Showing 3001 words to 6000 words out of 32935 words
na kuɗi wanda zai rasa a gidansu yasa rabin aikin da yakeyi a asibitin kyauta ne, idan yaga bakada kuɗi ma kyauta zai maka aikin.
office nashi me kyau ya zauna yana duba laptop nashi da yayi kwana biyu bai duba ba, wayanshi aka kira ya kalli sunan FADEEL dake yawo, fadeel yaron kanin Abi ne amma iyayenshi sun rasu tun yana yaro, a hanun Abi yake amma yana school, ya saba sosai da sultan hakan yasa da sultan ya tafi school shima ya tattara ya koma hostel da zama, Abi yaki ya haɗasu school ɗaya dan yasan ba karatu zasuyi ba, fadeel ya girmi sultan amma tasu tazo ɗaya sun zama kamar sa'o'i idan kazo gidan ba zakasan basu Abi bane suka haifeshi, karawa yayi a kunne yace "ina jinka"
yace "ya kaseem na gaji da zaman hostel ne shine zan dawo gida tunda saura watanni na gama school ɗin"
yace "shine kuma saika kirani? kaida gidanku amma saika kirani?"
yace "sorry ya j"
tsaki yaja kafin ya kashe wayan, wato fadeel ya maidashi yaro so yake ya nuna mishi baisan sultan ya dawo ba.
aiki yake bai dawo ba sai dare kamar yadda ya saba, da leda a hanunshi ya shigo, duk suna zaune suna cin abinci banda Abi dama yasan ba koda yaushe yake cin abincin dare tare dasu ba, tun kafin ya zauna yace "ina hameed?"
kamar yasan ya dawo a hankali yake saukowa daga stair yana yamutsa fuska, sleepy face ɗinshi yayi kyau lips nashi na kasa ya cusa cikin bakinshi yana tsotsa a hankali yake kallonsu da grey eyes nashi, a gefen ya kaseem ya zauna yayi shiru yana kallon fadeel daya maida hankali akan wayan sultan suna kallo, ko me suke kallo oho, jabeer yace "sai yanzu ka tashi a bacci?"
girgiza kai yayi alaman A,a ya jima da tashi, ledan ya mika mishi yace "gashi na kawo maka"
karɓa yayi ya buɗe, ganin ice cream yayi murmushi ya ɗau karamin spoon ɗin ya ɗibo ya kai bakin ya jabeer girgiza kai yayi yace "wa kai na kawowa"
a hankali ya kai bakinshi yana sha, da kallo Ammi take binshi, hawaye yana cika mata ido, a spoon ya ɗiba ya kai bakinta girgiza kai tayi hawayen yana wanke mata fuska, aje roban yayi yazo gabanta ya fara share mata hawayen yana girgiza kai alaman ta daina kuka, fadeel yace "yaya yarima ka kyale ammi kullum sai tayi wannan kukan ta saba"
harara yayi mishi da sauri ya rufe baki bai kara cewa komai ba, tashi kaseem yayi ya wuce ɗakinshi.
_Jiddah Ce....✍️_
08144818849
[20/08, 2:11 am] Shuraihu Usman: 🌸🌸🌸🌸🌸
*ƘADDARA TA*
🌸🌸🌸🌸🌸
Na
*Jiddah S Mapi*
*Chapter 2*
~Cikin dare kowa na ɗakinshi yana bacci gidan ya zama shiru kamar ba gidan sarauta me ɗauke da mutane dayawa ba, hameed wanda idonshi biyu ya kunna wutan ɗakinshi ya kasa bacci, zaune yake akan gadon ya rufa iya kafanshi da blanket duk yadda yaso bacci ya ɗaukeshi ya kasa, daga karshe ma pillow ya ɗauka ya rungume sosai yana rufe ido, wani azaban ciwon ciki yakeji kuma yasan yanzu haka ya kaseem yana bacci, wayanshi dake saman gadon ya ɗauka yana ciza lips nashi na kasa ya danna numbern da yayi saving da ya kaseem ya kira, karawa yayi a kunne yana jin kiran yana shiga amma bai amsa ba, katse kiran yayi ya tura mishi text _(ya kaseem my stomach_)
iya short rubutun da yayi ya aika da alama baya magana amma asali ba me yawan surutu bane domin ko messages ɗin da yayi ta turawa ya kaseem magana ne a yanke kaɗan kaɗan baya tura rubutu me tsayi.
ya kaseem daya fito daga wanka yanzu sabida aikin da yayi ya gaji sosai, har ya kwanta sai kuma yaga wayarshi yayi haske da sauri ya ɗauka ya buɗe yana karanta sakon hameed, kunna wutan ɗakin yayi ya sauka a gadon da sauri ya fita, direct ɗakin hameed ɗin ya shiga bai tsaya yin knocking ba sabida dare ne, yana shiga ya kalleshi zaune babu alaman bacci s tare dashi, tausayinshi yaji sosai da sauri ya karaso yace "meya samu cikinka?"
nuna mishi maranshi yayi da hanu alaman shine inda yake mishi ciwo, rufe ido yayi yace "oh my god hameed da wannan ciwon cikin ya zanyi gashi babu alluran a gida"
zama yayi kusa dashi yace "yaushe ya fara maka? yanzu?"
girgiza kai yayi kamar zaiyi kuka, yace "okay ɗazu?"
gyaɗa kai yayi, yace "to maganin da kake sha idan yana maka ya kare ne?"
jijjiga kai yayi zuwa yanzu idonshi ya kaɗa yayi jajur, zama yayi ya dafa kai ya rasa abinyi, birgima ya fara akan gadon yana hawaye, yace "stop crying ina zuwa"
fita yayi yaje ɗakinshi ya ɗauko ice a fridge dawowa yayi ya zauna a bakin gadon, mika mishi yayi "oya collect and calm yourself down"
ya gane me yake nufi hakan yasa ya girgiza kai, cikin jin haushin kukan da yake yi yace "karɓa mana hameed"
karɓa yayi yaja blanket ɗin ya rufe jikinshi kasa yayi da trouser ɗin jikinshi ya ɗaura kankaran daga maranshi zuwa kasa, ɗauke kai ya kaseem yayi daga kallonshi ganin yadda yake lumshe ido yana cija bakinshi, sam baison ko kaɗan yaga hameed cikin ciwo, wurgar da ice ɗin yayi ya kwanta rub da ciki ya fara raira kuka mara sauti, narkewa zuciyan kaseem yayi yaji kamar shima ya fashe da kukan, ganin kukan yaki tsayawa ya daka mishi tsawa yace "kamin shiru, meyasa baka daure ciwo ne?"
shiru yayi yana cigaba da birgiman, fita yayi yaje kitchen ya ɗauko lemon tsami ya yanka ya tsiyaya a cup sannan yasa ruwa kaɗan yasa lipton, fitowa yayi yana juyawa Ammi wacce ta fito ɗaukan ruwan sha ta ganshi da cup tace "me zakayi da tea yanzu?"
yace "ba tea bane magani zansha kaina ke ciwo"
tace "Ayya sorry may be stress ne yayi maka yawa sam baka hutawa"
yayi shiru kawai, ruwan ta ɗauka tace "Allah ya baka lafiya ka samu ka kwanta ka huta kaji?"
yace "to Ammi"
saida ta shiga ɗaki kafin ya koma ɗakin hameed ɗin, har yanzu yana kwance yana kuka, yace "tashi kasha"
tashi yayi da sauri sabida so yake yayi bacci kuma ciwon ya hanashi, karɓa yayi ya shanye duka, runtse ido yayi jin bala'in tsami, ji yayi babu sauki marairaicewa yayi ya fashe da wani irin kuka, kaseem ji yayi kamar ya kai mishi duka, cikin lallashi yace "ka daina kuka zaka samu sauki"
rage kukan yayi a hankali ya gyara mishi blanket ɗin hanunshi yasa a cikinshi daidai inda yake ciwon ya fara shafa mishi, rufe ido yayi yana jin ciwon yana sauki, gyara kwanciyan yayi zai cire hanun yayi saurin rikewa yana kara rufe ido, murmushi yayi ganin yanaso yayi baccin ɗayan hanun yasa a kanshi yana shafa mishi kanshi a hankali lokaci ɗaya yana shafa mishi maranshi dake ciwo, babu jimawa bacci ya ɗaukeshi, a ranshi yace "ya zama dole hameed yayi aure, zan yiwa ammi magana a nema mishi mata tunda duk tarin ƴammatan da suke aika mishi sakon soyayya yaki kula kowa"
a hankali ya zame ya kashe mishi wutan sannan ya fita daga ɗakin ya rufe mishi.
ɗakinshi ya koma ya kwanta take bacci ya ɗaukeshi, washe gari ya tashi da wuri domin zai tafi asibiti da wuri, shiri yayi cikin farin yadi me kyau ya ɗaura labcoat a sama sannan ya rike briefcase ɗinshi, farin glasses nashi a idonshi, yayi bala'in kyau kuma da manyance yake yin komai nashi a nitse, ganin an shirya abinci amma babu kowa kawai ya wuce part na mai martaba, sallama yayi ya tarar da hameed a fada ya kwanta kamar me bacci, murmushi yayi yace "hameed dama ka tashi?"
a hankali ya tashi ya zuba mishi kyawawan idanunshi alaman eh na tashi, mai martaba ya kalli kaseem yace "har ka fito? yau da wuri zaka tafi kenan?"
cikin girmamawa yace "Allah ya taimakeka yau zan tafi da wuri, ina kwana"
yace "lafiya ƙalau Allah ya maka albarka kaseem"
a hankali yace "ameen"
tashi yayi ya kalli hameed daya bishi da ido, yace "zamu je ne?"
da sauri ya gyaɗa kai, yace "tashi muje"
tashi yayi ya yiwa mai martaba bye kafin suka nufi dinning fadeel ne da sultan zaune sun zuba abinci amma suna hira suna ganinsu sukayi shiru, gaishe da kaseem sukayi ya amsa sannan suka gaisa hameed, hanu ya ɗaga musu alaman lafiya, abinci suka sa suma suka fara ci, Ammi da meenat tare suka fito meenat ta rike hanun ammi, tayi kyau cikin uniform black and white rataye da jakan school, cikin girmamawa ta gaishesu duk suka amsa shi kuma hameed ya mata alaman ya amsa kawai ya sunkuyar da kai yana cigaba da ci abinci, sam bai fiye shiga harkan kowa ba koda a gida yake saide shi da ya jabeer amma baya sakewa da kowa, kallonshi kaseem yayi ganin ya ajiye spoon yace "tunda ka koshi jeka shirya kazo mu tafi"
tashi yayi ya wuce ɗaki, bathroom ya shiga ya haɗa ruwan wanka, ya jima yana wankan kafin ya fito yana ɗaure da towel a kwankwaso, a gaban mirror ya tsaya yana kallon gashin kanshi dake a jiƙe, faffaɗan kirjinshi ɗauke da gashi kwantacce, kiran jikinshi kamar me yin gym a kullum, yanada cikakken sura me kwarjini sosai, dryer dake gefe ya jona ya fara busar da gashinshi, saida ya bushe sannan ya aje a gefe, tsadadden man gashin da yake amfani dashi ya shafa sannan ya taje kanshi, fuskanshi babu walwala kamar kullum, da wuya kaga yana murmushi bale yayi dariya, lotion me tsada da kamshi ya shafawa fatar jikinshi da ake kira da gold skin, wardrobe ya buɗe jerarrun tsadaddun kayanshi ya ɗau ɗaya kananan kaya yau yake da ra'ayin sawa, wandon ya fara sawa black ya ɗau pink ɗin polo zaisa, ta cikin madubi idonshi ya hango mishi wutan da yakeci kusa da dryer ɗin daya manta kashewa, grey eyes nashi ya waro a mugun firgice ya fara motsa bakinshi, kasa sa rigan yayi, wurgi yayi dashi ya fara yin baya ganin wutan yana nema ya fara cin ɗakin, jikinshi ne ya fara rawa, take idanunshi suka kaɗa suka koma jajur, banda motsa lips ɗinshi babu abinda yake yi, faɗuwa kasa yayi ya fara jan jikinshi zuwa waje, tsoron daya shiga ya nuna akwai mummunan alaka tsakaninshi da wuta, da kyar ya isa bakin kofa rasa abinyi yayi, hanu yasa da karfi ya fara bugun kofan, Ammi wacce take rike da cup na shayi jin bugun kofan da hameed yake yasa cup ɗin silalewa daga hanunta tarwatsewa yayi a kasa, tare duk suka juyo suna kallonta cikin tsoro ta tashi tana kallon stair, kaseem yace "menene Ammi?"
tace "hameed shikenan ciwonshi ya tashi, hameed ne yake bubbuga kofa ku saurara kuji"
shiru sukayi kaseem ne ya fara jiyo mugun bugun da hameed yake yiwa kofan, har rige rige suke dasu fadeel wajen haura stair, kofan ɗakin da yake a rufe suka fara bubbugawa kaseem yace "hameed are you okay? hameed ka buɗe kofan"
shesheƙanshi sukeji, hankalin kaseem ya kara tashi, bubbuga kofan yake kamar zai ɓalla, yana cewa "hameed relax and open the door"
zuwa yanzu ya fara rufe ido alaman zai iya suma a kowane lokaci, kaseem da gudu ya sauka kasa kitchen ya shiga ya ɗauko katon karfe zuwa yayi yace "duk kuyi baya"
baya sukayi ya fara ɓalla kofan, da kyar kofan ya ɓallu, gani sukayi yana kwance luf a kasa ya suma, da sauri kaseem ya kalli wutan da yakeci kaɗan kaɗan, yace "sultan kashe wutan"
zuwa yayi ya cire socket ɗin dryer ɗin take wutan ya tsaya, kaseem ya ɗaukeshi cak ya wuce dashi ɗakinshi, akan gado ya kwantar dashi Ammi wacce take kuka tace "wuta ya gani shiyasa ya fita hayyacinshi"
kaseem yace "kawo ruwa meenat"
da sauri taje ta kawo ruwan, karɓa yayi ya shafa mishi, ajiyan zuciya ya sauke me nauyi, ya kara shafa mishi buɗe ido yayi a firgice ya kalli kaseem sannan ya kalli gefenshi, da sauri ya rungumeshi yana hawaye, ammi juya baya tayi tana kuka, cikin muryan kuka tace "shikenan hameed rayuwarka ta lalace ba kamar hameed ɗina dana sani ba wanda bashi da tsoro, ba kamar hameed ɗina da baya tsoron komai ba a rayuwarshi, ba zan taɓa..."
kaseem yace "ammi ya isa"
juyowa tayi ta zuba mishi idanunta da suka jiƙe da hawaye tace "ya isa? ya isa fa kace kaseem kenan kada nayi magana akan ɗan dana haifa?"
sakin hameed yayi yace "maganan bashi da amfani da magana me amfani zakiyi saina kyaleki"
murmushin gefen baki tayi wanda yafi kuka ciwo, tace "kana nufin maganana bashi da amfani? kafi kowa sanin zafin da nakeji a kullum idan na kalli hameed, zuciyata kamar zata buga sabida abinda ya faru dashi...."
a gabanta ya tsaya yace "ya isa haka ammi maganan ya isheki haka"
kallonshi tayi da mamaki tace "kaseem ni kake yiwa tsawa?"
ya dunƙule hanu yace "idan kikace zaki tuno da abinda ya faru a baya ba tsawa ba har..." sai kuma yayi shiru, hanunshi ta kalla daya dunƙule ta riko hanun tace "har duka ba? har duka na zaka yi ba kaseem? to dakeni ka dakeni kaseem, idan har da gaske nice na haifeka kaseem ka dakeni"
huci yake yi, sultan jikinshi yana rawa yace "ya kaseem ammi dan Allah"
fadeel jingina yayi da jikin kofa yayi shiru, meenat juya baya tayi sam batason abinda ya faru ya kara faruwa, fizge hanunshi yayi yazo wajen hameed ya shafa kanshi yace "kar kaji tsoro babu abinda zai sameka ina tare da kai, bari na ɗauko maka riganka saimu tafi ko?"
gyaɗa kai yayi, ta gefen ammi ya wuce ko kallonta bai kara yi ba, zama tayi a kasa ta ɗaura kanta a bakin gadon, wasu zafafan hawaye ne suke wanke mata fuska, bata damu data share ba, kallonta hameed yake ya kasa yin komai sai binta yake da kallo, a hankali yazo yana share mata hawayen, a time ɗin ya kaseem ya shigo rige da rigan hameed ɗin bashi yayi yasa sannan yace "muje"
sauka yayi a gadon suka fita ammi tabi bayansu da kallo hawayen yana kin tsayawa.
"ɗan sarki jikan sarki yarima hameed barka da fitowa"
ko kallonsu baiyi ba suka shiga motan ya kaseem yaja suka tafi, har suka hau titi kafin ya kaseem yace "sai can dare zamu dawo"
gyaɗa kai yayi.
_jiddah ce...✍️_
08144818849
[20/08, 2:11 am] Shuraihu Usman: 🌸🌸🌸🌸🌸
*ƘADDARA TA*
🌸🌸🌸🌸🌸
Na
*Jiddah S Mapi*
*Chapter 3*
~Asibitin sukaje, ya saba zuwa dama a office ɗin kaseem ɗin yake zama, akan royal sofan ya zauna ya kaseem kuma ya zauna a kujeran da yake zama kullum, yana duba laptop nashi, ɗago kai yayi ya kalli hameed ɗin yaga ya zuba mishi ido, gira ya ɗaga mishi alaman ya akayi?
murmushi kawai yayi, wayanshi ya ciro daga aljihu ya fara typing ya kaseem ya ɗau wayanshi dan yasan sako zai tura mishi, gani yayi ya rubuta mishi "ya kaseem ka daina yiwa Ammi tsawa please"
kallonshi yayi sai kuma yace "okay zan daina"
wayanshi aka kira da sauri ya ɗaga ganin numbern asibiti ne, amsawa yace "dr na'eem ya akayi?"
yace "emergency ne yanzu sir kazo dan Allah abin yafi karfinmu"
da sauri ya tashi yace "ina zuwa"
fita yayi hameed yabi bayanshi da kallo, ɗakin emergency ya nufa, gani yayi rabin ma'aikatan lafiyan asibitin suna tsaye a kanta sun rirriketa amma duk da haka tana kokarin watsar dasu, jujjuya kanta take idonta a rufe, masha Allah kyakkyawa ce ajin karshe fara ce sal gashinta me tarin yawa ya barbazu a bayanta amma yayi datti sosai kuma da alama birgiman da takeyi yasa bakin kayan jikinta da gashinta sukayi datti, suna ganinshi sukace "ga babban dr yazo"
matsa mishi sukayi tana ganin sun saketa ta dira daga gadon zata fita ya rike hanunta cikin sanyin muryanshi yace "ina zakije?"
tunda aka kawota asibitin sai yanzu taji anyi mata magana cikin nutsuwa jikinta ne yayi sanyi ta tsaya amma bata juyo ba, bai saki hanunta ba yace "fita zakiyi? me zakije yi a waje?"
muryanta yana crack tace "zanje wajen mama na"
ya kalli dr na'eem yace "tare dawa suka zo?"
na'eem yace "mamanta ce kuma tun kafin a karaso dasu maman ta mutu itace tayi rai a motar da sukayi accident harda karamin yaro shima ya mutu"
jikinshi a sanyaye yace "zakije kiga gawanta ne? meyasa kike fizge fizge sabida zakiyi faɗa da ƙaddara?"
girgiza kai tayi, a hankali yazo gabanta ya tsaya sunkuyar da kanta dake fitar da jini tayi yace "koda kinyi kuka wanda ya mutu ba zai dawo ba"
faɗawa tayi jikinshi ta kanƙameshi, sai yanzu ta samu wani kuka me cin rai ya kubce mata, shiru yayi yana kallon bayanta, cikin kuka tace "na kasa taimakon mama da Aliyu duk sun mutu ina kallo na kasa yin komai yanzu banada kowa banada kowa"
cikin tausayinta da yaji ya ɗaura hanu a bayanta a hankali ya shafa bayanta yace "kiyi hakuri ki rinƙa addu'a insha Allah komai zai zamo miki da sauki"
tace "to na gode"
sakinshi tayi tace "zanje naga gawan mama"
yace "muje"
tafiya ta fara wani irin jiri da yunwa suka zo mata a lokaci ɗaya baya baya ta fara tana rike da kanta da har yanzu bai daina jini ba, zubewa kasa tayi, kaseem yayi saurin ɗagata, ta suma ya fita da ita, hameed daya gaji da zaman office ɗin ya fito domin yasha iska ganin ya kaseem rike da mace ga jikinta duk jini kuma a sume take yayi saurin bin bayanshi, akan gadon marasa lafiya ya kwantar da ita kallon hameed ɗin yayi wanda ya zuba musu ido da alaman tambaya akan fuskanshi, kaseem yace "accident tayi kuma da alama akwai damuwan da take ciki ka zauna kusa da ita bari naje na kawo abinda za'a bukata na kulawa da ita"
a hankali yaje kusa da ita ya tsaya, ido ya zuba mata yana kallon kyakkyawan fuskanta, babu jimawa kaseem ya shigo ɗauke da abubuwan buƙata, fara dubata yayi ya tabbatar bataji ciwo ta ciki ba, sannan ya wanke mata jinin goshinta yayi dressing ciwon, ɗaura mata farin bandage ya fara, gashinta da yake da tsawo ya rufe mata fuskan, baya kaseem ya fara maida gashin amma idan wuyanta ya