Showing 15001 words to 18000 words out of 33472 words

Chapter 6 - UMMI

Start ads

Unknown   

13 Aug 2025

125

Middle Ads

na bude flask din Ummi taji zuciyar ta na tashi, kaman zatayi kuka tace "Ammi Wlh bazan iya ci ba, amai nake ji" a hankali ammi tace "toh zaki sha fruits, a kawo maki"? Ummi ta gyada mata kai, Ammi ta kalle Sa'adatu tace "ki mayar da abincin, ki kawo mata fruits da ruwa" daga hakan Sa'adatu ta fita. Farid kuwa bai samu kwanciyan hankali ba, gashi shi kadai a side dinsu, Ummi kuwa ta samu ta sha fruits, tayi sallah sannan tayi bacci. Washe gari Ammi ta shigo cikin dakin ta gan Ummi zaune akan daduma tace "Ummi ya jikin naki"? a hankali ta mike tace "Ammi ina kwana" Ammi ta amsa mata tace "zaki iya motsa jiki"? ummi ta gyada mata kai, sai Ammi tace "toh yanzu Sa'adatu zata zo ta raka ki side dinku ki dauko wasu abubuwa da kike bukata, za ki dan zauna a side din nan for a while don in dinga duba ki, Kinji" Ummi tace "toh Ammi nagode sosai" Ammi tayi murmishi taceb"A'a ba komai daughter" daga haka ta fita daga dakin. Bayan wasu mintuna, Sa'adatu ta shigo dakin tare da sallama tace "aunty sannu, ya jiki"? Ummi tace "da sauki, Nagode" "daman Ammi tace In zo wai zan taya ki da wani abu" Ummi ta gyada mata kai tace "Ae muje side dina" daga hakan ta mike suka nufi bangaren su. Shiga parlon Ummi tayi Sa'adatu na biye da ita, Ummi tace "Sa'adatu ina zuwa inje in kawo kayan" daga nan ta hau sama ta bude dakin Farid, taji alaman yana wanka a bathroom. Fita tayi daga dakin ta shiga dakin ta, ta shiga closet dinta ta fito da wata mini akwati mai kyau sosai, ta saka Abaya guda biyu masu shegen kyau da tsada, ta saka atampa guda biyu da underwears and kayan shafe shafen ta da turarukan ta da su shower gel. Bayan ta gama zuba kayan acikin akwatin, tayi zipping dinshi ta tsayar da akwatin, kokarin dagawa tayi taji baza ta iya ba. Fita tayi daga dakin ta tsaya a corridor ta Sa'adatu "Sa'adatu dan zo ki dauka kayan ki kai chan" Sa'adatu ta hau sama da sauri ta dauka akwatin ta sauka ta fita daga bangaren su. Ummi ta koma dakin Farid ta ga haryanzu wankan yake yi. Cire Hijabin ta tayi ta ninke, ya rage daga Ita sai skimpy dress wanda bai wuce hips dinta ba mai spaghetti hand da yayi mata kyau Sosai, ga dogon gashin ta baki wul wanda tayi twisting dinshi. Kofar bandakin ta nufa, daidan zata bude kofar Shima ya bude ta ganshi yana daura da towel a waist dinshi. Yana kallon kwayan idanuwan ta itama haka, a hankali ya janyo ta jikin shi ya rungume ta sosai, itama ta kankame shi kaman Za'a kwace mata shi. Chak! Ya daga ta sama ya nufi gado ya zauna ya ajiye ta akan cinyan shi yana rike da waist dinta, Ita kuma tayi wrapping hands dinta around his neck tana kallon shi. Murya kasa kasa tace "baby I've missed you so much" yana shafa cikin ta yace "I've missed you more Wifeyyyy. Baby I hope little Farid is not disturbing you" turo baki tayi tace "bansani ba, little Farid is so hungry Wlh" ta fada kaman zata yi kuka. Dan murmishi yayi yace "let's take little Farid out for breakfast, yau banaso mu ci breakfast din gida" daga hakan ya fara kissing dinta yana kokarin cire mata hanun rigan ta ya kai bakin shi saitin kunen ta yace "I love you baby, Allah ya barmu tare" murmishi Ummi tayi tace "ameen latest daddy in town". Daga nan ya dan lallashe ta sanna suka mike, Ummi ta shiga bathroom din domin tayi wanka, Farid kuma ya shiga closet dinshi ya shirya daga hakan ya je dakin Ummi ya shiga closet dinta ya dauko mata wata Abaya pink and white mai kyau Sosai, ya dauko mata wata Chanel handbag white da takalmi Shima white, ya hada mata da inner wears ya fita daga dakin ya shiga nashi. Daidan lokacin daya shiga itama ta fito tana daure da towel taga kayan ta a hanun shi tace mai "Aww, so thoughtful of you, thanks baby" daga hakan suka shiga closet dinshi tare, ya zauna kan wata hadadden sofa yana danna wayar shi, Ita kuma tana aikin shafa kayan shafe shafen shi a jikin ta, minti minti yake satan kallon ta. Ummi ta gama yan shafe shafen ta tasss! Sannan ta saka kayan ta. Ba karamin kyau Ummi tayi ba, kayan ya karbe ta sosai. Farid na kallon ta yana hyping dinta kaman zai cinye ta Ummi cike iyayi irin na yan mata tace "you can't believe this sexy young babe standing before you is your wife ko"? yace "babe kin hadu ne over wlh" Ummi tayi murmishi tana kokarin shiga Snapchat a wayar ta, tayi musu mirror selfie masu shegen kyau. Daga hakan Farid ya dauka key din Brabus dinshi suka fita daga dakin suka sauka kasa. Ummi da Farid sun hadu ba kadan ba, gasu young couples.
Wani restaurant mai tsada sosai ya kai ta. Parking yayi suka fito daga motan suka shiga tare. Sai kallon su akeyi don sun birge mutane. Waje suka samu suka zauna wani dan matashi da ke aiki a wurin ya kawo masu menu ya tafi. Farid ya kalle ta yace "baby kiyi mana choosing abin da za muci sai kiyi mana placing order" tace toh, chan dai ta daga kanta tana kallon shi tace "then who will pay the bills"? yace "my wife of course" tace "and if I don't pay"? yace "you're a woman ai you can wash dishes" dariya tayi ta kira waiter din ta nuna mishi abincin da suke so daga nan ya wuce. Kallon ta Farid Yayi yace "I see you ordered expensive food, wife ita cash madam ce" murmishi tayi bata ce komai ba, haka Farid ya dinga tsokanar har aka kawo musu abincin su, suna ci suna hira har suka gama, suka bar restaurant din bayan Farid ya biya bills din. Yana parking acikin compound yace "babe bari na gaida baba" tace "okay baby sai ka shigo" daga hakan ta nufi side dinsu.

Ammi ce a bangaren Alhaji Nagoda suna dan hiran su a haddaden parlon shi. Sa'adatu ce ta shigo tare da sallama tana rike da tray din fruits da ruwa, tazo har gaban su ta ajiye tray din. Ammi tace "Sannu Sa'a, kin samu kin dauko kayan Ummin"? Sa'adatu tace "Ae ammi tun dazu na dauko na kai side dinki" Ammi tace "okay toh, ina Ummin take, ta ci abinci"? Sa'adatu tace "Ai Ammi a side dinsu na bar ta da na je kwaso kayan, da kuma na gama dafa abinci naje daki in sanar mata amman ban ganta ba kaman sun fita da yaya Farid" Ammi tace "okay toh, wuce abin ki" Sa'adatu ta fita. Ammi cike da tsokana ta kalle Alhaji Nagoda tace "Alhaji kaga yaran zamani ko, daga suje su dauka akwatin ta, shikenan ta makalle ma mijin ta. Shima Farid din ko motsin shi bamu ji ba yau" Alhaji yace "Toh in banda abinki Saratu mata ta dade bata gan mijin ta ba dan yayi tafiya, yanzu da ya dawo da za ta samu daman jin dumin mijin ta, kin ce taje ta dauko akwati ta dawo bangaren ki" Ammi tace "Haba Alhaji ai na fada hakan da in dinga duba ta ne ai, kasan Farid ba wani taimakon ta zai iya yi ba yanda ya kamata" Alhaji yace "Toh ba shi ya bata ciki ba, shi ne zai cigaba da kula da kayan shi, ki bar yaran nan su ji dadin su mu ma haka" Ammi tayi murmishi tace "toh shikenan Alhaji, mu sha fruits" daga hakan ta dauka fruits din suka fara sha tare.

✏📖

Kasancewa yau ranan sati, Ummi ce a kitchen tana hada coffee. Cikin Ummi ya sa tayi haske kuma ta rame amman ba Sosai ba. Skin dinta yayi kyau Sosai. Tana sanye da katon pink T-shirt da kuma jeans bum short amman bata yi zipping dinshi ba saboda cikin ta duk da bai fito ba, sannan kuma ta daura vintage scarf pink a kanta, tayi kyau sosai. Shigowa Farid yayi yana kallon ta yace " baby meye kike yi"? tace "I'm craving coffee, shine na hada wanda mummy ta bani jiya, it's really nice zo ka sha kaji" ta fada tana mika mai cup din. A shagwabe Farid yace "ni na bakin ki nake so" coffee din ta kai bakin ta, sanan ta janyo shi ta saka bakin ta a nashi ya shanye coffee din tasss, ya fara kissing dinta yana mata wasu abubuwa( Hegu Ummi da Farid yan bariki). Rayyana ce ta shigo side dinsu Ummi, tana ta sallama amman ba'a amsa ba ganin haka yasa ta nufi kofan kitchen din ta bude. Ganin su tayi a halin da suke ciki, da sauri ta rufe kofan ta koma parlon tana ajiyan zuciya. Farid kuwa bai sake Ummi ba duk da ya dakata da suka ji an bude Kofa( hege Farid😹💔) murya kasa kasa kamar wata munafuka tace "babe ka shigo baka rufe kofa ba" yace "mantawa nayi, besides naga dai nan side dinmu ne, duk wanda yazo yaga abin da yafi karfin shi, shi ya kawo kansa" Ummi tayi murmishi kadan. Daga hakan ya sake ta suka dan gyara kansu suka fita. Ganin cewa Rayyana bata parlon yasa suka hau sama tare.

Ammi ce zaune a parlon ta da wata mata da bata wuce 33 years ba tana kama da Ammi Sosai, tare da Rayyana. Ammi tace "Rayyana kin samu fada musu cewa yayar ku ta zo"? tace "Ammi da naje fah ina ta sallama ba'a amsa ba, kila sun fita" Ammi tace "fita kuma, bayan yanzu su chuchu suka ce motan su na nan, bari dai in kira Farid din a waya" ta dauka wayarta ta shiga dialing number Farid. Yana dauka tace "Farid ina kuke"? yace "Ammi muna gida" tace "toh Kuzo side dina kai da" ya amsa daga haka ya katse wayar. Ammi tace "gashi nan na same shi a waya yanzu zasu zo". Aikuwa ba da dadewa ba sai ga Farid da Ummi wace ta saka purple Abaya da yayi mata kyau Sosai suka shigo kuma suka karasa wurin Ammi suka gaishe ta cikin ladabi. Basu Lura da bakuwan dake zaune ba har Sannan bakuwan tace "lalai Lil bro, baka gan ni ba kenan" jin muryar Laila yasa ya daga kanshi da sauri, tini ya mike cikin farin ciki ya nufe ta suka gaisa, Ummi ma ta gaishe ta Sosai Sannan suka zauna a parlon Ammi duk suna hira. Bayan sunyi hirar su, mikewa yayi yace "Ammi zamu fita ni da Ummi yanzu, zan kaita gida ne" Ammi tace "okay, Inji dai ba damuwa ko" Ummi ce ta amsa "A'a fah Ammi ni ce kawai nake kewan gida" Ammi tayi murmishi tace "toh daughter, ki gaida yan gidan" sai ta kalla Farid tace "kai kuma kayi tuki a hankali, karka firgita min yarinya ehe" murmishi Farid yayi Sosai, ya kalla Laila yace "hope zamu same ki idan muka dawo, ai zaki kai magrib ko"? Hararan wasa Laila tayi mai tace " Ae, tunda kai nake aure ba da zan kai magrib" dariya duk suka yi, Ummi tayi mata sallama daga nan suka fita.

Cikin compound dinsu Ummi yayi parking sannan suka sauka daga cmotan. Baba mai gadi ne ya karasa wurin motan yayi musu Sannu da zuwa, daga nan suka shiga ciki. Ganin ba kowa a parlon kasa yasa ummi ta fara kiran mummy "mummy" Samirah wace take kitchen taji muryar Ummi ta fito da wuri "laaa aunty, sannu da zuwa, ina yini" Ummi tace "samirah ya kike, ya kwana biyu" "alhamdullilah aunty, ku hau sama su mummy suna nan, bari in kawo muku ruwa" Ummi ta amsa mata tana hawan staircase, Samirah ta gaida Farid dake zaune a parlon. Karo taci dasu aunty Shatu da Nana a parlon "Aunty shatu ina yini" aunty Shatu dake kallon Ummi tayi mulmul, ta danyi haske duk da cikinta ya sa ta dan rame amman ba Sosai ba. Aunty shatu tace "ah ah su amarya ne a gidan yau, kwana dayawa" Ummi ta amsa mata, har suka gaisa da Nana Sannan ta nufi dakin mummy. Nana wace ta bi Ummi ta kallo, muryar ta kasa kasa tace "kai Umma kinga wani kyau da Ummi ta kara, ni kaman ma tana da ciki, baki gan kaman cikin ya fito ba" aunty Shatu tace "Uhmm, Nana ki bar wannan maganan, na ma rasa mai zance. Lalai in dai cikin gare ta toh bilahilazi sai mun zubar da tsiyan da take dauke dashi" Nana ta zaro ido tace "Haba Umma, hakan bai yi yawa ba kuwa, banda hakan wane hanya zaki bi kiyi hakan bada an samu wani problem ba" A fusace aunty Shatu tace" tace Wlh ke ba kida hankali, wawiya shashasha kawai, ke nan har wani damuwa ki kayi da ita. Ita Ummin an gaya miki ta damu dake ne" Nana ta turo baki tace "Kaiiiii Umma ni dadi na dake kin cika concluding abu da sauri, ni ban damu da Ita ba...kawai ina tunanin hanyar da zamu bi mu zubar da cikin ne cikin sauki". Aunty shatu ta washe baki "tace, Yauwa yar albarka, yanzu kike maganan arziki. Toh bari kiji yanda abin zai kasance, zaki...." Nana tace "Umma nice plan amman Umma kina ganin zata yarda, bamu wani shaku ba" Aunty shatu tace "wannan kuma ki bar shi, na san abin yi" ( kai duniya abin tsoro, Allah dai ya kare mu🙏)

Ummi ce zaune akan gadon mummy suna hira da shewa, mummy tace "ina Farid yake, ba tare kuka zo ba"? Ummi tace "laaa mummy Wlh ni na manta ma tare muka zo, duk farin cikin ganin ki ya dauke min hankali" mummy ta harare ta tace "amman ke banza ce, mijin naki kike sakaici dashi" Ummi ta turo baki, mummy tace "dallah ni matsa min in fita" Ummi a shagwabe tace "toh mummy kwata kwata minti na nawa da shigowa" mummy bata kula ta ba, ta fita daga dakin ta sauka kasa. Farid na ganin mummy ya duka har kasa ya gaishe ta cikin ladabi, mummy ta sa mai albarka tare da tambayan shi ya yan gidan, ya amsa mata cikin ladabi kafin ya duba agogon shi yace zai je masallaci domin an fara kiran sallahn la'sar. Daga nan ya fita mummy kuma tasa aka jera abinci akan dining sanan ta hau domin yin sallah. Nana ce ta gani tare da Ummi a dakin, hakan ya bata mamaki, a ranta tace "toh, yaushe Ummi da Nana suka fara shiri" a zahiri kuma ta kalle su tace "toh a dai tashi aje a bauta ma Allah" Nana ta kalle Ummi tana murmishi tace "sis tashi muje dakin ki muyi sallan muma" Ummi ta amsa mata da fara'a domin ba wai bata son Nana bane, kawai rainin ta ne bata so kuma daman basu shaku ba, shiyasa bata shigan sabgar ta amman har ga Allah yanzu tana jin dadin yanda Nana take yi mata. Fita suka yi daga dakin mummy suka ci karo da aunty shatu, cikin munafurci tace "toh yan mata, zumunci haka" murmishi suka yi mata suka shiga dakin ummi. A nan suka yi sallah Sannan kowa ya sauka zuwa dining. Ummi ce tayi serving kowa kafin ta sa nata abincin dan kadan, kowa yayi bismillah suka fara ci. Bayan duk sun gama cin abinci, su Ummi suka shirya tafiya. Sosai suka gaisa da kowa tun ba mummy da Ummi takeji kamar Kar ta bar ta. Daga gidan su Ummi suka nufi gidan Inna.

ℹKuna ganin Shatu zata yi nasara wurin hada Nana da Farid su yi aure yarda ta rantse zata yi? And lastly jama'a dan Allah, daukan wankan Ummi bata birge ku?😍Sooo many questions, but you can only get your answers in the next chapters. Kafin mu karasa, ya kuke ganin novel din zata kasance? Send your comments and reviews via this number: 07046861910

🚫No CALLS please just comments.

✏📖

Ummi ce da Nana a parlon ta. Nana tana bata labarin Yusuf saurayin ta, harda nuna mata hoton shi. Ummi ta yamutsa fuska tace" kai amman sis bakiyi kokari ba Wlh" Nana tace "kaman ya kuma sis" Ummi tace "toh ai da wanan, ai gara babu, ni wlh da kike bani labari, na dauka wani abin azo a gani ne fah" Nana tace "uhm baza a dai ce banda saurayi ba" Ummi tace "Dallah malama rufe min baki, har wani takama kike da wannan dan daban, ni nama rasa Uban meye ya fada miki da kika like mishi, mtcheeew" mikewa Nana tayi cikin basarwa tare da cewa "ni dai yanzu, inyi miki salad din ko kin pasa ci" Ummi ta yamutsa tace "kiyi min kiyi shredding chicken aciki pls" dariya Nana tayi tace "toh, acici iyayen tauna" dariya dukan su suka yi, Nana ta wuce kitchen, Ummi kuma ta dauka wayar ta, ta nufi upstairs.

Dakin su ta nufa, ta shiga ciki. Hango Farid tayi cikin closet, yana waya yana cewa "toh daddy, zan bi flight din 8:00 pm " daga bangaren daddy yace "okay, nayi informing maman ka, sannan are you coming with your wife?" Kallon Ummi da ta zauna a gefen shi yayi, Sannan yace "no daddy, ai kasan tana zuwa school, kuma sun kusan fara exams" daddy yace "okay, ba damuwa, Allah ya bada sa'a" daga hakan suka yi sallama, Farid ya katse wayar. Ummi tuni jikin ta yayi sanyi tana kallon Farid tace "baby, are you traveling"? yanda tayi maganan, ya bashi tausayi, ya matsa kusa da ita, ya jawo ta jikin shi yana shafa mata hips dinta yace "yes baby, yanzu daddy yake fada min akwai business trip din da zamuje. Amman ba zamu dade ba, sati daya za muyi mu dawo, so karki damu kinji" gyada kanta kawai tayi. Chan sai tace "toh bari in hada maka kayan ka, ko" mikewa zatayi, Farid ya rike ta gam, ya marairace yace "sai kin bani abinci tukunan"

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login