Showing 18001 words to 21000 words out of 39140 words

Chapter 7 - LADIDIN KAUYE

Start ads

24 Aug 2025

245

Middle Ads

ta saida ta shanyeta tass tukun ta kuma kwanta 'a gurin bacci mai nauyi ya d'auketa ...

Jin wani sanyi mai kamada ruwan k'an k'ara ya tashe daga baccin da takeyi duka taji ko ta ina tarasa waye mai dukan 'nata ihu takeyi 'iya k'arfinta 'amma innaa bbu halin tashi bud'e idanuwanta dasukayi mata nauyi tayi ganin Humaid a tsaye kamar wani soja yasata cewa to Allah ya isarmin mugu kawai buge bakin yayi ya cire bell d'in wandinshi yana dukanta ta ko ina ganin babu mai ceton ta yasata juye juye tananeman abinda zata buga mai ,ganin babu komai yasata dai daitar saitin wandonshi ta murd'e gabanshi ta zura da gudu wani wahallalen k'ara yasa mai wuyar fassara wa yarasa maiyakeji ,jiyayi kanshi na juyawa rike da mararshi ya fad'i k'asa sumamme, Khadija ko kitchen tanufa ta fere doya ta wanke ta dafata daganan ta soya da mai tanayi tanacewa kafin ya tashi naci nak'oshi mugu kawai ,tana gamawa ta soya miyar k'wai kasancewar akwai kayan miya batasha wuyaba seda taci ta k'oshi dak'yar take iya tafiya da ruwan gora 'a hannunta ta k'arasa d'akin ,ganinshi kwance yarik'e gurinda ta murd'e kumfar yawu na zuba 'a bakinshi yasata rugawa d'akinshi da gudu cikin tashin hankali wayarshi tagani a kan gado duba number tahauyi ,ganin doctor Umar yasata danna kira ring d'aya ya d'auka 'a zatonshi Humaid ne ,jin muryar mace yasashi cewa madam barka dai, cikin firgici Khadija tace "Umar dan Allah kazo ka duba Humaid dan Allah kayi sauri ko motsi bayayi ,a tsorace Umar yace " karki damu ganinan zuwa to tace"kawai domin hankalinta yafi na 6arawo tashi.


Ba'a d'au wasu mintuna ba saiga horn d'in motar doctor Umar yana zuwa ya nocking d'aga murya tayi tace"shigo doctor ,da y'ar jakarshi a rataye ya k'araso yana haki'i tsabar kukan daya ku6ce mata bata iya magana ba nunamai d'akin da Humaid yake kwance tayi , shigewa yayi da sallama Doctor Umar ganin halinda Humaid yake ciki yasashi rik'e kai yana cewa innalilahi wa innailahirraji'un ya Allah help me,idonshi cike da hawaye ya kinkimi Humaid kamar gawa yasa 'a mota cewa Khadija ta kulle gidan ta biyoshi yayi to kawai ta iya cewa kasancewar gani takeyi kamar Humaid ya mutu ne."


Rufawa doctor Umar baya tayi dole ta shige gidan gaba saboda 'an kwantar da Humaid a back side ,tun doctor Umar na hanya yake waya akan a tanadar musu d'akin saboda Humaid babu lafiya kuma yana buk'atar temakon gaggawa kasancewar hospital d'in akwai nisa saida sukayi tayi maid'an 'nisa sannan suka iso a keken tura marar lafiya 'aka turashi direct d'akin da 'aka tanadar musu suka tafi likitoci biyar ne akanshi amma kowa sai share gumi yakeyi ,itako Khadija sai safa da marwa takeyi a harabar asibitin ,likitoci sun shafe wajen awa 1 hour suna bincike akan suma samu nunfashin ya tsaya 'abin ya citura sai da suka kuma shafe mintuna talatin sanan sukayi sa'a ceto rayuwar shi ,ba'amayi batun gurinda 'akayiwa illa ba tukun ganin ya bud'e ido yasa likitocin cewa Alhamdulilh Allah mun gode maka ,jin ana hamdalah yasa Khadija saurin k'arasowa tana kuka tana ganin Humaid ya bud'e ido takama dariya tana yiwa Allah godiya.



Likitocin'ne sukace to yanzu saimu koma kan inda yaketa nunawa tun d'azu a kunyace Khadija ta fice daga d'akin ganin ana k'ok'arin duba gurin bayan sunyi y'an bincike ne suka gano cewar yasami matsala 'agurin kuma indai ba fita dashi k'asar waje akayi ba to kafin yayi sex da matarshi zai iya kaiwa shekarar biyar kokuma k'asa da hakan kasancewar Nigeria basuda cikkakun kayan aiki,kwanansu hud'u a hospital d'in Doctor Umar shike jigila 'akan kayan abinci asibiti dai babu bataun biyan kud'in domin mai asibitinne a kwance babu lafiya.



Yaune aka sallamesu Khadija na tsoron gayawa momy halin da 'ake ciki saboda hukuncin dazai biyo baya ,amma babu inda ta iya dole ta sanar dasu ,tanashirin d'aukar wayane Humaid yace "karki kira su momy dan wallah natashi saina kusa karyaki ,Khadija ce taja baya ta murgud'a mai baki tace a hakanne zaka karyani tabb wlh gara kayi a hankali karka famo gurin da 'akayima bandeji hhh, harararta yayi sanin bazai iya tashi ba yasata fad'ar hakan, rugawa tayi da gudu ta d'auki wayar ta danna number momy ring biyu ta d'auka momy ce tace" my daughter yakike lafiya tace"cankuma tace momy Humaid babu lafiya fa momy ce tace"maiya sameshi ? Shiru tayi can kuma tace" fad'uwa yayi a toilet momy ce tace"to yaji ciwo ne?eh Khadija tace"dan yanzuma 'a kawance yake kwananmu hud'u a asibiti shine yace"wai karna fad'a muku,momy ce tace"to gamunan zuwa 'Allah yakawoku lafiya Khadija tace"daganan ta shige bedroom d'inta ta kwaso kayan abincin datakai can tana cikin kwasowa ne hankalinta yakai kan kwalin golden beer d'inda tasha tana karantawa tahau salati ,can kuma tayi gumm da bakinta mayar da kwalin golden beer d'akin Humaid tayi ta tura 'a k'ark'ashin gado sauran kuma takai kitchen ,wanka tashiga tayi kwaliya kamar maishirin fita anguwa ,shidai Humaid na parlor magana ma ta isheshi ....✍️✍️✍️.



Mom Islam ce

*LADIDIN K'AUYE*


Funny & love story.

*Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa*



*NA*

*MOM ISLAM*
*ZAINAB HABIB*


*MARUBUCIYAR:*

*ZAINABU ABU*



*AND NOW*

*LADIDIN K'AUYE*



*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


*Episode:* 29_30



_____Momy ce ita da dady suketa sallama cikin sassanyar murya Humaid yace"wa'alaikumussalam shifowa sukayi ,ganin Humaid ya mugun ramewa yasa momy k'araswa kusada shi da sauri tace"my son maiya faru dakai naga ka koma haka ?"cewa yayi momy babu komai kwai banida lafiya ne dady daya saki baki yace"to ai Khadija tace "mana zamewa kayi ?" shiru yayi yana tunanin k'arya irinta Khadija cewa yayi eh hakane kasancewar inya fad'a musu halinda suke ciki zai 'iya fuskantar matsala dukda ciwon dayake damunshi , Allah yabada lafiya sukace daganan saiga Khadija ta fito sake baki momy tayi ganin wata uwar 'rama da Khadija tayi amma taja bakinta tayi shiru ,rungume momy Khadija tayi tana murmushi tace "momy na kinzo lafiya ?dady ne yace" to gani a gefe tunda 'an manta dani rufe fuska tayi tace"dady afuwan kunzo lafiya cikin farinciki dady 'yace"lafiya yamai jikin ? dasauk'i tace "cankuma ta shiga damuwa momy ce taga 'alamun fuskarta tace" lafiya Khadija??" fashewa da kuka tayi shidai Humaid na gefe ido ne nashi ,tsagaita kukan tayi kana tace "momy matsala Yaya Humaid yasamu momy ta bud'e baki tace" a ina?shiru tayi can kuma tace"kuma doctors sunce sai an fitar dashi waje!!! jin wanan kalmar ta k'arshe ya girgiza su momy sukace to matsala yasamu a brain d'inshi?a'a tace" tashi tayi taje ta d'auko file d'in asibitin mik'awa momy tayi ,momy na kar6a ta mik'awa dady Humaid ko dariyace taso kufcemasa wai takasa fad'ar abinda yasameshi hhh,dady na dubawa yace"innalilahi oh Allah momy ce tace"maiya faru ne ?dady daya had'a zufa ba kud'in fita k'asar wajenne damuwar shi ba larurar Humaid d'ince damuwar shi ,dady ne yagawa momy komai dagan suka fara jinjina lamarin.




Dady ne yace ”Allah yakaimu gobe ,dady ne yakira waya airport saboda 'ayimusu tanadin jirgi , yayi sa'a zasu samu na k'arfe 4pm zasubi , dady ne yace ”maganar hospital d'in babu matsala wuyarshi Allah ya kaiku lafiya ,Khadija ce tace ”dady nidai bazanje ba momy ce tamaida dubanta ga Khadija tace ”to ko maiyasa bazaki ba Khadija? "shiru tayi ta sunkuyar dakai ,tana wasada fingers d'inta ,momy ce tace ”aikuwa tafiya dake dole kece matarsa mukuma daga baya zamu biyoku anjima zan sa driver yakawo miki waya saboda gaisawa ,to kawai tace” saboda musu ba halinta bane mik'ewa sukayi suna yiwa Humaid Allah yak'ara lafiya 'amen kawai yace”daganan suka fice ,mita tashiga yi tana cewa mutum bai damu dakaiba baidamu da damuwarka ba baisan darajar kaba 'amma kaje kayimai jinya daga baya 'yazo ya wulak'antaka,shidai Humaid na jinta bashida lokacin bata 'amsa kasancewar shi ta ciwon jikinshi yakeyi ,wurgamai harara tayi daganan takuma cewa wallahi mukaje ka walak'antani saina k'ara janyo wani jan aikin tunda mutum cin zali yayimai yawa ,zaro ido yayi kuma yana mamakin wai yatsaya wanan shegiyar yarinyar tana gayamai maganganu baid'au mataki ba ,tunawa yayi sai an temakamai zai 'iya tashi k'wafa yayi ya maida kai ya kwanta 'akan kujerar bud'e baki Khadija tayi tace ”da dukana zakayi ahayye ni Dije wallahi kama sameni ne da lokacin da nake garinmu ne tabb dakadinga yimin ladabi dan bana d'aukar 'raini, Humaid maganganun Khadija sun 6atamai rai sosai amma da yanada lafiya babu abinda zaihana ya hukuntata, amma 'akwai lokaci ."




Komawa d'aki tayi tafara had'a kayanta dakuma 'abubuwan dazata buk'ata kitchen ta wuce ta d'ebo naman kaza 'a fridge ta sa kayan k'amshi dasu atta ruhu ta tafasa naman yana dahuwa ta d'auko turmi tafara dakawa da 'alamu dambun 'nama zatayi bayan tagama ne tahau suya rana gama suya ta d'ibo dakkaken yaji ta zuba 'a roba takai jakar tafiya , d'akin Humaid ta nufa tana duba kaya tana dariya gajerun wanduna ta d'ibar mai sunkai guda ishirin sai t sheet guda goma ,nikwa nace to ina manyan kayan ?" golden beer d'inshi ta d'iba har guda biyar tasa 'a jakarshi ,saikuma man shafawa dakuma takalmanshi tana gamawa ta fice ta nufi d'akinta .

Washe gari misalin k'arfe 9am saiga driver da abincin karyawa dakuma kwalin waya ,tana rawar jiki suka gaisa mik'a mata sak'on yayi godiya tayimai tashige ciki da gudu ,ganin babu Humaid yasata rik'e baki tace ”toshi harya sami sauk'i ne?"batada mai amsa mata tambayarta yasata yin shiru ,tafara duba wayar spark 2 ce maikayau sosai bud'e abincin tayi ganin soyayyen dankali dakuma wainar k'wai a gefe yasata kwashe k'wan tabar dankalin a dining, komawa d'aki tayi tacigaba da shiri wnka tayi ta fifito da kayan data d'ibar musu komawa tayi hanyar d'akin Humaid tana shiga ta hangoshi rik'e da waya 'a hannu da 'alamu charting yakeyi ,girgixa kai tayi tafara cewa lallai to ai basai anje Indian ba tunda kaji sauk'i barin cewa su momy wai abarshi ,da mamaki yake kallonta dubanta yayi 'irin kallon kinrainani d'inan yace”wallah zan 6a66allaki wucemin anan dan ke bata yimiki amfani shine zakimin mugunta ko muguwa kawai dariya tasa tace”kai kadamu da iskanci nikam Allah ya sitiri buk'wai ,shiru yayi ganin raini zai shiga tsakani ,k'arawa gaba tayi tace ”daya d'auka ni yar iska ce ,hmm to ma wai da dayakecemin mazinaciya menene amsar hakan?tana yiwa kanta tambayoyi can kuma tace ”ok natuna lokacin da Ammar ya saceni shine yake zargin 'nice naje d'akinshi?rasa maibata 'amsa tayi hakan yasa takoma d'akinta tana saka sim card a wayar ta memo ta d'auko wanda tayi seven number k'awayenta dakuma ta momy saka numbobin tashiga yi tana murna."




Da misalin k'arfe 3:dai dai dady 'yakira Khadija kasancewar sund'au number tata tana d'agawa dady yace”to inkun kammalah gamu nan a hanyar zuwa airport ku hanzarto angama komai tun jiya to tace”gamunan zuwa dady ,zuwa d'akin Humaid tayi tace ”kafito gasu dady can a hanyar airport mik'ewa yayi jiki babu k'wari yace ina kayana?cewa tayi gasunan a jaka bud'e gurin kayan 'nashi yayi yakuma lodar 'rigada wando kamar yasan bata d'ibarmai ba ,cemata yayi bar 'rawar jiki dan kona sami lafiya 'aure zan k'ara ,Khadija ce tace ”a hakan da babu k'arfin jikin kana tafiya kamar mace,zaro ido yayi yace"wlh zanci ubanki shigewa tayi tarabu dashi tasandai koba komai ta gasamai magana.



Shigewa mota sukayi sun d'anyi tafiya sanan suka iso airport d'in samunsu momy sukayi a zaune suna jiransu k'arasawa gurinsu sukayi suka durk'usa suna gaisuwa Humaid dak'yar ya mik'e itako Khadija dariya takeyi k'asa k'asa jin lokacin tafiyarsu yayi yasa momy yimusu fatan 'nasara ta mik'awa Khadija wani babban jaka mai zurfi ,dady ne yace ”nayima transfer na kud'i bakada matsalar su godiya yayiwa dady daganan suka shige jirgi ,hawaye Khadija tafara shareware saboda tasan momy ma dauriya kwai takeyi ,jin tashin jirgin yasata rik'o Humaid ta matseshi tsaki yaja yace ”dalla ni karki sakamin k'azamin jikinki banza kawai ko kulashi batayi ba tacigaba da rik'eshi ,shikuwa bashida k'arfin kokawa yasa ya k'yaleta....✍️✍️✍️.


Mom Islam ce

*LADIDIN K'AUYE*


Funny & love story.

*Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa*



*NA*

*MOM ISLAM*
*ZAINAB HABIB*


*MARUBUCIYAR:*

*ZAINABU ABU*



*AND NOW*

*LADIDIN K'AUYE*



*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


*Episode:* 31_32



_____Suna sauka cikin ikon Allah saiga wani bature yazo yake cemusu ance yanuna musu masaukin su Humaid saboda rashin yarda yace "saiya kira dady aikuwa yana kira dady 'yace”nine na turoshi dafatan kun sauka lafiya ?lafiya Lou Humaid yace”daganan suka shige motar wanan bature ,itadai Khadija gajiyace ta buwaye ta dan burin ta bai wuce taganta tana hutawa ba ,wani katafaren hotel suka sauka Khadija ce tazaro ido tace"nifa tsoron jajayen fata nakeyi wallahi kar azo angama cinikinmu, Humaid ne ya gimtse dariyar sa shikuwa wanan Bature babu abinda baijiba wanada Khadija tafad'a kasancewar yana mu a mula musulmai sosai amma shi Christen ne saboda baya sallah ,door bell baturen ya danna k'ofar ta bud'e da kanta zaro ido Khadija tayi tace”to Allah gamu gareka tana tafiya tana sambatu shikuwa Humaid ko kallonta baiyi ba ,direct wani rantsatsen step naga sun hau d'aki mai number goma suka shiga ,Humaid ganin ba'ayi maganar komai ga shuwagabanin hotel d'inba yasashi cewa to sukuma masu hotel d'in anbiya sune?eh baturen yace”tun jiya dadynku yayi komai ,godiya Humaid yayimai mutumin 'ne yace”sunanan Joseph barin baka number ta musayar lamba sukayi daganan Joseph yace”suyi wanka su huta za'a kawo musu abinci .


Tana shiga d'akin Humaid ma yashigo tunda tashigo take kallon d'akin kyau tsari gakuma nerorin da 'aka kashemai tabb tace ”lallai wasu basusan zafin kud'i ba ,Humaid da gajiya ta tarumai yace”to sannu 'uwarsu zaki 'iya fita ki sanar musu ,ko kallon inda yake batayi ba tashige bathroom wanka tafarayi kasancewar akwai sabon sabulun wanka da sabbin brush da man goge baki saida tayi wanka sanan ta d'auro alwalah tafito ganin har bacci yafara d'aukar Humaid yasata kurma uban ihu tace”wayoo nashiga uku ,a firgice Humaid ya farka yana salati ganin Khadija tayi shuru yasashi cewa komai aka had'a da jaki saiyyaci kara ,zaro ido tayi tace”waye jakin nikake kira da jaki, murmushin takaici tayi tace ”d'an adam mai mance hallacci babu komai kasan ba'acin bashina ,mamakinta yakeyi dahar take gayamai maganganu san ranta saboda taganshi a kwance bazai 'iya 'aikin k'arfi ba yasa takeyimai wulak'anci ,dariya yasa lokaci d'aya kuma yace”yaro baisan wutaba saiya taka."




K'yaleshi tayi tafara sallah tana idarwa ta dubo al qur'anin data taho dashi tafara rera karatu , idon Humaid a lumshe kamar mai bacci ya bud'e ido yana saurarrar karatun Khadija jiyakeyi kamar karta dena ,bayan takammala karatunne ta mik'e tayi gurin kayansu bud'e jakarta tayi ta dubo atamfa rigada skirt mai adon flowers green zatasa kayan ta tuna 'aifa Humaid na d'akin juyawa tayi tace ”malam zaka iya juyawa saboda zansa kaya karkuma 'a kalleni ehe, juyowa Humaid yayi yace”wanan banzan jikin'naki mezan kallah jikinda kowa yagama ganinsa ,tanajin takaicin wanan kalmar amma 'akwai lokacin ramako, d'ibar kayan tayi takoma bathroom ta sanya sanan tazo tana shafa mai kasancewar garin da zafi kuma dukda sanyin AC mutum gumi yakeyi ,kwaliyarta tayi a nitse sanan wuce dining table d'inda 'aka kawomusu abinci ganin cimar kamar ba irin tata ba yasa ta had'e fuska tana rik'e ciki ,hango wayar tafida gidanka tayi ganin 'number su a calendar yasata d'auka cewa tayi nifa bazan iyacin wanan jagwal gwalon ba 'akawomin tuwo kokuma indomie mutumin da baigane maitake cewa ba yace ” give me one minute please am coming zaro ido tayi tace ”tabb 'banza shima turancin bai gama bakinsa bba."


Humaid daketa dariya yana k'arawa yace”LADIDIN KAUYE y'an mata had'e rai tayi tace”wallahi kabari dan banhuce na d'azu ba, shiru yayi dan yasan komaiye ma zata rina 'aikatawa ,nocking aka farayi Humaid ne ya lala6a ya mik'e saikuma ya tsaya yace ”saikije kiyimai bayani,Khadija ce tace”bagane nawa turancin zaiyi ba dan 'naga shima koyo yakeyi yanzu hakama brain d'ina tafi tashi ,wucewa kawai Humaid yayi ya bud'e k'ofar mutumin 'ne d'auke da farantin abinci bud'ewa yayi yaga indomie ne aciki godiya yayiwa mutumin daganan yasauka k'asa da tiren abincin samun guri yayi yafara loda indomie saida ya cinye duka sanan ya tashi yabar plet d'in agurin yakoma sama.



Samunta yayi ta rafka uban tagumi tana kuka ko kallon gunda take baiyi ba bare tasanma yaganta taji dad'in 'narkewa bathroom ya wuce yayi alwala yazo ya gabatar da sallah tunda yayi sallama yaketa jero adu'a 'akan Allah yabashi lafiya ,itadai Khadija tarasa meke yimata dad'i a duniya kasancewar bata ragawa ciki ko kad'an mik'ewa tayi taduba maid'an dama dama tafara tuturawa badan yayi mata ba tana gamaci ta d'auki waya takirawo momy cikin farinciki momy tace” daughter dafatan kuna lafiya dai ko?eh muna lafiya Lou "amma momy 'yaushe zakuzo?momy tana murmushi tace”gobe ne insha Allah muna zuwa zamu wuce hospital amma zaku rigamu wucewa,to kawai tace shikuwa Humaid dama can magana ba damunshi tayiba, daganan sukayi sallama da momy.


Dare nayi basuci wani abinci mai nauyi ba ,Humaid na k'ok'arin hayewa gadon tarigashi ,hak'ura yayi ya koma k'asa ya shinfid'a bargo ya kwanta .



Washe gari bayan sunyi sallahr ashba babu wanda ya koma shirin tafiya 'asibiti sukeyi bayan Humaid ya fito daga wanka yaduba jakarda Khadija, ta lodamai kaya 'acikin ganin gajerun wanduna yasashi salati yace”wato kinmaidani d'an iska kenan ko ?cigaba tayi da kwaliyarta daganan ta mik'e tana cewa to inka shirya nizan wuce ,Humaid ne yace”kin dad'e baki wuce ba banza kawai jibeta 'ahaka kamar saliha ,shiru tayi saboda batason wanan kalmomin da yake jifanta dashi amma burinta lokacin yazo .


Yana gama shirin ya fice ko magana baiyi mataba jitayi yana kiran Joseph a waya dagudu ta fito tana tsaki ,ganin Humaid yashige mota yasata bud'ewa tashige da sauri wani katafaren hospital suka nufa suna sauka koshi Humaid ' d'in saida ya jinjina kyau irinna asibitin suna zuwa 'aka tarbesu office suka wuce domin ganin babban likitan suna shiga

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login