Showing 27001 words to 30000 words out of 32935 words

Chapter 10 - KADDARATA

Start ads

11 Sep 2025

76

Middle Ads

ya hakura ya tafi, yana shiga gidan tana zaune tana kuka dan tasan yau kam abinda zai hanata dakuwa a hanunshi sai ikon Allah, yace "meyasa kikaje lambun malam garba? ban hanaki ba?"
ganin yana tsaye a kanta da bulala ta kasa buɗe baki sai girgiza kai take, watsa mata bulalan yayi rike bayanta tayi ta kwala wani uban ihu kamar zata fasa kunnen mutanen kauyen, shoɗa mata bulalan yake yana cewa "ban hanaki ba?"
tace "ka hanani wallahi ka hanani yaya"
saida ya zaneta me kyau, sai birgima take a kasa tana rokonshi yayi hakuri, meenat data ɓuya a ɗaki taki fitowa tana ji tana kiranta tazo ta taimaketa ta kasa fitowa, a hankali ta leka sukayi ido huɗu da najeeb da sauri ta koma ciki tana addu'a, yace "Ameenah"
fitsari taji yana shirin zubo mata, ya kara cewa "Ameena"
tana jin Asmeeta tana cewa "wallahi tare da ita mukaje"
yace "Ameena"
jikinta yana rawa ta fito ta durkusa kasa cikin tsoro tace "wallahi hamma najeeb na rantse maka da girman Allah itace tace muje nace mata kar muje kar muje tace sai munje"
babu dariya akan fuskanshi yace "kinje ko baki je ba?"
tace "na...."
ihu tayi jin bulalan da masifan zafi, shoɗa mata yake yi tana birgima itama tana rokonshi yayi hakuri, da alama fa idan ranshi ya ɓaci baida sauki domin haɗasu yayi yana jibga yana kallon yadda gidan yake kaca kaca basu kimtsa ba suka tafi yawo saida ya musu duka me kyau suna kuka kafin yace "gobe zaku kara"
barinsu yayi a wajen, Asmeeta tana kwance a kasa har yanzu bata daina birgiman ba, meenat kuma cikin rashin sabawa da duka tace "wayyo zafi"
mimi ce tayi tagumi ta fara kuka ta ɗauko mangoro tana sha tana ce musu sannu, alwalan mangariba yayi sannan ya fita a gidan, da kyar suka tashi suka shiga ɗaki salla ma a zaune sukayi, daga nan Asmeeta taci gaba daga inda ta tsaya tana kuka.

_Jiddah Ce....✍️_
08144818849
[20/08, 2:11 am] Shuraihu Usman: 🌸🌸🌸🌸🌸
*ƘADDARA TA*
🌸🌸🌸🌸🌸


Na
*Jiddah S Mapi*


*Chapter 11*


~Tun daga ranan meenat take mugun tsoronshi ko magana yayi da sauri take amsa mishi, tareda Asmeeta suke zuwa kiwo bata taɓa yadda tayi abinda ba daidai ba sabida ɗan banzan duka yake musu daga ita har Asmeeta tsoron yin abu suke, duk da Asmeeta bata jin magana idan taji muryanshi nutsuwa take, yauma kamar kullum sun dawo kenan daga kiwon shanu suna zaune yayi sallama, da sauri meenat taje ta karɓi ledan hanunshi ta mishi sannu da dawowa, ɗakinshi ya wuce sallama akayi suka amsa yarone karami ya shigo yace "wai ana yiwa Ameena magana"
dafa kirji tayi tace "waye?"
yace "wani yaro ne wai wanda kuka haɗu yau a hanyan kiwo"
alama take mishi yayi shiru amma saida ya gama maganan, hamma ne ya fito daga ɗaki yace "kace tana zuwa"
fita yaron yayi yaje yace tana zuwa, da mamakinsu sukaga ya fita, meenat tace "na shiga uku na lalace shikenan yau kuma sai ɗan buzuna"
babu jimawa ya dawo bai mata magana ba amma tana kallonshi a tsorace har dare yayi nisa mimi tayi bacci kafin yace "Ameenah"
amsawa tayi gabanta yana faɗuwa ta fito daga ɗaki, yana zaune akan tabarma ya nuna mata gefenshi yace "zauna"
zama tayi kanta a kasa yayi shiru kamar ba zaiyi magana ba sai kuma yace "Ameena?"
a hankali tace "na'am"
yace "ɗago ki kalleni"
ɗago kanta tayi a hankali ta kalli idonshi masu kyau, sai taga ya kara yi mata kwarjini sosai, yace "Ameena inaso na aureki amma ina tsoron ranan da zaki tuna komai da kika manta watakila a lokacin na riga nayi sabo dake sabon da bazan iya rabuwa dake ba, ni maraya ne Ameena kuma banida kowa sai Asmeeta da mimi su kaɗaine rayuwata sai kuma ke da kika shigo rayuwarmu, wallahi Inaso na aureki amma ina tsoron ranan da zaki barmu"
murmushi tayi ta ɗago kanta tace "hamma najeeb koda na tuna komai na rayuwata ba zan taɓa iya rabuwa daku ba, Asmeeta ta zama tamkar ƴar uwata da muka fito ciki ɗaya rabuwa daku zaimin wahala, idan har zaka aureni zanfi kowace mace farin ciki a wannan duniyan"
shiru yayi yana kallonta, yace "to amma idan kika tuna kuma kikaga matsayina da naki ba ɗaya bane ya zakiyi?"
tace "babu yadda zanyi saide na godewa Allah"
yace "tom Ameena na gode tashi kije"
tashi tayi cikin jin daɗi ta tafi ɗaki, Asmeeta data laɓe tana jira taji an fara jibgan Ameena sabida itama idan saurayi ya aika duka yake mata taji duk abinda ya faɗa, murmushi ne ya suɓce mata, da karfi ta rungume meenat kamar zasu faɗi tace "hamma zai aureki?"
itama cikin jin daɗi tace "eh"
murna sukeyi a ɗakin.

Ammi ta rame sosai saboda halin da take ciki na ɓatan meenat amma zuwa yanzu ta daina damuwa kamar farko, hameed ne kwance akan gado yana juyi lips nashi na kasa cikin bakinshi yana tauna cikin azaban ciwon ciki, kallon gefenshi yayi yaga babu Aneeta a kullum baya ganinta tafiya take ta barshi, waya ya ɗauka ya kira numbern ya kaseem, ya kalli time karfe ɗaya na dare, ganin bai ɗaga ba ya tura mishi text, ya kaseem dake zaune da laptop akan ƙafarshi yana kallo yaji karan kiran waya kafin ya ɗauka kiran ya yanke, da sauri ya fara karanta text ɗin da hameed ya tura mishi (_ya kaseem kazo cikina_)
yana sauka yace "ciwon ciki kuma? to ina Aneeta?"
fita yayi ya nufi ɗakin da mamaki yaga a buɗe, knocking yayi sannan ya tura ya shiga, da sauri yaje ya rikeshi ganin zai faɗi garin birgiman da yake, yace "subhanallah hameed ciwon yayi worst haka?"
jijjiga kai yayi yana rirrike hanun ya kaseem ɗin cikin azaban ciwo, yace "okay relax relax gani nan ai ko?"
gyaɗa kai yayi, ya kalleshi sosai yaga ya rame sosai kamar yana cikin damuwa, ya kula da hakan cikin kwanakin hameed baya cikin kwanciyar hankali, ya kalli ɗakin yace "to ina Aneeta?"
girgiza kai yayi alaman baisan inda take ba, ganin yanasa hanunshi a cikinshi yace "sorry amma ya akayi ciwon ciki yake kara maka Aneeta bata kulaka ne?"
hawaye ya cika mishi ido ya taɓe baki zai fara kuka ya kaseem yace "karka sake kamin kuka anan"
shiru yayi, yace "to me amfaninta? kayi s** da ita?"
shiru yayi, shima ya kaseem yayi shiru da alama koda yayi to ba sosai bane sabida gashi har yanzu yana ciwon cikin da yafi ma na baya, ganin yana hawaye ya fara lallaɓashi yace "don't cry Allah zai baka sauki kaji?"
a hankali ya jijjiga kai, jingina kai ya kaseem yayi da jikin gadon yayi shiru yana tunani, meyasa Aneeta zatayi haka? yadda ya yadda da ita yayi expecting idan hameed ya aureta zata kula dashi amma sai yaga kamar hameed ɗin ma yana lalacewa ne ya zama wani kala kamar akwai abinda yake damunshi, ɗaura kanshi yayi a cinyar ya kaseem ɗin yayi shiru yana kallon saman ɗakin hawaye yana wanke mishi fuska, ya kaseem yace "ya Allah ka ragewa kanina wannan wahalan, ya Allah yasha wahala sosai banaso ya kara shan wahalan da yasha a baya, hanunshi yasa a kanshi yana shafa gashinshi da suka hargitse, shiru yayi, sai kuma can ya kara fara jujjuya kai yana rike maranshi, ya kaseem yace "sorry bari nayi maka allura"
fita yayi yazo da allura, mishi yayi yana rungume da ya kaseem har ya fara bacci sabida alluran me karfi yayi mishi, shiru yayi yana kallon innocent face nashi, bai taɓa ganin mutumin da yasha wahala a rayuwarshi kamar hameed ba, tun yana yaro yake shan wahala har yanzu bai samu nutsuwa ba, tun daga kan zeenat daya aura basu taɓa kwana ɗaya cikin kwanciyan hankali ba har zuwa yanzu da yake ganin rashin dacewa da auren Aneeta da yayi, cikin sanɗa ta turo kofan ta shigo, turus ta tsaya ganin ya kaseem ne zaune akan gadon ga hameed rungume dashi yana bacci da alama da kyar yayi baccin duba da zufan dake goshinshi, jikinta ne ya fara rawa tana sanye da bakin riga silk tasa hulan net, kanta ta sunkuyar kawai ya sauke kan hameed daga jikinshi ya kwantar dashi, kallonta yayi sama da kasa baice mata komai ba kawai ya fita daga ɗakin, taɓe baki tayi bayan ya fita sannan tazo ta hau gadon ta kwanta.
ya kaseem safa da marwa ya fara a ɗakin a ranshi yace "anya bamuyi kuskure ba?"
sai kuma ya zauna ya dafa kanshi, kullum baya bacci tunani baya bari yayi bacci idan yayi bacci to saide ɓarawon bacci ne ya saceshi, ga ɓatan meenat da yaga ya dami sultan duk ya zama wani iri kullum yana nemanta babu dare babu rana ga damuwan da yake gani da rashin kwanciyan hankali ƙarara a tare da hameed, wannan damuwan kaɗai sun isa su hanashi bacci.

washe gari duk suna breakfast babu me yiwa juna magana, Aneeta ce ta fito tayi bala'in kyau cikin atamfa fited gown ya matukar kama jikinta ta ɗaura bakin After dress a sama, takalmi me tsini tasa sannan ta rike karamin jaka ta sauko ta kallesu duka bata gaida kowa ba ta zauna akan kujera itama ta fara cin abinci, kallo ɗaya ya kaseem yayi mata ya ɗauke kai, har suka gama breakfast ta tashi cikin yauki tana tafiya, ya kaseem yace "ai da tun farko kin nuna halinki da zamufi jin daɗin zama dake sabida babu wanda zaizo yayi tunanin akuya ce aka lulluɓe da fatar kura"
murmushi tayi sannan ta ciro bakin glasses a jakanta tasa, juyowa tayi tana kallonshi tace "ya kaseem duk gidannan akuyoyi ne aka lulluɓe da fatar kura so banga laifi ba dan surukur gidan ta zama akuya da fatar kura"
zaiyi magana hameed ya rike hanunshi ya girgiza mishi kai alaman please yayi shiru.
bai kara magana ba ita kuma ta fita domin zuwa school, Ammi murmushin da yafi kuka ciwo tayi sultan kuma ya sunkuyar da kai ya rasa yadda zaiyi abin yana damunshi gaba ɗaya ya zama shiru shiru.
ya kaseem labcoat nashi yasa ya fita a gidan ranshi a ɓace, sai dare ta dawo gidan, suna falo tace "sannunku"
ya kaseem yace "daga ina kike?"
tace "ya kaseem a ganina yarima hameed ne kaɗai yakeda iko akaina shine zai iya tambayata daga ina nake, to amma ba komai daga school nake"
zaiyi magana sultan yace "dan Allah yaya kada mu kara wani tashin hankalin akan wanda muke ciki a gidannan"
shiru yayi amma fa zuwa yanzu ranshi ya gama tafasa wallahi da yasan haka halin Aneeta da babu abinda zaisa ya taimaka mata harma tazo gidan bale ta samu fuskan auren hameed, banda ƙaddara ma ai tasan hameed ba sa'anta bane, hameed ya fita komai harma da kyau babu abinda bai fita dashi ba, amma tayi sa'a hameed yana sonta da wallahi saiya koreta, tashi yayi yabar wajen ranshi yana soyuwa.
murmushi tayi lokacin data buɗe kofa taga hameed zaune akan kujera yayi shiru abin duniya duk ya isheshi haka takeson ganinshi cikin damuwa abin yana bata nishaɗi, kallonta yayi yaga tana mishi murmushi, shima murmushin yayi mata, a hankali tayi wurgi da jakan cikin gajiya ta cire after dress ɗin shima ta wurgar, zuwa tayi inda yake ta zauna akan cinyarshi, rungume kanshi tayi a hankali tasa hanunshi a waist nata, riketa yayi sosai yana jin sonta har cikin ranshi, a kunnenshi tayi magana cikin wani kasalallen murya tace "am sorry my prince"
shiru yayi, a hankali ta haɗa bakinta da nashi, kissing nashi ta fara ta rufe ido, cikin damuwa da kewan da yake ciki ya fara mayar mata, Allah sarki jikinshi har rawa yake sabida Allah ya yishi da matukar needing, zuge zip ɗinta yayi yayi kasa da rigan, hanunshi yasa a chest nata ya fara wasa dashi, lumshe ido tayi cikin wani irin murya tace "Ahhh"
ji yayi gaba ɗaya yana neman zaucewa, fuskanshi ya ɗaura a chest nata, shafa kanshi ta fara tana kara matsowa sosai ta yadda bom bom ɗinta zai haɗu da jkinshi, saida ta tabbatar ta gama fitar dashi hayyacinshi kafin ta fara zamewa a hankali, riketa yayi sosai yana ji yau idan ta matsa a wajenshi babu abinda zai hanashi suma, cikin sanyi tasa hanu akan nashi ta rabashi da jikinta, idanunshi da suka tsume yake kallonta dasu a hankali ta sauka daga jikinshi ta shiga bedroom, rufewa tayi harda makulli sannan ta jingina bayanta da kofan tana maida numfashi idonta a rufe.
hameed sauka kasa yayi ya kwanta ya fara kuka, ya rasa yadda ma zai fara yi da kanshi.
wayanshi dake gefe ya kalla ya janyo ya turawa ya kaseem text (_yaya zan mutu_)
daga nan yayi jifa da wayan yana kuka sosai.
ya kaseem sai safa da marwa yake ya kasa zama sai tunanin mafita yake, wannan aneetan wani hali takeso ta fara nunawa koma yace ta nuna, dunƙule hanu yayi ya fesar da iskan bakinshi karan shigowan text da yaji yayi saurin ɗauka yana dubawa, da sauri ya fita a ɗakin, ko sallama baiyi ba ya buɗe kofansu ya shiga, gani yayi yana birgima a kasa, da gudu ya karaso ya ɗagashi, kwanciya yayi akan sofa, idonshi yayi jajur kamar yadda bakinshi ya koma red, daga idonshi kaɗai zaka san me yake damunshi, dafa kai yayi yace "hasbunallah yarima ina Aneetan?"
nuna mishi kofan ɗakin dake rufe yayi, a fusace ya tashi zaije ya rike hanunshi alama yayi mishi na yaya please, komawa yayi ya zauna, ganin yana kuka shima yaji kamar zaiyi kukan yace "yarima ya zanyi? da wanne zanji yarima? da wanne zanji?"
sai kuma yayi shiru, ganin haka hameed ya ɗan rage kukan.
tausayinshi yasa ya rike hanunshi yace "tashi muje ɗakina"
tashi yayi a hankali yake tafiya yana mishi sannu har sukaje ɗakin, ya mishi allura sannan yace "kwanta"
kwanciya yayi babu jimawa bacci ya ɗaukeshi, waya ya kira da sauri aka ɗaga yace "Alameen ya kake?"
ya amsa da "ina lafiya ya kaseem ya abokina?"
yace "gashi nan kamar yadda ka sanshi, kana gari?"
yace "gobe zan dawo dai"
yace "idan ka dawo ka rinƙa zuwa kuna fita da hameed"
faɗa mishi duk abinda ke faruwa yayi dama basa ɓoyewa Alameen komai sabida good friend na hameed ne, yayi shiru sai kuma yace "wai ya kaseem har yanzu komai bai daidaita bane?"
cikin gajiya shima yace "saima kara lalacewa da komai yake yi, please nasan yadda kuke aminta da hameed ya dawo kamar da ya rinƙa zuwa gidanku kaima ka rinƙa fita dashi may be ya ɗan samu sauƙin rayuwarshi may be ya rabu da depression, yanzu so nake ma ya rabu da wannan shegiyar Aneetan da naji na fara tsananta sabida abinda take mishi kuma naga kamar yana sonta sosai"
yace "ba komai ya kaseem gobe ina dawowa zanzo"
yace "yawwa Alameen Allah maka albarka"
yace "Ameen"
zama yayi a gefen hameed ɗin yace "ɗan albarka Allah ya baka ikon cinye jarabawa"
shiru yayi yana tunanin meenat wacce har yau babu labarinta kullum sai mai martaba yayi zancenta sun kasa mantawa da ita.

washe gari kamar yadda Alameen ya yiwa kaseem alkwari sai gashi ya shigo, duk sukayi murnan ganinshi cikin jin daɗin ganinsu shima yace "ina abokina?"
sultan yace "dama ai mun san shi kazo wajenshi ba muba ya Alameen"
dariya yayi, Alameen kyakkyawa ne sosai amma shi chocolate ne saide kalanshi me bala'in kyau ne, yace "wai ina yake?"
Aneeta data fito yanzu daga ɗaki sanye da simple riga da wando tace "waye yake tambayan mijina?"
murmushi yayi mata yace "nine amininshi sunana Alameen"
kallo ɗaya ta mishi ta watsar, jikinshi yayi sanyi yace "yana ciki?"
kaseem daya fito yanzu daga ɗaki yanasa uniform yace "meyasa zaka tambayi wanda basuda hakki a kanshi? ƴan gidansu zaka tambaya ba bare ba"
yayi maganan yana kallon Aneeta, murmushi Alameen yayi yace "ya kaseem banga meenat tawa ba ina take?"
yace "meenat ta ɓata"
yace "innalillahi yaushe?"
faɗa mishi komai yayi sannan yace "ka kwantar da hankalinka zamu samu meenat insha Allah kuma kamar yadda akayi maka alkwari kaine zaka aureta meenat ba zata auri kowa ba sai kai.
yace "amma ya kaseem meyasa baku faɗamin ba?"
yace "sabida nasan zaka iya barin komai da kakeyi a kasar waje ka dawo nigeria domin neman meenat sabida nasan yadda kake sonta da mukayi hakuri ba gashi ka dawo ba? kuma tare da kai zamu fara nemanta"
yace "insha Allah sai inda karfina ya kare sannan duk wanda yake da sa hanu saina wulaƙanta rayuwarshi"
ya kaseem yace "kaje ciki hameed yana ɗakina"
da sauri ya shiga ciki domin ganin abokinshi.


_Jiddah Ce...✍️_
08144818849
[20/08, 2:11 am] Shuraihu Usman: 🌸🌸🌸🌸🌸
*ƘADDARA TA*
🌸🌸🌸🌸🌸


Na
*Jiddah S Mapi*


*Chapter 12*


~Yau ake ɗaura auren meenat da hamma najeeb, banda murna da farin ciki babu abinda Asmeeta take yi, itama meenat ɗin murna take yi sunyi wanka me kyau duk da babu mutane dayawa amma sun ɗan zo har aka ɗaura aure, tunda aka ɗaura aure ya dawo gida ya cire kayan jikinshi daya taƙura mishi, kayanshi na zuwa jeji yasa sannan ya ɗau takobi zai fita, meenat wacce ta ɓata rai tana kallonshi tace "to ina zakaje?"
sajenshi me kyau ya shafa, sannan ya zuba mata kyawawan idanunshi da suke ɗaukan hankalinta kamat idanun turawa cikin idon brown ne, lips nashi na kasa ya tsotsa dama wannan ya zame mishi jiki yace "zanje bazan jima ba zan dawo"
kamar zatayi kuka tace "yau fa akayi aurenmu amma shine zaka fita?"
yace "kiyi hakuri ba zan jima ba zan dawo"
tace "gaskiya babu inda zakaje"
tsawan daya daka mata yasa tayi shiru tana kallonshi a tsorace
yace "ni sa'anki ne? ko kin manta ni yayanki ne kike min wannan maganan nace miki ba zan jima ba"
matsa mishi tayi ya wuce, ɗakinsu taje Asmeeta ta kalleta tayi shiru sabida tasan idan tayi magana hamma yana dawowa zata faɗa mishi daga karshe taci ɗan banzan duka shiyasa take kame bakinta yanzu ta daina ɓarin zance domin meenat tana mugun son hamma najeeb kamar ranta, ta harareta tace "wa kike kallo?"
kama baki tayi tace "ni ban kalleki ba kuma bance komai ba, ki barni da dukan da nakesha ma ya isheni"
tace "ni ɗin ya daina duka na ne?"
tsit tayi, duk rashin kunyar Asmeeta idan taji hamma najeeb to shiru takeyi dan tasan dakuwa take a hanunshi, mimi tace "Adda na

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login