Showing 54001 words to 57000 words out of 85226 words

Chapter 19 - BA SONTA NAKE BA

Start ads

20 Aug 2025

179

Middle Ads

ta ta gefen ido ganin hankalin ta baya kan shi ya mike ya dawo gabanta ya zauna cikin natsuwa yace " na duba su duk sunyi kyau sosai Baawa".

Murmushin jin dad'i tayi tana ajiye wayar ta a gefe sannan ta maido da hankalin ta gare shi ta fara magana tace" yanzu abinda ya rage ga kayan da zatayi amfani dasu a events na bikin ku naka da nata duk suna wajan mahaifiyar ka it's a small gift from me".

Mom da taji kaman tayi kuka dan haushi dama niyyan ta in har ba tayi magana ba ta tafi ba zata aika min su ba, cikin dauriya tace" eh gasu nan Son, zoka duba Baawar ka ta sayo muku latest designs na birgewa".

Karasawa yayi zuwa inda Mom take nuna mishi ya zauna ya bud'e had'add'un trollys d'in da wani cool suits mai d'an karan kyau ya fara arba wanda kana gani ba sai an fad'a maka kasan mai tsada ne, cikin farinciki ya cigaba da duba su d'aya bayan d'aya ko wani event da kayan da zai saka har zuwa ranar daurin aure kuma kowanne da takalmi da wrist watch d'in shi, godiya ya fara yi mata cikin jin dad'i dan kayan sun burge shi sosai.

"I'm glad u like it, sai dai ka manta baka duba na amarya ba" ta amsa mishi itama cikin farinciki, sai da ta fad'a ya tuna da wata amarya, bashi da wani zab'in illa kirkiro murmushi tare da bud'e first 1 dake kusa shi.

Sai da yaji numfashin shi ya d'an d'auke na second biyar da yayi arba da wata gown na Indian material sai walwali da d'aukan ido yake ya had'u har ya gaji da had'uwan, daurewa yayi ya cigaba da duba kayan Wanda gaba d'aya anko ne da nashi sai dai a tunanin shi wayan nan zasu fi nashi tsada tunda su kowanne ga jewelry da takalmi da jakan shi.

Tun yana kirkiro murmushi na kar a gane halin da yake ciki har zuciyar shi ta rinjaye shi fuskar shi ya nuna abinda ke cikin zuciyar shi, Baawa da hankalin ta yana kan shi tana jiran taga yayi ta murnan ganin irin kayan da ta hadawa amaryan shi sai taga tsab'anin haka fuskan duk a murtuke yake duba su.

Cikin sanyin jiki ta fara mishi magana" da alamu dai Zafar kayan amaryar nan basuyi maka ba ko?"

" Haba Baawa wad'an nan kayan ko makaho ya shafa su ya san sunyi matukar kyau, abinda yasa kika gan ni haka jikina ne yayi sanyi ban san wani kalamai zanyi amfani dasu ba wajan gode miki domin kayan sun burge ni sosai" yabata amsa yana gyara mood da kawata fuskar shi da yalwataccen murmushi.

"Menene a nan da har kake fad'in haka Son, ko ka manta kai d'in gudan jini nane?"

Girgiza mata kan sa da yake kasa yayi ya cigaba da murmushin dole.

"Good yanzu abinda nake so da ksi shine kada ka bar kayan anan ka kai su can bangaren ka ko zuwa dare sai ka kai mata ko?"

"Toh Aunty mun gode Allah ya saka da alkhairi" yace mata.

"Ameen my son Allah ya nuna mana ranan lafiya mu sha biki" tace tana d'an dariya 'yar uwar ta Hadiza na taya ta dan su Mom sun bar musu parlorn tuntuni.

Maida boxes d'in yayi ya rufe ya kira masu aiki suka taya shi d'auka yayi musu sallama ya fita, a parlour shi suka ajiye suka fita shi kuma ya nemi waje ya zauna yana ta jan tsaki dan shi raini ne baya so da girman shi da komai wai shi za'a aika wajan 'yar yarinyan ga Sadeeq ma jiya yazo mishi da rainin hankali wai shi zai kai mata invitation cards shi kuma yace in ba zai Kai da kan shi ba ya zubar dasu a bola shi Kuma ya watsar mishi akan gado yace ga bolan nan, da gudu ya bi shi ya fita yana mishi dariyan mugunta.

"D'an iska zamu had'u ai sai na koya mishi hankali" yace shi kad'ai kaman wani sabon kamu.

Ni kuma gyaran nan da akayi min na kwana 2 ya karamin masifan kyau kaman an canza min fata ta saboda yanda ya kara laushi da tsantsi ga kamshi na musamman da yake tashi jikina.

Da daddare bayan mun idar da sallah isha'i Inna ta kawo min wani had'i da akayi na madara tace in shanye in bata kofin ta, karb'a nayi na shanye na saboda ta zata auren gaskiya zanyi take b'ata kud'in ta bata san auren wata 2 ko uku bane.

Lafiyayyan abinci ta zubo min shima tace in cinye dan kwanakin nan abinci masu gina jiki take bani Kuma shine ya bada gudumuwar hana rama ta bayyana a idon mutane, ina cikin tsakurar abincin ina sauraron wa'azi da sheikh Aminu daurawa da yake akan rayuwa a tashan sunna tv,o sosai wa'azin ya saukar min da natsuwa domin kaman dani yake yi.

Sallaman yaron makocin mu da yayi yasa na dago da kai na tare da amsa mishi kasancewar ni. kad'ai ce a parlour Inna tana kitchen.

"Wai ana kiran ki inji wani mai mota a waje".

Rasss shine sautin da naji zuciyata ya bada, na kasa bashi amsa saima zuciya ta daya tafi tunani waye zai kasance kenan,Yaya na ko d'an rainin hankali nan ne?

Koma wanene ina daidai da shi, kamin in samu amsan da zan bashi naji muryan Inna a kaina tana " baki ji bane ana kiran ki kikayiwa mutane shiru ko duk salon wulakanci ne haka, wato duk maganganun dana gaya miki ta bayan kunne suke wucewa ko?"

Kamin in bata amsa ta cewa yaron yaje yace tana zuwa, shi kuwa ya amsa da toh ya fita abinsa.

Itama kitchen ta koma ba tare da ta kara kallon inda nake ba, hannu nasa na goge hawayen da suka zubo min sannnan na mike na d'auki hijabi na dake kan kujera na saka na kama hanyan fita nima.

Har na kai hannu zan bud'e kofa naji muryan Inna a bayana tace" ki tabbatar kin shigo dashi parlour baki na Baban ku kada ki bar shi a waje kuma in kun shigo ki zo ki kai mishi ruwa".

Da toh na amsa na fita, ina jan kafa har na fita waje na tsaya a kofar gidan mu da yanzu ya koma gate, na kusan minti uku tsaye a wajan ina kallon motan banida niyyan karasawa, shima kuma ko fitowa bai da niyyan yi balle in saka ran zai fito.

Tunawa da yanda naga Inna ta b'ata ran ta d'azu yasa na fara takawa a hankali kaman mai tsoron kasan har na isa jikin motan na tsaya.

Sauke glass d'in motan yayi yana min kallon up nd down fuskar shi d'auke da wannan shu'umin murmushin sa na gefen baki " 'yar Mallam Ni kike jira in je in same ki kenan, baki san cewa duk zuwan da zaki ga nayi nan dalili yake kawo Ni ba wai dan kin isa ba...."

"Kaman yanda nima dalili ne yake sakani fitowa ba dan kana gaba na" na katse shi nima ba tare da na bari ya gama ba.

"Really!!! I like ur courage, ki cigaba but ki rike a ran ki cewa zaki gane kuskuren ki when we are together under the same roof" yace har yana wani cize lebe.

Kaina na kawar gefe ina son bashi amsa amma abinda nake hangowa a nesa damu kuma cikin d'an duhu shiya d'auke min hankali har na kasa kula shi, shima ganin hankalin na baya tare dani yasa ya fito tare da sauke kayan da ya kawo ya kira yara da suke wasan su a gefe yace su shigar min dashi cikin gida.

Shiga motan shi yayi ya tayar yayi revise, karan motan shi da naji shiya da na mayar da hankali na kan motan ba tare da ya kara ko kallon inda nake ba yaja motan shi ya tafi na raka shi da ido, sai da ya kusan b'ace min sannan na dawo da ido na wajan dana d'auke sai dai Kuma yanzun naga wayam babu kowa a wajan sai duhu da ya kara mamaye wajan.

Dafe Kai na nayi da naji yana juya min saboda tsananin ciwo da yake min , da kyar naja kafafu na da suka min nauyi na nufi gida ina mai mamakin ya akayi Inga mutum kuma lokaci d'aya kuma ya b'ace, ko dan na kasa cire shi a raina shiyasa yake min gizo.
[6/16, 9:15 PM] Golden Pen Writers Associ: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹

_A story about love and sacrifice._

_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_

_*From The Fantastic Writer of*_

```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```
```UWANI```

*_And now_*

*_BA SONTA NAKE BA_*

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

*wΜΆΜΆΡ” Ξ±rΜΆΜΆΡ” Π²Ρ”Ξ±rΜΆΜΆΡ”rΜΆΜΆ'sΜΆΜΆ ΟƒfΜΆΜΆ sΜΆΜΆΟƒ gΜΆΜΆΟƒlΜΆΜΆdΜΆΜΆΡ”nΜΆΜΆ pΜΆΜΆΡ”nΜΆΜΆ*
*wΜΆΜΆΡ” wΜΆΜΆrΜΆΜΆΓ­tΜΆΜΆΡ” Ξ±sΜΆΜΆsΜΆΜΆΓ­dΜΆΜΆΓ­ΟƒuΜΆΜΆsΜΆΜΆlΜΆΜΆΡ‡ pΜΆΜΆΡ”rΜΆΜΆcΜΆΜΆΡ”Γ­vΜΆΜΆΡ” nΜΆΜΆΟƒ pΜΆΜΆΞ±Γ­nΜΆΜΆ,*
*sΜΆΜΆΟƒ mΜΆΜΆΞ±gΜΆΜΆΓ­cΜΆΜΆΞ±lΜΆΜΆ ΟƒuΜΆΜΆrΜΆΜΆ cΜΆΜΆrΜΆΜΆΡ”Ξ±tΜΆΜΆΓ­vΜΆΜΆΡ” gΜΆΜΆΟƒlΜΆΜΆdΜΆΜΆΡ”nΜΆΜΆ pΜΆΜΆΡ”nΜΆΜΆ* ✍ *,Π²Ρ”hΜΆΜΆΟƒlΜΆΜΆdΜΆΜΆ ΟƒuΜΆΜΆrΜΆΜΆ wΜΆΜΆΟƒrΜΆΜΆdΜΆΜΆsΜΆΜΆ.Ξ± pΜΆΜΆrΜΆΜΆΟƒdΜΆΜΆuΜΆΜΆcΜΆΜΆtΜΆΜΆ ΟƒfΜΆΜΆ ΟƒuΜΆΜΆrΜΆΜΆ pΜΆΜΆΡ”nΜΆ*ΜΆ *,sΜΆΜΆΞ±vΜΆΜΆΟƒuΜΆΜΆrΜΆΜΆ ΟƒuΜΆΜΆrΜΆΜΆ wΜΆΜΆΟƒrΜΆΜΆdΜΆΜΆsΜΆΜΆ, fΜΆΜΆΟƒrΜΆΜΆ Γ­tΜΆΜΆ wΜΆΜΆΓ­lΜΆΜΆlΜΆΜΆ* *cΜΆΜΆΞ±uΜΆΜΆsΜΆΜΆΡ” Ρ‡ΟƒuΜΆΜΆ nΜΆΜΆΟƒ pΜΆΜΆΞ±Γ­nΜΆΜΆ.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buΖ™ata namu daga farko.

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana Ζ™ara mana Ζ™arfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*26&27*

Haka na shigo ciki hannuna dafe da kaina, ragwajab na zube akan kujera ina lumshe ido ba tare da na lura da kayan da aka shigo da su ba Inna ta saka su a gaba tana aikin kallo.

"Ban san yaushe kika samo wannan halin na rashin ji ba Zareefa, yanzu duk maganan da na gaya miki amma babu wanda kika d'auka kika bar bawan Allah nan a waje ko balle ki kai mishi ruwan sha?"

Ban iya bata amsa ba sai goge hawaye da suka ki tsayawa nake dan na san ba lalle ne ta amince da abin da zan fad'a ba kasancewar bata san komai akai ba, nima kallon kayan da ban san daga ina suka zo ba nake domin ko za'a yanka ni ba zan iya cewa shi ne ya kawo su ba.

"Kai jama'a wannan lodin kaya daya kawo su kuma na menene, uhum harda su gwalagwalai kuma da alamu na fitan biki ne ko?" Na tsinkayi muryar Inna ta katse min zancen zucin da nake.

Bani da mafitar da ta wuce na amsa mata da " eh " tunda yanzu na fahimci daga ina kayan suka fito.

"Toh Masha Allah amma hidiman nasu yayi yawa bana so gaskiya ki gaya mishi su rage hakan nan kinji?" Nan ma dai gyad'a mata kan nayi ina mamakin dukiya da aka narkar wajan sayan kayan nan.

Nan na kwanta kan kujera duk abin duniya ya ishe ni na rasa ya zanyi da rayuwata, ban tab'a kawowa a raina zan shiga cikin irin tashin hankalin makamancin wannan ba

A kwana a tashi babu wuya wajan Allah dan yau shine karshen gyaran fata da ake min sai lalle da aka shiga yarfa min na jan lalle gwanin sha'awa taso a yi min kitso nace mata bana so ta bar min gashi na haka, ba dan taso ba ta kyale ni suka maida hankali kan lallen.

Sai bayan sallah isha'i muka samu daman komawa gida ta d'eba min wasu kayan gyaran tace in rinka yi a gida tunda auren saura kwana 3, karb'a kawai nayi na amsa mata da toh amma ba dan ina da niyyan yi ba.

A kofar gida suka sauke ni Maryam bata shiga ba saboda dare yayi suka wuce tana ta santin lallen da akayi mata wai yayi kyau, ni dai ban iya biye mata na juya zuwa gida abina kasancewar na kwaso gajiya.

Mutane na gani cike a cikin gidan mu ana ta cece kuce kuma kana jin maganan kasan kaman fad'a ake , d'an d'aga kai na nayi naga matan gidan mu ne harda makota, ban kara gigin d'aga kai na ba na wuce b'angaren mu tunda banga Inna ta a wajan ba.

A parlour na samu Inna da 'yan uwan ta zaune sun saka kaya a gaba suna maida abinda ya faru duk fuskan su babu dad'i sai ita Inna ce ba zaka gane mataa ba.

Zama nayi a kasa kan carpet na fara gaishe su d'aya bayan d'aya duk suka amsa min fuska sake, muna gama gaisawa na wuce kitchen neman ruwan sha anan ma wasu kayan abinci na gani gari guda.

Ina cikin shan ruwa ne naji Ya Maaji tana magana cikin b'acin rai wanda ya sani maida hankali kan zancen nasu I really want to know what happened.

"Ni dai idan kun san ba zaku canza halin ku ba wallahi karshen ta ba dani za'a yi bikin nan ba, haba wannan wacce irin rayuwa ce ayi ta cutan ka ana kunsa maka bakinciki amma ka kasa ramawa, wa za'a nunawa hakurin muma ai muna da itan matsalsr idan yayi yawa sai a maida ki kwandon shara yanda kowa ya kwaso nashi kan ki zai juye".

"Gaskiya ne hakurin Bintu yayi yawa sosai har ta doke Yaya wajan sanyin hali, amma wannan zalincin ne dai ba zamu bari ba dole ne a d'auki mataki saboda gaba" cewar Aunty Batool.

"Kina ji fa ita Bintun da bakin ta yanzu take cewa ba yau ta fara yi ba wai ranan da aka fara musu gini an ga wasu layu wanda aka kona ita kuma a take ta fara iface-iface wani babban abin takaici wai ita da Zareefa su sukayi mata addu'a har ta samu lafiya...."

"Har ta samu kafan komawa wajan bokan ta zaki ce Batool, in ba dan Allah ya takaita wannan yaro Ibrahim ya ganta yazo ya fad'a ba, da shikenan auren nan ya fasu amma da yake bata da kunya bakin ta bai mutu ba ana magana tana mayarwa" fad'in Ya Maaji.

"Ban ki ta naku ba nima ba wai kuma fad'an ne ban iya ba, amma abinda nake son in tuna muku duk wanda ya rike Allah in ba wani ikon sa ba babu abinda zai same ka, ku duba mana sau 2 tayi yunkurin cutar da mu Allah yana mayar mata da abin ta.

Ban so kuka kula ta ba, jibi yanda asirin ta ya tonu cikin bainar jama'a wannan ma ya ishe ta ishara, mu kuma bama gajiya da d'aga hannayen mu sama insha Allah, Allah zai kare mu" Inna ta basu amsa cikin sanyin murya babu wacce ta kara cewa kala da alamu maganganun ta ya kashe musu jiki.

"Innalillahi wa Inna ilahi raji'un" shi kawai nake ta maimaitawa tare da sulalewa na zauna dabas kan tiles na kitchen d'in, cikin tashin hankali amma ni kam Ibrahim bai kyauta min ba da yazo ya fad'a har aka dakatar da ita, ina ma tayi nasaran sake binnewa da shikenan na fita daga wannan cakwakiyar matsalan.

"Gata da hassada da ya gama bin jinin jikin ta dubi yanda ta fito wai tana nuna adawar ta a zahiri kan kayan cin-cin da aka kawo" naji muryan Aunty Fatima tana magana cikin d'acin rai.

Sai ana na fahimci ashe kayan da na gani kayan cin-cin ne kenan, shikenan yanzu da gaske ake aure za'a yi min, auren ma da wanda bai san daraja ta ba?

Hawaye sai rige-rigen saukowa suke banyi yunkurin hana su ba na bar su suna kwarara domin yana rage min rad'ad'in dake cikin zuciya ta.

Muryan Inna naji tana kwala min kira ba shiri na mike daga zaunen da nayi ina share hawaye na na fito duk suka bini da kallon tausayi .

"Me kike yi a kitchen d'in tun d'azu" ta jeho min tambaya,

"Ruwa na sha " na amsa mata cikin murya kuka, kan kace me kuma hawaye suka fara kwaranya.

"Daga tambayan ki shine zaki fara min kuka? Bari in tashi inyi miki abinda zakiyi kukan da hujja" Inna ke fad'an haka tana shirin mikewa, da gudu nayi d'aki na maida kofa na rufe ina jin su Ya Maaji suna mata fad'an kada ta kuskura ta tab'a ni ta bar ni inyi kuka na, ban ji karshen maganan su nayi shirin kwanciya na kwanta abina.

Da washe gari ga mamakina ashe duk basu tafi ba anan suka kwana sai ya Maaji da ta kwana gidan Maa, da rana ya fara yi sai ga gidan mu ya fara cika da 'yan uwa ashe wai yau ake cin-cin ni dai ganin sun fara yawa na wuce bangaren su Maman Dije saboda kowacce ta ganni sai ta kira ni da sunan amarya basu san hakan kona min rai yake ba shiyasa na gwammace in tattara in bar musu gidan su kara ta.

Kamin in wuce naji sun fara sa-in-sa da 'yan uwan Baba da suka zo cewar su zasuyi, su Aunty Batool kuma suka ce anyi magana da professional bakers su zasuyi kasancewar komai ya zama na zamani ita kuma Gwaggo Hinde ta fara masifa wai ai zagin su akayi a fakaice meye basu iya ba da za'a ce zasu kira wasu suyi dama sun raina su.

Wucewa ta nayi abina ban san ya suka kare

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login