Showing 21001 words to 24000 words out of 49959 words

Chapter 8 - SOLDIERS FAMILY COMPLET

Start ads

08 Aug 2025

8

Middle Ads

shiga tone k'asar wurin sunyi nisa sosai kana wani wani bak'in hayak'i yafara fita kallon alyasat gimbiya halila tayi tace kasa matarka ajikinka sabida wannan hayak'in...bamusu kuwa yarun gumeta ajikinshi seda suka gama tone wurin tsab kana gimbiya halila taduba ramen taga abunda keciki kana tace suzo suhad'a hannu wurin d'auko tukunyar dakecikin Ramin sud'aukota atare... duk'awa sukayi tareda zura hannuwansu atare sukarike tukunyar suna kamata hannunsu seda duka pert d'in yad'auki girgiza kamar rufin ze kifo akansu hakan yasa sukayi yunk'urin mayarda tukunyar cikin tsawa maheer yace karku kuskura kusaketa komiyeko zakuji harse kunfitoda ita...hakanko akayi Basu saketaba dudda sunaji ajikinsu yadda akeyiwa Naman jikinsu kamar ana konasu sabida azaba Amma hakan suka d'aure suka fitoda tukunyar daga ciki...cikin sauri maheerah tafidda wani ruwa tanazubawa tindaga damtsen hannun kowannensu suna sauka har akan tukunyar seda ruwan suka Kare duka kana tace kud'agata atare seku saketa kasa Kuna ambatar sunan Allah kunji...aikuwa cikin sauri suka d'aga hannuwansu sama dudda nauyinda sugaji tukunyar tak'ara hakan suka rod'ata a,k'asa ta tarwatse..cikin sauri maheer yacillawa abubuwan dake ciki wuta hakan kuwa yayidededa wata irin zaburada ammy tayi tana fad'ar sunnan Allah abakinta tareda bud'e idonta duka tana kallon bedroom d'in...cikin sauri habibbty dake kusanta takaraso tana fad'ar ma,Isha ma,Isha alhmdllh Allah..jiyowa ammy tayi takalleta tace na,am habibbty tafad'a dakyar sabida nauyinda bakinta yamata...Aiko habibbty tarungumota dasauri tana fad'ar Allah ngd maka ma,Isha kinsamu lpy Masha Allah...itako ammy hawaye kawai kefita daga idonta dudda batasan Kona mineneba Amma Idan yafahimci zancen habibbty tana nufin itadin tajima batada lpy sunjima ahakan kamun habibbty yasaketa tana fitowa dasauri perlon inda tasamu alyasat da mama d'uke domin Bata ganin su gimbiya halila cikin sauri tak'arasa tana fad'ar alyasat alyasat ma,Isha tafarka wlh tasamu lpy tadawo hayya cinta..aikamun tarufe Baki yanufi bedroom d'in da azabar gudu



Yanashiga yaganta zaune tadafe kanta cikin sauri yakarasa gareta Yana fad'ar ammyna...d'agowa tayi takalleshi tareda sakin D'an murmushin tace yaron ammy..aidasauri yak'arasa tareda rungumata jikinshi gabaki d'aya Yana sakin kukan farin ciki kukanda yajima yanaso yayishi Amma bezoba cikin tsantsar farin ciki yake fad'ar alhmdllh alhmdllh alhmdllh bini imati rabbi Allah..shiru duk sukayi tana shafa bayanshi kamar wani jinjiri imata k'wallar ce a idonta Jin sunzubo abayansa yasa yad'ago yanashare Mata hawayen tareda girgiza Mata kanshi...maheerah ce tashigo d'akin da murmushin nasara kwance akan fuskarta take dubansu kamun tace alyasat ba lokacifa katashi kuje kuk'arasa aikin zankai ma,Isha gun abban k'awata..jiyowa yayi Yana murmushi yake kallonta Wanda tinda taganshi bataga alamarma yasan miye murmushin ba..shiko cikin farin cikin dayake ciki yace waye abban k'awarki? ""General habibullah tafad'a atak'aice kana takama hannun ammy sukabar d'akin.

Tasowa yayi yabisu Yana tinanin wacce k'awarta take cewa abbe abbanta? Yana fitowa gimbiya halila tace yad'auko matarshi hakan yak'ara d'aukar mama suka nufi pert d'in habibbty.


Acan pert d'in dady kuwa duk suna zaune jugum2 banecewa komai domin dukkansu jiran tsammani sukeyi""assalamualaikum maheerah tafad'a tareda shigowa perlon ta,ajiye ammy kusan abbe kana tace abban zaraah kamatarka...abbe kuwa dayashiga shock tinda sukashigo dashi da duk Wanda ke perlon ganin abun sukeyi kamar a mafalki yau ma,Aisha ce tashigoda kafafunta batareda anrik'ataba ga habibbty biyedasu abaya..ai besan sanda yakankame abarsaba Yana yiwa Allah godiya su Al,Hassan da sauran yaran gidan harda matan bawanda be rungume ammy ba Yana farin cikin samun lpyr ta yusif da lateep kuwa kamar sutaka rawa Dan murna sunsan damuwar D'an uwansu tak'are tinda ammy tasamu lpy abbe Kuma Allah ya bayyanashi...mazama sunyiwa D'an uwansu murna nasamun lpyr matarsa.


Acan pert d'in habibbty kuwa wani kwarido sukashiga mezurfin gaske Wanda ko alyasat besandashiba agidan wani tsohon store sukashiga kana suka bud'e wani k'aramun d'aki aciki

Shidai alyasat Yana biyedasu kawai Yana kallon ikon Allah yayinda mama ke mak'ale ajikinshi..duhun wurin yayi yawa Wanda baka ganin komai aciki hakan yasa maheer bud'e hannunshi atake wani haske yafito yagauraye wurin

Cikin mmki alyasat ke kallon wani show glass dake mak'ale awurin dawani abun acikinshi kamar sak'aho...gun show glass din maheer yaje tareda b'antale murfin kana yajiyo yanayiwa gimbiya halila magana bayan sungama maganar ne tajuya tace"""alyasat zo kuhad'a hannu kaida zaraah kamar yadda kukayi d'azun kuciye wannan babyn k'arfe (Yar tsanar k'arfe) dakejikin wannan abun...bece Mata komaiba illah ajiye mama dayayi suka nufi abun shidai yaga kamar siffar mutin Kuma kamar yasan fuskar Amma yamanta Aina yasanta sekawai suka shiga b'anb'are Yar tsanar Amma suna Dora hannunsu akayi Bala,in cilli dasu seda sukayi sama kafin sufad'o maheer yayi saurin taresu Yana kallon abun kamun yasaukesu tuni gimbiya halila tayiwa wurin tsinkeda wani haske me,azabar zafi Wanda kefita daga idanunta atake shima maheer yayi hakan sesuka had'a k'arfi wurin d'aya kamun wani abun yace tusss yafashe Amma fa kamun yafashe sunjigata sosai Yana fashewa gimbiya halila tafad'i domin tajigata ba kad'an ba...cikin sauri mama tayi kanta tana fad'ar momma miyasameki? ""Bakomai Zara kuyi sauri kucire ba lokaci maheer zetemaka maku..Aiko suka koma wurin wannan abun tareda Dora hannunsu atare suna Kiran sunan Allah yayinda maheer yakafesu wuri d'aya dudda mama dabatajin tsoron wani abun Idan sukayi sabida tasaba dasu Amma wannan sedaya firgitata balle alyasat dabesaba ba Amma hakan yadake sabida namujine jajurtacce Kuma soja...datemakon Maheer suka samu nasarar b'anb'aro abun cikin iyawayar Allah da buwayarsa suna b'antaleshi sukazube awurin..yayinda habibbty tamik'e arazane tana fad'ar...!




*SOLDIERS FAMILY* na kud'i ne nera 500 kacal =?L? ga duk me buk'atar complete kuma 700 ne Idan kinshirya siya Zaki iya tuntub'ar wannan nomber =?I? 07037092176 on WhatsApp kokuma kikira wannan nomber =?I? 08107819124







Autar alheri
'?

*S F*

Page 29&30

__"tana fad'ar appey appey Imran na shiga ukku Ina appey d'inku yake? me ya sameshi?sekawai ta fashe da kuka!

Dukkansu y'ay'an Bata mik'ewa sukayi suma suna fad'ar innalillahi-wa-inna-ilaihi-raju'un to Miyake Shirin faruwa da sune? Ina mahaifin nasu? Sun dai san Yana raye bai rasu ba amma sun wofantar da lamarinshi hasalima sunmanta dashi gabaki d'aya arayuwarsu Kuma dukkansu ba wanda ya tab'a tunanin Ina mahaifin nasu ya shiga.

Allah humma ajirni fimuseebati wa,ahaleeqni khairan minhaa..shine kawai abunda suke nanatawa abakinsu..anrasa Wandama zai tunkari habibbty balle ya rarrasheta itako sai kuka takeyi domin ita kanta ta manta da mijin bata tsawon shekaru bama zata iya cewa ga iya marabarta dashi ba wannan wacce irin masiface...cikin k'arfin hali Lateep ya,Isa gunta yace""habibbty kiyi hak'uri zamu bincika duk inda appey yake afad'in duniya indai yana raye zamu kawoshi gareki Dan Allah kidena kuka komai tsanani yana tare da sauk'i Allah yakawo mana d'auki Dan Alfarman sayidina rasulillah (s.a.w) da Ameen suka amsa dukkansu domin Babu magwarinyin wani motsin sai dai sunsan tabbas akwai lauje cikin nad'i acikin wannan Al,amarin ruwa baya tsami banza tabbas akwai wata ak'asa duba da yadda Habibullah ya b'ata lokaci d'aya akazo ma,Isha Takoma kamar gawa kamin wannan lokacin Kuma duk Babu appey kana dukkansu ita da yaranta da jikokinta sun manta dashi acikin babin rayuwarsu.. k'wallar idonta ta share tana me rokon Allah yakawo musu d'auki acikin wannan mird'ad'd'in k'ullin..


Acan part d'in habibbty kuwa maheerah ce tayi kansu da sauri shigowarta kenan taga sunzube awurin""kiransu tafarayi tana girgizasu Amma ba Wanda ya motsa daga Alyasat har mama cikin sauri ta mik'e tana Kama gimbiya Halila ta mik'e tsaye da?yar kana tadubi maheer dariko wannan abun dake cikin show glass d'in Yana k'ok'arin bud'eshi""kitemaka masa maheerah kufitar dasu daga wurinnan kucece rayuwarsu shine kawai abunda gimbiya Halila ke fad'a cikin galabaita domin itama ta raunata...Aiko dasauri tad'auki Alyasat da mama duka tab'ace dasu daga wurin kamun tadawo Maheer ya gama bud'e abunda ke rufe abun mmki wani kyakkyawan tsohone duka sumar jikinshi tayi farin ko,Ina na jikinshi se karkarwa yakeyj kamar mejin sanyi..ahakan maheer ta d'aukeshi shima kana gimbiya Halila tabar wurin bayan sun kaisu wani bedroom sun kwantar da sune sukabi bayan yayarsu sai da suka Rakata har cikin masarautarsu ta shiga turakarta kana suka dawo dan temakonsu Alyasat.

Sunjima sosai akansu kamun susamu sudawo hayyacinsu sedai sulula dogon bacci

hakanma wannan tsohon ya dena karkarwa da yakeyi sosai shima baccin wahala yayi awun gaba dasu..sai a lokacin suka sauke numfashi kana suka fito perlon inda su abbe...duka kowa juyawa yayi ana kallansu Dan basu ga lokacin da suka shigoba har suka shiga cikin bedroom fitowarsu yanzu kawai suka gani...suko duk da cewa sunsan kallon da suke masu hakan besa suka basu damar yin wata magana ba.

"Kuzo muje kuga Amma karkuyi hayaniya kawai munaso ku ganine da idonku sannan muyimaku bayani munaso mutafi domin yayarmu ma taraunata tana da buk'atar taimakon mu atare da ita...Ido Jalaludeen da abbe suka zaro dumin sunsan gimbiya halila suke nufi....sedai kamun suyi magana maheerah tece karku damu tinda munyi nasara akan abunda mukeso ai ba wani abunda zaifaru insha Allah saboda hakan kuzo kawai tak'arasa zancen tana juyawa.

Dukkansu bayanta sukabi har bedroom d'inda suka kwantardasu Alyasat da mama akan bed d'aya wannan tsohon Kuma akan doguwar kujera...duk Wanda yashiga yagani seya firgita musamman appey ganinsu hakan sedai badamar magana doli ahakan zaka fito kabawa wani wuri shima yashigo....ahakan akayi sai da kowa yagama shigowa kab kana suka koma perlon da tambayoyi fal a zukatansu.

Sai da kowa ya samu wuri ya zauna kana Maheer ya fara magana kamar haka, "da fari dai nasan dukkanku nan baku san mu ba to ba muda lokacin yi muku bayani akan mu suwaye? sai dai nasan kunsan cewa mu ba mutane bane kamarku Kuma bamad a nufin cutarwa agareku. shiru ya Wanyi Yana kallon maheerah kamun ya cigaba da fad'in akwai abunda kefaruwa acikin ahalinku sai dai ba musan daga Ina abun ke zuwa ba abunda mukasani shine koma waye kebibiyarku ya bada matuk'ar ahad'ari saboda iya abunda yafaru a yanzu ya,isa yanuna hakan..Nan ya shiga basu labarin duk abunda ya faru tun daga shigowarsu stet d'in har hanawa mama shiga part Win ammy da masu tsaron wurin sukayi har kawo yanzuda suka fito da appey.

Kowa awurin ya shiga tashin hankali in banda tasbihi ga ubangiji Babu abunda mutanen wurin keyi gabaki d'aya sunshiga tashin hankali.

Ganin hakan yasa maheerah fad'ar karku tana da hankalinku insha Allah Babu abunda zaifaru muddin muna Raye bazamu Bari ahalin zaraah su to zartaba domin yanzu kunzamo ahali agareta....wannan tsohon Idan ya farka na,ajiye ruwan addu,a daza,abashi yasha saboda shekaru dayayi amatsayin sak'aho kamar Wanda baya duniya Kuma manta daku shine akayi ta yadda bazaku tab'a tunawa da shiba balle kuyi yunk'urin nemansa.


Alyasat da zaraah dolene su zauna acikin inuwa d'aya domin da temakon auren da ketsakanin sune muka karya wannan tsafin domin muddin suna tare baza,ataba cin galaba akansuba nasan yanzu mama zasu Hara itada mujinta sabida sune suka karya alkadarinsu Amma muddin suna tare hakan bazebasu nasara akansuba sabida hakan kukiyaye kurika addu,a danneman tsari agun Allah..suna gama fad'ar hakan du suka bace batt domin zancenne kawai sukeyi hankalinsu nakan yayarsu.

Shiru perlon yad'auka kamar ruwa ya cisu ko wada abunda ke ranshi sunrasa mai zasuyi farin ciki ko akasin hakan..sunjima awurin ba tare da kowa ya tab'ukawa kansa komaiba seda akayi Kiran sallar magarib kana duk mazan suka fita masallacin sake cikin stet d'in yayinda matan sukayi sallarsu anan cikin perlon

Mazan Basu dawo gidanba har akayi Isha,I seda sukayi sallar kana suka shigo Kuma har wannan lokacin su mama basu farka ba...ahakan suke zaune anan perlon har 10:00pm kana abbe da Abba suka nufi bedroom d'inda suke ciki...sukayi sa,a kuwa tashin Alyasat kenan Wanda mitsinshi ya tada mama sannu suka musu kana sukace sutashi suyi sallah

Seda sukayi sallar suka gama zasu fita kenan appey ya farka cikin sauri suka K'arasa gunshi suna mishi sannu...amsawa yayi Yana tambayar lafiya me sukeyi anan? Domin Shi gani yakeyi kamar baccine yayi ya farka... murmushi kawai sukayi tare da cemai ba komai Sam basu nunamai akwai wani abunba...ahakan suka rankaya zuwa perlon kowa yaji dad'in ganin sutashi cikin koshin lpyr su sedai bawanda ya nuna alamar komai sema cewa da Abba yayi kowa yajeya kwanta dasafe akwai meeting insha Allah zasu K'arasa Wanda sukeyi abbe yadawo kana zasuso suji yadda mama takasance matar alyasat...da hakan kowa yanufi part d'inshi inda mama abbe Alyasat Yusuf Lateep Alhassan da alhusain da ammy suka nufi pert d'in ammy...suko appey da habibbty se su sulaiman da najeeb Fahad suka nufi pert d'in habibbty kowada burin yaga wayewar garin gobe domin Jin abunda yashige musu duhu...!

Nima dai sai goben nan domin alkalamina yace atsaya yahuta gobe naji yadda wannan abun ya kasance:&?




*SOLDIERS FAMILY* na kud'i ne nera 500? kacal =?L? ga duk me buk'atar complete kuma 700? ne Idan kinshirya siya Zaki iya tuntub'ar wannan number =?I? 07037092176 on WhatsApp kokuma kikira wannan number =?I? 08107819124





Autar Alheri
'?


*S F*

Page 31&32

__"ahakan suka kwana ko a part d'in ammy kowa da abunda keransa...washegari da safe bayan kowa ya fito, aka sake taruwa a part d'in habibbty a wannan karon gabaki d'aya stet d'in kowana wurin manya da Yara bayan anbuWe taro da addu,a kana Jalaludeen ya fara basu labarin abunda yafaru A Ghana tin shigarsu k'asar har kawo abbe ya samu lafiya da labarin da gimbiya Halila tabasu na yadda suka samu abbe....kowa awurin yayi shiru yana saurarenshi har sai da yakai karshe

kana Abba yace, "Ikon Allah >?? lallai wannan abun ikon Allah ne kawai da buwayarsa tabbas wannan yarinyar alkhairi ce acikin ahalinmu, Allah yayi Miki albarka zaraah Allah yasaka miki da gidan aljannah.."

"Ameen Ya Allah" duk aka amsa kana habibbty tace, "lallai Zara kincika Yar baiwa samun yarinya irinki awannan lokacin abune me matuk'ar wahala kiyi abunda ko manyan mutane ba zasuyi ba Allah ya faranta miki yadda kikamana kema.."

Shiko Alyasat tunda aka fara bada labarinta abunda ya Waure mishi kai lallai wannan yarinyar ba abun wulakantawa bace agareshi ko dan soyayyar data kema abbenshi ba tare da tasan koshi waye ba gashi tabashi abubuwa ukku arayuwarshi da zuwanta ajiya Wanda kud'i ko muliki kowani muk'ami bazasu baduiba tadawomai da mahaifinshi mahaifiyarshi tasamu lafiya adalilinta kana tabashi budurcinta duk dan saboda iyayenshi shiko mai zai mata arayuwa yabiyata Yayiwa kanshi wannan tambayar!?

Shakka Babu yasan Ko da bayasanta bazai tab'a wulanta taba kuma tana da muhalli mai girma acikn zuciyarshi wanda bai tab'a bama wata maceshi ba...murmushi yasaki Wanda ya k'awata kyakkyawar fuskarshi yana mejin amsar da zuciyarshi ke bashi game da ita, maganar dady ce tadawo dashi daga duniyar tinanin da yaje

Inda yake cewa, "To ya,akayi takasance matar Alyasat Yaya Habeeb?

Nisawa Abbe yayi kana yafara magana kamar hakan, "Hak'ika zaraah matar Alyasat ce ta sunnah domin bayan nasamu lafiya na nemi sanin abunda zaraah keyi zaune acikin jeji Kuma tana rayuwa da aljanu a memakon mutane hakanne yasa gimbiya halila bani labarin zaraah atak'aice.


Wacece zaraah (mama)

A ?auyen shinkafi akwai wani bawan Allah wanda akafi sani da malam mai lazimi shi wannan bawan Allah Babu abunda yakeyi arayuwarshi face karya sihiri da d'aure miyagun aljannu Kuma Yana bada taimakon akan duk wani ciyo daya shafi iska.

Shi wannan Malam yana da Mata biyu Yara 4 maza dukkansu magidanta domin duk ya surardasu isah shine babba sai bello kana sama,ila sai kuma autansu manniru

Malam mai lazimi bayanda wata Sana,adata wuce noma sai ba yadda taimako Wanda ta wannan hanyar yakan samu alherai da dama yanada dukiya sosai inda yaransa suke tafiyadda komai na dukiyarsa kuma daga gefe bello na nashi kasuwanci Daban wandaba na mahaifinsu ba hakan yasaka duk yafisu rufin asiri.

Ana hakan watarana malam mai lazimi yarasu mutuwar da tagirgiza ilahirin garin zamfara harmada kewaye bayan rasuwar mlm da kwana arba,in yaransa suka tada fitina se anraba gado ba yadda isah magajinsu bai yiba amma fir su Sala,ila sukace basusan zancenba



Hakan yasa yacewa bello yaraba yabasu tasu tinda dama shine k'arfin kula da dikiyar hakan kuwa akayi ya raba ya bawa kowa tashi harya Kara masu datashi tindasu suna da y'ay'a shiko bayada d'a ko d'aya bai tab'a haihuwa ba dagashi se matarsa d'aya Nana asama,u Yana kirantada Nana...hakan rayuwa taci gabada tafiya tsakaninsu basuda wani kyakkyawan zumunci daga mlm isah se Bello kawai ke zumuncin su tsakanin su da malam ila tsangwama ne da Gori shidai Malam Isah ba ya da cikakkiyar lafiya, shiko bello betab'a haihuwa ba.

A k'allah bello sai da yayi shekara 45 da aure be haihuba hakan yasa yad'ebe Rai daga samun haihuwar dagashi har matarsa Nana..watarana Nana tatashi da matsanan ciyar rashin lafiya Ko da aka kaita asibitin cikin Gusau akace cikine da ita, abunda ya bawa duka likitoci mamakin kenan domin ganin dattijuwa Yar shekara 59 da ciki maimakon suga tashin hankali agunta ko mujita sai suka ga sabanin hakan domin farin ciki marar misaltuwa suka nuna gidiyarsu ga Allah dasamun wannan rabon

Malam isah yayi murna sosai yayin da ila yaji wannan labari kamar sak'on mutuwarsa..ahakan Nana taci gabada renon cikinta har ya,isa haihuwa....watarana Nana na tafe kan hanya zatakaiwa Bello abinci agona tayi tafiya mai nisan gaske inda tarabu da cikin gari kuma Bata karasa gonar ba tana Jin jejine kawai senak'uda tataso Mata gadan gadan abunga jikin manyanci kai tsaye Nana tagala baita...tana cikin wannan halinne Allah ya jefo wannan twins d'in maheer da maheerah zasu wuce sai kawai sukaga halin da take ciki.

Jin sukayi bazasu iya tafiya subartaba sai kawai maheerah ta taimaka mata harta haihu inda tahaifo yarta mace kyakkyawa San kowa kin Wanda ya rasa seda maheerah tayi Mata komai abunda yadace kana tarakata gida...ita Nana duk kallon takeyi wata mutunce irinta ta taimake ta batasan Sam abun ba hakan bane.

Ko da Bello ya dawo gida yasamu kawai Nana da yarta fad'in farin cikin da ya shiga awannan ranar bata lokaci ne domin duk wani Wanda yasan Bello yasan Yana cikin farin ciki...yayin da labarin haihuwa ya zamema ila tashin hankali da kiyayyar wannan yarinyar da,aka Haifa a cewarshi ta hanshi cin dikiyar Dan uwanshi..

Ranar suna yarinya taci sunan mahaifiyar malam Bello wato fad'imatu Zara,u Kuma sunan mahaifiyar Nana...wannan dalilin ne yasa suke kiranta da *mama* uwar kowace acikinsu kenan..hakan rayuwa ta cigaba da tafiya har mama tafara rarrafe daga gefe d'aya Kuma kullun twins se sunzo sunga mama domin hakan kawai Allah yasaka musu Santa Kuma tanamusu kamasa wata sarauniya acan jinsinsu wadda takasance k'anwace ga mahaifiyarsu maheer na kiranta da uwar gijiyata wannan dalilin ne yasa yake Kiran mama da hakan

Tintana k'arama suke bayyana tana ganinsu kuma Basu tab'a Bata tsoro ba ko firgita ta har seda ta saba dasu hakan yasa

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login