Showing 6001 words to 9000 words out of 85226 words

Chapter 3 - BA SONTA NAKE BA

Start ads

20 Aug 2025

173

Middle Ads

hanyan yasa nima na bisu a guje muna shan kwanan ashe mutumin yana bin mu sai muryan shi muka ji yana cewa," kai ku tsaya in akwai abu a hannun ku,ku kawo in ajiye muku kar ya fad'i wajan karb'an sadakan".



Gaba d'aya mu muka mika mishi duk kud'add'en hannun mu da alamu suma sauran yaran aiken su akayi,yana karb'a yace mana ga gidan can mu shiga shi yana jiran mu anan.



Ga gudu muka shiga gidan da sunan karb'an sadaka amma me sai aka ce mana ai ba anan akeyi ba,wata da zata girme mu a ciki tana jin haka ta fita da gudu muka mara mata baya amma muna fita muka nemi mutumin nan sama ko kasa muka rasa shi,kuka ko wannen mu ya fara dan sai yanzu muka gane cewa ashe b'arawo ne yayi mana dabara ya sace mana kud'add'en mu.



Gefen titi na samu nayi zama ta ina kuka na kasa komawa gida in naje me zan cewa Inna ta bayan kwanaki tayi min fad'a akan irin haka sai gashi na maimaita,bayan haka hulan nan yanda ta dage tayi ta d'inka shi ba dare ba rana dan ta samu saka ni a secondary school amma sai in koma ince mata wani ya min dabara ya kwace? gaskiya ba zan iya komawa ba.



Ina zaune ina kuka na d'aya daga cikin yaran da shima an sace mishi kud'in yazo ya zauna kusa dani muka cigaba abin mu,kaman daga sama naji ance," kanwata yauma kukan kike?"



Da sauri na d'aga kaina dan ganin waye sai naga wannan bawan Allah daya biya min kud'in jarrabawa ne hannun shi rike da bottle water inaga a shagon kusa damu ya saya ga mutane a wajan suna ta shiga da fita babu wanda ya kula mu sai shi da yazo yanzu.


Kin kula shi nayi na d'auke kaina ina goge hawayen ido na.


"Kai meya same ku kuka zauna anan kuke kuka?"ya tambayi yaron kusa dani.



Shi kuwa kama jira yake ya fad'a mishi duk abinda ya faru nan ya tambayi shi nawa ne kud'in?.

"Dari uku ne akace in sayo taliya da mai da maggi" ya bashi amsa.



Dari biyar ya ciro a aljihu usual sabo dal ya bawa yaron,cike da murna yaron ya karb'a yana godiya ya ruga da gudu ya tafi shagon kusa damu ya sayi kayan yanda ya fad'a ya dawo mishi da canjin shi,amma sai yaki karb'a yace ya tafi ya bar mishi.



Murna fal ranshi ya kama hanyan gida da gudu ya bar mu a wajan,ganin ban bi yaron ba yace min," ba tare kuke bane?" Jiki a mace na girgiza kaina saboda na zata yaron yana amsan kudin zai zama doya kaman yanda inna ta ta fad'a sai naga ba haka bane lafiya lau yayi sayayyar shi ya tafi gida.


"Ke kuma nawa ya sace miki?" Muryan shi ya katse min tunanin da nake.



"Kud'in hulan Inna ta ya karb'e gaba d'aya" na bashi amsa.



"Stop crying kanwata kinji,gashi karb'i ki kai mata".


Kallon kud'in na tsaya yi ina tunanin in karb'a ko a'a?



"Karb'a mana ki goge hawayen ki" saka hannu 2 nayi na karb'a cikin sanyin murya nace," nagode!"


Girgiza min kai yayi ya ce," kada ki damu tashi ki tafi gida".


Da azama na tastashi nayi gidan mu ba tare da nasan nawa ya bani ba.



A gida kuwa Inna duk ta damu tana tunanin me yasa na dad'e haka,tana ganina ta sauke ajiyan zuciya ta ce," zareefa me yasa kika dad'e haka?"


Banyi kasa a guiwa ba na kwashe duk abinda ya faru na gaya mata,karban kud'in tayi ta kirga taga dubu uku ciff,fincikoni tayi da karfin tsiya na fad'i akan simintin d'akin na bud'i baki zanyi ihu ta ce kada na kuskura inyi mata ihu anan dole na had'iye kukana ina zaro ido saboda ganin Inna ta ta fusata yau sosai.


" Wato ke ba kya jin magana ko zareefa duk abinda na gaya miki ta bayan kunnen ki suka wuce ko,baki san ki kama kan ki a matsayin ki na ya mace ba duk ko wani d'an iska ya baki kud'i karb'a kike yau kuma harda bin wani, Inna ilahi wa inna ilahi rajiun!!!

Toh tunda kunnen kashi gare ki yau zanyi maganin ki wallahi" ta karasa tare da murd'e min kunne.



Sosai ranan inna tayi min abinda tunda na san kaina bata tab'a yi min ba daga baya tayi min nasiha sosai mai ratsa jiki.



Tun daga wannan rana nayi hankali ya kasance babu ruwana da duk abinda zai had'a ni da wanda ban sani ba sosai na kama kaina.




Kullum Baba inya shigo gida Gwaggo Aisha itace zatayi ta dawainiya dashi dan ko Maman su Hafsa bata samu wannan matsayi a wajan shi ba,shi irin mazan nan ne da mace in zata rike shi tayi mai komai toh dad'i zaiji kwata-kwata bashi da zuciya d'aukan nauyin iyali da Allah ya d'aura mishi shiyasa gidan namu kullum sai kara hargitsewa yake.



Maman su Hafsa abin na damun ta sai dai babu yanda ta iya tayi-tayi amma ta kasa kamo Gwaggo Aisha dan tafi ta samu nesa ba kusa ba.



Ranan wani juma'a daya kasance girkin inna ta ne kuma a ranan munyi sa'a Baba ya kawo mana masara kusan kwano 10 ya ce a nik'a tunda babu garin tuwo.



Maimakon manyan gidan su kai sai suka ce ba zasu kai ba tunda ba girkin iyayen su bane,shikenan sukayi zaman su babu wanda ya ce musu wani abu.



Dole yasa wheelbarrow inna ta aro ta saka min a ciki ta ce in kai, ina turawa da kyar na kama hanya na fita a gida ga kuma inda zan kai nikan da d'an tazara da gidan mu.


Inna ta ana cewa tana da girki a gidan ne amma baba baya shigowa d'akin ta kaman yanda yake shiga sauran d'akin matan shi kuma baya cin abincin ta,na sha jin yana cewa nima Allah ne ya kaddara sai na taka duniya amma har yau yana jin takaicin wannan abin.



Na isa lafiya sannan nabi layi har aka zo kai na aka nik'a min mutumin shiya taimaka ya mayar min cikin wheelbarrown na kama hanyan dawowa gida.



Ina cikin turawa jikina duk gumi ban san taya wannan yaron ya shiga gaba na ba da keken sa da alamu ma dan koyo ne dan da kyar ma in ya kaini shekaru,duk yanda naso kaucewa amma abin bai yiwu ba saboda nik'an da nauyi kamin kace me dani dashi duk muka zube a wajan tare da kurkurjewa buhun nik'a na kuma sai cikin kwata da yake kusa damu.



Hannu 2 na d'aura a kai na rusa ihu ina gari na dan ko zafin kurjewan na daina ji saboda nasan in na koma gida babu garin nan wallahi Baban mu zai iya babbake ni da raina.



Sosai nake kuka kaman raina ya fita mutane sun taru suna mana sannu ko jin su bana yi har yaron ya d'auki keken shi ya tafi babu wanda ya hana shi kasancewar karami ne babu abinda zai iya yi.



"Oh not again yauma kuka take,meya same ta?"naji muryan shi kaman daga sama.



"Karo sukayi da me keke nik'an ta ya fad'a kwata" wani yaro ya bashi amsa yana nuna mishi buhun da aka ciro a kwata wanda ko akuyoyi ba zasu iya cin garin da yake ciki balle mutum.



Baice komai ba ya koma ya motan shi ya wuce,ajiyar zuciya nayi da Allah yasa bai ce zai ban wani abu ba yau,mutane suna bani bakin in tashi in tafi gida amma kirmitsitsi naki motsawa balle su saka ran zan tashi.



Bayan kaman mint 5 na kara jin muryan shi yana cewa," ga wannan tashi in ajiye ki a gidan ku".



Kallon inda yake nayi naga buhun shinkafa da wasu kwalaye harda jerrican mai ana saka mishi a boot din mota,kaman wanda aka jona da remote na tashi jiki na na b'ari na fara tura wheelbarrow na da gudu nayi hanyan gida na bar shi tsaye anan.


Ana gama saka masa kayan ya tambaya ko akwai wanda ya san gidan mu anan?


Wani yaro yayi caraf yace ya san gidan mu gashi can babu nisa sosai daga nan.



Motan shi ya shiga tare da cewa yaron yazo ya raka shi,ba musu yaron ya shiga suka bi baya na.
[8/31, 6:05 PM] Ummee Yusuf: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹

_A story about love and sacrifice._



_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_


_*From The Fantastic Writer of*_

```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```


*_And now_*


*_BA SONTA NAKE BA_*

*_4_*

*✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*🖊
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ 🖊 *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*


*Addu'ar Tsayuwa a Kan Dutsen Safa da Na Marwa*

Jabir, Allah ya yarda da shi ya ce, yayin da yake siffanta hajjin Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi; yayin da ya kusanto dutsen Safa sai ya karanta:

إِنَّ الصَّفَا وَالْمَرْوَةَ مِنْ شَعَائِرِ اللهِ.
أَبْدَأُ بِمَا بَدَأَ اللهُ بِهِ.

Bers Safa: Innas safa wal marwata min sha'a'irillah
Abda'u bima bada'al lahu bihi.

Hakika Dutdsen Safa da na Marwa suna daga cikin alamomin da Allah Ya sanya (na addininsa)".

Ina farawa da abin da Allah ya fara da shi.

Sannan ya fara da Dutsen Safa, ya hau shi har sai da ya hango dakin Allah, sai ya fuskanci alkibla, ya kadaita Allah, (ya yi hailala), ya girmama shi (ya yi kabbara) ya ce;

اللهُ أَكْبرُ! اللهُ أَكْبرُ! اللهُ أَكْبرُ!

Allahu akbar. Allahu akbar. Allahu akbar.
Allah ne mafi girma, Allah ne mafi girma, Allah ne mafi girma.

لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللهُ، اَللهُ أَكْبَرْ، لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ، لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللهُ وَحْدَهُ أَنْجَزَ وَعْدَهُ، وَنَصَرَ عَبْدُهُ، وَهَزَمَ اْلأَحْزَابُ وَحْدَهُ.
Bers la Ka'aba: La ilha illallahu, allahu akbar, La ilaha illal lahu wahdahu la sharika lahu, lahul mulku wa lahul hamdu, wa huwa ala kulli shay'in kadirun. La ilaha illal lahu wahdahu. Anjaza wa'adahu, wa nasara abdahu, wa hazamal ahzaba wahdahu.

Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai, babu abokin tarayya a gare Shi. Mulki ya tabbata a gare shi, kuma yabo ya tabbata a gare Shi; kuma Shi Mai iko ne a kan komai. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai. Allah ya gaskata alkawarinsa, Ya taimaki bawansa, Ya ruguza rundunonin kafirai Shi kadai.

Ya karanta wannan zikiri sau uku, yana yin addu'a bayan kowace marra. Da ya hau Dutsen Marwa ma ya yi kamar yadda ya yi a kan Dutsen Safa.

*~INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?~*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*


_Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samun wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook_. 👇


https://www.facebook.com/101594048306878?referrer=whatsapp


_Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu._


*_4_*


Ina isowa kofar gidan mu shima sun iso abinka da mota,ina ganin motan nayi jifa da wheelbarrow a nan bakin k'ofar gidan mu na shiga ciki da gudu ban tsaya a ko ina ba sai d'akin mu a d'akin ma a bayan k'ofa na b'uya ina lek'e.

Inna da tun shigowa ta take kallo na fuska d'aure ta ce," wa kika tsokono a wajan da kika shigo min a guce haka?"

Ban iya bata amsa ba sai zare ido da nake zuciya ta na cigaba da bugawa, Inna zata kara min magana muka ji muryan yaron daya rako mutumin nan ya ce,"wai ana neman zareefa".


Wani kallo Inna tabi ni dashi sannan ta dubi yaron ta ce," yana ina?" Yana nan k'ofan gidan nan" yana gama bata amsa ya juya ya tafi abinsa.


"Waye shi kuma me kika masa ya biyo ki har gida?"



"Sh...shine wan...wanda ya biya min kud'in jarrabawa" na bata amsa.


"Shine ya biyo ki har gida,ko dai da wani abu daban?" Shiru nayi na kasa bata amsa sai zare ido da nake saboda ban manta abinda tayi min akan shi ba.



Hijabinta da yake gefenta ta saka ta fita dan taji me yake tafe dashi,a tsakar gida ta tarar da 'yan gidan mu kwan su da kwarkwatan su suna tsatsaye suna k'us-k'us.



Suna ganin ta suka fara yi da karfi wasun su na cewa k'ila sata nayi mishi,wasu kuwa cewa suke asirin mu ne ya tonu k'ila yana cikin mazan da nake bi,tunda dama cewa suke karatun karuwanci nake.



Inna ta bata kula kowa ba ta fito 'yar rub'abb'en zauren gidan mu da niyyan yi mishi iyaka dani domin ta gane fad'an da tayi min kwanaki shi ya firgita ni haka.



Katuwar mota da ta gani ana sauke kayan abinci a ciki kaman za'a bud'e 'yar karamar shago yasa ta tsaya cak tana kallon d'an matashin saurayin da ba zai haura shekaru 21 zuwa 22 ba yana danna wata laftatiyiyar waya a hannun shi.



Inna sai yayi mata kwarjini ta kasa karasa fitan balle tayi mishi magana,shine dai daya gaji da danne-danne shi ya d'ago da kai karaf suka had'a ido da Inna ta,asalin kamanin ta na d'auko shiyasa yana ganinta ya gane ta.


Wayar nashi ya mayar aljihun rigan shaddar shi lafiyayya blue ya karaso gaban ta cikin sauri ya duka har k'asa ya fara gaishe ta,fuska a had'e ta amsa kana ta ce," lafiya kake neman zareefa,ko kuma akwai wani abinda kake nema daga gare ta,dan ta bani labarin duk abinda ta faru tsakanin ku kuma shine yau ka biyo ta har gida"?



Girgiza mata kai ya fara wasu waye na taruwa a idon shi ya ce," ba haka bane Aunty kada ki min mummunan fahimta saboda ni ba nufi na kenan ba,domin duk had'uwa da muke da ita Allah ne yake had'a mu,lokacin da na gan ta a hanyan makaranta na fito zan tafi wajan aiki ne na gan ta tana kuka sai na biyu kuma na tsaya siyan ruwa a gefen hanya ne na ganta ita da wani yaro suna zaune a gefen titi suna kuka,and still yau shima gefen kwata na ganta zaune tana kukan garin ta ya fad'a kwata mutane duk sun zagaye ta ana taje gida ta fad'a amma taki tashi saboda wai Baban ta ba zai bar ta duk taji ciwo amma ko jin zafin bata yi.


Ni suna na Abdulbasit kuma ni maraya ne da tunda na taso ban san kowa nawa ba,banida kowa akan titi nake rayuwata cikin yunwa,kunci da kuma kad'aici sai daga baya na samu wani bawan Allah ya tallafawa rayuwata har kika ganni haka sannan shiyasa na tsani inga karamin yaro yana kuka domin yana tuna min da lokacin kuruciya ta kuma duk yanda zanyi sai na san yanda zanyi in share mishi hawaye sannan hankali na zai kwanta.



Ba ita kad'ai nakewa haka suna dayawa Aunty bana son kowa ya sha wahalan da nasha a baya amma in har hakan ya b'ata miki dan Allah ina neman alfarman ki yafe min".



Inna da jikinta duk ya gama yin sanyi sai ta kasa furta komai saima jin ba dad'i da tayi kan yi mishi mummunan zato.



"Ga wannan kayan abincin a saka su ciki Aunty sannan a bawa Baba hakuri kada ya dake ta tsautsayi ne " taji ya yanke mata tunani.



Tulin kayan abincin ta kalla ido a waje ta girgiza mishi kai,"ta ce a'a ka tafi da kayan ka mun gode Baban ta kuwa zanyi mishi bayani zai fahimta kuma...."


Katse ta yayi cikin sauri ya ce,"haba Aunty ba'a maida hannun kyauta baya,sannan ni ina farincikin na samu ahali da zan iya nunawa a ko ina amma kika ce haka? Sannan hakan na nunawa baki karb'e ni a matsayin d'an uwa ba,ina neman alfarman ki rike ni a wannan a matsayin inji ya ake ji in mutum yana da ahali".


Wannan furucin da yayi saida yasa Inna hawaye,gyad'a mishi kai ta iya yi domin ta tabbata tana bud'e bakin ta kuka ne zai kufce mata saboda tsananin tausayi daya bata, shima cike da farinciki ya mike yana share hawayen idon shi ya ce,"nagode Aunty Allah ya saka da alkhairi zan tafi sai bayan kwana 2 zan rink'a zuwa mu gaisa".



Bai jira cewar Inna ba ya fad'a motan shi sai da yayi ribas sannan ya kira wani yaro ya bashi kud'i masu yawa ya ce ya kaiwa Inna ta,yaja motan shi ya fita a layin namu.



Inna tana tsaye ta rasa ta ina zata fara tab'a kayan sai ga yaron da aka bawa kud'in yazo gaban ta ya mik'a mata kud'in ya ce," wai gashi inji wancan mai motan ya ce in baki"


Wani yawu ta had'iye da kyar hannun ta na rawa ta karb'i kud'in a ranta tana ayyana anya wannan bawan Allah abinda ya fad'a gaskiya ne kuwa? Nan wani sashi na zuciyar ta ya ce mata tunda take bata tab'a cutar da wani ko tabi wani da mugun kulli ba insha Allah in ma da wata manufar yazo Allah ba zai bashi sa'a ba.



Da wannan kwarin guiwan ta samu ta kira wasu matasa da suke zaune gefe tace su taimaka mata su shigar mata da kayan abincin ciki,ba musu suka fara jidan kayan domin suna ganin girman ta sosai.



Su Gwaggo Aisha baki da hanci suka bud'e suna kallon kayan da ake wucewa dashi d'akin mu,bakin ya mutu murus sun rasa abin fad'a,nima ina nan a bayan k'ofa duk na had'a zufa naga a nata shigowa da kayan suna jerawa a gefe har suka gama suka fita ban fito daga mab'uya na ba

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login