Showing 3001 words to 6000 words out of 85226 words

Chapter 2 - BA SONTA NAKE BA

Start ads

20 Aug 2025

168

Middle Ads

Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce;

اَللَّهُمَّ فَأَيـما مُؤْمِنٍ سَبَبْتُهُ فَاجْعَلْ ذَلِكَ لَهُ قُرْبَةً إِلَيْكَ يَوْمَ الْقِيَامَةِ.

Allahumma fa'ayyuma mu'minin sababtuhu, faj'al zalika lahu kurbatan ilayka yawmal qiyamati.

Ya Allah! Duk wnai mumini da na zage shi, to ka sanya wannan ya zamanto sababi gare shi na samun kusanci zuwa gare Ka ranar kiyama.

*~INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?~*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*


_Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samun wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook_. 👇


https://www.facebook.com/101594048306878?referrer=whatsapp


_Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu._


*2*

Kasa cire rigan nayi na zaro ido waje ina kallon Innara na ce," Inna kud'in common entrance d'in kika basu?"


"Ya kike son inyi? Kin san halin Aisha sarai a gidan in ta fara fitina zata kai awa goma tana yi ba tare da ta gaji ba,ni kuwa kin san ba iyawa zanyi ba gwara in bata a rabu lafiya gobe ma idan zaki shigo gida kada ki natsu " Inna kenan ta bani amsa.


Zama nayi da rigan a wuyan na ina hawaye na ce," shikenan za'ayi banda ni kenan,ko yau ina kallo akayi ta rabon abubuwa a makaranta ni ban samu komai ba akan 200 balle 1500 nasan gobe ko class ba za'a barni in shiga ba".


"Haka Allah ya kaddara ba zaki rubuta ba a wannan shekaran amma kiyi hakuri zuwa shekara mai zuwa ko kuma muyi addu'an Allah ya kawo wata hanyan,kinji ko?" Inna ta fad'a min cikin rarrashi.


Goge hawayen fuskan ta nayi na tashi na cigaba da cire uniform d'in na ba tare da na kara cewa komai ba.


"Ki d'auki hamsin cikin d'ari ukun daya rage kije ki sayi wani abin kici" cewar Inna.



Dariya na fara kyakyalewa da shi harda rike ciki sai da nayi mai isa ta sannan na ce," ai inna ciki na kaman zai fashe saboda koshi, dan lokacin da Hajara tayi b'ari almajirai suka fara wawaso nima roba 2 na wawashe na cinye tas abina Gwaggo Aisha data ji haushi kinji yanda ta zuba min dundu a baya Wallahi ko jin zafi ma banyi ba".



Cikin tsuke fuska Inna ta ce," wai ya akayi kika yi musu b'ari? Kullum inayi miki fad'an ki natsu amma ba kya ji ko?"



Daina dariyan nayi sannan nayi kalan tausayi na fara bata labarin abinda ya faru a makaranta har zuwa yanda mukayi karo da Hajara,ajiyar zuciya Inna ta sauke tana mai jin tausayin na ta ce," hakuri zakiyi Zareefa insha Allah wata rana sai labari,karatu kuma da yardan Allah zakiyi shi".



Gyad'a kai kawai nayi na fita yin alwala zahar a lokacin duk yaran gidan anyi musu abin sana'a duk sun fita talla,ina idar da sallah na fara shirin islamiya shi kam cikin dokin zuwa nake shirin na kasancewar a can bana takura kaman boko.



Akwai wani Malamin mu da yake d'aukar mu Qur'an shi ya tsaya minsosai sabo kokarin na dan har kudin wata 500 shi yake biya min domin kullum dai-dai nake kawo hadda ta yanzu haka mun bawa izufi 30 baya.


Ina gama shirin na nayiwa Innata sallama na tafi.



Ina fita Inna ta kwaso uniform dana cire ta hau wanke min da sauran Omo da ta rage jiya,tanayi tana jin su suna ta haice-habaicen su ta gama ta shige d'aki ta rabu dasu.


Mun taso a islamiya ni da kawayen na muka nufi gida muna d'an wasan su na yara,muna zuwa dai-dai gidan mu na fara jin muryan Baban mu yana ta masifa kaman zai ari baki.


Dariya sauran yaran suka fara har suna lekowa ta rububben ginin daya zagaye gidan.


Jiki a sanyaye na nufi cikin gidan namu dan nasan yanda Baba yake d'aga muryan nan nasan da inna ta yake,muryan Gwaggo Aisha naji tana kara zuga Baba da fad'in karya da gaskiya.


"Toh ai Mallam dan ma baka ga irin rashin kunyan da yarinyan nan tayi min a waje ba,inda zaka san da gayya ta b'arar da kayan sana'a shine,itace farkon daka wawa sannan sauran almajirai suka bi bayanta.


Koda yake b'ata baki na nake ina gaya maka abinda ya faru na san babu wani hukuncin da zaka d'auka tunda 'yar amayar ka ce abin sonka".



A fusace Baba ya juyo kanta yana," wannan wani irin maganan banza kike min matar da *Ba sonta nake ba* aka lika min ita dole yasa na karb'a dan kar inyi asaran kud'i na,amma wallahi Aisha kin cuce ni"..


Gwaggo Aisha ta saki shewa dama Kalmar da take son ji kenan.



Baba ya cigaba da fad'an shi inda yake cewa," duk kin bi kin b'ata yarinya bata ganin kowa da darajan a gidan nan da anyi magana kice wai boko take sai kace ki d'in bokon kikayi aikin banza kawai zata zo ta same ni a gidan sai jikin ta ya gaya mata"


Yana juyowa muka had'a ido ina can makure karshen bango ,aiko baiyi wata-wata ba ya nufo ni zai sake min wannan rankwashin sa nan da sai yasa kullum na saki fitsari a wando.


A guje nayi d'akin mu na shige kamin ya kama ni sanin cewa in ba wani babban dalili ba baya shigowa,cikin sa'a kuwa bai shigon ba ya tsaya a tsakar gida yana cigaba da fad'an,sam na daina jin me yake cewa domin ganin Inna ta na kuka abinda ban tab'a gani ba kenan tun tasowa ta dan komai akayi mata a gidan ko Baban mu ko matan gidan sai dai tayi murmushin mai ciwo tace akwai Allah.



Toh tana furta wannan kalman duk yanda za'ayi da ita ba zata kuma tankawa ba na sha tambayan ta me yasa itama ba zata ke rama cin fuska da ake mata ba sai dai tayi wannan murmushin nata mai ciwo ta ce," bakomai Zareefa akwai Allah" daga nan kuma ba zata kara cewa komai ba.


Zuwa nayi har gaban ta na durkusa a gaban ta tare da d'aura hannu na kan guiwoyin ta na ce," Inna kuka kike,meya same ki?" Duk na jero mata wayan nan tambayoyi a lokaci guda.


Murmushin nan nata mai ciwo tayi min kana ta ce," babu komai ba kuka nake ba wani abu ne ya shiga ido na".


Ba dan na yarda ba nayi shiru nasan ko abinda ake mata a gidan nan dole tayi ta kuka kullum,komawa gefe nayi na zauna ina kallon ta tana dinke min wuyan uniform d'ina daya yage bata kuma yarda ta zubar da hawaye ba.



Da washe gari da safe bayan na sayo alale na naci Inna ta bani 200 a cikin kudin daya saura ta ce in kai makarantan nima a bani bani sabon uniform d'in inya so ko shekara mai zuwa sai in zana jarrabawan.



Cikin matukar farinciki na nufi makaranta yau nima za'a bani kyautan kayan makaranta kaman sauran d'alibai.



Direct office d'in principal na wuce ina jin kaina yau kaman bani ba,bayan na gaishe shi na bashi kud'in na ce ni jiya ban samu daman zuwa ba shiyasa ban samu komai na rabo ba.


Tambayan shekaru na yayi na fad'a mishi ya ko duba ya ciro uniform sabo dal ya miko min,murna fal jikina na karb'a amma sai na kasa tafiya ina jiran jaka da sauran tarkace.



Ganin na ki tafiya ya ce," me kike jira kuma?" Kasa nayi da kaina na ce," Sir su jaka da takardu suma ban samu ba".



"Okay toh sai gobe ko anjima dan suna store,ya suna ki kuma a wani class kike?"



"Suna na Fatima Hassan,kuma ina class 6A" na bashi amsa.



"Toh kije anjima zan sa akai miki" cike da farinciki na juya na koma ajin mu feeling proud.


A wajan assembly akayi announcing cewa duk wanda bai biya kud'in common entrance ba ya koma gida dan zuwa nan da awa 2 za'a fara kuma ba barin mu za'ayi mu shiga ba,nan take murna ta ya koma ciki.


Jiki a mace na kama hanyan gida dan nasan zaman nawa bashi da amfani,ina tafiya ina hawaye saboda na kwallafa rai na akan jarrabawan,shikenan inaji ina gani mates d'ina zasu wuce ni.



Ina tafiya cikin tafiya naji horn a kusa dani ,matsawa gefe na karayi maimakon ya wuce sai naga ya tsaya kusa dani yana kallo na ya ce," kanwata meya same ki kike kuka akan titi?"


Kallon shi na tsaya yi d'an kyakkyawa dashi duk da ba fari bane.


"Kiyi magana mana kanwa ta?"ya katse ni.


"Kud'in common entrance ake nema shine aka kore ni dan ban biya ba" na bashi amsa sabon hawaye na bin kunci na.



"Oh stop crying,kiyi shiru muje makarantan naku in gani" yace yana fitowa daga cikin motan shi.



Tsayawa nayi kallon shi ba tare da na motsa ba, murmushi shimfid'e a fuskar shi ya zagayo inda nake tsaye ya rankafo da kan sa kusa dani ya ce," me kike tunani ?"


"Inna ta zata min fad'a ta hana ni magana da wanda ban sani ba" nace ina kara komawa baya.



"Kada ki damu ni Yayan kine muje zan miki bayani kin ji?" Gyad'a mishi kai nayi muka koma makaranta dama banyi nisa ba.


Office d'in principal muka tafi bayan sun gaisa ya mishi bayanin cewa shi Yaya nane yazo biya min kud'in common entrance,ni dai ban ce komai ba sai bin su da nake da ido,a take ya cire kud'i d'ari biyar- biyar sabbi fil ya biya muka fito ya ce," kije class kuma kiyi kokari sosai kinji kanwata?"



Murmushi ne ya kwace min na gyad'a kai na tare da rugawa zuwa aji.
[8/31, 6:05 PM] Ummee Yusuf: 🦚🌹🦚🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹

_A story about love and sacrifice._



_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_


_*From The Fantastic Writer of*_

```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```


*_And now_*


*_💃🏻UBA SONTA NAKE BA💃🏻



*✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*🖊
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ 🖊 *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*


*Abin Da Musulmi Zai ce idan aka yabe Shi:*

اَللَّهُمَّ لاَ تُؤَاخِذْنِي بِمَا يَقُولُونَ، وَاغْفِرْ لِي مَا لاَ يَعْلَمُونَ (وَاجْعَلْنِي خَيْرًا مِمَّا يَظُنُّونَ)

Allahumma la tu'akhizni bima yakuluna waghfir lee ma la ya'alamun, (waj alne khayran mimma yazunnun).

Ya Allah! Kar Ka rike ni da abin da suke fada, Ka gafarta mini abin dab a su sani ba, Ka sanya ni fiye da yadda suke zato.



*~INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?~*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*


_Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samun wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook_. 👇


https://www.facebook.com/101594048306878?referrer=whatsapp


_Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu._


*3*

Koda na tafi class naga kowa harkan gaban shi yake kasancewar sai zuwa nan da awa 1 za'a fara jarrabawar, dan haka kawai sai na wuce bayan gida na canza sabon uniform nawa, na sanin cewar daga yau na gama amfani dashi dama Inna tasa na karb'a ne kan cewa zan ƙara wata shekarar amma Allah ya taimake ni ya kawo wannan mutumin da yake cewa shi Yaya nane.


Kayan ba ƙaramin kyau suka yi ba, sun zauna sosai a jikina dama gani ba za'a kira ni mai jiki ba kuma ba za'a kira ni da sirirya ba,ga fata ta irin mai tsadan nan ce, wato chocolate colour wanda yayiwa round face na kyau,bani da dogon hanci can amma inada daidai gwargwado sannan manyan idanu na da d'an ƙaramin baki na su suke sa mutane suke min kallon wata kyakkyawa,wajan gashi ma dai babu laifi dan ina dashi ba laifi.


A bola na watsar da tsohon uniform d'in nawa dan inada yakinin in aka bawa wani ko goge-goge ba zaiyi dasu ba,na kama hanyan class d'in mu sai na zama abin kallo ga sauran d'aliban wasu na min dariya wasun kuma na cewa sun min kyau,ni dai ban kula kowa ba nayi wucewa ta class d'in mu.



Nan ma bata canza zani ba dan wasu har tsokana ta suke,kala bance musu ba sai harkan gaba na nake zuciya ta fari kal zan rubuta jarrabawa tare da 'yan uwana.




Bayan wani lokaci malamai suka shigo raba mana paper, nan kowa ya natsu bayan sun gama raba mana kowa ya fara rubutu sai naga ashe abun ba wuya ba kaman yanda na tsorata da shi bane a farko,cikin kankanin lokaci na kammala na fito abu na ina mai jin farinciki a rai na.


Da daddaya kowa ke fitowa bayan mun gama fitowa aka raba mana abinci mai d'an karan dad'i jallof na shinkafa harda naman kaza da bobo.


Kin cin nawa nayi na kama hanyan gida da abinci na,ina tafiya ina ta dube-dube ko zan kara ganin bawan Allah nan amma ko mai kamanin sa ban gani ba har na iso gida.



Duk 'yan matan gidan mu yau suna nan basu fita tallah dan azahar batayi ba sai dai kowacce suna bakin murhu da uwayen su suna aikin kayan sana'ar su sai yara mazan ne da suka fita sai da pure water.



D'akin mu na wuce direct sanin cewa Inna ta tana ciki ko lura da kallon tsana da Gwaggo Aisha ke auna min banyi ba nayi sallama na shiga d'akin mu.



Inna ta na zaune da sabuwar multi na hula a hannun ta tana tsakawa ,da sauri na ida shigowa ina cewa," laa Inna hula kika fara,yaushe kika koya ko dama can kin iya?" Na jero mata tambayoyin nan duk lokaci d'aya cikin zak'uwa.



Murmushi shimfid'e a fuskar ta tace," kinga yanda sabuwar uniform d'in ya miki kyau kuwa,kinga har shekara mai zuwa zakiyi amfani da kayanki hankali kwance".



Zama nayi ina ajiye takeaway da bobo na hannu na, nace mata," ai Inna bana bukatan uniform d'in hasalima daga yau amfanin shi ya kare domin dani aka zana jarrabawan".



"Dake aka zana sun tausaya ne suka bar miki ko kuwa?"ta tambaya fuskarta d'auke da farinciki mai cakude da mamaki.



"Ko kad'an basu ji tausayi na ba Inna,kora tama sukayi har na fito daga makaranta zan dawo gida...." Nan na bata labarin abinda ya faru tsakani na da wanda ya ce shi Yaya nane.



Maimakon inga tana farinciki sai naga ta tsuke fuska ta fara min fad'an da kada in sake yarda da wani kan titi wanda ban sani ba ko ya bani abu in karb'a,a irin haka suke maida yara doya su tafi dasu suyi tsafi dasu ko kuma a yanke kan su.


Tsoro sosai ya kama ni nayi ta zare ido ina ganin na tsallake rijiya da baya ashe,nan na bata hakuri tare da alkawarin bani ba wanda ban sani ba nan gaba.



Daga nan hira muka zauna yi da Inna ta bayan na bud'e mana takeaway nace muci tare,kallon abincin tsaya yi kana tace,"yanzu dama irin wannan abincin ake raba muku harda naman kaza?"



Dariya na kyakyale dashi sannan nace," Inna baki ga harda bobo na ba?"


"Ikon Allah tunda nake ban tab'a jin labarin governor mai son talakawan shi haka ba sai akan bawan Allah nan,Allah ya kiyaye mana shi" cewar Inna .


Da "Ameen na amsa sannan nace mata muci mana,amma taki ci d'an tab'awa kawai tayi ta bar min kaya na anan ne take gaya min ashe 'yar wata makociyar mu mai suna Ya'ana ita ta koya mata d'inkin hula,shikenan ta huta da zaman banza inta gama ance ana saya da kud'i da d'an yawa,murna nayi tayi muma mun samu sana'a da zamu rinka samun kud'i kaman sauran 'yan gidan mu.



Tun daga wannan rana na mayar da hankali na kan makaranta islamiya da nake in kuma safiya ce Inna ta kan tura ni gidan kakanni na saboda gudun rigimar 'yan gidan mu sai lokacin islamiya yayi sai in dawo in shirya inyi wucewa ta domin Gwaggo Aisha tafi kowa iya tuggu kuma Baban mu sosai yake jin maganan ta in fact itace 'yar gaban goshin shi ba dan komai ba sai dan tafi sauran matan shi kud'i kuma tana bashi kud'i shiyasa yake ji da ita sosai.



Maganan shiga secondary school mun ajiye ta a gefe kan cewa sai inna ta dinka hula 2 ko 3 sai ta had'a kud'in ayi min komai dashi.



Cikin ikon Allah satin hulan 4 Inna ta kammala shi baiyi kyau irin na kwararre ba amma da yake cikin tsafta ta dinka shi babu datti ko kad'an a jiki sai ya zama abin sha'awa.



Ya'ana wacce ta koya mata itama ta gama nata zata kai sayarwa Inna tace muje tare sai ta sayar a bani kud'in kasancewar ita zata wuce gidan kakanni ta daga can kuma zata kwana 2 kamin ta dawo.



Bayan ta shirya ta biyo min muka tafi can London ciki wai can sun fi sayan hula da daraja, dubu da dari biyar aka sayi na inna ta ita kuma Ya'ana dubu tara aka sayi nata da saboda ita nata tangaran ne.


A leda baki ya'ana ta kulle min kud'in ta saka ni a napep na zuwa anguwan mu ita kuma ta wuce,muna zuwa kusa da layin mu suka sauke ni suka wuce.


Har nazo kusa da layin mu na had'u da wani mutum yace min," ke ana sadaka a wacan kwanan" kamin in bashi amsa wasu yaran su 4 suka zo wucewa ya fad'a musu ba musu suka bi hanyan daya nuna nuna musu,ganin sun bi

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login