Showing 30001 words to 33000 words out of 55760 words
Inayar ya qarasa ya tsaya akanta Yana sake kallon yanda fuskarta ta kumbura.
Zama yayi bakin gadon tun kafin yace wani Abu ta fashe da kuka tana cewa"
Abbi zaid yaci Amanata....
Ahankali yasake ajiyar zuciya sbd yasan zaa Rina ganin yanda Inayah take tsananin sonsa tun farko.
Ahankali ya Kai hannu ya zari tissue dake gefen gadon yafara share Mata wahaye Yana sake sakin ajiyar zuciya kafin ya kalleta cikin kulawa da kwantar Mata da hankali yace"
Ya Isa haka,
Tashi ki wanke fuskarki kizo kici abinci da magani zamuyi maganar daga baya.
Bata musawa Abbinta Dan hakan ta miqe tsaye sanyeda Riga da wandon bacci masu santsi ta nufi toilet.
Sunanan zaune duka ta fito ta zauna gefen abbin Ta karba abincin tafara da tea Mai zafi da umma yaganah ta dafa Mata da kanta.
Tana cikin cin abincin aka Kira wayarsa yamiqe ya fice daga dakin yabarsu.
Kallonta umma yaganah tayi tana cewa"
Inaga Inayah ki hakura da Zaid tunda dai da alama na Jin nasiha ko magana zaiyiba,
Nifa da kaina tun ranarda abin Nan yafaru kullum saina kirasa na Masa nasihu da nuni kan hanya Mai kyau Amma shine Dan baida niyar daidaituwa kullum Ina Masa nasiha yanacan Yana cigaba da aikata alfasharsa,
Tsakani da Allah da saninka dai auren mazinaci baida wata riba ko kwanciyar hankali,
Tunda baijiba Kuma baida niyar dainawa ki hakura ki cirewa zuciyarki ki dangana Allah yakawo Miki wani mijin Wanda yafisa kyawawan halaye..
Qala Inayah Bata iya cewaba saima danne 'dacin dayake taso Mata takeyi tana jinjina kanta.
Duk abinda umma yaganah ta fada akan kunnuwansa Dan hakan take ya dauki hannun abinda yake faruwa.
Fasa juyowa yayi ya juya ya komawarsa.
Gabaki daya wunin qin Kunna wayarta tayi sbd ko sunan Kiran Zaid Bata qaunar yi akan wayarta,
Tabbas tasan yanzu kam Abbinta dole zaisan komai Kuma hakan na nufin aurenta da Zaid ya Gama wargajewa Dan hakan zuciyarta tagama raunana,
Wuni tayi tana danne hawaye da baqin ciki.
Haka takuma kwana batareda Zaid ya biyota bada hakuri ba hakama koda ta kunna wayarta bataga kiransa ba Dan hakan taqara himmar kokarin fiddasa cikin ranta.
Ga Abbinta shima baice musu komaiba sai umma yaganah dayayi magana da ita ta zayyane Masa komai da komawarda Inayah takuma Yi gidansa.
Kwana biyu shiru ba Zaid ba wayarsa hakama Abbinta baice Mata komaiba duk saitabi taqarasa shiga wani hali.
Ta bangare daya basu daina shirye shiryen tafiya Nigeria ba Dan hakan takejin ko maganar aurenta da Zaid din tana Nan shiyasa wani bangaren takejin kaman zasu shirya komai ya wuce,taqi fidda rai.
*_Arewabooks for more pages_*
https://arewa-one.vercel.app/chapter?id=634d93b4bf002b318122db87
##MAMUH#
#LOVE/AYSHATOUH INAYAH
#ROMANCE/AA MAJEED
_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Shedar biya👇
07040727902
MTN card👇
09134848107
[10/19, 8:19 PM] Mariyamah: *_18_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Washe gari da safe tana zaune dakinta tana waya da Dr farhat kan itama Nigeria zataje saiga zubbi da soqo.
Sai data kammala wayar ta kalla zubbin tana cewa"
Yes zubbi?
Am Mr Zaid ne yazo Yana guestroom Yana buqatan ganinki.
Kallon bakin zubbin daya isar da sakon takuma Yi kafin ta Dan jinjina Kai ahankali tace"
Ok am coming.
Juyawa zubbin tayi ta fice tana cewa"
Ok Ma.
Zubbi na fita ta rintse idanuwanta tanajin yanayinta na sauyawa zuwa damuwar abinda yakawo Zaid din Kuma.
Bude idanuwan tayi tareda miqewa tsaye ta nufi gaban mirror takuma kallon kanta.
White Alexandra chiffon top ce ajikinta Mai tsada sai sky blue Levi's ripped jeans,
Kanta qaramin farin silky scarf ne a daure,
Ko turare Bata buqatan qarawa sbd Qamshin dake tashi jikinta ahankali already Dan haka juyawa kawai tayi ta fice daga dakin ta nufi hanyar palon tana jin gabanta na faduwa kaman yaune ranar farko da Zata fara haduwa da Zaid din.
Tun kafin ta Isa take Jin muryarsa qasa qasa Yana waya Dan haka saita dakata Jin abinda yake fada a wayar..
"Nafada Miki karki Kira idan nafita daganan din zan kiraki,
Meyesa bakya ganewa ne Amal?
Abbinta ne Allah kadai yasan abinda yayiwa dad dina da duk yabi ya rude yasani zuwa Bata hakuri dole,
Nafada Miki zan kiraki idan nafita Dan haka banason damuwa,
Karki qaramun pressure akan Wanda Abbin Inayah ya dorawa dad shikuma ya Dora mun okay??
Kashe wayar yayi Yana sakin qaramin tsoki Dan Amal dinma gabaki daya tagama fita ransa Dan kuwa tsakanin jiya zuwa yau dad dinsa duk yabi yagama haukace Masa akan abinda yayiwa Inayah,
Shi kansa yasan Yana Sonta Amma Kuma bayajin zai Dora soyayyar Tasu akan burika ko ra'ayin iyayensu Wanda ita Kuma gareta da mahaifinta ganin sukeyi komai suke zasu iya samunsa sbd dukiya kokuma wani ikon dasuke gani.
Bata taba Jin Zaid yafita ranta kwata kwata ba sai yanzu din dataji irin fassarar daya yiwa mahaifinta da ita,
Wani sanyayyan numfashi ta sauke ahankali tareda qarasowa cikin palon batareda ta iya kallon fuskarsaba Dan Zata iya Masa tsana Mai girma.
Kan Luxury sofa dake gefe ta zauna tana ajiye wayarta gefenta ta waiwayo ta kallesa Kai tsaye tace"
Yes?gani ance kanason ganina?
Zuba Mata idanuwa yayi yanajin Sonta na qara Masa yawa Amma Kuma yanda mahaifinta yayi amfani da dama ya rikita nasa mahaifin akanta yasa yaji son nata na komawa fushi Dan haka shima ya Dan kame fuska sosai zaiyi magana ta katsesa da cewa"
Please Zaid idan hakuri zaka bani banajin akwai buqatan hakan sbd na Riga na yarda da matar mutum kabarinsa ne so ba buqatan mu.....
Inayah kina tunanin ahakan zamuyi auren duk abinda ya hadamu Zaki kwasa ki fadawa mahaifinki shikuma Yana yiwa nawa mahaifin barazana kokuma nuna iko akan wani abin?
Kina tunanin abinda kike samu koyaushe da kina gidanku shi Zaki samu a rayuwar aure?
Look bazan yarda Kuma bazan dauka ba rashin girmamawa ga iyayena da mahaifinki keyi sbd koba komai nawa iyayen sun girma naki mahaifin ko yayane.....
Miqewa tsaye tayi tana kallonsa da mamaki akan fuskarta tace"
Zaid Dan Allah katafi bana buqatan ganinka,
Kaje kaji da kunyar dayake dawainiya dakai na abinda kamun....
Nace Miki inajin kunyar abinda nayi ne?
Kinga alaman kunyar hakan ataredani ne?
Sbd me zanji kunya?
Sbd Ina tareda wadda tasan damuwana shine zanji kunyarki?
Nayi tunanin kece wadda yakamata tafara duba yanayin Dana shiga tun wancan lokacin Amma kika nunan Sam bazaki iya take doka ko sharadin Abbinki ba,
You can't do sex before marriage,
You can't do this sbd Abbi,
You can't do that sbd Abbi,
You can't,you can't, you can't,duk sbd Abbinki,
Abbinki Annabi ne shi da bazaa.....
Wani wawan Marin da batasan yaushe tasamu qarfin yinsaba ta sauke Masa tana Masa kallon zallar tsana Bata iya furta komaiba sai"
I hate you Zaid,
Na tsaneka sosai,
Ban tsaneka sbd kaci Amanata ba sai sbd kalamanka akan mahaifina,
Dan haka kaje dakai da wanda yaturoka ban hakuri ku daina wahalarda kanku akan Abbina sbd Abbina nada business daku ne kawai sbd Ni
Ayanzu Dana cirewa zuciyata Kai Abbi ko Inda kuke Kuma bazai sake kallaba,
So please Mr Zaid can you kindly see your self out..." Taqarasa fada tana nuna Masa hanyar kofa idanuwanta jajir.
Wani shegen murmushin takaici da baqin ciki ya sake kafin ya kalli kofar yakuma waiwayo ya kalleta yace"
Bakomai bane agurin 'ya Dan ta gada ubanta,
Mahaifinki ma ya gagara Zama da mace tayaya kema ake tunanin kiyi aure ki zauna da wani?...
Wata irin tsawa Mai qarfi umma yaganah ta sakar Masa tareda Kiran sunansa da qarfi cikin tsananin fushi da bacin rai.
Kofa ta nuna Masa tana cewa"
Zaka iya ficewa rashin 'da'an ya Isa haka.,
Juyawa yayi ya nufa kofa yanajin sautin kukan Inayah data sake na tsananin baqin ciki.
Wani sanyi da damuwa yaji aransa lokaci daya,
Shi mutum ne da Baya Bari idan anmasa saiya rama,
Dan hakan ramawace yayi akan rashin da'ar da akaiwa mahaifinsa,
Yanzu daya Rama yaji daidai Dan haka zuwa gobe yasan ta sauka zai kirata a waya ya lallabata su shirya Kuma yasan idan ta shirya dashi dole yaganah dama Abbinta su shirya dashi.
Wani irin kuka Inayah keyi tun daga qasan zuciyarta takejin zafi da ciwon abinda Zaid din yayi Mata.
Janta umma yaganah tayi sukai ciki saidai abinda basu saniba shine MAJEED na gidan yadawo sbd wasu baqinsa dazasu samesa gida yakuma ji duk abinda suke fada.
Sam har baqinsa sukazo suka tafi har dare Bai nuna musu yasan abinda yafaruba sai washe gari ya sanarda umma yaganah maganar auren Babu Dan hakan da ita da Inayah din zasu Nigeria hutu sbd Inayah ta sake karta shiga damuwa sosai.
Bayanda Abbinta ya sanar da ita da kansa ba maganar aurenta da Zaid tayi kuka sosai sbd Tasan yanzu batada ranar wani auren kuma Dan haka da akace Nigeria zasu Bata wani damuba saima matsuwa datai su tafi ko Zata samu sassaucin tsananin damuwar data shiga.
Neesah hankalinta ya tashi Jin tafiyarsu Inayah din Nigeria Dan batada qawa ko daya bare aminiya idanba Inayah ba,
Taso binsu Nigeria din Amma momynta tace ba yanzu sbd sunata kokarin ganin tafara aikine yanzu,
Itama Inayah sbd Nigeria da zasu koma yasa batai saurin fara aikinba saita dawo tukuna.
Cikin kwanaki qalilan aka Gama Shirin tafiyarsu Dan haka Abbi na wucewa Singapore suma suka wuto Nigeria itada Umma yaganah da zubbi.
Saukar dare sukai a Murtala Muhammed international airport dake Lagos.
CM Nuraddeen da kansa ne yazo daukansu daga airport cikin lafiyayyar Cclass dinsa.
Cikin kulawa sosai yake musu barka da sauka tareda gaida umma yaganah cikin girmamawa.
Inayah datake amatuqar gajiye ma cikin Dan yanayi na sanyin murya ta gaidasa kafin suka shiga mota suka Kama hanyar gidansu.
Orchid Est Ikeja GRA suka iso Lafiyayyan qaton gidansu Wanda suna can abbin ya mallakesa.
Akwai Mai aiki daya sai securities dasuka sama a gidan Dan haka CM na ajesu ya wuce gidansa Dan dare yayi sosai.
Suna tareda gajiya dan haka basu wani tsaya komaiba kowannensu ya nufi Inda ya tabbatar Nan ne dakinsa sbd yanayin gyaransa.
Bedrooms hudu ne a qasa kowanne da toilet na Inayah ne kawai keda closet room na musamman sbd sanin yanda tsarin dakinta na Australia yake.
Dakin umma yagana ma babba ne da toilet dinsa aciki Babu abinda babu na Jin Dadi da kwanciyar hankali acikinsa.
Dakinsu zubbi Yana daga baya ta hanyar backdoor na kitchen.
Shi Abbi hanyar shigowarsama daban take saidai daga palonsa zuwa nasu akwai kofar wadda ta Nan zai ringa shigowa cin abinci a dining room dake babban palon gidan.
Babu Wanda yayi yunqurin komai bayan wanka da sallah dakuma bacci dayake cin Inayah Dan Sam acan Bata doguwar tafiya irin wannan.
Wanka tayo tafito daga toilet daure da blue towel tana gyara qaramin towel dake daure akanta ta nufi gaban maduba tana goge jikinta ahankali Amma da Dan sauri sbd sallolin dake kanta.
Body mist kawai ta shafa tabar gaban madubin ta janyo daya daga jerin akwatinan datazo dasu ta bude ta dauka Riga da wando na bacci masu Dan kauri ta saka tareda jallabiyanta na sallah ta saka.
Fitowa tayi tana tafiya Kaman qaramar baby ta qwalawa zubbi Kira.
Allah yasa Salimat na kitchen tana musu warming abincin data girka musu tun dazu
Itace taji Kiran ta fito tana cewa"
Ma, zubbi na daki wanka takeyi.
A kasalance Inayah ta kalleta tace,
Dama ke zance ta kirawo,
Inane gabas??
I mean alkiblah.
Nuna Mata tayi tana cewa"
Nan Zaki kallah Ma.
Gyada Kai kawai tayi tareda juyawa ta koma tana Jan qafa.
Sallolin dake kanta tayi duka
Tana idarwa Bata tsaya adhzkar sosaiba ta miqe ta cire abayar ta fada dan bubbuga gadon alamar kakkabawa kafin ta fada tashige bargo take bacci Mai qarfi ya dauketa.
Dama kusan koina na gidan gyare yake fes daga qamshi sai sanyin AC ke tashi koina.
Umma yaganah ce dai data Gama salloli da wanka ta Dan huta kafin tasa suka Kai Mata abinci a dakinta taci Salimat ta tattara gurin kafin takuma brush ta kwanta.
Inayah kam Salimat na zuwa dakinta so daya ta dakatar da ita akan kada su sake zuwa tadata su dameta sai gobe Babu abincin da Zata ci a daren.
Washe gari qarfe goma na safe ta fito a shirye tsaf cikin Riga da wando marasa nauyi na zaman gida fuskarta fresh sbd isashen baccin data samu Mai nutsuwa.
Wayarta ce a hannunta wadda take kashe tun ranarda Zaid yayi Mata Kiran farko bayan rashin mutuncin dayazo yayi Mata har gida.
Tun a daki ta zare layin sbd Baida amfani anan.
Palon take kalla koina tana Yana tsarin gidan da komai na gidan da yayi Mata daidai da can data baro,
Salimat ce datake bin kyakkyawar surarta data Gama bayyana a shape na yanayin kayan jikinta
Cikin girmamawa da sakewa tace"
Barka da fitowa Ma.
Sai alokacin Inayah ta juyo tayi Mata kallon tsaf fuskarta a sake sosai tace"
Good morning Ms.....????
Salimat Sharif"
salimat ta qarasa Mata.
Murmushi Mai kyau Inayah ta sake tana cewa"
Salimat ki kirani da Inayah,
Just Inayah okay?
Yes Ma.
Dakin umma yaganah ta nufa tana cewa"
Where's zubbi?
Ina buqatan Nigerian simcard.
Dayake akwai wayar Salimat a kusa ita Inayah din ta karba ta saka numbobin Abbinta ta Kira.
Yana tareda abokan aikinsa Amma Yana ganin Kiran Salimat daidai wannan time din yasan Inayah ce Dan haka Kai tsaye ya miqe tsaye tareda daukan wayar ya fice zuwa office dinsa.
A natse ya dauka da cewa"
Yes,Ms Salimat.
Wata qaramar dariya Inayah ta sake ahankali Tana cewa"
Abbi kasan nice ba Salimat ba shiyasa ka dauka Kira daya.
Murmushi ya sauke Me qaramin sauti kafin yace"
Meyasa Zaki kirani da layin?
Ba layin Nigeria a wayarmu duka and Abbi Ina buqatan abubuwa da dama kamansu kayan wankana da....
Ok,ok,ya Isa
Ya kuke?
Kinajin nutsuwa da yanayin gidan?
Ina tareda mutane yanzu I will call you back anjima okay?
Okay Abbi" ta furta cikin rashin Jin dadin samun lokacinsa.
##MAMUH#
#AA MAJEED
#INAYAH
#LOVE/MARRIAGE
_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Shedar biya👇
07040727902
MTN card👇
09134848107
[10/20, 12:59 PM] Mariyamah: *_19_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Breakfast sukayi na Lafiyayyan abincin da rabon umma yaganah dataci sa harta manta,
Soyayyar doya da egg sauce dataji Qoda da veggies salimata tayi musu sai chips da plantains da ruwan tea masu Dadi Amma tea kam zubbi ce data San zabin Inayah din akan tea ta dafa.
Bataci doyarba sbd Bata wani Saba da itaba chips din kawai taci da sauce sai tea suka koma Palo ta zauna tanajin kadaicin Neesah da batada wayar kiranta.
Da Rana gabaki daya familyn gidan CM sukazo gidan Yi musu barka da zuwa Dan haka gidan nasu yake cikeda Baki duk da suma ba wai wani yawane dasuba,
Matansa ne biyu haj Raliya da Anty Hafsat sai 'yayansa shida,
Biyu maza hudu Mata.
Babbar yarsa mace ce kusan sa'ar Inayah saidai tafi Inayah girman jiki sosai ta tsayi data jikin sbd Inayah rayuwar turaice atareda ita tana dieting sosai ba koyaushe takecin abinciba kokuma cin komai tasamu Anyhow
Dan hakan ita tana maintaining jikinta sosai sbd kaman yanda tafada so take jikinta yazama abinda zai qara haukatar Mata da mijinda Zata aura,
Tanason rayuwa shiyasa takeson Allah yasa ta aura mijinda yafita sanin cikakkiyar rayuwa.
Da farko zuwan baqin da hayaniyar da gidan ya dauka yasa taji kanta kaman zai fara ciwo sbd kwata kwata basu wani Saba da ganin baqi irin haka gidansuba musamman da Yara,
Ko gidajen friends nata da abokan hulda acan gida dayane take zuwa Mai Yara suma yaran biyu ne Kuma basada hayaniya kaman wainnan.
Umma yaganah kuwa Murna da farin ciki Kamar me sbd rayuwarta ta saba da hidimar mutane da hayaniyarsu Amma tunda suka bar qasar Takoma rayuwar kadaici ba mutane a rayuwarsu dagasu saisu sai qaidajjun mutane suma kusan duk turawane,
Hakan ne yasa cikeda Murna da farin ciki ta tarba baqin sunata gaggaisawa da firarraki duk duk da ita uwace garesu sai firar ta Zama ta mutunci ce sosai Dan kuwa bakowane yasan ba umma yaganah dince mahaifiyar AA MAJEED ba.
Inayah ma dole ta zauna tana Dan yaqen dole acikinsu sbd rashin sabo.
Matan Cm din kuwa kowaccensu kokarin jan Inayah take ajikinta sbd basu taba dauka haka Inayah din tasa takeba a fili,
Sunsha ganin hotunanta a media sbd mahaifinta da kowa ke mamakin son 'yaya irin nasa dayake fifita 'yarsa akan komai dakeda mahimmanci shiyasama duk Wanda yake hulda da AA MAJEED saiyayi Neman hoton 'yarsa da yake ganin tafi sauran 'yaya,
Sundada hotunanta da dama musamman na kammala karatunta dasuka Dan Yi yawo a tsananinsu sbd CM yaje taron kammalawar tasu har can qasar.
Haj Raliya da ake kira da Mimi mace ce da kusan komai nata take yinsa akan riba da qaruwa dakuma son yin suna acikin masu arziki,
Tunda dadewa takejin inama AA MAJEED nada Mata da duk yanda zatai saitayi sun Zama aminanai na gaske sbd abokanan huldarta duk matan manya ne,matan Naira.
Data Gama fahimta daga mijinta tako Ina AA MAJEED baida ra'ayin mace ko kadan yasa tasawa ranta burin ganin A MAJEED din ya aura yarta Safnah, wato babbar 'yar CM din,
A MAJEED ya Haifa Safnah sosai tunda kusan tsarar 'yarsace Inayah Amma ita agurinta shekaru ba komai bane idan har zaka sama miji cikakke,tsayayye,hadadde Kuma Wanda ya kafu kaman AA MAJEED.
Wannan burin nata yasa suna zuwa gidan taji duk duniya ba Wanda takeso irin Inayah sbd tasan ta hanyar yarsa komai zai iya faruwa.
Safnah Batasan burin mahaifiyarta ba sbd har lokacin karatu takeyi Kuma tanada saurayinta dasuka dade tare Dan haka Bata wani San menene yake faruwa Aran mahaifiyartaba.
Anty Hafsat ma tana ganin Inayah taji tana kaunarta saidai batai saurin saka wani buri ko qudirin komaiba akan Inayar
kaunace ta Gaskia ta shigeta ta 'yarinyar data tashi a hannun ubanta batareda uwaba.
Ganin yanda suke nuna kulawa da kaunar Inayah sosai yasa umma yaganah sake Jin Dadi tana Kuma girmama mutuncin iyalan CM din.
Safnah ce take Jan Inayah din fira wadda take Dan amsawa sama sama sbd gabaki daya hankalinta yakoma kan rashin layi akwai wayoyin datakeson yi.
Wani qaramin lunch party sukai a gidan sbd abinci kala kala da aka dafa tareda snacks dasu Mimin sukazo dasu.
Bata saba da yaraba Amma Yar qaramar babyn Anty Hafsat da Bata wuce 3yrs ba Mai suna Siyama tashiga ranta sosai hakan ne ma yasake taimakawa tasake Dan sakewa dasu.
Da daddare ma saida sukai dinner kafin driver yazo daukansu suka bar gidan.
Umma yaganah saidai taiwa yaran kyautar kudi sbd basuda wata tsarabar badawa duk sai Bataji dadiba sbd ita mutum ce Mai kyauta Musamman yanzu da akazo takanas Dan Yi musu barka da zuwa.
Hakan yasa taji tana buqatan siyayyan Yan abubuwa su ajiye ko Dan masu zuwa din.
Inayah kam kanta dake Mata ciwon gajiya da hayaniyar da aka wuni anayi ta dafe ahankali ta nufi dakinta tayi wanka da ruwan dumi tareda fitowa ta saka kayan bacci ta kwanta.
Bacci ne ya dauketa take sbd tagaji sosai Dan Bata saba hayaniya irin wannanba.
Washe gari doma sunyi da Safnah Zata kawo Mata layuka har biyu saidai Kuma dole zasuje ayi Mata register din layin