Showing 39001 words to 42000 words out of 55760 words

Chapter 14 - INAYAH

Start ads

20 Aug 2025

427

Middle Ads

shiga Dan haka Saida ya matse ayyukansa yazo Lagos din hankalinsa ya kwanta.

Da farko Inayah na ganinsa daya iso gidan nasu Batasan lokacinda ta fashe Masa da kuka ba tana sake maimaita Masa abinda yafaru.

Hankalinsa Bai tashi da abinda ya faru dinba kaman yanda hankalinsa yatashi da kukan datakeyi Wanda taketa riqewa da dannewa cikin ranta sbd gudun daga hankalin umma yaganah da Abbinta,

Amma tsakani da Allah har cikin ranta tanajin tsananin quncin rashin faruk Wanda gabaki daya yanzu idanma yakira bayan kuka Babu abinda take Masa harya daina kiranta sbd kukanta ba qaramin daga hankalinsa yakeyiba,

Kukanta zai iya sakasa bijirewa iyayensa ya dauketa suje suyi aurensu wani gurin Amma Kuma hakan ba qaramar fitina zai tadaba dan kuwa Yana shakkar mahaifin Inayah din sosai tako ina.,
Bayason ya jawa iyayensa 'daurin da zai taba tsufa da mutuncinsu Amma badan hakanba Babu abinda zai hanasa guduwa da Inayah wani gurin a daura musu aure.

Hankalin Dr Abdul ya matuqar dimauta da kukan Inayah wadda yakewa wani irin boyayyan son da yafara fin qarfin qarfinsa,

Shi mutum ne Mai tsananin zurfin ciki da iya danne Abu shiyasa son nata yake boye cikin ciki da zuciyarsa Amma irin son dayakejin yanai Mata a yanzu bazai iya barin wani ya auretaba koda zaaita saka ranar auren nata ana warwarewa har sai ranarda ya sameta.

Ita kanta tanajin Dr Abdul cikin ranta sosai Amma ba amatsayin masoyiba sai matsayin aboki wanda batada tamkarsa bayan Neesah.

A gidan ya qarasa wuninsa Yana rarrashin Inayah shida umma yaganah daketa qara gode Masa kan damuwarsa dayake nunawa sosai akan Inayah din.

Yana gidan Abbi yadawo Dan hakama Dole atare dasu yaci abincin dare dukkaninsu a dining.

Dr Abdulsamad yasamu shiga sosai agurin Abbi Wanda da farko harsu Inayah din sunyi mamaki sosai tunda sunsan shi mutum ne Mai wuyar sabo da mutane,
Bakowa yake yarda yashiga jikinsaba sosai
Amma Dr Abdul lokaci qanqani yashiga ran abbin ya kwanta Masa sbd sanin kansa dakuma qaunar Inayah Mai girman gaske daya hanga atareda Dr Abdul din.

Ya jima Yana fira agurin abbin kusanma duk akan aikin asibitin ne nasu da ake gab da kammalawa,
Sai dare yabar gidan yatafi lokacin INAYAH ta jima da yin bacci sbd yanzu Bata wani jimawa take bacci.

Neesah Takoma Abuja gurin momy datazo ta jajanta musu suka koma tareda Neesah din Abuja.



******Ahankali Dr Abdul ya Dage sosai gurin mantar da ita faruk dukda da Kamar wuya
Amma Kuma dagewar tasa da tsananin kulawarsa akanta yafara cin nasarar hakan Dan yanzu ba laifi tacirewa ranta faruk din ta hakura saima hankalinta data maida sosai akan Dr Abdul din kan aikinsu.

Faruk yakoma Malaysia qaro karatu Dan haka yanzu wayar tasu ma kusan kwata kwata sun daina saidai idan sunga juna a social network.



***Lokaci ya 'dan sake ja son da Dr Abdul ke Mata yafara juyewa zuwa wani Al'amarin daban,
Yanzu gabaki daya ya sauya akanta yakoma kaman ba Natsatsen Dr Abdul din dakowa ya saniba,

Wani irin so Mai zafin gaske yake Mata Wanda harya fara bawa umma yaganah tsoro gashi dai Bai fito yafada Mata Sonta yakeba Amma dai kowa ya kallesa yasan yagama zautiwa a Sonta Dan ko kallonta idan yanayi mantawa yakeyi da kowa.

Ita kanta Inayah lokuta da dama tsananin kulawarsa da abubuwan dayake Mata na kauna tsoro da shakka suke Bata Amma har lokacin batajin tana Masa son soyayya saina aboki,yanzuma ya wuce abokinta ya Zama wani bari na rayuwarta.

Abbinta ma ya lurada halinda Dr Abdul yake ciki akan Inayah,

Baida matsala akan bawa Dr Abdul aurenta Amma Kuma Yana shakkar irin son dayake Mata zai iya cutatar da ita akan kishi kokuma cutatar da duk wanda zai shiga tsakaninsa da ita Dan haka son shima yake sakasa shakku,
Ta wani bangaren Kuma tausayinsa yakeji Mai tsanani sbd son mace irin haka kaman ba so bane ciwo ne.

Anty Hafsat koda aka fasa auren Inayah da Faruk Bai taba alaqarsuba saima sake shaquwa dasukai Dan haka yanzu tazama antyn Inayah tamkar wata qanwar uwa ko qanwar ubanta
Komai na Inayah tasani da ita suke shawara so da dama
Hakama Umma yaganah ta zamar musu tamkar uwa a gurinta suke wasu shawarwarin.

Anty Hafsat din batai qasa a gwiwa ba takuma hada wani qaninta dasuke uba daya da Inayah.

Sadeeq qanin anty Hafsat yayi karatun likita shima anan Lagos yatashi Kuma sosai yakeda abun kansa saidai yayi irin wayewar datai qazanta shima Neman Mata yakeyi sosai Amma Kuma bazaka kallesa kace yanayi dinba Dan kuwa a kamile yake a zahirinsa.

Ba laifi ya Dan fara shiga ran Inayah saidai Bata wani zura da yawaba sbd tafara Jin shakkar Al'amarin maza da aure.

Shima dagewa yayi da soyayyarsa da kulawarsa harma da alqawuransa yasamu yashiga zuciyar Inayah din.

Wannan karonma ba Bata lokaci ya aiko iyayensa da maganar aure.

Abbin yaso su saurara Kar ayi rushing din Al'amarin Amma Dr sadeeq din ya dage da iyayensa har abbin ya yarda.

Dr Abdulsamad kusan zaucewa yayi da wannan maganar auren Kuma Saida kusan kowa yakusa gane halinda yashiga,

Kasa hakuri yayi sbd zuciyarsa bazata iya daukaba yabi ta qarqashin qasa ya lalata auren ta hanyar tona asalin waye Dr Sadeeq Kuma can ma gidansu anty Hafsat akai fitinar ta hada 'dan uwanta da 'yar gaban fatiha tunda ba uwarsu dayaba.

Wannan karon har asibiti Inayah ta kwanta ciwo sosai sbd zuciyarta tafara kasa dauka
Abubuwan sun fara tabata sosai.

Hankalin umma yaganah da mahaifinta ya tashi sosai sbd Saida suka dangana da zuwa Australia taga likita acan tayi jinya
Ta huta kanta ya Dan sake kafin suka dawo.

Ciwonta ba ita kadai ya taba ba harda Dr Abdul Wanda shima hankalin mahaifiyarsa yafara tashi da wannan mummunan masifar dake tunkarota 'dan ta namiji guda datake alfahari dashi Yana Neman samun tabin qaqwalwa akan son mace.
##MAMUH#
#AA MAJEED#
#AYSHATOUH INAYAH#
#DR ABDUL SALEES/HADIZA



_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya👇
07040727902

MTN card👇
09134848107
*_24_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Alaqarta da Anty Hafsat Bata taba girgiza ba sbd fashin auren da aka samu akaro na biyu saima tausayin juna dasuke,

Su suna ganin qoqarinta da tausayinta akan yanda taketa kokarin hada Alkhairi Amma Alamuran na lalacewa,

Itama tausayin Inayah takeji sosai sbd yanda Inayah duk tabi ta sukurkurce akaro na uku da fashin auren.

Alqawari tayi bazata qara kawo kowaba ya nema auren Inayah tun basu fara tsanartaba
Amma duk mijinta Inayah Zata aura alqawarine ta dauka itace Zata jajirce su tsaya sosai da umma yaganah suyiwa Inayah gyaran gaske da duk wainda sukaiwa kansu hasarar rashin aurenta sai sunyi kukan baqin ciki da Dana sani.

Yanzu sosai take tsoron kula mazama kwata kwata basa ranta sunma fice Mata Rai sbd a matsayin da raunin zuciyarta yakai aka Kuma samun matsalar rashin aurenta komai zai iya faruwa da ita Dan haka tayi nesa da duk wata alaqar dazata Kuma jefata soyayya.

Abbinta ma sosai yake data da taka tsantsan akan Wanda Zata Kuma samu yaanzu sbd kaucewa hadari da damuwa,
Duk aka Kuma samun irin wannan matsalar likita ya fada Masa zuciyarta ba lallai takuma daukan wani mummunan tashin hankalinba.

A yanayin weak heart irin na Inayah shi baimasan me zatayi da soyayya ba sbd duk wani disappointment Yana cikin soyayya yake gani.

Haka suketa lallabawa da tunanin ta Inda wani manemin auren zai bullo mata.,

Ita dai umma yaganah fargabarta da babbar damuwarta kada Inayah din itama auren yafita ranta kwata kwata kaman mahaifinta,

Shi namijine bazaiyi tsufa a aurenba Nan kusa barema kusan yanzu ne yake cikin shekarun da neman aure agurinsa abune Mai saukin gaske,

Ita Kuma yanzu tanada sauran kuruciya ayanzu ne auren ya kamaceta kaman yanda take buri da tsananin kaunar yin auren
Dan haka ta ninka roqonta gurin ubangiji Allah yakawo musu abokanan rayuwa masu albarka suyi auren.


***Familyn Dr Abdul hankalinsu yafara tashi akan yanda ya dauko hanyar tabarbarewa akan mace,

Duk Wanda yake Dan uwansa yasan INAYAH A MAJEED a rayuwar Dr wata babbar jarabawace,

Abin haushi da baqin cikin shine duk yabi ya lalace akanta Amma wai Bata saniba hakama iyayenta suna gani sunyi kaman basu ganiba,
Hakan yasa kusan duk wasu Yan uwansa sukaji basa kaunar Inayah din sbd Dan uwansu daya Zama gwanin tausayi baida zance sai nata.

Ana cikin hakan Inayah ta hadu da wani yayan abokin Safnah.

Mimi da gudu ta ringa Jin Dadi sbd yanzu mijin ta bangarensu ya bullo Dan haka ta zaqe tanata sake cusa zancen Ahmed din gurin Inayah da umma yaganah saidai Inayah Sam hankalinta Bai kwanta takuma sakewa sosai akan soyayyaba Dan har yanzu akwai sauran son faruk maqale acikin ranta.

A karon farko da zancen ya Isa kunnen Dr Abdul sanyi jikinsa yayi ya silale ya zaune Yana sauraren Inayah din dake fada Masa da kanta.

Bai iya ce Mata komaiba saima kasa kallonta da yayi sbd kada taga yanayinda yake ciki Dan kuwa Zata girgiza da ganin idanuwansa dasukai jajir.

Bai iya tsayawa yin aiki ba ranar sulalewa yayi ya koma gida sbd ciwon Kai Mai tsananin gaske daya taso Masa.

Itama haka Takoma gida jiki amace sbd yanayin Dr Abdul din daya sakata damuwa.

Baiyi bacci ba ranar haka ya kwana Yana juye juyen ciwon Kai Mai tsananin gaske da azaba,

Yasani matuqar Mai samu Inayah ba wlh zai iya haukacewa
Hauka tuburan ta gaske,
INAYAH tazamar Masa jarabawa Kuma qaddara.

Hawayene suka gangaro Masa masu zafin gaske ya miqe zaune tareda nade jikinsa waje daya Yana fashewa da kuka Mai tausayin gaske.

Washe gari Bai iya fita aikiba sbd ciwo ya kwantar dashi
Haka Inayah tazo tareda Dr Emma ya dubasa.

Ciwon kansa Mai tsanani ne Dan haka yayi requesting suje asibiti ya dubasa acan Amma yace AA ba buqatan hakan Inshallah maganin ma zaiyi Masa.

INAYAH ce tasaka aka kawo maganin daga asibiti yasha ya shige ya kwanta itama Takoma gida jiki duk amace.


Kwanansa biyu a kwance kafin ya Dan warware yaci gaba da fita aiki.

Babban abinda ya bawa Inayah tsoro itada umma yaganah da Anty Hafsat shine tun ba'aje koinaba akan maganarta da Ahmed Al'amarin ya lalace ta hanyar Kama Ahmed a drugs case.

Haka kawai hankalin Inayah yaqara tashi sbd ta tabbatar yanzu kam koma menene yake lalata aurenta daga gareta ne sbd shaidu da komai sun nuna Ahmed gskia mutumin kirkine baya hulda da drugs tako Ina Dan haka akafi tunanin sharri akai Masa.

Kan kace me mutane suka fara canfa daga Inayah ne duk Wanda yazo aurenta to masifu kala kala na zuwa garesa.

Hankalinta ya tashi sosai da wannan mugun Al'amarin har abin yaso tabata,

Abbinta kuwa take yafara Dana sanin dawo dasu Nigeria,
Da suna can duk da kila Canfi da wasu abubuwan rashin wayewa basu faruba,

A qasar waje da qabilu daban daban anan dinma basu damu da auren Wanda aka Haifa bada aureba sbd idanma hakane shi ai ba laifinsa bane,
A taqaicema shi abin tausayi ne Musamman ga Wanda hakan ta kasance dashi Yana musulmi.

Amma duk Anbi an hargitsa Masa rayuwa da tunanin 'ya Bayan duk tattalinsa da kulawarsa sun qare akan 'yarsa tilo guda.

Fara tunanin maidasu Australia yayi Nan Kuma hankalin umma yaganah yafara tashi sbd har ga Allah tafison zaman Nigeria sbd kana cikin qasarka kafi nutsuwa da kwanciyar hankali idan ba su dasuke Yan boko ba sunfi son rayuwar turai din.

Dama shi Abbin yafi kaunar zamansu acan ne sbd nesanta Inayah da irin wainnan maganganun dayasan matuqar suna Nigeria yau da gobe sai Mutane sunfara maganganun dazasu saka Mata wasi wasin asalinsu akanta.

Ya zabi barinsu zaman wata qasar ne da nesantata da bude Baki wataran ta tambayesa mahaifiyarta kokuma asalinsu,kokuma labarin yanda mahaifiyarta ta tafi tabarsu.

Gashi tun ba'aje koinaba anfara rikita Masa kanta da wainnan fitintinun,

Auren data sakawa ranta ta nace gashinan Bata samu 'dan amanar dazai iya aurenta dan Allah ba,
Daga Wanda keson aurenta Dan dukiyar mahaifinta sai Mai son wani bangare na jikinta sai masu aibata zuwanta duniya.
Dan hakan yanke shawaran maidasu kawai su koma sai Kuma gaba idan Allah yakawo dalilin dawowar.


Labarin barinsu Nigeria shine ya fidda asalin ciwon dake damun Dr Abdul akan Inayah Dan kuwa har Saida yayi Dana sanin lalata aurenta da Ahmed tunda wuri.,

Kusan zaucewa yayi Dan kuwa baimasan lokacinda yakai kansa gurin Abbinta ba Yana kuka da idanuwansa akan yabasa aurenta shi zai aureta sbd Babu Wanda yakaisa sonta.

Dama yasan za'ai hakan to Amma shi kam soyayyar Dr Abdul din shakku take sakasa,

Son yayi yawa,
Bai taba ganin irin hakan ba,
Basa Inayah din kaman yanada hadari sosai sbd irin wannan ya wuce so ya zama possession.

Amma Kuma ta wani bangaren tausayi Mai zurfi Abdulsamad din yake basa sbd mutum ne Mai nutsuwa da Kamala tareda ilimi sosai Amma sbd soyayya shima duk hakan na Neman gagararsa,
He is loosing everything slowly.

Ta wani bangaren yasan samun Inayah ce warakar Dr Abdul din haka zalika badan tabin kan son dake Neman yawaba yasan Dr Abdul zai Zama Miji nagari Mai kula da kauna ga Inayah.

Dan haka ko yanzu Bai cire ran Dr Abdul din zai kasa kula da Inayah ba,
Yana saka ran idan yasamu Inayah din bazai Bari haukarsa ya cutatar da itaba Dan haka yace yabasa dama ya nema Inayah din idan ta amince shikenan,
Amma da sharadin zai bisu can qasar zai Samar Masa aiki a one of the best hospitals dake qasar
Yaci gaba da aikinsa acan da matarsa.

Baiga abinda zai tsaya tunaniba matuqar zaa basa auren Inayah din Dan haka Kai tsaye ya amince,
Dan koba komai kusan qaruwarsa ce zuwa wata qasar aiki.

A natse abbin ya girgiza Masa Kai Yana cewa"

No Kar kayi rushing abubuwan
Zaje kayi shawara da iyayenka da mahaifiyarka dakace,
Sbd kaman abune da bazaka iya yankewa Kai dayaba Dole kana buqatan iyayenka aciki.

Shidai farin cikinsa ya hanama ya tsaya dogon zance ya amsa da cewa"

Inshallah zan tafi cikin satin Nan na sanar da ita komai Umman tawa.

Allah ya taimaka yasa hakan shine mafi Alkhairi.

Amin, thank you sir,
Ngd sosai Allah yaqara girma da rufa asiri.

Amin.



******Abbi ne da kansa ya sanarda umma yaganah da Inayah buqatan Dr Abdul na abasa damar neman auren Inayah din Kuma yabasa damar Amma sai idan ta amince.

Umma yaganah ba Bata lokaci ta bayyanarda farin cikinta sbd ta jima tana yiwa Inayah shaawar auren Dr Abdul din Dan nutsuwarsa da kamalarsa,
Gashi kyakkyawa shima da Dan arzikinsa ba laifi.

Shi kansa Abbi gskia Dr Abdul din ya kwanta Masa fiyeda duka maneman da Inayah din tayi a baya Amma Kuma yafison tayi zabi akan Dr Abdul din da kanta.

Wani iri taji Al'amarin a farko Dan haka batace komaiba.

Neesah tafara fadawa a waya
Aikuwa Neesah ta ringa tsallen Murna sbd tasan Dr Abdul tako Ina yayi gskia,
Ita da harta fara yiwa kanta sha'awar aurensa Amma ganin basa qasa daya yasa bata zurfafawa kantaba dakuma hango tsagwaron son Inayah a idonsa.

Safnah ma tsallen murna ta ringa Yi tana cewa"

Wlh dama nasan zaai hakan sbd Dr Abdul ya dade da mutuwa akan sonki Naga alama.

Anty Hafsat ma a nata bangaren hamdala da godewa Allah tayita yi sbd dukkaninsu sun yaba da mutuncin Dr Abdul dakuma shedar irin son dayake Mata bazai taba gudunta ba Dan duk wani abunda zaa fada.

Itadai Inayah tanajin 'yar shakkar Al'amarin sbd girman matsayin Dr Abdul a ranta idan sanadin auren Nan suka rabu tasan Zata shiga mummunan hali fiyeda lokutan baya sbd matsayin Dr Abdul a ranta jinsa take yafi Mata duk wata soyayyar datake abaya,

Kaunarsa takeyi sosai cikin ranta tana jinsa tamkar wani jininta,
Tasha gwada yimasa kallon wani bangare na rayuwarta sbd mahimmancin mutuncin dasuke da juna.

Umma yaganah, Neesah,anty Hafsat da Safnah ne suka taru suka ringa azalzala Mata soyayyarsa da nacin nusar da ita irin yanda yake Sonta.

Tun tana jin Al'amarin wani iri sbd Bata taba tunani ko kawo kwatancin soyayya harda aure zai shiga tsakaninta da Dr Abdul dinba har tazo nacinsu da kulawarsa daya soyayyarsa da yanzu yagama bayyanar Mata suka sauya matsayi da kaunarsa cikin ranta zuwa tsaftatacciyar soyayya Mai nutsuwa.
##MAMUH#
#RIBA BIYU
#AA MAJEED ABBI/AYSHATOUH INAYAH




_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya👇
07040727902

MTN card👇
09134848107
[10/25, 5:26 PM] +234 813 060 4664: *_25_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Ganin hankalinta ya kwanta akan auran Dr Abdul din sai kowa yaqara bada himma gurin qarfafa Mata gwiwa da sake kwantar Mata da Al'amarin cikin zuciyarta,

Bata sake sakankancewa ta budewa Dr Abdulsamad zuciyarta ba Saida Abbinta ya nuna Mata goyan bayansa akan auren Abdulsamad
Dan haka ta budewa Dr Abdul dukkanin zuciyarta ta karba soyayyarsa.


Abdulsamad tamkar a mafarki yakejin rayuwarsa yanzu dazai mallaki Inayah amatsayin matarsa halak malak batareda shamakin kowaba.,

Sosai kowa ke mamakin yanda duk yabi ya kasa sukuni ya rude Yana bayyanarda farin cikinsa koina.

Tamkar wani zautacce yakomawa Inayah soyayya yake nuna Mata kamar ba Dr Abdul din data saniba tuntuni.

Ita tausayinsama takeji Mai qarfi dayake qarawa soyayyarsa girma cikin ranta sbd Batasan haka yake tsananin sontaba da bazata taba tsayawa kula kowaba da tuni ta amince dashi anyi aurensu.

Mahaifiyar Abdulsamad kam sosai take qaunar Inayah sbd yanda 'danta ke tsananin sonta,
Da farko hankalinta yaso tashi sbd tunanin Bazaa bawa Abdul dinta auren Inayah ba duba da matsayinsu na wainda sukafi na Abdulsamad din kudi sosai sai gashi anyi halin girma anbasa aurenta Dan haka take kaunar Inayah har ranta duk da iyakacinsu waya haryanzu Allah Bai saka sun hadu a zahiri ba wata kila sai lokacin bikin Auren.


***Ansaka lokacin bikin Wata biyu masu zuwa Dan haka ko wannan karon su umma yaganah da Anty Hafsat da wuri suka fara shirya 'yarsu Inayah tako wane fanni.

Gyaranta akeyi sosai Dan kuwa Abbi ya sakar musu kudi suna yanda suke so dasu gurin harkar shirye shiryen bikin.

Wannan karon baiyi wani gayyataba sosai sbd kaucewa hayaniya albarka auren akeso ba taronba,
CM ne ma dai dayafi A MAJEED din shiga mutane sosai ya dauka nauyin gayyatar ta hanyar aikawa manyan mutanen dasuke taredasu special invitations na auren.

Anty Hafsat ta haukace tsima Inayah kawai takeyi tako Ina da abubuwa masu kyau da inganci nasu na manyan mata.

Umma yaganah Kuma masu gyaran jiki takuma sakawa aka kawo matasu daga maiduguri harma da 'yan uwanta biyu dasuka zo bikin auren Dan haka tako Ina families din guda uku nasu na A MAJEEDs,da iyalan gidan CM saina dangin ango dasuke Adamwa hidimar biki akeyi gadan gadan ta kowane bangare.

Inayah tana cikin wani irin farin ciki Mara misali sbd jikinta da dukkanin imaninta yabata wannan karon Zata auru Inshallah bazaa fasa aurentaba Dan haka taketa Jin farin cikin igiyoyin auren Abdulsamad dintane zasu hau kanta bana kowaba.

Shikan oga Dr

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login