Showing 6001 words to 9000 words out of 32935 words
ɗan faɗa sai gashin ya kara zubowa ya rufe fuskan, hameed dake tsaye yana kallonsu kaseem ya kalla, yace "taimaka min na ɗaura mata bandage"
zama yayi kusa da ita, zai rike hanunta yaga kaseem ɗin ya saketa ta faɗa jikinshi, ji yayi kirjinshi ya bada wani sautin da baisan na mene ne ba, ji yayi ya rasa duk wani tunaninshi na lokaci ɗaya, kaseem yace "gyara mata gashin"
a hankali ya dawo hayyacinshi kame gashin yayi ya mayar baya, ɗaura bandage ɗin yayi saida ya gama yace "yawwa kwantar da ita"
kwantar da ita yayi akan gadon kaseem yasa mata drip ɗin da zai kara mata karfin jiki, tashi hameed yayi zai tafi kaseem yace "ka zauna kusa da ita mamanta ta rasu tareda kaninta kuma inada tabbacin harda mahaifinta domin gawa huɗu ne a motan duk da driver, tana fizge fizge dole a samu me zama kusa da ita zanje ayi shirya gawan kafin ta tashi"
shiru yayi ya zubawa kaseem ɗin ido har ya gama maganan, bai jira reaction nashi ba ya fita ya rufe kofan, shiru yayi yana kallonta ji yayi tana bashi tausayi tunda mamanta da babanta sun rasu bayaso yaga mutum maraya sai zuciyanshi ya karaya.
Kaseem yasa aka shiryasu suna jiran tashinta kawai domin ta faɗi inda ƴan uwansu suke, yayi tagumi ya gaji gashi har yanzu ya kaseem bai shigo ba so yake yaje yayi bacci har kanshi yana ciwo sabida ɗan zaman da yayi, a hankali ya fara motsa hanunta kallonta yake tana buɗe ido har ta gama buɗewa ta kalleshi, kallon drip ɗin tayi sai kuma ta kara kallon ɗakin da take ciki, fizge drip ɗin tayi da ihu tace "mama, baba, Aliyu"
toshe kunne yayi sabida baison ihu, grey eyes nashi ya zuba mata yana kallonta, dira tayi daga gadon zata fita a guje, riketa yayi sabida tuna maganan ya kaseem kada ya bari ta fita, tana kwace kanta tace "ka sakeni nikam ka sakeni mama!!! baba!!!"
danneta yayi da karfi ta kasa ko motsi sai ihu take, akan gadon ya komar da ita ya kwantar da ita sannan ya zuba mata ido, tana kallonshi tace "waye kai? meyasa bakayi magana ba?"
ɗauke kai yayi daga kallonta amma har yanzu bai saketa ba, ta fara tsorata dashi tace "kai ba doctor bane kuma ban sanka ba, meyasa ka rikeni? ka sakeni naje nayi wajen mama"
bai saketa ba, shiru tayi ganin baida niyan cutar da ita, numfashi ta fara maidawa a hankali ta jingina kanta da bangon gadon tana kallonshi yadda ya kauda kai daga kallonta, a haka ya kaseem ya shigo, da sauri ya karaso yana cewa "am sorry na barka tun ɗazu wani aiki ne ya taso"
sakinta yayi ganin ya kaseem ɗin ya shigo, karkaɗe hanunshi ya fara wai sabida datti, sai kuma ya juya zai fita ya kaseem yace "hameed"
tsayawa yayi yace "dawo"
dawowa yayi, ya kaseem yace "ki faɗi gidanku da ƴan uwanku sai hameed ya kaiki ki kirasu suzo su karɓi gawan"
wani sabon kuka ne ya kwace mata, har tayi me isanta kafin ta share hawaye tace "banada kowa sai mama da baba da kanina Aliyu, baba yace baida dangi itama mama haka yauma barin garin zamuyi sabida baba baida lafiya kuma mai gidanmu yace idan bamu biya kuɗin haya yau ba zaisa a watsar mana da kayanmu waje hakan yasa baba yace mu koma kauye da zama shine a hanyan zuwa mukayi hatsari"
shiru sukayi suna kallonta su duka, tausayinta ya cika musu zuciya, kaseem ne yayi karfin halin cewa "kenan babu wanda za'a kira?"
jijjiga kai tayi, cikin tausayi yace "to bari mu tara mutane aje ayi jana'iza"
kanta kasa tana kuka me cin rai, tun kukan yana fita har muryanta ya dishe, kallon hameed yayi wanda ya kasa ɗauke idonshi a kanta, yace "muje hameed"
a hankali yabi bayanshi koda zasu fita juyowa yayi ya kara kallonta, fita sukayi aka kaseem yasa aka fito da gawan, kwantar dasu akayi a kasa kafin mutane su taru ya koma ya fito da ita domin tayi musu addu'a, babu takalmi a kafarta ga kanta dake ɗaure da bandage ga kuma idonta da suka koma kamar jan gauta, a hankali ta zauna a gabansu ta haɗa hanu biyu ta ɗaga sama, addu'a ta fara da larabci kamar ba zata tsaya ba, kowa saida ya tausaya mata, da haka har ta gama ta tashi ta juya baya, hameed ne yaji zuciyanshi yayi nauyi, ɗaukansu akayi aka fita dasu, a hankali yazo inda take ya rike hanunta, bata kalleshi ba amma tana ji yana murza yatsunta cikin nashi, kaseem ɗauke kai yayi daga kallonsu, har akaje aka birne suka dawo, cikin sanyin jiki ta janye hanunta daga nashi, ɗan durkusawa tayi cikin girmamawa ta cewa kaseem "na gode sosai da taimakon da kukamin Allah ya saka da Alkhairi Allah ya biyaka da aljanna, ni zan tafi"
tashi tayi zata tafi hameed ya kalli kaseem girgiza mishi kai yayi alaman kada ya bari ta tafi, kaseem yace "tsaya"
taki tsayawa tace "babu abinda zan tsaya yi taimakon da kukamin na gode"
kaseem yace "kinada inda zakije ne? ko a titi zaki rinƙa yawo ba tareda sanin inda zakije ba?"
kasa tafiya tayi, sai kuma tace "koda banida inda zanje asibiti ba wajen zamana bane"
yace "idan kin yadda muje gidanmu na tabbata amminmu zata rikeki sabida tanason rike marainiya"
shiru tayi tana tsoron binsu kuma aki karɓanta a gidansu, yace "idan kin amince to"
a hankali ta juyo ta share hawaye idanunta sunyi mata nauyi so take ta huta koda na ɗan lokaci ne, tace "na amince kuma na gode"
murmushi hameed yayi, kaseem ya kalleshi rabon da yayi irin murmushin ya jima, yace "ina zuwa"
office ya nufa ya ɗau makulli da laptop nashi da sauran kayan bukata ya rufe sannan yazo yace "muje"
cikin ladabi tace "to"
tafiya sukayi, gani tayi sun buɗe mata wani lafiyayyen mota, a hankali ta ɗago ta kalleshi cikin nutsuwanshi yace "shiga mana"
shiga tayi ta zauna a baya, shi da hameed suka zauna a gaba, jan motan yayi suka tafi, kallon titi take tana wasa da yatsunta, ta kasa sakin jiki domin bata saba da shiga mutane ba, bacci takeji a hankali ta fara rufe ido, baccin da bata shirya mishi ba ya ɗauketa, hameed ta cikin madubin ya saci kallonta, ganin tana bacci ya zuba mata ido yana kare mata kallo, murmushi ne akan face nashi, kaseem ya kalleshi sai kuma ya ɗauke kai yaci gaba da driving yana kula dashi har suka isa gida yana kallonta ta madubi, makeken gate ɗin aka buɗe musu ya shiga, a compound yayi parking sannan yace "ke? ke? tashi mun iso"
a firgice ta buɗe ido tace "mama!!!"
shiru yayi ganin yadda ta firgita, cikin tausayi yace "mun iso fito"
bin gidan ta fara da kallo, ganin gidan sarki ne yasa jikinta yayi sanyi ko dai sun kawota gidan sarki ne sabida ba zasu iya kaita gidansu ba?
hameed ne ya fita, kaseem ya buɗe mata marfin a hankali cikin tsoro ta fito tana kallon dogalin da yazo da bulala a hanu yana russunawa yana yiwa su hameed ɗin kirari, hameed yayi mata alaman muje, kin tafiya tayi, dogarin ya ɗaga bulala ya nunata dashi yace "hattara ƴar talakawa yarima hameed ke miki magana"
a tsorace taje bayanshi ta ɓuya domin ta tsani ko ganin bulala ne bale ace za'a watsa mata, murmushi yayi suka nufi ciki, a ranta tace "ashe yaran sarki ne"
sunyi knocking ammi ce ta buɗe kofan turus ta tsaya tana kallonsu, kaseem yace "zamu iya shiga?"
matsa musu tayi suka shiga, da ido yarinyar yake bin ko ina da kallo, a ranta tace "koda ta amince ba zan iya zama ba a wannan gidan ban saba da irin wannan gidan ba nafi sabawa da gidanmu wanda ɗakina dana Aliyu kanina katifa kawai muke dashi da kujeranmu guda ɗaya, sannan na saba da lalataccen gidanmu wanda muke zaman rufin asiri a cikinta, na saba da talauci ba zan iya zama a wannan kuɗin ba"
ji tayi kaseem yana bawa ammi amsan tambayan da tayi na wacece ita?
shiru ammi tayi jin abinda suka faɗa, sai kuma tace "amma kaseem...."
hanu ya ɗaga mata yace "na san me martaba ba zai taɓa yadda a kyaleta ta tafi ba domin koda yaushe shi yake faɗa mana kada mu kyamaci kowa musamman talaka"
tayi shiru tana kallon yarinyar data sunkuyar da kai kamar ma a tsorace take, tace "ya sunanki?"
shiru tayi ta kara cewa "ya sunanki?"
ganin batama san ana mata magana ba ta taɓata, firgigit tayi tace "wayyo"
hameed kallonta yake yadda take tsorata yafi komai tsaya mishi a rai, tace "ki nutsu babu me cutar dake a cikinmu ya sunanki?"
a hankali tace "ANEETA"
murmushi tayi tace "sannunki Allah yaji kan iyayenki"
tace "ameen"
meenat data shigo ta aje jakanta tana kallonta tace "Ammi wacece wannan?"
tace "sunanta aneeta kaita ɗakinki tare zaku zauna tayi wanka taci abinci ta huta"
tace "to"
hanunta ta rike tace "muje"
tashi tayi a yanayinta na tsoro take binta, stair da zasu hau tayi saurin yin baya taki tafiya, minat tace "muje mana"
tana kallon stair idonta cike da tsoro tace "ba zan iya ba"
dariya minat tayi sosai Ammi tace "ba dariyanta zakiyi ba riketa zakiyi sabida ba lafiyane da ita ba"
riketa tayi tace "to muje"
damke hanunta tayi suka fara hawa, ihu tayi kafanta yana rawa tace "zan faɗi"
minat tace "ba zaki faɗi ba"
da kyar ta haye da ita, kallon kasa tayi sai kuma taji jiri yana ɗibanta tace "ina jin jiri"
minat tace "ki daina kallon kasa"
tace "to"
hanunta ta rike suka tafi ɗakinta, a bakin gado ta zauna tayi shiru, minat ce ta shiga ta haɗa mata ruwan wanka tazo tace "muje kiyi wanka"
tace "to"
tashi tayi cikin tsoro ta bita, nuna mata yadda zatayi wankan tayi sannan ta fita, cikin rashin iyawa ta fara wankan bata taɓa ganin wannan abin ba ko a tv bata kallo bale tasan yadda ake amfani dashi, saida ta gama kafin ta fito ɗaure da towel kanta yana yoyon ruwa, minat wacce ta cire mata kayan da zata sa tace "kin fito?"
cikin sanyin muryanta tace "eh"
dryer ta ɗauka tace "bari na busar miki da gashin"
kallon abin take babu ko kyafta ido da alama fa yau ta fara gani, jonawa tayi zata kai kanta da sauri tayi baya, minat tace "busar miki da kai zaiyi"
tace "amma ba zaiyi zafi ba?"
tace "babu zafi"
dawowa tayi tana kallonta ta fara busar mata da kan, tace "yawwa ya bushe saura kisa kaya"
kayan ta karɓa tasa yayi mata kyau dogon riga ne na kanti ta bata hula tasa a kanta da tayi mata parking na gashin, tace "bari na kawo miki abinci"
fita tayi jim kaɗan ta dawo da katon plate, aje mata tayi tace "sauko kici"
girgiza kai tayi tana hawaye tace "ba zan iya cin komai ba"
minat ta lallaɓata da kyar ta yadda taci abincin kaɗan sannan tace "zanyi bacci"
tace "ki kwanta"
kwanciya tayi a kasa, da sauri tace "tashi ki hau gado"
tace "a,a anan ya isa"
tace "dan Allah ki tashi"
a hankali ta tashi ta hau gadon ta takura kanta ta kwanta ta rufe ido, wahallallen bacci ya ɗauketa.
Ammi ta kalli kaseem da zai tafi tace "baka tunanin zaka iya kuskuren kawo wata gidannan?"
yace "babu kuskuren da za'a kara yi a gidannan wanda ya kai naki"
tace "kaseem kasan fa..."
hanu ya ɗaga mata yace "dan Allah, dan Allah ammi ki kyaleni banaso ina faɗa miki magana mara daɗi"
ta goya hannaye a bayanta tace "shikenan kaseem komai kayi daidai ne"
tafiya yayi, hameed ya jima da komawa ɗaki, magani kaseem ya bawa minat yace idan ta tashi a bata tasha.
_Jiddah Ce..._
08144818849
[20/08, 2:11 am] Shuraihu Usman: 🌸🌸🌸🌸🌸
*ƘADDARA TA*
🌸🌸🌸🌸🌸
Na
*Jiddah S Mapi*
*Chapter 4*
~Har dare tana bacci babu wanda ya tasheta, sultan dake zaune a dinning suna cikin abinci tare yace "minat ya akayi bata tashi ba har yanzu? ko dai ta mutu ne itama?"
hameed wanda yasa abinci a baki kwarewa yayi jin abinda sultan ya faɗa, ruwa kaseem ya mika mishi, karɓa yayi yasha sannan yace "sultan ka rinƙa faɗan alkhairi ko kuma kayi shiru"
yace "to yaya"
a hankali take takowa tana rike karfen gam gam da iya karfinta, rufe ido tayi sabida tana tsoron abin sosai, minat data kula da ita da sauri ta tashi, missing step tayi zata faɗi duk suka waro ido a tsorace harda me martaba, minat ce tayi gudu ta riketa, kankame minat ɗin tayi sosai taki buɗe ido, karasa sauka sukayi tare, a hankali ta buɗe idon ta sauke akan hameed dake rike da spoon cike da abinci har yanzu yana kallonta, murmushi tayi mishi me sanyi, sunkuyar da kai yayi yaci gaba da cin abincin, minat taja mata kujera ɗaya tace "ki zauna"
kin zama tayi ta durkusa kasa ta gaida Abi, cikin kulawa ya amsa sannan yayi mata ya hakurin rashi, ta amsa da Alhmdllh, yace "tashi ki zauna ki saki jikinki ki ɗauka nan gidanku ne"
shiru tayi tana durkushe, yace "tashi mana"
cikin sanyin muryanta tace "zaifi kama na zama baiwa a gidannan banida matsayin zama ƴa"
da mamaki abi yace "baiwa kuma?"
tace "eh"
yace "no kema kamar ƴa kike a gidannan bada sonki kikazo ba, kuma ke marainiya ce gaba da baya insha Allah zakiyi zama kamar kowa a gidannan ki zama me ƴanci ba baiwa ba"
tace "to idan ba zaiyi na zama baiwar ba ko ƴar aiki zan zama"
murmushi yayi yace "tashi ki zauna ko ɗaya ba zaki zama ba"
a hankali ta fara kuka, yace "share hawayenki kema ƴa ce a gidannan tashi ki zauna"
ganin dogari ya shigo kuma da bulala a hanunshi shine yayi mata tsawa ɗazu tayi saurin tashi a tsorace ta zauna tana kallonshi da manyan idanunta, abinci minat tasa mata tace "kici sai kisha magani"
ta fara ci kamar bata son ci, sultan yace "ni sunana sultan shi kuma wannan sunanshi fadeel, wannan shine babban yayanmu ya kaseem, shi kuma wannan shine yarima hameed shine magajin sarki"
kallonshi tayi ya ɓata rai yana cin abinci, saida gabanta ya faɗi ganin yadda ya ɓata rai, a hankali tace "ni sunana Aneeta"
yace "nice name unty aneeta"
abincin taci kaɗan sannan ta karɓi maganin tasha, Ammi tace "sannu Allah baki lafiya"
tace "ameen"
Abi yace "gobe za'a naɗawa hameed rawanin yarima"
tsit wajen ya zama babu wanda ya kara magana ko motsin kirki, yace "kwarai gobe zai zama cikakken yarima"
ammi jikinta ya fara rawa, tayi karfin halin dannewa tace "Allah ya kaimu"
sultan kallon kaseem yayi saide kaseem hankalinshi akan abinci ya ɗago yace "Allah ya kaimu"
kallon Ammi aneeta tayi tana ganin yadda take danne halin da take ciki, da mamaki take kallonta to ba itace ta haifeshi ba?
sultan yace "na manta ban faɗa miki ba wannan itace ammi itace ta haifemu duka banda wannan iyayenshi sun rasu ɗan kanin abi ne"
ya nuna fadeel, murmushi tayi mishi tace "sannu"
yace "yawwa"
da haka suka gama cin abincin kowa ya watse, ɗakin ta koma itada minat taga minat tana karatu murmushi tayi tace "zaki rinƙa koyamin karatu?"
tace "eh me zai hana?"
tace "na gode"
kwanciya tayi amma bacci yaki ɗaukanta sai tunani kala kala take a cikin ranta da kyar baccin ya ɗauketa.
hameed yana zaune a bakin gado yayi tagumi, turo kofan kaseem yayi a tsorace ya kalleshi sabida yasan allura zaiyi mishi, murmushi yayi yace "sannu hameed"
ɓata rai yayi dan fa shi ya tsani wannan alluran, zama yayi kusa dashi ya mika mishi hanu suka gaisa yace "congratulations in advance"
taɓe baki yayi alaman for what?
yace "zaka zama cikakken yarima gobe duk ranan da babu Abi ina alfaharin zamanka sarki"
ɓata rai yayi, yace "ka daina ɓata rai sabida Allah ne ya baka wannan matsayin"
alluran ya ɗauka yace "time for injection"
hawaye ne ya taru a idonshi ya fara girgiza kai, cikin tausaya mishi yace "sorry bro ba zaiyi zafi ba i promise"
hanu ya mika mishi alaman yayi alƙawari, sarke hanun yayi cikin nashi yace "promise"
a hankali ya tashi da kanshi yayi kasa da wandon aka mishi alluran baiyi zafi sosai ba, yace "kwanta to"
kwanciya yayi akan gadon kamar kullum shafa lallausan gashinshi ya fara har yayi bacci kafin yayi mishi kiss a forehead ya fita, ɗakinshi yaje ya zauna akan sofa yayi shiru yana tunani idonshi a rufe kamar me bacci, ajiyan zuciya ya sauke ya fesar da iskan bakinshi.
Fadeel ne kwance akan gado ya ɗaura kanshi a kafar sultan dake waya, yana jinshi yadda yake hira kamar wani babba, saida ya gama yace "sultan"
yace "yes bro"
yace "meyasa ya hameed baison zama yarima?"
taɓe baki yayi yace "kuma dole zai zama ba?"
yace "to idan baya so kada a bashi mana aba ya kaseem"
sultan pillow ya janyo ya ɗaura kanshi yace "ka samu Abi ka faɗa masa"
tsaki fadeel yaja yace "kai sai ana magana ka sakowa mutane shirme"
yace "good night"
bacci ya fara shi kuma fadeel tunani yake meyasa zasu bashi bayan ya nuna bayaso? kuma ga ya kaseem shine babba meyasa basu bashi ba? sai wanda bayaso za'a bawa?"
da wannan tunanin yayi bacci.
washe gari shirye shirye ake a gidan sarkin duk bayin gidan suna girki saura suna shirya babban wajen da ake taro a gidan, komai ya zama daidai akan tsari ga kujerun manyan bakin da za'ayi ciki harda governor, wajen zaman yarima kusa dana sarki, ciki kuma kaseem ne yake shirya hameed wanda yaki yin komai tunda yayi wanka yake zaune yaki yin komai, da faɗa kaseem ɗin ya fara shiryashi, tsadadden alkyabban da Abi ya bashi yasa mishi akan shaddan jikinshi me tsada, murmushi yayi ganin yadda golding na alkyabban yayi mishi kyau sosai, hulan sarautan yasa mishi sannan ya bashi mafici irin na sarkin, durkusawa yayi kasa yana sa mishi takalmin da yake irin alkyabban, ido ya zubawa ya kaseem ɗin yana jin sonshi har cikin ranshi, a hankali ya ɗago ya kalleshi, yace "kanina kayi kyau sosai"
a hankali ya tashi ya rungume kaseem ɗin, shiru sukayi, kaseem yaji baida niyan sakinshi janye jikinshi ya fara sai kara kanƙameshi yake, da kyar ya janye yana kallon kyakkyawan fuskanshi da yake hawaye, share mishi hawayen yayi yace "yau ranarka ce bai kamata kayi kuka ba, idan Abi ya gani ranshi zai ɓaci"
sunkuyar da kanshi yayi, sandan sarauta me tsada da kyau ya mika mishi ya karɓa, nan take wankan ya kara mishi bala'in kyau, turare me kanshi ya fesa mishi sannan yace "masha Allah