Showing 21001 words to 24000 words out of 37959 words
bane...tunda yanzu aure gareta.
Harara aunty tazabgama Yusuf din.." Koranta kakeyi?."
"Ayya aunty na bahaka nake nufiba dai."
"Ca akai maka duka tadawo?,,kokaga ankera mata dakine? To mijinna tane yace tayi wata biyu..inkuma zaka maidata sai ingani ."
Dariya kasa2 Yusuf yayi.."Allah yabaki hakuri Hajiya auntyn mu.. Ninatafi ...saida safe .
Sallama yamusu yatafi part dinshi ,suma basu wani dadeba kowa yakama gabanshi aunty kuma tatafi part din Abba.
***
Washe gari Sunday bayan sungama breakfast Yusuf yacema zahra tasameshi a apartment dinsa. Jiki a sanyaye tayafa Vail akan duguwar rigar dake jikinta tashiga part din. Yana zaune falo yasa laptop agaba yana dannawa. Da sallama tashiga tasamu kasa gefen kafarshi tazauna. Tafi minta biyar da shigowa kafin Yusuf yadago yana kallonta.
"Tashi kizauna kan sofa." Yusuf yay commending dinta.
Bamusu tatashi tazauna kujeran dake gefen nashi.
Juyowa yayi yana fuskantarta yakira sunanta .
"FATIMA!."
Harcikin ranta taji sunan don mamarta ne kadai kekiranta da wannan suna. Kwallane yataru a idonta tunowa da mahaifiyar datayi.
"Bakijine?."
Goge kwallan idonta tayi tadago a hankali ta amsa.
"Kifada min abinda yake damunki..don insan yanda zanyi maganin matsalarki..hakanan yin aure kadai bazai sauyaki ba saidai inda wani abu."
"ZAHRA!."
Yakara kiran sunanta jin batace komaiba.
Amsawa tayi batareda tadagoba.
"Meye yazid yake maki wanda bakijin dadinsa?..kifadamin ina jinki."
Zahra tanason fada mishi gaskiya amma batasa how can be explain to him ..zan fada mishine yazid yana min kallon KARUWA? Yanda yaa Yusuf bai iya fushiba tasan everything can happen...
"Keee!. Ina tambayarki kina min shiru.. Kodan kinga nadamu dakene?" Cikin daga murya yake maganar.
Kara kasa tai da kanta tana hawaye harda shashsheka.
Sassauta murya Yusuf yayi yaci gaba dacewa..
"Haba lovely zahra na! Kinsan bansan kallonki cikin damuwa, wllh sam banjin dadin yadda nake kallonki shiru...kifada min inkinada matsa..nikuma naimaki alkawari insha Allah saina kawar maki ita...plsss kifada min gaskiya."
"Ni baabinda ke damuna..." Tafada kamar mai ciwon baki.
Lallashinta yarinka yi yana bata advice akan zaman aure har tadan saki jiki dashi.
Sai shabiyu tafito daga part din Yusuf takoma na aunty.
****
Bayan wata daya ..
A kano kam Hajiya zubaida tazama miji shikuma yazid yazama mata don sai yadda tayi dashi.
Hatta da gidan mami sai yafi sati baijeba while dakuma kullum saiyaje kafin yatafi office.
Mami duk tashiga damuwa tarasa gane kan only son dinnata saidai kawai addu'a datake binshi da i'ta.
Momy kam duniya sabuwa don tayi sabon d'a yazid yazama nasu sai yadda suka juyashi.
***
Yazid da zubaida na zaune falo kan sofa ta kwanta jikinshi ga waya hanunta tana karatun wani novel maisuna *mahimmamci budurci*. Dariya tayi kasa kasa "ohh..su budurci manya,,..mukan ai munkawo namu.." Tafada cikin ranta.
Yazid dake faman shafa mata dogon gashinta yace "baby yaushe zamuje gaida mami."
Bata rea tayi tana hararanshi. "Watoma maminka kadai kasani banda tawa uwar ko?."
"Noo..baby bahaka bane..duk zamuje har gidan momyn ma..." Karan wayarsane ya katsar dasu.. Sunan mami ne ya bayyana kan screen din.. "Kingama ..takira."
Tsaki tai k'asa2 tamayar da hankalin ta kan wayarta.
Mami ko amsa sallamarsa batayi ba bare kuma gaisuwa.."kazo yanzu ina naimanka."..daga haka takashe wayarta.
Kallon zubaida yake wanda itama kallonshi take cikin tuhuma..."wai me tace."
Dan gefen kansa ya sosa yace.."uhm..ca tayi inje yanzu tana menana."
Tsaki taja tareda cewa"to ba'inda zakaje,,ina bukatarka a kusa."
"A'a baby dan Allah kiyi hakuri kibarni inje,,,kinga mami ne."
Sauka tayi daga jikinshi tahaura sama tana cewa bazai jeba."
Shima tashi yayi yabita bedroom din yana bata hakuri. Dakyar yashawo kanta tayarda tabarshi,,amma tace kada yawuce minti talatin!.
Jiki na rawa yafita yashiga motarsa yay gidan mami.
*??BieBie Luv??*
[3/20, 2:42 PM] ??HABIEBA LUV??: *??KARUWA CE??.....47/48*
_Writing by_
*??BieBie Luv??*
_Editing by_
*??Sadnaf??*
~ ~*NOTE*~~
*MASU KARATU I'NASO KUGANE CEWA, NI _??BieBie Luv?? (HABIBA MOHAMMED)!_ NIKE RUBUTA LABARIN KARUWA CE BAI WAI _BIEBEE ISA!_ BA KO _BIEBIE DEE!_ KOKUMA _BEE BEEN MASOYA!_ BA....NI _??BieBie Luv??!_ NIKE RUBUTAWA YAKAMATA KUGANE WANNAN!.*
??????????????????
*_Y_*ana shiga yatarda mami falo sai zagaye take yi.. Kallo daya tai masa tadauke kanta tanema guri tazauna.. Shima gefen kafarta yazauna kansa kasa ya gaidata . bata amsa gaisuwarshi ba sai tambayar data jefo masa. "Ita kuma zahra n yaushe zata dawo?,,,tunda kungama cin amarcin naku ea saika dawo da i'ta." Ba yabo ba fallasa mami tai maganar. Shafa kyeyarsa yayi yace.."mami ea da canma bani nace tatafiba, ita tace tanason tafiyar...kuma tace wata biyu zatayi.." "Kana hauka ne Yazid dazaka barta hartai wata biyu?, to banyarda ...inaso acikin satinnan kaje da kanka kadauko ta kadawo da ita gidanta!." "Kobazaka iya bane ina maka makaga kayi shiru?." Mami tadaka masa tsawa , jiki a matukar sanyaye yace "to mami ." "tashi kabani gu...soko kawai..duk ka sakwarkwace akan mace."
Ikon Allah ne kadai yakai yazid gida..kansa sai juyawa yake saboda fargabar sanarwa zubaida zaije borno dauko zahra, damatukar wuya ta amince dazuwan!.
Tana kwance falo daga ita sai pant da bra gakuma eirpice kunnanta tanajin kida. Har yazauna gefenta batasani ba harsaida yarungumota jikinshi. Kara shigewa jikinshi tayi tamakalo hanunta tana shafa kwantaccen bakin gashin kansa. "Baby meye mamin tace?." Fuskarta yarike daduka hanayensa biyu yahade dahashi .. "Baby kinsan me?." Girgiza mai kai tayi batareda tace komaiba "mami tace cikin satinnan inje Maiduguri indauko zahra..." Kwace kanta tayi tana binshi dawata uwar harara "wllh ba inda zakaje ...bazakaje ba, saidai intagaji tadawo da kanta,,amma ba inda zakaje." Cikin masifa tai maganar.
"Kinga baby... Dakata tad'aga mishi hanu " ba'abinda zan saurara don baza kajeba..saidai ita mamin taje dakanta." Daga haka tatafi bedroom dinta. Sosea yaji haushin abinda tamasa, amma bayadda ya'iya yama matukar shakkarta ..tashi yayi yabi bayan ta.
***********
Yana sanye cikin kananan kaya masu kyan gaske sunyi matukar amsar sa.. Yana zaune falon aunty idonsa nakan wayarsa dake hanunsa yana dannawa. Suma fitowa sukayi cikin shirinsu sunyi matukar kyau, twice ne da zahra duk suna sanye cikin Arabian gown kowa tayi rolling dakaramin Vail din rigar. " yaa Yusuf mugama." Kallon salima datayi maganar yayi yawatsa mata harara.. "Saikubari nima nagama abinda nakeyi , don bazanyi tajiran Ku kuki fitowaba nikuma kuzo Ku azazzaleni." "We are sorry yaa Yusuf,, let's going...plss." Murmushi yayi yakalli zahra wanda tai maganar yatashi sukabi bayanshi. Shida zahra suna gaba twice kuma a baya suka tafi *KANTIAN* yin shopping don gobe Yusuf zaikuma Spain hutunsa yakare,,,kuma kowanne zuwanshi kafin yatafi sai yad'ebi kannansa sunje shopping yasai masu duk abinda suke bukata.
Sai yamma liliss suka dawo gida dakaya nik'i2 , kowa agajiye yake. Direct Yusuf yawuce part dinshi yasakarma kansa ruwa sannan yashirya yadawo falon aunty.. Suma lokacin duk sunyi wanka sunsanza kayi sunfito suna baje kayan a aunty.
Washegari..karfe hudu suka raka Yusuf airport, basu suka tafoba sai da sukaga tashin girginsu sannan suka tafi gida.
*******
Bayan sati.
Tun ranar da mami tama yazid maganar daukowa zahra bata karajin duriyarshi ba bare tasan yaje ko bai jeba. Halin da yazid yashiga na matukar damun mami, tana balain jin tausayinsa. Addua kawai tasa malamai namasa itama nakarawa danata.
Yau takama asabar, ranar daya ciki aure yazid da zubaida wata daya da sati biyu. Yayinda tafiyar zahra borno yazama wata daya da sati uku.
Yana durkushe gabanta yazuba gwiwoyinsa kasa yana rokonta.. "Don Allah baby kiyi hakuri, kitaimaka kibarni naje...wllh mami tace inbanje cikin wannan satinba tsinemin zatayi...don Allah ki amincemin." Kamar zaiyi kuka haka yake maganar.
Kokulashi batayiba idonta na kan wayarta datake dannawa. Tafi minti biyar haka kafin tadago tana kallonshi a yamutse.
"Zanbarka kaje, amma wllh aranar dakaje aranar zaka dawo kanaji?." Dasauri ya gyada mata kai eh...wllh nayarda.."bazan kwananba."
"Gud boy, to kabari sainayi tunani sai inbaka ranar dazakaje." "Baby mami fa tace cikin satinnan." "To katashi katafi yanzu man, tunda u ab ur own right.."
"Noo...baby don Allah kiyi hakuri.. Kawai natuna maki ne."
"Tashi kadawo kazauna nan." Tai commending dinsa tana nuna mishi gefenta. Jiki na rawa yatashi yazauna gefenta yana . cigaba tai da danna wayarta tana kada kafa."
Ranar jumma'a , shine ranar da zuby tacirema yazid zuwa Maiduguri.
Dawuri yagama shirinsa yama hajiyarsa sallama yashiga motarsa yatafi..dugun har yatafi a jirgi yarasa dawowa yaudin..
Acan kuwa tunda zahra tashiga satin tafiya gyara aunty tasa anai mata naciki dana waje saikace wata amarya.
Yau zahra na kwance a daki tun safe hakanan kawai kirjinta ke faduwa , addua kawai takeyi acikin ranta har tai bacci.
Kamar a mafarki taji muryan aunty na kiranta , a hankali take bude idonta har suka gama bud'ewa duka,
Aunty tagani zaune bakin gadon na zaune. Tashi tayi zaune bakinta dauke da salati tana tambayar aunty.
"Kedai, mijin kine yagaza hakuri yabiyoki, kinganshi can falo najiran fitowarki,,,,,,kuma yace kishirya yanzu zaku tafi."
Tunda aunty tafara maganar kirjinta ya tsananta bugawa. Dakewa tayi tace" nikan aunty kice mai yatafi ai wata biyun dayace nayi bai cika ba,,sai gobene zai cika." "Ke da'alla banson shirme,,,da yau dagoben ea duk daya ne kuma tunda yazo ai ko lokaci baicika ba dole kibishi....don haka kitashi ki shirya.
Tana hawaye tatashi tashiga bathroom aunty kuma tashiga hada mata kayan ta.
Cikin minti talatin tagama shiri suka sauko falo tare da aunty.
Wani wawan yankewa gabanta yayi lokacin data hangoshi zaune shima idonsa nakan ta. Wani iri taga yazama kamar ba Yazid ba,, sabanin yazid dayaga takara kyau sosea tayi kiba abunta gawani sheki da fatanta keyi. Sauri dauke idonsa daga kanta yayi tare da mikewa.
Inda yake suka karaso zahra tagaidashi cikin sanyi ya amsa . zaunar dasu aunty tayi tana musu nasiha sosea,,shide yazid duk bayan wani lokaci saiya duba agogo gudun har lokaci yakure yashi ubansa gurin zubaida.
Harbakin mota suka rakasu su twins na dagama zahra hanu har saida suka fita daga gidan...su hajiya zahra kam harda dan hawaye.
A mota bawanda yakallin dan uwansa bare magana ta hadasu,,haka suka ringa tafiya har suka shiga kano.
Ana kiraye2 n sallar magrib yazid yay parking a parking lot din gidansa, fito mata da kayanta daga Booth yayi yabar matasu gurin yay shigewarsa. Daukar akwatin tai dakyar tana ja tashiga falon.
Zubaida na zaune falon tasa wasu gantalallun kaya takure waka tana bi.
Tana ganin yazid tataso ta rungumeshi tana shigewa jikinsa ..."oyoyo baby..I miss you wollh" shima rungumeta yayi yarike west dinta yana kissing wuyanta.
Bakinta dauke da sallama tashigo falon , ido hudu sukayi da zubaida wanda idonta ke kan kofar falon. Kallonta kawai zahra takeyi ko kiftawa babu..
*??BieBie Luv??*
[3/22, 10:19 AM] 👄hαвєвαh luv👄: *💝K̥ͦḀͦR̥ͦU̥ͦWྂAྂ CྂE💝ྂ...... 49/50*
_wrítíng вч_
*👄hαвєєвαtєє👄*
_єdítíng вч_
*💅ѕαdnαf💅*
*🇳 🇴 🇹 🇪*
*ASSALAMU ALAIKUM MASOYANA, NA CANJA SUNANA DAGA 👄BIEBIE LUV👄 ZUWA _HABIEBATIE_. LURA DA YANDA SUNAN NAMU YAZO D'AYA DA WASU WRITERS: BIEBIE ISAH, BIEBIE DEE DA BEE BEEN MASOYA.. NAGA ANA TA CECE KUCE AKAI KOWACE TANA GUDUN ACE ITA TA RUBUTA NOVEL D'IN KARUWACE, INDA HAR AKA FARA WRITE UP DAN ANA YAD'AWA. TO SUNAN NOVEL BASHI YAKE NUNAWA NOVEL BANA ARZIKI BANE DARASIN DAKE K'UNSHE A CIKI SHI YAFI MAHIMMANCI KUMA ALHAMDULILLAH TUNDA NA FARA BABU WANDA YA ZAGENI SABIDA BA ABUNDA KUKE ZARGIN NA RUBUTA SHINE A CIKI BA,, KUMA BABU LAIFI MASOYANA DAKE BIYE DANI SUN SAN HAKA BABU BATSA A CIKI SAI DAI KUCE SUNAN NOVEL D'IN DAI BAI DACE BA BABU SUNAN KUMA DAYA DACE DASHI SAMA DA KARUWA CE DAN HAKA MASOYANA HANYAR LAFIYA A BITA DA SHEKARA DAGA YANZU HAR NAGAMA DA HABIEBATIE ZAN RINGA AMFANI HAKA KUMA A DUK WANI NOVEL DA ZANYI DAFATAN MASU TUNANIN BIEBIE ISA DA BEE BEEN MASOYA KE NOVEL D'IN KARUWANCI YANZU ZASU BANBANCE DAN IDAN KAI MAI BIN NOVEL D'IN MUTUM NE SOSAI YACI ACE KA GANE RUBUTUNSA HAKA MA DA TSARIN LABARINSA BA A FAKE DA HAKA BA NGD.*🙏🙏🙏🙏😎
_bansan iriyar godiyar da zan makuba mosayana masu kirana a waya damasu taramin sako..nagode sosea da kulawarku, Allah yabarmu tare..
#One ❤.
💝💝💝💝💝💝💝💝💝
Zarah tayi mamakin ganin zuby. dama itace amaryam yazid din?saurin kawar da tunaninta tayi aranta,, takama hanyar bedroom dinta .
"keee!" yazid yadakama zarah tsawa,, "baki iya girmama manya bane some?, dallah kizo ki kwashi albarka Kinga na auro yar mutunci ba karuwa irinkin ba!"
dago da idanuwanta dasuka kada lokaci Daya tayi, tai saurin tanne hawayenta .
wani shu'umin murmushi zubaida tayi tace "ayya my baby love ae ni zan gaidata kasan tarbiyya bata wadace tana, ina yini auntynerh kin,, dawo lfy? ae koba komai zaki mana yan amfani a gdan ko baby? ,kaga ae aiki yamin yawa."
yazid yace "hakane ."
"to aunty kidan bamu waje mana." Zuby tafada tana kad'a jiki.
jiki a sabule zarah ta shiga dakinta ta.
bayan ta gama aikinta tagyare dakinta ta tas ta kwanta wayarta dake side drawer (wanda yuzuf yasai mata) tafara ringing, dauka tayi sunan auntyne ya bayayyana akan screen din cikin jin dadin kirannanta a wanan lokacin takara kunanta .
sunyi waya sosea daga bisani sukayi sallamah.
shigowan yazid taji yana cewa "keee kifito ki dauramin abincin "
"Ya yazid matar taka bata iya abinci bane ko me!?, nipa dole nadawo gidannan, kasani cewa kaidin baka gabana kagane ko!?."
I'yaka mamaki yazid yayi "lalle wuyanki ya isah yanka!_ zaki tashine ko saina balballaki stupid ." ya dakamata wata uwar tsawar da ta gigitata, ae bashiri tafita.
bayan taje kitchen ne taji ya kwalla mata kira, suna falo shida zuby. "yawwa baby mezakici?." wani kallo wulakanci taiwa zarah kafin tayamutsa fuska ta tabe baki tace "inason coconut Rice with eggs source,coconut and pineapple juice sai tahada min dan wani snack haka." yazid yace "baby duka wannan kayan zata hada miki?, kinga it's almost 6:30." wani banzar kallo zubaida Taiwa yazid bai San lokacin da ya rufe bakinshiba yace wa zarah 'keeee tashi kibamu waje."
takai wajen 2hours kafin ta gama tai sitting na dinning table. Sai datayi kosan minti goma dafada musu kafin suka tashi .
"baby kace tayi serving dina to." Ok baby, keee zokiyi save namu." Zuzzuba musu tai tatafi dakinta .zuby spoon uku tayi tace "baby nikam bazan i'uacin wannan abincin ba, duk yayi danye ga k'auri dayake. Gaskiya bazan ciba kifita restaurants kasiyomin abinci ."da masiifa dakomai saida ya fita ya siyo .
Washe gari...
Yazid nadawo wa daga masjid yashiga dakin zahra, tanakan praying mat ta i'da salla tana tasbihi. "Kee!." Dagawo tayi tamishi kallo daya tamaida idonta. "Ina kwana.." Ko amsa gaisuwa baiyiba yace.. "Ba gaisuwarki nazo karb'a ba, ki tashi kishiga kitchen kihadamana break ..sannan kigyara ko i'na ...kitabbata dai kinyi duk aikin daya dace kafin mufito nida baby.. " gyada mishi kai kawai tayi batare data i'ya fad'in komai ba. Fita yayi daga dakin yana wani babbud'awa. Bayan fitarshi zahra tahad'e kanta da gwiwa wasu zafafan hawaye suna sauk'a mata.. "Wannan wace iriyar rayuwa ce? Baya ganin darajata, baya ganin kimata..shknn nazama baiwa kenan!?..." Daga hannayenta biyu sama tayi wasu hawayen nakara zuba.. "Yaa Allah.. Kafiddani daga wannan hali,,Allah kasakamin wannan zaluncin da'akemin.." Saida tayi mai isarta kana tashare hawayenta tatafi kitchen.
Misalin karfe tara takammala aduk aikin gidan ,,fitowa tai daga kitchen daniyar wucewa bedroom dinta dai2 yazid suna fito rungume da juna. Zuby tana sanye cikin wasu English wear dasukayi balain kamata ,kanta ba kwali tayi parking dogon gashinta. Kallo daya zarah taimasu tadauke kanta taci gaba da tafiyanta. Kallon kaskanci zuby Kevin zarah dashi.. "Baby waye zaiyi saving namu?." "Oh..sorry..kee!. " yafadama zahra da hartakai step din karshe. Sarai tasan da'ita yake amma taki juyowa don wannan rainin hankalin ya isheta. "Keee zahra! Badake nakeba?." Juwowa tayi tace "ai banyi tunanin dani kakeba..tunda banji kakira sunanaba.." Sakin baki da idon zuby tayi tana kallon yazid "kee! rashin kunyartata hartakai karinka fada min haka?.." Yamutsa fuska zahra tayi yajuyazata tafi, Hakan yay balain tunzura shi , taku dabaifi biyarba yayi yacafkota... "Noo! Baby dan Allah saketa, ai baiyi kahada jiki da wannan kazamar ba,,kasaketa nace. " saketa yazid yayi yadawo gurin zuby. "Koma dai baby meye abun damuwa ?,, mutumin da baida tarbiya ai agunta wannan abun datayi bakomai bane...don haka banaso kana damuwa da kananun rashin kunyanta." "Shikenan baby na ,muje." Rungumota jikinshi yayi, ahaka suke feeding junansu har suka koshi.
"*
Ahaka rayuwa tacigana da tafiya zarah tana matukar wahala itace shara wanke wanke wakin inners din zuby da kuma na yazid.
wata rana Momy sunzo da mama lokacin Zara na kitchen zuby da yazid suna kallo a falo. sunji dadi sosae ganin irin wahalar da zuby take bawa zarah,, SUNYI MATA CINFUSKA saikusan magrib sukatafi . ranar zahra kusan kwana tayi tana kuka zuciyarta namata ciwo don irin zagin wulakanci da suka taru suna mata.
***
Hisham yagama lalata farida yamayar da i'ta karamar karuwa don kamar mata da miji haka suke rayuwa, kullum saisun hadu a hotel.
Yau takama laraba, ranar farin ciki agun mama don yaune za'a kawo kudin auren 'ya'yanta. Abba baya Nigeria don haka abokin shine still dawasu abakansu biyu zukazo don karbar bakin. Saikusan karfe tara dangin nabil sukazo . manyan mutane biyune sukazo cikin shiga ta alfarma,,suna gama abinda yakawosu sukatafi. Tashin hankali! Mama da farida hankalinsu yagama tashi ganin har karfe goma dangin hisham basuzoba,, takira layikanshi kuma duk arufe . tayi kukan harta gaji mama sai hakuri take bata. Yayinda fauxy take cike da farin ciki ko ajikinta damuwan da farida ke ciki. Haka abokan abba suka gaji da jira harsuka tafi.
***
Yau misalin karfe sha daya mami tashirya zataje gidan yazid duba zahra don tunda tadawo batazo gun mami ba, ..mami kwa tadau aniyan bazata kara kiran yazid ba! Saidai inyaga dama yakira.
Karfe shadaya darabi driver n ta yay parking compound din gidan yazid. Dasallama tashiga falon, zahra da munarta tafito daga kitchen jin muryar mami tanata aiki sai zufa take had'awa.
"Mami..sannun da zuwa.".. Tafada tana karasawa gurinta. Mami ma da faraa ta amsa.." Yawwa zahra na ..sannu da aiki." Kitchen zarah tatafi tadoma mami snacks da drinks.. Gaisawa sukayi... " ni yazid din bai fitabane naga motarshi ?.". "Eh..mami hala baifita ba, don baiyi break ba." Mamakine yacika zuciyar mami, ace har kusan shabiyu mutum bai fita gurin aikiba..
Tana mika tafito daga daki tana sanye da sleeping dress sai yamutse fuska take.. "Kee! Inafatan kingama hada mana break... Turus zuby tayi tαnα mαmαkín gαnín mαmí. "αu kєcє α gdαn nαmu?,, kєє zαrαh míkσmín вrєαkfαѕt dínα чαnzu." mαmαkí neчαgama ciki mami, αnα