Showing 21001 words to 24000 words out of 55760 words

Chapter 8 - INAYAH

Start ads

20 Aug 2025

423

Middle Ads

slippers ne.

Gabaki daya Abbinta idan yayi shiga tamkar matashi yake komawa musamman irin wainnan shigar da yakeyi idan zaiyi geamin(exercise/motsa jiki) ko idan zai kwanta ranarda yakejin sanyi kenan,

Yawan geamin dinsa yasa kullum yake sake Zama tamkar wani sabon matashin da yanzune yake lokacinsa sudaima sun rasa gane irin kyan jiki da kyan siffarsa daya hanasa manyanta sosai.

Umma yaganah ce tafara bude Baki tana kallonsa tace"

ABDULMAJEED barka da fitowa.

Cikin yar girmamawa ya Dan kalleta kadan tareda dauke idonsa akanta yana cewa"

Mun wuni lfy umma yaganah?

Wata jarabawa kokuma ace lalura datake kansa tsawon shekaru shine Baya kallon mata kallon daya wuce daya zuwa biyu,

Sam ya dade da rufe shafin mace ata kowanne fani na rayuwarsa bayan 'yarsa,
Duk huldar aiki dazata hadasa da mata Baya wani maida hankali sosai akansu Wanda Kuma kusan ba kowane ya fahimci hakanba tunda dama shi ba mutum ne Mai sakewa mutuneba shiyasa baa wani ganewa
saidai umma yaganah da Inayah dasuka Sansa ciki da Bai sune sukasan babu macen dayakewa kallon daya wuce biyu zuwa uku,

Umman ma haryanzu idan yayi mata kallo daya zuwa biyu koda suna magana ne Baya qarawa shiyasa da yawa idan kana Masa bayani saika dauka hankalinsa Baya kanka and yafi maida hankali kan wani abun daban ko waya haka Amma Kuma ahakan yafi fahimtar bayanin da ake masa.

Wainda suka 'dan Sansa da kadan daga halayensa idan suna magana dashi sukaga Baya wani abun daban ya tsaya yana saurarensu to kuwa sun San tabbas Bayada niyar saurarensu ne,idan kanason Kama mutuncin kanka saika dakata kabar maganar Dan ba lokacinta zaiyiba.

Zama sukayi dukkaninsu a dining Inayah ta zubawa kowa abincin kafin Takoma ta zauna itama bayan ta zuba nata,

White rice ce da chicken vegetables with scrambled eggs.

Suna fara cin abincin Inayah ta kalli abbin dayakecin abincin a natse kunnuwansa na sauraren sautin yanayin cin abincinta take ya fahimci akwai maganar datakeson yi.

"Abbi" ta furta sunan ahankali cikin kulawa da bayyanarda 'yar shagwaban data taso acikinta.

Kallonta umma yaganah tayi cikin kulawa ya katseta da cewa"

Ba yanzu ba Inayah,
Bakiga Abbinki yanacin abinciba?
Surutu lokacin cin abinci baida amfanin kinmatane?

Marairaice fuska tayi cikin son fadar abinda yaketa nuqurqusanta Kuma tasan Idan ba fada Masa tayiba Dad din Zaid yayi Masa zuwan Kai tsaye da bazata ransa zai baci akan da sanin ta akazo maganar,

Bazata iya daukan fushi ko bacin ran abbintaba akanta Dan haka Kai tsaye takuma kallonsa bayan tayiwa umma yaganah fuskar riqon tabarta tayi magana.

Abbi Dad din Zaid Yana gari yazo fa....

Ahankali ya qarasa hadiye sauran abincin dayake bakinsa ya dauki ruwa mara sanyi sosai dake gabansa cikin glass cup yasha ya ajiye sauran ya dauki tissue Saida ya goge bakinsa ya dago da manyan idanuwansa ya kalleta hankali kwance yace"

Yes,Uhum?
Dad din Zaid Yana gari zan Masa wani Abun ne?
Gurina yazo ne?

Abbi dama gurinka ne zaizo kuyi magana,karyazo ne baka saniba ranka ya baci Abbi shine nafada maka Kuma banice nace suzoba Abb...

Umma yaganah ya kalla Kai tsaye da tambayar

"Kinsan da hakan ne umma yaganah?
Ta sanar dake Zata basu Daman zuwa neman aurenta?

Ajiyar zuciya umman ta sauke cikin sanyin jiki sbd Inayah dai Bata gane kwaba,

Kallonsa take cikin sanyin jiki tace"

Ta sanarmun da mahaifin nasa zaizo Amma na kaina na Kira Zaid din nace su dakatar da zuwan sbd Jan magana daya koyaushe baida amfani tunda dai anbasu auren Inayar
Yin auren ne dai tunda anfada musu ba yanzuba na rasa naci irin na 'yaran yanzu tunda ba cewa akai a gaban zaa fasaba...

Jin shirunsa Yana saurarensu yasa dukkaninsu suka Sha jikinsu sbd sanin hakan abinda yake nufi,

Dukkaninsu sun fahimci bacin ransa akan hakan shiyasa suka sake yin wani tsamo tsamo.

Cikowa idanuwan Inayah sukai da hawaye batareda ta saniba cikin sanyin murya da sigar ban hakuri ta taso tadawo gefensa tareda Dafa hannunsa ahankali tana cewa"

Abbi Banice nace suzoba wlh,
Nayiwa Zaid din maganar kada dad din yazo Amma baijiba,
Abbi wlh bani bace...

Batareda ya kalletaba yace

"It's okay saiyaxo Ina jiransa.

Miqewa yayi tareda kallon umma kadan yace"

Mu kwana lfy umma yaganah.

Allah ya tashemu lfy" tafada itama tana bin bayansa da kallo ranta babu Dadi da yanayin,

Babbar matsalar basa wani gane bacin rai ko fushinsa bare kasan halinda kake ciki shiyasa koyaushe irin wannan kuskuren yafaru sun ringa Kara kaina kenan gurin samun sanin yanda ransa ya dauki Al'amari.

Bayan barinsa gurin Kallon umma yaganah Inayah tayi da raunannun idanuwanta zatai magana umma ta tareta da cewa"

Inayah meyasa kikai maganar Nan?
Maimakon ki dakatar dasu Zaid din shine Zaki Kuma kawo maganar gaban mahaifinki bayan kinsan bayason maimaicin zance,
Anyita maimaita zancen Nan Kuma kinfi kowa sanin mahaifinki magana daya yakeyi akanki meyasa bazakiyi respecting hakanba?

Yanzu gashinan zakiwa kanki Dan kuwa Abbin zai iya Hana auren gabaki daya yace su hakura suje su nema wata su aura idan sunaga bazasu iya jiranba
Kinga kuwa wa garin ya waya.

Batada abin fada sbd jikinta daya Gama mutuwa da yanayin mahaifinta daya qi barin su gane yanda ya karbi zancen.

Cikin sanyi ta dauki orange juice din dake gabanta ta Sha sosai ta aje cup din sbd bazata iya cin abincinba Kuma.

Miqewa tayi tareda yiwa umma yaganah Saida safe ta wuce dakinta itama.

Itama umman kammalawa tayi ta miqe tabar dakin ta dauki sauran abincin datasan zai moru takai fridge ta jera kafin ta wuce nata dakin zubbi tazo ta tattara gurin ta gyare Takoma dakinta itama.

Bayan isarta daki ta Gama duk abinda zatayi ta hau makeken gadonta ta kwanta tareda daukan wayarta ta saka Kiran Zaid.

Daukan wayar yayi tun kafin yayi wata magana tace"

Zaid please ka dakatar da zuwan dad gurin Abbi banason cigaba da Bata ransa akan maganar wani auren yanzu,
Nidai gskia mu haqura abari sai lokacinda Abbina yace koma yaushe ne zamu jira
I don't want to stress him with unnecessary abubuwa kaman hakan tunda yace ajira kawai ajira
Dad dinka yakoma please...

Inayah are you out of your mind or what?"" yafada cikin Dan daga murya.

Kinajin kanki da abinda kike fada kuwa?
Dad ya taso all the fuckin way from Nigeria yazo kice yakoma sbd kada a dama Abbinki?
Are you for real?Kinajin kanki kuwa?

Zaid please karmu batawa juna Rai abanza mubar maganar auren Nan yanzu sai gaba....

Datse wayar yayi ya kashe gabaki daya ya jefar gefensa Dan zuciyarsa tafara baci sosai da yanda koyaushe Abbinta shine gaba shine yafi kowa mutunci,yanaji kaman mahaifinsa take kokarin ciwo mutunci Dan haka cigaba da wayarsu yanzu zai iya hadasu fada sosai shiyasa ya kashe din.

Inayah ma wayar tabi da kallo cikeda mamaki da Dan takaici,
Ita Zaid yake kashewa waya yau?
Wai kodai bayan matsalarsa ta buqatan aure yanada wata matsalar ne da ita Bata saniba Dan kuwa wlh bazata dauka wannan wulaqancin tun yanzuba tana magana ya kashe mata waya.
##MAMUH#
#A MAJEED/AYSHATOUH INAYAH/LOVE/ROMANCE/MARRIAGE
#RIBA BIYU


*_FOR MORE PAGES KUYI FOLLOWING DINA A AREWABOOKS@Mamuhgee_*



_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

_BREAKDOWN OF ZAFAFA BIYAR VVIP SINGLE PAID BOOK_

_4 BOOKS  4500_
_3 BOOKS : 3500_
_2 BOOKS : 2500_
_1 BOOK: 1500_

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107
[10/15, 3:51 PM] Mariyamah: *_Mamuhgee 13_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Da 'dacin Rai duka suka kwana a daren ,
Inayah Kuma harda matsuwa tayi garin ya waye ta nemesa taji dalilinsa na kashe mata waya sbd ko Abbinta baya kashe mata waya shi dayafi kowane namiji daraja agurinta da rayuwarta.

Duk yanda Abbi yakai ga bacin rai baya taba Bari agane Dan haka da safen koda ya fito kyakkyawar  fuskarsa na ayanda take koyaushe ba damuwa.

Black Armani's ne ajikinsa sosai yayi fresh acikin black kala din,

Cikin sanyi ta kallesa tanason shagwabe Masa Amma tunanin Tayi Masa laifi daren na jiya yasa ta Dan nutsu duk da hakan cikin marairaicewa tace"

Good morning Abbi" tana qarasowa gurinsa itama shirye cikin milk sleeves riga da skirt na Balenciaga.

Morning Inayah" ya amsa Yana kallon yanda idanuwanta sukai zuru zuru sbd daren jiyan da Bata samu bacciba.

Dining suka zauna bayan ya gaisa da umma yaganah yasake kallon Inayah din da itama taketa qara wani kalar tausayi ganin take ya nuna ya lura da yanayinta na rashin baccin da Bata samuba Kuma tasan dole zai nuna damuwarsa akan hakan shiyasa take sake yin kalar tausayi.

Black tea Ginger tea Mai zafi aka fara zuba Masa ya dauka yafara Sha ahankali tareda Dan sake kallon fuskar Inayah din ya dauke fuska Kai tsaye ya bude Baki cikin nutsuwa yace"

Inayah¿

A marairaice tace"

Yes Abbi¿

Kallonta yayi bayan ya aje cup din hannunsa fuska a Dan matse yace"

Next abinda zakiyi na soke alaqarki da kowanne namiji sai bayan kin Gama karatu kwata kwata shine kici gaba da saka damuwar soyayya aranki harya hanaki bacci irin haka,

Umma yaganah ya kalla cikin jaddada zancensa yace"

Yaushe tasan wani soyayya hakane?
Ki ringa Mata fada sosai idan ba hakanba zan tattara mubar qasar gabaki daya mu koma Nigeria ko Zata maida hankali a karatun can.

Hawaye takeson yi Amma tunowa da ya Hana yasata maida hawayen cikin sanyi tace"

Abbi Dan Allah kayi hkr,
Ba tunanin komaine yasa banyi bacciba inada test ne yau so I had to study all night...

Waiwayowa yai ya watsa Mata manyan idanuwansa ahankali Yana sake mamaki da jinjinawa sauyin sabbin halayenda Inayah ke dauka,
Yaushe Kuma ta iya harda yimasa qarya?

Sauke Kai tayi qasa tana Dan sosa wuyanta gabanta na faduwar kada yagane qaryarta saidai Batasan ta makaroba.

Qarasa Shan tea dinsa yayi Bai wani Abinci sosai ba ya kammala ya miqe Yana cewa"

Muje zan ajeki school.

Satar kallon umma yaganah tayi tana neman qaryar dazata Kuma shimfidawa yatafi yabarta ta tafi school din da kanta Dan dole tana buqatan biyawa gurin Zaid suyi magana.

Rasa abin fada tayi dole badan tasoba ta miqe suka bar gurin umma nai musu adduar dawowa lfy.

Shi kadaine ya amsa Banda ita data shiga tunanin abinyi Dan yanzu tasan kila Abbin zai qara Mata tsananin fita akan na dah.

Yau bashine yake tuqa motarba driver dinsa ne yake jansu.

Har suka Isa makarantar kame kamen basa hakuri takeyi Amma Bai wani bi takan zancen nataba saima zancen karatun dayayi Mata daban.

Suna Isa aka sauketa suka wuce sai alokacin yabi bayanta da kallo,
yanajin tausayin 'yarsa fiyeda komai,

Hakama Baya iya hakurin damuwarta,

Ya rasa waye yake gurbata Masa tunani da tarbiyar 'ya akan ire iren hakan,

Kwata kwata haryanzu bayajin sha'awar kowace irin mace bare marmarin ajiyeta shiyasa yake tsananin mamakin yanda Inayah ta qwallafa Rai a soyayya da son aure tunda ba ganin tayiba a gidansu ana soyayyar, hasalima shi soyayyarce sam baisan yama akeyintaba bare harka Gama macewa akan wani kaje kana Hana kanka bacci a wofi.

Motar Abbin na barin makarantar ta fito zuwa coffee shop din dake makarantar ta samu Neesah dake can ta zauna tareda fidda wayarta batareda ta iya wata doguwar maganar da Neesarba tafara saka Kiran zaid.

Kasa samunsa tayi dole qarshe tabar Masa sakon murya da cewa idan ya kunna waya yakirata Kuma ya tabbata Dad baije gurin Abbinta ba sbd zasu iya yiwa kansa Abbin ya dakatar da soyayyarsu sai gaba din.

Bayan Gama tura Masa sakon muryan aje wayar tayi gabanta zuciyarta ba wani Dadi ta Dan yamutsa fuska tareda Kiran sunan waiter a tushe tace"

2 Cappuccino's please.

Kallonta Neesah tayi tana cewa"

Kodai zamu samesa ne?

Bazai tsaya sauraren wannan ba namafi zatan Dad din nasa ya riga Abbi Isa office dinsa jiransa.

Kasa cewa komai tayi Saida aka kawo Mata cappuccino din ta fara Sha ahankali kafin tace"

Banajin komai sai bacin ran mahaifina,
Zuwan dadyn Zaid zai fusata Abbi Kuma na fadawa Zaid kada yaje Amma Yana banza da zancen yakuma Dan akan Abbina bana daukan wannan so gwarama ya daina wannan saurin.

Bari naji Inda yake saimu samesa" cewar Neesah tana fidda wayarta daga qaramar Louis Vuitton handbag dinta.

Kinason Abbi ya daina kulani kwata kwata yayi fushi danine?
Kinsan halinda mahaifina zai shiga kuwa idan yaji naje gidan namiji
Gskia bazan iyaba,
Bari anjima idan Bai kiraba na sake kiransa.

Maida wayar Neesah tayi tana cewa"

Amma dai bafa lallai yazoba Sai sungama magana da Abbin hakan Kuma shine qarshen Bata komai.

A qasan maqoshi ta furta"

Allah ma yasa Abbi ya gaji da wannan zaryan ya amince musu ayi auren yanzu sbd Gaskia Ina son Zaid dina sosai,I can't live without him, duk wannan fadan danake na qarfin haline Ina tsananin sonsa gaskia.


********
_AAM's BUILDINGs_

Zaune Yake kan sofa dake makeken office dinsa hankali kwance ya jingina bayansa kadan yana sauraren Former Ambi Mukhtar Asheer mahaifin Zaid.

Gabaki daya idanuwansa dake Dan rikata wanda duk ya zubawa sbd kwarjini su ya zubawa Ambi din Yana kallonsa Yana saurare.

Da gaskiyarsa ta hakika yake sake tsaro jawabansa Dan shawo kan A MAJEED din ya amince da auren 'yayan nasu a yanzu sbd kaucewa barna tunda yaran sun matsa sunason ayi.
Amma abinda Bai saniba gameda A MAJEED shine wannan zuba Masa idon da yayi baida niyar daukan zancen ne.

Qaramin numfashi ya sauke a natse kafin ya Dan dauke kallonsa daga Ambin ya dauki wayarsa dake gefensa ya ajiye gabansa cikin nutsuwa yakuma nagowa ya kallesa yace"

Kaman yanda nafada last time dakuma farkon zuwanku neman auren maganar dai tana Nan a hakan,

Hakuri zaa cigaba dayi inshallah babu wani abinda zai faru ko biyowa Baya dangane da wata barna ko makamancin hakan...

Inayah dai tunda nace nabawa Zaid aurenta bazan fasaba kokuma sauyawa matuqar ba itace tace ta fasa Dinba kokuma wani dalilin dazai iya hanawar Kuma ba'a fatan hakan,

Dan haka Ambi Ina sake baka hakuri kuci gaba da hakuri inshallah lokacin ya kusa sbd tana gab da kammala karatun tunda duka duka shekara dayane ya rage Mata inshallah...

Amma tunda Kai kana hango wata barna da Zata iya biyo bayan rashin auren da wuri
To inaga na dakatarda haduwarsu kawai su tsaya iya waya zuwa sbd kiyayewa sai a sanarda shi Zaid din
Inayah Kuma zan fada Mata
Daga yanzu haduwarsu iya wayane ya dakata da zuwa gurinta for now,

Allah yayi Mana jagora duka.

Sake da Baki Ambi yake kallon A MAJEED din Yana sauraron bayanansa dake fitowa suna zuwa Kai tsaye,
Yasani yakuma ji wainda suka San A MAJEED din suna fadar Kai tsaye yake magana Baya wani kwana kwana ko lanqwasa Musamman zancen daya shafa 'yarsa dayake ganin baida abinda yafita.

Jin shiru yasa Ambi ya rufe bakinsa tareda sauke numfashi Yana yaqen dole yace"

Shikenan ba komai zamu cigaba da jiran tunda Shima akwai nasa programs din dazai kammala zuwa next year din
sai abin yazo musu duk a natse ma,
Allah yasa hakan shine mafi Alkhairi.

Amin" ya furta Yana kallon ruwa da aka kawowa Ambi din Bai Sha ba yace"

Me zaa kawo maka?
Any drink, coffee or something?

No,no,no I don't think i need anything
Thank you,
Ruwan ma is okay.

Daukan ruwan yayi yasha kadan tareda ajiyewa suka Dan fada wata firar daban wadda Bata shafi iyalansuba ta business industries ahakan har ya Dan ja lokaci sosai sai lokacin tashinsa suka fito tare ya maidasa har masaukinsa kafin ya wuce gida da driver dinsa.


Da daddare zaid yazo masaukin dadynsa Dan jin yanda aka Kai qarshe Dan Shikam ma wlh yanzu yafara gundura da qaidan abbin Inayah

Lokacinda dadyn Zaid ke yiwa Zaid bayanin komai Shima sai alokacin yake bayyana zallar bacin ransa da yanda A MAJEED din yaketa ja musu Rai akan 'yarsa saikace itace 'yar datafi kowa gata a duniya,
Saikace shine kadai Mai arzikin dayake da 'ya.

Cikin damuwa Zaid yace"

Dad inason Inayah sosai Amma gskia bazan iya wannan hakurin ba,
Is either ta dagawa babanta hankali akaina kokuma na barta sai ranarda Abbin nata ya tashi aurar da ita Amma gskia zan nema wata yanzu.

Cikin takaici dadynsa yake kallon bakinsa dake magana yace"

Bakada hankali ko?
Kasan me ake nufi da auren connection kuwa?
Duk da connecting naku akaiba kune kuka hadu da juna da kanku Amma wannan auren shine yanzu kowa keson ace 'yayansa sunyi wato auren arziki da samun connections.

Duk tarin arzikinsa da uban dukiyar daya tara 'yarsa 'daya,
Hakama Bayada Mata bare asaka ran zai Kuma haihuwar wasu 'yayan,
Duka wannan arzikin da dukiyar 'yarsa yake tarawa Dan haka duk Wanda zai aureta shine Mai babban rabo tunda 'yar tasa mace ce wani abun dole saidai mijinta,

Ahakan kake maganar ka nema wata ka bar Inayah din?

Ka kuwa San waye A MAJEED da abin daya mallaka?
Ka kuwa San tarin arzikin dayakedasu a Nigeria ma kawai?

To idan kanka ya daina lissafi Bari na maka budaddiyar wasika,
Idan ka rabu da Inayah wlh ka tabbatada wadda zaka kawo mahaifinta yafi A MAJEED Jan wuya,

Dama ba sonta kakeba dakaketa ikirarin bazaka iya rayuwa babu ta ba,zaka mutu idan baka sametaba,
Nonsense,
Uban me kakesha da duk kabi ka dagawa mutane hankali akan son auren yanzu?
Duk ma abinda kake biyewa su Sufian suna baka kanasha da kabi duk da rikice da Neman mace gwara ka daina Sha sbd Ni Future dinka tsayayya nake hango maka,

Duk tarin nawa arzikin danakeda kaima kakesa nafison ka hada Dana uban matarka koina yazama kanada connections dinsa da tarin arziki
So idan ma ki fita hankalinka better cm back to your damn senses
Neman Mata ko buqatan mace bashine naka ba yanzu.

Duk abinda dad din yafada Masa yasan hakan ne Amma dai gaskia shi yanzu mace yake buqata matuqa,

Kuma kaman dai yanda dad yafada akan abinda yake ikirari kan son dayakewa Inayah gaskia ne
haryanzu tsananin son Inayah na Nan daram a ransa saidai Shima tasa buqatar Gaskia ce Kuma tabbas wasu abubuwan sukesha taredasu Sufian.

Dan haka zai sama Inayah suyi magana dole ita kadaice Zata iya saka Abbinta yabarsu suyi aure yanzu.

Koda yakoma gida Bai kirata ranarba sai washe gari da safe.

Tana ganin kiransa lokacin tana taredasu Abbi da umma kan dining Dan haka tsulum ta miqe tareda cewa ta koshi tabar dining din.

Umma ce kawai tabi bayanta da kallo Shikuwa abincinsa yake cigaba daci hankali kwance bawai Kuma Dan Bai fahimta komaiba.

Fada sosai tayi Masa a wayar Shima farko fadan yayi Mata kafin ya sauko Yana rarrashinta.

Kashe wayarta tayi itama tareda jefarwa tana cewa"

Saina Rama Nima kaji yanda naji.

Bai sake kiraba kaman ita yanda tayita yi daya kashe Mata wayar

Sai abin yamata ciwo itama ta sharesa badan tasoba.

Sanin Inayah nayi Masa tsananin so yasa ya daga mata hankali kwana biyu da rashin Kira kafin Kuma daga baya qarshe Bai Ankara ba yafara mata yar barazanar auren wata kafin tagama nata karatun saiyayi ta biyu da ita.
#MAMUH#
#RIBA BIYU/MARRIAGE
#A MAJEED/AYSHATOUH INAYAH/LOVE/ROMANCE


*_FOR MORE PAGES KUYI FOLLOWING DINA A AREWABOOKS@Mamuhgee_*


_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

_BREAKDOWN OF ZAFAFA BIYAR VVIP SINGLE PAID BOOK_

_4

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login