Showing 15001 words to 18000 words out of 33833 words

Chapter 6 - FIRST RAMADAN WITH HABIBI

Start ads

Unknown   

13 Aug 2025

234

Middle Ads

data iya ta koya ne da Alkur'ani mai  translation ɗin larabcin zuwa Turanci,kamar yanda ta sha faɗa min yayinda nake zuwa hira,A wata tattaunawar da muka yi da ita bayan na mata tambayoyin da suka shafi addini ce wa ta yi"Sam Mahaifiyata ne duk ta jawo min wannan matsalar saboda ta ƙi bani damar zuwa islamiyya in zauna gaban malami ya koya min karatu saboda in na yi laifi takakkiya take yi ta je har islamiyar ta masife malamin a ce warta"Bata haifa ma mai dattin hula ɗiyar da zai yi ta jibga ba."
"Dan haka ta cireni tun ina da ƙuruciya, ta sanyani a makarantar boko mai tsada wanda inna tafi tun bakwai na  safe sai huɗun yamma nake dawowa,ina dawowa kuwa na cire kaya wanka zan yi in ci abinci in hau yin assignment tare da lesson ticana,Asabar da Lahadi kuwa ranar kitso ne da bacci sam Mahaifiyata bata taɓa koya min sallah ba,na dai tashi naga Abbiy na zuwa massallaci,Ammina kuwa sam ibadar ba damunta ya yi ba sai jifa-jifa idan ma tana yin to sai dai ko a Office,a makarantar boko na koyi sallah ganin sauran ƙawayenaa musulmai da muke zuwa Salla massallacin makaranta,ina bin su muje in tsaya ƙiƙam duk abinda naga sun yi nima in yi  har dai na gaji na faɗa ma ɗaya daga cikinmu ni fa ban iya karatun Sallan  ba,jin haka sai ta yi mamaki dan ko su  basa zuwa Islamiyyar amma malami na zuwa har gida ya musu karatu, washegari ƙawart tawa ta min kyautan Alkur'ani mai fassara,idan mun yi break ta koya min Ni kuma da dare in yi bita ta hanyar amfani da karatun turancin da aka rubuta,haka na tashi in kaga a gidanmu wani wani ya yi sallah bayan Abbiy to kuwa Kulu ce mai aikinmu ita kam ina ganinta tana yi sau biyar a rana ranan weekend,da ke Ni kuma gwanar tambaya ce sai na yi ta jero mata tambaya tana faɗa min iya abinda tasani,Abbiy kuwa matuƙar yana gida yana ƙoƙarin sanyani  na yi alwala ya ce in yi sallah ya fice massallaci sam bai san ban san ya ake ibadar ba ma,kuma yanayin aikin shi yasa sam bai san bana  zuwa islamiyya ba saboda yawanci sai dare yake shigowa gida.
  (Wannan babban ƙalubale ne gareku iyaye maza damƙa ma mace ragamar gida dan kawai ta Fika hali Babban ɓaraka yake kawowa a rayuwar iyali,yana da gayen muhimmanci uba ya yi iya ƙoƙarin shi ba ya bar ragamar ma mace ita kaɗai, dangane da koyar da yara ibada shi ma iyaye suna sakaci yawanci ba ma ƙoƙarin zaunar da yaranmu mu koyar da su yanda ake karatun Salla mun bar ma malaman islamiyya wannan ragamar shiyasa ga irin su Farrah wanda mahaifiyarta ta hanata karatun addinin aka samu mishkila,ina shawartan iyaye da su rage sa soyayyar ƴaƴa a rai wanda yake hana ba ma ƴaƴa ilimi, wannan matsalar yana faruwa ne ga ƴawancin yaran masu ƙumban susa kaɗan ne daga cikin yaran Malam Shehu ke kokawa da malamai idan an daki ƴaƴansu, Allah yasa mu fi ƙarfin zuciyarmu Amin.)

Ammina wacce ta hanani  zuwa Islamiyyar kullum ta shigo cikin gida tambayarta na farko"Kin yi Assignment?na amsa da "Eh"wanda kuma ya gagareni in lesson ticana ya zo kuma ya ɗaura min a  inda na tsaya,a haka ta taso tun ƙuruciyata."Ajiyar zuciya mai ƙarfi ya sauke bayan tuno wannan labarin sannan ya fara hasko yanda haɗuwarsu da Farrah ya kasance"Mun haɗu ne a wani taron ƙarawa juna sani a wata jami'a,Farrah ta fito gaban stage ta fara zubo speech cikin ƙwarewa da har sai da maɗaukacin mazauna gurin suka tafa mata nan take ta siye zuciyata dan haka ana tashi a gurin taron  tsareta sai dai ko saurarona bata yi ba saboda jan aji,wani daɗi ne ya tsirga zuciyata dan komai nata birgeni yake ,ganin ta nufi motarta yasa nima na yi sauri na rufa mata baya,anan na san gidansu tun bata kulani inna zo har na ƙulla alaƙa da ita mai ƙarfin gaske, kasancewar bata taɓa soyáyyá ba yasa na saye zuciyarta lokaci guda, ranar da ta gabatar dani a gurin mahaifiyarta sam ban samu karɓuwaba dan a gaban idona ta ce"In gama ɗaura burin duniya a kanki amma ki rasa wanda zaki ɗakko a matsayin miji sai mai 206(Mota)."nan take Farrah ta bijire mata tare da kafewa akan tana sona kuma har aka mana maure mahaifiyarta bata taɓa so naba."

Ban fahimci zaɓen tumun dare na yi ba sai yanzu da wannan matsalar ta shiga tsakaninmu da Farrah in da ta gwada min Jahilci ne ke mata jagora a zamantakewarmu na aure amma da yardan Allah zan yi ƙoƙarin gyarata da ƙarfin soyayyar da take min,miƙewa na yi cikin sanyin jiki na fara gabatar da nafilfilu a sujjadata na ƙarshe na koka ma ubangiji akan sauyin halin matar shi.

Jin ana kiran sallah yasa na fice zuwa ɗakinta na tasheta dan ni masallaci zan wuce sai dai na sami ƙofar a garƙame in da bacci mai nauyin gaske ya yi awon gaba da ita a daidai lokacin da muminai ke neman rahamar Allah ba ita ta farka ba sai 9 na safe,duk nacina HABIBI dole na haƙura har sai da ta tashi dan kanta sannan na samu na shigo sai a sannan take Sallan asuban in da naji gabaɗaya rayuwata  ya ɓaci amma tuno da duk wanda ya kauce akwai buƙatar a janyo shi a jiki yasa na sassauta.

"Bani wayata Habibi."ce wa ta ina nufar in da yake zaune a bakin gado,

"A haka ake gaida miji dear?"yanayin yanda ya yi maganan yasa na ji wani kunya ya kamani dan haka cikin kawar da kai na ce"Good morning Habibi,fatan ka tashi lafiya?"

"Bana lafiya?"

"Meya sameka?"na furta haka ina kallon shi.

"Damuwa dear,ina jin ciwo a cikin ƙirjina,damuwa na shirin yi min illa Diyah kuma duka ke ce silah"

"Ni kuma?" na furta hakan idanuna na bisa kan shi ganin idanun  shi na sheƙi ya yi ruwa-ruwa alamun hawaye ne kwance a cikinsu ya sa na ji na karaya,

"Eh ke."

"Mai na yi maka dan Allah."

"Hana zuciyata sukuni da nuna min Ni ba kowan kowa ba ne face faƙirin da kika nace sai kin aura, tabbas na san naci darajar so shiyasa har kika aure ni amma ban cancanci wannan kalar horon daga gareki ba."ya ɓullo mata ta hakanne dan ya san shine hanya mafi sauƙi da zai iya koya mata komai a sauƙaƙe dan tana son shi.

"Ban yi komai ba Ni dear,a sanin dana maka kai mutum ne wayayye mai iya tarairaya amma daga yi maka laifi sau ɗaya shikenan sai ka dinga wahalar da Ni?"

"Kin bani haƙuri da kika yi min laifin?"

"No...no...no saboda the way You treat me,make me crazy and i AM disappointent."

"Duka laifin ki ne tunda kin fi kowa sanin halina sannan mun kuma tsara yanda zamu gudanar da rayuwar mu a sauƙake so now tell me sorry."

"So so sorry Habibin Diya."na furta hakan ina tale baki,

Wani daɗi ne ya ziyarci zuciyar Habibi har ya kamota ya sumbaci goshinta jin tana mi shi kuka ƙasa-kasa ya ce"Mene ne?"

"Kaine ka ƙi appreciating ɗin abinda nake mama Habibi You know i love You and spend my time gurin koyan girke-girke duk saboda kaine amma ka dinga masife Ni Meyasa?

Ajizanci"ya furta hakan a taƙaice,

Amma kafi kowa sanin ina maka wani irin so mai wuyar fassara Meyasa komai na yi baka yi min uzuri har kake waya da wasu matan a waje bayan Ni har wata ke faɗa min zata aure ka ohhhhh!

"Na daina kuma wacce kike tuhumata a kanta yarinyar nan ce fa jawahir ke ma kin san ai ba ajina ba ce mai zan yi da ita wacce ko Hausa bata iya karantawa ba gani da Queen Elizabet a gidana."Ya fasa min kai,

Murmushin farinciki ne ya suɓuce min sai na ji rabi daga cikin damuwata ya kau saboda girman kishi a zuciyata kuma ga HABIBI yana gwada min matsayina a gurin shi nan da nan na yi laushi na sauke nauyina akan ƙafan shi ina bin shi da wani shu'umin murmushi,

Murmushi ya yi wanda ya ƙara fito da ainihin kyawun shi sannan ya ce"Dear inasonki."

"Me yasa kake sona Habibi?"

"Saboda kin cancanci in so ki dan kin sadaukar da rayuwar ki ma Ni  shiyasa nima na miki kyautar rai,ruhi da gangan jiki."

"Zuciyar fa?"na tambaye shi ina turo baki,

"Da man taki ce matata sai dai kin san meye?"

Na girgiza kai" I have a special gift For You amma sai kin ɗaukar min alƙawarin Inna umurce ki ba zaki ƙara yi min musu ba, promise?"

"Yeaah HABIBI."nan take ya miƙo min wani ɗan akwati na ga zoben azurfa na walwali tare da sheƙi ai nan take na miƙe na rumgume shi sai da ƙyar ya ɓanɓareni daga jikin shi saboda azumin da muke yi murnan bai gama sakina ba na ji yace

"Another suprise for You Dear,close Your eyes."

Da sauri na runtse idona  nan ya zaunar dani tare da ajiye min wasu manyan littattafai akan cinyata kafin ya ce in buɗe ido da sauri na buɗe idon na fara bin littafan nake da kallo ina jujjuya su,ganin sai rarraba ido nake yi yasa ya ce"Ki duba su ɗaya bayan ɗaya sai kiji ƙarin bayani."

Dudduba su na shiga yi duka na ga littafai ne na addini,wasu hukunce-hukuncen azumi da Sallah ne,wasu akan tsarki nan take naji wani sanyi ya mamaye ruhina dan har ga Allah inason karatu dan Ni ma'abociyar son karance-karance ce, yawanci labarai nake karantawa wannan da ya kasance na addini sai naji ina muradin karanta shi dan jin meya ƙunsa,

Dan haka a hankali na fara zubo mi shi godiya har sai da ya rufe min baki cikin raɗa ya ce min"Zan fita in je in dawo kafin na dawo ki fara duba wannan duba na tsanaki kuma duk in da baki gane ba ina dawowa ki tambaye ni."

"Toh HABIBI gaskiya You really make my day today Allah ya saka, amma wayata fa inason kiran Ammi ne."

"Wasu karatuttuka zan turo miki na saurare dana  karantawa wanda suka shafi addini musamman na wannan watan da muke ciki mai albarka,dan so nake a cikin wannan watan mu yi gamda Katar da ganin daren lailatul ƙadri.

"Lailatul ƙadri wani dare ne kuwa wannan Habibi?"

"Darene da Allah ya ambace shi a cikin Alkur'ani mai girma......"


*Maƙasudin rubuta wannan littafin da man janyo hankalin mata akan girman wannan wata mai alfarma ne masu hisabi suka fara yi min kwarwa,da yawan mata sam basu damu da yin bincike akan addini ba da wayoyin su na hannu ko neman littafin da suka shafi tsarki, Salla,azumi alhalin kuma da yawanmu muna buƙatar sani dangane da addininmu musamman manyan mata da basu da lokacin kan su sai na aikinsu,dalilin hakan na zaɓi yin rubutu dan mata mu ƙara ƙaimi mu tashi tsaye mu sa Ni Ramadan ba kawai girke-girke yake buƙata ba hadda shiri na musamman dan neman kusanci da Allah, Allah ya karɓi ibadunmu.*



Ummu-jidda.

FIRST RAMADAN WITH  HABIBI.
  💔Heart touching story.💔

FARIDAT HUSAIN MSHELIA (UMMU-JIDDA).

*ZAFAFA WRITERS ASSOCIATION*

https://chat.whatsapp.com/H16N47YvbD60SKUCaNRF6Z

TSARABAN RAMADAN.
*Alƙur'ani*
Duk yadda mutum zai samu magani mai gusar da damuwa ba zai samu kamar *Alƙur'ani* ba.



LAMBA NA SHA BIYU.
HABIBIN DIYAH.
"Lailatul ƙadri darene da Allah ya ambace shi a cikin Alkur'ani mai girma saboda girman shi,a cikin shine ake ƙaddara abubuwan da zai faru da mutum a cikin wannan shekaran wa lau na alhairi ko sharri,shiyasa ya ke da gayen muhimmanci mutum ya hana idanuwan shi barci domin roƙar ma kan shi alhairi ta yiwu ƙarfin addu'a yasa masifun da za su sami mutum a cikin shekarar ta ragu tare da maye gurbin sa da alhairi.

"Kudus Habibi, gaskiya na ji daɗin wannan taƙaitaccen bayanin amma Ni fa a labarin da Kulu take bani a wata tatsuniya ta ce"Idan mutum ya yi katari da ganin wannan daren mafarki zai yi ya gan shi cikin koren ciyawu bishiyoyi na rangaji suna ambaton Allah."

"Allah masani amma gaskiya wannan shaci faɗi ne kawai Ni dai kamar yanda Malamaina suka sanarmin dangane da dacewa da riskar wannan daren shi ne"Zaka tsinci kanka a cikin wani irin walwala mara misaltuwa sannan ni'ima zata yalwaci washegarin ranar ta yanda rana kan shi ba zai yi fitowar da zai dami mutum ba, za'a samu lullumi ta yanda ni'ima zata riski ma'abota bautar Allah."

"Very good Habibi,to yaushe ne daren lailatul ƙadrin kenan?"

Annabi ya faɗa mana ce wa"Ana riskan daren a goman  ƙarshe na watan Ramadan."

"Ba tsayayyen rana?"ta tambaye shi.

"Ba bu saboda malamai sun sassaɓa a kan shi wasu sun ce ana riskan daren a daren ishirin da ɗaya,wasu sun ce daren ishirin da uku wasu kuma sun ce daren ishirin da bakwai so abu dai mai gayen muhimmanci ana  son a waɗannan dararen sam kar mutum ya shagalta da bacci ko yin wani aiki har sai ya yi bauta cike da ikhlasi."

"Da yardar Allah nima zan dage Habibi ko zan yi gamdakatar da wannan daren, tabbas kai haske ne ga rayuwata fitila mai haskaka min duhun da rayuwata ta shiga."Murmushi ya bini dashi mayalwaci kafin na jefo mi shi tambaya,

"Shin an keɓe daren da yin wata addu'a ta musamman ne ko kuma duk wanda ka iya zaka yi?"

"Ba zance ba kin san nima ba malami ba ne sai dai zan bincika miki kamar yanda ke ma nakeso ki bincika da kanki.

"Ta ya ya Habibi?"

"A duniyar yanar gizo Diyah."

"Da yardan Allah zan dage  amma ada kai wanne kake yi idan goman ƙarshe ta riskeka?"


"Karatun Alkur'ani da yi ma Allah kirari sannan in roƙi Allah da irin sigar da annabawa suka roƙe shi da shi ina mai zubda hawaye tare da neman gafarar shi akan laifin dana aikata da wanda ma nake shirin aikata shi a gaba sannan ina kamun ƙafa da Annabi da iyalan gidansa in fara addu'ar da salatin Annabi in rufe da salatin shi wannan ma wata hikima ce na amsar addu'a."

Lumshe ido na yi wani irin daɗi na ratsani tabbas sai yanzu na san ina addini mai daɗi adah can sunan Musulma kawai nake,jin ya tsareni da ido yasa na yi saurin buɗe ido na ce"Ka yi haƙuri na san na cika tambaya."

Murmushi ya yi kafin ya ce"Yi tambayarki farinciki nakeji mara misaltuwa in har nasani ina amsa su."

"Toh,wani irin siga ne Annabawa suke roƙon Allah da shi."

"Ayoyin suna cikin Alkur'ani mai girma har ma an yi littafi na musamman domin saukaƙa ma bayin Allah su dinga karantashi a saukaƙe, sunan littafin 40 rabbana."

"Zan nema in sha Allahu Habibi dan daga yau ina son in ji na iya komai wallahi."


Murmushi mai ƙayatarwa ya yi mata dan shi kam har ga Allah yana son Diya musamman halinta na son bincike akan duk wani baƙon ilimi da ta ji shi,godiya ya yi ma Allah kafin yasa kai ya fice domin zuwa tura mata karatu na musamman wanda ya shafi tsarki, Salla,Azumi har ma da Ahlaƙ da sauran ilmummukan da ya kamata ace ta sani a matsayinta Na Musulma.

Wucewar shi ke da wuya na duƙufa akan duba littafin da ke hannuna wanda aka rubuta shi musamman akan tsarki da Sallah,ɗumi-ɗumin hawaye na ji yana bin kumatuttukana dan na kasance mace mai wasa da Sallah kuma ba ko yaushe nake damuwa da yin shi ba musamman in azumi ya wahalar da ni ranar,auren da nayi nema har nake ramakonta in ban yi shi akan lokaci ba ashe shi kan shi yin sallar an fi so a yi shi a farkon lokaci tabbas rayuwata tana cikin duhu mabayyana kuma da izinin Allah zan bi Habibi sau da ƙafa dan in kori wannan jahilcin da yake damuna.

Ina cikin wannan tunanin Hakeema ce kawai ta faɗo mun a rai ashe-ashe kallon da muke mata na wacce bata waye ba mune manyan gidadawan ba ita ba?

Ashe keɓance kanta da take yi ita ce wacce ta san kanta mu kawai duniya ce a gabanmu ba muma san lahirar mu ba?

Tabbas lokaci ya yi da zan yaƙi duhun(Jahilci)da ke bibiye da rayuwata da ikon Allah.

Nan na duƙufa da karatu har sai da naji ƙiran sallar azahar na yi wuff na miƙe dan ina kwaɗayin samun ladan da ke cikin yin Salla a farkon lokaci kamar yanda na ji wani hadisi ya yi magana akai.
(Wasu ba'adin mata suna sakaci da yin Sallah a cikin wannan wata mai alfarma wasu ta hanyar jinkirtata wasu kuma sam yinta ne basa yi sai jefa-jefa dan haka wannan shafin ke jan hankali dangane da masu irin wannan hali da su ji tsoron Allah su daina dan Salla ita ce Farkon aikin da za'a fara dubawa na ɗan adam idan ta cika to komai zai zo mi shi da sauƙi dan haka a kula,a rage yawan girke-girken da zasu shagaltar da mu ga yin ibada a wannan watan,yin girki ba laifi ba ne amma a samar da lokacin ambaton Allah ta yanda ruhi zai tsaftata, Allah ya karɓi tubanmu ba dan halinmu ba."

HAKEEMA.
Washegari ko baccin asarar da Uztazuna ya saba komawa duk bayan Sallan asuba bai koma ba,sa kai ya yi ya fita, ya barni zaune akan dadduma ina karanta Alkur'ani ban kai ga tashi ba na ji sallamar shi shi da wani mutum wanda bansani ba ,amsa sallamar na yi ina mai kai dubana kan agogon dake sagale a bango na ga ya nuna ƙarfe 7 daidai,mamaki ne kawai ya kasheni ganin Uztazuna yana shirin fita da keken zuwa ƴar barandar mu domin a haɗa min shi tare da yi mi shi service,ɗayar zuciyar kuma yana mamakin meyasa baya kwatanta kwatankwacin wannan himmar a fita nema tunda har yana da ita ban samu mai bani amsa ba dan haka zuciya ta cigaba da min saƙa,ganin tunanin ba amfanin komai zai min ba yasa na ci gaba da karatun Alkur'anina har suka kammala ya sallame shi,ban san in da ya samu kuɗin biyan mai gyaran ba Ni dai koda ya gama naga ya sallame shi da wasu kuɗaɗe bayan shafe awa biyu yana aikin cike da ƙwarewa,taimaka ma Uztazuna na yi muka shigo da keken ɗaki gudun kar ya yaga min ledar dake Malale a tsakar ɗakin,nan na shiga  lallaɓashi ya yi wanka mu yi bacci amma fir yaƙi kwanciya ce wa yake" Ba yau kika ce za su zo ba?"

"Su wa kenan?"

"Baƙinki mana."

"Eh in sha Allah amma ka san su fa masu kuɗi basa fitan sassafe suna bacci

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login