Showing 15001 words to 18000 words out of 55760 words
Mai zuwa da ciwon Mara Dan haka hankalinsa yayi matuqar tashi musamman wata na biyu da abin zai sake zuwa saiyafi na farkon sbd na farkon Bata wani wahalaba gashi umma yagana ma Bata tsaya fada masa ko meneneba kawai dai ya dauka zazzabine tayi ta Kuma warke,
Amma Wannan watan dayaga yanda take zuba amai tana kukan ciwon Mara hankalinsa tashi yayi damuwa sosai kan fuskarsa.
Asibiti ya dauketa suka kaita sai acan likita ke masa bayanin menene ciwon,
Da farko Bai Gama ganewaba sai daga baya Umma yaganah tasake masa budadden bayani akan jinin haila ne Inayar tafara.
Tsit yayi Yana kallon kofa da fararen idanuwansa zuciyarsa na Dan yin nauyi sbd wani matakin girman ne Inayah takuma hawa yanzu tarbiyarta da kula da ita zaifi hatsari.,
Shi gabaki dayama Banda Umma yaganah tai masa bayani baiwani San yayane Mata ke wannan al'amarin,
Sam bayada sani ko kadan akan Mata da yanda suke su irin wannna din duk kuwa da yanada ilimin addininsa daidai gwargwadonsa Amma Sam baida sani anan, a ilimance a al'adance a rayuwance ma Dan haka Koda suka dawo gida gurin aiki yakoma
dazai dawo yazo Mata dasu pads daga gurin aikinsa,
Dazai siya dinma Dole cikin ma'aikatansu Mata wata ta zabar masu masu kyan ya siya yazo dasu yabawa Umma yaganah,
Su panties Bai siyaba sbd yasan koyaushe cikin siya Mata undies sababbi yake sbd kiyayewa da tsaftarta.
Tun daga Wannan lokacin duk wata haka ake fama da ita har aka samu ta saba ta iya danne ciwonta idan lokacin period din yayi tadawo ma bamai sanin lokaci yyai tayi ta gamawarta sabanin farkon da duk wata Abbin yasan lokacinda takeyi sbd yanayinta da wuyar datake Sha.
********
Shekara daya da Gama masters dinsa komai nasu yagama sauyawa tako Ina,
shekaru sun qaru sun fara zama manyanci,
Arziki ya fara zaunuwa ta hannu ta banki,
Hakama rayuwa ta sake budewa tako wane fannin sbd tuni yabar mall a asalin kamfanin yake aiki kuma a babban matsayi yafara zama sbd qualification dinsa da zurfin Aiki da iliminsa dayakeda.
Da farko sosai Yaso samun matsala sbd Yan hassadar zuwansa da finsu matsayi da yayi
Hakan ya haifar masa da matsala sosai har yaji yafara gajiya da gurin aikin musamman sbd bayason Al'amarin damuwa da tashin hankali.
Ta wani bangaren yanata samun invitation na offern aiki daga guraren dayayita neman aiki dasu tun wancan lokacin
Yanzu sai babban matsayi Mai kyau suke masa tayi Amma dai sbd halacci ya zabi ya zauna Nan din Amma al'amarin Yana neman gagara.
A gida sbd lokaci girma sosai dayazo masa yasa yanzu akwai qarin ganin girman juna sosai fiyeda da tsakaninsa da Umma yaganah sbd yanzu yafara wuce matsayin matashi Dan haka ganin girman tsakaninsu yafara qaruwa Amma dai ita sakewa har lokacin akwaita sosai tsakaninsu Bata sauyaba.
Inayah kuwa haryanzu shaquwarta da abbinta saima abinda ya qaru sbd yanzu ma kusan itace ke gyara bagarensa duk da sunada Mai aiki dake zuwa tayi aiki Takoma gida sbd Abbin dayace Umma yaganah tasa asamo sbd Inayah karatu take bayason tana tsayawa aiki,
Hakama itama Umma yaganar yakamata ta huta a rayuwa yanzu tunda an bautu iya bautuwa yanzu hutu yazo ahuta tunda Allah yakawo damar.
Daga Umma yaganah sai Inayah ne kawai suka San abinda yakeso dakuma abinda yafi buqata Dan haka acikin akwai Mai aikin gidan har lokacin Umma ce kawai ke girkin dayake ci hakama Inayah ce yanzu ta karbar Mata gyaran palonsa zuwa dakinsa duk da dama can bedroom dinsa ne kawai Umma yaganah bata shiga Inayah ce kawai Mai shiga shima Idan bayanan datai girma yanzu.
Yanzu yanada arzikin siyan mota Amma har lokacin Bai siyaba sbd yanke shawarar komawa Lagos a reshensu na aiki dake can sbd Nan din fitinar tafara yawa yadda abubuwan aikin nan din sun fara rushewa Dan kuwa maha'intar kamfanin sun fidda zalamarsu a fili take komai yafara rushewa.
Yana ganin hakan ya rubuta takardar aje aiki yafara aikawa Nuradden dake Lagos ta email.
Da farko hankalin Nuradden yatashi da barin aikin na A Majeed sbd sun riga dama suna kokarin rasa reshensu na can Idan A Majeed yabar aiki zasuyi Rashin babban gifted Dan haka da wuri ya sanar fa mahaifinsa dake Singapore halinda ake ciki.
***Kwana biyu Yana hutawa sosai a gida cikin iyalinsa hankali kwance musamman daya kasance dama baya wani yawo sosai daga aiki sai gida sai wasu guraren qalilan sai Kuma makarantar Inayah da har lokacin Yana zuwa kaita.
Ganin Abbinta gida kwana biyu kuwa Inayah sai takejin Dadi sosai sbd Dana aikinsa Yana riqesa sosai Lokacin Kuma yake gida itama Kuma makarantar yamma Dan gaka yawanci sai dare suke samun lokacin zama dashi.
Satinsa biyu a gida Yana hutu ana ukun ya shirya zuwa wani aikin da akeson daukarsa saiga sakon Amb Ibrahim Dikko mahaifin Nuradden daga Singapore.
Sabuwar offer ce na aiki dasu a Singapore.
Kai tsaye farko dakatar da offer din yayi sbd bayajin zai iya barin qasar yaje wata qasar aiki yabarsu Inayah anan su kadai Dan haka Kai tsaye bayan kwana biyu yayi rejecting offer din.
Wancan aikin ya karba harya fara Amma Nuradden suka kasa barinsa sunata bibiyarsa.
Sake sabon nazari yayi akan aikin sai kawai ya amince bayan an amince masa da zuwa dawu Inayah Amma Lagos zasu zauna tsawon lokaci kafin.
Lokaci qanqani suka dauka kafin suka tattara suka koma Lagos gabaki daya acan suka dasa sabuwar rayuwa.
Da farko sunsha wahalar rayuwar garin kafin suka saba saidai kam makaranta da Dole da qarfin hali Umma yagana ce aka koyawa mota Kuma Allah yasa ta iya tunda ba wani manyata tayiba dan haka ya siya musu mota itace take kaita tana daukota,
Koda minti daya Bata taba Bari tayi lattin Isa makarantar daukan Inayah ba sbd maimaicin dokar hakan daga gurin mahaifinta.
Aiki yamasa yawa sosai yanzu dan haka sosai baya wani zama,
Haha tafiye tafiyen garuruwa harma da 'yan wasu qasashen daya fara sbd aikin nasa shiyasa yanzu Dole tarbiyar Inayah tadawo hannun Umma yaganah gaba daya saidai koyaushe cikin Kira da maimaita akula yake nanata musu.
Inayah na kammala secondary school bada jimawaba ya tattarasu suka koma Singapore sbd hankalinsa daya rabu biyu.
Rayuwarsu a Hougang Singapore wata sabuwar wayayyar rayuwace ta hutu da Jin Dadi sbd arziki daya zaunawa Abbin.
Watansu tara a Hougang suka dawo cikin asalin Singapore Singapore,
Bayan aikin kamfani wani karatu yasake jonawa cikin shekara biyu ya kammala tareda samun wani babban aiki a Australia suka bar Singapore.
Bayan barowarsa Nigeria ko shekara hudu Bai gama rufawaba kamfanin gabaki ya rushe akai gwanjonsa Wanda shine tashin farko ya siye kamfanin da malls malls din na can Nigeria harma Dana Singapore ya damqawa Nuradden da mahaifinsa Wanda manyanci yasa shima yace abawa Nuradden din yaci gaba da kularwa da A Majeed din dasu tunda yanzu komai ya zama mallakinsa ne
Amma hallacinsa yasa yabar kamfanin a hannunsu suci gaba da kulawa.
Sun sallami dukkanin ma'aikatan dasuke zargi da ha'incin Daya kaisu ga rushewa suka rasa komai aka Kuma zuba sabbin ma'aikata bayan ansake gyara companies din da malls malls dinsu.
*_BAYAN WASU SHEKARU....._*
#MAMUH#
#ZAFAFABIYAR#
#A.A MAJEED#
#INAYAH#
#AYSHATOUH#
#RIBABIYU#
*_Dan samun cigaban labarin follow me @Mamuhgee at arewabooks_*
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
_BREAKDOWN OF ZAFAFA BIYAR VVIP SINGLE PAID BOOK_
_4 BOOKS 4500_
_3 BOOKS : 3500_
_2 BOOKS : 2500_
_1 BOOK: 1500_
YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902
IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107
[10/15, 4:03 PM] Mariyamah: *_Mamuhgee 9_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
_A.A MAJEED's_
_659 Melrose victoria mosmon,_
_SYDNEY,AUSTRALIA._
A hankali ta qarasa zare navy blue turkian doguwar rigar dake jikinta ta jefar kan brown Chiara Andreatti sofa dake babban bedroom din nata.
Kyakkawar fuskarta datai ja ta Dan kalla ta cikin mirror tana Dan yamutsa fuska kafin takai hannunta akan fuskar ta shafa gefen damarta da wani Dan qaramin pimple ya fito mata qwaya daya tal daya hanata fita koina tun shekaran jiya.
Ajiyar zuciya ta sauke tareda zare fararen undies dake jikinta ta nufi toilet dasu a hannu tana shige ta jefa cikin laundry ball dake gurin ta nufi inda brushes dinta suke ta dauka daya tareda diban Toothpaste tafara brush tana kallon fuskarta jikin mirror tana sake Jin damuwar kurjin fuskar tata,
Tana gamawa jacuzzi ta nufi ta shige tareda sakarwa kanta ruwan dumi tana Dan lumshe ido sbd damuwarta ta Dan saketa.
Mintuna qalilan ta dauka tana wankan kafin ta fito daure da brown towel kanta ma daure da brown towel din qarami
fatar jikin qyalli takeyi tana bayyanarda tsananin hutu,Jin Dadi da tsadaddiyar kular datake samu ta hanyar amfani da skin products masu tsananin kyau da tsada.
Kai tsaye gaban madubin dakinta ta nufa ta zauna tareda kunna hand dryer tafara busar da gashin kanta data kunce bobmarley braids (kitso/kalban Bob Marley) jiya da yamma.
Doguwar malaysian riga ta saka har qasa Mara nauyi ash kala ta zira Burberry slippers ta fito daga bedroom din nata hannunta riqeda wayarta tana kokarin saka Kira.
Qamshin turarenta na Versace(Bright crystal) ne yafara bayyanarda fitowarta daga bedroom dinta zuwa babban yalwataccen palon gidan dake.
Zubbi Mai aikinsu tun a Singapore Yar Amana wadda Alhaji Nuradden Aminin Abbi ya Aiko musu daga Nigeria itace ta dago daga kunna qatuwar Humidifier dake palon bayan tagama gyare koina na gidan ta tsaftace ta kalli hanyar da Inayah ta fito tana kallon kyakkawar fuskarta ta saki dan gajeran murmushi tana cewa"
Good morning Inayah.
Kallonta Inayah tayi da fararen idanuwanta tana amsawa Kai tsaye da cewa"
Morning zubbi.
Hanyar bedroom din Umma yaganah ta kalla tana cewa"
Umma yaganah ta tashi?
Yes ma" zubbi tafada tana qarasowa Dan shiryawa Inayah breakfast dinta kan dining ta nufi babban Australian kitchen dinsu ta shige.
Kai tsaye ta murda kofar dakin ta shige tana qaramar sallama da cewa"
Umma yaganah yauma bazan fita koinaba fuskana ta sake kumbura da ja...
Zaune umman take kan wata tattausar sofa kalar ash na komai dakin dayake ash Mai haske,
Farin glass ne a idonta tana karanta wani Arabic hisnul Muslim
Jikinta sanyeda doguwar rigar plain cotton Swiss Mai tsada light pink.
Dagowa tayi tana kallon Inayah cikin kulawa da tsananin bayyananniyar kaunar Inayah data Dade da shiga jininta ta ajiye littafin gefe kan table tareda maida hankalinta kan Inayan gaba daya tace"
Yau kam saikin fita Inayah,
Meyesa kike Wasa da karatunki ne yanzu?
So kike abbinki ya dawo yasan kwana biyu bakya zuwa makaranta?
Karatun likitanci fa kikeyi karki manta,
Ahakan zakiyi wani abin arziki kullum cikin shiriritar Gayu ya hanaki Wannan da wancan?
Akan pimples bazakice kindaina fitaba sai kin warke Dan haka
Ki Gama breakfast kije kiyi Shirin zuwa makaranta.
Zama Inayah tayi gefen umman tareda yamutsa fuska tana kokarin yin magana umman ta katseta tana cewa"
Abbinki kinfi kowa sanin fadan bacin ran dazai nuna Idan yasan kina skipping ranakun zuwa school,
Banason bacin ransa akan Rashin dalilinki.
Kai Umma yaganah Abbi fa idan yaji abinda ya hanani zuwa bazaiyi fada ba.
Inayah please Mana,
Ki daure ki cire Rashin son makaranta a ranki bayan kinsan Abbinki yanada riqaqqen raayi akan son karatunki.
Bari sai Akira likita tazo ta sake duba fuskar taki,ok?
Gyada Kai tayi tareda miqewa tana kokarin barin dakin tace"
Good morning,ban gaishekiba Dana shigo.
Wani qayataccen murmushi Umma yaganah ta sake tana kallon fatar wuyan Inayar dake bayyane tana sheqi sbd yanayin rigarta cikin Yar dariya tace"
Barkanki da safiya kema Inayah Majeed.
waiwayowa tayi ta kalli Umman tana Yar murmushi sbd friends dinta ne masu Kiranta Kai tsaye hakan Amma ko umman sau tari hakan take kiranta itama.
Dining ta nufa ta zauna hankali kwance Tasha black tea da toasted bread biyu da kwai ta tashi tabar gurin ta nufi dakinta tana sake Danna Kiran Mahaifinta dataketa Kira tun dazu takasa samunsa sai yanzu Kiran yashiga.
***Zaune yake a palon madaidaicin duplex dinsa dake Singapore tareda CM Nuradden Aminin huldodinsa suna meeting akan aikin da zaaiwa sabon kamfaninsa da aka bude reshensa a portharcourt Nigeria.
Kan couch Mai zaman mutum biyu yake zaune sanyeda sky blue English kaftans masu tsananin taushi da tsadar dake bayyane.
Wayarsa dake gefensa ajiye ya waiwaya a natse ya kalla ganin hasken data kawo alamar shigowar Kira ko saqo.,
Fararen idanuwansa yafara Dan juyowa ya kalla CM Nuradden dasu Ahankali cikin nutsuwa yace"
One minute.
Hannunsa yakai ya dauki wayar kai tsaye tareda kaiwa kunnensa cikin nutsuwar murya da Allah yayi masa Mai tattareda kamewa saidai kasancewar 'yarsa ce tilo datafi masa kowa da komai daya mallaka a duniya ahakan muryar tasa a bayyane take da kauna da kulawa
Kai tsaye ya furta"
Yes,INAYAH.
wata ajiyar zuciya ta sake tana zama bakin gadon dakinta cikin tsananin kauna da kewan mahaifin nata tace"
Good morning Abbi.
Ahankali ya dago fararen idanuwansa ya kalli agogon _Patek Philippe_ dake daure a hannunsu ya maida idanuwanta ya dan kalli CM Nuradden
yasan Inayah zataci lokacin magana dashi sosai Dan Kuma CM flight zaibi yakoma Nigeria zuwa 11 dan haka Kai tsaye cikin nutsuwa da kulawa yace"
Morning Inayah,
Kintashi lfy?
Lfy kalau,
Abbi haryanzu kana Singapore?
Yaya aiki?
When are you coming back?
Cikin nutsuwa ya amsa ta da cewa"
Inayah Ina magana da CM yanzu,
Anjima I will you back,ok?
Ki kula,Ki gaida Umma yaganah.
Ok Abbi sai anjima.
I miss you.
Kashe wayar yayi tareda ajewa gefensa kafin ya dago ya kalli CM dake jiransa dan harya fara shiga yanayi na damuwa sbd sanin wayar Inayah ga mahaifin nata sai tasa a rasa meetings masu mahimmanci dazasu kawo manyan dukiya da dama Dan ansaba
Indai akan Inayah ne AA MAJEED nada raunin duba al'amura da dama masu mahimmanci Kuma hakn wani al'amarine da kusan duk wnada yake hulda ko mu'amala dashi yasani,
'yarsa Inayah itace Rauninsa da kowa yakasa sani duniya akansa sai Aminin nasa Cm Nuradden sai Kuma Umma yaganah sbd sune sukeda cikakkiyar shaidar yanda 'yarsa take a Ransa fiyeda duk abinda yakeda,
Hakama 'yarsa Inayar itace qarfin Rayuwarsa,
Duk Wannan arzikin da dukiya Mai yawan daya Tara basukai masa mahimmancin farin cikin yarsa na wuni daya ba,
Inayah da kanta tasan itace hasken rayuwar Mahaifinta kaman yanda itama kowa yasanta yasan Mahaifinta shine abinda Bata iya hada girma da tsananin kaunarsa da komai,
Shine Abbinta,shine mahaifi Uba Kuma mahaifi UWA.
Numfashi CM ya sauke ya sauke yana kallon A MAJEED din sbd ya dauka zaman jiran yagama wayar ya samesa ne saigashi Allah yasa yau A MAJEED din ya taqaita.
A MAJEED ya fahimci zullumin da CM ya shiga dan haka ya taqaita wayar
Cikin nutsuwa ya dauki takardun da zai saka hannu akai yafara signing Yana cewa"
Sauran takardun na AIA sa hannun Inayah zaa saka a takardun Amma ba yanzuba saita kammala karatunta tukuna so agama aikin kawai kafin lokacin.
Alright Inshallah.
Sai 10 suka rabu da CM bayan daya daga cikin ma'aikatansu yakaisa airport ya wuce.
11:30 shima yabi jirgi tareda secretary dinsa suka bar Singapore zuwa Australia.
****Badan tasoba haka tayi Shirin makaranta ta fice daga gidan zuwa school bayan tayi waya da qawarta da itama duk sunne ba wani son karatun sukeba sunfi ganewa Gayu da rayuwa kawai irin ta 'yayan gata masu abin duniya.
Duk da Bata wani son karatun sosai bashi yasaka Bata maida hankali ga karatunba idan taje,
Wuyarta dama dai taje din sbd idan taje sosai take maida hankali ga karatun Kuma Allah ya taimaketa tanada qwaqwalwar daukan karatun sosai Dan ahakan Bata taba failing ba
Koyaushe tana samun grades masu kyau,
Kawai dai Allah Bai saka Mata wani son karatun bane
Abinda Allah yasaka Mata so shine Tanada shaawar yin aure kawai sbd ta daina zuwa makaranta tayi rayuwarta yanda taga dama daga shopping sai zuwa beauty parlor dasu spa sai yawan qasashen dataga dama.,
Ko yanzu kusan rayuwarta hakanne,
Batada wani aikin bayan yawon shoppings da zuwa su spa day guraren gyaran jiki sbd Bata hada gyaran jikinta da komaiba Wanda kusan hakanne yasa koyaushe fatarta da jikinta koina yake sheqin hutu da lafiya cikakkiya da zallar gyara na musamman,
Yawon qasashene Bata wani Yi sbd duk qasashen datake zuwa tareda Abbin take zuwa kokuma zuwa umrah ko Hajj tareda Umma yaganah Dan haka Bata wani samu tana yawon yanda takeso sbd haryanzu dasuka samu sauyin rayuwa mai tsananin nisa Abbinta baya barinta tana yawo yanda takeso duk da kuwa ba wani zama yakeyiba Amma dokarsa na aiki a gidan duk inda yake kuwa.
Hakan yasa takeson aure fiyeda karatu musamman ma auren irin na wayayye irinta dazai barta tayi rayuwar datakeso ta Rashin takura da damuwa kawai suyita soyayya suna shaqatawa sbd love na cikin abubuwan datake yiwa kanta shaawar samun kanta aciki hakanne ma yasa bayan abbinta da yaganah to Babu Wanda takeso sama da saurayinta Zaid.
Soyayyar Zaid tayi wani irin nisa a ranta Kaman yanda shima yake tsananin son Inayan,
Kusan yanayin rayuwarsu daya sbd shima iyayensa masu arzikine sosai Amma suna Nigeria Dan asalin portharcourt ne karatu yake a qasar,
Kaman yanda take wayayyar Yar gata girman turai hakan yake shima sbd tun Yana yaro shima kusan a qasahen turawan ya tashi tareda iyayensa sai daga baya Suka koma gida sukabarsa Yana karatu.
Dan haka da rayuwar Zaid tayi daidai da tata sai soyayyarsu takeda wani irin qarfi da shaquwa.
Abbinta yasan raayinta na Rashin maida hankali kan karatu yakuma san aurene takeso fiyeda karatun Amma yaqi nuna Mata ya sanin sbd karta sake samun damar nuna batason karatun,
Shikuma raayinsane riqaqqe dakuma buri akan bazatai mata aureba saita Gama karatun.
##MAMUH#
#ZAFAFABIYAR#
#AA MAJEED#
#AYSHATOUH INAYAH#
#LOVE
#ROMANCE
#MARRIAGE
_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
_BREAKDOWN OF ZAFAFA BIYAR VVIP SINGLE PAID BOOK_
_4 BOOKS 4500_
_3 BOOKS : 3500_
_2 BOOKS : 2500_
_1 BOOK: 1500_
YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902
IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107
[10/15, 4:03 PM] Mariyamah: *_10_*
*_Arewabook@Mamuhgee_*
Tana isowa gidan tun a compound tasan Abbi yadawo gida sbd ganin sabuwar motarsa da tunda sukazo take a gefe rufe ruf Amma gatanan a fake gefe da alama da ita aka daukosa daga airport.
Kofar palonsu ta dosa tana warware nadin qaramin gyalen dake kanta tun daga hanya
Tana isa ta bude kofar Kai tsaye ta shige.
Bakowa a palon sai Qamshin RoseNight da Sanyin AC daya Gama cike palon
Saikuma qatuwar tv dake aiki ba murya sosai.
Su zubbi da Salimat tuni suka Gama aikinsu suka nufi bangarensu tunda Mai gidan na gari Dan haka idan ba aiki ba Babu abinda zai Kuma shigowa dasu saikuma idan kiransu akai.
Dakinta ta nufa direct ta tube tafada toilet tayi wanka ta fito daureda towel.
Kiran Dr ne yashigo wayarta da sauri sauri ta dauka tace Masa"
I'm kinda busy
I will call you.
Aje wayar tayi tareda nufar gaban madubi ta shafa Neutrogena oil dinta ta fesa spray kawai ta koma gurin kayanta ta saka wata chiffon wide neck gown Mara nauyi ta ziro slippers ta fito ko wayarta Bata daukoba.
Kai tsaye hanyar