Showing 30001 words to 33000 words out of 33833 words

Chapter 11 - FIRST RAMADAN WITH HABIBI

Start ads

Unknown   

13 Aug 2025

233

Middle Ads

da tunanin meya hana Uztaz shigowa wajena,rage kayan jikina na yi na faɗa banɗaki na shirya a gaggauce kiciɓus muka yi da shi yana shirin shigowa gurina ya yi saurin cafkoni ya min ɗaukar jarirai bai direni a ko'ina ba sai a kan gadon shi nan muka fara mulmula ganin ina shirin faduwa yasa ya yi saurin kamoni ya rungume.
Godiya ga Allah ya fara yi min sannan ya bidi da in faɗa mi shi komai nake so ya min a wannan duniyar matuƙar bai fi ƙarfin shi ba zai min.

Shiru na yi ina nazari cikin sanyin murya na ce"Fashion House nake son ka buɗe min,a zuba min industrial machine tare da ɗaukan kwararrun teloli wanda sun iya ɗinkin amma ba su da halin buɗe shago,za mu dinga sayar da yadi,in ka saya mu ɗinka maka sannan zamu dinga saida ready made da kayan ɗinki."

An gama Hakimar Zuciyata Your wish Is my command Biliyan uku ya isa?"

Biliyan?ya ɗaga min kai ganin ina mamaki yasa ya ɓata fuska cikin sanyi na ce"Idan Allah ya sama wannan sana'ar albarka gidan marayu zan buɗe wanda da ribar da muke samu zamu dinga ɗaukar ɗawainiyarsu tare da inganta rayuwarsu.

Sakin baki ya yi yana kallona cikin murya mai sanyi ya ce"Fara mai farar Aniya,zuciyarki fari burinki aikata alhairi,kin goya ƙannenki yayinda kike hana idaniyarki bacci domin ganin rayuwarsu ta inganta yayinda mata ke burin mallakar gidaje da motoci na alfarma tare da suturu ke kuma burinki ki share hawayen marasa gata,tabbas rayuwarki abin koyi ce ga duk wanda ke da dama irin taki Allah ya albarkaci rayuwarki."

"Amin ya rabbi,mallakar abin duniya bashi ne abu mai muhimmanci ba saboda duk abinda ka tara anan duniyar zaka barta,babban guzuri a ranar lahira shine sadakatul jariya ."

DIYAN HABIBI.






Ummu-jidda


FIRST RAMADAN WITH  HABIBI.

  💔Heart touching story.💔


FARIDAT HUSAIN MSHELIA (UMMU-JIDDA).


*ZAFAFA WRITERS ASSOCIATION*


https://chat.whatsapp.com/H16N47YvbD60SKUCaNRF6Z





ƘARSHEN LAMBA.
DIYAN HABIBI.
Yanzu gabaki ɗaya haske ya baibaye rayuwata tunda na fara neman ilimin addinin musulunci hakan  yasa ko zama a  online ya daina damuna,yanzu haka ina zaune ne ina kallon wata tasha in da ake bayani akan wafatin Nana A'isha matar Manzon Allah wanda lamarin ya faru ne a cikin wannan wata da muke ciki na Ramadan wayata ta yi tsuwwa,ɗaukarta na yi sai dai ta katse dan haka nabi numban da kira amma bata shiga sai dai guntun saƙon da ya biyo baya daga Hakeema kamar haka"Na ajiye maki saƙo a Whatsapp and Habibinki zai baki wadataccen kuɗi da zaki iya wadata marayu dubu da kayan sallah sai dai ki sa lura gurin rabon kin san wasu da haɗama,yanzu haka muna Airport za mu Umura da Uztazuna ki yafe min in na taɓa miki laifi."Kabbara mai ƙarfi na yi tare da durƙushewa na yi  sujiudar godiya ga Allah mahalicci sannan na miƙe na zauna, farinciki biyu zuwa 3 ne ya zo min lokaci guda na farko samun ni'imar da Hakeema ƙawata ta yi duk da ba wani ɗasawa muke yi ba dan ta cika iyeyi komai ta ce Allah sai kace Allah nata ne ita kaɗai, lokacin haka nake cewa saboda rashin fahimtana da addini,na biyu shawarar Habibina Uztazu ya bi har ya kai wannan matakin na samun Hakeema a matsayin matar shi duk da Habibi bai taɓa faɗa min plan ɗin Uztaz ba sai da abu ya bayyana sannan yake sanar da ni,na uku cikar burina na zamtowa bango majinginar marasa gata,baya mai goya marayu ya tabbata dan haka tuni na buɗe data na hau domin duba sakon Hakima,godiya ce ga Allah tare da ƙarfa min gwiywa akan aikin Allah dana assasata, sai biyo yi min babban albishir da ta yi akan Uztazu ya naɗa Mijina matsayin Manaja na babban kamfanin su dake Jahar Kano ta dabo babban birni yaro koda mai ka zo an Fika sannan an ba shi kwangilar gina Fashion House da samar da duk abinda ake bukata tare da gina gidan marayu,Ni kuma ta naɗani matsayin mataimakiyarta wanda tun daga Rana Mai kamar ta yau in fara tattara marayun da na  tabbatar sun rasa iyayensu dan a shirye take ta tallafa musu da dukkanin wani ƙarfi wanda Allah ya bata, dan wata 3 kacal aka ba Habibi ya kammala gina wannan shararren Fashion House ɗin tare da gidan marayu,albishir ɗin salaryn mai tsoka ta yi  min nan take na ƙara jinjina lamarin Allah tabbas kowani mutum da baiwar da Allah ya mi shi ga shi dai Hakeema dana raina yau ita ce ta ɗaga likafata gaba tunda ta samar ma mijina babban aikin da zai riƙeni ya riƙe Ahalin shi gabaɗaya,ita da bata yi zurfin ilimi ba na boko ita ce mai ba mai degree aiki(Ni kenan.)Tabbas na jinjina lamarin Allah zuciyata ta ƙara sakankancewa da Allah buwayi ne gagara misali.
Koda Ammina ta ji madarar albishir ɗin dana yi mata take yanke ta fashe da kuka jin dare ɗaya Allah ya yi Bature ma'ana Habibi ya tashi daga talakan da take ƙi ya dawo babban mutum dan kwangilar da aka bashi kaɗai ya isa ya tabbatar da yanzu ya shiga cikin manyan mutane tunda ya zama na hannun daman Social Uztaz ɗan Alhaji Bisallah bata ƙara shiga cikin farin ciki ba sai da taji irin aikin alhairin dana assasa da karɓuwan da ya samu nan take ta ce"Ita ma zata bada Tata gudummawar ta hanyar duba lafiyar marayun kyauta sai dai a siyo magunguna ."tunda likita ce ita,nan fa wani daɗin ya ƙara rufeni na ƙira Hajiya Amina itama na sanar mata da Abbiynmu,nan take Hajiya Amina ta lissafo min matan da mazajensu suka mutu wanda ta sani aka bar mata da yara sun kusa ishirin jin ita ɗin mai jama'a ne yasa na ce dole mu haɗa hannu da ita da  yin wannan aiki na alhairi,koda Habibi ya shigo sosai muka taya juna murna,nan take muka zauna muka tsara jadawalin yanda abubuwan zasu kasance,harkar yadi abokin shi Sayyadi Ali ya ba wannan kwangilar sai nemo teloli masu amana wanda cikin sati guda kacal zasu ɗinka ma yaran kayansu takalma,hijabai, ɗan kunne duka ya sayo su dan haka washegari za mu shiga gari dan fara wannan aikin alhairin,ban yi ƙasa a gwiywa ba gurin sanar ma ƴan First Ramadan with HABIBI nan take wasu suka amsa kira dan haka washegari muka shiga cikin unguwan marasa ƙarfi muka fara zaƙulo marayun da ke a galabaice Ammie ta fara basu kulawa tare da kayan abinci masu gina jiki,

Ƙauyen dake arewa da garinmu muka shiga nan fa muka tarar dá babban tashin hankali wanda yawanci mutanen ƙauyen sun yi Ridda saboda Malamai basa bin ƙauyuka yin da'awa kiristoci kuwa suna kai musu tallafi na abinci da suturu kai har ma da kuɗi tare da tallata musu addininsu nan take suka koma faɗin"Yesu Almasihu."su fara bautar wanin Allah.

Dawowa gida muka yi jiki duk ya yi tsami koda na sanar ma HABIBI halin da ake ciki nan take ya fara buge-bugen waya,abinka da lamari na ƴaƴan canji tuni ya samu matasan yara malamai aka haɗa mu dasu washegari muka je muka musuluntar da  dayawa daga cikinsu,dake cikin ƴan group ɗin First Ramadan with HABIBI akwai matan manyan ƴan siyasa har alƙawarin samar musu da tituna da magudanan ruwa da tsaftataccen ruwan sha suka yi kuma cikin ikon Allah ya tabbatu dan da muka koma rabon kayan sallah ma marayu da gajiyayyu da mabuƙata tuni muka ga an fara aiki.

Komai muke yi muna da mai ɗaukar mu video coverage ganin zirga-zirgan ya mana yawa yasa Habibi ya bude mana temporary Office a shagon dake ƙofar gidana na karɓan record ɗin duk wani Maraya dake Unguwar mu da unguwar dake nesa da mu ma,al'umma sun tuttuɗo ciki kuwa hadda waɗanda ba marayun ba duk an taimaka daga ƙarshe har sai da muka fara neman taimako Uztaz na ji ya ƙara ƙaro mana wasu dalolin, Cikin ikon Allah haka muka gudanar da goman ƙarshe na wannan wata cike da ayyukan alhairi masu gamsarwa dan tabbas marayu sun dara kuma sun samu aikin yi ƙarƙashin wannan cibiya,masu dayes da kitso da ɗinki duka mun samu daga cikin marayun suna yi ma takwarorinsu ƴan yuyuyu kuma mun biyasu,Hajiya Hakeema da kullum nake tura mata Video ta Whatsapp tana ganin ayyukan alhairin da mijinta yake yi da sunanta kuka take fashewa da shi a mafiya yawan lokaci tare da gode ma Allah da gode min da wannan kyakykyawan tunanin da yazo min ita kuma ta ƙaddamar,Ni kuma Habibina nake rumgumewa kuma duk sujjadata da addu'o'ina rabi na nema mi shi yardan Allah ne shi da iyayena tare da addu'ar Allah ya sanya shi a aljanna da ya zama Silar shiryuwata,ta bangaren shi kuwa ittaƙafi ya shiga Ni da ganin shi sai ranar Sallah a ganina tunda Allah ya bamu duniya ai da ita zamu nemi lahirar dan haka sam ban so ya yi nisa da Ni ba,kalmar dai da ya faɗa min ita ce"Wata duniyar abin gudu ne Gara mu nemi lahirar dan ita ce abin nema tunda can ne gidanmu na asali,Dukiya da ƴaƴa duka musiba ce a garemu matuƙar zasu hanamu ambaton Allah."jin haka yasa na bi shi da fatan alhairi nima kuma na zage dantse ina ta addu'a gwargwadon wanda na iya sam bana bacci da dare dan in samu in riski wannan dare na lailatul kadri.

A SAUDIYYA.
Ni Hakeema Ni ce rumgume da kaba'a ina kuka tare da nema ma Mahaifiyata gafara,Abbana wanda tare da shi muka zo dan tunda labari ya riske shi akan basajar da Uztazuna ya yi ya nemi ya dawo masa da ni gida,sam bai Mu sa ba ya ɗauke ni ya kaini Sannan ya mi shi gamsasshen bayani dangane da lamarin da yasa ya yi haka, ya gamsu tare da bin mu da kyakykyawan addu'a tare da fatan alhairi,a ranar aka mana cuku-cukun samun passport tare da biza cikin kwana biyu muka ɗage bayan Uztazuna ya aura ma Abbana wata matan dake kula damu mijinta ya daɗe da rasuwa maƙwafciyarmu  ce kuma aminiyar mamanmu dan tunda Mamanmu ta rasu Abbana yaƙi aure shekara goma sha kenan, dan haka tare da ita aka bar ƙannena mu kuma muka shillo cikin wannan alƙarya ta ni'ima da rahama.

Sosai na zage ina addu'a ba dare ba rana dan haka wata irin nutsuwa ke shigata surfa-surfa ji nayi a jikina tabbas wannan dare ta kaddara alhairi da sharri na risketa saboda yanda na gudanar da ibadar cike da sakankancewa nan take ƴanuwana Teloli suka faɗo min a rai ganin Ni ce yau ke ɗawafi a gaban ka'aba bayan na saba duk goman ƙarshe ina nan kan keke Sallah ma ta farilla fizgar jiki nake in yi  shi da ƙyar saboda aikin da yake min yawa, sam bana raya wannan dare da wata ibada babban burina in kammala kayan mutane dana kakkarɓa da wannan kuɗin nake samun inyima marayun ƙannena ɗinki da sauran hidimomin dana wajabta ma kaina yi musu dan Mahaifinmu miskini ne duk da sam baida mutuwar zuciya amma samun shi ya yi ƙaranci Ni ce babban ƴar shi dake tallafa mi shi,

Hawaye na ji yana bin fuskata nan take na fara suburbuɗo ma Teloli addu'ar fita daga ƙangin talauci wanda duk shi ke sanya su ƙuƙewa su yi dan wannan lokacin shine lokacin samuwarsu,ta baya na ji an taɓani ina juyowa na ga Abbana ne zaune akan keken guragu Askarawa na tuƙa shi
,hawaye na ji ya zubo min saboda irin addo'in dana ji yana fita daga bakin shi mai albarka akaina da mijina,ganin hakan yasa Uztazuna ya taho gurina dan lokacin komawar mu gida ya yi dan haka muka tari taxi muka shige sai masauki tare da Ummiee da Abban Uztaz muka yi buɗa baki cikin farinciki da walwala.
Duk tarin gajiyar da muke ciki sai da Uztazuna ya ƙara tsumani da soyayyar shi mai tsayawa a rai dan ya ce"Babban burin shi mu samu ciki a garin Madina."aikuwa anan ɗin Allah ya azurtani da samun Madaniyya (Fatima)idan namiji ne kuma za mu ƙura shi da suna Shakur(Muhammad)kenan.

A haka har muka kammala ibadarmu cikin ɗimbin nasara muka dawo ƙasar mu ta gado bayan Sallah,na yi ƙiba na yi mul-mul dan sam cikin ba mai laulayi ba ne sai ma wani haske da cika daya sani,a sabon gidan mu mai kama da wata masarauta a Dubai tsabar tsaruwa muka tare in da Farrah ta fara kawo min ziyara, rumgumar juna muka yi Ni da ita hawaye kwance akan fuskar mu dukkaninmu rayuwar mu ta baya muke tunawa, Uztaz da Habibi da suka shigo hannayensu cikin na juna dariya suke mana,sai dai Hakima hawaye yaƙi barin fuskarta har sai da Uztazu ya fara yi mata nasiha cikin daddaɗan murya sannan ta shagwaɓe fuska ta ce"Naƙi yin shirun har sai ka fadamin."ta fashe da wani irin kukan tabara take jikin shi ya fara rawa a diririce ya ce"me kike son in faɗa maki?",

"Wanda ya koya maka basajar zama Uztaz." Dukkanin mu dariya muka fashe da shi dan Ni har ga Allah na ɗauka wani abin ne na daban ta ruɗa ɗan talikin nan a gaban idonmu ko kunyar Habibi bata ji ba,

Ganin tana niyyar fashe mi shi da wani kukan ya sa ya ce"Wait my lady Please kar ki  koya ma yarona rigima Ni kam,zan faɗa miki."Murmushi ta yi bayan ta bamu guri mun zazzauna haɗe da abin sha ya ce"Daman dai sunana ne Social Uztaz kamar yanda ki ka ji abokaina na ƙirana da shi saboda na tsani duk wata saɓon Allah duk da kasancewata shahararren ɗan boko dake na ƙoshi da ilimin addini yasa duk wata wayewa ta Bature na san koma bayan namu ne dan haka a komai nawa Addinin Musulunci a gaba sam ban damu da akida ba,Ni dai kowace Aƙida kake a gurina in dai kai Musulmi ne zan yi aiki da kai dan haka sunan ya samo asali ne tun daga rayuwar mu ta jami'a, dangane da basajar da na miki kuwa na Uztazanci shiga cikin su na yi na gabatar ma babban Malaminku buƙatana nan take ya yi maraba da Ni ya rungume ni hannu bibbiyu,cikin kwana uku kacal na dawo yanda zaki so Ni larabci kuwa shine course ɗin da na fara karanta a jami'a dan haka ina jin shi fiye da tunaninki."

Ma sha Allah yanzu na ji magana amma da kullum Inna tambayeka sai dai ka yita kame-kame."dariya kawai muka yi nan muka fara sabon gaisuwa bayan mun nitsa muka gabatar da ayyukan da muka gudanar da basa nan suka gani,sun yaba da ƙwazonmu da Himmarmu dan haka bizar mu na tafiya China yana fitowa na yi ma HABIBI rakiya ya je ya yi odar kekuna,kujeru da duk abinda Fashion House da gidajen marayu zai buƙata acan cikin dake maƙale a marata ya bayyana in da tashin zuciya ya hanani zaune da tsaye,murna a wajen Habibi ba'a magana bayan mun zaga gari mun gagga wajaje muka biyo jirgi muka dawo ƙasar mu ta gado.
  Alhamdulillah cikin watanni ukun aka kammala ginin har gashi yau ana bikin buɗe Fashion House da gidan marayu,taro ya yi taro in da hadda mai girma gwamna sai da ya samu halartar bikin buɗe gidan Marayu mai suna"HAMSAL ORPHANAGE AND FARRAH FOUNDATION",Sarkin garinmu shine ya zama babban baƙo,manyan attajiri da masu hannu da shuni duk sun samu halartar bude Gidan marayu da GIDAUNIYAR da Farrah ta buɗe na tallafa ma gajiyayyu,an ci an sha zuciyoyin ilahirin Ahalin mu duk sun sanyaya,masu hannu da shuni da manyan yan kasuwa sun zuba hannun jari a HAMSAL(Hakima Bisallah) FASHION HOUSE dan kara mata karfin gwiywa akan ayyukan alhairin da ta yi,mai girma gwamna ya samar da nagartattun ma'aikata ma marayu na gidan dan akwai katafaren makarantar boko tun daga matakin Nursery har zuwa Sakandire da babban makarantar addini wanda ya tara manyan malamai,sai asibiti da Ammi ta zama babban likita Hajiya Amina kuma ta zama uwar Raino mai ba yara tarbiyya saboda sanyin halinta,tabbas labarin wannan taro wanda gidajen rediyo dana jaridu har ma dana talabijin ya ja hankalin mutanen arewacin ƙasar nan musamman yanda ƴan group ɗin first Ramadan with HABIBI suka gayyato manyan jaridun online aka watsa shi a media,Hajiya Farrah da Habibinta sun zamto abin kwatance a cikin al'umma yayinda HAMSAL da mijinta suka fi ƴan siyasa farinjini.

Tammat bi hamdillahi wa husni aunihi wassalatu wassalamu ala Mustapha Abul ƙasim Muhammadur-rasullullah, Muhammadur-rasullullah wa ala Alihi wa sahbihi wajma'in.
  Ina mai godiya ga Allah da ya bani ikon kammala rubuta wannan littafi Mai albarka,

JINJINA.
*Jinjina ga ɗaukacin marubuta na hannun damana Musamman Malamaina waɗanda idan sun ga kuskurena basa sanya gurin gyara min Oga Bamai dabuwa,Malam Mubarak Saulawa,MALAM JIBRIN RANO,Sarauniyar tsokana(Hajara Oum Nass)ina godiya a gareku Allah ya ƙara muku ɗaukaka da tarin nasarori.*

*Kakata Hadiza D Auta gaisuwarki ta musamman ce saboda kin tsaya tsayin daka hadda tare min faɗa akan rubutun wannan littafin Allah ya saka miki da alhairi ya kuma bar soyáyyá a tsakanin mu tabbas kina da kishin marubuta ƴan'uwank*i.

*Jarumar jarumai.*
*Sarauniyar jarumai writers wato Maman Amatullahi tabbas kin ciri tuta kin kasance abokiya mai ƙoƙarin ƙarfafa min gwiywa a duk inda na ji rauni,ina godiya da muhimman shawarwarinki wanda tabbas ba dan ke ba da tuni na ajiye rubutun wannan littafin Allah ya raya min yarana ya kuma sa musu albarka,fagen rubutu kuwa Allah ya kara basira da ɗaukaka*

USMAN IlIYASU MAJIDAƊI.
Ka kasance ƙashin bayana mai kara min karsashi a duk lokacin da na yi niyyar kwantawa tabbas kana ɗaya daga cikin sirrin nasarata Kandenmu,Ubangiji ya azurtaka da samun mata ta gari ya jiƙan Abba da Hajiyata ya kuma yalwata maka samunka ya shirya mana kai shirin addinin musulunci alfarman wannan wata mai albarka.

Kungiyata Abar alfahari na.
Jinjina gareku gabaɗayanku,shugaba Pinky Cutie,Dotana Jidda washa,Jikalle Hilfat,sirikata Matar Sayyadi, Shalelen....,FATIMA,Laurat da saurann duk waɗanda ban ambata ba ina godiya.

MARUBUTA.
Gareku Marubuta ina godiya da karfafa gwiywarku da juriya da bibiyata duk da raunina musamman S Fulani daddyn dota,Hajara,Rukayya Ibrahim Gazawa,Qamshi and co Allah ya saka da khairan ya kuma karbi ibadanmu.

Masu share.
Musamman Hajiya Maryam da babban admin na hairan and teddys palace ina godiya ɗan'uwana,Fatima Abubakar Saje da ma wadanda ban ambata ba jazakumullah.

*First Ramadan with HABIBI group 1 and 2*
  Kun ji jarumaina,masoyana,ƙawayena masu ƙara min ƙarfin gwiywa,tabbas yawanku ya yi yawan da ba zan iya ambatar sunayenku ba dan kar ku

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login