Showing 30001 words to 32935 words out of 32935 words

Chapter 11 - KADDARATA

Start ads

11 Sep 2025

79

Middle Ads

miki kitso?"
tace "ban son kitso taho muje yawo na siya miki mangoro kinji ɗiyata?"
cikin jin daɗi tayi tsalle tayi kyau da kwalliyan da Asmee tayi mata, durkusawa tayi ta ɗale bayanta zasu fita meenat tace "ku jirani zan biku"
Asmeeta tace "ki tabbatar idan yaya ya dawo ba zakice tare muka fita ba"
tace "naji"
fita sukayi kamar ranan yauma dare suka dawo, cikin sanɗa meenat ce ta fara shigowa hamdala tayi ganin baya nan tace "ku shigo baya cikin gida"
Asmee dake goye da mimi wacce tayi bacci tsaban gajiya ta shigo ta kwantar da ita a ɗaki kafin ta fito tace "da alama yau hamma ba zai dawo da wuri ba, kai amma fa na iya rawa kinga kuɗin da ake watsamin a filin wasa?"
meenat tace "kin iya rawa sosai, ai nima yau nayi rawa ba kaɗan ba"
fitowa yayi daga ɗakin ya kallesu, Asmeeta da gudu ta juya zata shiga ɗaki meenat ta bita yace "ku tsaya"
tsayawa sukayi meenat tace "dan girman Allah kada ka dakemu mun tuba kuma Asmee ce tace muje"
dafa kirji tayi manyan idanunta ta zuba mata tace "ni kuma ameena? a tashi mimi zata faɗi waye yace zai je"
yace "kuzo magana zamuyi"
sun kasa yadda dashi da kyar suka zauna, gani sukayi ya zauna yayi shiru, Asmee cikin mutuwan jiki tace "hamma kana lafiya?"
ɗago kai yayi ya kalleta sannan ya girgiza kai, cikin sonshi da tausayinshi tace "hamma me yake damunka?"
yace "Asmeeta"
tace "na'am hamma"

"tunda iyayenmu suka haifemu muke fama da talauci da rashin jin daɗin rayuwa, kin san duk duniya babu wacce nake so sai ke, bayan ke kuma sai mimi sai kuma Allah ya kawo mana Ameena cikin rayuwarmu wacce nake jinta har cikin raina, Asmeeta duk da mutanen kauyen nan suna ganin kin kai aure amma ni karamar yarinya nake ganinki hakan yasa ban damu kiyi aure ba, kullum addu'ata Allah ya baki rayuwa me kyau wanda zakiyi farin ciki saboda kin taso cikin maraici babu uwa babu uba nine uwa kuma nine uba a wajenki"
tace "hamma soyayyan daka nunamin ko mama da baba sai haka"
yace "Albishir nakeso nayi muku"
da sauri tace "na me?"
ya nuna musu wani dutse dake hanunshi yana yalƙi sosai, tace "me wannan hamma najeeb?"
yace "wannan shine asalin gold, na samu a cikin ruwa yau da naje wanke takobina, nasan kuɗin gold wanda bai kai wannan bama zai iya ciremu a talauci bale wanda na samo dayawa"
tashi yayi ya shiga ɗaki, fitowa yayi dasu dayawa a bakin leda yace "wannan sune arzikin da Allah ya bani a yau bayan aurena da Ameena"
rufe baki asmeeta tayi tana kallonshi with surprise, bakinta yana rawa tace "hamma gold?"
ya bata a hanunta yace "tabbas Allah ya karɓi addu'ar mu zakuyi rayuwa cikin farin ciki, zamu bar wannan kauyen zamu koma birni muyi rayuwa me ɗauke da gata, dama alƙawari nake miki tun kina karama cewar zan kula dake kamar sarauniya yanzu tare da matata Ameenah zan kula daku tamkar ƴaƴan sarki"
tashi tayi ta rungumeshi tana murna, Ameena hawayen farin ciki ta share tace "Alhmdllh dama banada buri kamar naga yana cikin farin ciki gashi yau yana dariya"
ido kawai ta zuba mishi yadda dariya yake bala'in yi mishi kyau.
hanu ya buɗe mata tazo itama ta rungumesu, yace "gobe zan tafi birni da asuba zan tafi ba lalle ya zama kun tashi a bacci ba, zanje na siyar may be na kwana may be na dawo da wuri, zanja kunnenku musamman ke Asmeeta na sanki da taurin kai da rashin jin magana, ku kula da gidannan ku kula da mimi kunji?"
duk suka amsa da "to hamma"
sakinsu yayi yace "shine maganan dana kiraku muyi"
murmushi akan face nasu suka koma ɗaki, yana kwance a ɗaki yayi shiru yanata juye juye tunanin yadda zai gyara rayuwarsu yake, sallama yayi, da mamaki ya amsa jin muryan meenat, shigowa tayi ya kalleta ta cikin haske kaɗan na fitila yace "Ameena kece?"
tana tsaye ta gyaɗa kai a hankali, yace "me kikazo yi?"
tana turo karamin bakinta tace "Asmeeta ce tace min idan anyi aure ɗaki ɗaya ake kwana da miji shine nazo"
dariya yayi kaɗan sannan yace "to ki karaso"
a hankali ta karaso ta zauna a gefenshi, ba zato taji ya janyota jikinshi, rungumeta yayi cikin sanyin murya yace "ina sanki sosai"
wani sanyi taji a ranta jin kalman daya faɗa, ta jima tanason jin wannan kalman daga bakinshi, a hankali tace "nima ina sanka"
yace "kar kice nima kice ina sanka"
tace "ina sanka"
a hankali ya juyo da face nata yana kallonta, lumshe ido yayi yace "kimin alkwari duk inda naje ba zaki taɓa mantawa dani ba"
murmushi tayi tace "ba zan taɓa mantawa da kai ba har karshen rayuwata"
a hankali ya kara mannata da jikinshi, ji tayi ya fara yawo da hanunshi a bayanta yadda take jin sonshi batajin zata iya hanashi yin komai da ita.
a hankali ya matso da lips nashi ya ɗaura akan nata, kiss ya fara mata ta rufe ido, a hankali yake sauke numfashi me wuyan fasara, kashe fitilan yayi sannan a kunnenta yace "kiyi hakuri zakiji zafi kaɗan"
rufe ido tayi tace "idan kaine ko mutuwa zanyi ban damu ba"
wani irin sonta ya mamaye zuciyarshi, a hankali yake bi da ita, duk da taji zafi amma ta daure saida zafin yayi yawa kafin ta buɗe baki zata fara kuka cikin lallashi yana hana kanshi rasa control yace "yi hakuri"
a daren saida ya tabbatar ya maidata nashi kafin ya fara bata hakuri, sai kuma yayi shiru yana jin saukan numfashinta a faffaɗan kirjinshi.
ji yake kamar su dawwama a haka, karo na farko daya fara jin farin ciki da kaunar mace a ranshi ji yayi Ameena ta zame mishi komai a rayuwa idan ya rasata da Asmee zai iya rasa rayuwarshi.
bacci ne ya ɗaukeshi. washe gari ya fara ɗaukanta da asuba ya kaita banɗaki ruwan zafi ya dafa sannan yazo yayi mata wanka, sai ciza baki take cikin azaba yace "sannu kinji?"
alwala yayi mata sannan ya fito da ita, kwantar da ita yayi a ɗakinshi yace tayi salla, salla tayi shima yayi salla sannan ya shirya yace "kiyi hakuri nayi ɓarna kuma zan tafi na miki alkawari zan dawo duk inda naje kina raina kuma zan dawo bada jimawa ba zan baki rayuwa me kyau zakiyi rayuwa kamar ƴar sarki"
a hankali ta shafa kanshi tace "Allah baka sa'a amma ka dawo da wuri"
yace "insha Allah"
yace "kimin murmushi to"
a hankali tayi murmushi yace "yawwa matata abin alfaharita"
tashi yayi ya ɗau jakan da gold ɗin yake ciki yace "na tafi"
tace "Allah tsare hanya"
a hankali yace "Ameen"
fita yayi ya shiga ɗakinsu Asmeeta baccinta da takeyi kamar wacce ta mutu shi takeyi yasan ko za'a kwana ana tashinta ba zata buɗe ido ba, tsaki kaɗan yaja yace "Allah shiryamin ke asmeeta Allah yasa ki girma kisan fari da baki"
kallon mimi yayi yace "Allah yasa kada kibi halinta"
murmushi yayi yace "na barku lafiya"
fita yayi daga gidan.
saida gari yayi haske sosai kafin Asmeeta ta fara buɗe ido, tashi tayi da sauri ta kame tulin gashinta daya barbazu ta tashi da sauri tace "Allah sa hamma najeeb bai tafi ba"
ɗakin ta buɗe taga meenat ce kaɗai kwance tana bacci, da sauri ta fara tashinta, cikin gajiya meenat ta buɗe ido, kallonta asmee tayi cikin wauta da rashin sanin komai tace "kinzo sai bacci kike ina hamma najeeb?"
tana hamma tace "ya tafi"
shiru tayi bataji daɗi ba taso suyi sallama kafin ya tafi, cikin kwantar da hankali meenat tace "kiyi hakuri zai dawo ko yau ko gobe ba zai wuce jibi ko gata ba"
tace "to wanne zan ɗauka? yau? gobe? jibi? gata?"
tace "zai dawo Asmee karki damu kinji?"
tace "to Allah yasa ya dawo mana da kuɗi dayawa dako kullum sai mun siya abu me daɗi munci"
dariya tayi kaɗan sai kuma ta rufe ido zata koma bacci tace "bakida lafiya ne?"
gyaɗa kai tayi, tace "Ayya sannu kinji?"
shiru tayi bacci har yayi gaba da ita, fita asmee tayi ta fara salla sannan tazo ta fara girki ta gama ta kawo musu sukaci meenat ta kara komawa baccin.

Aneeta ce tsaye a cikin school ta kasa zaune ta kasa tsaye hanunta goye a baya kawarta billy wacce suka alaka sosai tazo ta dafata tace "haba Aneeta meyasa kike wannan damuwan?"
ta kalleta sannan ta cire glasses black na idonta tace "meyasa nake damuwa kuma billy? kin san ni ƴar sarki ce ban taso cikin wahala ba, na taso cikin jin daɗi da kwanciyar hankali yau ace bayan tashin hankali da nake ciki wai ina ɗauke da ciki? ciki nefa dani billy cikin yarima hameed"
billy tace "common Anee ai yarima yana son yara sosai kema kin faɗa me zaisa ki damu to?"
tace "ya zanyi da karatuna? kuma ya zanyi na haihu na tsufa kenan?"
tace "Aneeta..."
rufe mata baki tayi tace "please billy idan zaki taimaka ki taimakamin na zubar da wannan cikin"
tace "karki damu muje yanzu ma zan kaiki wajen dr na zai zubar yau ɗinnan"
ajiyan zuciya ta sauke tace "ko kefa billy ta?"
tace "muje class zuwa anjima"
tace "da zafi ake dukan karfe mu tafi yanzu"
zatayi magana ta turata suka tafi kawai, motar billyn suka shiga direct sai wajen Dr ɗinta, da suka mishi bayani magani ya bata a wajen ta haɗiye sannan ya bata sauran yace zuwa azahar tasha cikin zai zube yau, ta amsa da godiya sannan ta bashi kuɗaɗe masu yawa, school suka koma sai kusan azahar tasha sauran ta fito daga school ɗin tana jin cikinta har ya fara ciwo, motar yarima ta gani da sauri ta karaso tana mishi murmushi shima murmushin yayi mata yayi bala'in kyau cikin ƙananan kaya, shiga tayi ya tada motan suka tafi, suna isa gida taga yasa hanu a baya ya ciro leda, mika mata yayi ta karɓa tana buɗewa, teddy ta gani da sauran kayan jarirai, gabanta ne ya faɗi tayi saurin rufewa tace "sunyi kyau sosai my prince amma basu kaika kyau ba"
ta lakaci karan hancinshi, murmushi yayi suka fito tare, tsayawa yayi yana duba flower ɗin da yaga sun karye kuma ba'a cire ba shiga ciki tayi tana amsa call ɗin daya shigo, da sauri tace "billy inaga fa cikinnan yama fara zubewa kuma banaso yarima yasan na zubar da ciki sabida inada task dayawa da ban gama ba a gidannan..."
sauke wayan tayi tana kallon fadeel da yake kallonta cike da zargi da alama yaji duk abinda ta faɗa, zata wuce ya tare hanyan, tace "ka matsa na wuce meyasa zaka taremin hanya fadeel?"
yace "Anty Aneeta meyasa kike cutar da innocent soul? meyasa kike cutar da yaya yarima bayan kin san baida niyan cutar da kowa a ranshi?"
tace "me kake nufi fadeel?"
zaiyi magana ta tureshi ta wuce binta yayi yace "naji duk abinda kike faɗa kuma wallahi saina faɗa mishi"
tafiya take har ta kusa haura stair ta juyo tace "fadeel kada ka shiga abinda bai shafeka ba"
yace "wallahi saina faɗa"
ya kaseem daya fito yanzu ya tsaya yana kallonsu, zata wuce fadeel ya rike hanunta, tace "ka sakarmin hanu fadeel"
yace "ba zan sakeki ba har sai yaya yareema yazo...."
juyi tayi ta rike hanunshi gam ta fara gangara daga stair wani irin ihu ta kwala tace "cikina ya zubar da cikin"
yarima daya shigo yanzu tsayawa yayi a razane idanunshi sunyi girma yana kallonta jini yana zuba daga kasanta, fadeel ya fara girgiza mishi kai yace "wallahi yaya yarima na rantse da Allah...."
kuka ya fara ganin yadda take rike cikinta tana ihu, take abi dake salla ya idar da wuri baima san sanda ya shigo ba, ammi ma da hijabi a jikinta da calbi ta tsaya ta kasa sakin kofan tana kallon Aneeta dake kwance tana birgima jini yana zuba, ya kaseem ya kasa gane me yake faruwa, abinda be gane ba shine itace ta faɗi da kanta ko fadeel ne ya tureta?
fadeel wand ya gama tsorata yazo da gudu zai ɗagata, marin da hameed ya ɗaukeshi dashi saida ya faɗi a gaban ya kaseem da yake zuwa wajen, ba bakin magana amma wani kallo yake mishi, nufanshi yayi zai rikeshi ya kanƙame ya kaseem yace "dan Allah ya kaseem na san fushinshi na san idan ranshi ya ɓaci ba abinda ba zai iya ba dan Allah ka tainakeni karya kasheni"
jikin Ammi ya fara rawa, Aneeta sai juyi take a kasa cikin azaba tana kuka domin ciwon da gaske yake mata bada wasa ba, da tasan haka azaban yake da bata zubar ba.
hameed da hanu ya nunawa fadeel kofa, yace "yaya yarima kayi hakuri wallahi"
idanunshi sunyi jajur ya kara nuna mishi kofan, abi wanda ya kasa magana da kyar yace "hameed ka kyaleshi dan Allah abi komai a hankali"
idanu jajur ya juyo yana kallon abi, sai kuma ya nuna mishi Aneeta dake kwance a kasa ya girgiza kai ya kara nuna mishi hanya, ammi tace "hameed kada kayi abinda zakazo kayi dana sani"
wani bugun daya yiwa tv ɗin ɗakin saida tv ya tarwatse, ya juya ya bugi showglass da hanunshi take shima ya fashe, yana huci yake kallon fadeel, aneeta dake kwance tace "ya zubar da cikin hameed ya zubar da cikin zan mutu"
a hankali fadeel ya raɓa ta gefen sultan zai wuce sultan ya rike hanunshi yace "dan Allah kada ka tafi fadeel na saba da kai ina zakaje?"
ganin yadda hameed yake huci ya sakeshi, yana kuka ya fita, hameed ne yaje ɗakinsu ya buɗe wardrobe ya ciro duk kayan da yasan fadeel yana sawa yasa a akwati ya fito, buɗe kofan yayi ya kira dogari ya bashi ya mishi alama ya kai mishi, karɓa yayi shi kuma ya koma ya rufe kofan, kaseem wanda ya rasa abinyi kawai sai kallonsu yake zuwa yanzu ya gaji, yarima yayi mishi alama da roko akan ya dubata, ɗagata yayi ya kaita ɗaki ya canja mata kayan da ya ɓaci sannan yazo ya goge jinin, ya kaseem wanda jikinshi kamar an zare laka yazo yana dubata, kallon yarima yayi cikin jin tausayinshi yanaso yace mishi magani tasha ya zube amma yasan ba zai taɓa yadda ba sabida ya yadda da Aneetan, kawai yace mishi "cikin ya zube saide kayi hakuri"
daga haka ya fita daga ɗakin, zama yayi a kasa ya fara kuka, ɗaki kaseem ya shiga yayi shiru yana, yace "me yake faruwa ne?"
hameed fita yayi daga gidan yaje gidansu Alameen acan zai samu yayi kuka cikin kwanciyan hankali, da gudu yake jan motar har ya isa gidansu me kyau ne sosai, shiga yayi mamanshi dake zaune tace "A,a yarima yau kaine a gidan namu? wato abokinka ya dawo ko?"
murmushi yayi mata sannan yayi mata alaman gaisuwa ta amsa sannan tace "yana ciki"
tashi yayi ya shiga, yana shiga dakin yaga Alameen kwance akan gado yana kallo a laptop, jingina yayi da kofan kuka me zafi yana zuwa mishi, a hankali ya silale kasa Alameen ya kashe laptop ɗin ya sauko daga gadon yace "yarima meya faru kuma"
wani irin kuka ya fashe dashi, Alameen cikin damuwa yace "wai yarima har yanzu baka daina wannan kukan naka ba idan abu ya sameka? zaka karyawa mutum zuciya"
kukan yake yi sosai, shiru Alameen yayi yana kallonshi harda shesheƙa saida yayi me isanshi kafin ya tashi ya hau gadon yaja bargon ya rufe har kanshi yayi shiru, Alameen ma baiyi magana ba yayi shiru yayi tagumi, rayuwan yarima abin tausayi ne kullum yana cikin damuwa.

_Jiddah Ce....✍️_
08144818849
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login