Showing 24001 words to 27000 words out of 32935 words
yake kallonta bakinshi yana rawa yace "m...m..me?"
ta saki hanunshi ta juya baya tace "eh sunana kenan na gaskiya"
yace "kenan ke kanwar zeenat ce?"
juyowa tayi tana smiling face "unty zeenat ko kuma zeenat haka gatsau? Anyway ni kanwar zeenat ce wacce kuka kashe a ranan data haihu ba ita kaɗai ba har jaririn data haifa saida aka salwantar, kuka bata wahala kamar baiwa, kuka sa ta tsani rayuwa da abinda ke cikin duniya baki ɗaya, kuka azabtar da ita har saida ta haukace sabida azaba daga karshe kukayi ajalinta, na rantse banzo gidannan ba saida na shirya, dukanku saina ɗau fansan abinda kuka yiwa yayata, daga ni sai ita mahaifiyarmu ta haifa na taso cikin kaunar yayata zeenat, batada masoyiya saini"
share hawaye tayi tace "dani da zeenat wannan auren shine ya fara raba duk wani shaƙuwan da mukayi, yayanku hameed shine mugun daya fara lalata mata rayuwa yasa mata ɗaci a ranta, yasa ta rasa hope, daga karshe ya kasheta"
kallonshi tayi tace "jeka ka faɗawa kowa cewar ni kanwar zeenat ce, jeka"
a hankali ya fara yin baya yana kallonta, hanu yasa akan kofa zai fita tace "sultan"
tsayawa yayi, tace "idan kaje faɗa musu kada ka manta ka faɗa musu kana canja alluran da ake yiwa hameed"
a razane ya cire hanunshi dake jikin handle yana kallonta idanunshi kamar zasu zubo, tayi murmushi me sauti tace "ka fasa zuwa ne? kaje mana sultan allura kawai kake canjawa idan ka faɗa musu ba zasu maka komai ba"
ganin ya tsaya turus ta fara takawa a hankali tasa hanu akan handle ɗin tace "tunda ba zaka faɗa musu ba ni bari naje na faɗa musu"
hanunta ya rike yana girgiza kai, murmushi ta kumayi tace "sakeni mana sultan"
bakinshi yana rawa yace "ki rufamin asiri ya kaseem zai kasheni"
tace "zan rufa maka amma akan sharaɗi"
ganin ya kasa magana tace "ko da wasa kada bakinka yayi kuskuren faɗawa kowa abinda ya faru, sannan duk abinda zanyi ya zama dole ka tayani ko kanaso ko baka so har sai na cimma burina a gidanku"
tace "ka amince?"
a hankali ya gyaɗa kai, tace "deal"
fita tayi daga ɗakin ta gansu tsaye hameed kuma yana zaune dafe da kanshi.
_Jiddah ce...✍️_
08144818849
[20/08, 2:11 am] Shuraihu Usman: 🌸🌸🌸🌸🌸
*ƘADDARA TA*
🌸🌸🌸🌸🌸
Na
*Jiddah S Mapi*
*Chapter 10*
~Share hawaye tayi tace "na bashi hakuri kuma ya fahimci banida sa hanu akan ɓatan meenat hasalima ban san komai ba"
tayi maganan tana kallon sultan daya fito jikinshi kamar ba jini, tace "ko sultan?"
gyaɗa kai yayi, tace "amma idan kuna zargina zan bar gidan"
kaseem yace "babu inda zakije"
ta tsaya kawai tana kuka, a hankali hameed ya daure ya tashi, share mata hawayen yayi ya rungumeta, ammi da kallo kawai take bin Aneeta, kashe mata ido tayi.
har kwana uku babu meenat babu dalilinta har ammi ta fara cire abin a ranta, cikin baƙin dogon riga me masifan kyau Aneeta take saukowa daga stair, dogon takalmi ne a kafarta me tsini ta rungume alkyabba a kirji tana taku kamar hawainiya, saida ta sauko ta tsaya tasa alkyabban da yayi masifan yi mata kyau, har kasa bayan yake ja, kallon sultan dake cin popcorn tayi sai kuma ta kalli fadeel tazo ta kwace popcorn ɗin, murmushi tayi mishi ganin yana kallonta tace "baka iya bismilla bane?"
shiru yayi, fadeel yace "unty aneeta kinyi kyau"
tace "sosai ko kaɗan?"
yace "sosai"
dariya mara sauti tayi sannan tace "sultan ka rakani mana"
a tsorace ya kalleta yace "zan zan"
tace "common yanzu fa zamu dawo ba nisa zamuyi ba"
a hankali ya tashi yace "to"
hanunshi ta rike zasu fita muryan ammi sukaji tace "ina zaki kaimin ɗana?"
tsayawa tayi bata juyo ba, ta karaso ta cire hanunshi daga nata tace "ina zaki kaishi nace? ko shima kashe shi zakije kiyi?"
murmushi tayi tace "ni ba kamarki bace..."
ammi cikin hasala zata mareta sultan ya tare, girgiza mata kai yayi alaman dan Allah kada ta mareta domin yanzu yana masifan tsoron aneeta zata iya kashe kowa kamar yadda ta faɗa.
murmushi tayi tace "tare mata kake sultan?"
yace "ammi please"
tace "shikenan ka bita amma inaso ka sani wannan yarinyar batada imani zakazo kayi dana sani"
yayi shiru, juyawa tayi zaiyi magana Aneeta taja hanunshi suka fita.
motar dake wanke tas bakin jeep me tsadan gaske ta shiga, gani yayi ta zauna a mazaunin driver tace "shigo mana ka tsaya kana kallona"
shiga yayi taja motan suka fita, ganin yadda take gudu da motan cikin kwarewa yasa yake kallonta, murmushi tayi bata kalleshi ba tace "karka damu bazan kasheka ba"
shiru yayi yana kallonta har suka yi nisa da gidan, wani unguwa yaga ta shiga dasu, a wani gida ta tsaya tayi hon buɗe gate akayi ta shiga, parking tayi ta fito, ganin baida niyan fitowa tace "fito mana"
a hankali ya fito, hanunshi ta rike suka shiga ciki, wutan gidan a kashe ta kunna sannan taja hanunshi zuwa wani ɗaki, buɗewa tayi suka shiga, ya kalli matar dake kwance akan gado ansa mata oxygen idonta a rufe duk gadon ansa wayoyi da remote nasu da alama kyakkyawan kulawa ake bata, tayi kissing na matar a forehead sannan tace "zauna mana sultan"
a hankali ya zauna akan stool dake gefe, tace "kasan wacece wannan?"
girgiza kai yayi
tace "wannan itace momy itace ta haifeni kuma itace ta haifi zeenat wacce yayanka ya kasheta, kasan meya sameta take kwance haka?"
girgiza kai yayi, tace "sabida mutuwan zeenat shi yasa tsinkewan zuciya ya sata a wannan halin har yau bata kara tashi ba, tana da likitoci biyu masu sirri da suke zuwa dubata a lokacin da abin ya sameta sai kuma daga baya na gane bs likitocin amana bane domin alluran da suke mata na kashe gaɓoɓin jiki ne, kasan da nayi bincike mena gano?"
girgiza kai ya kuma yi, tayi murmushin da yafi kuka ciwo tace "na gano wannan likitan da yake mata wannan mugun alluran hameed ne"
a razane ya kalleta sabida yasan hameed ba likita bane, tace "kana ganin karya nayi?"
yayi shiru, buɗe side drower tayi ta ɗauko wani waya ta kunna, hoto ta nuna mishi hameed ne sanye da kayan dr yana tsaye a ka matar yana jan ruwan allura, tace "wannan bashi bane? shine yake mata alluran da yake kara ɓata jikinta har yasa bata iya taka kafarta ta zama mara amfani tun tana iya magana har tazo ta daina, bayan ya kashe ƴarta kuma yazo ya lalata rayuwarta?"
share hawaye tayi cikin bushewan zuciya tace "bana kasarnan amma na dawo sabida ciwon da momy take ciki, na tsaida komai nawa na bar komai na bar karatuna da nakeyi a kasar cyprus, na rasa yayata wacce nafi sonta akan komai na wannan duniyan na rasa farin ciki na rasa komai sabida hameed kana ganin zan iya yafe masa?"
shiru yayi yana karewa hoton kallo tace "idan na yafe mishi ai Allah ma ba zai barni ba"
tace "wannan shine abinda yasa na fito da kai"
baice komai ba sai kallonta da yake, ta share hawaye tace "muje lokacin alluranta yayi dr zaizo yanzu"
binta kawai yake yi har ta rufe kofan suka koma motan, yana kallo ta share hawaye taja motan suka tafi, koda suka koma gida ɗaki ta wuce ta barshi a wajen.
Asmeeta Asmeeta?
sunanta yake kira yana haska toci, cikin bacci ta murza ido tace "uuumm waye yake tashina a baccina me daɗi?"
cikin tsawa yace "tashi mana"
tashi tayi da sauri tace "hamma najeeb meya faru?"
yace "ina take?"
da sauri ta kalli gefenta cikin yarantan da bata iya dainawa tace "ko ya shiga banɗaki"
yace "babu fito inaga ya tafi a shikin daren nan"
da sauri ta tashi ta fito, yana haska fitilan yace "muje"
fita sukayi domin nemota, da mamaki ya ganta a kofar gida tayi tagumi tana kallon shanyen dake cikin garke, lumshe ido tayi ganin suna haskata da fitila, itama sanye take da kaya irin nasu, murmushi tayi ganin ya haskata tace "hamma najeeb kaine?"
ya sauke ajiyan zuciya yace "me kakeyi anan? mutanen wannan garin basuda imani zasu iya kasheka tashi mu tafi gida"
tashi tayi suka sata a gaba suna baya, har ɗaki ya rakasu da fitilan ya fita yaji Asmee tace "meyasa kake son fita waje?"
murmushi tayi tace "idan mace ne ba kake zaki ce ba kike zaki ce, kice meyasa kikeson fita"
murmushinta me bala'in kara mata kyau tayi sannan tace "to me yasa kike son fita?"
tace "sabida banason ina zama a gida ina kallon hamma najeeb"
da sauri tace "sabida me?"
tace "ban sani ba amma idan na kalleshi sai naji zuciyata tana narkewa kuma nasan zan iya faɗawa soyayya dashi kuka na zan sameshi ba dan naga duk ƴammatan kauyen nan naku idonsu a kanshi kuma naga baya kula kowa ni kuma banaso nayi abinda zaizo ya dameni"
shiru tayi tana kallonta batace komai ba, murmushi tayi mata tace "amma Inaso wannan maganan ya zama tsakanina dake karki fada mishi kinji? sabida nasan watarana dolene mu rabu"
shiru tayi tana kallonta, tace "amma meyasa kike ganin ba zai soki ba?"
tace "sabida naga abinda yake gabanshi kawai yake yi baya shiga harkan kowa gashi baya magana wani lokaci idan kika tafi kiwo baya magana sai shi da mimi kawai yake surutu idan ta fita kuma sai gidan ya zama shiru"
murmushi tayi tace "ki mishi uzuri abinda ya faru a rayuwarmu shiyasa baya kula kowa ya saba da hakan idan kinga yana magana sai idan dani ko mimi, hakan ya samo asali ne saboda rashin kaunarmu da mutanen kauyen nan suke yi, hamma najeeb yasha wahala sosai kafin mama ta mutu"
tace "zaki iya bani labarinku?"
gyaɗa kai tayi tana kuka tace "babanmu ya mutu tun mama tanada cikina, mama batada lafiya mutanen kauye sunki kulata sunce wai itace ta kashe baba sabida ta gaji shanayenshi, hakan yasa suka tsanemu duk inda hamma yaje neman taimako sai su koreshi hakan yasa baya zuwa gidan kowa harda ƴan uwan babanmu dana mama, da haka har mama ta haifeni cikin wahala da azaba ta bawa hamma amanata, duk duniya babu abinda yakeso sai ni wacce na ɗaukeshi kamar babana shi yake kula dani tun ina jaririya har na girma, sana'ar baba ne bada magani hamma ya koya tun yana yaro yake bada magani hakan yasa nake binshi jeji kullum idan zai tafi har nima na iya bada maganin watarana idan baya nan nice nake bawa mutane, hamma yasha wahala kuma har yanzu yana sha shiyasa kikaga baya kula kowa, kada kiga laifinsa ko abokai baya dasu basa sonshi tun yana karami hakan yasa shima yake janye jkinshi daga su.
tace "kenan duk iyayenku sun rasu?"
tace "sun rasu hamma shine iyayena sabida yana sona fiyeda yadda yake son kanshi"
tace "to mai zai hana ku bar kauyen ku koma wani wajen da zama"
tace "ba zai yadda ba sabida na taɓa mishi maganan yashe zamanshi anan yafi mishi domin yana taimakon mutane da magani, macizai suna yawan taɓa mutane yana basu magani sannan duk wanda yake rashin lafiya da yaddan Allah idan hamma ya bashi magani yana jin sauki"
murmushi tayi ta lumshe ido haka kawai taji yana kara kwanta mata a rai.
wucewa yayi ɗakinshi bayan ya gama jinsu, akan tabarman da yake kwana ya zauna yayi shiru yana juya zancen ta a ranshi, bai taɓa jin zuciyarshi ya buga a lokacin da wata ta furta tana sanshi ba sai akan wannan aminan to amma yasan wannan batayi kalan kauye ba, daga ganin kayan jikinta da suka tsinceta dashi da kuma fatar jikinta duk da suma fatarsu me kyau ne amma nata ana gani zaka san wannan ba ƴar talakawa bane, kada ya yadda ya fara sonta shima suyi aure tazo ta tuna komai data manta, yasan ba zata yadda dashi ba idan ta tuna komai a kanta, har dare yayi nisa yana tunani da kyar ya samu bacci.
washe gari tunda tayi salla take zaune akan tabarman tana kallon Asmee wacce har yanzu salla take, saida ta idar tace "Asmee"
tace "na'am"
"sallah raka'a nawa kikeyi?"
tace "ni raka'a shida nake asuba shi kuma hamma da shike namiji ne yana yin takwas"
dariya tayi sosai saboda abin dariya ya bata, ta turo karamin bakinta tace "to me kina mana dariya? ba haka bane?"
tace "ba haka bane"
fara mata bayanin yadda ake salla tayi, mimi ta tashi daga bacci tace "Adda zanyi salla"
meenat wacce take jin yarinyar har cikin ranta tace "muje na miki alwala"
tace "to"
fita sukayi tayi mata alwala sannan ta dawo da ita ɗakin, salla me kyau ta sata tayi tace "haka zaki rinƙa salla kullum"
hamma ne yayi sallama ya ɗaga labulen cikin rashin magananshi yace "kuna lafiya?"
meenat data kasa ɗauke idonta daga kan kyakkyawan fuskanshi tace "muna lafiya"
ya kalli Asmee yace "zan fita idan kika kuskura na dawo gida naji kinyi faɗa da mutane a wannan kauyen wallahi saina kakkaryaki"
ta sunkuyar da kai tace "to"
fita yayi ta leka tace "yawwa ya fita yau zan zagaya dake ko ina na cikin kauyennan ki gani"
tace "to shikenan"
nono sukasha sannan sukaci shinkafa da wake tace "muje"
kallonta tayi babu mayafi babu komai amma wai zasu fita?
tace "kisa ɗankwali"
bata musa ba tasa ta duƙa mimi ta hau bayanta suka fita, yawo ta kaita ko ina na kauyen har wajen me tsire da yace yana sonta ai kuwa ya cika musu leda Asmee sai jin daɗi take ta karɓi ledan, murmushi meenat take tana kallonta wallahi yarinyar tana ranta sosai take jinta har cikin zuciyarta, ɗago manyan idanunta kamar kwai cikinsu fararen sal tayi ɗan karamin bakinta da nama tana tauna tace "kici mana ƴar uwa"
murmushi me kyau tayi sannan ta fara ci, tace "kin san me?"
girgiza kai tayi tana cin naman tace "kinga wannan me naman? kullum cewa yake yana sona, ni kuma sai naje kiwo na dawo saina ɗauko mimi muzo nan muci nama mu koshi da dare hamma najeeb ya kara kawo mana bakiga banida rama ba? baki ganni da kiɓa kaɗan ba?"
tace "sosai kinada hips kuma ance me cin nama sosai shine zai zama da hips"
tace "me kuma hips?"
bayanta ta taɓa tace "nan"
dariya tayi tace "amma da turanci ko?"
tace "eh"
tace "nima hamma yace idan yayi kuɗi zai kaini birni nayi karatu"
wasu ƴammata ne sukazo wucewa meenat taga sunata hararan Asmee itako asmee abinda ke gabanta take yi, har suka wuce basu daina hararanta ba harda tsaki, meenat tace "me haɗinki da waɗannan naga suna hararanki?"
haɗiye naman bakinta tayi sannan tace "ai Indai harara ne suyi zasu gaji idan har an haifi yarinya da jini tayi kuskuren kiran sunana ko taɓani, saide su kare a harara domin ko mimi suka taɓa saina kusan kashesu"
tace "me kika yi musu?"
tace "cewa suke wai nayi cikin shege na haifi mimi wasu ma wai cewa sukayi hamma ne yamin ciki"
shiru tayi tana kallonta zafi takeji a ranta idan tana maganan duk da tana kawarka ta mayar kamar ba komai ba amma zakaga tsantsan zafin da takeji akan fuskanta.
ta kula batada kawaye babu me zuwa mata amma da alama tanada faɗa sosai, ta rike hanunta tace "sharri kayan kwalba ne gashi kin fisu da komai kinfi duk ƴammatan garinnan kyau duk da kyawawane amma kin fisu kyau ga kuma yayanki da yake bala'in sonki bayason abinda zai taɓaki"
ta turo baki tace "to na gode"
saida suka cinye tas kafin tace "mimi hau baya mu tafi lambun malam garba"
hawa bayan tayi duk inda zasuje sai ta goyeta duk da yarinyar batada rama amma bata jin nauyinta ko ina zasuje tana goye a bayanta, tafiya sukayi da nisa har meenat tace "na gaji gaskiya ba zan iya tafiya ba"
Asmee tace "kiyi hakuri ki daure mun kusa zuwa"
saida suka kara tafiya me nisa kafin suka isa lambun, sauke mimi tayi ta kalli meenat da take tsoron wajen domin ga duhu ga kukan tsuntsaye, tace "rike mimi ku tsaya anan ku shirya zamu iya gudu a kowane lokaci domin idan malam garba ya kamamu zai kaimu gaban me gari ayi mana shegen duka a gaban mutanen gari"
dafa kirji tayi tace "na shiga uku Asmeeta mu gudu to karki shiga"
tace "ke dalla matsoraciyar banza ni ai sai idan banyi niyan tsinkan komai ba wallahi babu wanda ya isa ya hanani"
tattare zaninta tayi tace "ku jirani"
tace "dan Allah Asmeeta kar..."
cikin sanɗa taga ta shiga lambun, a hankali take tafiya har ta shiga ciki, tsinkan mangoro da ayaba da gwaiva ta fara, tsinka take tana sawa a ɗankwalin data cire, tun daga nesa taji muryanshi yana cewa "waye? waye yake min sata?"
durkusawa kasa tayi ta rufe baki cikin sanɗa take gudu har ta samu ta fita daga lambun, gani tayi ya biyosu a guje, tace "Ameena mu gudu"
meenat cikin tsoro ta fara gudu da mimi a bayanta, tun yana binsu har ya gaji ya tsaya yana ɗura ruwan Ashar da tsinuwa, saida sukayi nisa kafin meenat ta sauke mimi cikin wani irin gajiya ta kwanta a kasa tana nishi, itama Asmee zama tayi a kasa tana numfashin gajiya, mimi tace "kin tsinko mana Adda?"
ta gyaɗa kai tace "gasu nan"
saida meenat ta huta tace "gaskiya Asmeeta bakyajin magana"
dariya tayi sosai tace "tashi muje gida kinga har dare ya kusa yi"
tashi sukayi suka fara sabon tafiya suna isa gida ta fara shiga cikin sanɗa sabida kada hamma najeeb yaji shigowansu may be ya dawo, tana sa kafa taci karo dashi tsaye yana rike da bulala, mimi tace "wayyo kawu da bulala?"
Asmeeta hawaye ta fara ganin kallon da yake mata, bulalan ta kalla take ta zubar da abinda ke hanunta, kallo yayi sannan ya kalli Ameena da itama take ɓuya a bayan Asmeeta, yace "ina farin shanun?"
waro ido tayi ta dafa kirji tace "laaa na manta banje na ɗaukoshi ba yau"
juyawa tayi zata fita a guje tace "yana bakin kogi"
yace "dawo"
dawowa tayi tace "hamma dan girman Allah kayi hakuri wallahi zanje na ɗauko"
yace "bayan an sace shine zakije ki ɗauko? sau nawa nake faɗa miki ki rinƙa maida hankali akan kiwo kisan duk yawan shanayen?"
cikin rawan murya tace "sau dayawa"
yace "ina kika samo wannan abin?"
tace "a..a...a wannan ne"
mimi tace "a lambun malam garba"
sallama akayi ya kalleta kafin ya amsa ya fita, malam garba ne ya kawo kara kamar yadda ya saba tareda cewa "wallahi dan inajin nauyinka ne sabida kaine kayi jinyan mahaifina kafin ya mutu ba dan haka ba wallahi dana jima da ɗaure kanwarka, yarinyar nan sata take min a lambu kuma ta gudu?"
hakuri ya rinƙa bashi da kyar