Showing 27001 words to 30000 words out of 48145 words
Alhaji." Hannu ya mik'awa su Hakkim sukayi musabaha ga juna yace." Hala kune bakinmu na jiya da daddare ko."?
Yusuf yace." Mune wallahi."
D'alha yace." To bari in shiga gida in sanar da mahaifiyata dama yanzu muke shirin futa."
General yace." Babu laifi samari." D'alha ya shiga gida cikin sauri.
Gogon ku na tsaye jikin mota ya harde hannuwansa a k'irji jira kawai su shiga gidan ya kara yin ido hudu da marakaunyar yarinyar nan yaga tayi ladaf ko kuwa.
Minti biyar D'alha yayi ya dawo da sauri yace." Bisimillah Alhaji ku shigo daga ciki."
Bayan sa suka bi. Yaran unguwar dake tsaye na kallonsu suka biyo su yuuuuuuu! D'alha ya buga musu tsawa, suka koma gefe,wasu na cewa Ladidi ce taje ta jawo futuna.
Mai koko na zaune gefan tabarma ta lullub'e jikinta da mayafi. Sukayi sallama suka shiga gurin zama ta nuna musu tana musu Barka da zuwa cike da mamakinsu
Suka zauna babu kyankyamin komai domin gidan tsaf yake tun safe tayi shara da wanke wanke ko ina tas iskar Safiya na kadawa
Gaisawa suke cike da mutumchi, General yace." Ina fata nan ne gidan su wata yarinya Ladidi."
Mai koko tace." K'warai kuwa nan Alhaji ina fatan ba wani abun tayi muku ba."
Cike fa tausayi yake kallonta yace." Mine dai mukayi mata laif............ Kafin ya gama maganar shi Ladidi ta bayyana a gurin, ta tsaya tsakinyar ta barmar idonta kan Hakkim! suka kurawa juna ido. Ihu!!! Ta kurma tana nuna shi da hannunta tace." Iya!!! Gashinan shine ya dinga dukana kamar zai kashe ni wallahi Iya shine, Allah ya kawo shi gidanmu mu dauki fansa domin bazan barshi ba."
*COMMENT VOTE AND SHARE*
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
*🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚*
*🧟♀🧟♀🧟♀K'WADAGA🧟♀🧟♀🧟♀*
~*NA*~
_BINTA UMAR ABBALE_
*BINTUBATULA👄*
*MARUBUCIYAR*
```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```TSANTSAR BUTULCI```
*LOADING:*
*{LADIDI K'WADAGA🌚}*
_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_
_______________________
```We are here to educate motivate and entertain our reades```
_______________________
*JAN KUNNE⚠*
_*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_
*DEDIGATED*
*TO*
*RAHAMA ALIYU*
~*ABUJA*~
_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_
*🅿23*
Cike da mamaki General yake kallon Ladidi. dake tsaye Kansu D'alha mata tsawa ta matsa daka kan mutane amma kamar kara ingizata ake tanayi kamar zata kaiwa Hakkim duka.
General ya kalli Yusuf da alamun tambaya.
Yusuf yace." Itace yarinyar Dady."
Sosai General yayi mamakin kankantar ta ya kalli Hakkim cike da takaici yace." Meye abun duka jikin wannan k'aramar yarinyar."?
Sunkuyar da kansa kasa yayi. Yana jin tsoron kar dady ya tsinkashi a gaban mutane.
Ladidi ta ruga kicin da gudu! Duk suka bita da kallo. D'alha kamar yasan abunda zatayi ya mike da sauri zai bita.sai gata ta futo hannunta rike da doguwar muciyar da Iya take dama koko tayi kan Hakkim da gudu.
Hakkim yasan gurinsa ta nufo sai ya shirya tsaff ta d'aga muciyar da k'arfi zata maka masa.ya rike ta da sauri yw fuzgota sai gata ta fad'o jikinsa,cike da mugunta ya wurgar da ita gurin kanta ya bugu da bango ihu!! Ta kurma tana fadin." Wayyo kaina."!! D'alha yazo ya daga ta cike da jin haushi ya kwarfa mata mari yana fad'in." Ashe rashin lafiyar naki na k'arya ne."
General yace." Yi mata a hankali samari." D'alha yace."Alhaji baka San halin yarinyar nan ba ne."
General yace." Koma meye dai ni ta burge ni tunda take k'okarin k'watar 'yan cinta ga Wanda ya cuce ta, saboda rashin imani kamar Hakkim da shekarunsa da komai ya zage k'arfin shi kan yarinya k'arama kamar wannan."
Mai koko tace." Alhaji bamu game me kake nufi ba."?
General yace." Wannan da yake zaune shine ya sumar muku da ita jiya nine kuma mahaifinsa Nazo domin in nemi afuwar Ku."
Iya ta mike tsaye da sauri ta gyara d'aurin zaninta tace." Ko dana ji ahwo!!! Shiyasa naga yana sinne kai tamkar b'arawo a hannun mata,wato dama kaine kake k'okarin kurman tamin da jikita. ? Babu shakka Ladidi ta kurmance sai munyi sha'ra'a dakai."
Wani mugun haushin Matar yaji a zuciyarsa yace." Da zata kurman ce ma ai da kowa ya huta da alak'ak'ai."
Ladidi ta taso da sauri tana rike Iya tana kuka take fad'in." Iya kar ki barshi nima bazan barshi ba."
General yace." Innalillahi wa'inna ilahi rajinu. Ashe abun yayi tsanani haka,shiyasa zuciya ta kasa amunta nace dole sai Nazo naga halin da take ciki. Tabbas dole ki dauki hukunci Iya amma ki zauna muyi mgn dake ta fahimta. "
Mai koko ta koma ta zauna tana maida nuffashi Ladidi ta jawo jikinta ta rungume ta tana rarrashin ta.
Haushi duk ya tuk'e D'alha ya kalli General a nutse yace." Alhaji ka kwantar da hankalin ka don Allah ni nasan duk abunda ya faru da dalili haka kurum shi bazai kamata ya doke ta ba."
General yace." Haka kake gani samari inace gashinan a gabanka ya wurgar da ita da mugunta ta buga kanta a hango ko baka gani bane."?
D'alha yace." Nagaji Alhaji ai kana ganin abunda tayi masa ko."?
Shiru General yayi yana girgiza kansa.
D'alha ya bugawa ladidi tsawa tare da fad'in" yimana shiru shashasha kawai kin bude baki kina kukan banza da wofi."
Iya tace." K'yaleta tayi kukan ta to kaji."!!!!.
General yace."ina me bawa zuciyoyin Ku hakuri sosai domin narasa dame zan fara a halin yanzu amma kafin wani hukunci ya biyo baya ina rokon Ku da muje mu kai yarinyar nan asibiti a duba ta, domin hankalina ya tashi da jin maganar da kikayi."
D'alha yace." Dama yanzu zamu tafi asibitin cikin gari."
Mik'ewa General yayi yace." Maza Ku futo muje Allah ya kiyaye gaba."
Mai koko ta zura mata hijabinta tana goge mata fuska suka futa
To gurin shiga motar ma Ladidi ki tayi ta dinga turjewa wai bata yarda ba gurin yankan kai za'a kaisu a siyar musu da kai.
Da k'yar Dady ya rarrashe ta ta shiga motar. Hakkim kamar ya Dora hannu aka Dan takaicin ta.
*Comment vote and share*
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
*🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚*
*🧟♀🧟♀🧟♀K'WADAGA🧟♀🧟♀🧟♀*
~*NA*~
_BINTA UMAR ABBALE_
*BINTUBATULA👄*
*MARUBUCIYAR*
```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```TSANTSAR BUTULCI```
*LOADING:*
*{LADIDI K'WADAGA🌚}*
_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_
_______________________
```We are here to educate motivate and entertain our reades```
_______________________
*JAN KUNNE⚠*
_*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_
*DEDIGATED*
*TO*
*RAHAMA ALIYU*
~*ABUJA*~
_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_
*🅿24*
Cikin gari suka futa General yace." Zamu samu pravite hospital anan kurkusa sai mu tsaya kawai ba sai mun je babban asibiti na Murtala ba."
D'alha yace." Za'a samu Alhaji." Yace." Sai mu tsaya anan kawai a duba ta."
Cikin birget suka samu hospital.Hakkim ya kashe mota duk suka futo suka shiga ciki.
Idan da kud'in ka babu wahala da kaskantar da kai da zakayi,D'alha yayi mamakin yanda ma'aikatan asubitin suke karrama Alhaji sai rawar jiki suke.nan ka yanki kati likita na ofis General yace." Da Ladidi tazo su shiga tare. Mak'ale kafad'a tayi tana b'uya bayan Mai koko, murmushi yayi yace." Zo muje ciki dactor ya duba ki kinji ko." Ladidi ta zumb'uro baki gaba. Yace." Dawa-dawa kike so mu shiga tare." ? Shiru tayi masa. Haushi yasa D'alha ya buga mata tsawa tare da fad'in." Idan baki sake ta wallahi sai Nazo nan na gaura miki mari."
Mai koko tace." Kaga D'alha rabu da ita don Allah.Ina dalili nifa wannan asibitin be kwanta min a rai ba,asibiti ko ina sanyi hatta k'afar ka in ka aje ta a kasa sanyi ga wasu abubuwa a bango naji fa ana cewa wasu asubitin duk barna suke aikata wa. Gwara muje na Murtala kawai."
Takaici ya hana D'alha cewa komai. General yace." Iya wannan hospital din ana biyan kudi sab'anin sa dana gwamnati kenan kinga ai baza mu bi wannan dogon layin ba, kiyi hakuri mu shiga tare dake babu abunda za'ayi mata."
Mai koko ta kalli Ladidi tana yi mata magana k'asa-k'asa sannan ta sake ta suka mike General yayu gaba suka bishi a baya. D'alha ya nemi guri ya zauna yana sauke ajiyar zuciya.
Hakkim kuwa takaici ya hanashi cewa komai yarasa me yasa Dady ya damu da al'amarin yarinyar nan wallahi. Shiko Yusuf Dariya yakewa Ladidi ganin yanda take ta kalle-kalle kauyacinta kawai take.
Dactor suka gaisa da General cikin mutum ci yana tsokanar Ladidi bata San ma yanayi ba domin tana can tana kallon tv mak'ale a bango na wani India film na fad'a, amma ba fassarar hausa bace. Dariya ta kyalkyale dashi tace." Iya kalli wannan film din ki gani don Allah, na fada miki afton nan Dan bala'in ne hinefa singam da nake fada miki,hahahahahaha."
General da Dactor suka saki baki suna kallon mara lafiya tayi tsalle gaban tv tana kallo tamkar zata rikito da ita daga sama.
Wannan karon kunya ce ta kama Iya ganin abunda Ladidi take babu kamun kai,kokari kawai take tayi tsalle ta tab'o tv in da jarumi Ajay devgan yake ragargaza 'yan gidan boss da bundigar sa,Ihu!! Kawai ta kurmawa tana buga tsalle.
Sosai dariya take cin General yana k'okarin dannewa sai da ta subuce. Ganin yana dariya yasa Dactor ya fara yi shima Suna kallon juna.
Iya tana k'okarin kamo ta tana fuzgewa duk kunya ta ishe ta gashi tun farko dama bata iya sarrafa Ladidi. Dactor ne da ya gaji da abunda take ga jama'a a na jiran shi a waje yasa ya buga mata tsawa! Tare da fad'in." Ki nutsu yanzu ko in sa a zo a zuk'i jinin ki kuma inyi miki allura goma.''
Firgigit ta dawo nutsuwar ta jin zan can Allura sai taji kallon ya fuce mata daga rai mugun tsoran dactor ya shiga zuciyar ta simi-simi ta dawo kusa da Iya tana zare ido.!
Iya tace." Ke kam anyi mara wayo wallahi ke da baki da lafiya kike tsalle-tsalle."
Da sauri tace." Nifa lafiya na lau ni dai kice kar ayi min allura bana so."
General yace." Ai dama ba allura za'ayi miki ba, dawo nan kusa dani dactor ya duba ki kaman matsalar kunnen ki,sai ya baki magani bazan bari yayi miki allura ba."
A d'arare taje ta zauna inda yake nuna mata sai harara Dactor take yi, bai lura ba yana can yana aikin sa. Ya d'ago kansa a nutse yace Alhaji meye Matsalar ta ne." Iya da ba'a tambaya ta fara zayya no masa abunda ya faru."
A hankali ya ambaci sunan Ladidi Wanda ya gani jikin kati wato Amina sai yaga bata dago kai ta kalle shi ba, da Ladidi ya kira ta da k'arfi sai ta dago kanta tana kallonsa. Mik'ewa yayi hannunsa rike da wani Abu,ganin yana zuwa inda suke ne yasa ta tsora ta ga wani Abu a hannunsa. Kafin General ya ankara ta buga tsalle, wajan kofar futa suka tsince ta tana kici-kicin budewa ta futa.
General ya mike da sauri yana kiranta ko sauraron sa ba tayi ba Allah ya bata sa'a ta bude tayi waje da gudu.!
Su Hakkim na zaune reception suka ga futowar ta kamar walkiya tayi kofar futa. D'alha gyangyad'i yake bai ganta ba, kasan cewar jiya baccinsa ragagge ne.
General suka gani ya futo hankali a tashe yake fadin "Tana ina ne." Kofa ya kalla yaga gilmawar ta ta futa, ya bugawa Hakkim tsawa tare da fad'in" Maza tashi kaje ka dauko ta.wato kana kallo ta futa baka yi wani Abu akai ba ko."?
Hakkim ya mike da sauri ya futa yana kunshe dariya yaji dad'i da Ladidi ta nunawa Dady wacece ita.
General ya jin gina da hango yana sauke ajiyar zuciya gefe guda kuma yana mamakin halin yarinyar kamar aljana, yanzu ya fara sarewa da lamarinta.
Hakkim na futa ya hango ta bakin get tana rigima da masu gadi, dole sai sun barta ta futa su kuma sun hanata saboda ganin yanda ta futo daga ciki tana fella guda sai kace me tab'in hankali. Kuma sunga lokacin da suka zo cikin mota sosai asibiti yake da tsaro. A hankali ya Isa inda suke dama tun kafin ya k'arasa yayi shiri ya tattate hannun rigarsa, yana isa ya sunkuce ta, sosai ya rike tamau! Ya had'e k'afafun ta da hannaye ta ya sab'a a kafad'arsa. Ladidi ta dinga ihu! Tana zandare masa a baya Hakkim ya rik'e hannuwan balle ta doke shi, sai ta kafa kanta a wuyansa ta gartsa masa cizo. Ko a jikinsa, bai sauke ta ba sai ya kaita har ofis din dactoe.
Iya tace."Sannu na yaba da k'okarin ka samari da baka d'auko ta ba wallahi futa waje zatayi k'arshe mu rasa inda take, Maza danne ta likita ya duba ta." Hakkim ya b'ata fuska bai mata komai ba ya fara k'okarin futa sai suka ci karo da General da D'alha suna k'okarin shigowa, Dady yace." Koma muje ka riketa a duba kunnen nata. Babu yadda ya iya ya koma ya zauna kan wata kujera Ya jawo Ladidi tana turjewa ya rike tamau! A jikinsa Dactor yazo da Abu a hannunsa ya kunna hasken sa, ya kafa kunnen Ladidi yana dubawa.
Ihu!!!!! Take kurmawa tun k'arfin ta,tana haure-haure da hannuwata da k'afafun ta tare da ya kushin Hakkim ko ta Ina.ganin hakane yasa D'alha zuwa gurin ya rike hannunwan nata tamau! Dactor ya cigaba da aikinsa.
*COMMENT VOTE AND SHARE*
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
*🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚*
*🧟♀🧟♀🧟♀K'WADAGA🧟♀🧟♀🧟♀*
~*NA*~
_BINTA UMAR ABBALE_
*BINTUBATULA👄*
*MARUBUCIYAR*
```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```TSANTSAR BUTULCI```
*LOADING:*
*{LADIDI K'WADAGA🌚}*
_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_
_______________________
```We are here to educate motivate and entertain our reades```
_______________________
*JAN KUNNE⚠*
_*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_
*DEDIGATED*
*TO*
*RAHIMA ALIYU*
~*ABUJA*~
_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_
*🅿25*
Hakkim zuciyar sa zafi take masa yana jin kamar ya saki Ladidi ta fad'i kasa saboda yanda take ta faman duk k'irjinsa duk ta ya kushe masa fatar hannunsa ga majinarta da miyau duk sun b'ata masa jikinsa, lokaci guda yaji zuciyarsa na tashi kyamkyamin Ladidi yake sosai.ya dinga kauda fuskarsa har dactor ya gama dube-duben sa ya matsa daga gurin.
Da sauri ya sake ta ta fad'i kasan gurin ya mik'e da sauri yana duba jikinsa. Saboda fargabar da suke ciki babu Wanda ya damu da fad'uwarta a gurin itama bata damuba ta mik'e zumbur tana sharb'e hawayen fuskar ta.
General ya k'araso kusa da ita cikin taushin harshe yace." Yi hakuri kinji Aminatu kinga ni ai na fada miki ba allura za ai miki ba kin tashi hankalin ki da namu kiyi shiru ki fada min me kike so in siya miki."
Ya k'arashe maganar sa lokacin da suke zama kujerar dake fuskantar ta dactor.
Tsabar takaici da b'acin rai yasa Hakkim kasa cewa komai ya bude kofa ya futa a fusace.!!
Dactor ya gama rubuce-rubucen sa ya d'ago yana kallon General yace." Alhaji gaskiya ta samu matsala daga kunnen ta na hagu, Wanda ya dumd'e ba taji sosai ta bangaran sa,amma insha Allahu in an bi doka zai dawo dai-dai yanzu zan dorata kan magani kuma kullum za'a dunga kawo ta ana mata wankin kunnen tsahon sati uku, insha Allahu idan akayi haka za'a samu maslaha."
General ya d'aga kansa cike da takaici yake Neman Hakkim a gurin sai ga babu shi girgiza kai yayi ya maida kallonsa gurin Dactor yace." Babu damuwa dactor INA so ka tsaya min kan yarinyar nan domin bana so ta rasa wani Abu me muhimmamci a rayuwar ta mussaman ma kunne domin jikin dan Adam yana da muhimamci duk abunda ake buk'ata zan biya insha Allahu a kula min da ita."
Dactor yace." Insha Allahu za muyi iya iyawar mu Matsalar daga yarinyar ne Allah yasa ta bamu hadin kai."
General yace." Insha Allahu babu Matsala." Dactor ya mik'e tsaye yace." Muje pharmacy zan had'a mata magani gobe misalin takwas na safe sai a kawo ta domi fara yi mata wankin kunne."
Duk suka mik'e suka futa a reception suka zauna Dactor shi da wata nurse suka nufi dakin magana.
General ya dinga laluben inda Hakkim yake bai ganshi ba Yusuf ya kalla da fuska a daure yace." Ina Hakkim yake.?
Kai a sunkuye Yusuf yace." Ya tafi sanjo kaya."
Cike da mamaki General yace." Kamar yaya ya tafi sanjo kaya wato yana nufin mu tsaya jiran shi ya tafi da mota sai sanda ya ga damar dawowa ko me.?
K'asa da kai Yusuf yayi cike da girmamawa.
General yace." Ya kyauta ai."
Suna zaune Dactor ya dawo hannunsa rike da Leda me tambari da sunan hospital din nasu cike da mugunguna nasha dana digawa a kunne dactor ya mik'awa General yana fad'a masa yanda za'ayi amfani dasu.
Nan General ya karb'i numbar account ni dactor din domin ya turo musu da hakkin su sukayi sallama suka futa.
Hakkim ne ya shigo asibitin cikin mota General ya sauke ajiyar zuciya a fili yace." Kayiwa kanka k'iyamun laili wallahi da ka bari mun bi motar haya sai na b'ata maka rai."
Shiru yayi yana