Showing 3001 words to 6000 words out of 39140 words

Chapter 2 - LADIDIN KAUYE

Start ads

24 Aug 2025

236

Middle Ads

,tara da kwana goma Allah ya albar kacesu da samun k'aruwa kya'kyawan yaro me farin jini ya taso cikin gata da nuna kulawa ,kwatsam tana yaye Humaid se cikin jalal Allah yara bata da cikin lpy anyi hidima sosai tundaga lokacin aihuwa ta,tsaya mata .


*_BACK TO STORY*_
Bafula tanin ne ya d'auko jar, kar ,ruwan shi ya shek'a mata duka a jiki ware idanu tayi kana tace ,wai shin idan mutum ya mutu yana dawowa ne bafula tanin ne ya dube ta kana yace tunda kinga yanzu kindawo ba.

Shirin muguntar da zata yiwa bafula tanin takeyi sandar ,da ya buga mata ,ta d'auke ta ruga a guje .

Shikuwa bafula tani basan gidan su Ladidi ba yaro ne yazo wu cewa kiran shi yayi kana yace kasan gidan su Ladidi¿" yaron ,ne ya d'aga kai ,kana yace babu nisa ai bafula cewa ya yi to don Allah zoka ,rakani .


Barin shanun yayi suka nufi gidan su Ldidi yaron,ne ya shige cikin gidan ya diko ya samu tana shara gai sheta yayi kana yace ana sallama da Ladidi yadiko saboda jin dad'in yar tata zata fara zuwa hira ta ce kace gatanan fitowa .

Yaron ,ne Yakoma ya gayawa bafula tanin wai gatanan zuwa .

Ladidi ce ta fito daga d'akin yadiko tasha kwaliya in kagan,ta kace sabuwar aljana washe hak'ora tayi kana tace yadiko nayi kyau ¿"

Yadiko ce ta jin ,jina mata ,kana tafara yimata kira ,ri.


Kaga yar gidan yadiko ,washe bakin ta kumayi tana dariya.

Lek'awa tayi dan taga me sallamar hango shi tayi ,yana ta dunk'ule hannu kamar me shirin kai naushi .


K'ara mai da hanka linta tayi gurin sauraran abin dayake cewa jitayi ya na fad'in wlh tana fitowa zan ,zuba mata naushi .

Itako Ladidi jin haka yasa ta koma gida yadiko ce ,tace har kin dawo ¿".

A, a Ladidi tace kana ta shige d'an k'aramin d'akin ta ,,ta d'auko sandar bafula tanin ta dawo ta la6e kusa da inda yake zaune seda ta dede,ci ya juya baya ai kuwa ta d'aga sandar ta sheme shi fad'uwa k'asa yayi ita kwa Ladidi gaba ta k'ara ta barshi ,shida sandar shi a gurin yakasa tashi yana ta ihu.

Tana cikin tafiya ta ci karo da wasu samari su biyu .

Tana ganin su ta ,tuno inda ta, ta6a ganin su Humaid ne shi,da Jalal sun fito kewaye .
*LADIDIN ƘAUYE.*


_funny & love story._


*_Labari mai ban dariya haɗi da faɗa karwa_*


*NA*


*ZAINAB HABIB*
_{MOM ISLAM}._



*MARUBUCIYAR*


*ZAINABU ABU*


*AND NOW*


*LADIDIN K'AUYE*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*



*Episode: 5_6.*


____Humaid yasa shadda fara shi kuma jalal k'ana nan kaya ne a jikin shi Ladidi ce ta rik'e baki shagon da take kusa dashi ta shiga kana tace "dan Allah me manja samin a hannuna me manja ne ya dubeta kana yace "ke baki da hankali ko¿ LADIDI ce ta dubi me manjan kana tace "zaka ga aikin masu hankali roba ta hango a can waje zuwa ta yi ta d'auko robar shidai me manja yana kallon ta be ankara ba ta dumbula robar cikin manja .


Me manja da yaga barnar da LADIDI tayi mai mik'ewa yai kana ya nufo ta da niyar kai mata mari.


Ya d'aga hanu ze mare ta yaji an wanke mai fuska da manja sakinta yai kana ya nemi gurin zama .

LADIDI kuwa ganin haka ta kuma dum bular manjan tayi gaba .


Hango su Humaid tayi a gindin wata bishiyar mangoro suna hutawa .

A hankali ta tako kana ta zagaya ta bayan su inda bazasu ganta ba saboda bishiyar k'atuwa ce .


Juye manjan tayi a rigar Humaid ta baya sunata hira basusan abinda ke faruwa ba a jiye robar tayi a gefe .

Hango cinnaku tayi da yawa d'auko biyu tayi tasawa Humaid a dede gurin zaman shi kuma d'auko biyu tayi kana tasawa Jalal a daidai saitin da ya zauna.

Tashi tayi taje wani shagon da ake siyarda yar bebi jitayi anata ihu Humaid ta hango yanata tsalle shima jallal d'in tsalle yakeyi a tak'ai ce dai babu me temakon d'an uwansa.

Sun rasa inda za suyi aikuwa suka zuba a guje .

Kamar mahaukata Jalal ne yace "Humaid wlh bayanka manja .


Zaro ido Humaid yayi kana yace "kai k'yaleni bata manja nakeyi ba.


Mutane sa kallon su suke ta famanyi, ita kuwa LADIDI barin gurin tayi dan karsu ganeta da k'yar suka gane hanyar gidan malam Adamu saboda zuwansu na biyu kenan .


Da gudu su ka shige cikin gidan inna hauwa tanajin an shigo gidan da gudu bata tsaya ganin kosu waye ba itama ta ruga d'akinta da gudu.


Su Humaid ne suka shige d'akin da malam ya basu wanan na ihu wancan na ihu se zuwa can anjima ya lafa musu .


Humaid ne ya hau tattaro kayansu yana had'awa guri d'aya jalal ne yace "Humaid me zakayi da kayannan .


Humaid ne ya kalli jalal kana yace "insha Allah gobe zamu bar wanan k'auyen .

Jalal ne ya tuna da gudu da suka dinga kwasa ya kyalkyle da dariya .


LADIDI ce ta fito d'auke da tiren tuwo da miya malam adamu ne da malam musa suna zaune suna hira kasa kunne tayi taji suna cewa ai bak'in gidana gobe zasu tafi .

Tsalle LADIDI ta buga kana ta je gurin kayan wasan ta kusa da bishiyar kuka .

Dakin YADIKKO ta nufa samun YADIKKON tayi tana sallahr isha I .

Fitilar d'akin ta d'auko kana ta koma gurin kayan wasan .

Farar k'asa ta d'auko taje kan dutse ta dan dak'ashi seda yayi laushi.

Ta kwashe shi a leda d'akinta ta nufa mudubi ta samu .


Ta lakato mai me yawa ta shafa a fuskarta ta d'auko farar k'asar da tadaka shima ta goga a fuskarta, tunawa tayi ai batasa kwallin ba d'auko kwalkin tayi ta zana baki a bakinta takuma zazzana a duka fuskarta kayanta da suka yayyage ta d'auko .


Riga tasa me yagaggen hannu se wandon atamfa shima ta gwuiwa ya yage .

Dan k'aramin gyalenta ta d'auko ta kuma nan nad'ashi a kanta .


Duk wanda yaga Ladidi to ze d'auka aljana ce saboda ba lallai ka gane taba .

YADIKKO ce keta k'wala mata kira amma tana ji taki kulata .

Kuma lek'awa kofar gidan nasu ta yi hango su baban ta da malam adamu suna tsaye da alamu baban nata gida ze shigo shikuma malam adamu zashi masallaci ya kwana .


Wurga sandar ta tayi kana ta dura ta katanga .


Tunda tafara tafiya bata had'u da kowa ba ta kusa isa gidan malam adamu ta had'u da wani mutumi me tallan tsire yana ganin ta .



Ze ruga da gudu kenan Ladidi ta nunashi da sanda tace "wlh ko ka tsaya ko kuma yanzu inkaika gurin baba ifiritu me tsire yaji za,a kaishi gurin aljani ya dur k'usa har kasa ya ce ku kuke ganin mu ba mu muke ganin kuba dan girman Allah kuyi hakuri LADIDI ce ta zaro jajayen idanuwan ta kana tace

"Zamu kyaleka amma da sharad'i me tsire ne yace "kome kukeso zan Baku indai zaku barni da raina da lpy .



LADIDI jin hakan ta dubeshi kana tace "tashi ka bud'emin wannan kwanon .


Me tsire na rawar jiki yaje ya bude kwanon ya mik'owa LADIDI tsire ne aciki tsinke biyar .


Kwashewa ta yi duka ta had'esu guri guda tana tafiya tana ci shikuwa me tsire tunda yaga tayi nisa ya ruga da gudu yabar kwanon a gurin.


Kafin ta k'arasa gidan su malam adamu k'arfe 9 tayi kowa ya kwanta suma su jalal sun gaji saboda gudun da suka kwasa d'azu.

Taci sa,ar gidan a bud'e yake tunawa tayi da malam adamu a masallaci ze kwana kai tsaye d'akin nashi ta nufa lek'awa tayi ta windown d'akin suna kwnce suna danna waya.

Basu ankara ba sukaji durowar mutum da farko hankalinsu be tashi ba seda suka hango farar fuska kamarta aljanu .

Dakin nasu babu haske sosai .

LADIDI ce taje bakin k'ofar d'akin tasa sak'ata tanata zaro jajayen idanuwan ta .


Humaid tunda ya firgita ya koma kusada jakar kayan su ya 6uya shiko jalal dur k'usawa yayi yana bata hakuri .


LADIDI ce ta dubi Humaid kana tace "kai bakan manya bako to yau karyarku ta kare .


Rik'e hanun juna sukayi suna matsawa da baya da baya Humaid ganin abin yakeyi kamar a mafarki d'ago kan daza suyi suka hango nama a hanunta kurma ihu suka dingayi .

Humaid tsabar tsorata fitsari yayi a wando shi kuma jalal yaje yin tusa ya had'o da kashi .


Ladidi ce ta lura da abinda sukayi tace "kowannen ku ze kar6i wanan naman yaci Humaid ne yace


"Ai Allah yayi kune dan Ku temaki mutane amma kunzo zaku cutar damu .


LADIDI ce ta daka musu tsawa kana tace "tunda bazakuci naman ba to Ku cire wandunan Ku kai da kayi fitsari ka tsotse kai kuma me k'aton kai dakayi kashi kaci kad'an .


Zaro ido sukayi kana suka fara "dan Allah kuyi hak'uri tsawa takuma daka musu tace Ku za6a yaji ta hango a gefen ta a kulle a leda ajiye musu a gaban su tayi ta finciko nama a tsinken tsiren tace to sekun shanye yajin nan duka .

Humaid yana kuka yace Jalal gara musha yajin.


Dukufa shan yajin da da d'an guntun naman sukayi idanunsu yayi jajur ga kuka ga shan yaji .


Suna tsayawa zata daka musu tsawa inna hauwa ce tajiyo tsawar.

Fitowa tsakar gidan tayi bata gane ta ina akeyin tsawar ba seda ta jiyo k'arar bud'e k'ofar d'akin malam adamu wanda su Humaid suke ciki .


Kafin ta ankara taji an turo ta d'akin su Humaid juyowar da zatayi suka had'a ido da LADIDI .


Inna hauwa ce ta kurma ihu tana salati tana fad'in dama ashe aljana ce tashigo mana gida shine bata k'arasa maganar ba taji LADIDI na rawa .

LADIDI ce ta zaro musu ido kana tace rawa zakuyi ina hauwa ce ta zaro ido kana tace "kuyi hakuri kusan mu bil adama bamu da k'arfi .

LADIDI ce ta d'aga sandar ta zata buga musu sukasa ihu rawa sukeyi kamar mahaukata inna hauwa ta dage se rawa take kwasa.


LADIDI ce tace "jibeku dame k'aton kai dame k'aton hanci.

Kekuma yar tsohuwa me k'aton goshi ki k'ara shiga abinda babu ruwanki .

Inna hauwa ce ta had'a hanuwan ta biyu tace "kiyi hakuri bazan sake ba .


LADIDI ce tace musu "kowa ya rife idanu kuma karku bud'e har senace inkuma ba haka ba to zaku tsinceku a duniyar aljanu .

Kafin ta gama ,magana har sun rife ido .

Ficewa tayi a d'akin ta nufi d'akin inna hauwa ......✍🏽✍🏽✍🏽.



*Mom Islam✍🏽.*

*LADIDIN K'AUYE*


_Funny & love story._


*_Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa_*


*NA*


*MOM ISLAM*

*ZAINAB HABIB*.


*MARUBUCIYR :*

*ZAINABU ABU*


*AND*

*LADIDIN K'AUYE*




*BISMILLAHIR RAHMANIR _RAHIM*


*Episode: 7_8*

_____kwanuka tagani wanda akaci abinci wani kwano ta hango a rufe bud'ewa tayi abinda idanunta suka hango ya bata mamaki sosai.


K'ara bude ido tayi nama ne soyayye cike a kwanon leda ta hango ta d'ibi iya san ranta ta fice a gidan .

Tana fita suka bude ido sunata mamakin aljanar da suka gani .

Inna hauwa ce tace "jalal zoka rakani d'aki jalal ne ya zaro ido ya dubi inna hauwa yace "walh inma zaki tafi ki tafi babu inda zani.

Inna Hauwa ce tayi a uzubillahi ta ruga d'akinta da gudu .

LADIDI ce ta koma gida duk mutanen gidan sunyi bacci lalla6awa tayi ta shige d'akinta ta kwanta babu maganar sallah .

Washe gari bayan sallar asbah Humaid ya fito da jakar kayan su ko wanka basu yi ba malam Adamu ne ya dube su kana yace "badai tafiya zakuyi ba da wanan duku dukun safiyar gari be gama haske ba.

Jalal ne yace "wlh mun shirya inna hauwa ce ta fito da carbi a hannun ta ,tana lazimi ta ce "malam ai dole suce zasu tafi, malam Adamu ne ya nemi guri ya zauna kana yace "meke faruwa.¿

Humaid ne ya nisa kana yace "wlh malam aljana ce tashigo gidannan jiya da daddare tadin ga yimana mugunta.
malam Adamu ne ya jinjina lamarin ya ce to shine dalilin tafiyar Ku da wanan safiyar .

Jalal yana gyara takal minshi yace "insha Allah yanzu zamu wuce jos .

Ina hauwa ce taje d'auko kwanon da ta zuba soyayyen nama ganin naman ciki befi biyar ba yasa ta rafka salati har su jalal suna rugawa da gudu .

Malam Adamu ne ya lek'a d'akin kana yace "meke faruwa ne¿
inna hauwa ce ta dubi malam da alamun damuwa tace "kaga naman da kasiyo wlh ragowarshi kenan malam be nuna dumuwar komai ba yace "karki damu kawo a kai musu .

Barinje in siyo musu lemon kwalba ficewa yai .

Ba dad'e ba se gashi ya dawo da lemon kwalba guda hud'u .

Inna Hauwa ce ta kai musu d'aki suna zaune suna jiran lokacin tafiyar su yayi .

Inna Hauwa ce ta mik'a musu had'e " da nama kar6a sukayi ci sukeyi da sauri sauri nan danan suka gama .

Fitowa sukayi rataye da jaka a kafad'ar su inna Hauwa ce tayi musu Allah ya tsare.

Humaid tsabar ya matsu su tafi harya shige mota Mallam Adamu ne ya fito d'auke da tsaraba a hannun shi bud'e bayan motar Jalal yayi ya shige motar suka d'auki hanya se jos.

Washe gari Malam musa ya tashi babu lpy duk iya gigiwar LADIDI seda tayi sanyi ganin jikin mahaifin nata kwance yake se nishi yakeyi kamar me ciwon zuciya YADIKKO da jikinta yagama yin sanyi .

Tanaji kamar Malam musa baze tashi ba tari ne ya sark'e mai wuya .

Yafara k'ok'arin magana sunan YADIKKO ya kirawo wato Aisha amsawa tayi da na,am Malam yunk'urawa yayi .

Kana yace dan Allah ki kula da LADIDI kinga y'a mace ce tunda Malam musa yafara magana YADIKKO ta fara hawaye .

Tari ne yakuma sark'eshi YADIKKO ce ta umarci LADIDI ta kawowa mahaifin ta ruwa bayan ta kawo yasha .

Yak'ara da cewa na bawa Malam Adamu LADIDI YADIKKO ce ta rushe da kuka ta aika LADIDI ta kirawo Malam Adamu ba,a jima ba se gashi sun dawo tare da gudu Malam Adamu ya k'araso ya rik'e hannun Malam musa jiki a sanyaye yace "sannu Malam .

Amsawa yayi da yauwa ga amanar LADIDI nan nabaka jikin Malam Adamu yakuma yin sanyi sosai ya daure yace "insha Allah zakaji sauki .

Murmushin yak'e Malam musa yayi daga nan ya kirawo LADIDI matsowa tayi kusa dashi ya kamo hannunta ya rik'e gam daganan yafara shak'uwa .

Kulli nafsin za,ikatul mauti ..

Allah yayiwa Malam musa rasuwa kowa ya jimama mutuwar Malam musa .

YADIKKO inta kalli k'ofar Malam musa setaji hawaye ya zubo mata .

LADIDI kuwa takoma kamar mutuniyar kirki bata fad'a bare neman tsokana duk wanda ya tsokaneta bata kulashi.

Bayan anyi sadakar bakwai kowa ya watse YADIKKO ta kwanta rashin lafiya har asibiti Malam Adamu ya kaita amma an rasa gane ciwon dake damun YADIKKO .

Kulum cikin ciwo take LADIDI kuwa tunda taga YADIKKO na ciwo shikenan ta karaya tana ganin kamar itama zatabi mahaifinta ne a kulum YADIKKO in suka zauna da LADIDI basayin wata magana kamar tadinga cemata ki rik'e mutuncinki a matsayinki na y'a mace, LADIDI na kuka tana jin YADIKKO.


Ciwon YADIKKO ne yatashi sosai da gudu Ladidi ta tafi domin kiran Malam Adamu YADIKKO na d'agawa LADIDI hannu akan tadawo ina LADIDI ta kid'ime bata ankara ba tafice da gudu Malam Adamu tasamu a zaune shida inna Hauwa suna hira ganin ta cikin wanan yanayin yasa su mik'ewa a zabure LADIDI tana kuka tana cewa su Malam Adamu YADIKKO na zata mutu kuzo duk wanda yaga LADIDI a lokacin komi rashin imanin shi seya tausaya mata .

Kafin inna Hauwa ta d'auko gyale ta fito har Malam Adamu ya isa gidan su LADIDI salati yahau yi ganin YADIKKO rai yayi halinsa .

Inna Hauwa ce suka k'araso itada LADIDI Malam Adamu na ganin su ya juya fuska yana sharar kwallah .

Tunda LADIDI taga haka itama ta zauna ta rafka uban ihu tareda birgima a k'asa babu wanda yayi yunk'urin hanata kukan mutane ne suka fara shigowa masu kuka nayi masu salati nayi masu adu,a nayi hak'ik'a mutuwar YADIKKO ta girgiza mutane sosai .

Tsakaninsu da mijinta Malam musa wata d'aya bayan anyi sadakar uku inna Hauwa tasa LADIDI ta kwaso kayanta ta dawo gidanta da zama duniya tayiwa LADIDI kunci kwata,kwata batajin dad'in zaman duniyar.

Bayan sadakar bakwai aka rufo gidan da kwad'o tunda LADIDI ta dawo gidan inna Hauwa takoma shiru shiru ko abinci takeso bata magana sedai in and'auko anbata.


JOS tunda su Humaid da Jalal suka koma garinsu kowa ya koma bakin aikin shi Humaid aiki yakeyi a hospital d'in dadynshi daya bud'e mai , shikuma Jalal aiki yakeyi a ma,aikatar mahai finshi.

Wato saida kayayyakin mata na sawa dana maza da sauransu sun maida hankali akan sana,ar sosai .

Dady ne zaune a dining suna breakfast shida su momy da Humaid da Jalal kirane ya shigo wayar dady d'auka yayi kana ya kara a kunnenshi jinayi yace innalilahi yaushe ¿"dady ne ya ajiye wayar yana jimama rasuwar Malam musa da Aisha wato YADIKKO.

Jalal ne yakalli dadyn nashi kana yace "badai iyayen LADIDI bane suka rasu¿ daday ne ya amsa da cewa dama sunada y'a LADIDI ne ?

Jalal ne yace inadai kauyen da muka jene to tabbas iyayenta ne abokin Malam ne dadyne yace tabbas sune momy ce ta fara tambayar dady kwatance yayi mata inda zata gane adu,a sukayi musu daganan kowa ya wuce gurin aikin shi.


★ ★★ ★ ★ ★

Bayan shekara uku LADIDI tana da shekara 14 years tayi tsayi tayi k'iba farinta ya k'ara fitowa ga k'irjinta yafara cika tafiya takeyi tana waka ta hango me tallar k'uli,k'ulli tana zaune a gindin bishiyar kukar dake k'ofar gidan Malam Adamu da tazamo gurin zamanta tun ana hanata har anzo ana barinta.

Me k'uli _k'uli ne ya kawowa Ladidi ,'d'agawa tahauyi tana cewa nawa nawa yaro me tallan k'uli yace "ashirin,ne Ladidi ce tace "za6omin d'auri d'aya kuma

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login