Showing 27001 words to 30000 words out of 39140 words

Chapter 10 - LADIDIN KAUYE

Start ads

24 Aug 2025

244

Middle Ads

walaikumusalam kazo ka d'auki matarka tarasa mota ,cikin zumud'i yace ”ganinan zuwa momy ,Khadija ko harta shige gida sa kaya saboda kafin ta tafi tayi wanka , wow tana sanya kayan suka fito da ainihin kyawun ta inka ganta zaka rantse itace amaryar dukda nima banga amaryar ba ,da k'yar tasa skirt d'in domin ya matseta sosai gakuma takalmi mai tsini sosai ga nad'in gwagwaro da 'akayi mata ,d'ankunne da sark'a tasa ta d'ibi kud'ad'en datakai akayimata canji aka bata sababi ,mayafin kayan ta yafa a kafad'a ....✍️🤙.



Mom Islam ce

*LADIDIN K'AUYE*


Funny & love story.

*Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa*



*NA*

*MOM ISLAM*
*ZAINAB HABIB*


*MARUBUCIYAR:*

*ZAINABU ABU*



*AND NOW*

*LADIDIN K'AUYE*



*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


*Episode:* 43_44




_____D'akin momy ta nufa ,momy na ganinta ta rangad'a gud'a mutane sai kallonta sukeyi wasu na gulma wasuna cewa tabasu sha'awa ,momy ce tajata gefe tace ”please daughter karkiyiwa mijinki rashin kunya kinga can jama'a suna kallonku dan Allah badan niba ,sunkuyar da kai Khadija tayi tace ”momy wallahi bazan yimai rashin kunyaba ,cikin jin dad'i momy ta mik'o mata dubu biyar sabbi tace ”tayi manni ,godiya tayiwa momy ,suna cikin magana saiga Humaid nan yashigo cikin shadda mai ruwan coffee shimafa ba k'aramin kyau yayi ba kai kace shine angon ,durk'usawa yayi har k'asa ya gaida momy ,bayan ta 'amasa ne yashiga ya gaida jama 'ar dasuka taru ,daganan yafito ,ya yiwa Khadija magana ,cikin yanga tace ”inzo mutafi ? wani kalo yake yimata mai kamada na so hhh masoya kenan 😘,momy ko ganin hakan yasata shigewa ciki ,Humaid cikin wani salo maijan hankali yace”muje lokaci na tafiya ,ohk tace ”daganan suka wuce ,gidan gaba ya bud'e mata ,shigewa tayi shima yashiga hmm riders duk wanan ladabin da khady take yiwa humaid duk a cikin umarnin momy ne hhh🤣 driving yafarayi cikin k'warewa rik'o hannunta yayi da d'ayan hannunshi d'ayan kuma yana driving dashi ,ko k'ala batace ba ....



Da isarsu yayi parking gurinda kowa ya parka motarshi ,fitowa yayi yana jiran Khadija tafito ,hhh abinku da gimbiyar mata saida ta jima yana tsaye sanan tafito ,a yangace take tafiya ,Humaid ne ya hango wasu samari suna k'arewa shigar Khadija kallo, cikin zafin nama ya rik'o mata hannu suka wuce ,da shigarsu Hall din kalo yakoma gunsu ,sai tafi ake yimusu ,kusada ,amarya Khadija ta zauna shikuma Humaid friends d'insu nacemai ga guri yana cemusu shifa kusada gimbiyar zai zauna ,dole aka mik'o wata ha d'ad'iyar chair ya zauna ,kammo hannunta yayi yana mata rad'a 'a kunne ,nimafa banji meyace ba nadaiga suna dariya ,duk abinda sukeyi doctor Umar yana yimusu photo ...




Kiran Amarya akayi dakuma k'awayenta ,mik'ewa amaryar tayi Jalal kuwa yana rik'e da 'amarya dan haka suka mik'e a tare yana cemata wananfa matar yayana ce ,cikin fara'a 'amaryar ta rik'o hannun Khadija tace" kitaso muyi rawa dayake Saudat tasan rigimar Humaid ko kallonshi batayi ba 'amma tana jan hannun Khadija ,saboda daga ganinta saudat taji tashiga ranta sosai da sosai ,humaid kuma damk'e hannun Khadija yayi wai adole bazatayi rawa ba ,fakar idonshi Khadija tayi ta mik'e aka fara cashe rawa ,ganin bai hangota ba yasashi tashi yana lek'e ,hangota yayi kusada mai d'aukar photo ,zuwa yayi ya janyota yana mata kallon soo💖 ammafa 'akwai kishi over, ahaka dai akayi abubuwa kamarsu yanka cake dakuma bada tarihin amarya da sauransu ,ana shirin tashi ne aka sake kid'a mata da maza suna rawa ,Humaid na waya Khadija ta mik'e taje tafara rawa ,cikin zafin nama ya figota yana cewa kinada hankali kuwa ?ko kulashi batayi ba ya rik'e mata hannu suka fice.....





Direct wani katafaren hotel sukaje kayan dad'i yasa 'aka kawo musu ,sunci sun k'oshi daganan ya wuce gurin mai saida kaza tofa🤦‍♀️,


Guda biyu yasiya saboda yasan mutuniyar akwai son cin dad'i ,daganan ya wuce da ita wani katafaren shago kayane na Makkah su dogayen riguna da etc.. cemata yayi kiza6i wanda ranki yakeso cikin zumid'i ta hango wata riga da tun tana budurwa take burin sata 'amma saboda tsananin tsadar 'rigar yasata hak'ura ,yaukam zata gwada d'auka ko zai siya mata ,nuna rigar tayi tace ”nidai wanan rigar nakeso ,Humaid ne yace ”to ita kad'ai ta isheki ?eh tace ” saboda tana tunanin inyaji kud'in rigar cewa zeyi ya fasa ,mik'a rigar yayi ,mai lissafin kud'in kayanne yace”50k take ,cikin ko d'ar yace ”ok yabada ATM aka cire suka wuce,mamaki ne yacikata ,amma babu bakin mgna tayi shiru ,hanyar gidanshi ya nufa da ita ,zaro ido tayi tana kallon ikon Allah ,momy ce take kiranshi a waya ,ganin kiran yasashi cewa osh momyyy ,d'auka yayi ,yace ”momy mundawo fa momy bata yardaba tace ”to yanzu kuna ina? Munje kasuwa yace”a tak'aice hmm momy tace ”to maza _maza kudawo gida ,farinciki ne ya lulu6e khadija ta fara murkishi tana cewa hhh kaza zanciki ina komawa gida ,shiko humaid haushine ya cikashi ganin yaufa momy ta takura masa ,yanzu yasiyo kajin a bati kenan ya tambayi kanshi ,juya kan motar yayi zuwa unguwar su momy ....





Suna isa yayi Horn mai gadi ya bud'e mai ya shige da motar ,khadija ce ta juya ta hango ledar kazar a back side ,saida tafara bud'e k'ofa tukun ta janyo ledar ta ,arce da gudu tana dariya ,wata muguwar yaunwa humaid yakeji gashi Khadija ta d'auke kajin ,kaii yace yana mai d'ora kanshi a booth d'in motar ,





Cikin sanyin jiki ya shige parlor yana mai sallama wucewa part d'inshi yayi ya kwanta idanunshi a rufe amma ba baccin yakeyi ba,yanason su zauna da khadija yaji ko tana sonsa kokuma zata sauya ra'ayi ,amma yana tsoron yimata magana ta taso da 'abinda yariga ya wuce , bacci ne ya d'aukeshi yana cikin tunanin khadija ,wani mumunan mafarki yayi wai ga khadija nan wani mutumi ya rik'e mata hannu sunata gudu, a tsorace ya farka yana salati ,çikin azama yayi part d'in khadija ,samunta yayi tayi bacci akan sallahya gakuma plet d'inda taci kaza ga ragowar kazar a gefe,zama yayi shima ya cika cikinshi sosai sanan yashiga toilet d'inta yayi alwalah yazo ya tada sallah ,yana idarwa ya kwnta ta bayanta ,khadija jin mutum a kusada ita yasata kurma uban ihu tana salati ,lokacin dare yayi sosai dan 11pm na dare ,dady ne yafito shida momy cikin razana ,kai tsaye d'akin khadijan suka nufa ,humaid najin alamun zasu shigo ya shige toilet yana rawar jiki ,ganin harta koma bacci yasasu komawa bayan momy tayi mata 'adu'a ta fice .....


humaid ganin khadija zata iya tona masa 'asiri yasashi komawa d'akinshi babu shiri ...


Dady ne yata humaid da khadija akan maganar komawarta hhh jiyafa humaid kwana yayi yana sallah akan Allah yasa khadija ta yarda ,dady ne yace ”to gareki khadija zaki koma gidan humaid 'd'inne kokuwa ,dogon 'nazari tayi akan hallacin da su momy sukayi mata ko d'an cikinsu albarka gaskiya koda batason humaid bazata iya duban idanunsu tace ”bazata komaba ,sunkuyar da kai k'asa tayi tace ”na 'amince wow kuzofa kuga rawar jiki ko kunyar dady baiyi ba ,ba humaid ba har dady 'yaji dad'i sosai ,albarka yadinga samusu dakuma fatan alkairi da zuri'a d'aiyyiba ,momy ce tafito itama tana tsaye tanajin duk abinda 'ake cewa ba k'aramin murna tayi ba.....



Washe gari wani gyara momy tafara yiwa khadija su dilka ne su tsumi ne dasu garin sha magani dai kala_kala gasu humra da ta jiki data kaya gakuma kayayyakin d'aki da dady 'yasa 'akawo daga kamfani a fitar da na gidan......✍️.




Kwanaki k'alilan khadija ta sauya tayi kyau sosai ,humaid kuwa jira yakeyi ace yatafi da ita 'amma shiru ,hhh yadai fara shawarar ya gudu da ita , saida 'kayi one month da magar sanan momy ta amince yake zuwa gurin khadija washe gari kuwa dady 'yace ”ya tattara matarshi su wuce ,aikuwa kamar yana jira yace ”tafito ,momy ce tace ”ya kara mata one week 'komawa d'aki yayi yana kuka hhh manya, washe gari kuwa ko sallama baiyi musu ba Yakoma can gidan ganin Sabin gyaran da dady 'yasa 'ayi yasashi farinciki....


Yana 'alfahari da iyayenshi sosai da sosai adu'oi yadiga kwararo musu ,yana cikin hakanne yaji ana nocking zuwa yayi bud'e k'ofar yana budewa yaga khairat ce ,tsaki yaja ,cikin k'ufula yace ”mekuma kikazoyi gidana ?"tsaki taja tace ”naje na zubar da cikin kuma yanzu takarda ta nake jira ,cikin sauri yayo kanta ,kome ya tuna ya fasa ,cikin azama tace ”wallahi daka doka hmm kabani takaddata in ficema daga gida ,domin wanan ai bak'inciki ne ace mutane na sonka insunji da igiyar aure a tsakani saisu gudu mtsw ,humaid ne yaje ya d'auko takadda ya rubuta mata 'abinda ta buk'ata ,godiya tayiwa 'Allah daganan ta fice ,shikam ko damuwa baiyi ba tunda Khadijanshi zata haifamai y'ay'a ...


Sati ya cika yaune ake shirye shiryen komawar khadija ,humaid ne yakoma gun doctor Umar akan ak'ara dubashi ,congrat yayimai yana dariya yace ”aci amarci lafiya yanzu kazama normal fa ,dariya humaid yayi yace ”nikam tun yau na d'auki hutu sai wata biyar dariya sukasa ,daganan yawuce gida zuwa d'auko gimbiya khadija ,tana kukan rabuwa da momy ,yashigo momy ce tace ”ka kula min da yarinya dan Allah ,insha humaid yace ”daganan momy ta rakata zuwa mota ,tuk'i yakeyi a hankali ,har Allah ya kawosu gida lafiya tana sauka zata fito ya ,sunkuceta ya goyata ya direta 'a k'ayataccen d'akinta ,ammafa d'akin yayi kyau ,tafad'a cikin zuciyarta ,humaid ne yace ”lovely dan zaki biyoni shine harda kuka ?"murmishi tayi ta nemi gefen gado ta zauna ,soyayya 'kuwa humaid ba bayaba dan jin k hadija yakeyi inta k'ara guduwa bazata dawoba*LADIDIN KAUYE*


Funny & love story


45 _46

Zai iya rasa rayuwar shi lalla6ata yakeyi akan taci kaza 'amma sai wani sharewa takeyi murmishi ne ya su6ucewa Humaid cikin zuciyar shi yace ”kamar ba ita bace kwad'a yayyar kaza ba ,haka yadinga bata 'a baki tana ci tana yanga suna gama ci yace ”taso muje muyi sallah dan nuna godiya ga Allah ,a gajiye take amma batada za6i dole ta mik'e sukaje yin alwalah ,suna idarwa ne yazo yaja musu sallah raka'a biyu sukayi yai sallama bayan sunyi adu'oi masu yawa , ya d'ora hannu a kanta yana yimata 'adu'a ,suna kammalawa ya mik'e ya nufi bedroom d'inshi sleeping dress yaje ya sako ita kuma lokacin tsabar gajiya kwanciya tayi da kayan jikinta ,Humaid bai kulata ba yaja filo ya kwanta 'acan gefe ."

Washe gari bayan tayi sallah ta duba bataga Humaid ba ,jin alamun shigowarshi yasata durk'usawa har k'asa tace ”barka da safiya yaya ,yww barka dai amaryar yaya ,da 'alamu baki damu da yayan naki ba ko ¿sunkuyar da kai k'asa tayi tana wasa da fingers d'inta surarta yai yace ”zomuje mu kwanta bacci nakeji please ya marai raice kamar yaro ,dariya yaso bata tace ”gaskiya not ni yanzu bazan kwanta ba buh wlh wanka zanyi tana magana kamar zatayi kuka Humaid ne ya shige ya barta 'a gurin ,juyi yakeyi baccin ma yak'i d'aukarshi tunani ya fara ,ina murna farinciki na ta dawo ashe akwai problems a gaba oh god Allah kadawo min da Khady kan hanya ."

Breakfast ta had'a musu mai rai da lafiya chips ne na dankalin turawa sau wainar k'wai dakuma tea mai kauri wanda yaji kayan kamshi ,dining room ta wuce dashi kasancewar ankuma gyara gidan ,tana fitowa ta koma kitchen kayan data 6ata ta wanke ta rufo kitchen d'in ,tsintsiya ta d'auko tafara share parlorn tanayi tana hutawa 'a haka ta gama mopping d'in tayi daganan ta kuna turaren wuta ,wani sihirtaccen k'amshi ke tashi a gidan ,bedroom d'inta ta shige ta cire kaya ta d'aura towel ta shiga wanka ,ta dad'e tana wanka da sabulun da momy ta bata mai kamshi tana fitowa ta ciro kayanta , gaban dressing mirror ta zauna simple makeup tayi ammafa ta had'u atamfar ta d'auko mai ratsin wait and black tayi d'auri mai kyau ,kin shiga bedroom d'in Humaid tayi can kuma ta shige da sallama tana cewa yaya Humaid katashi breakfast is ready ohk yace ”dagan ya mirgino yana yimata wani kallo cikin sigar wasa yace ”ke bakisan inda ake tashin miji daga bacci bane ¿" am sorry tace "daganan ta fice, brush yaje yayi daganan yai wanka ya shafa manshi man kamshi ya fito sanye da shadda pink sai d'aukar ido takeyi ,murmishi ya sakarwa Khadyja yace ”lovely mai yasa baki kirani nazo na tayaki ba ¿cikin sanyi murya tace ”nagama ai ,janyo gwangwanin madara da ragowar kayan tea yayi saida ya k'ara komai bacin wanda tasa dagan yace ”to bud'e baki naga 'alamun bakison cin abinci sosai ko ¿shiru tayi daganan tafara cin abincin ,kad'an taci tace ta k'oshi."


Kallonta Humaid yakeyi yarasa mai yasa yarinyar nan yanz bata sakewa dashi ,duk rashin kunyarta da neman tsokana yanz duk sunyi sanyi ,tunani ya shigayi to aure babu hira ina labari ,duk inda naso naga ta fahimceni amma lamarin ya citura ,mik'ewa yai yace ”lovely biyoni ki kar6i wani abu ,cikin sanyin murya tace ”ya Humaid banajin dad'i ynz kaina nayimin ciwo ,subhanallah to zomuje hospital a'a kabarshi inada maganin a d'aki please zani in kwanta ohk yace ”yarasa mai yaiwa khady take wanan slow d'in ,kodai har yanzun bata sonshi ne kwai tabi umarnin Momy da dady ne ,iska ya fesar mai zafi ya bugi bango yana dogon nazari itako tun tuni ta shige part d'inta."



Kwance take tana kallon sama tana tunanin rayuwarta tada 'a cikin gidan hmm da yace ”baya sona yanz kuma yace ”yana sona kai da 'ayar tambaya wlh but naji masoya na cewa in mutum ya k'ika daga frko to karshe koyace yana sonka yai karya , haka ta dinga juyi a bed d'inta tarasa maiyake damunta .


Washe gari ai yuka ta gabatar inda tasaba ko ina ta gyareshi gidan sai zuba k'amshi yakeyi ,yau 7 days da auransu ,nocking taji batayi azamar tashi ba saboda Humaid na nan ,ganin gimbiyar bata tashiba yasashi mik'ewa ya bud'e k'ofar ,su inna Hauwa ya gani ita da wata yarinya zatakai 13yrs a duniya sanye take da rigar banba lasta rigada wando sai hijab da yaji jiki ,inna ce tace ”munsha hanya fa khadija najin muryar inna ta mik'e da gudu tana oyoyo ,Humaid ne ya kar6i kayansu ya shige dashi d'akin bak'i yadawo suka gaisa ya fice sbda ana kiran sallah ,khadija ce tace ”inna kunsha hanya ya su baba ,lafiya Lou inna tace ”tana kalle² khadija ce ta dubi wanan yarinya tace ”inna naso in ganeta amma ta 6acemin ,yarinyar ce tace ”uhm ai wanan daular haka dole bazaki ganeni ba to inkin manta nice sahura waro ido khadija tayi tana duban sahura tace ”wai kece kika girma haka ? Sahura ce ta dubi khadija tace ”to ke kinga inda kika koma ne walahi kamar matan turawannan da muke gani a shagon mai shayi na anguwarmu ,dariya sukasa dukansu ,khadija ce ta shige kitchen sbda yimusu girkin lokacin 11am shinkafa jollof mai kifi da carrot dakuma green bean's dataji alaiyahu lokaci k'alilan gidan ya kaure da kamshi sosai ,Sahura ce tayo kitchen d'in da sauri tana cewa kufa y'an gayu inzakuyi girki bakwa gayya dariya khadija tasa tace ”to a wanan girkin menene abin wahala ?Sahura ce tace ”walhi ku kula saboda ance yawan ciye _ciyen kayan dad'i nasa ka mance da lahira Khadija dai bata kulata ba sai aikinta takeyi ,Sahura ce taga bread a saman fridge tsalle tayi ta d'auko ta yaga tace ”oh sai natuna lokacin da kike cutar mutane ki gudu amma yanzu ana yimiki magana ma sai kinyi ra'ayi ,hmm kawai khadija tace ”sbda hankalinta na kan girkinta."



Khadija ce ta dubi sahura tace ”to muje muyi sallah sai muci abinci ko ?Sahura ce ta yago bread tace ”tabb inma zaki zubo abinci ki zubo dan ni wata shegiyar yunwa nakeji yasin khadija ce tace ”zan zuba miki naki nikam zanyi sallah , tunda khadija ta zubo abinci Sahura ke had'iyar yawu tana lashe baki ,khadija ce ta mik'a mata tare da wani soyayyan nama a kai Sahura ce tace ”ke bakida wayo nikam kawo naman injishi a hannuna kar azo ba'a sawa inna ba tace saitaci ,khadija kam wucewa tayi tabarta a gurin tana tura nama cikin aljihun wando, bayan sun kammalah cin abincin khadija ta kwashe takai kitchen saida ta wanke sanan ta fito ,inna ce ta mik'o wa khadija wani k'ullin buhu tace ”lalle ne da barkono da kuma citta godiya khadija tayi sosai daganan inna tace ”zasu wuce Sahura da ido yai ja tace ”nifa inna kitafi walahi bazan koma k'auye ba kicewa babanmu sai yazo aurena ,dariya suka sa khadija ce tace ”to kizaune in kikayi sati biyu ko uku saiki koma ,tsalle sahura ta doka ta cakumi khadija tana murna ,inna ce tace ”to anta6a yanke hukunci babu mai gida khadija ce tace ai ya Humaid bashida matsala, haka inna ta tafi tabar Sahura ."


Washe gari Sahura ce gaban TV tana kallo a MBC action wani film suke yi mai fad'a suna cikin fadanne wani ya kaiwa dan uwansa naushi Sahura ce ta doka tsalle ta kaiwa khadija naushi har tana neman k'ara mata ,a razane khadija ta dago tana kallon Sahura da hankalinta ya tafi ga TV nuno gurin kuka 'akayi aifa ta zauna tadinga kuka harda gumi ,khadija ce ta tashi ta kashe TV n sallamar humaid sukaji Sahura ce ta dubi humaid tace ”barka mijin ta jikin t b juyiwa yai yace ”to waye ta jikin t b ?kallon khadija data had'e rai tayi tace ”to ai naga yan gayu idan mijinsu ya dawo fara'a sukeyi kekuwa kin wani had'e rai kamar dillaliya anzo cin bahi lolz ,wani mugun kallo khadija ta jefeta dashi shikuma humaid na kallonta baice komai ba ya *LADIDIN KAUYE*


funny & love story

47_48

Ganin abin zuba sharar gidan ya cika mai zuwa kwashewa bai zoba yasata d'auka ta nufi wani guri tafiya takeyi tana dube dube a uban kwandon zuba shara a kanta ,hango wani k'aton kare tayi yana shirin dosota jikinshi duk gashi cikin tsoro tafara gudu

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login