Showing 3001 words to 6000 words out of 33472 words
salaman. Tace "daman na kira ne in gode maka" yace "oh never mind at all" tace "okay, sai da safe" yace "wait, shikenan kawai" ta turo baki tace "da abin da kasani inyi maka ne" yace "A'a madam rigima, sai da safe" ya katse wayar, ta dan yi murmishi kafin ta gyaran pillow ta kashe wuta tayi bacci
✏📖
A kwana a tashi ba wahala, Farid da Ummi sun shaku sosai, sun zama cool besties. Sun shaku to the extent tasan kusan duk sirin Farid sabida yayi trusting dinta as his friend and kuma yayi developing feelings for her. Yau dai yazo ya kaita lunch a one of the best and most expensive restaurant in town, so yana jiran ta acikin mota. Fitowa tayi cikin wata silky purple and white floral material wanda aka dinka mata flay gown mai ajihu da crossed neck, ta dauka wani karamin jaka white wanda it can only contain her phone and ATM aciki, tayi crossing dinshi, ta dauka flat half shoe shima white tasaka, tayi rolling white jersey scarf dinta sanan ta daura beach hat dinta mai Uban fadi akai. Kallon ta yayi ya dan lumshe idanun shi kafin ya bude su. Ta bude motan ta shiga tare da cewa "Hey favorite, Inji dai baka dade ba" yace "nope, anything for my favorite" ta dan yi murmishi suna hira har suka kai, shiga suka yi, aka kawo musu menu kafin suyi placing order dinsu. Bayan sunyi having lunch dinsu, suna hanyan komawa tace "favorite, event din da za'ayi , kana da date dinka"? sai yace "yes ina da date" tace "wacece Ita din" yace "yellow" ta hada rai taja wata Uban tsaki tayi shiru tana kallon waje ta glass din gefe. Murmishi yadan yi kadan, Watto tana kishi kenan. Basu kara ma juna magana ba har ya ajiye ta a gaban gidansu, zata bude ta fita ya kara locking, sai yace "Menene, are you jealous" hararan shi tayu ta kara jan tsaki tace "yo ko kaine autan maza, bazan yi kishi da wanan psychopath din da kake yawo da Ita ba.Ni dai bude min in fita" ya dan kalleta yayi shiru sai ya bude....fita tayi daga motan kaman ana yaki. Compound dinsu ta shiga, tagan baba Salisu tace "Baba ina wuni" baba yace "sannu da zuwa Hajiya karama" karasawa tayi cikin gida, a ran baba yace "oh Kaga yarinya mai kirki, duk kudin su ba girman kai". Tana shiga parlor din ta Nufi dakin mummy, ganin cewa mummy bata nan ta shiga dakin ta ta Kwanta. Sai ta tuna abin da ya fada mata dazu a mota, ta kara jan tsaki, a hankali tace "ba yellow ba saura black, rubbish"
Bayan sunyi fada basu kara magana ba kuma yau kwana hudu. Washe gari, Ita da mummy sun gama cin breakfast suna hira suka ji anyi sallama. Zahra da Iftihal suka shigo suka je wurin mummy "ah ah yau dai gaku kun zo, ya kuke, ya gida, ya karatu da iyayen ku" mummy ta tambaye su, suka amsa mata cikin ladabi "toh sannu da zuwa, bari akawo muku abinci ko snacks" suka ce "a'a mummy mun gode ki bari tukunan" mummy ta mike ta bar su ta wuce sama tana hirar ta a waya. Ummi kuwa Tahi dadin ganin su, sai hira suke zubawa "toh Ummi yanzu waye date dinki " Inji Zahra, ta turo baki tace "Uhmm, ni dai banida dan Allah kar ku ishe ni da batun wani date, yanzu dai ku tashi mu hau sama in shirya mu tafi boutique neman kayan event din" Iftihal tace "ke ko Ummi event din nan kowa da saurayin shi zai je, ke ko da uban wa zaki oho" Ummi tace "hmm nima fah saurayin nan ba rasa shi nayi ba, ehe" daga hakan duk suka mike suka hau sama, suna ta hiran su a daki, Ummi kuma tana shirin su fita.Ta gama shiri cikin wata red Abaya mai shegen tsada,ta saka shade, ta rataya wata white Chanel bag da kuma half shoe mai da tsini Shima fari... Kaiiiii bawa wa ne matan president. Su Iftihal ma wasu tsadadun atampa suka sa kuma suka kashe dauri, kwa ce matan shugaban kasa ne su, daga nan suka yi wa mummy sallama suka fita. Dukan su suka shiga motan Iftihal suka kama hanya. Suna kai boutique din, Iftihal tayi parking, kowa ya sakko daga motar suka Nufi entrance din, maza da mata kallon su ake tayi irin ga yaran barayin kasan nan😹💯 shiga suka yi suka fara duba kayan.
✏📖
Wani mutum ne a tsaye ya saka bakin kaya kuma yasa glass ba'a iya ganin idanuwan shi, yana waya. A dayan bangaren wani mutum yake cewa "Mark ya ake ciki" "Boss yanzu nan yan matan suka shiga ciki" "toh you should do as I have said, just the girl and make no mistakes"! Ya kashe wayar. Mark ya shiga cikin shagon, yana ta raba ido ta cikin glass din sai ya hango su Ummi. Ya rabe wani lungu, ya fito da tear gas...Haba kafin ka sani wuri ya rikice ana ta hayaniya ana kokarin fita. Mutumin ya je inda su ummi suke suna ta fama suna ta tari, mutumin ya chapke Ummi ya fita da Ita yasa ta a motan shi yayi zooming off. Su Zahra kuwa sai ihu sukeyi suna fama har suka samu suka fita. Hankali ya tashi da suka gan ba Ummi, suna ta kuka,suka shiga mota don su koma su je su gayawa mommy abin da ake ciki. Ummi kuwa tari ta dinga yi har ta zama unconscious. Tashi tayi tagan kanta acikin wani daki mai duhu Ita kadai, taji jikin ta yayi mata nauyi dan an daure hanayen ta da kuma kafafuwan ta, sai dishi dishi take gani. Kwalla ihu tayi tana kuka."Innalalahi wa'ina ilaihi raji'un, na shiga uku, ina aka kaimin yarinya, wayooo zuciya ta" cewar mummy dake zaune a kasa tana zuba kuka, su Iftihal ma haka, duk sunyi butu butu tsaban tashin hankali. Sun sha kukan su har sun gode wa Allah. Bayan su Iftihal sun tafi, mummy daukan wayarta tayi tana dialing wata number, daga wayan akayi da sallama, mummy tana kuka aka ce "Hadiza lafiya, mai ya faru, why are you crying"? Mummy tace "Alhaji my daughter" Kasa karasa maganan tayi tana kuka, Alhaji cikin tashin hankali yace "mai ya faru da Ummi, ina take"? Mummy ta kwashe komai ta fada wa. Alhaji yace "they're targeting my family, they're messing with the wrong ones" "who are they Alhaji" yace "don't worry, yanzu zan sa a karo maki securities, sanan ki kira wata yar uwar ki ta zo ta zauna da ke, Kar kije ko ina tukunan sai abubuwa sun laffa, Kinji ko" tace "toh, aman mai ke faruwa ne"? yace "ki Kwantar da hankalin ki, I'll take Care of everything, Ummi zata dawo gida" daga nan suka yi sallama.
Bude kofan akayi tagan wasu katai sun kai goma kuma sun saka mask, gaban ta faduwa ya dinga yi, a ranta ta sai addu'a take yi. Bayan su wani mutum fari mai uban kyau da ba zai wuce 46 years ba, yana sanye da suit mai tsada, ya saka glass, sanan ya rike wata sanda a hannu shi. Daga gani shi ne boss din. Tsayawa yayi agaban ta, sauran mazan suna tsaye a bayan shi. Ummi ta dago kanta tace "waye kai" fuskar shi a hade yace " Ke yarinya don't question me" with full confidence tace" I'll question you tinda nasan banda wata alaka da ku" daya daga cikin matasan yace" ke dan ubanki, boss din kike ma magana haka " cike da raini ta mayar mishi da magana tace" uba na dai ya fi uban ka, kuma anyi ma boss din naka maganar banza, ai ba shine Allah ba" boss ya daka mata tsawa yace" Yarinya naga kina da taurin kai, toh walahi idan baki natsu ba sai na sauke miki aljannun dake kanki" cikin kuka tace " ni meye nayi muku ni ban san ku ba" yace "bake ki kayi mana laifi ba, baban ki yayi mana"
Kansancewa baban Ummi mai suna Alhaji Aminu babba ne Sosai a EFCC inda yake aiki. He's a very strict man kuma baya cuta baya cutarwa. Wanda yayi kidnapping Ummi kuma wani babba ne acikin gwamnati mai suna Alhaji Muhammad Tahir wanda ya sace kudi over 600 billion Naira. Kansancewa Alhaji Aminu yana ta tracing dinshi for a long time ya samu yayi freezing accounts din Alhaji Muhammad kuma ya kwace most of his properties and businesses, kuma yana kokarin kama shi.
Alhaji Muhammad yace wa Ummi "Baban ki yana da abubuwa na a hanun shi, that's why nima na dauka something that's precious to him" tana hararan shi tace "Allah ya wadar, amman anyi tsohon banza,ace tsoho da kai amman bakada tsoron Allah" yace "Ke ban kawo ki nan kiyi min nasiha ba" cike da karfin hali tace "ai nasiha ya zama dole kam da irin wannan hali, ba ko tausayin yarinya kamar ni balle babba, tuuur Allah dai ya wadar gaskiya kai ta istighifari dan...." "ke! One more word from you, I swear to God I'll blow your brains out" Inji wani dan matàshi. Shiru tayi tana kallon su, hawaye na sauko wa daga idanuwanta ba dama tayi magana salon su harbe ta.
ℹNiko nace dole ummi tayi karfin hali, ganin EFCC ne suka daure mata baya
Gaban gate wata mata da yar buduruwa suna magana da daya daga cikin sabon securities din gidan su Ummi. "Kai ni fah ban son rainin wayo, Ita Hadizan bata gaya maka zan zo bane" yace "bata gaya mana ba, ki kira ta a waya ki sanar da Ita" ta bishi da harara, ta fito da waya tana dialing number. " Hadiza kina jina, wai wannan gajiyayen security naki ya hanani shigowa" mummy tace" yi hakuri shatu, bashi wayan" shatu ta mika masa wayar" Hajiya" " Ka barsu su shigo, she's my cousin and she's together with her daughter " "okay ma'am" yace, ya mika mata wayar ya bude koran. Shatu tace "dan iska sai kayi da na sanin yimin wulakanci a gidan yar uwata, Nana zo muje" ta wuce piiiii kaman zata tashi sama. Cikin parlor Shatu da mummy suna magana "Shatu Wlh ina cikin wata irin hali" shatu tace "Kar ki damu" bayan sun gama maganganun su mummy ta kai shatu dakin da zata dinga zama, dakin yayi mugun haduwa gashi girma. Daga nan ma Nana ta je dakin da aka bata. Zasu dinga zama da mummy domin rage mata damuwa. Nana ce ta sauko ta nufi kitchen ganin samirah na wanke plates tace" ke" samirah bata juyo ba balle ta amsa, cikin tsawa tace" wai ba da ke nakeyi ba kika manna min hauka ko dai kina shaye shaye ne" samirah ta juyo tace" au, ai bansan dani kike ba" Jan tsaki tayi tace "ki hada min tea yaji madara sosai, ki saka like 7 tablespoons of it, yaji Milo Sannan sugar dai dai, sai ki dafa min indomie guda biyu half done da kuma soyayen kwai guda 4" daga hakan, ta fita samirah tace" ae lalai, kaji ra'ayi Watto an samu banza". Washe gari, mummy na zaune akan dining tayi tagumi ga abinci kala kala a gabanta amman ta kasa cin kowanne, sai dai tunani iri iri. Nana ce ta sauko ta nufi dining ta gaida mummy kafin ta zauna, Shatu ta sakko suka gaisa da mummy "Hadiza na gaya maki ki daina damuwa dayawa, so kike kiyi rashin lafiya" "Shatu, this is my daughter and only child we are talking about, idan ban damu da Ita ba, dawa zan damu. Ace yau kwana yafi a kirga shiru muke ji, Alhaji kuma yace wai he's working on it, ya kike so nayi" mummy ta fada tana goge hawayen ta. "Hm, Allah ya sa mu cika da imani Hadiza, yanzu dai kar ki fasa mata addu'a" cewar Shatu. Daga nan mummy ta hau sama taje dakinta, ya rage Shatu da Nana a dining, murya kasa kasa Nana tace" Hm,umma ni fah ban yarda anyi kidnapping Ummi ba, kilan dai wata gantalin ta tafi a wani garin don irin kudin da iyayen ta suke danka mata, ai wani zai iya ciyar da iyalinsa for many years da shi" Shatu tace " ban taba sani na haife butulu ba sai yau, ke dai kulum ban san maiyasa bakin baya shiru ba, uban meye ta miki, yo dan ubanki idan ma gantalin ta tafi ba albarkacin gantalin bane kike zaune a gidan su ana miki gata yarda ake mata. A gidan uban naki da muka baro waye kika ishe shi kallo balle a kula da ke" turo baki tayi tace "uhm Umma dai abin zuciyata na fada" Shatu tace "tashi ki bani wuri dan kaniyan ki" tashi tayi piiiii ta koma parlor tana kallon TV.
✏📖
Ummi kuwa tayi butu butu, ta rame kaman ba Ita ba. Idanuwan ta sunyi baki sun kumbura tsaban kuka da rashin bacci. Bude kofan akayi tana kallon wanda ya shigo ciki, karasowa yayi, ya kwance mata igiyoyin da aka daureta dashi yace "tashi" a hankali ta mike, jiki ba kwari yace "muje" tace " ina zamu" wani shegen kallo yayi mata, ta dauke kanta ta nufi kofar ta fita. Bin mutumin tayi har inda akayi parking wani mota ya bude ta shiga Shima ya shiga ya fara tuki, suna cikin mota Ummi tace "dan Allah zan sha ruwa, I'm thirsty" kallon ta ya dan yi bai amsa ta ba, suna cikin tafiya yayi parking daidan wani karamin shago a siya bottle water mai sanyi, ya bude ya mika mata. Godiya Ummi tayi mai ta amsa ruwan, bayan ta shanye tace "you're a good person" kallon ta ya kara yi bai ce komai ba. Gaban gate dinsu ya ajiye Ummi ta sauka da sauri, mutumin yayi zooming off. Knocking ta dinga, mai gadi ko yana kankame da radion sa ya ji ana knocking. Tashi ya yi bude da sauri, Ummi ya gani tsaye, ya goge idon shi dan ya tabata ko Ita ce, sanan ya leka waje ya gan ba kowa yace mata "shigo ciki da sauri kar su dawo" Ummi ta biye mai ta shiga sa sauri. Shiko har da saka sakata. Tuni Ummi ta shiga cikin gida ta tarar da Samirah na goge goge, jin an bude kofa ta juyo, da mamaki tana kallon ummi tana mata sannu. Ummi tambaye ta "ina mummy" "tana sama tare da su aunty Shatu" ta hau sama ba kowa, ta shiga dakin mummy ba kowa, sai taji alaman cewa mummy na bandaki. Hawan gadon mummy tayi ta Kwanta. Mummy ko da ta fito taga Ummi akan gado....ta nufe ta da sauri tana kuka, Ummi ta mike tayi hugging dinta for almost 5 minutes. Chan mummy ta sake ta tana duba ta tace "Ummi ba suyi miki komai ba ko, kalla yanda kika rame" ta fashe da kuka "mummy dan Allah ki Kwantar da hankalin ki, ba gashi na dawo ba, basu yimin komai ba" mummy ta tashi ta shiga bandaki ta hada mata ruwan wanka tace "taso muje kiyi wanka", Ummi ta zaro ido tace "mummy ke zaki min" "ke banson surutu, taso nace" ta tashi suka shiga bandaki, Ummi ta cire kayan ta, ta shiga bath tub din da mummy ta hada mata ruwan zafi da kuma disinfectant aciki. Sun fi 20 minutes aciki kafin Ummi ta dauraye jikin ta tayi alwala suka fito. Mummy ta kira Samirah a waya tace mata ta kawo abinci dakin ta sannan ta sannar ma Shatu dawowar Ummi, daga nan ta katse wayan. Ummi ta saka kayan bacci ta hau gadon mummy ta Kwanta, ummi na magana "sun ce wai daddy ne ya kwace wasu properties dinsu, and that's why they kidnapped me. Apart from that basu ce komai ba mummy" mummy tayi ajiyar zuciya, sallama Shatu tayi Nana na biye da ita suka shigo cikin dakin "Ah ah Ummi barka, ke nake gani yau haka...oh Allah mun gode maka" ta karaso tana taba Ummi "aunty ina yini, Nana ya kike" Ummi ta gaishe su, suka amsa mata. Suna ta magana har Samirah ta kawo ma Ummi abinci, Ummi ta mike ta je dakin ta rike da tray din, Nana na biye da ita suka shiga dakin Ummi. Nana ko sai zare ido takeyi kamar wace tayi sata, a ranta tace "Chaap Lalai masu kudin nan akwai albazaranci, wai dakin yar su ce nan, mu ko dakin uwata bai kusan wannan kyau ba balle a kai ga namu" Ummi ta zauna akan cushion ta kuna TV tana kallo tana yan ciye ciyen ta bata kula Nana ba dan daman ba wani shiri suke ba. Ita ko Nana tayi nisa a tunanin da takeyi. Ummi ko ta cinye abincin ta tass ta sha fruits ta mike taje tayi alwala nan ma Nana ta fita daga dakin. Ummi tana kan daduma ta tuna su Iftihal ta mike don taje dakin mummy. Shiga tayi ta gan mummy na danna wayarta, mummy kaman tasan abin da ke ranta tace "Ummi yakamata ki kira friends dinki, da ba kya nan wlh ko wane weekend sai sunzo su duba ni, ranan ma sun hada ni da iyayen su akan waya suka gaishe ni" ummi tace "ai mummy abin da yasa na shigo kenan, sun kwace min wayata mummy" mummy tayi ajiyar zuciya, cike da masifa tace "amman shine da kika zo baki sa anyi blocking number din ba salon su zo suyi wani mugun abu da layin naki" "mummy yi hakuri, it skipped my mind" mummy ta mika mata wayarta "yanzu ga nawa maza kiyi calling customer care ayi blocking yanzu yanzu kafin ki kira su kawayen naki" Ummi ta kira akayi mata blocking Sannan ta fara kiran Iftihal "Assalamu Alaikum mummy ina yini" Inji Iftihal "toh mabaruka ba mummy bace" jin muryar Ummi ne yasa ta saki wani ihun murmishi tace "Ummi kece, ina aka kaiki Wlh munyi kewan ki ba kadan ba" suka dinga zuba hira, daga karshe Ummi tace bari in kira Zahra" daga nan ma ta kira zahran. A kwana a tashi,