Showing 30001 words to 33000 words out of 39140 words
aikuwa kare yadinga binta duk inda ta shiga saiya bita gudu takeyi da kwandon shara a kanta ,tama manta layin dazata dosa gashi gidajen duk kusan kala d'aya wani mutumi ta hango yana gyra parking din motarshi k'arawa tayi da gudu tace ”dan Allah ka temakeni karya halakani ,mutumin ne ya kalli karen yace ”mai tayi ma kake binta ?itako Sahura ganin yana neman raina mata hankali tace ”shi mutumne dazaka tsaya tuhumarshi ko kaima mugune irin karen ,mutumin ne ya rike baki tana salati cewa karen yayi duk inda tashiga kabita karka raga mata."
Aikuwa kare yafara bin Sahura gudu take ci babu mai temakon ta ,humaid ne tafe a cikin mota hango ta yai tana gudu ashe harta zo anguwar takuma juyawa yanzukuma ta dawo duk bata sani ba ,fitowa yai daga cikin motar yana cewa keee!!da k'arfi ziwa tayi ta cakumeshi tana ihu ,karen humaid yabawa hak'uri daganan yace ”to ga gidan nan amma ina zaki da kwandon shara cewa tayi naje zubar muku da shara shine kare ya biyoni wata shu'umar dariya humaid yasa yace to jeki gida maganin mai yawo kenan ,murgud'a mai baki tayi ta shige ciki , tana shiga tafara cewa Ladidi ki fito yau nakusa mutuwa ,da sauri Khadija ta fito tana cemata na k'arshe karki sake cemin ladidi ,to natuba dan kunga ku yan gayu ne shine kikeso kisa a maidani gida to ta Allah ba takiba ta shige d'akin da yake mazaunin nata."
Washe gari salamar momy ce ta karad'e harabar gidan da gudu khadija ta fice tana oyoyo momy a tare suka shigo parlor rik'e da hannun juna ,Sahura na zaune tana kallo tace ”hajiya barka da zuwa momy ce tace ”yww daughter yar aiki kika samu ne ¿khadija ce tasa dariya tace ”tare sukazo da inna hauwa ,oh momy tace ”na tuna ai ta fad'a min amma bbu wani matsala kho eh momy komai normal , nan momy ta jata zuwa bedroom d'inta tanata bugar cikinta 'akan ko tana cikin wata damuwa ,juyin duniya khadija tak'i fad'awa momy komai,momy ce ta fiddo da wani turare tace ”yau d'inan 'nakeso kiyi using dashi ,to Khadija tace ba tare data musa ba ,nasihoyi momy tayi mata akan ladabi dakuma hak'urin zaman aure,momy ce ta d'au jakarta tana shirin tafiya narai _narai Khadija tayi da fuska zatayi kuka momy tace ”nazo kuma dan inganki inji dad'i shine zakiyi kuka kull kiyi hak'uri zaman aure ba wasa ba ,raka momy tayi har gurin motar da tazo sukayi sallama ,magrib nayi tayi wanka tasa riga da wando rigar dai _dai cinya wandon kuma dai _dai gwuaiwar k'afarta ,turaren da momy ta bata ta fito dashi shafawa tayi a fuska tana mai jin k'amshin yayi mata dad'i ,,jin sallamar Humaid yasata fitowa a kunyace tace ”barka da dawowa yaya uhm barka yace yana k'are mata kallo ,wani lamari yakeji mai wuyar fasarawa sabda inya kalli fuskarta ,cewa yai kaimin bag d'innan ciki ohk tace ”ta wuce taje kaiwa ,tana shirin fitowa taga an kashe light d'in d'akin anbar kadan zaro ido tayi lokaci guda kuma tsoro ya baiyana a fuskarta ,cikin zuciyar shi yana cewa da nace sai lokacin da kika amince to yau na soke wlhi ,nufota yakeyi tana ja da baya ,a haka har tasamu tayi d'akinta da gudu ,6acin rai ne ya dirarwa Humaid sabda yafara wani tunani daban akan Khadija yafara zarginta sosai sabda had'in kan datak'i bashi tana nufin Allah bazai kamata da laifi ba kenan?takoma kamar jahila wacce batayi karatun islama ba ,yau dai 6acin rai yasa Humaid maganganu marasa kan gado juyi yakeyi yana tunanin anya wani bai rigashi ba hmm ."
Yaune Sahura zata koma gida sai kuka takeci kamar an aikota wai zatayi kewar burodi da shayi ga kayan dad'i harda bubuga k'afa ,a haka suka had'a mata goma ta arziki akwati sabo Humaid ya siya mata hardasu atamfofi driver akasa ya kaita.
Khadija batada wal walah kwata ²komai cikin sanyin jiki takeyi gashi ta koma very silent abin haushi ma dariya tsada takeyi mata ,washe gari da safe kira ya shigo wa Humaid cewar wanan doctorn yanason suyi wani aiki tare urgent yaje ya sanar dasu momy fatan alkairi sukayimai sanan sukace to matarka fa ?"sosa kai Humaid yai yace ”tace batason yawo lolz tunkafin ka tambaya hh,a tunanin su momy cikine da ita dan yau bikinsu 1 month kenan ,ficewa yai sunata sanya mai albarka komawa gidansa yai yasami gimbiyar na goge TV k'arasawa yai ya rungumeta yana cewa lovely munsami cigaba fa kitayani murna ,murmishinta tayi mai tsada tace ”Allah ya tabbatar da alkairi ,wanan adu'ar tasa yaji dad'i sosai ,yace to kishirya muje tare a'a tace ”a tak'aice shiru yai bai sake magana ba ,yanason cewa ki shiryamin kayana a jaka yakasa ,hakadai ya shirya da sauri sauri ,Jalal ya kira akan yazo ya kaishi airport sai ya dawo da motar ,yayi yayi Khadija ta rakashi koda airport d'inne amma ttak'i."
Haka tayimai Allah ya tsare ,yana tafiya ta fashe da wani matsanancin kuka ,ring d'in wayarta taji mik'ewa tayi ta d'auko wayar ganin number babu suna yasata kallon number, dauka tayi had'e da sallama dagacan 6angaren akace ya kike kwalli lpy Lou Khadija tace ”dan bata gane mai maganar ba Fati ce kokin manta da mukayi school tare oh na tuna yakk hope kina lpy eh ya amarci dariya Khadija tasa tace ”amarci nan sai wanda ya k'aru daganan sukayi sallama ,zaman shirunne ya isheta ta zari hijab ta shiga mak'otan su gidane tangameme kuma tsararre da yafi nasu komai ma nocking takeyi amma shiru , can mai gadi ya bud'e yana kallon Khadija yace ”daga ina ne ?cewa tayi ga gidnmu nan wanan na jikin nakun ,Allah sarki yace dagan an yabata hanya ta shige ,da isaera k'ofar parlorn wata k'ofa ce ta glass tana haske kala kala sallama tayi jitayi an amsa ,matar dai batasan Khadija ba amma dayake batada girman kai yasa tace toshigo mana sister."
Shiga tayi matar da a shekaru zatayi 27 tace ”saidai ban ganeki ba wlhi tana murmishi ,Khadija ce tace ”ga gidanmu nan jikin naku ,oh ko kece amryar da aka kawo kwanaki 8 months da suka wuce ,jinjina maganar Khadija tayi tace ”wata takwas kina nufin Humaid yayi aure kenan ?matar ce ta dubi Khadija tace ”oh su6utar baki please karki tada hankalinki ita wacan ba zaman aure ya kawo ta ba ,kinga ni sunan na Rahma yarana biyu kin gansu nan a photo yarane kyawawa masu kamada uwarsu sunsha kyau sosai Khadija ce ta dubi Rahma tace ”ni kuma sunana Khadija danan hira ta 6arke kamar sun dad'e da sanin juna horn sukaji Rhma ce ta mik'e tana lek'awa ta window ,oh kinga sweety ya dawo please ina zuwa , Khadija ce ta mik'e window da Rahma ta lek'a nanta fara lek'awa wani kya kyawan magidanci ta gani fari sol kamar bature ,hango Rahma tayi ta bud'e masa mota ta kar6i jakar ta rataya ta kuma ruk'o masa hannu shikuma ya rungumota suna tafiya suna dariya ,Khadija ce tace ”danasan iskancin da zan gani kenan da banzo gidannan ba wlhi ni nazo domin d'ebe kewa amma naga abinda yafi k'arfina nifa bazan iya k'arewa a yiwa namiji bauta ba hmm ,ita kad'ai taketa maganarta ,can kuma taji gabanta na fad'uwa sosai ,yarinya tagani wacce zatayi shakara hud'u a duniya tace ”jeki cewa momynki bakuwar ta tafi ,da gudu ta shige tana cewa momy bakuwa zata wuce ,OK kice ganinan Rahma ce tace ”sweety zani yiwa bakuwata sai gobe ,janyota yai yace ”daga ina tazo a mak'otanmu take ,Rahma ta fice tana dariya ,samun Khadija tayi a bakin get a tsaye ,Khadija ce tace ”to aunty Rahma sai wani lokaci godiya Rahma tayi mata ,Khadija ta fice.shige ciki....✍️.*LADIDIN KAUYE*
funny & love story
49_50
Jin fad'uwar gaban ya tsananta sosai yasata k'ara saurin tafiyar ta ,tana dosowa bakin get abinda taganine yasata kurma uban ihu ta fad'i sumammiya .
Sahura ce zaune tana cin tuwo tana turo baki ,inna Hauwa ce tace ”nifa banasan kinibibi garama abincin gidanmu naku da ko kafi zabo babu ,kuka Sahura ta fashe dashi tace ”ni walahi sonakeyi in koma jos gurin Ladidi ,zaro ido inna tayi tace ”to ga hanya nan kitafi k'wad'ayayya sunmayi namijin k'ok'ari da har kikayi musu sati biyu batare da sun koroki ba ,wani kallo tayiwa inna harda murgud'a baki tace ”to dan kiji ma yasin ni bazanyi aure a nanba saboda talauci yayi muku kanta ,salati inna keta jerowa ita ko sahura surutunta take jerowa ,jin salamar yaro yana tallar alele hhh fans means allale ,tace ” kai d'an hanse kawo dan uwarka ,inna ce tace ”walhi ki kiyayi zagi saikace baki zuwa islamiya ,mugud'a inna baki tayi hakan yabawa inna damar yin shiru ,Sahura ce tace ”wa yaron biyar biyar ko¿" a'a yaron yace wake ya k'ara tsada goma goma ne , cewa tayi to sako na wazobiya inna mik'omin kwanon kusa dake ,mik'o mata inna tayi duban yaron tayi tace ”kasamin manja da yaji sosai ,bayan yasa ne tace ”inna bismillah kawo kwanonki ,inna da bata wuce tayi ta mik'a kwano aka samata guda d'aya ,Sahura ce taga yaronna kallonta cewa tayi d'an hanse zakaci alelen ne eh yace aikuwa tace to ci d'aya da rabi ninikuma inci biyu inna ga wanan rabin ki kara ,inna na rawar jiki ta kar6i alale tanaci tana lashe rroba."
Saida suka gama ci yaron yace ”Sahura bani kud'in ?" cewa tayi kai na nawa kaci ?" yace ”to ai kece kika bani kyauta ,juyawa tayi gurin inna tace inna kinci na sha biyar ko ? eh inna tace tana zaro ido to talatin kenan ungo murtala sauran kuma sai kubiya ,yaronne yafara kuka yana ihu ,shigowar malam Adamu yasa Sahura zamewa ba tare da kowa ya ankare ba ."
6angaren su Jalal kuwa soyayya suke zubawa wacce babu algus kowa bayason yaji 6acin ran d'an uwansa shiri takeyi zatace hospital gaishe da Khadija da ake yimata k'arin ruwa Jalal ne yace ”Honey inkin gama kizo mutafi ,shagwa6e fuska tayi tace ”anya babyn ma zaibari na fita kuwa ,k'arasowa Jalal yai dai _dai saitin cikin nata da zaiyi wata hudu ya kasa kunenshi yana dariya ,girgiza kai yayi yace ”to baby's sunce ko America zaki saikin dawo ,dukan wasa ta kaimai tana cewa tabb barinzodai mu tafi dan naji ance jikinata yayi tsanani ."
Emergency room aka kwantar da ita saboda lokacin da ta yanke jiki ta fad'i Allah yasa da mutane a gefe ,kwance take ansa mata oxygen wato abin nunfashi ,nunfashinta baya fita sosai kowa ya cire rai da khadija momy kuwa sarkin kuka kullum cikinsa take tanacewa kukuma jarabawarku kenan wayo rayuwa, Saudat ce tayi sallama ita da Jalal amsawa su momy sukayi itada k'anwarta durk'usawa har kasa sukayi suka gaidasu momy dagan an ya ajiye food folks a gefe yace "ya jikin Khadijan da sauki momy tace ”had'a baki sukayi gurin cewa Allah yabata lafiya amen momy tace ”bayan Jalal ya zauna ne yace ”momy number ya Humaid bata shiga yau 3 days kenan ina gwadawa amma a kashe ,momy ce ta share hawayen da suka zubo mata tace ”shima dajin wanan lamarin da yafaru a gidannasu ya kwanta rashin lpy dan naji ance jikin ya tsananta sosai ,Jalal ne ya tausayawa yayan nashi yace ” momy insha Allah jibi zantafi dubo shi to Allah ya kaimu tace ”daganan shiru ya biyo baya."
Momy ce ta shiga room d'inda aka kwantar da Khadija samunta tayi ido a kakkafe tana kuka momy tsabar firgici tayi gurin doctor tana kuka ,da sauri doctor Umar ya shigo yafara gawaje gwaje ,cikin sa'a nunfashin ta ya dawo normal can tafara bud'e ido ruk'o hanunta momy tayi tace ”alhamdulilh daughter Allah yakara miki lafiya ,Khadija babu bakin magana sai kalle kalle takeyi..
Tabarmai nagani da mutane a k'ofar gidansu dady kowa kaganin fuskarsa bbu dad'i zaman makoki akeyi dakuma adu'oi , dady ne keta kar6ar gaisuwa gurin jama'a suna yimasa ya karin hakuri ,washe gari jikin Khadija yayi kyau sosai dan har tana cin abinci sosai ,sallama aka basu suka wuce gida ,Khadija na ganin yan zaman makoki tafara tambayar waye ya rasu ,momy ce ta tuno da sharud'an da doctor ya gaya mata akan ta kiyayen 6acin ranta kokuma shiga damuwa ko gani ko jin fargaba ,momy ce tace ”suna hutawa ne kinsan wanan watan dolle sai anyi meeting da ma'ai kata ta gamsu da baya nin momy shiyasa ma bata k'ara d'aga hankalinta ba....
Kai nimafa mom Islam abin ya d'auremin kai 😢meya faru a gidansu Khadija ??waye ya rasu ??? tabb todai kubiyoni danjin inda muka dosa👏.
Kwance take tana wani matsanancin kuka rabonta da abincin kirki tun da wanan abin ya faru ,tarasa ina zatasa kanta gashi Allah ya jarabeta da abubuwa duka biyu ,alwalah ta d'auro tazo tafara nafilfili tana gayawa Allah damuwarta ,washe gari yaune akayi sadakar uku mutane sun ragu sosai ba kamar daba ."
Kale ² takeyi a d'akin tarasa meyafaru bazata iya tunowa ba ihu tafarayi dan razana take koda wane lokaci ,momy da tatashi akan darduma tayo d'akin da gudu ta sami Khadija nata juya kai tana ihu ,wasu zafafan hawayene suka zubowa momy tayi waje da sauri ,driver ta k'walawa kira cikin azama yazo ya drk'usa a gaban momy _momy ce tace ”maza ka fito da mota mu koma hospital ,komawa tayi ta ruk'o Khadija tafito da ita hijab d'inta ta Sanya mata daganan sukayi mota ,dak'ayar momy ta sata a mota suka wuce hospital, sunyi sa'ar ganin doctor ,inda yake sanar musu cewar su dage da adu'a kuma akwai abinda take tunawa yake tsorata ta magunguna ya kuma basu yace ”ku kulla sosai da ganin tasha magani."
Haka driver ya dawo dasu gida ,matane keta shigowa gidan momy suna yimata ya karin hakuri ,wanan su shigo wanan su fita dayake momyn ta mutane ce .
*KAUYE*
Sahura ce ta shigo gidan inna da gudu tana shewa ,had'e fuska inna tayi tace ”fitarmin a gida nace kifice ko ,dariya Sahura tasa tace ” inna ya alelen ranan waya biya kud'in ¿"ubanki ne ya biya kinji ,sahura ce ta zaro ido tace ” ubana fa sirikinki ne ,inna ce ta d'auko sanda tana shirin buga mata wani yaro yai sallama yace ” Aslamu alaikum zakusi kai da kafar kaza ?" tsalle Sahura ta doka tace ”kai yaro kawo nan shigowa yaron yayi ya nemi guri ya zauna ,Sahura ce ta dubi inna tace ” hmm sai na tuna lokacin da mukaje gidansu Ladidi kullum sai naci kaza ,amma yauma Allah yasa inada ragowar kud'in da Humaidu ya bani d'ari biyu na siya ,dajin haka inna ta washe hak'ora tana dariya tace ”yoo ai siyama zakiyi koda na d'ari ne Sahura ce ta tambayi yaron nawa nawa ashirin ashirin yaron yace ”kasiyar uku hamsin ¿"eh kawo .
Kai ta d'iba guda biyu k'afa kuma d'aya duban inna tayi data zuba tagumi tace ”toke bazaki d'auka bane ?inna ce tace ”to masu abin basuce in d'auka ba ni na isa ,dariya Sahura tasa tace ”laaa ina ki d'auki na hamsin ,inna na sid'ar hannu ta d'auka harda zubo romo ,yaron yana zaune har suka gama ci Sahura tace ”ga hamsin d'inka kajira wanan tsohuwar ta baka kud'inta inna na sud'e hannu tace ”kan uban ke kin biya naki hakafa kikayimin ranar sai malam ne ya biya yana fad'a Sahura dake taunar k'ashi tace ” maganin mai kwad'ayi komai mutum saiyyaci ,inna ce ta kunto zaninta gudar d'ari biyar ce a jiki mik'a wa mai kai da k'afa tayi tace ”k'aromin na hamsin ,dan ubanta ni zata rainawa hankali*LADIDIN KAUYE*
funny & love story
51_52
Yaro dai na ganin ikon Allah ya je ya samo canji ya kawowa Inna ,Sahura ce tace ”au kewai inna kina gadarar zaki bani haushi ne aikin 6urr saidai inbaki haushi ta ja gyalena ta d'aura a kwankwaso ta fizge kwanon da inna tasa a dad'o mata naman ta ruga da gudu ,kuka inna tasa tana tsinewa Sahura tana cewa ,shegiya ga kashe d'ari danayi tashi d'aya gashi iya romo na tsaya sud'a ta wafce kwanon ,shidai mai talla gaba yai yabar inna tanata surutunta."
_JOS_
da sallama ya shigo yana cewa momy yau akayi sadakar bkwai to Allah ya gafarta masa kuka momy takeyi sbda inta tuno abinda yafaru amma aikin gama ya gama rayuwar batajin dad'in yinta sbda Khadija har yanzu sai sauk'in Allah yanzu ciwon 'nata ya koma kamar na mai aljanu in ciwon ya tashi to guduwa take burin yi dady abubuwa sunyi mai ywwa sosai duka dai familyn gidan basuda wal wala ,kwance take tana bacci sai kuka takeyi kuma da k'arfi ,momy ce ta shigo d'akin ta sameta tana bacci kuma tana kuka ,adu'oi tashiga yimata tana tofa mata ,yunk'urowa tayi tana gurnani zata hankad'e momy ,cin sallamar Jalal yasa momy k'wala masa kira ,da sauri ya shigo yana cewa momy lafiya kuwa ¿inafa lafiya Jalal ?narasa yaza’ayi da ciwon Khadija kullum abin baya lafawa kullum cikin fad'a muke gashi banda kunu batacin komai y'an aikin gidan suntafi garinsu ,sai kuma tasa wani kuka mai ban tausayi ,hak'ik'a momy mace ce wace batada zalunci batada mugunta kuma bata fifita wani akan wani ,Jalal shima abin yafara damunshi kukan da momy keyi ya kuma tayarmai da hankali ,sukan sunga jarabawa Allah yasa su cinyeta duka."
Washe gari antashi da wani sanyi mai shiga mai shiga jiki tunda gari ya waye khadija keta ihu tana k'ok'arin fitowa wani girgiza d'akin yakeyi ga wasu k'ara dake baiyyana a cikin d'akin ihu takeyi iya k'arfinta ,dady daya shigo yanzu yai d'akin da sauri ,ganin inda jikin khadija keta 6ari yana makyar kyata yasashi cire hular kanshi adu'oi yaketa karanto mata amma sauki sai lokacin da Allah ya nufa ,gefenta wasu abubuwa take gani masu ban tsoro sai nuni take yiwa dady ina shikam bai gani ba ,ihu take kuma yi tana ruk'o hannunshi amma dady babu abinda yagani yarasa wane ciwo ne ke damun khadija , adu oin da yai mata yasamu jikin ya lafa dan har bacci ya d'auketa."
D'akin momy ya nufa zaune ya sameta kan sallahya