Showing 39001 words to 42000 words out of 48145 words

Chapter 14 - LADIDI KWADAGA

Start ads

24 Aug 2025

72

Middle Ads

yau ba sunan ki Ladidi ba, sunan ki Aminatu."

Baito tace"Suna me daraja sunan mahaifiyar Annabi MUHAMMADU (Slw)." Ita dai Ladidi shiru tayi kawai tana satar kallon hoton Hakkim dake mak'ale a bango.. Take wani irin fargaba da tsoro suka shige ta, Sai hawaye sharrrr! Suka fara biyo kumatun ta.

Salima tace"Kuka kike yi Aminatu." ? Mik'ewa tayi zumbur!! Ta kama hanya zata futa." Baito ta matsa gefe ganin tana k'okarin buge ta.


Salima ta mike da sauri tana k'okarin rike hannunta LADIDI ta fuzge hannunta tana kokarin futa.. Cikin sauri Salima ta kara rike hannunta, wata irin bangaza tayi mata sai ga Salima a k'asa, Ladidi ta bude kofa ta fuce da gudu.

"Momy"!!! Salima ta kwalawa Hjy Asiya kira, da sauri Hjy Asiya ta sauko jin irin kiran da Salima ta kurma mata fad'i take " Lafiya kike kurma min uban kira haka."?

Baki na rawa tace" Amin.... Kafin ta karasa Hjy Asiya ta katse ta da fad'in",Tana ina."!? Da hannunta ta nuna kofa tana fad'in"Ta futa da gudu." Cikin sauri Hjy ta bude kofar parlor ta futa tana salati.

Can ta hango Ladidi bakin gate suna rigima da masu gadi, sai kuka take tana burgima a kasa wai dole sai sun bud'e mata k'ofa.

Tun daga nesa Hjy Asiya take fad'in"Kar Ku Bari ta futa duk Wanda ya bar ta ta futa a bakin aikin shi."

Jin abunda Hjy take cewa ne yasa Ladidi zabura! Ta buga wani uban tsalle! Sai gata ta d'are gatangar dake kewaye da gidan, duk da cewa akwai k'ananun k'usoshi saboda tsaro (Security) Hjy Baito masu gadi sakin baki suka yi suna kallon hatsabiban cin yarinyar.

Cikin rarrashi Hjy tace"Aminatu ki rufa min asiri ki sauko don girman Allah kar ki kashe min aure na."
Ko kallonta Ladidi ba tayi ba, k'okarin dirga k'asa take k'afafunta har sun fara fidda jini.

Hjy ta kalli Salima dake tsaye tsoro ya cika mata ciki tace"Maza je ki kira Dadynku nasan dai yau sai ta Allah, bazai tab'a karb'ar uzirina ba."

Salima ta wuce cikin gidan da sauri. Rarrashin ta suke sosai kan ta sauko kar ta jiwa kanta ciwo Ladidi ko sauraran su bata yi, kokari kawai take ta sauka k'asa.

Hawaye Hjy Asiya ta fara sharewa tana fad'in"Ashe tsautsayi ne yasa muka d'auko ki muka kawo ki anan Amina ki rufa mana asiri idan kika fad'o daga wannan ginin ai idan baki mutu ba, to babu shakka sai kin kakkarye."

Ganin tana k'okarin zura k'afar ta k'asa yasa d'aya daga cikin masu gadin gidan ya futa da gudu, domin ya tare ta ko da zata fad'o.

Raba k'afafunta tayi d'aya cikin gidan d'aya a wajan gidan, ta kalli Hjy Asiya tare da turb'u ne fuskarta tace'Wato kun kawo ni nan gidan domin Ku yanka min kai ko? Hahahahaha na gane ku ai."

Hjy Asiya ta fara rantse-rantse muryar ta na rawa! General na hango ya tawo a sukwane! Tun daga nesa yake hango abunda yake faruwa, wani irin zufa ne ya tsinke a jikinshi kamar ba daga wanka ya futo ba. Ya k'arasa gurin da sauri yake fad'in"Aminatu me akai miki? Sauko kinji ki fad'a min me kike so in siya miki kar ki fad'a kasa Aminatu."! Dariya tayi tana kallonsa tace"Baba duk na gane Ku wato kun kawo ni kuyi cinikin kaina ko hahaha to kafin Ku siyar dani ni zan siyar da kaina, domin fecewa zanyi sai inga Wanda zaku siyar."

General ya sharce gumin dake tsatstsafo mishi a goshi duk ya rasa me zaiyi, Salima ya kalla da sauri yace." Kira min Hakkim a waya kice masa duk inda yake yazo yanzu-yanzu."

Da sauri ta koma Cikin gidan domin ta dauko wayar ta.
Har yanzu Ladidi na tsaye kan Katanga tana kallonsu suna kallonta

Da wayar a hannunta ta futo tana laluben numbar Bigbrth kamar yanda suke kiran shi, "Dady wayar tak'i shiga." Tafad'a bakinta na rawa.General ya karb'i wayar da sauri yana k'ara gwada kiran.


Cikin sa'a ta shiga,Hakkim ya dauka had'e da Sallama, Dady yace"Kana ina ne."?
"Dady muna tare da Salmanu muna k'arasa shirye-shirye mybe ma, ba a gida Zan kwana ba."

General yace."Kwana a gida ya kama ko domin mun shigo garin yanzu haka ma muna gida, maza! Ka bar Abunda kake yi kazo, yarinyar nan tana kokarin jawo min bala'i."
Yace." Wace yarinya Dady." ? Kashe wayar general yayi ba tare da ya amsa masa ba.

Da sauri ya mike hade da d'aukar key d'insa sukayi sallama da Salmanu ya futo cikin sauri ya shiga motar sa, hade da fuzgarta da gudu.


Tunani yake a mota me Salima take kokarin ta aikata Wanda har ta tayar da hankalin Dady haka, shi Sam! Bai kawo cewar Ladidi ba ce.









*BINTA. U ABBALE*
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

*🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚*
*πŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€K'WADAGAπŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€*



~*NA*~
_BINTA UMAR ABBALE_




*ZAMANI WRITES*
*ASSOCIATION🀝🏻*
___________________
```We are here to educate motivate and entertain our readas```
____________________
*10/November/2019*
^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^


```Shirafa'u 'yayan Nana kusa ni cikin masoya```
_________________________



*DEDIGATED*
*TO*
*RAHIMA ALIYU*
*ABUJA*




```BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM ```





*πŸ…Ώ35*





Tun da ya shigo da motar layin nasu hango abunda yake faruwa.
Cikin mamaki ya k'araso da motar tare da yin parking ya futo da sauri idanunsa a sama yana so ya gazgata abunda idonsa yake nuna masa.
Tabbas Wannan aljanar yarinyar ce,kenan Dady da ita ya tawo garin abuja.
Tambayar kanshi yake babu amsa.
Haladu mai gadi ya k'araso kusa dashi bakinsa na rawa yace." Allah ya taimake ka ka taimaka mana ka sauko mana da wannan hatsabibiyar yarinyar daga sama ga Hajiya can tana zubar da hawaye... Hakkim bai karasa jin abunda Haladu yake fad'a ba ya wuce da sauri! Cikin gidan ya shiga.
Dady ns tsaye sai magiya yake zabgawa LADIDI kan ta sauko daga saman gurin, Momy da Salima na gefe suna matsar hawaye.
Daga kansa yayi yana kallon Ladidi dake tsaye tsakanin wayoyin dake kewaye da gurin ta raba k'afafun ta gida biyu d'aya a cikin gidan d'aya a waje.

Sosai yake mamakin yanda a kayi ta hau gurin tunanin yake ya za'ayi ya fuzgota daga gurin, futa yayi waje da sauri, Haladu na tsaye hankalinsa na sama yana gadin LADIDI ko da zata fad'o sai ya tare ta.


Cikin ikon Allah hankalinta na cikin gidan General ya dauke mata hankali gurin magana, Hakkim yace da Haladu yayi masa dokin wuya aikuwa haka aka yi dokin wuya yayi masa jikin duguwar gatan gar akwai guraran rodi da a had'a dasu ba gurin gini nan Hakkim ya kama cikin dubara ya haure katangar hannunsa suka cake da k'ananun k'usosi jini ya fara zuba!

K'afar ta guda ya fuzgo da k'arfi ta kifo jikinsa suka fad'o k'asa tare. General da sauran mutanan gidan suka runtumo da gudu suna salati domin su duk a tunanin su ta fad'a ne kamar yanda take fad'a musu.

Sai suka gan ta kwance saman ruwan cikin Hakkim, Wanda yake mata wani irin mugun kallo na tsana idonsa yayi jawur!! Ga hannunsa yana d'igar da jini.

Ladidi idanunta a k'ek'ashe take kallonsa, babu alamun risina a tare da ita,Hakkim ya mike a zafafe! Ya watsar da ita a gurin.

Ta mike da sauri hade da d'ibar k'asar gurin kamar yanda ta saba ta watsa masa a jikinsa ta runtuma da wani irin gudu ta dauki hanya ...... Da gudu ya bi bayan ta, General ya zube a gurin hade da dafe kansa Cikin tsantsar tashin hankali.

Salima tace"Dady dama na fada maka wannan yarinyar zata iya d'ora wa mutum hawan jini Dady tun kafin ta jawo mana wani bal'in gwara gobe a mayar da ita gudansu.

Hajiya Asiya kuwa ta daina matsayar hawayen yanzu abun tsoro yake bata sosai take zargin yarinyar da motsuwar k'wak'walwa idan ba haka ba kuma to tabbas da akwai aljanu a kanta.

Gudu take kamar wata filfilwa, Hakkim ya k'ure gudunsa domi ya tadda ita Sam baya son ta futa titi a haka yasan ba k'aramin kunya bane a ganshi yana falfala gudu kamar wani zararre. Duk iya gudu irin na Hakkim kasa cin mata yayi, ya sare mutuka yanzu ya kara tabbatar wa da cewar yarinyar annoba ce a gare su.

Cak!!!! Ta tsaya jin haushin karnuka wan! Wan! Wan!wan! Haushin ya cika gurin.
Tana haki! Ta waiwaya bayanta ta hango Hakkim ya kusa cimma ta, ta kalli gabas kudu a rewa babu gurin b'uya ga karnuka sun taso mata, ihu!! Ta kurma hade da d'ora hannunta a kanta tana fad'in"Wayyo Allah Mai koko Wayyo na Iya shikkenan mun rabu da juna sun kawo ni gidan yankan kai, Dama sai da kika ce kar na zo nace sai Nazo shikkke....... Bata karasa ba ya k'araso gurin yana wani irin huci! Ya sanya hannunsa ya kwad'e mata bakinta da. Mugun k'arfi
Bakin ya fashe da sauri! Ta sanya hannunta ta Dan gwalo jini daga bakinta. Wani razanannan ihu! Ta kurma Wanda har sai da gurin ya amsa! Dan dai unguwar ma ta masu hannu da shuni ce ko wane gate a gark'ame da irin unguwar yaku bayi ne da tuni ai gurin ya cika da 'yan kallo.


Blet din jikinsa ya cire ya fara zabga mata a jikinta kamar Wanda Allah ya aikoshi, dukan ta yake babu sassauci ita Kuma tana ihu! Hade da zaginsa tana yi masa Allah ya Isa.

Bai fasa dukan ta ba har sai da yaji bakinta ya mutu ta kwanta a gurin tana nishi hade da ne kare kanta sannan ya mai da blet din jikinsa, ya bar gurin a fusace.



Motar su Dady ya ci karo da ita tsananin b'acin ran da ya ke ciki bai sa ya tsaya ya saurare su ba ya wuce abunsa.

Tun daga nesa suka hangota kwance hasken Fitilar motar ne ya nuna musu General ya kara sauri har suka Isa inda take kwance nuffashin ta na futa sama-sama a gigice general ya dauke ta ya shiga motar da ita.

Hajiya Asiya ta dawo mazaunin dravar ta kunna motar, da sauri General Yace. " Maza mu tafi babban asibiti yarinyar ta suma."!!! Hajiya Asiya ta k'ara k'arfin motar tana fad'in *"Innalillahi wa'inna ilahi raj'inun*







*BINTA U ABBALE*
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

*🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚*
*πŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€K'WADAGAπŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€*



~*NA*~
_BINTA UMAR ABBALE_




*ZAMANI WRITES*
*ASSOCIATION🀝🏻*
___________________
```We are here to educate motivate and entertain our readas```
____________________
*Fadima Ummul hasnaini ya tsokar jikin Habibi*
____________________




*DEDIGATED*
*TO*
*RAHIMA ALIYU*
*ABUJA*




```BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM ```






*πŸ…Ώ37*





D'aya daga cikin likitocin dake duba LADIDI ne ya futo yana goge gumin fuskar sa, General ya mike da sauri tare da tarar gabansa hankali a tashi yace." Dr ya jikin yarinyar ne."?

Cikin yanayin damuwa Dr ya kalli General yace." Gaskiya yarinyar tayi dogon suma sosai duk iya bakin kokarin munyi domin ta dawo hakan bai yi wu ba, but kwantar da hankalin Ku, zata dawo normal insha Allahu daga nan zuwa gobe."


General ya share gumin dake tsatstsafo masa a goshinsa hankalin sa a tashe yake fadin"Innalillahi wa inna ilahi raji'un."


Dr ya gyada kansa cike da jimami yace." Yarinyar ta furgita ne kuma anyi mata dukan mutuwa sosai ta jikkata gaskiya duk Wanda yayi mata wannan duk bashi da imani, yarinya k'arama anyi mata duka irin na masu laifi."


General Yayi shiru domin bashi da ta cewa Dr ya girgiza kansa kawai ya bude ofis d'insa ya shige. General zubewa yayi a gurin hankalinsa ya tashi mutuka yanzu yake da ya sanin dauko yarinyar ganin tsautsayi yana nema ya haushi.



Hajiya Asiya tazo ta zauna kusa dashi tare da dafa kafad'ar shi muryar ta a sanyaye tace." Dady ka kwantar da hankalin ka insha Allahu komai zai zo da sauki na lura yarinyar bata da cikkakiyar lafiya, sai futuna da ibilici ina ganin Idan komai ya dai-dai ta mai zai hana ka kirawo Liman ya duba ta sosai nasan Idan akwai wani jinnu da suke damunta to zai fada kaga sai mu san ta inda zamu fara."



General ya dago kansa yana kallon matar tasa Yace. " Babu babban Mara hankali irin Hakkim da zai kama d'iyar mutane ya dinga jibga kamar Wanda Allah ya aiko shi, yanzu idan wani Abu ya samu yarinyar ba fata nake ba, in je in ce da iyayen ta me."?



Hajiya Asiya tace." Dady ka manta Halin yarinyar ko? Ni a ganina abunda Hakkim yayi mata shine dai-dai in ba haka ba baxa ta tsaya ba, yanzu idan ta gudu ta ina za mu fara neman ta cikin wannan gari mai girman gaske."



General girgiza kansa kawai yake tabbas shawarar da matar shi ta bashi itace abun dubawa tunda ya Riga ya dauki amanar rike yarinyar tsakani da Allah kuma ya dauko ta daga gurin iyayen ta Dole yanzu duk wani nauyi ta yana kansa.




Hakkim kuwa ranshi a masifar b'ace ya koma gida diract part d'insa ya wuce Salima ta biyo shi a baya tana tambayar sa ladidi wata irin shegiyar tsawa ya buga mata, wacce ta sanya ta rugawa da gudu part dinsu. Ya ja tsaki ya wuce part dinsa .

takalmin shi bai cire ba ya kwanta rigingine kan bed dinshi yana sakin ajiyar zuciya kana ganinshi kasan a cikin b'acin rai yake, ya rasa wane irin mutum ne Dady dinshi daka ganin sarki fawa sai zak'i, haka kurrum ya d'ako musu alak'ak'ai cikin gida, Ladidi Annabo ce,domin shi kwata-kwata baya yi mata kallo mai hankali ta yaya zasu yi rayuwa da mahaukaciya, dole ma ya bar garinan. Domin bazai iya zama inuwa guda da yarinyar ba, yana jin wata irin tsanar ta cikin zuciyar sa.



Kusan awar shi guda a kwance yana sak'e-sak'e daga bisani ya mike jikinshi duk babu dad'i ya fada toilet dinshi ruwa ya hada mai dumi yayi wanka, ya futo daure da towol mai girma wani rataye a wuyan shi, ko mai bai shafa ba, ya zura boxer hade da singilet yayi kwanciyar shi kan bed yana lumshe idon sa, wayar sa ce ta fara ringing yana dubawa yaga Dady ne , gyada kansa yayi yace." Dady kai ka jawo wa kanka wannan masifar wallahi babu ruwana, gobe iwar haka ma ni na bar garin."



Har wayar ta tsinke ba dauka ba, wani kiran ya k'ara shigowa hararar wayar yayi, yace." Nasan kan yarinyar zai yi min magana yanda na kwanta ina hutawa ta,wallahi bazan tashi ba." Juyawa yayi hade da gyara kwanciyar sa.



General ya kira wayar yafi sau biyar Hakkim bai dauka ba, kuma yana ji, Dan ma kar ya kashe wayar ne General din ya fuskanci wani Abu shiyasa ya k'yale ta, gobe yana tambayar sa yasan k'aryar da zai shirga masa, amma shi babu yadda za'ayi ya tada hankalin sa, kan wata banzar yarinya kidahuma 'yar kauyen k'ayau.



General da Hjy Asiya haka suka kwana cikin tashin hankali da damuwa, b'angaran Hakkim kuwa baccin sa ya shirga babu abunda ya dame shi, a subar fari ya tashi, yayi wanka kamar yadda ya saba ya wuce masjid, k'arfe shida shaura ya shigo gidan, ya fara shirinsa domin Sam baya so Dady ya dawo ya tadda shi gidan, yasan wata masifar ce, cikin wasu suit ya futo black and White sunyi mishi kyau sosai ya matse wuyan shi da necktie lafiyayar sumar shi tasha gyara sai kyalli take, kafarshi sanye da helf cover black sai shaining yake yi yayi kyau sosai kalar fatar shi ta futo kamar wani black america haka ya futo hannunsa rike da wata k'aramar jaka.




Salima da Baito mai aiki suna Palo Baito na gurin daining tana gyarawa Salima kuwa na zaune kan kujera cikin damuwa kana kallonta kasan bata yi baccin kirki ba, ta na ganshi ta sauke ajiyar zuciya hade da fadin "Broth barka da Safiya ."



Nazarinta yake ganin yanda tayi figai-firgai yace." Barka kadai, ni zan wuce idan sun dawo ki Sanar musu, bakinta na rawa tace"Bro ladidi fa har yanzu bata farfad'o ba." Wata irin muguwar tsawa ya buga mata tare da fadin"Don Ubanki ni ina ruwana! Da zaki wani dame ni ki damu kanki, ko wa ya siyi rariya yasan zata zubda ruwa kuje Ku k'arata da ita tunda kune kuka dauko ta ni nayi tafiya, wallahi ko da wasa kika kara yimin maganar mahaukaciyar yarinyar nan sai na ballaki! Wallahi Idoit kawai !."""
Yana gama maganar shi ya fuce a fusace!

Salima tayi tsuru-tsuru tana bin hanyar da wuce da kallo ita kanta tana jin tsoron masifar yayan nasu hade da b'acin ransa, lallai yau zuciyar sa a tunzure ta, tana ganin ko Dady ne yayi masa magana zai iya fada masa magana me zafi indai akan LADIDI ne.







*BINTA U ABBALE*
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

*🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚*
*πŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€K'WADAGAπŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€*



~*NA*~
_BINTA UMAR ABBALE_




*ZAMANI WRITES*
*ASSOCIATION🀝🏻*
___________________
```We are here to educate motivate and entertain our readas```
____________________

```Shugabar mataye Binta taga mala'ika da idonta, ba shamaki ba tafinta, har ya aike ta gun Habibi```
*Fad'ima Umul Hasnaini ya tsokar jikin Habibi*
______________________



*DEDIGATED*
*TO*
*RAHIMA ALIYU*
*ABUJA*




*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*





*πŸ…Ώ39*





Cike da rashin tsoro general ya tsuguna kusa da Ladidi dake wani irin Abu da idonta, yace." Kuji tsoron Allah da manzo sa ku rabu da wannan 'yarinyar marainiyar Allah me tayi muku? Kuka yi aure kuka tare a kanta, shine me zaku cewa ubangji ranar alkiyama."?

"Hahahahaha!! Suka ji wata mahaukaciyar dariya, Ladidi nayi, tafi minti uku tana yi daga bisani tayi d'if!! Gurin yayi shiru
Lokacin Salima sai da ta saki futsari a wando. Tsoro duk ya cika zuciyoyin su daga ita

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login