Showing 27001 words to 30000 words out of 55760 words

Chapter 10 - INAYAH

Start ads

20 Aug 2025

425

Middle Ads

ciki da wajeba,hakama kallo daya yake musu kowannensu ya gane halinda suke ciki sbd Sam Baya Wasa da kulawa dakuma tarbiyar gidansa Wanda umma yaganah ta jima da Zama cikin ahalinsa Dan haka itama duk da tana matsayin uwa shine Mai lurarda ita lokuta da dama.

Ruwan sanyi da aka Dan zubawa lemon ya dauka ahankali yakai bakinsa yasha tareda ajiyewa ya dauki tissue ya goge bakinsa ya miqe yabar dining din.

Daga umma yaganah har Inayah babu Wanda yayi Magana daya miqe din sbd hankalinsu Baya Kai Kuma hakan yasake tabbatar Masa da zarginsa akansu na akwai abinda suke boyewa basason ya sanin Dan Bai taba miqewa daga dining batareda dayansu ya ringa maimaita Masa ko ya qoshi da abincinba Dan sun San rashin zamansa yasa Baya wani samun damar cin abinci yanda ya kamata shiyasa daya miqe zasu fara tambayar ya koshi kokuwa ya zauna yaqara ci.

Yana barin dining din Umma yaganah ta kalli Inayah cikin qosawa tace"

Inayah kinason sakawa Abbinki tunanin akwai wata matsalar ne?

Ba nace Miki da kaina zan sanar Masa ba idan aka bada lokaci akasan Gaskiar lamarin¿

Kallon umman tayi tana jin damuwa sosai,
Ita sbd batada uwa batama San uwartaba shiyasa Abbinta takejin idan Abu ya sameta Bata sanar masaba kaman zuciyarta Zata buga.

Ahankali ta gyada Kai tana cewa"

Abbi fa kinsani kwana biyu cikakki bazamuyiba muna wannan boyon zai gano mu.

"Nasani shiyasa nakeson kiyi kokarin cire damuwar komai aranki.

Bata iya cewa komaiba ta miqe tana daukan tissue tace"

Zan kwanta da wuri umma,
Goodnight.

Daqyar ta iya tattara kanta ta nutsu yanda Abbinta bazai gano kamaiba ta qarasa palonsa cikin sanyi da shagwaba ta nuna Masa bacci takeji Zata kwanta da wuri tai Masa goodnight Shima ta fice.

Bai bi bayanta da kalloba sbd Baya buqatan qari fahimta yasan for sure akwai wani abu,

Idan irin hakan tafaru bayace musu komai sharesu yake sbd cikin kwana biyu yasan zai Gama sanin meke faruwa.

Tana barin palon Abbi taji idanuwanta na cikowa da hawayen rashin sanar dashi damuwarta sbd Abbinta shine maganin kowacce damuwarta Wanda Allah ne ya tsaya musu duka akan hakan.
#MAMUH#
#LOVE#
#MARRIAGE


_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya👇
07040727902

MTN card👇
09134848107
[10/16, 8:20 PM] Mariyamah: *16*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Tana Isa bedroom dinta ta kwanta ko kallon Inda wayarta take bataiba.

Bata wani qin samun bacci ba,
Sosai tayi bacci kaman yanda ta saba saidai tana farkawa damuwar dake dabaibaye cikin ranta ta dawo Mata sabuwa fil harma wani 'dacin maqoshi takeji sbd tsananin damuwa da fargabar abinda zaije yadawo,

Tanajin wani irin tsananin bacin Rai da zafin abinda Zaid din yayi Mata da har takejin bazata taba iya mantawaba Amma ta wani bangaren tana cikin tsananin fargaba da tsoron rasashi sbd girman son datake Masa.

Tayi lattin sallah Dan haka alwala tafara yowa tazo tayi sallar asuba tukuna tayi adhkar.

Tana gamawa ta koma kan gadonta tashige bargo tana son komawa bacci.

Rufe idanuwanta tayi tana sake gyara kwanciyarta Amma takasa Jin dadin kwanciyar,

Sake juyawa tayi dayan banagren tana Dan yamutsa fuska cikin yanayi na qosawa.

Jin duk batajin dadin kwanciyar yasata yaye bargon datake rufe dashi tareda tashi zaune ta kalli wayarta dake kan bedside, takuma dauke Kai tana Dan sake yamutsa fuska.

Mintuna biyu ahakan kafin ta qarasa yaye bargon tayi gefe dashi tareda ziro qafafuwanta qasa tana daukar wayarta ta kunna ko duba wayar bataiba daga kunnawan darai ta ajiyeta Nan Inda ta dauka ta miqe tsaye tareda nufar Inda tarin jerin takalmanta suke jere Kaya guda,kusan babu designer shoe brand dinda batada masu zallar tsada.

Time ta kalla taga yanzuma 6:30 tayi Dan haka tasan har yanxu dadynta Yana geam,

Riga da wandon Nike ta saka black da Triple S Balenciaga sneakers farare ta fito ta nufi gym Dinsu dake gidan Wanda saika ratsa palon daya raba palonsu Dana Abbinta zaka Isa watadaccen gym din Mai girma da tsari.

Tana Isa knocking daya tayi ta tura kofar da kusan tafi karfinta sbd qarfin kifar tashiga tana gyara qaramar Vandanar dake kanta.

Sanye yake da black Lululemon wears na exercise,
Bench press yakeyi da nannauyan qarfe a hannayensa Yana dagawa da dawowa,

Shigowarta baisa ya dakataba Kuma Bai waiwayo ya kalli Wanda ta shigoba Dan yasan babu Mai shigowa Nan din kaf idan ba 'yarsaba.,

Cikin kauna da kulawa ta qaraso gurinsa tana cewa"

Good morning Abbi"

A natse ya qarasa abinda yakeyi ya ajiye qarfen tareda tashi zaune wasu qananun zufa abinda ya Gama suna gangara kan lafiyayyar fresh fatarsa ya kalleta lokacinda take daukan ruwa tana basa takuma cewa"

Abbi ka tashi lfy?

Idonta yafara kalla baiga alamar rashin bacci atareda itaba Dan haka Kai tsaye cikin nutsuwa da kulawa yace"

Morning Inayah,
Lfy kalau alhmdllh,
Me zakiyi da gymin yanzu?
kinason ki rage keda kike amarya?
Ko Kin manta kin daina zumudin auren ne tun yanzu?" ya qarasa cikin yanayi na Wasa da 'yar tasa tilo.

'yar qaramar dariya tayi tana hawa kan leg press machine tafara ahankali tana cewa"

Abbi naji banason auren Kuma yanzu
Banason tafiya nabar gida,
Abbi kullum zanyi missing naka,
Gskia Zaid zai ajeni a Inda zanna ganinka.

Murmushi kawai yasake ahankali Yana goge qananun zufansa da wata farar towel qarama yace"

Zaki Saba ahankali musamman idan kika Zama uwa,
And kafin can ma you will be busy with your work bazaki samu lokacin tunanin kewan gidaba.

Abbi duk da hakan nasan kullum sainayi kewanka,Dan Allah Abbi kace musu anan zasu ajiyeni.

Girgiza Mata Kai yayi Yana murmushin wautarta da har take cewa ta girma yanzu idan Yana Mata fadan wani abun,

Haryanzu jinjira ce shi agabansa Dan ko wannan auren Dan kawai ta nace tanaso ne yanzu yasa zaiyi Mata Amma tabbas da saita sake wayo da girma sosai
Aqalla saita fara aiki tasan ciwon kanta Dana rayuwama Dan kuwa haryanzu Batasan komai na rayuwaba,
Babu abinda tasani daga mahaifinta sai mahaifinta tukuna sauran abubuwan.

Tare suka qarasa gymin din suka fito itace mai surutu Yana saurarenta hankali kwance daga shi har ita skin Dinsu glowing kawai suke gasa ta tsantsar hutu da wadata kasancewar shi rigarsa armless sai dogon wando,
Itama rigarta qaramin hannu me da ita sai dogon wando.

Kowannensu hanyar dakinsa ya nufa,
Wanka tafara tubewa tayo ta fito kenan wayarta tahau ringing ta qarasa tana dubawa taga Zaid ne.

Wani zafin gaske ne ya taso Mata daga qasan zuciya,
Duk lokacinda sunan zaid ya fado ranta Jin take tamkar Zata Kama da wuta sbd tsananin zafin kishi da baqin ciki.

Jefar da wayar tayi tareda nufar gaban madubu tafara shiryawarta.

Oil ta shafa tareda moisturizer kadan ta fesa su spray da body mist dinta ta nufi closet.

Sai after 9 tafito sanye cikin fitted long sleeve gown kalar blue sai qaramar scarf nade akanta.

Dakin umma yaganah take kokarin Isa Amma taji kaman muryan Abbinta a dining room Yana waya Dan haka ta juya ta nufi dining din.

Shi da umma yaganah ne zaune Dan haka itama ta qaraso tana cewa"

Tun yanzu anfara ware ni a gidan Nan.

Umma yaganah ce tayi Yar dariyar Jin Dadi ganin Inayar ta sake
Dama Allah Allah take MAJEED yafita gidan kafin ya dagosu su samu sugani idan zasu iya kashe zancen iya tsakaninsu.

Ita harga Allah babbar damuwarta irin fushi Mai tsanani da MAJEED din zaiyi idan yaji 'yarsa da duk arzikinsa da zamansa busy Bai hanasa tsayawa yana ture komaiba Dan ginarda tarbiyarta tun tana jinjira har zuwa yanzu yaji sunje gidan saurayi tasan wlh ranar ransa qarshen bacin Rai zaije,
Hakama Kuma qarin abin bacin ran da baqin cikin yaji Inayar da bakinta tana fadar hannun Zaid acikin riga Yana latsa nonuwan wata,su kansu sun San ranar sai yanda Allah dai yayi dasu daga ita umman har Inayar.

Ata wani bangaren tasan Sarai Inayah Zata iya fadar hakan gaban Abbin nata.

Dan hakan yanzu ba qaramin farin cikin ganin Inayah ta sakeba tayi har Saida kusan Abbin yagane Amma dai baice komaiba har lokacin.

Breakfast sukai suka Gama ya fice zuwa aikinsa.

Yana fita Inayah ta tattaro bacin ran da baqin cikin dataketa dawainiyar boyewa cikin ranta kaman zai kasheta.

Bata wani tsaya dogon zanceba tacewa umma yaganah Zata gidansu Neesah tadawo Dan tanason Jin komai dalla dalla daga gareta idan ba hakanba zuciyarta tashiga tunani kala kala da zasu iya hallakata.

Sanin irin tsananin zafin kishi da Allah yayiwa Inayah yasa umma yaganah barinta zuwa gidansu Neesah din.

Tana barin gida batabi ta hanyar da saita bi ta anguwarsu Zaid kafin ta Isa gidansu Neesah ba Dan Bata buqatan ganin gidan ko kadan,
Jin take ta tsana gidan da anguwar gabaki daya.

Tana Isa gidansu Neesah itama Neesar na kokarin fitowa da motarta Zata gurin Inayah din.

Komawa ciki Neesah tayi da tata motar INAYAH taqarasa shigowa da tata motar sukai parking tare suka fito kusan lokaci daya.

Kallonta Neesah keyi lokacinda ta fito mota fuskarta duk babu walwala.

Cikin kulawa tace"

Hey babes,
Yaya?
Are you okay?

Wani kallo Inayah tai Mata tana qarasa Kama hannunta data miqo Mata tana cewa"

Nai Miki Kama da wadda take okay?

Kina tunanin zan Zama daidai bayan abinda idona ya ganarmin jiyan?

Ciki suka qarasa suna magana ahankali sbd rashin walwalar Inayah.

Momy na gurin dadyn Neesah Dan hakan Kai tsaye dakin Neesah suka wucewarsu.

Zama sukai Inayah na wurgi da handbag dinta da car key dinta ta kalli Neesah dake miqo Mata bowl din Candies tace"

are you for real?
Me zanyi da candies bayan 'dacin da zuciyata take ciki.

Ajiyar zuciya Neesah tayi tana Zama cikin sautin Mai mahimmanci tace"

Maganar 'dacin Rai ko baqin ciki bashine abinda yakamata ki fuskantaba,

Zaid dai wallahi Neman mata yake,
Nasha ganinsa da Amal a yanayi marasa kyan gani,
Nayi bibiyarsa Dan tabbatarwa Kuma na tabbatar Dan haka bawai maganar kishi ake ananba
Maganace ta ki nutsu kisan wanda Zaki aura da halayensa,

Bansan yaushe ya sauya yakoma hakan ba Amma a zahirance ya dade a wannan rayuwar da Amal Dan hakan maganar sauyawarsa lokaci daya zaiyi wuya....

Kasa magana Inayah tayi ta zubawa Neesah idanuwanta dasukai jajir sbd tsananin baqin ciki da zafin zuciya.

Cikin takaici da masifa tace"

Shine Baki taba fadanba?
Da banganiba da kaina ahakan Zaki Bari ayi auren nagama haukacewa a sonsa shikuma Yana can Yana kwanciya da wata macen?

Cikin damuwa Neesah tace"

Inayah Kona fada ba ganewa zakiyiba sbd idonki ya rufe akan Zaid,
Tayaya Kai tsaye zance Miki Zaid is sleeping with another woman?
Zaki yarda ne idan nafada?

Kalman "sleeping with another woman" shine yafi komai gigita dukkaninta Dan hakan Batasan lokacinda hawayen baqin ciki Mai qarfi suka fara gangaro mataba.


Sanyi jikin Neesah yayi ta matso kusada ita cikin tausasa murya tace"

Inayah wannan shine Namiji,
Duka wannan kadan ne idan baka nutsu kasamu mijin dakakeson more rayuwan aure dashi,

Inason aure nima kinsani sosai Amma Kuma bazan iya auren Wanda nakewa so irin hakan dakikewa Zaid ba sbd disappointments na cikin irin wannan son..

Gudu hawayenta suka qara sbd ba itace ta sawa kanta son Zaid ba Allah ne ya jarabceta da irin wannan son datake Masa,
Uwa uba ga zafin kishi datakeji Kamar ta hadiye zuciyarta ta mutu.

Rarrashinta Neesah tafara yi Amma Sam takasa Jin sassauci Dan hakan ta miqe tareda daukan Jakarta da key dinta tana nufar kofa.

Binta Neesah tayi tana cewa"

Babes Ina Zaki?

Cikin qunci tace"

Zanje naji daga bakinsa meyesa zaimun hakan.

No Inayah please karki Kuma zuwa gidansa sbd kada komai ya qarasa lalacewa,
Qazantar da baka ganiba tsaftane.

Bata sauraretaba tayi gaba tana cewa"

Idan bazakiba please kibarshi a iya.

Bazan iya Bari kije ke kadaiba Kuma ai dole zanbiki,
Bani key din I will drive.

Miqa Mata key din tayi tareda budewa ta shiga kafin Neesah din tashiga mazaunin driver ta tada motar suka fice daga gidan.

Tafiya suke zuwa gidan Amma babu wadda zuciyarta Bata bugawa acikinsu,
Neesah tasan tabbas sai sun samu Amal a gidan.,

INAYAH Kuma fargaba da shakkar samun mace take agidan tareda zaid sbd wannan karon bazata iya daurewaba komai zai iya faruwa Dan kuwa zuciyarta Zata iya bugawa.

Kuma ganin Zaid da wata tamkar qarasa buga zuciyarta ne zatai.

A slow Neesah ke tafiyar itama tanata adduar Allah yasa kada su tadda Zaid a gidanma gabaki daya bare wata Amal.
#MAMUH#
#AA MAJEED
#AYSHATOUH INAYAH
#MARRIAGE
#LOVE/ROMANCE



_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya👇
07040727902

MTN card👇
09134848107
[10/18, 1:57 PM] Mariyamah: *_17_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Suna Isa kofar gidan dake cikin jerin irin tsarin gine ginen turawa da basada gate sai harabar gida.

Parking Neesah tayi tana kallon motar Zaid data tabbatar da Yana gidan,

Kallon Inayah da idanuwanta sukai jajir tayi duk saitaji ranta yasake dugunzuma itama,

Allah yasani tafi kowa sanin irin son da Inayah kewa Zaid tunda itace aminiyarta,
Mahaifinta yasan tana son Zaid shiyasa dole shima yake kaunar Zaid
Hakan yasa duk suma suke kaunar zaid sbd Inayah na sonsa.

Wannan abin dayayiwa Inayah yasa taji duk ya fita ranta,

Takuma San tata tsanar Mai saukice akan wadda mahaifin Inayah zai Masa duk ranarda yasan abinda yayiwa 'yarsa.

Motar INAYAH ta bude Kai tsaye tareda nufar hanyar kofar gidan
Neesah ta fito da sauri tabi bayanta tana cewa"

Inayah give him a call atleast yasan da zuwanki,
Banason asake samun.......

Maganarsu ce ta katse daidai bude kofar da Zaid yayi zai fito Amal na bayansa riqeda hannunsa tana Masa magana Kamar wata karuwa.

Ba zato ba tsammani yagansu kofar,

Qwace hannunsa yayi da sauri daga na Amal Yana kallon Inayah dake kallonsa cikin Ido da jajayen idanuwanta.

Matsowa yayi gabanta zaiyi magana ta girgiza Masa Kai idanuwanta na kasa riqe Mata hawayen dataketa kokarin riqewa.

Cikin yanayi na tausasa harshe da damuwa yace"

Baby babu wani abinda yake faruwa anan,
She's just a friend.....

Cikin baqin cikin abinda yafada Amal ta matso gaban Inayah tana kallon kyakkyawar fuskarta datai jajir tace"

Banajin fa tana fahimtar abinda kake fada besides inaga ba illa bane idan friends sunje gidan juna hakama ke da qawarki ke kwana gidanku ya damu daya tambaya abinda ke tsakaninku ne......

Wani mahaukacin Mari Inayah ta saukewa Amal sbd baqin cikin abinda take nufin fada akanta da Neesah,
Sai alokacin ta juyo ta kalleta cikeda tsana tace"

Banajin nayi magana dake bare kiban amsa.

Kan Zaid din ta maida kallonta a tsananin qyamace take kallonsa zuciyarta na tafasa da wani irin baqin ciki tace"

Me take dashi daka zabi rayuwar shashanci da ita akaina?
Tafini kyau ne kokuwa?
Ita wacece?
Daga Ina ta fito?
Ina Zata?
Kudi tafimu ne?

Cikin Dan daga murya Zaid din ya katseta da cewa"

Inayah please duk ba wannan bane,
Qaddara ce...

Ahankali ta iya bude Baki ta furta"

Neesah muje.

Juyawa tayi ta wuce tabar gurin ko ganin gabanta batayi sosai.

Amal dataga ba'ayi balai da masifar dataso ayiba ta tafi da sauri Tasha gaban Inayah tana cewa"

Idan na fahimci maganarki ta qarshe da kyau kina nufin son kudi yasa Zaid da iyayensa suke son aurenki??

Kina tunanin mahaifinki fin nasa mahaifin yayi kome?

A wulaqance da zafin kishi da baqin ciki tace"

Mahaifina ba abun wasar dazaki iya hadawa da tarkacen haukarki bane so better watch out you bitch....

Da mamaki Zaid ya katseta da cewa"

Kece Zaki San abinda zakina fada Inayah sbd Alan haukar kishi ko zafin kanki karki zaga nawa mahaifin..

Murmushin Jin Dadi Amal tayi sbd dama tasan babu Wanda zai dauka zancen banza akan mahaifinsa Musamman Inayah dako Wasa ba'ayi da sunan mahaifinta Dan kuwa Bata dauka ko kadan.

Tsoki Mai zafi Inayah tasake batareda tasan ta sakeba zuciyarta na tsananta kuna tace"

Ba karuwarka kadaiba ko Kai na haramtawa fadar sunan mahaifina a bakinka bare hadasa da kowa.

Juyawa tayi a zafafe tabar gurin tareda nufar mota.

Neesah ce ta iya tsayawa qarasa musu da cewa"

Zaka iya jawa budurwarka kunnen daina shiga abinda Babu ruwanta.

Juyawa tayi itama tabi bayan Inayah dake Jan numfashi cikin mawuyacin hali tamkar Mai Asthma.
Da sauri ta tada motar ta nufi hanyar gidansu Inayah din tana adduar kada su sama Abbi a gida.

Suna Isa gida umma yaganah na ganinsu tasan ankuma kenan.

Dakin umman suka kwantar da ita suna faman kwantar Mata da hankali da kokarin ganin tadawo daidai.

Wata irin weak heart gareta da bakomai take iya dauka ba na tashin hankali ko quncin shiyasa tunda take duniya mahaifinta AA MAJEED Bai taba Wasa da duk abinda ya shafi 'yar tasaba,
Duk wani gata da walwalar rayuwa ya wadata Yar yasa dashi,

Sbd ita yayi gwagwarmaya da Fadi tashin rayuwa ba dare ba Rana Saida Allah yabasa arziki
Duk sbd wadatar da 'yartasane gashi lokaci 'daya wani qaton gardin banza zai lalata Masa rayuwar 'ya.

Daqyar suka samu ta iya dawowa daidai tayi shiru daga kwance hawayen baqin ciki na gangara daga idonta suna jiqa pillon datake kwance akai.

Tunda suka dawo Bata iya fadar kalma ko dayaba sai hawayen baqin cikin datake zubdawa zuciyarta na quntatuwa da rashin Zaid da zatai ta bangare daya Kuma gabaki daya neman fita ranta yakeyi sbd Sam lokaci daya take tsanar duk Wanda ya nuna rashin girmamawa ga mahaifinta.

Har Neesah ta wuce gida Inayah taqi cewa komai saidai kukanma ta daina saidai dukkanin fuskarta ta Gama yin ja da kumburar data bayyanarda zallar kukan datasha.

Bayan tafiyar Neesah umma yaganah tasata taje tayi wanka da sallah tayi kwanciyarta daki abincima taqi ci tace Bata buqatan komai.

Har dare Inayah din Bata fitoba har Abbinta yadawo baisan abinda yake faruwaba dayake latti yadawo gidan Dan hakan yasan sun Riga sunci abincinsu sun kwanta.

A cikin daren daqyar Inayah ta iya bacci sbd tsananin ciwon Kai na kuka da damuwar data cikata.

Gari na wayewa har 10 Abbin baigantaba Kuma baiga kirantaba Dan hakan Kai tsaye ya daga waya ya Kira wayarta amma yaji akashe.

Da Dan mamaki ya kalli wayar tareda ajiyewa ya miqe tsaye Kai
Tsaye ya nufi hanyar bedroom dinta.

A hanya ya hadu da umma yaganah zubbi na biyeda ita da tray a hannu jere da breakfast zaa kaiwa Inayah din.

Da mamaki ya kalli umman Yana sake maida kallonsa kan abincin da zaa kaiwa Inayar harda maganin da tunda safe umma yaganah tasa Dr farhat takawowa Inayah din Dan basuso ya sani.

A natse ya bude Baki yace"

Meyake faruwa anan?
Inayahn batada lafiya ne?
Meya sameta?

Ajiyar zuciya umman tasake sbd tasan yanzu kam Babu wani sauran boye boye Dan dama ciwon Inayah mahaifin natane yasan yanda yakeyi da ita Tasha magani.

Jiki amace tace"

Ciwon Kai ne taketa fama dashi Mai Dan tsanani,
Dr farhat takawo wannan maganin abata.

Manyan fararen idanuwansa ya zubawa umman batareda zallar mamakin dake ransa ya bayyanaba ko kadan sbd qwarewarsa gurin riqe emotions.

Kai tsaye dakin ya bude yashiga da nutsatsiyar sallama.

Jin muryar Abbinta yasata bude idanuwanta ahankali ta kallesa tanajin wata sabuwar karyewar zuciya da kuka na zuwar Mata.

Fuskarta da idanuwanta ya kalla take yasan Bata rintsaba kuka tayi Wanda Bai taba barin tayiba shida yake ubanta,
Uban waye yasaka 'yarsa a wannan halin ya furta a zuciyarsa data dauki 'daci da mamaki.

Maida kallonsa yayi kan umma data sake shiga kame kamen Inda Zata fara bayani.

Gurin

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login