Showing 15001 words to 18000 words out of 39140 words

Chapter 6 - LADIDIN KAUYE

Start ads

24 Aug 2025

242

Middle Ads

cikin zuciyar shi kuwa ji yakeyi kamar yaje yai hugging d'inta tunda matsayin da 'a gurinshi yayi kawai sai ya had'e rai ,ya dubeta tana neman gurin zama yace"keee!!saida gabata ya fad'i tashi ki gyaramin d'akina baki iya gaisuwa bane ?"na iya tace"a tak'aice ,Humaid ne yace "to kullum zaki dinga zuwa gaisheni ko sau goma zan fita kuma in dawo ,to kawai tace" ganin yayi hanyar dining ne yasata k'arawa da gudu ta kwashe kulolin tayi d'akinta dasu ,key tasa ta rufe k'ofar.....✍️✍️✍️.




*~MOM ISLAM CE~*
*LADIDIN K'AUYE*


Funny & love story.

*Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa*



*NA*

*MOM ISLAM*
*ZAINAB HABIB*


*MARUBUCIYAR:*

*ZAINABU ABU*



*AND NOW*

*LADIDIN K'AUYE*



*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


*Episode:* 23_24



_____Saida ta tsince naman kaff tukun ta ci tuwon bayan tagama cine ta fito da ragowar parlor, bata lura da mutum a parlorn ba direct ta wuce dining ,saida ta 'ajiye kular ta hango shi yana kan doguwar kujera maicin mutun uku ,zata ruga da gudu ya daka mata tsawa yace"kee!!zonan zataci gaba da tafiya ya mik'e da gudu ya janyota ya wurgata gefe kana yace "wuce ki dafamin dambu,zaro ido tayi kana tace"me kuma mai suna haka?".


" Cewa yayi ubanwa zaki rainawa hankali ¿"cikin jin tsoro da fargaba tace"ni ba rainama hankali zanyi ba ,gani 'nayi ban iya ba shiyasa nake tambayar ka, tsawa yakuma daka mata saida ta tsorata yace"kin zo bariki kin manta da shan garin kwaki ko ?"to kitashi ki goge gidannan kuma kar in dawo insami akasin hakan, haka ta shiga bedroom d'inshi tafara wanke toilet sanan ta dawo gyara bed d'inshi tayo kan TV da sauran kayan kallon ta gogesu kana ta dawo tafara shara tana gamawa tayi mopping, bayan ta gama ne kawai tad'an kishingid'e a gefen bed' d'inshi saboda wata gajiya da tayimata sallama ,bacci ne mai nauyi ya kwasheta 🤭nikuwa nace"anci an k'oshi zaki gane, jin shiru har tayi 1 hour bata fito ba yasashi kashe kallon daya kunna kana ya wuce bedroom, samunta yayi kwance tayi d'ai_ d'ai ,zaro ido yayi kana yafara tunanin irin muguntar da zaiyi mata."



D'auko alurar malaria yayi wacce yake ajiyewa 'a gida saboda koda wata matsalar zata taso, bayan yagama zuba magungunan dayasan Khadija zata bada labari ,komawa yayi kusa da ita yana k'are mata kallo can kuma yaji muguwar tsanarta tana kuma baiyyana cikin zuciyar shi.



Tunda 'akayi bikin Humaid 'da Khadija babu wanda yayi k'ok'arin kiran su momy gashi yau har kwana biyu da wuni saidai momy na 'aiko da 'abinci kullum ,amma hakan bai sata kwanciyar hankali ba , kiran Jalal tayi a waya yana d'auka tace" dan Allah kazo inason ganinka .

"Cewa yayi momy lafiya dai ko ?"lafiya tace masa daganan ta kashe wayar ba'adau lokaci mai tsayi ba saiga Horn d'in motar Jalal nan kasan cewar baya gida ,yana shigowa tun daga parlor yafara k'walawa momy kira yana cewa momy gani na iso, sako tayi daga matatrakar dake tsakiyar d'akin tace"gidan Humaid nakeson kaje inasan kadubo su ko lafiya ,itadai Khadija nasan batada waya , dariya ce taso ku6ucewa Jalal ganin damuwa k'arara 'a fuskar momy sun kuyar da kansa k'asa yayi kana yace" momy lafiya suke saboda da babu lafiya 'ai dakinji , momy ce ta d'ake tana masifa tana cewa yanzu ka nuna ban isa dakaiba kenan ko?"to walhai tun wuri kaje ka dubomin su kokuwa ranka ya 6aci !!Dady dake saukowa daga bene yace"karka kuskura kaje gidan su , nagaya maka d'ago kai momy tayi tana kallon fuskar dady _dady dake magana cikin bada umarni yace "ka koma gurin aikin ka, to Jalal yace" batare da yakalli k'wayar idon momy ba."



"Momy ce takalli dady can kuma tayi k'asa da murya tace"haba habiby maiyasa kayi hakan?" tana dad'a matsowa kusa dashi , dady ne ya kawar da kai alamun maganar da momy tayi d'azu nazuwan Jalal gidansu Humaid ya 6atamai rai, k'arasawa kusa dashi momy tayi kana tace"haba mana mijina banason fushinka ta kuma marai raice fuska kamar zatayi kuka tace" please afuwan habiby, hugging d'inta dady 'yai tare da janyota jikinshi a lokacin da yake k'ok'arin zama akan d'aya daga cikin kyawawan kujerun,dasuka haska parlorn ,dady ne yake rad'awa momy a kunne yana cemata walhai Aisha saboda salonki dakuma siye zuciyata da kyawawan kalamanki yasa nak'i k'aro aure amma badan hakaba da yanzu matana hud'u .



Tunda ya gama had'a komai ya bud'e mata gefen hanunta jitayi abu na shigarta kamar'ruwa kasancewar ko a hospital ne kowa nason alurar shi saboda batada zafi,haka yayi mata 'alura tana bacci ,jin alamun kamar ana tsikarin ta yasata saurin motsawa, Humaid na ganin haka ya koma parlor saboda karta gane ,tun tanajin abin kad'an har tazo tanajin k'ai k'ayi sosai, inta Sosa k'afa saitaji a kunne inta sosa kunne saitaji a baya ,haka tadinga susa kamar mahaukaciya ganin lamarin yafi k'arfinta yasa tafara ihu tana tsalle tana cewa wayo Yadikko,
da gudu ta fice a d'akin tayi d'akinta tana tsalle ,rasa 'abinda yake yimata d'ad'i tayi ganin batada mafita yasata d'auko farar hoda ta cire kayan jikinta duka ta shafe ko ina na jikinta ,ganin abun babu sa'a yasata cewa yaya Humaid!!,
"Kazo ka temakeni walahi narasa inda na kwaso k'ai k'ayi ,shiko Humaid ganin tana magana tana soshe _soshe yasashi sakin killer small yace" to yanzu mekikeso inyi miki nikuma ?"kije wanda yafara ganin komai ,ya baki magani ,tana susa tace"bangane ba sokakeyi kacemin 'ni mazinaciya ce?!!! menayi ma dahar zaka k'ullamin wanan mummunan sharin oho yace"daganan yabarta tana soshe ssoshe.



Tana kuka tana susa wani gurin har yayi rud'u rud'u tsabar susa tausayin da tabashi ne yasashi shigowa ya mik'o mata magani k'waya biyu yace"ta shanye duka ,babu musu ta k'ar6a tanasha ba'a d'au lokaci masu tsayi ba ,bacci ya kwasheta , said a ya koma d'akinshi yadinga dariya yana k'arawa saboda ya 'ajiye CCTV a bedroom d'inshi kuma bakowane zaisan akwai CCTV a d'akin ba ,kusan k'arfe hud'u na rana ta mik'e had'e da salati a bakin ta ,wata masifaffiyar yunwa takeji mik'ewa tayi ta nufi kitchen tana shiga taji k'amshin indomie jollof ,bud'e murfin tukunyar tayi ganin kayan k'wad'ayin da 'aka samata yasata zaro ido k'wai ne dafaffe sai karas ,abinka da gidan kwad'ayi ai dandanan taji ranta ya biya tuno mai girkin tayi wato Humaid tsaki tayi kana ta sunkuci tukunyar tayi d'aki ,bathroom ta shiga seda tayi wanka tayi brush sanan ta fito ta zauna 'a gaban dressing mirror tana shafa mai tana wak'a tunowa tayi ai bata kulle k'ofa ba ,dagudu ta mik'e taje tasa key tadawo taci gabada Kwaliya bayan ta d'au makeup mai kyau ta ciro shadda bugaggiya mai ruwan coffee tasa takuma ciro bra da pant da warwaro da sark'a wow ba k'aramin kyau tayi ba ,zama tayi gurin tukunyar indomie tafara baiwa cikinta rabonsa saida taci ta k'oshi tayi gyatsa sanan ta mik'e tayi gurin madai daicin fridge d'inta taciro hollondia mai sanyi ta kkora."


Daganan ta 6oye tukunyar .




Yana fita direct kitchen yanufa ganin baiga tukunyar daya d'ora ba yasashi zaro ido had'e da dogon tunani ,komawa parlor yayi ya murd'a handle d'in k'ofar jin a kulle yafara tunanin kodai Khadija ce ta d'aukemai hanyar d'akinta ya nufa jin k'ofar ansa key 'yasashi cewa "wallahi koki bud'emin kokuma duk lokacin da kika fito sainayi maganinki , tanaji yana sababi amma fur tak'i fitowa ,gajiya yayi da tsayuwa , komawa d'akinshi yayi ya watsa ruwa daganan ya fito yayi shirin tafiya gurin cin abinci .

Tanajin k'arar motarshi ta fito rik'e da gyale a hannunta dakuma takalmi mai tsini yiwa drivern gidan "magana tayi da saurinshi ya taho ya durk'usa 'a gabanta yace " hajiya Mota zakishiga ?"eh tace"daganan ta shige mota suka nufi 6ukur park wato anguwarsu momy ,murna take sosai kamar mai shirin tafiya hajji ,suna isowa kusada gate d'in drivern ta yafara horn mai gadi ne yaje ya bud'e mai daganan suka kutsa ciki ,suna sauka ta ruga ciki da gudu,turuss tayi ganin Humaid zaune yanacin farfesu ,zaro ido tayi tana jujuyasu shikwa yiyayi kamar bai ganta ,fakar shi tayi ta shige bedroom d'in momy da gudu ....✍️✍️✍️.



~MOM ISLAM CE~✍️.

*LADIDIN K'AUYE*


Funny & love story.

*Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa*



*NA*

*MOM ISLAM*
*ZAINAB HABIB*


*MARUBUCIYAR:*

*ZAINABU ABU*



*AND NOW*

*LADIDIN K'AUYE*



*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


*Episode:* 25_26



_____Samun momy tayi ta fito daga wanka ,dagudu taje ta rungume momy saikuma ta fara kuka Momy datake murna saikuma 'annurin fuskarta ya disashe kasancewar taga Khadija na kuka ,janyota momy tayi zuwa bakin gado bayan sun zauna ne "momy take tambayarta tare sukazo da Humaid ne ?" saboda taga Humaid 'din bai dad'e da zuwa ba ,Khadija ce ta share hawayen ta tace"momy babu komai kawai farincikin ganinki ne ,badan momy ta yarda ba tace"to nima nayi farinciki da ganinki my daughter ,saidai naga kin rame sosai kodai da wata matsalar ne? a'a tace" Momy ce tace"to gyramin gaban mirror d'innan ,to Khadija tace" tafara 'abinda momy ta sata momy tayi hakane domin tasami damar zuwa gurin Humaid saboda shid'in ma ya rame sosai,bayan momy ta fita ne Khadija tace" na shiga uku gara da ban fad'awa momy komai ba da walhi zata iya fushi da Humaid.


"Momy nazuwa parlor tasamu Humaid na danne _danne a waya yana ganin momy 'ya d'ago kai yace" barka da fitowa momyna dafatan kin fito lafiya ? Lafiya lau momy tace"Allah yayi albarka cike da kulawa yace amen momy _momy ce takai dubanta ga Humaid tace"amma dai kuna zaune k'alau ko?"cikin rawar baki yace"eeh eeh lafiya Lou ,momy ce tayi murmushin su na manya tace"bakwa zaune lafiya Humaid a zabure Humaid ya kalli momy 'yace ita Khadijan ce tagaya miki haka ? ko d'aya momy tace"daganan kuma duban Humaid a karo na biyu saboda 'akwai abinda take karanta "cewa tayi karka manta yarinyar nan marainiya ce bamu baka ita dan ka cutar da ita ba kuma na fuskanci ko a lokacin auran kayi farinciki amma metayima dahar zaku dinga cutar da rayuwar ku?" sunkuyar dakai yayi kana yace nikam 'momy saidai kiyi hak'uri dani dan wallahi bazan ta6a son Khadija ba kuma wlhi ko meye ya wanketa zaro ido momy tayi had'e da d'an gutun hawaye tace"ni Humaid kake gayawa wanan kalmar ni ko kukane ya kufcewa momy cikin k'araji tace tunda kazo.duniya bamu ta6a musu dakai ba 'amma zuwa yanzu ne zakace zamudinga musayar yawu dakai ,hak'uri ya shiga bata ganin bata kulashi ba yasa ya durk'usa kan guwaiwar shi yana bata hak'uri,ko kallon shi momy batayi ba ta mik'e cike da matsanancin 6acin rai tace "wallahi wallahi inhar ka cuci Khadija 'Allah ya isa tsakanina dakai!!!."


Cikin firgici ya d'ago kanshi da yayimai nauyi yace "ni momy kike yiwa mugun baki " nafad'a nace nafad'a kozaka mareni ne tunda yanzu ka isa yiwa kanka komai "momy tace" cike da takaicin halin da takeciki, komawa tayi cikin bedroom ta sami Khadija ta zuba uban tagumi girgiza kai momy tayi daganan tace"kitashi kibi mijinki ,Kadija ce ta dubi fuskar momy tace"momy maiya faru naga kamar kuka kikayi ?cikin sasanyar murya momy tace "ba kuka nayi ba kwai raina ne ya 6aci ,adu'a Khadija tayiwa momy daganan ta d'auko mayafinta ta fice, bata sami kowa 'a parlorn ba hakan yabata damar wucewa parking spice da sauri jin anata kiraye _kirayen sallah magrib yasa ta k'walawa drivern daya kawota kira jin shiru bai zoba yasa fara jin haushi tafara cewa kodai'in kar6o keyn mota ta ne?komawa tayi tace" momy bani mukullin motar da dady 'yasiyamin 'nabaki ajiya ,momy ce tace"ina mijinnaki yayi ?"cewa tayi ya tafi wlh kuma driver ba banganshi ba ,d'auko mata momy tayi daganan tayiwa momy sallama ta wuce mota .



Ganin motar a lulu6e yasata yayewa ta shige da bismillah ta fita daga cikin gidan tahau titi ,tafiya takeyi cike da kulawa har Allah yakawota gida lpy, da saukarta ne taga Humaid bai dawo ba hamdala tayi daganan ta wuce kitchen ta d'ebo kayan shayi duka har indomie kwali biyu ta d'ibo kwai kuma ciko kwali tayi kasancewar yafi k'arfin abin d'ora k'wan a cewarta tadena fita mancewa tayi bata d'auko abin girki ba zuwa tayi tana tunanin da gas da electri wane zata d'auka ,kinkimo gas tayi tana cikin tafiya ne taji alamun dawowar Humaid ,cikin azama ta ruga dashi d'aki tana nishi ,ta rufe k'ofar da key.



Yana shigowa da sallama 'a bakinshi ya doshi k'ofar d'akin Khadija jin ta rufe k'ofar ne yasashi k'wafa yace"wallahi tunda kikaje kika had'ani da momy na wallahi saina miki jina jina ,tana daga d'aki tana yimai gwalo haka yagama sababin shi ya fice ,yayi d'akinshi".






Bayan Khadija tayi sallah taji wata fitinanniyar yunwa na mata sallama mik'ewa tayi ta kuna gas duba tukunyar dazata d'ora ruwan zafi tayi bata gani ba zaro ido tayi tana salati tace yanzu ni mezanci d'anyan k'wai kokuma d'anyar indomie kokuma lifton zanci? babu madara babu sugar ?wayo Allah na nashiga uku ni LADIDI!!.tasa indomie a gaba tayi ta farke leda d'aya tanaci tanashan ruwa kasancewar lemu ya k'are a d'akinta bayan tagama cine tayi ,isha 'I daganan ta haye gado bayan tayi addu'oin dasuka zamemata wajibi ta kwanta badan ta k'oshi ba , asbha ta gari.
Washe gari bayan tayi sallahi ta mik'e tanason fita tanajin tsoro ,shiko gogan tunda yadawo daga masallaci ya zauna ' a parlor ya kunna TV kuma yaune komawar shi gurin aiki wato hospital d'inshi dan tun dare ake ta yimai waya'akan anason ganinshi ,shi burin shi bai wuce yaga ya illata Khadija ba ,ita kuma Khadija tak'i fitowa saboda tsoron Humaid ,gajiya yayi da zama duba 'agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunshi yayi ,k'arfe goma da rabi 10:30 bai fita ba duk akan wanan shegiyar yarinyar?"yake tambayar kanshi tsaki yaja ya fice zuwa bedroom d'inshi wanka yayi yana fitowa yaga har sha d'aya tayi 11:am zaro ido yayi ,kamar maijin kashi ,shiri yakeyi jikin gaggawa kamar mai tashi sama da sauri yayi waje gurin motar shi , ya tayar ya mik'i hanya".


Tanajin fitarshi ta fito da gudu tayi d'akin shi ganin kayayyakin daya siyo tayi zaro ido tayi tace"shiyasa ko ya nemi abubuwan dana d'ebo tabb aikuwa saina kwashe wa in an ma ,fara jidowa tayi tana haki ta kwashe kayan abincin dukka harda su carton d'in maltina dana madara dakuma k'wai duka ta kwashe tana dawowa taga wani kayan ganin jikin kwalin anrubuta golden ai kawai ta loda takai d'aki a ranta ko tana cewa shikenan 'na huta da girki ko lemon kwalba ma ya isheni, kitchen taje ta d'auko tukunya da wuk'a dakuma mangyad'a da kayan miya tadawo d'aki tasa key .


Misalin k'arfe biyar na yamma yadawo a gajiye ya shige toilet ya watsa ruwa yana fitowa kwai yaji yana sha'awar shan golden beer zuwa inda ya 'ajijiye kayan yayi ganin baiga komai ba yasashi zaro ido ,cikin kunar 'rai yace "wato wanan tsinanniyar bacin zina har giya takesha?" zama yayi a bakin gado yadinga girgiza k'afa yana bala'i arayuwa bayason a d'auki abinshi ba'a tambayeshi ba ,cikin masifa yafice daga d'akin 'nasa yana zage zage kuma ya kudurta 'a ranshi ko k'ofar zata 6alle yau saiya ci uban Ladidi ,yana zuwa yaji kamar kullum k'ofar a rufe take da key dukan k'ofar yakeyi kamar mahaukaci amma tak'i bud'ewa itako tana tsoron karfa ya 6allah k'ofar nan yazo yakusa kasheta dan yau kamar yasha ya bugu,shigewa cikin drower tayi tanata zaro ido kasancewar akwai gurin sa sak'ata ta ciki kuma tanada zurfi ba lallai mutum ya bud'eta da garaje ba....✍️✍️✍️.



Mom Islam ce


*LADIDIN K'AUYE*


Funny & love story.

*Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa*



*NA*

*MOM ISLAM*
*ZAINAB HABIB*


*MARUBUCIYAR:*

*ZAINABU ABU*



*AND NOW*

*LADIDIN K'AUYE*



*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


*Episode:* 27_28



_____Cikin k'arfi ya bigi k'ofar har saida ta bud'e tsayuwa yayi yana maida nunfashi kasancewar k'ofar bata ra'go bace ,kutsa kai yayi cikin d'akin yana haki yana cewa inakike dan ubanki yau saina karyaki ,dube dube yakeyi amma ina baiganta ba bud'e toilet yayi nanma bata nan rik'e k'ugu yayi kamar mace yanason yaga ta inda zata bullo amma inna ko alamun ta baigani ba, wata muguwar tsawa ya daka, Khadija dake cikin kaya saida ta firgita 'amma dayake tasan tayi lefi ko k'ok'arin guduwa batayi ba , ficewa yayi da gudu yaje ya d'auko wani key a d'akinshi yazo ya kulle k'ofar a tunaninshi ta fice yawo ne, yana fita ta fito.daga ma6oyar ta sai gumi take sharewa ,zuwa gurin kwalayen data d'ibo tayi ganin golden beer dama tasa biyu a fridge ta bud'e ko karantawa batayi ba ta hau sha jin zak'i zak'i yasata lumshe ido ,tanagama sha ta wurgar da gwangwanin ."



Luuu tafara gani wata zabura tayi tafara maganganu tanacewa wai naga kamar duniyar tak'ara haskene tabb naga ta kaina yaukuma gashi goma na dare amma basai ankunna fitillah ba tafara layi tana surutai ,gyatsa tayi tace"sweet lemu kamar nasha zuma kai firig zonan kabud'e in k'ara ,ganin dai fridge bashida niyar zuwa yasata mik'ewa tana layi ta bud'e zata d'auka tafad'i k'asa tana cewa to wane mugunne kuma yake k'ok'arin ganin bayana?"can kuma tasa dariya tace"ni wallahi nagaji da wannan duniyar kuzo ku kaini duniyar ku.

Jin alamun bud'e k'ofa yasata zubawa da gudu yana bud'e k'ofar yad'n matsa yana so ya kamota aikuwa ta fice da gudu tayi kitchen tasa sak'ata lokacin tafara dawowa hayyacin ta ,baibi takan d'akin 'nataba bare yaga 'abinda tasha hannu ya buga'a bango yanacewa kokuma 'ajanun k'auye sun shafeta ne shiyasa take 6acewa?"can kuma ya mik'e yayi d'akinshi jin ana kiran sallahr mgrib , bayan yayi alwala ne ya kulle gidan ta baya ya wuce masallaci ,Khadija najin fitarshi taja jiki tana tafiya tana layi tayi d'aki ,ganin gwangwanin madara yasata bud'ewa

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login