Showing 18001 words to 21000 words out of 33833 words
su more ma ran su."
"Au nine talaka ko dan haka bana bacci in more ma rayuwata, to daɗin abin dai duniya da kayanta aro ce ga mai hankali kuma suma ba rawa suka taka Allah ya basu arzikin ba."
"Ni fa ban ce ba Noor haba mene na min mummunan fassara."
"Ni kuma na san kin ce su masu kuɗi Ni talaka."
Dariya ce taso suɓuce min na yi saurin rufe bakina saboda yanda ya yi kicin-kicin da fuska na ce"Talaka bawan Allah ba."
Ya yi murmushi yana jifata da kallon zan rama cikin hanzari na haɗa hannayena biyu alamun roƙo na ce"Afwan Noor, ƙarfe 12 suka ce zasu iso kuma da yardan Allah za su zo ɗin, ka san Classic ladies na First Ramadan with HABIBI group masu koyi da turawa ne dan haka suna kiyaye lokaci kuma suna ƙoƙarin cika alƙawari."
"Kyakkyawan halayya ta Annabinmu dai ai turawa kwaikwayo suka yi tare da yi mana wayo suka ɗauki cika alƙawari abu muhim suka bar wasunmu da wasa da lokaci da rashin sanin muhimmancinsa,uwa uba alƙawari wanda sosai Annabi ya yi jan kunne a kan shi har ma ya siffanta rashin cika alƙawari da alamu ne na munafurci."
"Hakane tabbas to Ubangiji ya yi mana muwafaƙa."
"Amin ya hayyu ya ƙayyum,to ni zan fita na ga 10 ya kusa yau Ni zan ja ma Malam aya a gurin tafsir."
"Ma sha Allah,Ubangiji ya sa a mizani ya kuma kai min kai lafiya ya dawo da kai lafiya."
"Amin."ya sa kai ya fice wani irin daɗi naji jin gurin yaɗa alhairi zai je na tsani jin ya ɗauki mashin yana shawagi da shi a gari,tashi na yi na kimtsa wajena tare da feshe shi da turare(Airfeshner),sannan na bi lafiyar kujera nan da nan wani bacci mai daɗin gaske ya yi awon gaba dani.
Ƙarar wayata ne ya farkar da Ni ganin numban dake kirana yasa naji wani daɗi ya kamani na kai dubana kan agogo naga shabiyu dai-dai na yi saurin amsa kiran ina musu kwatance har suka gane gidan,jin ce war sun iso yasa na sa hijabina tare da ficewa waje na musu iso,
Ba yabo ba fassala haka suke amsa min komai dan basu ƙarajin sun rainani ba ma sai da suka ga tsakurkurin muhallin da nake rayuwa a ciki wanda suka tabbatar da na hayane,ko a jikina wai an mari kakkausa sai ma washe musu baki da nake yi Ni dai babban burina su bani ɗinki,
ganin yanda na musu yasa kowacce daga cikin su ta bani kala bibbiyu akan in fara yi musu a matsayin gwaji bayan sun tabbatar min da Inna ɓata musu zannuwansu ba sa Ni ba sabo nan take na ji sun wanke min ido dan haka na gwada kowacce tare da cajar kowaccensu dubu goma -goma kowani kala ɗaya yana matsayin dubu biyar na yi musu hakan ne dan su san na san kan aikina dan haka a take suka bani dubu biyar biyar kafin muka yi sallama suka fice da sauri da man kamar a ƙaya suke jin kansu.
Kiciɓus.........
*Da fatan munsha ruwa lafiya Fans a min afuwa abubuwa sun sha kaina jiya zuwa yau ga double page nan,ina yinku fisabilillah*
Ummu-jidda.
FIRST RAMADAN WITH HABIBI.
💔Heart touching story.💔
FARIDAT HUSAIN MSHELIA (UMMU-JIDDA).
*ZAFAFA WRITERS ASSOCIATION*
https://chat.whatsapp.com/H16N47YvbD60SKUCaNRF6Z
TSARABAN RAMADAN.
*Duk abinda ka rasa, matuƙar imanin ka na tare da kai wallahi ba ka yi hasara ba, haka duk abinda za ka samu kuma, matuƙar ka rabu da imanin ka wallahi ka yi hasarar duniya da lahira.*
LAMBA NA SHA UKU.
ABBIYN DIYAH.
Mahaifin Farrah kuwa tunda yake a Rayuwar shi da matar shi(Ammi)bai taɓa jin ya yi danasanin yanda ya sake mata jan ragamar rayuwar gidan shi ba sai da faɗan da taje ta yi da sirinkinta(HABIBI)ya ji zuciyar shi ta shiga ƙunci mara misaltuwa dan haka a karon farko na tsawon rayuwar su da shi da ita ya ɗauke mata wuta,ko kallo bata ishe shi ba,ya daina cin abincinta ya ƙaurace mata a shimfiɗa ko gaishe shi tayi irin na su na ƴan boko ciki-ciki yake amsawa,nan fa ta shiga cikin ruɗani kamar yanda ta kirani a waya take sanar da ni halin da suke ciki da mahaifina bayan an sha ruwa,
Haƙuri na bata tare da bata shawarwari dan Ni kaɗai ke gareta babbar ƴa dan haka sam Bama ɓoye ma junanmu sirrinmu,
Tashi ta yi bayan mun gama wayar ta je ta fara aiwatar da ƙudurinta sai dai hango katin ɗaurin aure zube a gaban Abbiy bayan shigarta cikin ɗakin tana gwalangwatso yasa ta ji ƙafafunta sun yi sanyi,
Ƙara sawa ta yi cikin son jan magana ta ce"Auren wa za'a yi kuma ba labari Abban Farrah duk cikin fushin........"sauran maganan ya maƙale a bakinta hango sunan mijinta ɓaro-ɓaro a jikin katin tare da wata mace da sauri ta zabura ta yo kan shi ta ce"Aure Mansur!
"Ni zaka tozarta ka cima mutunci bayan shekara arba'in da aurenmu sannan ka ce zaka yi min kishiya?"ɓanɓare hannunta ya yi daga jikin shi ka fin ya ce"Ai an daɗe ana ruwa ƙasa na shanyewa Fatsuma saboda haƙurina ya yi yawa,sai dai ban san ashe haƙurin nawa lalata tarbiyyar ƴaƴana zai yi ba,rashin tarbiyyar ya bibiye su har cikin gidan aurensu su da mazajenmu in sun hayayyafa ya bi jikoki hadda tattaɓa kunne duk tsawon shekarun nan ban fuskanci hakan ba sai da kika bi ƴarki har cikin gidan mijinta kina shirin faɗa da sirikinki saboda kin saba yi min faɗa da tsawa daga ƙarshe kuma in dawo ina baki haƙuri saboda sanyin halina,ina hakan kawai dan son zaman lafiya ne ba wai dan abin baya damuna ba ashe-ashe babban kuskure na tafka na rashin taka miki birki da banyi ba ga shi ya wuce kaina da mutanen gari da ƴan'uwana ya komq kan mijin ƴar........"ta katse shi cikin zafin rai,
Duk wannan dogon jawabin na son ka gamsar da ni ce wa faɗan da baka bari munyi da Mashkur ba shine dalilin da yasa zaka ƙara aure?
Ko mai kake son fahimtar da nine dan Allah bana fahimtar ka sam."
Abin da na ke nufi zan yi aure dan in raya sunnar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama tare da gyara kuskuren da na yi na zaɓenki a matsayin mata kuma uwar ƴaƴana.
Buɗe baki na yi zan yi magana ya yi saurin dakatar da Ni"Ba shawara nake nema ba na riga da na aiwatar da ƙudirina kuma a shirye nake da duk wani mataki da kike ganin zaki ɗauka ko min muninshi,ba kuma sai mun je kotu ba kamar yanda kike iƙirarin kai sirikinki kina iya faɗa min a yanzu in baki takardar ki.!
Daramdam!haka zuciyarta ta yi wani irin bugu dan jin Abbiy na nuna mata ita yanzu bata gaban shi ko rabuwa ce ta shirya zai rabu da ita lallai abin babba ne bata dawo daga vibration ɗin da yasa ta ba ya ƙara ce wa"Sai dai ki sani ke kaɗai kika shigo gidana ba tare da ƴaƴana ba dan haka ki tafi ke kaɗai Matana zata riƙe kuma ta basu tarbiyyar da duk Yakamata uwa tagari ta ba ƴaƴanta."durƙushewa ta yi a wajen ta rasa ma a wata duniyar take ciki nan take jikinta ya fara rawa ƙirjinta na sama na ƙasa take yanke ta fara kokawa da numfashinta sam yaƙi daidaita take yanke ta faɗi a wajen sumammiya,
Ko a jikin Abbiy hasalima tashi ya yi ya fice ya kira Kulu akan ta zo ta zuba mata ruwa ko zata farfaɗo sai dai ina ta yi nisan zango dole sai da ya figi mota zuwa babban asibitin da take aiki a ciki nan take likitoci suka rufu a kanta domin ceto rayuwarta sai dai ko ta farfaɗo tana tuno Abban Farrah zai yi aure take fara jijjiga kafin ta kara komawa gidan jiya,
Abbiy kuwa addu'a kawai yake mata na samun sauƙi dan alƙawari ya ɗauka koda Ammin Farrah mutuwa zatayi to wallahi sai ya yi aure dan ya zamto ma mata darasi a rayuwar su musamman irin matan da ke maida mazajen su tamkar ƴaƴan da suka haifa kawai saboda Allah ya yi zuciyar mazan na su da haƙuri.
Kwananmu biyu a asibiti da Ammina alhamdulillah jikin da sauƙi sai dai tana zaune zakaga ta firgita tsigar jikinta ya miƙe a ranar kuma aka ɗaura auren Abbiy da tsohuwar budurwansa wacce iyayensa suka mashi zaɓi ya tubure shi bai son baƙauyiya ƴar boko zallah yake so,ta yi aure hadda ƴaƴanta Allah ya karɓi rayuwar mijinta Abbiy na shiga cikin ruɗanin halin matar shi yasa ya ji ya kamata ya mata kishiya wataƙil hakan zai sa ta dawo cikin hayyacinta ta gyara halayyarta.
A daren ranar suka zo shi da matar ta shi asibitin domin duba Ammina da jiki in da ta......
HAKEEMA.
Kiciɓus suka yi da Uztaz wanda yake shirin shigowa sai dai irin kallon ƙasƙancin da suke mi shi yasa ya haɗiye sauran kalmar gaisuwar da yake musu cike da fadanci,
Sai shegen kallo kamar mutum zai haɗiye mu."ce War ɗaya daga cikin ta furta hakan tana tsaki suka raɓa ta gefen shi suna fice,ƙara gyara tsayuwar ya yi har sai da ya ji dirin tashin motocin su sun tafi sannan ya shigo ɗakinmu sallama ɗauke a bakin shi,
Matse fuska na yi dan har ga ina jin haushin yanda Uztazuna ya iya ƙare ma mata kallo wannan halin shi ne koda kina cikin Hijab da liƙabi ne balle kuma waɗannan da ke yafe da gyale iya kafaɗa.
"Baƙin Alhairi sun zo har sun tafi."ya furta hakan ko damuwa da yanayin fuskata bai yi ba,
"Eh sun zo."na amsa mi shi a taƙaice,
"To ma sha Allah,ki ce yau a kwai mu da cin ƙwalam da maƙulashe?"
Da kuɗin kayan aikin ko kuma kuɗi ka samo mana?
Da ribar ki na ɗinkin dai za ki bani in sayo mana irish da ƙwai,mangyada sai mu yi stew na kwana biyu kin ga kin samu damar hutu kina tashi sai dai ki ɗora mana shinkafa ko taliya."
"Hakane gaskiya Noory,lallai yau kayo mana samuwa tunda har dage-dage za mu ci."na furta mi shi haka cike da gatse cikin wasa ya ce"Tabbas yau na samu kyautar kuɗi har dubu goma amma...."
Me?na yi saurin katse shi,
Na canza ma tsuntsun soyayyarmu robar gaba dana baya dan haka dubu 1 ne kacal a tare da Ni."
Ya yi kyau Allah ya ƙara arziki.
Ya amsa da "Amin."
Shigewa ciki na yi saboda takaici da baƙin cikin da Uztazuna ya ƙunsa min wato Mashin ɗin shi yafini muhimmanci tunda ko ƙwayar shinkafa ba mu da shi amma zai iya kashe ma Mashin dubu tara kawai dan ya cigaba da bagu to Allah kuwa zai sa Ni.
Biyoni ya yi cikin raha ya ce"Ai in faɗa miki alhajin nan namu(Mai makarantar su) miliyan goma ya cire a cikin dukiyar sa ya ce a raba ma mabuƙata musamman mu da muke aiki a ƙarƙashin shi amma saboda mugunta irin na ɗan Arewa ƴan'uwan shi suka rabe kuɗin a tsakanin su,wani ya ɗau miliyan 5,wani 3 wani biyu sauran miliyan ɗayan shine aka kakkasa mana hadda gero da su suga."
Ina suke to."
Na sadakar mana to Ni dake da ke Hajjaju mai zamuyi da wani gero ai sai dai kiyi mana kunun gadara da madara ya ji kwakwa a ciki,
"Zaka sha kuwa."na furta hakan a cikin zuciyata tare da raɓawa gefen shi zan fice ya riƙoni yana ce wa"ina zaki je?"
"Banɗaki kuma a uzurce nake."
Sakina ya yi tare da samun bakin gado ya zauna yana jirana in dawo in ba shi kuɗin cefane mu ci irish da ƙwai ,da miyan dage-dage har mu kora da Kunun gadara da madara mai kwakwa.
To fah bari muga ko tare zasu sha kunun nan tare da ku Fans idan Hakeema ta ba shi kuɗin ribar ɗinki.
*Kun rage comments shiyasa jikina ya yi sanyi da typing ɗin fatan za ku gyara in ci gaba da typing sau biyu a rana Na gode."
Ummu-jidda.
FIRST RAMADAN WITH HABIBI.
💔Heart touching story.💔
FARIDAT HUSAIN MSHELIA (UMMU-JIDDA).
*ZAFAFA WRITERS ASSOCIATION*
https://chat.whatsapp.com/H16N47YvbD60SKUCaNRF6Z
TSARABAN RAMADAN.
Haƙiƙa shi ilmin addini shine ado da kwalliya a garemu, dukkanin wanda bashi da ilmin addininsa, to haƙiƙa yana cikin duhun jahilci wanda shaiɗan ya dilmiya shi cikinsa,dan haka wannan littafin ki zaburantar da mata ƴan boko zalla da su miƙe su nemi ilimin addini saboda sai min san Allah kafin za mu bauta mi shi,kuma bai yiwa ka san ubangijinka batare da ka nemi ilimi ba.
LAMBA NA SHA HUƊU.
AMMIN FARRAH.
A daren ranar suka zo shi da matar ta shi asibitin domin duba Ammina da jiki in da ta fara kokawar miƙewa zaune sai dai kash ta kasa saboda yanda jikinnata ke mata matuƙar nauyi cike da nadama ta ce"Mansur amaryan taka kenan?"
Abbiy ya ɗaga mata kai alamun "Eh."
To Ubangiji ya baku zaman lafiya mai ɗorewa.
Suka amsa da "Amin."Fashewa ta yi da kuka Zuciyarta na mata ƙona tsabar kishin da ke azalzalarta amma ciwon da Allah ya jarabeta da shi sam bata da wani kuzarin gabatar da dukkanin ƙudurin da ta yi niyyar aiwatarwa idan mijinta ya mata kishiya,
Lallai ɗan adam ba a bakin komai yake ba kuma ba zaka san da hakan ba sai Allah ya baka komai na duniya ya hanaka lafiya hawayen tausayin kanta take yi har Abbiy ya ƙaraso gaban gadon ya kama hannayenta biyu cikin son kwantar mata da hankali ganin yanda ta yi laushi yasa ya ce"Ki yi haƙuri Fatima, wannan auren ƙaddara ce da rabo dan rabon shi ya kashe mijinta dan in aureta, babban abinda nake sonki da shi ki kwantar da hankalinki ki samu lafiya alfarman Annabi da Alkur'ani zan kwatanta adalci a tsakaninku Ni dai babban burina ki canza halayya kin ji."
Da yardan Allah zan canza dan inaji a jikina ba zan ƙara rayuwa ba a duniya tunda har wata ta mallakeka,Gara in kyautata tsakanina da Allahko zan dace da aljanna.
To ai aljannar sai ya ɗaga ƙafa sannan zaki shiga ƴar'uwata ki yi hakuri sannan ki rungumi ƙaddarar ki in sha Allahu Ni ɗin alhairi ce a gareku ba zan taɓa shiga tsakanin soyayyarku da mijinki ba."Ce War Amaryan Abbiy wacce ta tattako ta ƙara so gaban gadon da Ammie ke zaune ta ja kujera ta zauna tana fuskantar Ammina fuskarta ɗauke da murmushi,
Wani sanyin daɗi ne ya shiga ratsa kowani lungu da saƙo na jikina har ban san lokacin da na furta Alhamdulillahi ba a zuciyata ashe a fili na furta hakan har yasa hankalin Abbiy da amaryan ya dawo kaina dan sam basu san ina cikin ɗakin ba saboda sun shigo ina salla idarwata kenan,
"Farrah mai kike yi anan baki koma gida kin ma mijinki abin buɗa baki ba?"
"Na je dawowa na yi Abbiy na kawo ma Ammina abincin dare shi ne Mashkur ya ce in kwana tare da ita."
"Sam ba za'a yi haka ba maza kira shi a waya ni aikin me nake yi da ɗiyata amarya zata kwana a asibiti ta bar mijinta."Ce War Amaryan Abbiy.
Ganin duk mun zura mata na mujiya mamaki shimfiɗe a fuskarmu ya sa ta ce"Maza kira min sirikin nawa ki koma gida Ni anan zan kwana da mamanki ai kin yi ƙankanta da jinya irin wannan."
Tuni asirin zuciyata ya fallasu akan fuskata dan haka na fara murmushi cikin jin kunya na fara ƙoƙarin gaisheta,
Buɗe min hannayenta biyu ta yi alamun in iso gareta da man na santa tunda daɗewa mutuniyar kirki ce ta bugawa a jarida muna haɗuwa da ita a duk wani sha'anin ahalin gidan su Abbiy,Ammi ce ta gargade Ni da daina gaisheta ko ta cire min kwankwaso tunda ta san an so haɗata da Abbiy dan haka take kishi da ita ala dole in muna tare da ita nake kauda kai sai dai in mata sansanyar murmushi itama ta maida min da nata sansanya dan mace ce da bata son matsala,ko da naji hukuncin da Abbiy ya yanke akan Ammina jinjina mi shi na yi dan hauka ɗaya ma HABIBI na karɓi bulala to ina ga shi daya ɗauki tsawon shekaru arba'in tare da Ammi mace mai shegen mitan tsiya da faɗa,gwaliya,ƙyaliya da raina duk wanda bai kaita ba shine halayyarta,kamar yaron aikinta haka ta ɗauki Abbiy yana zaune zata aike shi ya ɗakko mata abu kuskure kaɗan zai yi mata ta balbale shi da faɗa kamar zata duke shi,ita kaɗai ce gwana a duniya duk wanda ya aikata saɓanin abinda take so ya shiga uku ai ma ya yi matuƙar ƙoƙari wallahi dan kullum cikin nasiha da faɗa mata matsayin shi a gareta yake amma ta gagara ganewa ina da tabbacin ba dan ya mata hakan ba ba zata taɓa nadama ba (Ni kuwa na ce Allah dai ya so ta da shiriya ai ba dan yasota ba da akan kishiyar sai ta ƙara zarmewa, Allah ya shiryi mata masu irin halin Ammi ya sa kuma su yi nadama tun kafin lokacin da nadamar bata da amfani zata riske su.)
Ganin na zurfafa a cikin tunani yasa Hajiya Amina tasowa ta iso gurina ta ɗago Ni duba na kai kan Ammina wacce jikinta ya mata nauyi ta gagara miƙewa naga hawaye na zuba a idonta da sauri na ƙarasa gurinta cikin gunjin kuka na ce"Dan Allah dan Annabin shi Ammina ki cire damuwa ki rayu ko dan mu da ƴan'uwana kin san daga Allah da Annabin shi bamu da kowa sai ke,ke ce sanyin idaniyarmu kar ki tsawwala ma kanki damuwa akan Abbiy ya ƙara aure Sunna ce ta Annabinmu,wanda ya fi kowa ma a duniya da lahira matan shi sun zauna da kishiyoyi to ina gamu?.
Still hawayen take yi bakinta sai rawa yake yi yana ɓari amma ta gagara motsa shi ta yi magana,hannun Hajiya Amina na kama na haɗa shi dana Ammina cikin kuka na ce"Ammina ga amanar abokiyar zamanki na baki haƙika na yarda da halayyarta da kyakkyawan ɗabi'unta ke ce kawai zuciyata ke taraddadin yanda zaki karɓeta Ni kam zuciyata ya natsu da ita."
Bisa ga mamaki sai na ji Ammina ta ce"Nima na karbi ƙaddarata hannu bibbiyu tabbas idan har Allah ya ƙaddara zan miƙe akan dugadugaina sabuwar Fatima ce wannan mai koyi da halayyar ɗiyar Manzon Allah da yardan Allah."
Take Abbiy ya durƙushe akan gwiywowin shi biyu ya sa fuskar shi a ƙasa ya yi ma Allah sujjuda ta godiya da farincikin ganin wannan rana na shiryuwar masoyiyar shi kuma uwar ya'yan shi,
Koda ya ɗago rungume su ya yi dukkanin su biyu yana shi musu albarka kafin aka