Showing 1 words to 3000 words out of 32935 words

Chapter 1 - KADDARATA

Start ads

11 Sep 2025

69

Middle Ads


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[20/08, 2:11 am] Shuraihu Usman: 🌸🌸🌸🌸🌸
*ƘADDARA TA*
🌸🌸🌸🌸🌸


Na
*Jiddah S Mapi*


*Chapter 1*


~Garin yomen babban gari ne me ɗauke da yaruka da ƙabilu dayawa, amma yawanci kabilar fulani sunfi yawa, yau an wayi gari da ruwan sama, tun safe ake ruwa har zuwa yanzu ruwa bai tsaya ba, hakan yasa mutane basu fito ba kowa yana gida sai ɗaiɗaikun mutane da suke fita sabida uzurin dole, gidan sarkin yomen babban gida ne wanda yake ɗauke da family's dayawa, an ƙawata gidan da kayan sarauta na zamani dana gargajiya, sarkin garin sunanshi ABDALLAH ya kasance mutum ne wayayye wanda yake gudanar da sarauta cikin wayewa da sanin ya kamata, matarshi sadiya kyakkyawar macece me tsananin kama da larabawa, mutane dayawa suna mata kallon balarabiya har sai ta buɗe baki tayi magana da hausa zaka gane ba balarabiya bace, bafulatana ce ta asali, shima sarki hausa fulani ne, kyakkyawa ne shima ajin karshe amma shi chocolate color ne ita kuma fara ce dal, bari mu leƙa gidan sarki muga meke faruwa a wannan gari da masarautar, kyakkyawan main parlour ɗinsu ɗauke yake da furnitures farare sal royal ne komai anyi adon sarauta a jikin komai na ɗakin, busy falon yake kasancewar yau ɗansu dake karatu a kasar italy zai dawo hakan yasa suke shirye shirye kamar yadda suka saba idan zai dawo, kyakkyawar matar sarkin ce ta fito sanye da riga da skirt na atamfa tayi bala'in kyau tsayawa tayi hanunta rike da bowl cike da flower ganin yadda mai martaba da kanshi ya zage yana shirye shirye yasa tazo ta tsaya a gabanshi ta zuba mishi kyawawan idanunta kallonta yayi sai kuma yaci gaba da aikin yace "ya dai? kin sani a gaba kina min kallon soyayya?"
ɓata rai tayi tace "waya faɗa maka kallon soyayya nake maka? sau nawa zan faɗa maka ka daina aikin nan kaifa sarki ne ya kamata ka gane, idan bayinka suka shigo suka ganka a haka ya kake so su fara kallon mu?"
murmushi yayi ganin yadda ta ɓata rai yace "to na daina"
zama yayi akan sofa yana kallonta, fara aikin tayi wani kyakkyawan matashi me nutsuwa sosai ya fito daga ɗaki yana mika tareda yin salati, sanye yake da farin siririn glasses a idonshi jallabiya ne me taushi a jikinshi da alama yanzu ya tashi, gashin kanshi kamar na larabawa ga kuma sajenshi da yake a kwance luf, a hankali ya karaso, ganin shirye shiryen da akeyi cikin nutsuwanshi yace "ABI meyasa ake shirye shirye waye zai zo?"
kallonshi yayi cikin kaunan da yake yiwa yaron sabida nutsuwanshi yace "SULTAN ne zai dawo"
da sauri ya cire glasses ɗinshi ya kalleshi da idanunshi masu kyau yace "sultan zai dawo yau?"
jijjiga kai yayi yace "yes sabida kuna bacci ne yasa ban faɗa muku ba amma ya kiramu ya kammala secondary yau zai shigo nigeria harma sun tashi"
da mamaki yace "ya Allah ai ban sani ba da zanzo na tayaku"
kallon matar yayi yace "AMMI sannu da aiki"
murmushi tayi tace "yawwa KASEEM"
cikin nutsuwa yazo ya karɓi plate na hanunta yace "kawo na aje miki"
kaiwa yayi dinning sannan ya dawo yace "sai kuma me za'a tayaki?"
girgiza kai tayi tace "karka damu mun gama duka da Abbinku"
ya sunkuyar da kai yace "to ammi bari naje ɗaki na shirya sai muje ɗauko sultan ɗin"
tace "karka damu kaseem ana ruwa fa har yanzu ruwa bai tsaya ba"
yana tafiya yace "ba zan iya zama a gida kanina ya dawo ba dole naje ɗaukoshi"
murmushi tayi, muryan mace ne daga stair ta buɗe murya tace "waye zai dawo yau ya kaseem?"
kallonta yayi sanye take da riga da wando na bacci gashinta ma bata rufe ba, kyakkyawa ce sosai da sosai tana matukar kama dashi da kuma Ammi, farace sal da gashi me tsayi yace "sultan ne"
tsalle tayi tace "wayyo yau sultan zai dawo?"
murmushi kawai yayi ya wuce ba tareda ya kara mata magana ba, ammi wacce take gyara labule tace MEENAT zoki rikemin stool ɗinnan kada na faɗi"
da sauri ta sauko daga stair ta rike mata, shiri yayi ya fito sanye da shadda yayi bala'in yin kyau sanye yake da siririn glasses ɗin da alama baya rabuwa da glasses, zai fita sukaji tafi, da sauri ya juyo domin yasan mutum ɗaya ne yake tafi a gidan idan zaiyi magana, subhanallah tsarki ya tabbata ga ubangijin da yake halitta, wani kyakkyawan matashi ne da alama shine kaninshi na dab yayi bala'in kyau cikin yadi black color tamkar balarabe ga wani kwantaccen gashi dake kanshi me yawa, murmushi ammi tayi ganin yana saukowa tace "ABDULHAMEED"
a hankali ya lumshe ido ya gama saukowa, kallonshi yayi, kaseem ɗin yace "hameed zamu je ne?"
gyaɗa kai yayi alaman eh, murmushi yayi yace "to taho mana muje"
a hankali ya fara takowa, ɗauke kai ammi tayi tana share hawaye, Abi ne yayi mata alaman ta daina kuka, da sauri ta share hawayen, itama meenat jikinta yayi sanyi ta sunkuyar da kanta, hanunshi kaseem ya rike suka fita, ruwa ya tsaya gari yayi haske hakan yasa yanayin garin yayi daɗi sosai, jerin manya manyan motocin da aka shirya domin ɗauko kaninsu sultan suka nufi wajen, dogari da masu gadin gidan duk sun shirya domin ɗauko kaninsu hameed, cikin girmamawa suka fara russunawa kasa suna aika gaisuwa tareda kirarin cewa "takawarku lafiya YARIMA HAMEED da yayan yarima, yarima me jiran gado"
ɓata rai yayi sabida ya tsani ace mishi yarima"
murmushi kaseem yayi ganin yadda ya ɓata rai, buɗe motan akayi musu suka shiga zazzafan tsadadden motan da suke fita dashi, convoy suka haɗa suka fita a gidan, kallonshi kaseem yayi ganin yadda ya ɓata rai sabida ance mishi yarima me jiran gado ya rike hanunshi a hankali ya murza kyawawan fararen yatsunshi da suke da laushi kamar hanun mace, ya kalli kyakkyawan fuskanshi ji yayi sonshi yana karuwa a ranshi, a rayuwa babu abinda yake so kamar hameed kaninshi, idan yaga hameed cikin damuwa sai yaji komai na duniya ya fita ranshi, nutsuwan hameed yasa duk cikin yaran gidan babu wanda yake so kamar shi, a hankali yace "hameed kar kayi fushi dan ance maka yarima Allah ne ya baka wannan matsayin kaga duk da na girmeka Allah ya zaɓeka ya baka matsayin yarima sannan nasan bakaso ace yarima me jiran gado sabida kana ganin kamar Abi zai mutu ne ko?"
a hankali ya gyaɗa kai yana zubawa yayanshi da yake jin tsananin sonshi a ranshi ido, yace "karka damu kowa da lokacinshi idan lokaci yayi babu abinda zai hana mutum mutuwa, sannan matsayin yarima da kake dashi bashi zaisa abi ya mutu ba domin ka zama sarki kuma bashi zaisa abi ya rayu ba domin kada ka zama sarki, sabida haka ka saki jikinka ka daina sa komai a ranka kaji?"
a hankali ya gyaɗa kai, murmushi kaseem yayi yace "yawwa kanina smile for me"
a hankali ya saki wani smiling da yasa kyawunshi kara bayyana, ga wani lotsawa da gefen kumatunshi yayi, ya lumshe kyawawan idanunshi yana kallon titi, har yanzu ya kaseem yana rike da hanunshi.

babban airport na garinsu suka shiga, ana ganin motocin gidan sarki ne aka basu hanya, tun daga wajen mota aka shimfiɗa red carpet har zuwa bakin jirgin da yanzu yayi landing, basu fito daga motar ba dogali da security's ne suka fito suna jiran fitowanshi, shine first na fara fita, yayi masifan kyau cikin baƙin jinx da riga polo da facing cap, yana kama dasu shima sosai da sosai, saide shi yaro ne sabida akwai yaranta sosai a tare dashi, dube dube ya fara yana karewa kowane mota kallo, turo karamin bakinshi yayi ganin babu ƴan uwanshi ko ɗaya da suka zo sai tarin dogarai da masu tsaron gidansu, ɓata rai yayi, ya kaseem da sauri yasa hanu zai buɗe motan hameed ya rike hanunshi, kallonshi yayi da mamaki girgiza kai yayi alaman kada ya fita ya ɗan dakata tukunna, yace "bakaga ya matsu ya ganmu bane?"
taɓe baki yayi, saida suka ɗan ɓata lokaci kafin kaseem ya janye hanunshi ya buɗe ya fita, shima hameed fita yayi ya harɗe hanu a kirji yana kallon sultan, waro ido yayi yace "ya kaseem? yaya yarima?"
da wani irin gudu yazo ya rungumesu a tare, cikin kewansu yace "i miss you all"
murmushi ya kaseem yayi sannan ya zameshi daga jikinsu yace "let's go home ammi da abi sun damu su ganka"
murmushi yayi yace "to ai har nayi expecting babu wanda yazo a cikinku"
kallon hameed yayi da suka shiga mota yace "amma nayi mamaki da yaya yarima yazo"
ɓata rai yayi, jikinshi a sanyaye yace "sorry yaya hameed"
duk sukayi shiru, tafiya sukayi zuwa gida, sai hura algaita ake, shi kuma sultan sai farin ciki yake ya dawo gida yanzu zai fara zuwa wajen abokanshi zai samu sakewa ba kamar acan da Abi yasa ake tsareshi babu inda ya isa yaje ba, suna shiga Ammi ta rungumeshi kanƙameta yayi sosai yace "oyoyo Ammi"
Abi dake tsaye ganin ba zasu saki juna ba yace "to sakemin matata hugging ɗin ya isa haka"
dariya yayi ya saki ammi, rungume Abi yayi yace "i miss you so much Abi"
yace "i miss you too my son"
meenat ta baya ta rungumeshi tace "welcome sultan bro"
yace "dallah sakeni ko so kike mu faɗi?"
tace "wallahi ba zan sake ka ba nayi kewarka"
tsaki yaja, ammi tace "zaku fara ko?"
sakinshi tayi ammi tace "to dama babu wanda yayi breakfast a gidannan sai kuzo muci abinci"
kalle kalle sultan yake yi, ammi tace "me kake nema?"
yace "ina....?"
shiru yayi ganin kallon da abi ya mishi, a hankali ya sunkuyar da kanshi, itama ammi ta ɗauke kai daga kallonshi kamar yadda ya kaseem ya ɗauke kai, dinning suka nufa jikin sultan a mace ya zauna suka fara cin abinci babu wanda ya kara magana a cikinsu har suka gama, hameed ne ya fara tashi cikin kulawa kaseem yace "ka koshi?"
gyaɗa kai yayi, yace "ka tabbata?"
ya kara gyaɗa kai alaman eh, cikin sanyinshi da nutsuwa ya fara tafiya, stair case ya haura ya shiga ɗakin da yake mamakinshi, zama yayi akan royal sofar da yake ɗakin, masha Allah ɗakin yayi masifan yin kyau ga wani maƙeƙen royal bed nashi, kamar parlour haka bedroom yake duk fararen funitures ne, lumshe ido yayi ya ɗaga kanshi sama yana tunani, turo kofan akayi ya buɗe ido a hankali ya kalli wanda ya shigo, ya kaseem ne rike da plate na yellow juice a hanu, zama yayi a hanun sofan kusa da hameed ɗin yace "karɓi kasha"
a hankali ya girgiza kai alaman A,a ba zai sha ba, haɗa fuska ya jabeer yayi yace "ka karɓa nace ina wasa da kaine?"
a hankali ya karɓa yasa a baki yasha kaɗan, cikin rashin dariya yace "shanye duka"
girgiza kai yayi sannan ya marairaice fuska alaman cikinshi ya koshi, yace "ka shanye nace"
da sauri ya shanye domin yana tsoron ɓacin ran ya jabeer ɗin, karɓan glass cup ɗin yayi ya ɗaura akan plate ɗin, ya tashi ya buɗe side drower ya ɗau wani kwalin magani karami yazo ya buɗe fridge ya ɗauko allura da ruwan da yake sawa a fridge sabida kada ya lalace, zuwa yayi yaja ruwan cikin sirinji, idanun hameed ya cika da hawaye ganin abinda yafi komai tsana a duniya wato allura, marairaice fuska yayi kamar zaiyi kuka yake girgiza kai alaman baya son allura, murmushi kaseem yayi yace "kai ko hameed shagwaɓanka yayi yawa, allura kullum ana cikin yi maka amma har yanzu baka daina tsoro ba oya tashi"
kin tashi yayi, ya ɓata rai yace "ka tashi nace"
a hankali ya tashi yana rufe ido, cikin tausayinshi ya ɗaga riganshi, sauke wandon yayi kaɗan, ji yayi ya rungumeshi ya rufe ido, haka ya saba yi idan za'a mishi allura, alluran yayi mishi kanƙameshi yayi sosai har ya gama kafin ya sakeshi, yace "sorry"
a hankali ya koma zai zauna rikeshi yayi yace "ka kwanta a gado dan nasan yanzu zakayi bacci"
rikeshi yayi ya taimaka mishi ya kwanta a gadon, duvet ya rufeshi dashi sannan ya kashe ac sabida sanyi, juyawa yayi zai tafi ya rike hanunshi, jikinshi yayi sanyi sosai a hankali ya juyo yana kallonshi, so yake yayi bacci dan sai lumshe ido yake, gashi ya rike hanunshi baida alaman saki, dawowa yayi ya zauna a kusa dashi, pillow ya gyara mishi sannan yasa hanu akan lallausan gashinshi ya fara shafawa, rufe ido yayi jin ya kaseem yana shafa mishi kanshi haka ya saba bacci sai yaji hanun mutum a kanshi yake iya bacci cikin kwanciyan hankali, saida yaji numfashinshi ya canja alaman bacci me nauyi ya ɗaukeshi kafin ya zame hanunshi a hankali ya gyara mishi duvet ɗin ya tashi ya fita daga ɗakin.

Ammi tayi tagumi ta zauna tunani kawai take batama san ana knocking ba, kaseem daya fito yanzu ya kalleta sannan ya kalli kofan da ake knocking da sauri yaje ya buɗe, baiwa ce daga cikin bayin gidan, durkusawa kasa tayi tace "Allah ya taimakeka yayan yarima dama sako aka kawo wa mai martaba"
kallonta yayi yace "wani saƙo?"
tace "wani mutum ne ya bani wannan yace na bashi"
karɓan takaddan hanunta yayi yace "to mun gode"
ganin tana jiran ya tafi kafin ta tashi yace "tashi karki damu"
tashi tayi ya shiga ciki, kallon Ammi yayi wacce ta dawo daga duniyar tunanin yace "ga sako an kawowa Abi"
karɓa tayi ta kalli takaddan buɗewa tayi ta karanta sai kuma ta ɗago kai ta kalli ya kaseem daya buɗe ɗakinshi zai shiga, saida ta jira ya shiga sannan ta yaga takaddan, sultan wanda ya fito yana waya kallonta yayi da mamaki, saida ya gama wayan yazo ya tsaya gabanta yace "Ammi meyasa kika yaga sakon da aka kawowa Abi?"
wani kallon da tayi mishi yasa yayi shiru bai kara cewa komai ba, tashi tayi zata tafi tace "matukar baka san yadda zaka iya da bakinka ba zakasha wahala a rayuwa"
shiru yayi ta wuce ta barshi a wajen, juya maganan yayi a ranshi sai kuma ya taɓe baki ya zauna akan sofan yana kara kiran wayan ana receiving yace "yawwa baby kina jina? yanzu na dawo nigeria ba koda yaushe zamu rinƙa waya ba"
da sauri ya katse wayan ganin ya kaseem ya fito sanye da labcoat yasa telescope a wuya, yayi bala'in kyau da uniform na doctor, kallonshi yayi cikin nutsuwa da sanin ya kamata yace "dawa kake waya?"
da sauri yace "da abokina nabil"
baiyi magana ba kawai ya wuce yana amsa call da alama kiranshi ake na gaggawa, hamdala sultan yayi yasan ba dan yana sauri ba saiya karɓi wayan ya duba.
motarsu me kyau wanda yake zuwa asibiti dashi ya shiga, da kanshi yake driving bai yadda driver yana kaishi asibiti ba, a kullum shi yake kai kanshi, special hospital ne me matukar kyau da kuma tsafta asibiti ne kamar a kasar waje kwararrun likitoci yake dasu a asibitin, mallakinshi ne domin da kanshi ya buɗe DR K yayi matukar suna a garin sabida kwazonshi yana taimakawa mutane dayawa bai ɗauki kanshi komai ba duk da matsayin da Allah ya bashi na babban ɗan sarki, a rayuwarshi babu abinda yake kauna kamar family ɗinshi zai iya yin komai akan family ɗinshi, musamman hameed wanda yakejin har kyautan ranshi zai iya yiwa hameed, idan kanaso kaga ɓacin ranshi to ka taɓa hameed ya haɗiyi yaron a ranshi, shekaru dayawa ne tsakaninsu domin ya girmewa hameed nesa ba kusa ba, akwai mutum ɗaya tsakaninsu wanda ya jima da rasuwa, yana biyan ma'aikatanshi fiyeda aikin da sukeyi, kasancewar babu abinda zai bukata

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login