Showing 6001 words to 9000 words out of 39140 words

Chapter 3 - LADIDIN KAUYE

Start ads

24 Aug 2025

239

Middle Ads

k'atoto mik'o mata yaron yayi kunce ledar tayi tanaci tana jefa k'afa yaro ne yagaji da zama yace ba bani kud'in kafin ya k'arasa Ladidi ta buge bakin yaron tace tunda har katambayeni wlh bazan bada kud'in ba kuka ya hauyi yaron tasowa tayi ta kama kunnenshi ta murd'a seda ya kwala k'ara ta sakeshi kana tace daga yau ka karayimin rashin kunya kagani.....✍🏽✍🏽✍🏽








*MOM ISLAM✍🏽✍🏽✍🏽.*

*LADIDIN K'AUYE*


Funny & love story.

*Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa*



*NA*

*MOM ISLAM*

*ZAINAB HABIB*

*MARUBUCIYAR:*

*ZAINABU ABU*



*AND NOW*

*LADIDIN K'AUYE*



*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


*Episode:* 9_10


______malam Adamu ne yakira dadyn su Humaid a waya akan cewar Ladidi zata dawo gurinshi saboda tasami ,ilimi sosai"beyi musuba yace ranar lahadi se su Humaid suzo su d'auketa malam adamu ne yace da muna shirin kawota gobe nida Hauwa dady ne yace to ai babu damuwa duk d'aya ne sekun so Allah yakawoku lpy daganan sukayi sallama".

Inna hauwa ce ta ,tattaro wa Ladidi kayanta had'i da bata kud'in sabulu akan tayi wanki gobe zasu wuce birni aikuwa Ladidi jin haka ta fara murna tana tsalle ta kar6i kudin tafice siyo sabulu tana cikin tafiya ,ta had'u da k'awarta tana siyarda d'anwake gashi Ladidi najin yunwa k'awar ce tace Ladidi barin zuba miki d'an waken saboda tasan inta wuce Ladidi zata iya 6aro da robar d'an waken".

Fara zubawa tayi Ladidi tace ke barshi haka yarinya gobe zamu tafi birni mushi kayan d'ad'i kawar Ladidi ce ,tace nima inason zuwa birni sedai bamuda y'an uwa a birni .


Bayan ta siyo sabulun tafara wanki seda tagama duka sannan ta zauna tana jira su bushe ta ninke ".

Washe gari bayan sunyi sallahr asbh malam adamu yashigo yace su shirya da wuri saboda wuyar mota.

K'arfe goma suka tafi tasha sunyi sa,a wata mota bata cikaba suka shige malam adamu yabiya kud'in motar suka d'auki hanya zuwa jos".

Tunda suka shiga mota Ladidi ta hango wani k'aton arne yana cin Apple lek'enshi takeyi tana lashe baki had'a ido sukayi ta sunkuyar da kai a karo na biyu takuma d'ago kai tayi sa,a shima yad'go suka had'a ido ita kuma Ladidi ganin yanata kallon ta mugud'a mai baki shikuwa yana ganin haka ya bige bakin inna Hauwa ce ta ce kaikuma metayi maka dazaka bigi yar marainiyar Allah .

Da hausar da bata game bakinshi ba yace wanna yariya batada hakali Ladidi ce ta ,tuntsire da ,dariya shikuwa yaji haushin wanan dariya ana zuwa gurin sojoji ya bawa Ladidi 6awon gyad'a yace tazubar mai Ladidi bata ta6a shiga motar da zatayi tafiya me nisaba aikuwa ta watsa 6awon gyd'ar kusada wani k'aton soja suna ganin haka suka tare motar su Ladidi suka ce kowa ya fito da kuma wacce ta watso 6awon gyad'a ".

Ladidi ce tahau zaro ido saboda tana tsoron masu bakin kaya malam Adamu ne yace mekuma mukayi arnen ne yace daughtern kuce ta zubo bawon gyada malam Adamu ya bud'e baki yace ba ita bace".

Koda zamu fito bataci gyad'a ba kuma babu komai a hannun ta Ladidi ce ta nuna arnen tace wlh shine yabani yace in wurgar sukuwa sojoji sun rasa wazasu kama sukace Ladidi itada Arnen su fito suyi tsalen kwad'o .

Sojanne ya k'araso kusada su kana yace ku za6a ko tsallen kwad'o ko ayi muku bulala Ladidi ce ,tace wlh gara ayimin bulala tunda wanan k'aton arnen yajamin bulala biyar sukayi mata lafiyayyu malam Adamu bashida ta cewa kar a had'a dashi yaja baki yayi shiru direban motar sune yaketa masifa .

Ladidi ce tashige mota tanata kuka shikuwa arnen yak'i zuwa ayimai d'ayan sojan ne ya nuno arnen da bindiga da gudu yazo ganin sun saita kanshi.

Tunda aka fara bulalar yafara kuka yana basu hakuri ,ita kuwa Ladidi se dariya takeyi.

Malam Adamu ne yace wlh da tuni mun isa bayan an gama bulalar suka shige mota kowane fasinja yana fad'ar albarkacin bakinci har suka iso well come to plateau .


Kowa ya sauka a mota Ladidi tak'i fitowa seda ta ciro wata allura a kanta lokacin su malam Adamu sun tari adaidaita sahu zasu shiga ta sokawa arnen ta shige da gudu ".

Sun isa 6ukur park G.R.A anan ne anguwar su dadyn Humaid take wato alhaji abdullahi tsaya sukayi a bakin get d'in megadi ne ya lek'o kana yace daga ina kuke malam Adamu ne yace daga kano muke ni yayan mai gidannan ne seda megadi yakira a waya tukun yabarsu suka shige".

Tun daga k'ofar gidan Ladidi ke kallon tsarin gidan tunda tazo duniya bata ta6a kallon kyau da tsarin gida irin wanan ba sekace baza,a mutu ba inna Hauwa ce ta janyo mata hannu suka shige domin malam Adamu yarigasu shigewa.

Da sallama suka shigo itada inna Hauwa k'asa Ladidi ta zauna ina Hauwa a kujera malam Adamu shima yana kujera suna jiran mutanen gidan wata wata mata ce fara sol da ak'alla zatakai shekara arba,in a duniya sanye take da wani dakakken leshi me duwatsu tafiya takeyi kamar wata sarauniya ta iso gurin su inna Hauwa ta nemi kujera ta zauna .

Inna Hauwa ce ta fara gaida hajiya amina hajiya amina batasan inna Hauwa ba amma ganin malam Adamu yasa tagane matar shice bayan sun gaisa hajiya amina ta gaida malam Adamu Ladidi kuwa ta ,tafi a kallon palon dan batasan me akeyi ba seda inna Hauwa tace Ladidi baki iya gaisuwa bane ¿".

Ladidi ce,tace ina wuni hajiya amina tace lpy daughter ya kike shiru Ladidi tayi taci gaba da kalle kallen ta .

Hajiya amina ce ta k'walawa yar aikinta me suna ummi kira dagudu ummi ta k'araso ta durk'usa a gaban hajiya amina.

Cewa tayi kikawowa su malam abinci amsawa tayi da to hajiya ta mik'e ta nufi kitchen jollof d'in taliya ce wace taji kayan lambu sai k'amshi take zubawa da hollondia yogurt me sanyi ta d'oro akan turai ta kawo musu mik'awa malam Adamu tayi takuma mik'awa inna Hauwa nata ta d'auko wani ta mik'awa Ladidi nata da rawar jiki Ladidi ta k'ar6e abincin ta cire cokalin hajiya amina ce ,tace daughter kisa cokalin mana Ladidi ce tace a a wlh da hannu ma ya nak'are bare nasa cokalin.

Bayan dare yayi suyi sallah hajiya amina ta nunawa inna Hauwa d'akin da zasu kwanta suna shiga d'akin Ladidi ta d'are gado tanata tsalle tana cewa wanan aba kamar burodi mu agarinmu babu wanan aba me laushi haka inna Hauwa tana jinta bata kulataba.

Inna Hauwa ce takira sunan Ladidi tsayawa tayi da tsallen tace na,am inna kinsan me nakeso dake Ladidi tace a a".

Kinga kindawo birni da zama tsalle Ladidi tayi tana murna inna Hauwa ce ,tace kirik'e mutuncin ki dan Allah kinga ke marainiya ce kar ,rud'in duniya yasa ki zubda tarbiyarki to Ladidi tace".

Washe gari su Humaid sun shigo part d'in momy take gaya musu suje su gaida matar malam Adamu jalal ne yace ai tun jiya muka gaisa da malam Adamu sedai ,inna bari muje momy ce tace musu amma zaku shigo kafin kutafi ko Humaid ne yace eh insha Allah momy.

Direct dakin da momy tace musu inna Hauwa na can suka nufa sallama sukayi ,inna tana kan sallahya tana lazimi suka shigo gyaran murya tayi musu ,bayan ta shafa adu,ar ne suka fara gaisawa inna tace jiya tunda mukazo bamu had'u dakuba Humaid ne yace wlh inna aiyuka ne sukayimana yawa shiyasa inna ce ta sanya musu albarka suna cikin hira sega Ladidi nan tafito daga toilet da gudu batama lura dasu Jalal ba tahau jikin inna tana ihu Humaid ne yace inna a ina kika samo wanan yarinyar Jalal ne ya zaro ido ganin kamar yarinyar da tabige k'afar Humaid ce ,a zabure Jalal ya mik'e yadubi Humaid kana yace wlh brother wanan yarinyar ce da ta addabi mutanen k'auyen su d'ago kai Ladidi tayi suka had'a ido da Humaid .

Humaid ne yazaro ido yace yaushe zaku tafi ne inna¿" inna Hauwa ce ta washe baki ,kana tace ni da malam yau zamu wuce ita kuma Ladidi anan zamu barta .

Kwata ,kwata Ladidi batasan gidan su Humaid suka zoba sai yanzu ,

Humaid ne ce munshiga uku "inna Hauwa ce ta dubi Jalal da yakasa cewa komai se Humaid ne da keta salati duban su tayi kana tace wanan yarinyar yar uwar kuce dan Allah ku, kula da ita sosai duk cikin su babu me magana suka mik'e suka wuce d'akinsu .

Dayake d'akinnasu a had'e yake Jalal ne yadubi Humaid yace wlh brother ankawo mana bala,i cikin gidan mu.....✍️✍️✍️






Mom Islam ce ✍️✍️✍️

*LADIDIN K'AUYE*


Funny & love story.

*Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa*



*NA*

*MOM ISLAM*
*ZAINAB HABIB*


*MARUBUCIYAR:*

*ZAINABU ABU*



*AND NOW*

*LADIDIN K'AUYE*



*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


*Episode:* 11_12


_____washe gari ,inna Hauwa ta shirya malam Adamu ya aiko jalal ya kirawo ta dan bayason suyi tafiyar dare shigowa inna Hauwa tayi ta sami guri ta zauna dady ne shida malam Adamu suna hira dady ne yace ina Ladidin inna Hauwa ce ta kwalawa Ladidi kira segatanan da gudu ta k'araso dady ne yace sannu baiwar Allah ina kwana tace bayan ya amsa ne malam Adamu yadubi Ladidi kana yace yanzu ,zamu tafi amma inna tagaya miki anan zaki sauna ko ¿"Ladidi tana murna tace eh ta gayamin malam Adamu ne yafara yimata nasiha da fad'a akan tarbiya dakuma tayiwa su dady biyayya to tace musu daganan suka mik'e Humaid ne da Jalal suka shigo suka durk'usa suka gaida malam Adamu shida dadyn su ".

Mik'ewa sukayi sega momy nan d'auke da wata leda mekyau ta mik'awa inna Hauwa godiya inna Hauwa tayi mata daganan suka fito waje" Ladidi ce ,tace inna yaushe zaku dawo"ina Hauwa ce tadube ta da alamun tausayawa tace karki damu zamuzo dubaki Ladidi bata nuna 6acin raiba saboda tana son zaman birni "Humaid ne yatada mota suka shiga dady ,yaciro dubu goma yabawa malam Adamu godiya malam Adamu yadinga yiwa dady daga nan suka fice daga gidan suka zarce tasha suna zuwa suka shige mota se kano.


Ladidi ganin babu wanda tasani acikin gidan yasata yin sanyi gashi yunwa takeji tarasa inda zatasa kanta tagumi tayi seta fara tuno inna Hauwa da acan k'auyen,nne da ko tuwo ne taci sau biyu su nan idan aka bawa mutum shayi da burodi abincin rana se k'arfe d'aya na rana" dady ne yazo wucewa yaga Ladidi a kan dakalin wucewa palon tazuba uban tagumi "dadyne yadube ta kana yace Ladidi meke faruwa ne Ladidi da tarasa abinda satace seta k'ak'alo karya tace dama narasa d'akin dazan shiga ne dady ne yarik'e hannunta ya nuna mata d'akin da suka kwana jiya yace nanne d'akin ki ,kinji to tace mai shikuma yafice daga part d'in ,nata.


Tunda tashiga taji kamar an karo yunwar ne juyi tadingayi a katifa yar aikin gidan ce wato ummi tashigo da tiren abinci doya ce da miyar k'awai se lemon gora fanta da sauri Ladidi ta diro daga kan gadon ta kar6i abincin ita ko ummi mamakin ci ,irinna Ladidi takeyi " ko wanke hannu batayi ba tadinga tura doyar tana kur6ar ruwa seda taciye duka sanan takoma kan miyar kwan tana ta lasa tarasa miyar menene amma dai koba komai tayi dad'i tak'yar ta mik'e tanufi bayi kashine ya matseta seda tashiga ta tuna tunda suka zo batayi kashi ba seyau lek'a bayan gidan tadingayi kozataga masai "ina sewata kwalba fara mekamada kujera sekuma baho a gefe shima na kwalba .

Ihu ta kurma saboda kashi na neman zubo mata da gudu momy tashigo d'akinnanta taduba bata ganta ba k'wala mata kira tayi momy ce taji Ladidi takuma kurma ihu k'ofar toilet d'in ta ,tura ganin Ladidi a zaune tana ihu tayi" k'arasawa kusada ita tayi kana tace Ladidi meke faruwa tundaga room d'ina najiyo ihunki Ladidi batasan room ba sedai cewa tayi kashine ya matseni wlh na kusa yi a wando momy ce ta rik'o mata hannu ta mik'e nuna mata inda zata zauna tayi Ladidi gani takeyi kamar zata fad'a ciki se zaro ido takeyi kamar an tare kwarto.

Yau watan Ladidi daya a yaune dady ,ya samowa Ladidi makarantar primary a class 5 aka sata kasancewar sunje anyi mata interview tanada basira bazatayi wuyar d'aukar karatu ba "tunda tafara zuwa makarantar bata shiga sabgar kowa ,wata rana suna zaune a class teacher yashigo yace a fad'a mai masu ,surutu kowa a class d'in Ladidi yanuna kasancewar tunda tashigo school d'in ba,a ta6a kawo k'ararta ba ai kuwa malamin ya kamata yayimata duka sosai seda yafasa mata farcen baban dan yatsa" kuma tasha alwashi seta rama tunda yanaso tadawo Ladidin k'auye .


K'arfe hud'u na yamma dady ,yakirawo Humaid yana gurin aiki akan yaje ya d'auko Ladidi a school ranshi ba k'aramin 6aci yayi ba amma babu inda ya iya dole ya ajiye abinda yakeyi yaje d'aukarta babu kowa a school d'in kowa yatafi gida se teachers dasuke office suna ta ttaunawa tana hango motar Humaid gabata yashiga bugawa shigewa baya tayi seda yatada motar ya daka mata tsawa yace ubanwaye drivernki fitowa tayi saboda yunwa takeji dukda anbata kudin break amma ,a banza.

Tun kafin takoma gida take ciwon ciki sosai tarasa inda zatasa rayuwarta Humaid ,da yalura da halin da take ciki seya rud'e ko magana bata iya yi hospital d'inshi ya wuce da ita wani d'aki ya kaita da babu kowa aciki se karar Ac daketa bada iska yaje siyo mata abincin turo k'ofa yayi yaga jini yana zuba zaro,ido yayi yadubi Ladidi da ko motsi batayi seda ya,yayyafa mata ruwa kana ya murd'e bakin ,nata ko kulashi batayi ba dan ita kad'ai tasan wahalar da takesha alura yayi mata daganan yafice d'auko mata magani wayarshi ce take ringing dady yagani d'agawa yayi dadyne yace ina Ladidi Humaid cikin jin nauyin maganar da zegayawa dady yace gatanan a hospital zaro ido dady ,yayi kana yace meke faruwa da ita Humaid ne yakasa yiwa dady bayani yace am dady in momy na kusa please kabata wayar dady ne yahau banbamin fad'a kana yace ubanme kayi mata dabazaka fad'amin ba itako Ladidi hatta jinin da yazuba a jikinta duk bata sani ba tunda tana farfad'owa daga suman datayi yayi mata allurar bacci .

Dadyne rai a 6ace yamik'awa momy Humaid ne yace momy zakizo hospital d'innne¿" eh momy tace gamunan nida dadynka"hijab momy ta d'auko zuka nufi hospital d'in Humaid itada dady da isarsu direct office d'inshi suka wuce dady ne ya nannad'e malun malun din'shi yace to gamu maunzo nace uban me kayiwa yar mutane momy ce ,tace katsaya a tambayeshi mana kanata fad'a Humaid dai yakasa magana dan yana ganin kamar inya cewa iyayenshi Ladidi tafara period zasuce bashida kunya" sunkuyar da kai k'asa yayi kana yace 6atan wata tafara kuma yau d'inan momy ce tadubi Humaid tace to wanan shine abin 6oyewa dady ne yanemi guri ya zauna yace to yanzu tana ina Humaid ne ya mik'e yace kuzo muje d'akin "suna zuwa suka samu haryanzu tana bacci momy ce takalli fuskarta hak'ik'a tayi rama sosai Allah sarki.


Momy ce ta ,tambayi Humaid kasiyo mata pad kuwa eh yace kana yabawa momy ledar harda sababin pants yasiyo mata dady bece komai ba yana tsaye yazuba hannu cikin aljihu.

Farkawa tayi taga su momy a kanta tuno ciwon cikin datayi ne a mota sekuma taga jini a zaninta zaro ido tayi tafara kuka dady ne suka fice shida Humaid momy ta k'arasa gurinta tayi mata bayani dakuma inda zatayi ta gyara kanta momy tayi mata fad'an sallah akan lokaci " bayan ta gama shiryawa ne momy takira Humaid a waya tace yasiyowa ladidi riga ko doguwa ce "be jima ba segashi da rigar "dayake basuda nisa da masu saida kayayyaki".

Ruwan zafi yasa akawomata bayan tafito daga wankan ta kintsa kanta suka nufi gida momy a motar dady suka tafi shikuma Humaid da Ladidi suka tafi tunda suka fara tafiya talura da kallon da humaid yake yimata amma seta basar".



*BAYAN SHEKARA DAYA*

Ladidi na hango takuma kyau tayi haske tayi k'iba sosai gashi tafara jin turanci kuma tadena wauta irinta yan k'auye " samarine da ita sunkai biyar amma Humaid na ganinsu seyace anyi mata miji "itadai Ladidi batasan hujjar yin hakanba " tagama primary yanzu tana jss 2 komai nata yak'ara baiyana ".

Batada abokin shawara inba jalal ba duk wata damuwa tata yasani basa shiri da jalal " wata rana tana cikin tafiya zataje gidan wata k'awarta ta had'u da wani saurayi kya kyawa yana cikin mota ita kuma tana tafiya a k'afa"baya yayi da motarshi yace ya ,yammata ina magana kink'i kulani cigaba tayi da tafiya jitayi ya rik'o hannunta a zabure ta juye dan tunda take babu namijin da yata6a gigin rik'e koda gefen mayafinta ne........✍️✍️✍



✍️Mom Islam ce

*LADIDIN K'AUYE*


Funny & love story.

*Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa*



*NA*

*MOM ISLAM*
*ZAINAB HABIB*


*MARUBUCIYAR:*

*ZAINABU ABU*



*AND NOW*

*LADIDIN K'AUYE*



*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


*Episode:* 13_14

___durk'usawa yayi a gabanta yace please beautiful ki saurareni wlh tunda naganki naji nasami matar aure ko banyi miki bane Ladidi ce ta yamutsa fuska kana tace bancema haka ba"mik'ewa yayi yace sunanan Amar jitayi sunan yayi mata d'adi sosai Ladidi ce ta fad'amai asalin sunanta wato khadija wow Amar yace daganan yace kozan iya d'aukar ki a mota ,ta eh tace babu damuwa daganan ya maidata gida sunyi musayar number tashige gida mom ce take tambayarta daga ina take cewa tayi daga gidansu yar ajinmu ne naje dubota babu lpy momy ce ,tace to kiyi sallah kici abinci semu shiga kitchen ".

Bayan tayi sallah taci abinci ta d'auko wayarta tana duba massage number Amar tagani ya rubuto mata sak'on" kin budewa tayi saboda batason seta fara karantawa momy ta kirata kuma taga sak'on da yawa tana shirin tashi tajiyo kiran momy amsawa tayi ta jona wayar tata a charge ta,tafi kiran direct kitchen tawuce tasami momy tana

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login