Showing 27001 words to 30000 words out of 33833 words

Chapter 10 - FIRST RAMADAN WITH HABIBI

Start ads

Unknown   

13 Aug 2025

235

Middle Ads

Allah akan baƙin kishi da zuciyarki ke da kinji Dear and ki roƙi Allah ya mallaka miki zuciyar mijinki idan kuma ya ƙaddara miki zama da kishiya ya ba ki hakuri da juriyar danne duk abinda zai kawo miki danasani."

"In sha Allah amma Ammi na ƙarshen nan Ni........."

Common ki yi na ce kuma ki daina kambama kishin hakan ke sa mata shiga uku,ke ko miji ne kika sa a gaba da fitina da shegen dube-duben waya ai baki da sukuni balle kuma wacce zama da ita ya zama miki dole."

"To na ji."na furta hakan ina turo bakina gaba sam banda wadatacciyar walwala tunda ta ambato min kishiya tana datse kiran wata ta ƙara shigowa ganin Sarauniyar jijjida kan First Ramadan with HABIBI group ce ke ƙirana(Shamzee),

"Egiyar gari ina kika shige ne 2days."

Na koma ga Allah stop calling me with that stupid name."

Shegiya na ce do what You can banziya kawai."

Dariya na fashe da shi na ce"Allah ya shirya min ke Shamzee(Zainab ta Shamsuddeen.),Hope dai bakya azumi tunda na ji kina zagi."

Ina yi sai dai in ke zaki min breaking na shi with Your shegen iyeyen tsiya."

Annabi ne ya faɗa not Farrah so mind Your tongue.

"SAW to na ji Astagfirullah wallahi ban taɓa sa nin zagi na karya azumi ba."

Zan turo miki audio clif ɗin ta Whatsapp Habibi ya tutturo min."

Zan kuwa saurara na gode,Kin san mai yasa na kiraki?

No Shamzee

Gidan wancan ƙawar taki Uztaziyyar muka je what that her name i even forget ma Billah."

Hakeema.

Yeahhh ita,shi ne kika sa mana ita a group ga shi kina shirin janyo mana asarar manyan classic ladies dan labarin ghetto Area da muka je muka sameta da muka bayar ya janyo cecekuce a group amma fa ta iya ɗinki gaskiya,kira na yi akan ki je ki cireta if not group ya tarwatse dan we can stay with Fakiriya gaskiyan magana a group."

So what idan group ɗin ya tarwatse,talaka ba mutum ba ne da har zaku fita dan kuna amsa sunan Classic ladies,a matsayinku dana iyayenku me yasa ba zaku yi ƙoƙarin tallafa mata dan ganin kun cireta a halin da take ciki ba,

Haka ne kuma fa wallahi balle in da ta birgeni ba maula take ba hajarta ta tallata amma duk da haka bata cancanci zama a cikinmu ba maganar Allah kawai ki cireta Ni dai.

"Ba zan cireta ba because tama fiku cancanta da ta zauna a wannan group ɗin."

Hujja

Tana auren Social Uztaz the must richest guy a wannan town ɗin .

You mean da gaske ne shi muka gani zai shiga wannan ƙazantaccen gidan rannan har yana gaishe mu muna wucewa,sai da muka shiga cikin mota muka yi ribas sannan Juwairiyya ke ce min Kamar"Social Uztaz."

Na ce mai zai kawo shi wannan jujin amma Meyasa shi yin wannan basajar da matsayin shi da komai na shi.

Neman mai son shi dan Allah.

Aikuwa ya samu am happy For her yanzu kuwa zan je musu da sabon gist."

Alright mu haɗu a group zuwa dare akwai shawarar dana yanke a matsayinku na ƴaƴan masu akwai ya kamata mu kafa gidauniya domin tallafar marayu da kayan sallah,start yours now.

Me ɗin

Investigation

Akan me

Akan gidajen masu ƙaramin ƙarfi a Unguwarku dan ki tallafa musu.

Ba bu ai kin san a GRA nake.

Ok zan je unguwar su Hakeema na da zan binciko the only thing da zan roƙe ku shine ku daure ku tallafa ku bada ƙalilan Allah zai baku kasiran.

To malaman Ramadan."Kit ta kashe wayarta raina ya so sosuwa amma tuno da ɗimbin ladan da zan samu yasa na ji dole zan yi kuma insha Allahu sai marayu sun sa kayan sallah kamar yanda kowane ƴaƴa ke sawa.
  (Dan Allah makaranta littafin nan ku taimaka ma marayu da kayan abinci,kayan Sallah gwargwadon iyawarku,ku tuna kuma watarana ƴaƴanku zasu zama tamkar su kar ku yi tunanin kun bar musu dukiya mai yawa idan wata musiba ta faɗa ma dukiyar fa,idan kuma sun rayu cikin daula ba lallai ne ma su tuna da ku ba tunda baku horesu da tausayi da jinƙan na ƙasa da su ba,talakawa na cikin wani hali a ƙasar nan ku taimake su da abinci da dukkanin abin buƙata kuma Allah zai yalwata muku a sanda babu mai taimakon ku idan bashi ba,ga masu buƙatar tallafawa kuma babu hanyar taimakon ma'ana unguwannin da suke rayuwa ba mabuƙata kuna iya tuntuɓata,kar dai ku manta da har yanzu Yusuf na littafin SUN GUJE NI yana nan yana rayuwa akan keken guragu duk da yana sa ran zai miƙe in kun tallafa, Allah ya bamu abin tallafama na ƙasa da mu alfarman Annabi.)

HAKEEMA.
Miƙewa yake da shirin yi na yi saurin janyo shi dan ina da tarin tambayoyin dake ƙunshe a ƙirjina dangane da shammatata da ya yi,sai dai yanda ya ruƙunƙune Ni ya hanani furta komai dan dole na gumtse bakina tare da rumgumar shi ina shaƙar daddaɗan turaren da ke fita a jikin shi har na ji ana horn a waje,

Kafin ƙiftawar gira da bismillah zarata majiya ƙarfi suka bayyana a ƙofar ɗakin namu wanda alamu sun nuna masu tsaron lafiyar shi ne,gyara min zaman hijabin dake jikina ya yi tare da gyara min nikabin da ke jikin shi kafin ya saƙalo hannuna a cikin nasa muka fito,muna fitowa suka rufa mana baya,

Motoci ne na alfarma guda uku reras a bakin ƙofar gidan yara sun kewaye su tare da yi musu daɓa-daɓa har muka fito,

Umurtan ɗaya daga cikin masu rakiyar na shi yayi da yaga yaran nan kuɗi,dan haka ya fara yi musu rabon ƴan dubu-dubu before You know har manya sun shiga cikin sahu ganin abun bana ƙare ba ne yasa Social Uztaz ya umurce su da su shigo mu je gobe zai zo ya yi rabon kayan abinci,kayan sallah da gyara hanyar ruwa da samar da rijiyar burtsatsi da yin kwalta duk zasu biyo baya da yardan Allah dan a dan zaman da ya yi a wannan unguwar har kamuwa ya yi da zazzabin cizon sauro saboda yawan kwatoci da suka buwayi unguwar tabbas zasu ga aikin Social Uztaz soon.

Iya na hango ta fito ba ko ɗankwali alamun labari ya risketa akan ana rabon kuɗi sai dai ƙurar motocin mu ta hango dan haka aka barta da cizon yatsa ta jikin madubi na hango ta na yi murmushi jin Uztaz ya matse min gefen ciki yasa na yi ƙara da sauri ya rufe min baki tare da ce wa"Idan kika kuskura kika karya min azumi Hajiya will make sure ta rama min."Sororo na tsaya kallon shi ganin yanda yake magana cike da shagwaɓa da sangarta tuni zuciyata ta ƙara dulmiya a cikin ƙaunar shi,

Sannan na yi mamakin yanda ya iya yin basajar dawowa mafaɗacin ƙarfi da yaji,ban gama mamakin wannan ba sai da naga motocin sun tsaya suna horn a wani makeken Estate wanda ya yi gari guda,buɗe mana get ɗin suka yi sannan suka cilla motocin saman kwaltar da ke shimfiɗe,a daidai wani tamfatsetsen gida wanda na yi ma laƙani da aljanar duniya Suka yi parking nan take suka fiffito suna jiran namu fitowar,Uztazuna kuwa sai kallona yake yi ganin yanda na sake baki da hanci ta cikin nikabin ina kallo,lakuce min hanci ya yi kafin ya ce"Mu je ko Qalbee and kar ki badani wajen kallon nan naki Please a cikin Family kin ji You Are my choice forever and ever."

Sunne kaina na yi alamun jin kunya sannan ya kama hannuna muka shige bayan ya dakatar da masu tsaron lafiyarsa,wani tamfatsetsen ƙofa muka dumfara bayan ya danna wasu lambobi gilashin ƙofar ya bude muka shige.

Tun daga bakin ƙofa yake ƙwala ma Ummiee ƙira bayan mun yi sallama,jin bata amsa ba yasa ya ajiyeni a falo ya shige in da nake da tabbacin uwarɗakanta ne,buɗe manyan idona na yi ina kallon Royal chairs ɗin dake cikin ƙasaitaccen wannan falon,na yi saurin kai dubana kan katifa-katifar da ƙafata ke nutse a ciki na ga ashe kafet ne,ƙare ma ko'ina kallo nake dan har ga Allah Ni tunda nake a duniyata ban taɓa ganin gida mai kyan nasu Uztazuna ba sai dai a irin fina-finan ƙetare,jin motsi daga gefena yasa na yi saurin daidaita nutsuwata sai dai jin Muryar wata hamshaƙiyar mace da ƙamshinta yasa na ji kawai na raina zamtowata sirika a wannan gida ya kamani.

Tuni na tsantsani kaina na takure waje ɗaya,yayinda take dumfaro Ni haka duk takun nata ke tafiya da bugun da zuciyata ke yi da sauri-sauri har ta iso gareni tana yi ma ni wani irin kallo.......

To fah Fans ana wata ga wata mu je zuwa,ya dai kamata a samu wata ƴar aljannar ta haɗa mana document na littafin nan dan sama min sauƙi na gode.




Ummu-jidda.
FIRST RAMADAN WITH  HABIBI.
  💔Heart touching story.💔


FARIDAT HUSAIN MSHELIA (UMMU-JIDDA).



*ZAFAFA WRITERS ASSOCIATION*



https://chat.whatsapp.com/H16N47YvbD60SKUCaNRF6Z


TSARABAN RAMADAN.
Ka zamo mai kyauta, Amma kar kyautar ta janyo maka riya.

LAMBA NA SHA TAKWAS.
Har ta iso gareni tana yi ma ni wani irin kallo mai cike da tsantsan soyayya da sauri ta ɗagoni tare da rungumeni a cikin jikinta,Muryar Uztaz na ji yana ce ma Ummiensa"Wayyo Ummiee kar ki karya min ita bata da ƙarfi."

Daƙuwa ta yi masa ya yi saurin ƙarasowa yana niyyar zuwa gurina na yi saurin hararar sa ƙasa-ƙasa ina yi masa gargaɗi da idona cikin sanyi Ummien ta fara yi min sannu da zuwa na yi saurin duƙawa na gaisheta cike da girmamawa,amsa min ta yi cikin sakin fuska da soyayya kafin ta umurci Uztazuna ya kaini sashenshi mu shirya muna da hadaɗaɗen buɗa baki wanda aka shirya na musamman domin taryata a cikin wannan zuriya mai albarka,

Kama hannuna yake shirin yi ta yi saurin bige hannunsa tare da kama hannuna muka yi cikin ɗakinta ya yi saurin mara mana baya,

"Ni dai naƙi wayon Ummiee ki bani matata kawai,ke fa kika ce in je mu shirya kuma kina shirin yi min ƙwalele."

"Anƙi ɗin je ka faɗa ma Abbanka in yaso ya zo ya ƙwatar maka matar mara kunyan yaro kawai,ƙiri-kiri ka maidani kakarka ta ƙarfi da yaji."

Ficewa ya yi fuuu ya barni da baki hangame cike da mamakin gidansu da tsarinsu mai cike da gamsarwa,ji na yi ina kewar nawa Mahaifiyar na ji hawaye ya taru a idona jin an dafani na yi fara ƙoƙarin maida shi,zaunar da ni Ummiee ta yi tana min hirar Social Uztaz, murmushi kawai nake zabgawa har ta kama hannuna zuwa banɗaki,sake hannuna ta yi  bayan ta nunnuna min yanda zan yi amfani da komai a taƙaice,saurin kai hannuna kan famfon na yi naga ya zubo ina cirewa na ga ya ɗauke a zuciyata na ce lallai duniya ta cigaba Allah ya azurta duk wani bawa da arzikin duniya dana lahira amma tabbas masu akwai suna walawa,gani dai a banɗaki amma kamar a wani ƙayataccen ɗaki nake,jin alamun motsi yasa na miƙa bayan na gama ƙare ma shahararren banɗakin kallo mai kama da wata daula,

Shafe kusan minti talatin na yi ina cuccuɗa jikina da  sabulai masu ƙamshin gaske kafin na ɗaura tawul a kirjina na zuro hijabina na fito zuwa ɗakin bakina ɗauke da sallama,ba kowa sai kayan da zan sa a kan gadon dan haka na cire hijabin na fara shafa mai wanda rabona da shafa mai ai tun kafin azumi amma tunda na shigo gidan nan sanyin Ac yasa na mance da ana zafi ma hadda zama ina ƙalailaye jikina,ina cikin shafa na ji an turo ƙofar an shigo dan haka na dirirece sai dai ganin Uztazuna ta jikin standing mirror yasa na turo baki,

Rungume hannun shi ya yi a kirji yana ƙare min kallo ta jikin madubi jin wani kasala na niyyar rufe shi ganin lafiyayyen fatata da rabin ƙirjina a waje yasa ya juya cikin muryan tsokana na ce"Ina zuwa rasa kunya."

"Azumina zaki karya min Allah matuƙar na tsaya ina kallon wannan lallausan fatar naki."ban ce mi shi komai ba har ya fice nima na cigaba da shirina na gama sa kaya kenan wata matsashiyar budurwa ta shigo ta gaisheni kafin ta sauke jakarta ta fara tsamtsara min light makeup wanda ya yi matuƙar dacewa da round face ɗina,

Warware ɗankwalin kaina ta yi ta min ɗaurin manyan mata kafin ta ciro wata alkyabba a kwali ta warwareta ta samun bayan ta umurce Ni da ,miƙewa,baƙace adon dake gabanta golden ne,dan haka sarƙar da ta sa min da ɗan kunne ya kasance golden
takalmi ma haka, turarurruka masu sanyin ƙamshi ta feffesa min tare da gyara min zamar hular alkyabbar a kaina.

Fatubarakkallahu ahsanu khalikin!Gaskiya matan Social Uztaz ke kyakykyawa kuma kin yi dace da samun miji nagari.

Murmushi na mata bayan na ɗago fuskata na kalli kaina a madubi,gani na yi kamar bani ba dan Ni kaina bansan haka nake da kyau ba sai yau,da man Ni fara ce dan haka adon baƙin kaya da brown na leshin ya fito da Ni.

Chanchaɗi!Muryar Uztazuna ya daki kunnena na yi saurin ɗagowa ina ƙare mi shi kallo dan shigar shi mai kama dana Yarima ya yi matuƙar tafiya da imanina,baƙin yadi ne kofta aka mi shi ado irin na sarakuna a ƙasan wandon da hannun sai gaban rigar sai farin gariyar da yasa wanda tasha aiki kamar daga Mali(Daga Zaria ne kun san nan ma muna da ƙwararrun masu aikin hannu da designers)Hular shi mu haɗu a banki ya kafa mai ruwan fari da baƙi sai ɗigon ruwan kunkumadi a jiki,sai half Cover daya sanya baƙi mai design ɗin aikin da ke jikin shi,nan take na ji haiba da kwarjinin shi ya cika ruhina dan haka na yi saurin yin ƙasa da idona ina gode ma Ubangijin sammai da ƙassai,

Ɗagoni ya yi yana shaƙar daddaɗan turarena duk da tun daga shigowar shi ƙamshim shi ya buwaye mu,hoto ya fara yi mana ganin yanda muka zamto zara a cikin taurarin da ke sama,

Ban san lokacin da mai min kwalliya ta zurare ba dan zuciyoyinmu ya yi nisa Ni da Uztazuna sai jin muryan Ummiee na yi na fara kiciniyar ya cikani yaƙi,

Murmushi Ummiee ta yi irin nasu na manya kafin ta ce"Sai hakuri ba ɗiyata dan wannan da kike gani ba kunya ce da shi ba sai du'a'i."

Zumburo baki ya yi zai yi magana ta yi saurin nuna mi shi agogon dake ɗaure a jikin hannun shi(Rollex)ganin lokaci ya tafi yasa ta yi gaba muka rufa mata baya.

Faffaɗan falo wanda zai iya cin mutum ɗari hadda ɗoriya muka shiga,nan muka tarad da mutane zaune akan daddumomi na alfarma suna jiran isowar mu,tada salla aka yi muka bi sahu dan lokacin shan ruwa ya gabato,ana idarwa Uztazuna ya ja hannuna zuwa gaban Alhaji Bisallah muka durƙushe muka yi gaisuwa, addo'o'i ya dinga sharara mana kafin aka fara shigowa da abin buɗa baki kamar mutum dubu ne zasu ci,ɗaukacin ilahirin Ahalin su ne a wannan Estate ɗin kuma alhamdulillah duk sun hallara an gabatar musu da Ni a matsayin matar Uztaz wasu sun karɓeni hannu bibbiyu wasu kuma ta ciki na ciki musamman kishiyoyin maman shi dake jin kamar su shaƙeni in mutu,an ci an sha kuma an mana nasiha mai gamsarwa nan take aka dinga bina da kyaututtuka na alfarma.

Ganin na gaji yasa Ummiee janyeni muka shige ciki kamar jira yake mu shiga ɗakinta ya biyo mu cike da gajiya ya ce"Ya kamata mu kwanta, Allah na gaji."ya furta hakan yana cire babban rigar dake jikin shi da hular yana mai kwanciya akan gadon Ummiee .

Oh ni ƴar nan me haka kuma goɗoɗo da kai a gadona dan Allah,na ga abinda ya isheni bai ishi Allah ba."

Dariya ya shiga yi ya ce"Nima yau anan zan kwana a gadon Ummieena."

"Saboda matarka ko?"ta tambaye shi ya fara sosa ƙeya yana dariya ƙasa-kasa sunne kai na yi ina jin tamkar ƙasa ta buɗe in shiga dan kunya dan sam Uztazuna bai da ta ido ina cikin tunanin hakan na ji Ummiee ta ce"Ƴar albárka tashi kije ku kwanta kin ji."

Ya daka tsalle ya miƙe tare da ɗaura min babban rigar shi a jikina ya riƙe ƙugu alamun in miƙe,bin shi da throw pillows Ummiee ta yi da sauri ya yi waje yana dariya,ganin naƙi motsawa yasa Ummiee ta ce"Tashi ki bi mijinki kinji ina jin motsin shi a falo."

Ni a nan zan kwana."

Kul ɗinki yanda mijinki ke son ki da mararinki sam kar kiyi wasa da damarki na riƙe shi gam-gam dan maza tsada suke a wannan lokacin ko so kike ya miki kishiya."

Na girgiza kai tare da rufe idona da tafukan hannuna guda biyu,nan take ta shiga yi min nasiha da yanda zan kula da mijina tare da faɗa min duk wani abinda ta san Uztazuna na so tun daga girman shi har yarintar shi,hannuna ta kama ta fitar dani daga shashinta tafiya mai tsawo muka yi har muka riski sashin shi wanda tun daga ƙofar shiga na ga alaman yafi na Ammi haɗuwa har cikin falon mai kama da aljannar duniya ta shigar dani jin alamun motsi daga cikin banɗakin falon yasa ta zarce da Ni uwarɗaka,anan na saki baki da hanci ina ƙarema gadon shi mai siffar mota kallo jin na lumtsuma akan katifar dake ɗaure akan yasa na jini a wata duniyar na daban nasiha sosai ta yi min kafin ta fice bakinta ɗauke da albarkar da take ta sanya min dan tun data ɗaura ido akaina ta ji na kwanta mata arai ta ji tana min kwatankwacin ƙaunar da take yi ma ƴaƴan cikinta,shiru na yi ina nazari can dai na ɗakko wayata na buɗe data dan ganin wainar da ƴan group ɗin First Ramadan with HABIBI ke toyawa.

Hirar su na dinga bi ɗaya bayan ɗaya har na ƙara so kan hirata da yanayin gidan hayar da nake ciki bayyanar social Uztaz a matsayin mijina ya yi matuƙar ɗaga musu hankali,dan basa sona sam tunda Ni talaka ce sai ga shi Allah ya azurtani da samun miji wanda ya wuce tunaninsu,ƙalilan ne daga cikin su suka tayani murna Farrah ita ce kan gaba kafin aka dawo tattaunawa dangane da tallafin marayu da Farrah ke son wakilta, ya samu karɓuwa ba laifi sai dai an samu masu kushe tsarin,

Tun ina zaune har na kai ga kwanciya dan saƙonnin sun yi yawa,duk wanda ya kamata in mi shi reply na mi shi sannan na fita a group ɗin,duba Farrah na yi naga bata online dan haka na ajiye mata saƙo zuciyata cike

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login