Showing 6001 words to 9000 words out of 33833 words

Chapter 3 - FIRST RAMADAN WITH HABIBI

Start ads

Unknown   

13 Aug 2025

232

Middle Ads

kuma yafi karamci a cikin Watan Ramadan, kuma lallai Manzon Allah (SAW) yafi karamci da Alkhairi sama da iska mai ratsa jiki.
*[Bukhari da Musulim].*

LAMBA NA BIYAR.
Dararam! haka na ji zuciyata ya buga ganin ya juyo da hankalinshi kacokan a kan allon wayar yasa na ƙara sauri burina dai in cimmasa sai dai ina aikin gaba ya gaba ko kafin in iso har ya karanta,

Fizge wayar da ke hannun shi na yi ina hakin uban saurin dana sha na ce"Bani in gani"

Yanayina kaɗai ya kalla ya tabbatar mi shi da zargin shi dan haka ya kauda kai daga gareni Ni kuma na miƙa ma Lukman mijin Hakeema basket na abincin na juya,

Wayar Aliyu ne fa Farrah"muryan HABIBI ta tsayar da ni juyawar da na yi ina tafiya zan tafi ɗaki da wayar,

A kiɗime na dawo cikin son basarwa hannuna na rawa na miƙa ma HABIBI wayar amsa ya yi yana bina da wani mugun kallo ganin ya karɓa yasa na juya da sauri na shige ɗaki jikina sai rawa yake yi,key na sa ma ɗakin na sulale a wajen hawaye na kwarara a idona,

Ina jin HABIBI ya dawo daga rakiyar abokan shi na ji cikina ya murɗa dan na san tunda muka yi aure ya hanani shiga TIKTOK da FACEBOOK Whatsapp ɗin ma daya yarda dan yaga sabon layi ne,

Banɗaki na faɗa na je na zazzage cikina da ya ruɗe sai dai ina fitowa na fara jin ƙara tsakanin kicin da Falo,nan na ji tsoro ya kamani dan ji nayi ana jan abu kamar a buhu haka dan haka a hanzarce na buɗe ƙofar sai dai bisa ga mamaki HABIBI na hango yana jan buhun shinkafa ɗayar hannun shi riƙe dana Semonvita ya nufi hanyar ɗakin shi,hangangan haka na yi da baki a buɗe na rasa mai ma zance mi shi tsabar mamaki,

Ko kallon gefen da nake bai yi ba ya shige da su ya ƙara fitowa da Taliya,macaroni da jarkan mai ya kai ɗaki ya dawo ya ƙara komawa cikin ɗakin,

Kaf kayan cikin freezern mu dake kicin ya kwashe tare da gurguro da freezern ya nufi hanyar ɗakin shi da shi,dan da man cikin ɗakin na shi apartment ne guda har store akwai a ciki da kicin,

Mutuwar tsaye na yi ina kallon ikon Allah haka ya shigar da shi ciki ya dawo ya fara kinkimar su robobi da tukwane yana shiga da su kai a sannan ne naji zuciya ta kawo min wuya na ji wani ƙululu ya tattaru min a wuya dan haka na ce"Kwamared Mashkur wannan tattara kayan na meye wai."

Shiru ya min yana niyyar shan gabana na yi saurin yin birki a gaban shi na ce"Kaf kayan da ka ke yunƙurin shiga da su apartment ɗinka garata ne wanda Ubana ya min na ga ba kai ka siya ba amma sai kwasarsu kake kana shigar da su cikin ɗaki sai ka ce wani ɗan ƙauy............"

Ai bai bari na kai ƙarshe ba ya falla min mari dama da hauni,nan take na ga wasu taurari masu hasken gaske sun haske min idona tare da tafiya da jina da ganina lokaci guda,

Dafe kuncina na yi ina ƙoƙarin buɗe idona na ji ya ce"Ni za ki kunyata a gaban abokai in kyaleki tare da yi miki uziri akan yarinta ke damunki sannan ki kwashi sirrina ki kai kafar sada zumunta na Facebook?"

Giyar wake kika sha ko ta burkutu da za ki maida rayuwar mu topic of discussion na wannan week ɗin?

Nayin Mashkur(yau ba HABIBI ba Kwamared)ka kasheni.

Saukar belt na fara ji a jikina amma saboda kafiya da naci irin nawa ko gezau ban yi ba sai faɗi yake yana maimaitawa"Ko ban kasheki ba tabbas zan koya miki darasin da duk wacce ta ji labari makamancin naki ba zata yi yunƙurin maimaitawa ba,dan in ma bata fara biye ma Ramadan time-table na social media kar ta soma tunanin farawa."

Duka yake shauɗo min a haukace Ni kuma ina danno mi shi ashar ganin yana shirin sauya min kamani ya sa na riƙe belt ɗin tare da rantawa ana kare,ban dire ko'ina ba sai ɗakina na danna key,

Biyoni ya yi a fusace ya ce"ashe ke a marasa kunyar ƙarama ce ai da kin barni ki ga in ban kashekin ba doluwa kawai wacce bata iya riƙe sirrin gidanta ba,zan ga kuma wanda ya isa ya sa ni in canza ƙudirina na tuwon dawa da koriyar miya a social media tunda ke har kin rasa mafaɗi."

Eh na rasan kuma ka rabu da Ni tare da dawo min da kayan garata azzalumi macuci kawai,ashe da man haka ka ke bansani ba"na furta hakan duk da raɗaɗin da jikina yake min na dukan da na sha,

Ba zan rabu da ke ba har abada,Gara kuma tawa ce dan lefen da na yi muku na al'ada shiyasa aka biyoki da kayan waɗannan ƙananan kuɗin dan haka na ci halas,ki kuma kai ƙarata duk in da kike tunanin zaki kai ko da kuwa Kotun jemage ne"yana gama faɗin haka ya shige ɗakin shi yana haki tsabar ɓacin rai ya barni da dudduba jikina ganin yanda duk ya yi ruɗu-rudu wayata na janyo tare da danna ma Ammina ƙira,bugu ɗaya ta ɗauka bakinta ɗauke da sallama sai dai jin na fashe mata da kuka yasa ta ce"My Farrah what is wrong with You."

"Mashkur Ammi zai kasheni ya.............."ai bata bari na ƙarashe zancen ba ta katse kiran nan take ta fara ƙwalama ƴar aikinta kira domin ta ɗakko mata mayafi,

Gudu-gudu sauri-sauri haka take tafiya har ta baro cikin layinmu ta shigo layin su HABIBI in da nan ta yi kiciɓis da Abbiy ya dawo daga masallaci,

"Lafiya Ammin Farrah?."ya tambayeta a kiɗime dan har ga Allah ya tsorata da ganin yanayinta,

Ina fa lafiya Mashkur na can yana shirin kashe min........."

Katseta ya yi bar barta ta ƙarasa ba ya ce"Kuma shine za ki je ku daku da sirikin naki?"ta mi shi shiru ganin yanda take cika take tumbatsa ya ce"To shige muje gida in har na isa dake."

Mugun kallo ta jefe shi da shi ta ce"Gaskiya Alhaji sai dai ka yi hakuri ba zan iya ƙyale ɗiyata a cikin irin halin dana jita ba"dan haka ta wuce shi fuuuu jikinta har wani mazari yake yi,

Sumar tsaye ya yi yana mamakin iyayen yanzu da suka maida bayyana soyayyar ƴaƴa a wannan zamani tare da yanda wasu matan suka raina mazajensu musamman idan sun ga mazajen ba su kai su ƙarfi ba dan Mahaifiyata babban likita ce dan haka ita ke jan ragamar duk wata ɗawainiya ta mu data raina wanda mahaifinmu ke ba mu duk da mutum ne mai zuciya malamin jami'a ne kuma yana iya ƙoƙarin shi wajen ganin ya hidimta mana amma bata gani.

Shiru ya yi na wasu ƴan mintoci kafin ya tsaida shawarar abinda ya ke ganin ya kamata ya yi dan haka ya zaro waya daga cikin aljihun shi.

HAKEEMA.
Hakeema wacce tun bayan gama chat ɗin su da Farrah take tsimayen ganin mijinta ya dawo shiru har aka soma ƙiraye-ƙirayen Sallan magrib,Iya wacce ke daf da ɗakinta ne ta leƙo ta ce"Ke kowa yau lafiya baki fito ba yarinya?"

"Kaina ke ciwo."ta furta hakan a taƙaice dan tun zuwanta gidan ta karanci halin duka halayyar matan gidan na son tsegumi da shiga abinda ba ruwansu,ga kuma kwaɗayin tsiya su dai burinsu ta girka ta basu kamar wasu mayunwata,

Kasancewar tunda gas ɗin ta ya ƙare Lukman bai siyo mata wani ba yasa take aiki a ƙofar ɗakinta a gawayi sai dai in akwai wuta ta yi a electric cooker,kuma matuƙar ta girka a waje to zata zuba ma kowa zuwa anjima kaɗan kuwa in sha Allahu duk wanda ya girka zai sa mata idan taƙi karɓa Lukman ya yita faɗa wai hana alhairi ne dan dole take amsa yana lashewa,

ganin ta yi zurfi cikin tunani ya sa iyan ta ce"ku ci me kenan to?"

Zai shigo da shi"ta bata amsa ranta a ɓace ganin hakan yasa ta juya cikin sigar munafukan asali ta ce"Oho ki ce yau amarcin ne ya tashi,kaji da burodi da ƙwai zai siyo muku a sokaway(Take-away)."

Shiru ta yi mata tare da raɓawa gefenta ta isa gaban fanfo ta fara alwalla tana yi zuciyarta na mata suya tare da nadamar auren Uztaz Lukman da tayi tun ba'aje ko'ina ba.

To fah Fans ga fa uwar DIYAN HABIBI ta je tare ma ƴarta faɗa ko ya zata ƙarke ku biyoni a sannu.

Share
Like
Comments
Fisabilillahi.


Ummu-jidda.

FIRST RAMADAN WITH HABIBI.
  💔Heart touching story.💔


https://chat.whatsapp.com/LM4sMyc4lT5Jgnv9lw1vOS

FARIDAT HUSAIN MSHELIA (UMMU-JIDDA).

TSARABAN RAMADAN.
*Daga cikin Sunnonin da aka shar’anta ga Azumi.*
*Shine cin abincin Sahur da kuma jinkirta shi saboda taimakawa mai Azumi don kar ya sha wuya.*

LAMBA NA SHIDA.
Zuciyarta na mata suya tare da nadamar auren Uztaz Lukman da tayi tun ba'aje ko'ina ba.

Tabbas duk wanda ya ƙi jin bari ba zai ƙi gani ba da ace ta yi amfani da nasihar da Mahaifinta ke mata na zaɓen miji na gari bata biye ma banbancin ra'ayi da aƙida ba da bata dawo tana danasani ba dan ya sha faɗa ce War"Ɗiyata Hakeema na tabbatar da ke mai ilimi ce da riƙo da addini nasani amma yanda ki ke fifita aƙida fiye da komai abin yana bani tsoro."

Murmushi na ke yi mai sanyi sannan in kalli fuskar kyakykyawan farin dattijo(Mahaifina)in ce"Abba kenan,babban burina a duniya shi ne auren miji mai tarin ilimi,mai ruƙo da sunnar ma'aiki sam bana son ɗan bidi'a a zuciyata wallahi dalilin hakan ya sa ka ga sam bana kula kowa sai uztazan da muke haɗuwa da su a islamiyya ko wajen tarukanmu na addini,shigarsu,ɗabi'unsu kaɗai na ke buƙata domin raya sunnar ma'aiki."

Murmushi irin ta su ta manya yake min sannan ya ce"Allah ta'ala ya baki nagari,Ni dai abinda nake son nutsar da ke shi ne duk wanda ya furta kalmar shahada musulmi ne a gurin Allah kuma Annabi ya faɗa mana musulmi ɗan'uwan musulmi ne dan haka nake son duk wanda kika ga ya karkace ki bi shi da addu'ar shiriya,ba wayonki ko dabarar ki ba ce ta sanya ki ka zama kamila mace mai ruƙo da addini, sannan a zaɓen mijin aure Annabi ya umurce mu da yi muku zaɓi amma saboda hani da ya yi da auren dole ya sa muka damƙa muku ragamar zaɓar mijin aure,idan kin zaɓo mai addini da tarin ilimi ki duba halayya dan da halin shi zaku zauna kin ji ɗiyar albarka."

"In sha Allah Abba."

"Allah ya muku albarka."

Sai in amsa da "Amin." sai dai a inda ya min wannan nasihar a gurin nake bari Ni dai babban burina in auri Uztaz mai gemo,ya goyo Ni a bayan mashin ɗinsa tsuntsun soyayya mu je islamiyya da taron addini aikuwa na samu Uztaz lukman in da Allah ya haɗa ni da shi a wata musabaƙa da muka yi na zama ta ɗaya a jaharmu,nan muka fara shimfiɗa nagartacciyar soyayya ya shigo gida na gabatar da shi ma Abbana,ko da aka yi bincike ba'a same shi da wani mugun hali ba kuma babban Malami ne a wata makarantar islamiyya dan haka yana karɓar salaryn dubu ishirin,zaunar da Ni Mahaifina ya yi ya gwada min muhimmancin sana'a a rayuwar aure ko da na sami Uztaz lukman da zancen sai ya ce min ai yana tsare wani shagon litattafai a kasuwa a na bashi albashi ashe duk  kanzon kurege Ni dan Daga yin auranmu na tabbatar da dubu ishirin din albashinsa kaɗai ya dogara kuma ko kafin watan ya ƙare mashin ɗin mu(tsuntsun soyayya)ya cinye rabin kuɗin,

Haka aka ɗaura aurenmu zuciyar mahaifina sam bai natsu da shi ba amma ganin na kafe ina ganin Lukman shi ne zai bani farinci tare da shimfiɗa nagartacciyar zuriya a ban ƙasa yasa ya haƙura ashe ba anan gizo ke saƙar ba zan fuskanci rayuwar yunwa tun auren bai yi nisa ba,

Da wannan tunanin na miƙe na gabatar da Sallah a daddafe saboda jirin da nake gani na kwanta samɓal a wajen ina ambaton Allah.
Sai bayan ishsha Uztaz Lukman ya shigo gidan da basket a hannunsa,sai dai yana hango yanda na zama ya fara muzurai dan shi har ga Allah ya ɗauka matan gidan da muke haya sun sammana abincin da suka sa a  bani idan na basu bai san duniya na tafiya akan karin maganar"Yi in yi maka"ba ne yanzu,

Duk a tanajin shi sahoor zai yi da abincin DIYAN HABIBI dan haka ya ɓata rai,Ni kuwa da murna na na tarbe shi sannu da zuwa ɗauke a bakina,

Ciki-ciki ya amsa min sannan ya ce"Da fatan kin sha ruwa lafiya?"

"Alhamdulillah amma ban ci komai ba bayan ruwa."

Wani irin mugun kallo..........
   (Assalamu alaikum, wannan labarin na Hakeema jan hankali ne ga ƴanmata masu zurfafawa a kan aƙida ban yi shi dan cin fuskar wani ko wata ba,hasalima abinda idona ne ya gani na rubuta saboda haka idan ya yi daidai da rayuwar ki ko na wani ku min afuwa,A kowace aƙida da muke da su a addinin musulunci akwai nagari akwai na banza shi ne abinda nake son yin jan hankali a kai tare da nuna muhimmancin sana'a a cikin rayuwar aure Na gode.)

HABIBI.
Kuwa ya kasa zaune ya kasa tsaye sabo da ran shi in ya yi dubu ya ɓaci,sai maimaita Headline ɗin da yaga abokanan shi wanda suka yi fushi akan gayyato su buɗa baki da ya yi yake yi"MUN GA GIRKI GANIN IDON MU GURIN AMARYAR HABIBI."
  A akwatin gurin aje bayanai(Comments)kuma shaguɓe ne kala-kala ake yi ana tagging ɗin sa,ayayin da kuma posting ɗin Farrah ya karaɗe sosai media sai Yaga sun sa daga gani wannan hukuncin Kwamared ne ga Amaryarsa,nan take ya ji fushin shi na ƙara hauhawa tabbas ya ɗebo ruwan dafa kan sa ji ya yi zuciyarsa na zafi ga zagin da Farrah ta dinga aiko masa yana masa amsa kuwwa a cikin kunnen shi,jin kan shi na niyyar tarwatsewa yasa ya fara ambaton Allah sai dai tun kafin nutsuwa ya game da jikin shi yaji muryan sirikar shi tana ƙwala mi shi kira tamkar maƙoshinta zai fita MASHAKURU!

Ya yi saurin dafe kunnuwan shi tare da afkawa a cikin dogon tunani wato hukuncin da ya yanke akan Farrah shi ne har ta ƙira mara mutuncin mahaifiyarta gidan shi har ta mance ɗauki ba daɗin da aka yi tsakanin shi da ita kafin auren su dan ita sam bata so auren ba ta so Farrah ta auri mai dukiya ne ba Kwamared kamar shi ba wanda da ke riƙe da kwali ba fus tunda  ingantaccen aiki ya gagara,

Wani ƙara ƙiran sunan na shi ta yi a hassale ta ce"Mashakuru ka fito dan na san kana jina,Ka fito in rama ma ɗiyata dukan da kamata mugu azzalumi kawai,ina dalili ina mafari daga baka yarinya ka mata wannan mummunan aikin,wannan ai rashin sanin haƙƙin mace ne dan haka ka fito ka bata takardan sakinta ko kuma mu dangana lamarin da police station, kai wallahi idan ya gagara ma har Human right sai na kaika dan Ni na san mutuncin ƴata."

"Yo banda sanin darajar mace ta ya ya gandamemen kamar ka zaka zage ƙwanji ka zane min ɗiya kamar wata dabba........"bai kai ga jin ƙarashen zancen ta ba ya fara Kokawada zuciyar shi akan ya fito ko kar ya fito sai dai ɗayan ɓarin zuciyar tafi ƙarfi a kansa na ya fita ayi duk wacce ma za'ayi dan haka ya nufi bakin ƙofar ɗakin wanda Farrah ke bubbugata kamar zata karyata,

Wayar shi ce ta yi ƙara dan haka ya juya ya ɗakko shi ganin mai ƙiran yasa ya ɗaga da gaggawa a hanzarce ya ce"Abbiy ka zo ka fitar Ammin Farrah daga gidana dan Allah."

Da "To"ya amsa nan take ya ci burki ya yi baya ya dumfari gidan sirikin na shi da matuƙar sauri,

Ihun Farrah da masifar Amminta kaɗai yake jiyowa tun daga ƙofar get ɗin gidan,dan haka jikin shi na rawa har baya ganin gaban shi ya afka cikin falon kamar zai kifu, tamkar mahaukaci haka ya isa gurin Ammin Farrah ya janyo ta tare da sauke mata yatsu biyar akan ƙonanniyar fuskarta da man bilicin duk ya gama siɗewa,A firgice Farrah ta dakata daga bugun ƙofar da take yi falon ya yi tsit tamkar ruwa ya cinye ma'abota cikin shi,

Jin shirun yasa Mashkur (HABIBI)ya buɗe ƙofan ɗakin jikin shi duk a sanyaye dan tabbas ya ji ƙarar marin da sirikin shi ya sauke ma matar shi wacce takaici, mamaki da ta'ajjubin marinta da mijin da ta raina yasa tayi mutuwar tsaye sai dai ganin shigowar Mashkur ya sa......

Tabbas na ga ruwan comments da madaran ƙauna gareku masoya wannan littafin,ina roƙon mai kowa mai komai ya sa littafin ya amfanar da ni daku gaba-daya,ya sa Amaren FIRST RAMADAN WITH HABIBI su ɗau darasi,wacce bata yi haukar da farrah ta yi ba dan Allah kar ta jaraba irin kalan girke-girken banza da wofin nan ta yi na masu hankali, wacce kuma ta yi oga ya yaba sai ta ƙara ɗamara, dangane da illar zaɓen mace ko miji nagari kuma ga shi duk muna gani a cikin wannan littafi Mai albarka.




Mu je zuwa shin Ammin Farrah shaƙe HABIBI za ta yi?









Ummu-jidda.

FIRST RAMADAN WITH HABIBI.
  💔Heart touching story.💔


https://chat.whatsapp.com/LM4sMyc4lT5Jgnv9lw1vOS

FARIDAT HUSAIN MSHELIA (UMMU-JIDDA).

TSARABAN RAMADAN.
Manzon *Allah* (SAW) yana cewa:

(تسحروا فان في السحور بركة)

*“Lallai ku yi sahur saboda acikin yin sahur akwai albarka”.*

[Bukhari].

LAMBA NA BAKWAI.
HAKEEMA.
Wani irin mugun kallo Uztazuna ya bini da shi sai dai ganin yanda na langwaɓar da wuya ya sa yaji wani tausayina ya kama shi amma sai ya dake ya ce"Ittaƙillaha ya Uztaziyya ko dai dan kin ganni da Gara."

Ji na yi raina ya ɓaci amma sai na danne cikin muryan shagwaɓa na ce"To mai ka bar min da zan ci Fisabilillahi ya Uztaz ummm, har kana wani in ji tsoron Allah."

Dage kafaɗa ya yi cikin nuna halin ko in kula ya ce"Allah dai ya so ba gidana ne kaɗai ake rasa abincin ci ba har gidan Annabi an sha yin kwana da kwanaki ba'a ɗaura sanwa ba haka ma gidan Sahabbai na san baki manta da ayar da ta sauka akan Imam Ali Bin Abi Thalib ba da matar shi."

"Ban mance ba tabbas amma misalin da ka kawo na gidan ma'aiki ba sam ba haka abin yake ba,Annabin rahama mai neman na kan sa ne kuma  ayar Haƙuri da jarawabawa take nunawa wanda hatta a gidan ma'aiki an rasa abin ci amma ba dan bai

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login