Showing 3001 words to 6000 words out of 33833 words
mata tambayar a harzuƙe dan ya san DIYAH ɗin sa ta iya girke-girken alfarma to mai yasa a wannan karon za ta kunyata shi.
A Tiktok na ga wata Chief ta ɗaura,sunan shi kawai ya ja hankalina na sauke shi a kan wayata kuma musamman na tanaje shi sai a farkon watan Ramadan dan in burgeka da shi HABIBINA.
Tiktok........
More comments
More Typing..
Ummu-jidda.
FIRST RAMADAN WITH HABIBI.
💔Heart touching story.💔
https://chat.whatsapp.com/LM4sMyc4lT5Jgnv9lw1vOS
FARIDAT HUSAIN MSHELIA (UMMU-JIDDA).
TSARABAN RAMADAN.
*LADUBBAN HAWA KAFAR SADARWA A RAMADAN*
*Mu nisanci yaɗa musu, jayayya, da zage-zage ko ƙarya musamman kan Addinin Musulunci. Da masu zama su ƙirƙiri labarin ƙarya mara amfani.*
LAMBA TA UKU.
TIKTOK ki ka ce fa?
cike da mantuwa na furta "Eh wallahi ka san ai manhajar akwai ababe kala-kala na amfanin rayuwa na banzan ne kawai aka fi sani."
"Tabbas haka ne akwai tatattun mahaukata masu koya ma masu taɓin hankali irinki girki tunda kun raina na iyaye da kakanni da kuka gada."
"No no no HABIBI wallahi ba haka ba ne kasan fa mu ƴan zamani ne kuma dole mu yi amfani da hikimomin mu na masu jini a jika domin burge mazajenmu ta kowani fanni musamman fannin girki."
Harara ya banka mata cikin ƙofula ya ce"ɗauki abincin nan ki cinye, kuma This should be the last warning da zan miki magana a kan shiga TIKTOK da FACEBOOK in kunne ya ji gangan jiki ya tsira."
Ɓata rai na yi ina muy-muy da baki ba a zuciyata kuma na ce"Bai isa ba."
Ko duba yanayina bai yi ba ya cigaba da faɗan shi kamar zai aro baki"To banda hauka da shiririta ina naki ni Ko a jerin girke-girken zamani da na ke haɗuwa da su a kafafen sada zumunta ban taɓa jin wani mai suna Iranian friend rice ba sai a gurinki,kuma ko da banga bidiyon ba na tabbatar da cewa daga kan green beans da duk wani abu mai tauri na tabbatar da sai sun tafasa shi sau ɗaya kafin a haɗa shi a cikin girkin amma saboda ke hauka na damunki haka kika cunkusa mana shi"jin ya yi shiru yasa na ɗago na kalle shi ganin ba alamun rahama a fuskar shi yasa na ajiye cokali gefe guda na tattara kayan lambun da suka sa shinkafar take gagara wucewa a maƙoshi na fara afawa ina yamutsa fuska,hannu baka hannu ƙwarya haka na cika cikina da fried rice ɗin mara daɗi,bayan na cire mata ingredients ɗin da yasa ta zama Irian fried rice,
Ruwa na kwankwaɗa sosai na yi gyatsa ganin yanda HABIBI ya zage yana gyara duk abinda zai iya gyaruwa a cikin girke-girkena yasa na sa hannu na fara tallafa masa,mun yi nasarar soye kajin nan bayan mun sulalata da su citta,kanumfari da albasa da sinadarin ɗanɗano sannan muka komo kan source ɗin naman rago wanda maggi ya masa yawa muka ƙara masa kayan miya dan haka ya dawo daidai muka sashi a fridge,sai kunun gyaɗar da na yi wanda tsami ya mi shi yawa nan da nan na ƙara dama wani muka gauraya shi da wancan mai tsamin ya dawo daidai dan haka ya zama mun cika wani ƙaton kula da shi babba,nan da nan HABIBI ya mance da laifin da na masa ya riƙoni bayan mun kammala aikin muka shige cikin ɗakin mu,
Ƙarfe huɗun asuba ya fita ya nufi masallaci mafi kusa da mu in da ya tarar da masu abinci duk sun fito dan haka ya damƙa amanar rabon abincin ga wani mai sai da rake akan a raba ma mabuƙata, ruwan addu'o'i ya sha a gurin ƴan ciranin da ke barin matansu a garuruwan su suna zuwa neman kuɗi garinmu,sun sha kunun gyaɗan nan kamar me tare da irish ball wanda na ƙara dafa wani na marmashe shi da wancan sai ƙwai dana ƙara soya shi da shi,Fried rice ɗin ma ruwa na ƙara mi shi ya dahu dan haka na zuba shi a ƙaton kula aka ba su suka hau rabo bayan sun yi layi daga ƙarshe har dambe aka kaure da shi dan wasu suna karɓar sau biyu.
Kajinmu kuwa da farfesun kifi duka mun adanasu a firiji bayan mun yi sahur muka koma ramakon baccin da ba mu samu mun yi ba,
Sai guraren ɗayan rana muka farka in da muka tashi da wata sabuwar fitina daga HABIBI,neman ya sadu da Ni yake ta ƙarfi da yaji saboda yanda muka kwanta manne da juna dan haka daga farkawar sa Hajiyarsa ta fara haniniya tana wani zabura ita ala dole tana neman abincinta,a gigice na fara hankaɗe shi ina tuttura shi sanin muna cikin wata mai alfarma kuma duk jahilci na dai na san ba'a tarawa da miji in ana azumi,
Amma ina ɗan talikin nan ya fututtuke ido yana son jawo min hadisan ƙarya dana gaskiya dan haka na zabura na miƙe tare da shigewa cikin bayi na danna mi shi makulli a guje ya biyo NI yana bubbuga ƙofar ya na ce wa"in buɗe ko ya ɓalla ƙofar" ko mai ya tuna kuma sai na ji ya bar bakin ƙofar yana kwafa can kuma ya rufo ƙofar ɗakin a hassale nan na fara sauke ajiyar zuwa a jajjere kamar wacce ta sha gudun tsere, wanka na yi sannan na ɗauro alwalla na fito tare da rufe ƙofata gam.
A can ɗakin Habibin Diyah kuwa istigfari ya fara tare da roƙon Allah yafiya akan abinda ya yi shirin aikatawa wanda cikin mafarki ya ga suna wasa da Amaryarsa DIYAH,farkawar sa yaji ta a jikinsa yasa ya ji sha'awar ta ƙara rufe shi sam ya manta da suna azumi kasancewar kuma tana gudun shi tunda ya amshi budurcinta yasa yake ganin kamar har yanzu tsoron ne shiyasa ya dage.
Nan take yaji wani nadama da takaicin auren gaf da Ramadan ya kama shi dan kan shi har ga Allah yana cikin wani hali yanzu,kuma da ace yana da hanyar da zai ɗaga sautin shi har iyayen yara su ji tabbas da ya ɗaga tare da gargaɗin su akan yi ma zalamammun matasan yanzu aure gab da azumi dan da yawansu suna karya azumin su dan biye ma sharrin zuciya,
Ya san dayawan iyaye suna aurar da ƴaƴansu ne gab da Ramadan dan su samu ladan wannan wata amma sun mance da wata ibada wanda amaren da angwayen suka mai dashi abin da yafi komai marmari a tsakaninsu tabbas ana tafka kuskure Allah dai ya kula mana da imaninmu kawai,da wannan tunanin ya shiga banɗaki ya kwara ma kan shi ruwa nan da nan sanyin ruwan ya ratsa har ƙwaƙwalwar shi,ji ya yi jikin shi ya ƙara sanyi,
A daddafe ya yi wanka ya ɗauro alwalla kafin ya fito yasa jallabiyya ya tada kabbarar salla dan a yanayin da yake ciki sam ba zai iya fita ba,karatun Alkur'ani ya yi bayan idar da Sallan nan take nutsuwa ya mamaye ruhin shi,nan ya ji sanyi ya cika ƙirjin shi,a ɗikance ya fara yi ma ubangijin Annabi Muhammadu kirari da mafi daɗaɗan kalmomi har bacci ya yi awon gaba da shi mai cike da nutsuwa.
DIYAN HABIBI kuwa Data ta buɗe ta haye online,da ƙawarta Hakeema suka gaisa sama-sama dan ta tsaneta saboda ta cika yi musu karan tsaye akan shirye-shiryen su da suke gabatarwa a First Ramadan with HABIBI group,a kan komai ita bagidajiya ce kuma ana fara hiran miji zata fara sako musu Allah da Annabi dan haka suka maida ta saniyar ware tunda sam bata biye ma shirmensu,ita ɗin sam bata waye ba balle ta kile,
Sai dai tana hawa Facebook ta ci karo da abin da ya kusa sata ciwon zuciya saboda ganin matsalarta da ta tura ma admin na SIRRIN YA MACE group ya zama topic of discussion a social media,har maza sanya shi suke yi ana tattauna irin shirmen da ta tafka a newsfeed, babban abin da ya karyar mata da zuciya shi ne,
Yanda ta bada labarin da ta bada sam bata sakaya ba in Habibinta ya gani tabbas zai gane labarin na su ne,nan da nan na ji hancin cikina ya murɗa dan haka na yi banɗaki a guje,
A wahale na fito dan duk abin da ke cikin cikinna sai da ya fita,jin numfashina na fita da ƙyar tsabar tsoron da n ke ji hakan yasa na miƙe tare da ɗaukan wayana na koma Whatsapp in da na shiga group ɗinmu na amana,amma bisa mamakina sai na ga anan ɗin ma zancen da ake tattaunawa kenan dan haka na fice tare da shiga wani gurup,sai dai duk kanwar ja ce duk in da na shiga labarina ake, masu screen shot sun yi sun turo ƴan copy and paste ma sun tura dan haka na fara zarya kamar zararra na rasa wani mataki yakamata in ɗauka.
Hakeema ce ta faɗo mata a rai dan haka na tura mata emoji mai alamun Sannu,baiwar Allah wacce ke zaune a kan dadduma tana karatun Alkur'ani a wayarta ta ji saƙo ya shigo mata ta yi saurin kashe datan sai dai ga mamakinta bayan ta kammala karatun ta tashi da niyyar yin aiki sai ta ga numban ƙawarta Farrah ya shigo cikin wayarta,
A gadarance ta ce"Ki hau Whatsapp ina son mu yi magana ƴar wulaƙanci kawai."
To fah kun ji isasshshiyar taku ko?
Ummu-jidda.
FIRST RAMADAN WITH HABIBI.
💔Heart touching story.💔
https://chat.whatsapp.com/LM4sMyc4lT5Jgnv9lw1vOS
FARIDAT HUSAIN MSHELIA (UMMU-JIDDA).
TSARABAN RAMADAN.
*LADUBBAN HAWA KAFAR SADARWA A RAMADAN.*
*Mu zamto masu yin post na faɗakarwa musamman akan abin da ya shafi Ramadan, ya zamana abin da yake shigo da mu Facebook ko Whatsapp kenan, in ma muyi posting ko kuma mu karanta rubututtukan malaman mu domin samun ƙarfin guiwa akan Ibadun mu.*
LAMBA TA HUƊU.
A gadarance ta ce"Ki hau Whatsapp ina son mu yi magana ƴar wulaƙanci kawai."
"To fah! mai kuma na yi miki DIYAN HABIBI?"
"Kina ganin magana na a online kika ba banza ajiyata daga ƙarshe ma kika sauka tsabar banda muhimmanci."
"Bana Online Datar ce a kunne."ta furta hakan a taƙaice,
Kwafa ta yi kamar tana Kallonta ta ce"Ina cikin matsala ne gaggaruma Billah,and i am totally confused That is the reason da yasa na ke nemanki"
"Turƙashi!Mai kuma ya faru?"ta furta hakan a kiɗime.
"Zan faɗa miki dan ina neman mafita ne kawai kuma kar ki min dariya dan Allah."
Murmushi ne ya suɓuce mata jin abinda ta ce amma tuno da tana cikin matsala ya sa ta ce"kai tsaye ki faɗi matsalarki ba zan miki dariya ba matsalarki ai tawa ce."
"Promise."
"Yeah i mean it, straight forward Please zan fara aikin girki."
I Don't now from where to start na furta hakan cikin zuciyata amma sai na kwantar da kai na fara shiryi mata yanda lamarin ya faru tun daga farko har ƙarshen shi,
Shiru ta yi na wasu sakanni saboda yanda ta ji wani shock ya kamata har sai da DIYAN HABIBI ta ce"Kina tare da Ni?"
"Sosai ina jinki,kawai na yi suman zaune ne wallahi Farrah,Haba ina hankalinki da tunanin suka tafi da har zaki kwashe sirrin gidan aurenki ki kai shi Facebook ko da yake rayuwar da mata suka ɗauka kenan na yayata sirrinsu a social media abu ne dake ce min tuwo a ƙwarya,ba ga ƴanmata ba wanda su nake musu uzuri da ƙuruciya ce,sai dai matan aure nasu abin ya fi munana a ganina."
Hararar fuskar wayar tawa na yi na ce"Ji wani baƙin iyeyi a gurinki dan Allah, yanzu mene ne illa dan matan aure ta je group ɗin mata zalla ta kai damuwarta dan ta samu mafita?"
"Babban matsalar ita ce dubannin gardawan da ke buɗe akawut da sunan mace suna shiga suna leƙan mana sirrikanmu har ma su yi copy and paste su yaɗa ma duniya,shin wai mun rasa mafaɗa ne ko kuwa ba mu da iyaye,kanne,yayu,ƙawaye da za mu yi shawara da sune muke yaɗa ma duniya?"
"Ɓatan basira mana yanzu da ta kwaɓe min ba ga shi ke na nema ba."
"Allah ya mana magani to amma dai ya kamata mu yi ma kanmu faɗa wallahi dan wasu dayawa sun rasa mutuncinsu a idon mazajensu sanadin wannan shirmen."
"Ke ni fa ba dan kin hango matsalar ba wallahi Ni normal ce a gurina dan dai ke ɗin akwai zurfafa tunani ne Ƙawata."
"Dan dai ba ki san yanda wannan matsalar na rashin riƙe sirrikan gidajen mu na aure ya ke taka muhimmiyar rawa wajen janyo ma mata n matsala ba ne."
"Kan aje da nisa ma ai gani nan ma Hakeema,ruwa cikin cokali ya ishi mai hankali wanka sannan na tabbatar da in wani ya taka rawa aka masa liƙi to wani ɗan karan duka zai sa dan in HABIBI ya ga labarin da nasa ake yamaɗiɗi da shi wallahi na kaɗe,dan Allah ki bani mafita ba dan halina ba ƙawata."
Voice ta min na minti biyar nan take ta sauka ganin har ƙarfe huɗu ya yi ta san mijinta ya kusa shigowa kawo mata abin da za su sarrafa dan buɗa baki, addu'a ta shiga yi akan Allah ya sa ya samu abinda suka je nema dan ba su da ko ƙwallin shinkafa balle ƙwayar gero jiya haka ta yi buɗa baki da ruwa zalla shi kuwa Angonta na can yana bibiyar gidajen abokai kwaɗayi,ya gagara tsayuwa da ƙafarsa ya nemi sana'a domin dogaro da Kai,dan tunda garar bikinsu ya ƙare wanda rabi ya kwashe ya sayar suka yi cefane shikenan ta fara zama da yunwa har gara ma da take azumin ta san azumi take.
DIYAN HABIBI.
Bayan na gama sauraran voice ɗin Hakeema nan da nan na ji hankalina ya kwanta dan haka na fice zuwa kicin ɗina wanda himilin wanke-wanken jiya ke jirana kamar mai ƴaƴa goma,ji na yi sam ba zan iya tsayuwar ba tsabar yawansu dan haka na ɗau kujera ƴar tsugunno na fito da kayan harabar kicin na fara wankewa,na shafe awa ɗaya da rabi ina wanke-wanken ƙarshe dana ga yaƙi ƙarawa na ji kamar in rusa kuka(Shawara kyauta ga mata a cikin wannan aikin Ramadan ɗin,sam bai kamata kina aiki ko mai kika ɓata ki bar shi ba,kamata ya yi kina ƙoƙari kina wankewa hakan zai sa gobe ki tashi da wanke-wanken kaɗan.)
Ƙarin minti talatin na ƙara wanda ya zama awa biyu cut kenan sannan na kammala,na shige Falo na gyara,uwarɗakana sannan na shiga ɗakin HABIBI na tadda shi tsaye yana shirin fita,dakatawa na yi ganin ba alamun rahama har yanzu akan fuskar shi na ce"Mai zamu girka yau."
Zuro jikin shi ya yi ya idasa fitowa daga ɗakin kafin ya ce"White rice da Coslow tunda muna da source na naman ragon nan,sai kunun tsamiya da ƙosai."
Gwalalo ido na yi na ce"Duba agogo fa HABIBI."
"Shida ne dai-dai Farrah,dafa farar shinkafa da dama kunun ne abu mai wahala kome?"
"Na surfa wake da hannuna tun kafin Ramadan na sa shi a rana ya bushe na sheƙe tare da ɗura shi a bokiti jiƙawan ne ki markaɗa ki soya min ne zai gagareki ko me?"
Shiru na yi ina zare ido danni har ga Allah na gaji haba FIRST RAMADAN WITH HABIBI ko first Ramadan with cin uban aiki da wahala,
Jiki a sanyaye haka na juya na nufi madafar har na kusa isa cikin ɗaga murya na ji yace" Kuma ki haɗa min juice na ƴaƴan itatuwa kar ki kuskura ki sa min kayan zaƙi a ciki."
"Ka kasheni kawai ka huta HABIBI."na furta hakan ina shigewa cikin madafar a guje,
Tausayinta ya ji ya kama shi amma sai ya danne tare da biyota madafar cikin son tura mata haushi ya ce"Bar ganin yau ban niƙo miki garin dawa dana masara ba tare da daddawa da kuka da kuɓewa ki min iskanci,wallahi in aka samu akasi akan aikin dana baki zan tsaurara matakai wannan ma ba haƙura na yi ba."Ficewa ya yi yana cewa"Jiya da kika so yin haukarki ai bakiji zan kashe ki ba sai yau dana baki umurni.
Uffan ban ce mishi ba dan matuƙar na buɗe baki ba alhairi ne zai fito daga bakina ba dan haka na sa ruwan shinkafa akan electric tare da kunna gas tare da jiƙa waken,
Tamkar ƙiftawar gira da bismillah na dafa shinkafar ,na ɗumama source ɗin haɗe da haɗa Coslow,na jere su akan dinning tare da kunun tsamiyan da cups,ina suyan ƙosan gefe guda ina haɗa mi shi fruit salad, kammala aikina ya yi daidai da kiran sallan magrib nan take na faɗa ɗaki na sillo wanka na shirya cikin doguwar Armenian gown, feshe jikina na yi da turare kafin na zura Hijab na kabbara sallah,
Lokacin na ji shigowar HABIBI tare da abokan shi ƴan amana su biyu,mijin Hakeema Lukman da Sayyid Ali nan take na ji farinciki ya mamaye ruhina dan haka na ƙara so cike da ƙarfin gwiywa muka gaisa kafin na zuzzuba musu abinci da abin sha,
Lumshe ido HABIBI ya yi cikin jindaɗi ya bini da wani sansanyar murmushi mai nuna alamun albarka yake sa min a cikin zuciyar shi,
Sosai suka duƙufa suna cin abincinsu a nutse sai ƙarar cokula da filet tare da cups kake ji sai da suka ci suka yi nak sannan aka fara yi min santi"To ko ke fa Amarsu,ai abincin gargajiya dabanne a gurin mu."
"Musamman ma mu ƴan gargajiya mun fi son namu,mu ba irin su Kwamared ba ne turawan Ingila"Cewar Sayyid Ali suka fashe da dariya dukkanin su.
"Ni kaina bar ni a mutunta turanci amma nafi girmama cimar mu fiye da tasu gaskiya haba mai ake da abincin da ba kayan ƙamshi sai kala Kore shar."
Miƙewa na yi na fara tattare wajen sai dai tun kafin in kai ficewa falon na tsinkayo muryan Lukman mijin Hakeema yana ce wa"A min take away na shinkafa da source da Coslow ɗin nan dan gaskiya raina ya biya."
Murmushi na yi kawai tare da shigewa ina ƙunƙuni a zuciyata haka na haɗo mi shi su a cikin wani madaidaicin basket albarkacin ƙawata Hakeema ya ci Allah,sai dai me ina shiga cikin Falon na tsinkayo muryan Sayyid Ali yana ce wa"Kalli wani shirme dake yawo a Facebook yau."
Dararam! haka na ji zuciyata ya buga.......
To fa ko ya zata ƙarke a tsakanin HABIBI da DIYANSA?
*Bakwa comments Readers kar in maida littafina na kuɗi ku ga rashin kirkina,Fatan kun sha ruwa lafiya, Allah ya karɓi ibadumu ya yafe mana zunabanmu yasa muna daga cikin ƴantattun bayi."
Ummu-jidda.
FIRST RAMADAN WITH HABIBI.
💔Heart touching story.💔
https://chat.whatsapp.com/LM4sMyc4lT5Jgnv9lw1vOS
FARIDAT HUSAIN MSHELIA (UMMU-JIDDA).
TSARABAN RAMADAN.
*Nana Aisha (R.A) tana cewa*
كان اجود الناس وكان اجود ما يكون في رمضان فلرسول الله صلى الله عليه وسلم اجود باالخير من الريح المرسلة
Manzon Allah (SAW) yafi kowa karamci,