Showing 3001 words to 6000 words out of 55760 words
Bata konewa shiyasa kusan koina tagama kokkonewa hannuwa da qafafu
Har fuska ma wani lokacin idan Mai yayi watsi.
Ba laifi yanzu basa neman komai a gurin kowa Wanda dai zasuci saidai Dan abinda baa rasaba.
Inna ma tuni dole suke komai tare sbd aikin yanawa hadizan yawa ga koko dasuke hadawa dashi yanzu da safe,
Da Rana ma yanzu ba awarar kawai sukeba harda dankalin hausa da wainar rogo.
Dole dai yanzu innace take aikin kosai da kokon safe ita Kuma tana awarar da sauransu da Rana sbd dukkaninsu aikin yayi mutsu tsananin wuya musamman tunda aikin wuta ne,
Mama ba cikakkiyar lafiyayyaceba shiyasa Basu taba barin ta shiga sana'ar ba,
Tunda mahaifinsu ya rasu haka take yau lafiya gobe ciwo,
Hawan jini da ciwon sugar ke tsananin damunta Dan haka lallabawa kawai takeyi tana rayuwar.
Ahaka hadiza ta samu ta sanya Abdul a makarantar gwamnati yafara zuwa
Kullum ita ke rakasa da qafa tadawo
Idan antashi haka take komawa ta dawo dashi sbd akwai Dan nisa sosai.
Hutun farko na makarantar tabi taqarasa hargitsewa sbd yanda kullum saita kaisa ta daukosa ga lattin fara sanaarta datakeyi Idan taje daukosa,
Dole Inna ce take fara yimata kafin ta dawo daukosa ganin mutane sun fara janyewa ansamu wata Yar baqin cikin ta fara sana'ar a makwaftansu.
Ganin Inna ma wahalar duniya tafara sakota gaba sbd ayyukan sun mata yawa ko baccin arziki bata samu sosai dole mama ta ringa karba tanayi sbd Suma su ringa samun sassaauci tunda Allah yasa yanzu da aikin suka dogara kacokam.
Tsawon lokaci rayuwar tana yanda take garesu ba wani dogon sauyi saima ciwo daya kwantar da mama Dan haka suka sake zagewa da Sanaa ga Inna itama karfinta yayi qasa,
Ga Abdul yanzu karatun nasa yafara nisa tunda Yana aji biyu yanzu.
Ita kanta lafiyarta wani lokacin qaranci take mata sbd ciwon mararta har lokacin Yana taso mata akai akai gashi wani babban ikon Allah dayake kamata shine tunda tayi Bari lokacin rasuwar Salisu har yau Bata taba yin wani al'adar ba,
Tayiwa Inna maganar innar tace mata wasu matan na hakan musamman Idan suntaba samun matsala ta Bari Dan haka ko jinin Al'adar zai koma ya ringa zuwa daidai sai tayi wani auren kilan.
Da Wannan zancen ta tattara maganar Rashin zuwan Al'adar ta watsar tafara neman wata sana'ar sbd wannan din ta daina tafiya sosai sbd kusan anguwar ganin ana samu duk sun fara sana'ar shiyasa yanzu ba mutane sosai.
Ganin wata sana'ar taki samuwane
Duk Wanda tafara Bata karbuwa gashi jarin nata tafiya gurin hidimar gidan yasa dole tafara zuwa aiki wani gida acan GRA da mama Indo qanwar Inna ta Samar mata.
Fara aikinta sai rayuwa kuwa ta sauya musu Dan yanzu da albashin suke komai.
Bata wani jimaba da fara aikin saigashi hajiyar suka tattara suka bar qasar itada 'yayanta dole tadawo zaman gida ba wani aikin.
Jin bazata iya zaman ba aikin komaiba yasa takuma zuwa tasamu mama inda dake shirye shiryen tafiya Lagos itama aikin Sanaa tace takuma samar mata wani aikin.
"Babu wani gidan aiki Idan ba Lagos Zaki shirya ki bini ba kya ringa musu aike daga can kokuma abaki Aron kudi ki bar musu Idan munje can kya ringa biyana da kudin aikinki??"
Haka mama indo ta sanar mata Dan haka batada wani sauran zabi bayan amincewarta sbd suna cikin tsananin halin nema gskia.
Ko data sanar dasu Inna farko sunso hanawa Amma ganin yanda mama Indo tai musu bayanin aikine kawai a wani babban restaurant na masu kudi da aka bude Kuma sunada masauki Mai kyau da restaurant din suka tanadarwa ma'aikatansu a tsaftace cikin kwanciyar hankali.
Hakan yasa suka amince tareda bawa mama Indon Amanar kula da hadizar duk da ba yarinya bace.
Kudi sosai hadiza ta karba gurin mama Indo ta siyawa su mama abinci Mai Dan yawa tareda dinkawa Abdul uniforms har kala biyu da sabbin takarman zuwa makaranta da slippers harma da sababbin litattafai.
Sauran kudin taje takuma siyo musu sabulan wanka da omon wanki dasu lalle da kanwar dazasu ringa saidawa daga zaune cikin gida ta damqawa Inna sauran kudaden a hannunta.
Daga Yaya Umar har Yaya kabiru babu Wanda yayi yunqurin hanata tafiya sbd su yanzu siyasar gabansu ta ishesu shi Yaya kabiru harda tattara aikinsa yayi ya ajiye sbd ganin sun fara samu ba laifi.
_LAGOS_
Da farko tafara Shan wuyar rayuwar garin data aikin dasukeyi sbd wani sabon hotel ne da aka bude aka daukesu aikin Dan haka wainda basajin turanci bangaren restaurant aka ajesu gurin harkar abinci.,
Farko ganin baa bacci kwana akeyi aiki yasa tafarajin zuciyarta tayi sanyi da rayuwar,
Amma ana Bata albashin farko taga irin yawan kudin sai kawai ta tattara kyuya da damuwar komai ta watsar ta zage da aiki gadan gadan.
Kasancewarta mai tsananin kokarin aiki da Amana da ladabi yasa cikin wainda aka daukesu tare watansu biyu aka qara mata matsayi tareda dauketa daga kitchen aka maida bangaren tsafta,
Ma'ana bangaren masu Kai abinci dakunan manyan Idan sunyi odar abinci Dan haka kusan yanzu hutawa takeyi sosai sai anyi odar abinci taje takai.
Gidan dasuke cikin kudinsu na albashi ake Dan tsakura duk wata ana biyan haya Dan haka hankalinta ya kwanta sosai gashi ahakan duk wata take turawa su Inna Yan canji ta hanyar Mai pos din kusada gidan nasu data baro.
Kwanciyar hankali da hutu da Kuma nutsuwar datake samu yasa tafara sauyawa sosai sbd abinci Mai kyau na hotel din sukeci,
Nama da kayan Dadi kala kala haka suke ci dan haka tafara sauyawa sosai,
Mama indo dai ita a bangaren abinci take har lokacin Kuma babu ranar sauyata daga gurin sbd yanda ta iya wata irin lallausan sakwara da Amala,Eba,semo
duka dai kalolin swallow babu Wanda mama Indo Bata qwareba shiyasa saka barta agurin Kuma itama ahakan ba qananun kudi take samuba sbd yanda suke tsananin son aikinta.
Hutu da nutsuwar da kwanciyar hankalin data samu tareda abinci mai kyau yasa tafara sauyawa jikinta yafara budewa da wata irin kiba,
Hasken fatarta daya jima da dafewa saigashi yafara washewa Yana dawowa,
Da farko tayi mamakin hakan Amma ganin rayuwar nutsuwar datake yasa Bata damuba saima Jin dadin hakan datai sbd tasan inshallah yanzu zata iya samun miji tayi aure tunda tayi kyan gani.
Ba laifi cikin qanqanin lokaci tasan mutane dakuma Yan tsirarrakun areas da streets sbd tana fita Yar siyayyarta
Yanzu har maganin gargajiya take siya daga nan ta aikawa mama da koyaushe take fama da jiki duk da ana cemata taji sauki din saidai yanayin muryar maman yasa ta fahimci suna fadane kawai Dan kwantar mata da hankali.
Hakama Abdul tana Dan yimasa siyayya idan zatai Aiken ta aika musu.
Tana gab da cike shekara a sabuwar rayuwarta ta Lagos ta fahimci wani babban alamari Mai tsananin ban tsoro da firgitarwa a tareda ita.
Bata tabbatarba Dan haka ta saka lokacin zuwa wani qaramin asibiti dake kusada anguwar dasuke,
Ana albashi da kwana biyu ta kwasa ta nufi asibiti a dubata sbd tabbas Idan tanaji Kuma tana fahimtar daidai motsin ciki takeji a cikinta Wanda girman daya fara yasa ta dauka kibar datayi ce Kuma hakan Wainda take taredasu suke fada tayi qiba tayi tumbi.
To me take Shirin ji ne?
Tsakanin kwanaki Biyar zuwa yanzu take Jin motsin sosai da juyi Wanda ta tabbarda cikin haihuwane kawai yake Wannan motsin.
#MAMUH#
#LOVE#
#ROMANCE#
#ZAFAFABIYAR#
[10/15, 3:51 PM] Mariyamah: *_INAYAH_*
_Mamuhgee_
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
3
InnalillahiWainna ilayhirrajiun"
Shine abinda zuciyarta tafada lokacinda take zaune cikin jerin layin ganin likita data buga sammakon zuwa.
Gyara zamanta tayi a karo na Bata lissafi sbd gabaki daya takasa nutsuwa ta aje jikinta guri daya,
A tsananin matse take datasan asalin Menene ajikinta,
Shin wani ciwon ne yasameta?
kokuwa wata lalurarce Wannan da batasan da itaba?
Itadai a yanzu koma menene gata agaban dakin ganin likita Allah yasa taji abinda zuciyarta zata iya dauka sbd koma wane irin ciwone atareda ita Bata tunanin Mai saukine sbd girman motsin datake ji.
Dago Kai tayi ta Dan bude manyan fararen idanuwanta dasukai jajir da tsantsar damuwa da fargabar fake gamutse cikin ranta da kanta
Ta kalla inyamurar data fito daga ganin likitar wadda daga ita mutum biyune ya rage layin yazo kanta.
Bin bayan wadda ta shiga tayi harta shige kafin ta dauke kanta tana sunkuyar da kanta gefe tareda rufe idanuwanta tana sake Jin motsin da akeyi acikin cikin nata.
Haka ta muskuta tana cigaba da zaman jira zuciyarta na cigaba da cika ta koina da damuwa da fargabar abinda zaije yadawo har tsawon mintuna ashirin kafin aka kirata ta miqe tareda gyara zaman qaramar Jakarta dake rataye kafadarta ta nufi kofar dakin ganin likitan tashige tana kokarin samarwa kanta nutsuwa sbd tayiwa likita bayanin yanayinta a matse.
Dr Adebayo A Aziz tagani rubuce a gaban farar Lab coat din dake jikinsa
Ta qaraso ta zauna jiki a sanyaye sbd taso tasamu likita Mai Jin hausa koda Yar kadan ce sbd tasamu ya fahimci zancenta dakyau hakama itama ta fahimci abinda zai sanar da ita da kyau.
Tanajin dan pidgin dinta data koya a zaman garin Lagos din saidai bazai isheta suyi magana da kyauba Dan haka sai kawai jikinta yakuma sanyi ta gyara zamanta ahankali tana dagowa ta kallesa lokacinda ya bude Baki Yana kallonta Kai tsaye yace"
Yes, what's the problem madam?
Dan rage kallonta akansa tayi cikin sanyin jiki ta bude Baki tana Kai hannu kan cikinta da yayi tauri cikin kwanakin ta nuna masa tana harhada turancin da qyar cikin gwamutsawa tace"
Something is moving inside my here" ta qarasa fada tana nuna masa cikinta da hannuwanta biyu.
Is moving very very much,
But no pains,
No fever,
No anything only the movement inside here.
Idanuwansa ya Dan zuba mata tareda sakin murmushin bayanin nata.
Ya kalli cikin dakyau Yana cewa ta janye hannunta ya gani.
You said no any pains or fever?
Gyada Kai tayi tana kallon fuskarsa.
Rubuce rubuce yayi cikin file dinta kafin ya aje ya miqe tsaye.
Gadon dake dakin ya nuna mata Yana cewa tahau ta janye rigarta ya duba cikin.
Ajiye Jakarta tayi gefe tareda moqewa ta nufi gadon tahau zuciyarta na cigaba da tsalle cikin rudani da fargaba.
Tana janye rigarta tun kafin yakai hannunsa kan cikin idanuwansa suka tabbatar masa da cikine a jikinta Kuma tabbas inshallah zai Kai wata Biyar zuwa shida haka.
Hannu yakai yafara Danna cikin da Dan qarfi Yana examining nata aikuwa saiga cikin Yana sake motsawa.
Kallonta yayi Yana zare Safar hannunsa yace"
Madam ciki wata nawa???
Kallonsa tayi da sauri tana kokarin Jan rigarta ta rufe cikin ta tashi zaune tana Kuma kallonsa Kaman Bata gama fahimtar abinda yafadaba tace"
Eh??
Komawa yayi ya zauna gurin daya tashi Yana kallonta bayan itama tadawo ta zauna yace"
Madma ciki naka wata nawa??
Girgiza Kai tayi tana kokarin Hana kanta shiga firgici sbd zancen nasa buga kirjinta yake.
Ganin halinda take ciki take ya fahimci batasan da cikinba kokuma cikin Bata shirya daukarsaba kokuma ma batada tabbacin na waye acikin mazan datake taredasu dan haka rubuce rubucensa yayi yagama ya kalleta tareda miqa mata takarda yace"
Madam you are pregnant,
I mean kanada ciki zai Kai like 5mnth
Take this kaje kayi scanning ka kawo.
Wata takardar yakuma miqa mata yace"
And this one,test ne go lab zasu dauka blood naka ayi test na ciki da shauransu, then you'll come back on Monday and bring the results to me.
Hannuwanta dake tsananin rawa takai ta karba takardun tareda miqewa tsaye ta fice zuciyarta na wani irin azabar bugawa da nauyin gaske.
Kasa barin asibitin tayi Kai tsaye ta nufi bangaren da ake scanning ta biya ta shiga akayo mata cikin mintuna qalilan saigata da result din ciki a hannu.
Rufewa idanuwanta sukai da wani irin tsananin duhu,
da daddafawa ta samu wata kujerar plastic dake hanyar fita asibitin ta securities ta zube zaune hannuwanta da qafafunta sosai suka dauki wata Mummanan rawa zuciyarta na qafewa da zallar tashin hankalin da Bata taba shigaba ko alokacin mutuwar Salisu.
Takardar dake damqe hannunta ta Kuma dagowa ta kalla kafin takuma budewa hannuwanta na rawa tafara bin rubutun dake ciki daki daki da idanuwanta dake mata zallar yajin radadin Neman hawaye Amma Sam babu alamar zuwansu.
Daya bayan daya take bin kalmomin tana karantawa da 'Dan ilimin bokon datake dashi na iya secondary.
Hawaye ne taji suna ciko idanuwanta take data Gama duba takardar,
Ko ba Dan ta karanta ba Wannan takardar da abinda ke cikinta ya tabbatar mata da zancen likitan sbd Zak irinta wannan bayanin ne na ciki ajikin takardar dasukai scanning tareda Salisu wancan lokacin cikin Abdul.,
Kenan da gaske ta tabbata cikine ajikinta?
Tayaya?
A Ina ya fito tunda tasani Kuma Allahn da yayita shine mafi sanin Bata taba aikata komaiba a duniya da wani da namijin bayan salisunta.
Dama Ace shekarar data gabata ne da saitace cikintane da Salisu ya barta dashi Bai bare ba.... InnalillahiWainna ilayhirrajiun,,
Ni hadiza wane irin Mummanan haline Wannan nashiga Wanda bansan meyake faruwaba.
Sai alokacin tafashe da wani irin Mummanan kukan mawuyacin halin datake ciki
Ga cikin sai sake motsawa yakeyi alamar Yana cikin cikakkiyar koshin lafiyarsa data sanyashi kwanci tsawon shekara biyu sai yanzu daya samu tashi.
Kukan fitar hankali tayi tsawon lokacinda Bata saniba agurin har Saida taji idanuwanta da fuskarta sun kumbura kafin ta iya miqewa ta kama hanyar komawa gida.
Isarta gida Bata Bari kowa ya gantaba ta shige daki ta aje Jakarta ta fito tayi alwala Takoma dakin sallah kawai tayi ta fara rokon Allah mafita tana hawaye
Ahaka ta Gama ta miqe Takoma ta kwanta Bata Kuma fitowaba sai washer gari.
Gurin aikima datazo nokewa kawai taketa faman yi tana kame kame sbd ganin Kamar kowa zai fahimci cikin jikinta Dan haka duk tabi tayita Jin kanta a muzance.
Tana tashi aiki Bata koma gidaba Kai tsaye gurin wani gurin scanning din daban ta nufa takuma yi,
Shima result daya tasamu na akwai ciki.
Wani gurin takuma zuwa Shima duk daya,
Haka tayita yawon guraren scanning ana Bata result daya
Ta tattara tadawo gida hankalinta zuwa lokacin yagama barin jikinta,
Tashin hankali da tsananin tsoro takeji yanzu sbd ta tabbata takuma shaidar kanta Idan har Wannan cikin na haihuwane bana aljanuba to wlh cikin Salisu ne ajikinta Wanda yabarta dashi tunda tasan Bata taba ko tunanin 'da namiji ba bayan rasuwar salisunta.
A daren kwana tayi wani irin kuka da quncin zuciya mai nauyin gaske.
Tayaya zata fuskanci duniya da ciki a jikinta?
Cikin da bai tashi fitowa ya bayyana kansaba sai data baro gaban iyayenta tazo Lagos,
To tace me akan cikin?
Zaa yarda da itane?
Cikin qanqanin lokaci damuwa da kunci sukaiwa rayuwarta mugun baibayi,
Sam tarasa walwala da kwanciyar hankali da nutsuwarta,
Kullum cikin zullumi da tashin hankali take tashi takuma wuni acikinsa sbd ciki dai yanzu gadan gadan fitowa yakeyi Yana girma ahankali Kaman yanda kowanne lafiyayyan cikin keyi.
Lokaci na Ja tadain shiga mutune Sam yanzu Takoma tamkar mujiya sbd yanda cikin yagama fitowa kowa ya ganta Kai tsaye zai shaida cikine a jikinta,
Hankalin mama Indo yayi Mummanan tashi da girman mamakin ganin Wannan alamari,
Tashin farko Bata yardaba da anata gulmar cikin Hadizar sai data tinkareta ta ganarwa idonta ta tabbatar musamman yanda hadizar takasa hada ido da ita sai hawayen baiqin ciki takeyi.
Babu kalar diban albarka da Rashin mutuncin da mama Indo batai mata tareda gori da zagi kala kala karshe ma haka ta tara mata jamaa agabansu tai mata Mummanan wulaqanci har Wanda baima Gama sanin halinda take cikiba yasani,
Take gurin aikin dama gidansu aka fara zundenta,
Masu zaginta da masu tausayinta dama wainda suke ganin ba komai bane Dan tayi cikin,
Haka aka ringa yi da ita tun tana daurewa zuciyarta harta fara gazawa sbd babu inda take Jin Dadi ko sassaunci alamarin duniya yataru yayi duhu,
Babbar fargabarta da tashin hankalinta Kar mama inda ta sanarwa su mama da Inna halinda take ciki
Dan haka duk tabi ta daga hankalinta wata sabuwar damuwar da tashin hankali yakuma shigarta.
Ahankali Ahankali lokaci yakuma tafiya Amma a rayuwar hadiza kullum da'da zurfafa take cikin tashin hankali da damuwa da qunci take sbd rayuwa tayi mata tsanani sosai sbd ciki kam ya tsufa sosai kowanne lokaci zata iya haihuwa,
Kullum adduarta Allah yasa ta Haifa abunda yake cikin yazo ba rai ta huta ta tattara Takoma gida sbd bazata iya zuwa gaban iyayenta da Wannan cikin ko abinda zata haifa barema yayyunta data San basuda imanin karbanta da abinda zataje dashi,
barinma yanzu dasuke siyasa bazasu yarda da abinda zai taba qimarsu dasuke tunanin sunada ita a manyansu.
Wani sabon tashin hankalin ta shiga Rana tsaka da gurin aikin suka sallameta bataredama sun jira watan yaqare anbata albashintaba.
Lokacinda taringa roqar Manager tana basa hakurin yabarta zata iya aikinta koda cikin Amma ya rufe ido ya sallameta tareda Bata awanni akan ta tattara tabar gidan kamfani tunda gurin aikinne suke Basu gurin zaman Dan haka Kai tsaye gida Takoma bayan tagama ganin tonan asiri da tozarci iri iri daga gurin abokan aikinta da jamaar hotel din.
Kuka zuwa Wannan lokacin ya 'dauke mata zuciyarta bayan radadi da tsananin qunci babu abinda take Mata
Dan haka ta tattara kayanta da duka abubuwanta ta fito Kai tsaye ta nufi inda zata shiga motar dazata kaita tashar da zata siya ticket din motar komawa Adamawa.
Tunda tashiga mota zuciyarta tai Mata nauyinda Bata ko iya kuka sbd dole dai Takoma gida ta fuskanci Wannan sabuwar qaddarar data zo Mata.
Har motarsu tayi wuni guda a Tasha tana zaune guri daya sallah kawai ke tada ita har dare yayi suna tashar Basu tashiba sai tsakiyar dare motocinsu suka tashi aka dauki hanya.
A hanya asuba tai musu,Rana tayi musu,yamma tayi sunata Dukan hanya har wani daren yakuma yi suka kwana ahanya sai ana gabanin asuba suka iso cikin garin Adamawa kowa ya sauka.
Lokacin har anfara Kiran sallar asuba a masallatai da dama Dan haka dole da yawansu suka tsaya anan tashar sukai sallar asuba ciki harda ita sbd batasan abinda zata tadda a gidan ba gwara tayi sallar ta nema sassauci daga ubangiji dayake jarabtarta da Wannan rayuwar.
Qarfe 5:24 mashin ya sauketa bakin kofar gidansu datai mamakin ganinsa bude lokacin ta sauka daga kan mashin din tana miqa masa kudin data fidda daga jaka tun a hanya sbd daga ta saka ya miqa masa ta shige gida batareda ta tsaya jamaar anguwa sun gantaba.
babu kowa tsit anguwar sbd garin da Bai Gama haske ba
ta kinkimi qatuwar Jakarta da akwatinta harma da wasu ledojin ta nufi cikin gidan zuciyarta na tsananta bugu duk da tayi imanin da iyayenta bazasuyi Mata zargin Zina ba tunda sune suke tarbiyanceta Kuma sunsan halinta da abinda zata iya dama wanda bazata iyaba koda kuwa inda yafi Lagos taje.
Ganin Sabon mashin fil a soron gidan yasata kallon kofar cikin gidan zuciyarta na neman karaya sbd fahimtar tabbas kodai Yaya kabiru kokuma Yaya Umar ne acikin gidan.
Siririyar shaqurarriyar sallama ta saki