Showing 30001 words to 33000 words out of 33472 words
harda wanda suke kusa da table dinsu da suka ji Inna. Ummi kuwa sai da ta dandana komai abin ka da mai ciki. Ansha shagali sosai kafin aka yi closing event din, lokacin har 12am yayi. Parking lot aka nufa inda ake ta kokarin shigan motoci. A yanda duk wa'enda suka fito daga gidan biki suka zo, haka suka koma.
Gaban gate Farid yayi parking, su Ummi suka fita daga motar suka nufi cikan gidan while yana bin su a baya. Dakunan su yan matan suka wuce direct, Farid kuma ya nufi dakin su Ammi dan yi mata sallama. Bayan yayi ma Ammi sallama, ya fito daga dakin yaji ko'ina tsit alamun kowa ya shige daki dayake dare yayi ga kuma gajiyan biki. Dakin da Ummi take ya nufa, a hankali ya bude kofan ya shiga sanan ya rufe tare da saka key. Saukan ruwan shower yaji daga bathroom alamun wanka Ummi takeyi, ya taka har bakin kofan ya bude ya shiga. Samun ta yayi tana kokarin daura wani pink bathrobe din mink, a hankali ya karasa yayi hugging dinta, a shagwabe yace "my baby boo" itama shagwabe fuska tayi tace "yes papiii" murmishi yayi and kissed her kafin ya dauke ta suka fita daga bathroom din. Taimaka mata yayi ta shirya cikin baby pink pyjamas mai kyau sosai, sanan suka yi addu'a tare da tofa ma junan su, ya kwantar da ita tare da jawo mata bargo, yayi kissing dinta goodnight Ummi ta bishi da kallo har ya fita daga dakin. Awww Farid is just so cool and has his ways of captivating her heart.
ℹ It's important couples su san cewa all these little things matter, su suke kara bond tsakanin couples. Ba kullum za'a je other room ba, una no dey tire ne?! Sometimes kuyi sallah tare, read the Al-qur'an together, play games together etc. Oga, sauran kuma kace "can't be me" ko kuma kace you're a man kai Ka wuce hakan, ba zai yu ka biye mata kuna wasan yara ba, blah blah blah.Kema madam ki bada hadin kai, ba wai when Oga is trying to make efforts ba ki tsaya kina hura nose kaman balloon ke wai boss lady. Toh nidai na baku hint, sauran ya shiga kunne daya ya fita daga dayan.
✏📖
Bayan fitar Farid daga dakin Ummi, parlour ya sauka sanan ya fita daga gidan gaba daya ya nufi hotel din da suke. Washegari a gidan biki, bayan yan matan sun idar da sallahn asuba, bacci suka koma. Gari na wayewa duk suka fito dan yin breakfast as usual. After breakfast suka fara normal activities din nasu wato hira da sallah kafin lokacin dinner. Ana idar da sallahn isha, aka fara shiri kaman dai yanda aka yi jiya. Ummi ta saka wani expensive black and golden color lace, tana rike da wani black ball bag kafan ta kuma sanye da black half covered heel na company din Charles and Keith, kanta kuma daure yake da turban din raw silk material. Woah guys bazan iya cigaba da fadin irin kyau da Ummi tayi ba, "damn, that's my gurl" ta fadan Farid. Ummi is just too cuuute! Kaman jiya, haka Farid yazo suka tafi event center, amma fah da kyar, dan Farid ya kusan causing musu accident tsaban yanda ya dinga kallon Ummi. Yauma hall yayi kyau sosai, ga mata sanye cikin various dinner gowns while mazan suna sanye da tuxedos kala kala, bayan anyi opening prayers, DJ ya saka old school, nan fah iyaye manyan mata suka fara fitowa suna rawa da liki. Inna dake zaune tasha ado cikin Swiss lace, dinkin Abuja bubu ta mike ta nufi wurin MC dake rike da microphone tace "Dan nan, wane irin waka ne wanan sai kace an shaqe kazar mayu, bayan ga wakan su Shatta dasu Altine Jibo" nan fah mutanen hall suka kwashe da dariya dan muryar Inna ya fito rass ta microphone din. Komawa sit Inna tayi tana faman tabe baki. Bayan iyaye mata sun gama rawa aka saka wakan zamani nasu Davido, wizkid, Ayra Starr, Young jonn, Rema, Burna boy, Kizz Daniel da suaran su, nan ma yan mata da samari suka yi caaaa suna following dance trend din kowane waka da aka saka hardai amarya Nabeelah da angon ta, Ummi ma ba'a barta a baya ba da aka saka favourite trending song dinta 'Kehlani' by Jordan Adetunji. Mikewa tayi lokacin da aka fara playing wakan taje ta janyo Farid dinta, suka je dance floor suna bin dance trend din da lyrics din wakan
'I like the way your body is i do'
'Is that too obvious'
'Okay I like your confidence'
'Oh that's what good karma is, okay'
Li'l like Kehlani is, bad just like Kehlani is, okay'.
Nan take jama'a suka fara shewa ana hyping dinsu da musu video ganin yanda Ummi da Farid suke Kehlani dance challenge cike da nishadi, ji kake "aww, osheyyy, God when". An sha rawa an gaji, kafin aka fara raba abinci in order to retain energy. Yau dai English food irin su (French fries, omelette, Vienna sausages and grills, glazed sticks, brewed coffee, cocktails and mocktails etc) Ummi kuwa taci glazed sticks ya kai goma dan abin ya mata dadi, Farid kam sai faman tsokanan ta yake wai ta cinye rabin glazed sticks din da aka hada. Bayan angama cin abinci, akayi games da karaoke sanan akayi closing prayer daga nan kowa ya nufi gida. A gajiye kowa ya shiga daki kamar dai jiya, Farid yayi ma su Ammi sallama kafin ya wuce dakin Ummi, tsaye ya gan ta da black color skimpy nightwear, kanta daure da wani ash color vintage scarf tana shafa night face cream dinta. Murmishi tayi mai tana mika mai hannu, kaman yaro kuwa yaje da dan gudun shi yayi hugging dinta yana cewa "I'm eager to go back home baby, I'm being punished, bana samun jin dumin mata ta yanda ya kamata" murmishi ta kara yi kafin tace "you're naughty" lakace mata hanci yayi yace "and you're naughtier. Baby, I'm getting late, zan wuce, do you need anything"? Kallon shi tayi kaman mai tunani kafin tace "I want to eat olives" "I think naga wani a fridge dazu, bari na kawo" cewar Farid da ya saketa ya fita daga dakin, ya sauka kasa sanan ya nufi kofar kitchen. Yana bude kofan yaci karo da wata budurwa da baza ta wuce 26 years ba, tana da dan kiba, fara ce amman ba sosai ba kuma tana da kyau daidai. Zaro ido Farid yayi yana kallon ta da mamaki, ya nuna ta da yatsa yace "Nafisa! Ko ba Nafisa bace, meye kike yi a gidan nan"! Ya karasa maganan a dan tsawace. Kallon banza tayi mai kafin tace "ni din ce, kuma bikin kawata nazo. Abu kuma yayi kyau da na gan ka because I've been trying to reach you across all platforms amman kayi blocking dina. It's high time you meet our son, dan ka na bukatan ka at this stage" wani irin kallon tsana ya watsa mata yace "are you crazy? ko wiwi kika busa ne? We've had this discussion and it's good as dead. Babu yaro tsakani na da ke, in fact bamu san juna ba. Ina biyan ki dubu dari shida every month for his upkeep yanda kika bukata idan ma kari kike so zan miki, but stay out of my life, I have a wife, I love her and I'm happily married. What happened between you and I years back was a mistake that will never repeat itself, kuma hakki na is on you because you masterminded and planned everything, Allah ya isa tsakani na dake" ya karasa maganan yana huci. Daga murya Nafisa tayi tace "wallahi, tallahi, bilahillazi ha' illa huwa baka isa ba. Yes I did what I did sabida son da nake maka and so what ai ba kaina aka fara ba, amman baka isa kace you don't know me ba, baka isa kayi denying dan dana haifan maka ba! I don't need your money anymore, ina karban kudin ka bawai dan i can't afford to take care of our son ba, ina karba ne because i want you to know that kana da responsibility akan ka apart from your so called wife, all I need is for you to show some fatherly love to your son. Wallahi kayi wasa Farid I promise you I'll mess you and your family up, just try me you son of a b!tch"!
ℹAna wata ga wata, waye Nafisa, kuma meye alakar ta da Farid da? Why is she saying she has a son with him? Farid ya taba aure ne bamu sani ba? Meye take nufi da "Yes I did what I did sabida son da nake maka", what did she do? Why is Farid mad at her da har ya ja mata Allah ya isa? Is she at fault da tace he should take fatherly responsibility for his son? I mean that's what every father should do right? Ga kuma madam wato Ummi, ko wane hali zata shiga idan ta ji? Sooooo many questions, and you can only get your answers in the next chapter. Sanan nasan baku ji dadin na kawo obstacle tsakanin Farid da Ummi ba, but haka rayuwa take, gbas gbos up and down, yau dadi gobe tsami. Sai dai a cigaba da hakuri sanan a dogara ga Allah. Don't forget to send your comments or reviews via this contact: 07046861910.
🚫No CALLS please just comments.
✏📖
Wani gigitacen mari aka dauke ta dashi, a tare, cikin rudewa suka juya suna kallon Ummi da basu lura da shigowan ta kitchen din ba. Daga hannu Nafisa tayi zata rama marin da Ummi tayi mata Farid ya kama hannun ta, a tsawace tace "sake ni inci uban yarinyar nan. Ni kika mara shegiya" ta karasa maganan tana kokarin kwace hannun ta. Basu ankara ba, Ummi ta kara daukan Nafisa da wani marin tana cewa "kece dai shegiya ba ni ba. Ke har kin isa ki shigo gidan mutane kina zagin maman wani, ke mahaukaciyar ina ce"! Farid ne ya fara kokarin raba fada ganin Nafisa tayi nasaran kwace hannun ta ta kaima Ummi naushi. Nan fah hayaniya ya balle tsakanin su, Farid yayi nasaran bambare Nafisa daga jikin Ummi, ya dauke Ummi ya nufi parlour da ita Nafisa na biye dasu tana bala'i. Hayaniyan dake tashi a parlour ne ya farkar da sauran mutanen gidan. Ammi ce ta tashe Aunty Turai tana cewa "ke ina jin kamar muryar su Ummi ne fah" mikewa suka yi da sauri, a atare suka fita daga dakin, daidan lokacin su Nabeelah da Inna suka fito daga dakunan su cikin sauri. "Innalalahi, Feenart meye haka"? Nabeelah ta fada cikin daga murya tana kokarin rike ta. Da sauri su Ammi suka karasa cikin parlon suna kallon Ummi dake zaune a kasa tana hawaye, hancin ta da gefen bakin ta na jini, ga kuma Farid da tissue a hannu yana kokarin goge mata tana ki tana cewa "wlh karka taba ni, don't you dare touch me"! Kallon mamaki kawai mutanen parlon suke musu. Ammi ta kalle Farid fuska a daure tace "what just happened here"? Kasa amsawa yayi, Ammi ta mai tsawa tace "da kai nake fah, meya faru"? "Ff fada suke yi Ammi" ya bata amsa, "ai wlh baza ta sabu ba, yanzu wancan mai kama da danyen gyada ta maki wannan danyen aikin? Kuma Farid sabida kai rago ne ka tsaya wata bagidajiya ta maka Jinajina da fuskar mata. Toh wlh ban yarda ba, yanzu nan zamu chaji ofis a garkame mani yar banza, zaki san jika ta kika daka yau. Ke Ihsaanu yi maza dauko min mayafi na a daki" cewar Inna tana duba fuskar Ummi. Sauke ajiyar zuciya aunty Turai tayi kafin tace "A'a mama, kiyi hakuri bai kai haka ba, a nan za'ayi ta ta kare" ta kalle Nafisa cikin dakewa tace "ke Feenart meye ya hada ki da matar Farid"? kasa magana tayi, aunty Turai ta daka mata wani tsawa da sai da kowa a parlon ya firgita "ki bani amsa, meye ya hada ki da ita da har kika fida mata jini"! Cikin rawan jiki Nafisa tace "t..tt ta mare ni shine na rama". Wani matsiyacin kallo Ummi ta watsa mata, kafin tayi magana Inna tace "yo an ce maki Aminan mahaukaciya ce da zata mare ki babu dalili" ta karasa maganan ta watsa ma Nafisa harara. "Bari dai mu ji daga bakin Ummi Inna" cewar Ammi, sanan ta tambaye ta meye ya hada ta da Nafisa, kasa amsawa Ummi tayi kawai ta fashe da kuka dake nuna cewa she's deeply hurt, mamaki da tausayi ne a fuskan kowa banda Nafisa because Ummi was really crying her heart out. Sake baki Inna tayi tana kallon Ummi sanan tace "yau ina ganin gantalewa ni Yakwalo. Yo kodai baki da gaskiya ne, atoh idan ba rashin gaskiya ba taya daga tambaya ki hau kuka wiwi, maimakon ki fada mana laifin da tayi maki, a kai ta chaji ofis a garkame ta ko da na wata shida ne" duk da halin da ake ciki, sai da yan parlon suka yi murmishi amman banda Farid, Ummi da Nafisa da duk suke ji da abin daya dame su. Kallon su Nabeelah da sauran yan matan aunty Turai tayi tace "ku je ku kwanta, dare yayi and we'll handle it" daga nan suka yi musu sai da safe, ya rage Inna, Ammi, Aunty Turai, Farid, Ummi da Nafisa a parlon. Ammi ce ta dago Ummi daga zaman kasan da tayi, ta zaunar da ita kan kujera tana tapping bayan ta a hankali kafin tace "daughter, ko meye ke damun ki you know you can always come to me and tell me, I'm also your mother and bazan ji dadin ganin ki cikin rashin walwala ba considering your current condition, please ki dinga guje duk abin da zai bata miki rai, always remember that you're a married woman so you have to overlook some things. Ba komai bane idan aka miki kice za kiyi retaliating ba kinji, ki rike girman ki as a married woman, okay"? gyada mata kai Ummi tayi still crying. Aunty Turai ta daura nata fadan kafin Nafisa ta shiga daki bayan tayi musu sai da safe, lokacin Inna ma ta shiga daki. Ammi ta kalle Farid daya hada uban gumi tace "kai Ummi daki kazo ka same ni" da toh ya amsa mata yana kokarin rike hannun Ummi da already ta mike, watsa mai wani matsiyacin kallo tayi daya sa Farid shan jinin jikin shi. Bin bayanta kawai yayi dan kar su Ammi su fahimce komai har suka kai dakin, Farid yana cewa "baby I'm soo sorry, pls let's settle this amicably, na san nayi miki laifi amma...." Kafin ya karasa, Ummi cikin muryar ta daya fara dashewa tsaban kuka tace "how could you, meyasa zaka jefa mu cikin wannan masifar. What on earth were you thinking, a child outside marriage? And you hid it from me all these while tun kafin muyi aure har muka yi aure. Na dauka kowanne irin hali da zamu tsinta kanmu aciki, we'll share it with each other and find a solution to it. Baka yi tunanin zaka salwantar da family name ba? Wanne hali kake tunanin Ammi da Abba zasu shiga if they get to find out that their first and only son has a child outside marriage? Banda wannan ma kana tunanin hakkin yaron nan bazai bi ka ba? I'm so hurt and angry but zan fada maka gaskiya, kana tunanin kudin da kake aika musu is enough, do you think wannan matar zata bari muyi zaman auren mu in peace with kids bayan ita tana rainon dan ka that you don't want anyone to know of? How do you really think that feels huh? Bawai ina supporting abin da kuka yi bane, wannan tsakanin ku da ubangiji and I'm not on anyone's side but that little boy is innocent and how could you be so selfish? What if maman shi tasa mu a danger gaba dayan mu"? Ajiyar zuciya Farid ya sauke dan maganganun Ummi ya shige shi "Mimie (abinda yake kiran ta kenan idan suna serious talk) nasan nayi babban kuskure a wurin Allah sannan I know I hurt your feelings and I'm deeply sorry. Wlh Mimie I was afraid I would loose you idan na fada miki, kila ki ki yarda ki aure ni cause I know you don't like competition. But Mimie it's not my fault that all these is happening" wani irin kallon ka ma raina min hankali Ummi ta mai kafin ta dauke kai. "Mimie dan Allah say something, kar ki min wannan silent treatment din, it's killing me, bazan iya jurewa ba" a kufule tace "ba nida abin fada maka, just leave I need some rest" ta karasa maganan tana kashe switch din wuta dake gefen gado, sannan tayi addu'an kwanciya ta tofa kafin ta shige bargo. Farid kuwa mikewa yayi, ya karasa gefen da take kwance sannan yayi kissing goshin ta yace "I'm really sorry Mimie, I never meant to hurt you and nayi alkawari I'll fix this. Amma dan Allah kar ki guje ni, I really need you to stand by my side to fight this battle. It's going to be a tough battle, but Mimie I need you by my side, ki zama armour dina" ya karasa maganan yana hawaye, manna mai hauka Ummi tayi, daman Farid ya san halin kayan shi hakan yasa ya fita daga dakin bayan ya kara tofa mata addu'oi sannan ya fita. Yana fita Ummi ta mike tana hararan kofan dakin sannan ta wuce bathroom ta tsaya gaban mirror tana kallon hancin ta da jini ya dan fara bushewa. Tsaki taja tana cewa "mtcheew, karfiya kawai" ta karasa maganan tana wanke fuskar ta kafin ta koma dakin, ta shafa night face cream, ta kara addua'a sannan ta kwanta. Koda ya sauka kasa, bai gan su Ammi ba, fita yayi daga gidan gaba daya ba tare daya leka dakin su Ammi ba, dan baya jin zai iya wani dogon zance.
Washegari kuwa