dasu a baya, sai kallon su akeyi. School recreational center dinsu suka je, dukansu suka samu wurin zama. Iftihal da Zahrah suna hotuna a snap, Ummi kuma na zaune da Farid. Zakariya kuwa na tsaye kaman statue a bayan Ummi. Murya kasa kasa yace "Favorite, welcome, it's good to have you back" Ummi ta kaleshi kawai tayi nodding kanta, yace "Menene naga kaman you're not comfortable" tace "how will I be comfortable, kawai ka shigo cikin bainan nasi kazo kayi kneeling down as if you were proposing, gashi na lura a gaban psycho din can akayi komai, salon ta zo ta kara zagi na a kanka, ai ko Wlh this time around I won't take it likely with her if she tries such" murmishi kawai yayi dan maganan ta ya bashi dariya, cikin tsokana yace "Fisabillilahi mai tayi miki, mai yasa kike kiran ta psychopath, she's not mad and bakisan cewa she's my friend ba a close one for that matter, so kina hurting feelings dina idan kika zage ta" last kalmar shi ne ya bata haushi wai tana hurting feelings dinshi, to hell with his feelings ta hada rai taja tsaki tayi shiru. Shigowan yellow kenan cikin recreational center din Ita da friends dinta ta hango Farid da Ummi, ta nufe wurin su tana kirkiro murmishi. Tana zuwa wurin su ta tsaya kaman pole wire tana rangwada tana kalon Farid wanda shima ke mata kallon irin are you alright. Ummi ta daga kai ta mata kallon tara saura ta cigaba da dana wayarta sai yellow ta kalle ummi tace "ke kuma ya da kallo haka dai, ko kanki na hau na tsaya ne mallama" daga haka ta ja tsaki tana hayaniya tana spark, ummi tace ma Zakariya "fita da mahaukaciyar nan out of here, kaina na ciwo" ba wasting time ya janye yellow, daman ba nauyi gareta ba, su Iftihal kuwa suka yi streaks da yellow ana jan ta, Farid ko sai bin su da kallo kawai ya keyi ya girgiza kai irin Sai da tasa akayi embarrassing dinta. Mikewa Ummi tayi tana kallon Farid tace "I guess i hurt your feelings again right" daga haka ta wuce suka fita daga recreational centre din suka koma class. Ana ta gulman abin da tasa akayi yi wa yellow, suna shiga suka tarar da yellow na kuka friends dinta na bata hakuri, daya daga cikin friends din yellow tace "Kema gaskiya yellow akwai karambani, kina ji kina gani yarinyan can tafi ki kusan a kowanne bangare amma still kina shigan sabgar ta bayan ba Ita ta fara miki abu ba. Kina gani dai duk kudin Ummi bata isa ta nuna ma Farid kudi ba amman a hakan dai da kyar ya shawo kanta har suka fara abokantaka. Yellow abin da zan gaya maki shine ki cire Farid daga ranki, don naga akan shi kike wannan haukan, Farid ba class dinki bane Wlh kuma ba sonki yake yi ba, he's just being nice to you amman it doesn't mean he's in love with you. In ba abinki ba ina ke ina competing da yarinyar can, yarinya da ko kayan jikin ta kadai zai iya biya miki school fees dinki na gaba dayan semester nan. Ke ko mai kike dashi, dan Allah ki fita daga sabgar su, they're not your class kiyi hakuri Allah zai kawo wanda ya dace dake" yellow ko sai shakan kuka takeyi suka cigaba da bata hakuri.
Su aunty Shatu kuwa da yar ta sun baje kolin su, sai zuba mulki da iko su keyi kaman gidan uban su. Shigowan Ummi kenan daga school, ta tarar da aunty shatu da Nana suna kallon TV, Ummi tayi musu sallama da gaisuwa amman basu amsa ba. ko a jikin ta, ta hau sama taje dakin mummy, ganin cewa bata dawo daga office ba, ta fita ta je dakin ta, ta shiga bandaki ta yi wanka da alwala Sannan ta fito tayi sallah bayan tasa wata simple kayan gida. Ta sauka kasa, ko kallon su aunty Shatu bata yi ba taje dining tana kiran samirah. "Samirah meye kika dafa yau" "aunty paten doya nayi don shi mummy tace a dafa, nasan ba kya ci amman ban daura abincin ki a wuta ba don mummy tace in bari sai kin dawo sai ki fada abin da kikeso" Inji samirah, ummi tace "Kar ki damu ba sai kin dafa min komai ba, kije ki huta" cike da damuwa samirah tace "toh mai zaki ci, ai ba zai yu ki kwanta haka ba" ummi tayi murmishi tace "no don't worry, Zanyi ordering abinci yanzuvkawai ki kawo min fruits amman Kar kisa pineapple pls" Samirah ta amsa mata daga hakan ta juya. Su aunty shatu kuwa da suke jin komai sai mamaki suke yi ace wai bata cin paten doya, Lalai Hadiza ta bata yar ta. Suna nan zaune a parlor har mummy ta dawo daga office, Ummi ta mike da gudu taje tayi hugging dinta, mummy ta gaisa da su aunty Shatu Sannan Ita da ummi suka hau sama Ummi na rike da handbag dinta. Bayan sun shiga daki, mummy tayi wasu ayyukan ta. Ummi ta turo baki tana kallon mummy da ke Danna wayarta "ke lafiya kin kura mini ido haka" Inji mummy "toh mummy wai yaushe zasu tafi, sun fah dade, Ita aunty Shatu baza ta koma gidan mijin ta bane. Tun da su ka zo suke wulakanta mana ma'aikata all they do is sleep, eat and cause trouble all the time. Ni shiyasa ma bana shigan sabgar su" mummy tace "ranan nayi mata magana, amma gani take Kaman koran ta nake yi" ummi tace "toh mummy sai meye wannan damuwanta ne ba naki ba" mummy tace "ya isa toh, tashi ki bani waje" Ummi ta fita tana tabe baki. Washe gari, kasancewar ranan event din kenan, Ummi tayi wanka bayan tayi sallahn asuba sanan ta koma kan gado ta Kwanta. Wuraren 8:30 na safe ta sauka don tayi breakfast, tana gama breakfast ta kira makeup artist dinta. Around 10:00 makeup artist din tazo ta fara shirya Ummi, ana cikin yi mata makeup, sai ga kiran Iftihal ya shigo wayan Ummi "Hello babes kin shirya n " Ummi tace "ana yimin makeup ne yanzu, an kusan gamawa" "okay toh, gani nan bada dadewa ba zan shigo layin ku, Zahra ma tace yanzu ta fito daga gida" Ummi tace "toh sai Kun zo" daga haka ta katse wayar ta. An gama yiwa Ummi makeup dinta, very light makeup akayi mata but tayi kyau sosai, sai manyan idanuwanta da small lips dinta suka fito. Ummi ta nufe wurin wardrobe dinta ta fito da gown din event din wani off white, Kaiiiii kayan ya hadu sosai gashi kayan ya kamata chass, ta saka wata black half shoe mai shegen tsini da tsada, ta rike purse dinta Shima black wanda tare yake da takalmin. Makeup artist din ta daura wa ummi dankwalin ta kuma yayi kyau. Ummi ta hadu Sosai. Bayan ta gama pesa turarukan ta masu tsada ta sauka kasa bayan ta sallame makeup artist din. Ummi ta tarar da Nana wace take ta bin ta da kallo tun da take saukowa. "Toh Ummi ina zuwa haka kamar wata Amarya" Ummi ta danyi murmishi tace "muna da event a school yau ne, ina aunty" Nana tace "au, toh Allah ya tsare, umma ta fita ai" ummi tace "oh okay, bari in jira friends dina" daga nan ta zauna a parlon, Ita kuwa Nana sai kallon Ummi take kamar mayya. Suna zaune suka ji anyi sallama, Iftihal da Zahrah suka shigo tare, suma sunyi kyau, ko wace outfit dinta ya hadu, haka Nana ta dinga kallon su har suka fita daga parlon bayan sunyi mata sallama. "toh yanzu ya za'ayi, kowa ya tafi da motarsa ne ko kuma mu tafi tare a mota daya, idan yaso in mun dawo kowa ya dauke motarsa" Inji ummi, sai su Zahra suka amince Wai su tafi a mota daya. Ummi ta nufe wurin Zakariya da already yana jiran su, ta mika mai makulin wata baban mota hadadiya tace "da wanan zamu je yau" yace "okay ma'am" daga hakan, kowa ya shiga mota suka fita. Tun suna cikin mota Farid ya kira ta wai yana waje yana jiran ta, ta sanar mai ta shigo already. Dukan suka sauka lokaci daya daga motan, date dinsu na jiran su. Kowace taje ta samu date dinta, Farid na ganin Ummi, yayi saki dan murmishi ya fara walking towards her. "Wowww" ya fada yana zare Idanu, sai ya kara cewa "favorite kinyi kyau Sosai, kamar wata angel" hararan shi tayi tana murmishi tace "thank you fav ,kaima kayi kyau and I like your tuxedo" murmishi yayi yace "thanks, can we go in now" ya fada yana mika mata hannu suka shiga, sai baza kamshi suke yi. Zo ku gan yanda jama'a ke kallon Ummi da friends dinta with their dates, wasu sun saki baki suna kallo, wasu kuma suna ta hyping dinsu, wasu kuma suna tayi musu video. Wlh ko kai makiyyin su Ummi ne, sai sun burge ka Wlh. Kujerun da Farid yayi reserving ma dukan su, suka je suka zauna. Event kam yayi kyau, around 7 suka koma gida, daga nan su Iftihal suka wuce.
Ummi ce zaune a parlor tare da aunty shatu da Nana. Sallama akayi duk suka kalle Kofan, Inna ce ta shigo tana kalle kalle. Ummi ta mike da sauri da nufin runguman ta, Inna ta daga mata hanu tace "ke banson shiririta, inda kinyi kewata da gaske ai da zaki dinga zuwa ko" Ummi ta turo baki tace" Inna fah makaranta nake Kema kinsan ba sauki, Inna kawo jakan ki" Inna ta tsuke fuska ta danka mata jakan ta, tana kallon su aunty Shatu wanda suke mata kallon banza. Inna ta karasa cikin parlor Ummi na biye da Ita ta zauna tace "su kuma waye wa'enan gajiyayun babu sannu balle ya hanya" Ummi ta zaro ido tace "Inna yar uwar mummy ce fah da yarinyar ta" Inna tace "au toh taya zan sani, tunda sun tsaya kallon mutane kaman ba yan halak ba" Ummi ta kalle su aunty shatu tace "aunty, Nana kun gane inna kuwa, mahaifyar daddy" suka gaida Inna sama sama, Inna ko kula su ma batayi ba tace "ke ina maman ki" Ummi tace "ta fita zuwa gidan rasuwa" Inna tace "au toh shikenan" Ummi tayi shiru chan tace "Inna bari a kawo maki abinci" daga nan ta mike ta shiga kitchen. Inna ta ci abinci tayi nak har ta fara gyangyadi, mummy ce ta shigo cikin parlon da sallama ta nufi wurin Inna da sauri ta gaishe ta da ladabi Inna tace "tashi ki zauna yar albarka" chan Inna tace "na shigo na hadu da wasu rudadu suna ma mutane kallon uku kwabo, amman Ummi tace wai yar uwarki ce tare da yar ta" mummy tayi murmishi tace "eh Inna, Ita yar kanwan mamanmu ce Inna" tace "au toh, ni dai yanzu Yaushe Aminun zai dawo daga legas din ne, ace mutum ya kai wata biyar bai dawo ya duba iyalin shi ba, ai hakan bai dace ba Hadiza" mummy tace "Inna ai muna waya, Kema kinsan yanayin aikin shi, amman yace ba da dadewa zai dawo" daga hakan suka cigaba da wasu hirar su har magrib. Mikewa mummy tayi tace "Inna zo muje in kai ki daki" Inna ta tsuke fuska tace "sai kace wata tsohuwar banza, in ba ke ba ina ni ina kwana a gidan yara" mummy tayi dariya Sosai tace "toh, Inna ai dare yayi, bai kamata ki tasa kanki a hanya ki tafi ba, sannan ma meye aciki idan kin kwana a nan din ma" da kyar Inna ta yarda ta kwana.
✏📖
A kwana a tashi, Ummi da Farid sun fara Soyyaya har an kai ga maganan aure tsakanin su har. Farid tuni ya gama school dinshi harda service, kuma ya samu aiki a CBN sanan kuma yana running family business dinsu. Kasancewa lokacin da ya hadu da Ummi, shi final year chattered accounting student ne while ummi kuma tana 200lvl. Inna tazo gidansu Ummi ranan, ta shigo babban parlor kenan