Showing 18001 words to 21000 words out of 55760 words

Chapter 7 - INAYAH

Start ads

20 Aug 2025

424

Middle Ads

palon Abbi ta nufa tana tunanin yanda ya shammaceta Saida yadawo ya fada Mata da ba lallai ta jima gurin aikinba ayau.

Da farin ciki bayyane kan kyakkyawar fuskarta tayi knocking kofar harso biyu kafin taji muryarsa daga ciki a natse ya furta"

Yes Inayah,
You can cm in.

Shigowa tayi da sallamar dake bayyanarda farin cikinta na ganinsa ta qaraso har gefensa ta zauna tana cewa"

Abbi kana tunawa danima kuwa?
You look more than cool and calm.

Wani qayataccen murmushi Mara sauti ya sake Yana kallon yanda itama tayi Yar rama ta yanayin aikin data samu kanta aciki da cikakkiyar kulawa yace"

Dr INAYAH A MAJEED ko gaisuwa babu tukuna kafin complains su biyo baya.

Cikin murnarta tace'

Abbinah barka da dawowa
Munyi kewarka
Kagani har Rama nayi sbd ban saba dadewa hakaba bakanan,
Ga stress na aiki.

Yar dariya kadan yayi Yana cewa"

Duk kokarin Dr Abdul akanki menene da stress acikin aikin?

Dr Abdul yana fadamun irin kokarin da kike keep it up okay.
Tun yanzu Ina alfahari da 'yata Zata Zama babbar likita wata ran.

Taji dadin kalmomin nasa Dan babu abinda yafi komai faranta ranta kaman ta faranta ran mahaifinta harya bayyanarda hakan.

Firar familyn CM tafarai Masa tana sanar dashi irin kulawa da kaunar dasuke Mata harma da umma yaganah.

Sosai yaji dadin hakan Kuma a gaban nata yakira Cm yayi Masa godia a gajarce na yanda iyalansa suka karbi nasa iyalin da hannu babbiyu.

Daganan firar Dr Abdul suka koma wadda kusan duk Rabin firar itace taketa fadar halayen Dr Abdul din dakuma yanda take kulawa da tattalinta.

Abbinta saurarenta kawai yakeyi Yana nazarin irin shaquwar data samu da Dr Abdul din lokaci daya,

Yana fatan alaqar da tsaya iya ta aiki sbd irin wannan yabo da Inayah ke Masa baya fatan tasake shiga wata soyayyar yanzu Musamman ko Dan yanayin weak heart nata
Duk da wani bangaren Dr Abdulsamad ya kwanta Masa sosai a Rai.

Sai dare tabaro gurin Abbin Dan abincima acan palonsa sukaci tare sbd shi kansa yariga yashige ne bazai fitoba sai gobe shiyasa shima Bai fito main hall ba cin abincin dare.

Tana baro palon Abbin gurin umma taje sukai Saida safe ta wuce daki ta kwanta bayan tayi waya sama sama da Dr Abdul akan daga gobe a
Shift din dare zasu sake komawa.


Washe gari da safe batada zuwa asibiti Dan haka baccin safe tayi sosai sai 11 ta fito lokacin Abbi baya gida ya fita.

Sanye da Riga da skirt na atampa ta fito tana waya da Neesah.

Breakfast tayi ita kadai sbd tasan ko umma ta jima da yin nata.

Tana gamawa ta nufi dakin umma yaganah acan tayi kwanciyarta tana chatting sama sama saiga su Mimi sun taho gidan dukkaninsu yiwa Abbi barka da zuwa aikuwa take gida ya kaure da hayaniya.

Mimi harda tsarabar wasu kayan atampopin tayiwa Inayah aikuwa umma ta gode Mata sosai itama Inayah din tanajin dadin kayan Dan haka ta gode mata.

Dakinta suka koma itada Safnah suna firarsu ta matasan 'yan mata,

Fira suke akan anty Hafsat da Bata isoba sun biya sun ajeta gidan yayar mijin qanwarta dasuke tsananin mutunci sosai, daga can zaa kawota Nan din.

Saida suka gama cin abincin Rana kusan karfe biyu da mintuna kafin Anty Hafsat ta iso gidan.

Da farin cikin ganin siyama Inayah tarbota tun daga harabar gidan.

Faruk Ismail shine Wanda yakawo anth Hafsat daga gidansu.

Kallo daya yayiwa Inayah yaji Tai Masa sbd shima tunda yayo karatu a Malaysia yadawo yakasa ganin macen datai Masa gashi dama iyeyensa sun takurasa akan aure.

Ganin dayayiwa Inayah da yanayin gidan nasu yasa Kai tsaye ya 'dan fahimci wayayyu ne jama'ar gidan,
Da alama sun danyi nasu yawon bude Ido wata qasar.

Inayah gabaki daya batama wani lura dashiba sbd hankalinta dake anty Hafsat da Siyama tana murmushi dukkanin kyanta na Kuma bayyana.

Anty Hafsat ce ta juyo ta kallesa tana cewa"

Ok faruk nagode sosai
Ka Isa gida lafiya.

Gyada Kai kawai yayi tareda tada motarsa yabar harabar gidan ya fice Yana ayyanawa aransa shikam yaga matar aure irin class dinsa dayakeso.

Inayah kam Anata bangaren ko kula batai dashiba Dan a daukarta driver nema yakawo antyn.

A gidan suka wuni Anata fira da hayaniya sai yamma da Abbin yadawo aka kaisu palonsa suka gaisa a matuqar mutunce da girmamawa.

Sai dare suka tafi bayan Abbi yayi musu kyautar kudi na Musamman ga Yara.

Inayah Jin tayi kaman kada su tafi sbd yanzu da qarfi da yaji tafara sabo da rayuwar hayaniya Dan duk Wanda zai Yi rayuwa a Lagos dolensa ya koya daukan hayaniya duk da sukam anguwarsu batada abinda ya hadata da hayaniyar ko hayaniyar ma Kai securities basa Bari magana suke maka sbd gudun shiga haqqin wasu.















_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya👇
07040727902

MTN card👇
09134848107
[10/15, 4:03 PM] Mariyamah: *_Mamuhgee 11_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Washe gari ba wani dogon walwala ta tashi
Saima guraren 9 ta tashi Dan tun asuba tayi sallarta,

Zare dukkanin kayanta tayi ta jefa kan kujera ta wuce toilet tashige tana kokarin daura towel jikinta.

Sosai ta jima tana wankan sbd tasaba Bata lokaci gurin kyalekyalen wankan,

Sai bayan mintuna ta fito daure da milk towel kanta Kuma nade da wani towel din mara girma.

Natsatsen Qamshin shower gel dinta na AESOP Mai sanyin Dadi ne ke tashi ajikinta ta kalla Inda qaramin bedside agogonta yake ta kalli time taga goma yakusa Dan haka Kai tsaye ta nufi gaban mirror tagara shiryawa.

Moisturizer kadan ta shafa na LA PRAIRIE sai oil na Neutrogena da kome Zata shafa saita shafasa takejin skin dinta daidai.

Dama kafin ta fito daga wanka zubbi tagama gyara mata dakin ta kunna humidifier dasu fresheners masu sanyin qamshi ta fice da kayan data cire zuwa laundry.

Elira kaftan dress ta saka dark brown da scarf sai Cassandra wedge sandal ta fito gabaki daya qamshinta na JO MALONE sea salt yana gauraya iskar hanyar datake biyowa.

Kai tsaye dakin umma yaganah ta nufa tasan lokacin umman bacci takeyi sbd a qaidarta haryanzu data fara tsufa Bata daina saka hannu akan aikin abincin A MAJEED matuqar yana gari tariga ta saba
Matuqar baka ganta kitchen ba A MAJEED baya gari Dan hakan Bata komawa bacci bayan asuba saita tabbatarda abincin breakfast yagama kammaluwa a dining saita koma ta kwanta sai 12 take tashi tayi wanka ta Kuma leqawa kitchen din sakawa zubbi hannu a abincin ranar.

Kaman yanda tasani bacci umman keyi Dan hakan fitowa tayi dakin Kai tsaye ta nufi hanyar dakin cin abincinsu tana shiga abbin na shigowa ta dago ta kallesa da fararen idanuwanta dasukaji tsadaddiyar fenty beauty mascara da eyeliner

Qamshinsa daya doke nata ta shaqa tareda dakatawa daga zaunawan da zatai cikin nutsuwa da girmamawa tareda tsananin kauna irin ta 'da da mahaifi tace"

Good morning Abbi,
Barka da fitowa.

Saida ya kalleta cikin nutsuwa ya ja kujera ahankali ya zauna yana sake kallonta ganin yanayinta na sanyi jiki har lokacin
Basarwa yayi sbd karta samu damar fara Masa hawaye agurin yace"

Morning,
Kin tashi lfy?
Ya umma yaganah?
Tana bacci ne?

Zama tayi tana cewa"

Eh Takoma bacci.

Itace ta zuba Masa breakfast din kafin tazuba nata Takoma ta zauna tafara ci.

A natse yakecin brown past din da aka hada da soyayyan dankali da hanta sbd Sarai umma yagana tasan Baya wani cin kayan fulawa sosai yafison abinci Mai suna abinci bawai wani jagwalgwalon gayuba.

Satar kallonsa Inayah keyi tanason magana akan roqonsa maganarsu ta jiyan amma tana shakkar hukunci ko dokar ta qara tsanani akan iya ta jiyan.

Kasa daurewa tayi ta aje fork din hannunta tareda dagowa ta kallesa a marairaice tace"

Abbi....

Tissue ya dauka tareda goge bakinsa kafin ya dago ya kalleta da dukkanin fararen idanuwanta ya zuba mata yana jiran abinda takeso fada.

Ganin yanda ya zuba mata idanuwansa yasata sauke Kai tana qaqalo hawaye cikin idanuwanta ta dago ta kallesa hawayen na gangarowa kan kumatunta tace"

Abbi Dan Allah kayi hkr bazan sake tsallake zuwa school ba I promise
Amma Dan Allah kada ka hanani fita ko zuwa wani gurin.

Hawayenta dake gangarowa ya kalla tareda Dan sake wani gajeran murmushi dayayi Masa zuwan bazata sbd ganin qarfi da yaji wai 'yarsa daya Rena da hannunsa keson yimasa dabara,

Duka duka Inayah nawa take?
Yaushe tayi girman da wayon datake ganin Zata iya Masa wani sisina da hawayenta tunda tasan bayaso..

Ita Bata tashi da mahaifiyaba bare ace takoya ko tagani agurinta Amma wai hartasan taringa Masa hawayen kirsa Dan yaringa barinta tana yanda takeso.

Sake fadada murmushinsa yayi kadan yana Kuma kallon hawayen nata datake tsiyaya da gaske Wanda badan yagama saninsu a yanzuba da tuni zuciyarsa zatayi 'daci da ganinsu Amma yanzu mamaki yake sosai ta yanda take iya hakan.

Numfashi ya sauke ahankali tareda zaran tissue dake kan dining din ya miqa mata yana cewa"

Ya Isa idan kingama tashi muje nine zan aje school din yau kafin na wuce office.

Share hawayen tayi da tissue din daya Bata tana jin Dadi cikin ranta na yanda kwata kwata Abbinta baya juran hawayenta.

Miqewa tayi tabiyo bayansa tareda daukan LV hanbag dinta tafito tana duba wayarta dake ringing da sunan Zaid akai.

Bata wani dauki wayarba ta jefa jaka sbd tanason samu ta lallaba abbinta yabarta taringa zuwa duk Inda ta saba zuwanta itadai tanaso gskia.

Cikin black BMW 7 series suka fita shine da kansa yake tuqa motar tana gaba zaune,
gabaki daya Qamshin tsadaddun turarukansu yagama sauya numfashin motar Amma dayake motar tasace shine Wanda yafi shigarta sai nasa ya take natan sbd tuni akwai qamshinsa acikin motar.

har bakin makaranta ya ajiyeta batareda ya tankawa uban magiya ra rokon datake masaba,

Saida yayi parking ya juyo ya kalleta fuska a Dan sake cikeda kulawarsa da taushin murya yace"

Inayah.¿

Dagowa tayi ta kallesa tana kokarin qirqiro wasu hawayen dasuke son qin zuwa,
Ahankali tace"

Naam Abbi.

Wannan kukan na karya dagayau gabaki daya na sokesa Shima,
Meye amfanin hawaye Dan ki dagawa mahaifinki hankali?
Akwai wani Wanda yake Baki shawaran yin hakan ne sbd kawai kisa mahaifinki yamiki abinda kikeso?

Girgiza Mai tayi tana kallonsa da rauni tace"

No Abbi.

No Inayah fadamun gaskia sbd nasan banbawa 'yata tarbiyar hakanba,
Meye amfanin hawaye kawai sbd dagawa iyaye hankali,
Wannan ne last time dazan Kuma ganin wannan hawayen ok?

Gyada Kai tayi tareda maida hawayen dama Kuma fama taketayi akan suzo din basu zoba sbd Allah yasani batada wani dalilin kuka a rayuwarta sbd alhmdllh Allah ya wadatar da mahaifinta abinda duk take buqata a rayuwa,
Mahaifiya kawai ta rasa wadda koda ganganci ko subutar Baki Bata taba ambatar ko sunan uwa agaban abbin harma da bayansa sbd tsananin fushi da bacin ran dayake nunawa sosai wadda kusan itama sai hakan ya samu shiga zuciyarta na fushi dajin bacin rai aduk lokacinda ta tuno da dole tanada uwa kodai tabarta da mahaifinta lokacin dayake cikin zafin talaucinsa kokuma ta tafi tabarsu sbd bazata iya hakuri da wani hali daga murdaddun halayensaba Dan kuwa tasani abbin nata murdadden mutum ne itada umma yagana ne kawai suke iya Zama da abinsu sbd sunsan komai dayakeso da Wanda bayaso.

Bata saba batawa Abbinta raiba ko tayi Bata iya hakurin dacin ransa akanta Dan haka ta kallesa tareda dafa hannunsa ahankali a marairaice tace"

Abbi kayi hkr nadaina daga yau.

Gyada mata Kai yayi tareda dafa kanta cikin kulawa yace"

Shikenan kije karkiyi latti,
Ki kula.

Murmushi tasake tana cewa"

Ok bye Abbi Allah yabada sa'an aiki.

Fita motar tayi tana daga Masa hannu daya kafin ta juya ta wuce.

Neesah dake jiran isowarta taqaraso suka nufi ciki suna maganar Abbinta daya soke zuwanta spas kwata kwata.

Saida suka shige ya juya yabar gurin sai alokacin ya dauki wayarsa dake ajiye ya kunna ya nufi hanyar office.

Yau daga makaranta gida ta wuto direct basu tsaya yawon dasuka sababa na gurare
Itama Neesah yau dole gida ta wuce Amma badan sunso hakanba sai Dan bata iya take umarni Abbinta dakuma Bata Masa rai.

Kwana biyu haka suka daina yawo suka maida hankali kan karatu musamman dama sunyi nisa sosai.

Kwana biyun ita kanta umma yagana Saida taringa jinjinawa sabon umarnin na A MAJEED sbd a duniya shi kadaine yakai yakuma Isa yakeda ikon Hana Inayah yawo,

Sam batason Zama gida itada Neesah Dan hakan yanzu kwanakin duk sunbi sun wani sukurkurce sbd daga makaranta sai gida.

Shi kansa abbin yana lure da duk wani motsinsu sbd 'yarsa,
Bai taba tunanin rabata da Neesah ba sbd bincikensa tun farko dayasa ana bimasa akan Neesah batada wata gurbatacciyar tarbiya
Gata ne kawai itama da 'yanci yayi mata yawa da iyayenta suka bata Dan hakan bayan yawon shoppings dasu beauty spa sai yawon dai guraren dasuke zuwa tareda friends Amma sosai batama alaqa da harkar data shafi na banza shiyasa baiyi yunqurin rabata da 'yarsaba yabarsu suna rayuwarsu tunda dama dole Inayah zatai rayuwarta da friends.

Ahakan suka dauki tsawon lokaci har suka samu 2 weeks break a lokacinne Zaid yafara takura mata sosai akan maganar aurensu.

Kai tsaye yafito yake matsar da ita akan sosai yake buqatan aure sbd shi buqatarsa tafara zuwa na Neman mace.

Da farko fada sukayi sosai ta nuna Masa ya rabu da friends dinsa da basu dauka sex abakin komaiba sbd yanayin rayuwar turai dasuke dakuma kusan dukkaninsu tashin turai dinne.

Shawararta ya dauka ya daina biyewasu zacks kwana biyu sbd dama sune suke tada Masa da shaawar hakan,
Da yawa yan matansu a gida suke kaisu suna wasu abubuwan gabansa gashi dama babban gidane suke zaune su ukun kowa da babban bedroom dinsa da fadeden bathroom aciki harma da closet room.

Su ukun friends ne tare suke kusan tun yarinta,

Zacks bama musulmi bane black American ne,
Sai Sufian shikuma kusanma 'dan uwansa ne sbd fmly friends ne ahalinsu.

Tare suke lafiyayyar rayuwa a gidan sbd kowannensu yanaji da kudi da gata ba laifi,
Yan mata kuwa kusan kullum cikin sauyawa sukeyi babu ranarda mace Bata kwana gidan
Idan zacks Bai kawoba Sufian zai kawo Dan hakan yau da gobe suka ringa saka Zaid cikin yanayi na damuwa gashi yanzu tsakani da Allah yakan ji shaawar mace lokuta da dama.
Kwana biyu yafara kasa daurewa shine yafara takurawa Inayah maganar aurensu.

Yauma kusan fadan sukayi akan maganar cikin yanayi na takaicinsu zacks tace Masa"

Baby nafada maka Abbi bama zai kalleniba naje da maganar Kuma shikenan nice zanje na rokesa akan ayi aure yanzu?
Kana tunani kuwa?
Please ba Abbi ba Nima banajin na shiryawa auren yanzu idan har sbd wannan maganar kakeson auren yanzu...bazan iyaba please baby mubar maganar Nan banason jinta tana damuna ma.

Shima ransa Dan baci yayi Dan haka Bai Kuma tayar mata da maganarba saiya koma kiran dad dinsa yana matsa Masa sosai akan maganar auren Dan hakan dole dad din nasa ya nema A MAJEED da maganar idan da hali suna son ayi auren yanzu.
##MAMUH#
#INAYAH#
#RIBA BIYU#
#LOVE/ROMANCE#



_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

_BREAKDOWN OF ZAFAFA BIYAR VVIP SINGLE PAID BOOK_

_4 BOOKS  4500_
_3 BOOKS : 3500_
_2 BOOKS : 2500_
_1 BOOK: 1500_

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107
[10/15, 4:03 PM] Mariyamah: *_Mamuhgee 12_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Dad din zaid yasan Sarai waye A MAJEED Dan hakan Bai tsaya nemansa a wayaba sbd sanin babu abinda zai gane a wayar tunda A MAJEED din ba wai son auren yanzu yakeba yakuma sanar dasu hakan batareda ya fada dalilinsaba saidai Kuma kusan duk Wanda yasansa yasan dalilin nasa ba boyayye bane duba da yanda yake Da zurfi da ilimin boko sosai daya Gama ratsasa sunsan babu yanda mutum irinsa zai aurar da yarsa qwalli daya dazata gadi tarin dukiya da companies dinsa batareda tasamu ilimin itama Mai zurfiba Amma ya suka iya tunda sunaso dole haka ya tattara ya tsaro tafiya ya taso zuwa qasar.

Shi dad din tun farko bakin rai bakin fama yakeson auren tsakanin 'yayan nasu sbd burinsa nason qulla alaqa Mai qarfi da A MAJEED,

Babu wani Mai son abun duniya da kudi daba zaiso shi ko 'dansa su auri 'yar A MAJEED qwaya daya tal ba wadda zai iya bada duk tarin himilin dukiyarsa akantaba
Dan haka ba dauki bare wasa shi kam so yake ayi auren kota yaya Dan Inayah idan tana hannun 'dansu tamkar suna riqene da mukullin dukiyar A MAJEED da Baya tabuwa bare juyiwa ga kowa,Dan banzan naira da dollar sungama zauna Masa tako Ina,sun girmesa Sbd har lokacin baiyi shekarunsuba badan yanada zuqeqiyar budurwar 'yaba ai yanada sauran lokaci a cikin matasa Amma dai koma menene yaro da kudi abokin manya dama abokanan huldarsa manyan ne na gaske.

Zuwan dadyn Zaid Sydney yasa damuwar da Inayah tafara shiga ya dan fara raguwa sbd gabaki daya kwata kwata yanzu itada Zaid din kullum cikin hayaniya suke,

Bazata iya daukan fada bare rabuwa da Zaid ba
Ayanzu din tafison Dad din nasa yayiwa abbin mgn idan ya amince ayi auren Dan gskia tana tsananin son Zaid dinta koma menene ayi auren zatai maganin wannan iskancin da yayi mata daga baya.

Yau daga makaranta Saida su biya ta siyo wasu abubuwan wankanta dasu undies da Bata rabo da siya akai akai,

Sai yamma suka dawo Shima tun acan take waya da abbin akai akai tanaji idan yadawo gida sbd kada ya rigasu komawa yaga sunyi yammacin dawowa.

Da motan Neesah suka dawo sbd yauma Abbinta ne ya ajeta makarantar Dan dama haryanzu data girma dinnan idan yana gari yawanci shine yake ajeta school saidai driver yaje ya daukota kokuma su dawo a motar Neesah.

Neesah Bata shigoba ta wuce Dan hakan itama Kai tsaye tana shigowa bakowa a palo dakinta ta nufa.

Ajiye kayan hannunta tayi tana ajiye numfashin 'yar gajiya da yunwa datake ji Dan haka tubewa tahi ta fada toilet tayo wanka tafito ta sanya Abayar sallarta tana idarwa tayi adhkar ta miqe ta sanya ash riga da wandon Burberry masu kauri saidai qananun size ne Dan sun zauna daidai jikinta,basu matsetaba hakama basuyi mata yawaba daidai jikinta.

Sponge resort Slippers ta zuro ta fito tana qamshinta hankali kwance.

Dakin umma yagana take kokarin zuwa saiga umman ta fito.

Cikin shagwabe fuska ta rungumo hannun umman suna juyawa zuwa dakin cin abinci tana cewa"

Umma yaganah yunwa nakeji sosai.

Murmushi umman tayi tareda Dan janye jikinta daga Inayar tana cewa"

Haryanzu kin kasa iya fara gaisuwa kafin komai ko Inayah?

Sake kwantar da kanta tayi kafadar umman tana cewa"

Umma yaganah kullum fa Ina gaisheki kafin nafita idan nadawoma inayi ranarda na manta ba sai ayi hakuri Amin uzuriba for God sake,Kuma ma fa na........

Qamshin Turaren Abbinta yasata shanye abinda Zata fada din suka kalla hanyar palonsa atareda umma yaganah aikuwa shi dinne tafe cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.

Sanye yake da fararen Adidas riga da wando masu kauri hular dake hadeda rigar itace rufe akansa
Qafafunsa kuma black santoni

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login