Showing 3001 words to 6000 words out of 48145 words

Chapter 2 - LADIDI KWADAGA

Start ads

24 Aug 2025

61

Middle Ads

hango shi ya karyo kwana, zai shiga gida, da sauri ta shige soron wani gida tana lek'en shi, har ya wuce, tai sauri ta futo da gudu ta bar gurin.


A mutuk'ar gajiye ya shiga gidan, Mai koko na tsaye tana aikin tata sai sauri take saboda magari ba tayi,, guri ya samu ya aje abun sana'ar tashi,, ya zauna kan tabarma cikin gajiya, yace"Iya sannu da gida da aiki"

"Yawwa Sannu ka dawo kenan"?
"Eh Wallahi Allah yayi mana dawowa"
"To masha Allah" Iya tafad'a ta cigaba da abunda take
Kishingid'a yayi yace"Iya ina Ladidi take ne? Yau naga aiki yayi miki dare, ko ta futa yawon da tasaba ne"?

Ajiyar zuciya ta sauke tace"Yanzu ta futa ashe ba ka ganta ba, tana futa kana shigowa"

K'wafa yayi cikin b'acin rai yace"Wato yarinyar nan bata jin magana ko Iya"?

"To yaya zakayi ne, sai kayi mata addu'a k'uruciya ce take damunta"

"Nifa Iya babban bak'in ciki na da Ita rashin kamun kai da wasa da maza da take in taje dandali babu shirmen da bata yi wallahi"


"To wai yaya zakayi ne D'alha, nifa bana son kana takura mata, nasan duk abunda take k'uruciya ce watarana zata daina"

Shiru yayi ya daina wahalar da bakinsa domin yasan duk surutun da zaiyi Iya sai ta kare Ladidi duk wani iyashege da yarinyar take itace take daure mata gindi.
Mik'ewa yayi ya d'auki buta ya futa waje domin ya d'aura alwala.


Suna zauna gidin wata k'atuwar bishiyar mangwaro, sun kai su Tara zuwa goma duk sun kewaye ta itace shugaba,, duk sun mimmik'e k'afafunsu suna wasan *nanje na gidan gona* in an cinye mutum sai su kwashe da dariya har da burgima,, ihu! Suke suna fad'in Ladidiya don Allah yanzu ki sauke a kaina,, muga wa za'a kad'awa barbad'in tusa"
"Ku tsaya!Ku tsaya kuji! Ku tsaya kuji"! Ladidi ce take fad'in haka.
Tsit! Sukayi suna sauraron ta,, k'aykayin da taji kanta nayi ne ya katse mata abunda take so tace, cire d'ankwalin tayi ta jefar k'asa ta sanya hannuwan ta biyu ta dunga kartar kan tana lumshe ido,, dad'i take ji sosai in tana sosawa, shiru sukayi kowa yana jin tsoro kar yayi dariya ta doke shi,, tafi minti biyar tana aikin sosa kanta sannan ta cire hannuta tana muzurai,, kallonsu take ta sha kunu domin shaf ta mance a inda take idan tana Sosa kai kwata-kwata mance komai take,, so take taga ko akwai wanda zai mata dariya a cikin su, sai taga duk sun nutsu,, ba tare da ta mayar da d'ankwalin nata ba tace" Ku san me"? Had'a baki sukayi gurin fad'in "A'a sai kin fad'a"

Dariya ta kece da ita tace"Wallahi duk wacce k'arshe ya sauka a kanta to ta saddak'ar da cewar sai anyi mata ihu an k'ada barbad'in tusa kuma har gida za'akai ta anai mata ihu! Kun yarda ko"?

Ihu! Suke suna fad'in "Mun yarda" Mun yarda"

"To kowa ya mike k'afarsa a sako daga farko"

Mik'e k'afafun su sukayi, ta fara yi musu,, duk wacce ta futa sai ta koma gefe tana murna ya rage saura mutum biyu Murja da Indo kenan duk sunyi tsuro-tsuro dasu,, ita ko Ladidi sai dariya mugunta take musu,, Nan je na k'arshe ya sauka a k'afar Indo ta mike da sauri tana murna,, Murja ta mik'e da sauri zata gudu,, Ladidi ta tad'o k'afar ta, tafad'i gurin ,sai suka dauk'i ihu!!!!! Yeeeee!! "Murja warin wando Murja mai wari tusa,akad'a mata barbad'in tusa, a kad'a mata bar bad'in tusa!!!! Su ka ture Murja suna yi mata ihu!! Suna ja mata k'afafu saurin muryar Ladidiya yafu na kowa tashi a gurin.

Hankalin masu sai da nama fura da nono da duk wani mai sana'a gurin ya dawo Kansu,, Mutari me nama yace " Wannan yarinya baza ta tab'a barinmu mu huta ba wallahi duk itace shugaba" Haliru me fura da nono ya nufi gurin a fusace yana fad'in "Bari naje nayi maganin su" Yana zuwa gurin ya d'aga murya yana fad'in "Ke " yar gidan mai koko, zan ci ubanki wallahi idan baki ja zugar ki ba kun bar gurin nan ko an fad'a miki kowa mahaukaci ne irin ki"?

Tsittt! Sukayi jin abunda Halliru yake fad'a, Ladidi ta kura masa ido tana jin takaicin zagin da yayi mata, amma tasan abunda zata yi masa,, ganin sun daina ja mata kafa yasa ta mike da sauri zata gudu, Ladidi tayi saurin damk'e ta tana fad'in " Murja me warin wando Murja me warin tusa yeeee! a kad'a mata barbad'in tusa!!! Aikuwa sauran suka d'auka gurin ya k'ara kacamewa da ihu!! Halliru ya gama b'ab'atun sa ya hak'ura ya tafi domin ko sauraron sa ba suyi ba, haka suka tasa Murja suna ihu! gami da dungure mata kai, har suka kai ta gida,, sai kuka bak'in ciki take,,nan ta basu umarni tafiya kowacce ta kama hanyar gidan su, ita kuwa dandali ta k'ara komawa domin ta aiwatar da k'udirinta. Kan Halliru a ganinta tana raye babu wanda ya isa ya zagar mata iyaye ba ta hukun tashi ba,,

Ta bayan gatangar da suke zaune ta bi,, sosai gurin yake da kwazazzabai gami da ra muka katangar ta d'ane sosai ta hau ta dura, a hankali ta tsuguna tana tattaro k'asar gurin,, zanin ta ta kwance ta zuba k'asar a kai ta nufi inda suke zaune,, Halliru na can gurin wani mai rake suna magana, shi kuma Mutari mai nama kasuwa ta bud'e ana ta cini ki,, da sauri ta bud'e doguwar robar dake cike da nono ta zazzage wannan k'asar me uban yawa da ta d'ebo ta cikin zaninta, ba tare da ta d'aura zanin ba ta bar gurin kamar walk'iya.
Halliru ya dawo gurin da sauri hannunsa rik'e da wata roba me kamar kwanon sha, da ledoji a hannun sa,, wasu matasa na bin bayan sa, da sauri ya bud'e robar nono sa ya zura k'aton ludayi da yake motsa wa,, sai yaji gurin-gurin d'in dutsina da k'asa a ciki,, salati ya rafka da sauri ya zaro cocilan d'insa daga cikin aljuhu yana haskawa, innallahi wa'inna ilahi raji'un , nono ya rine! Ya koma jajazur dashi, ya kalli Mutari mai nama dake hada-hadar sallamar jama'a yace"Mutari"!!!!!





*COMMENT VOTE AND SHARE*
[9/23, 7:47 AM] 8k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

*🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚*
*🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀*




*NA*
_BINTA UMAR ABBALE_
~*®BINTUBATULA👄*~



*MARUBUCIYAR*

```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```TSANTSAR BUTULCI```

_*LOODING:*_
_*{LADIDI K'WADAGA🌚}*_




_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_

_______________________
```We are here to educate motivate and entertain aur reades```
_______________________





_*DEDIGATED*_
*TO*
_RAHAMA ALIYU_





```Komai yayi tsanani yana tare da sauk'i, cikar muminin mutum yarda da k'addara mai kyau da mara kyau, idan ubangiji ya jarrabe ka, da musiba ka karb'a hannu biyu kar kace wani ne yayi ma, ko da wani mutum ne silar faruwar haka to kasani babu abunda bawa ya Isa yayi face da sanin mak'agin ka, Ubangijin baiwa kenan alimul gaibu washahadati, ka mik'a masa al'amarin da sannu zai yaye maka damuwar ka, Allah kasa mu dace```






_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_





*🅿4*





Da sauri Mutari ya juyo jin irin kiran da Halliru ya kurma masa, baki na rawa yace"Akwai wanda yazo gurin nan bayan naje guri Umaru mai rake yanzu"?

Cikin mamaki Mutari yace"Gaskiya babu wanda yazo kan kayan ka ina kallo tun d'azu"

Kamar ya fashe da kuka yace"Zo kaga abunda akai min"
Mutari ya baro gurin sa da sauri yazo yana dubawa,, salati yasa yana mamaki tare da fad'in"Wannan aikin Ladidi ne wallahi, d'azu ba kaje har inda suke ba, ina jin kana zaginta" Halliru yace"To kuma da kace baka ga wanda yazo gurin ba"

"Tabbas ban ga kowa ba, amma na tabbatar da cewar Ladidiya ce zatayi maka wannan aikin, wallahi kasan ta kamar aljana take, sam ba'a ganinta a guri" Cikin fushi Halliru yace"Billahillazi sai sun biya ni kud'in nono na, idan ta saba yi wa wasu suna k'yaleta to ni wallahi bazan d'auki asara ba"

Murmushi Mutari yayi yace"Shiyasa d'azu kamar in ce maka kar kaje inda suke saboda nasan halin yarinyar bata da mutum ci wallahi shiyasa kaga ni bana shiga sabgar ta, ko kaman ta lokacin da ta watso min ruwan kwata kaina kasan ranar har nama da gurasa basu tsira ba sai da ruwan kwatar ya same su,, ko da na je na fadawa kakarta hakuri kawai ta bani, da k'yar na kara tayar da wani jarin"


Halliru ya tsuguna yana goge gumi, Ladidi ta kassara masa rayuwa ta rusa masa jarin sa, yau-yau d'in nan ya d'auko sabon nono duro guda dubu goma sha biyu yarinyar nan ta zuba masa k'asa a ciki,, kewaye shi sukayi suna bashi hakuri wasu na bashi shawarar kawai ya tafi ya fadawa mai gari a bi masa hakkin sa.


Tana tafe tana d'aura zaninta,, gami da kad'e ragowar k'asar dake jikin zanin,, ta gyara d'aurin d'ankwalin ta,, ta cigaba da tafiya fagam-fagam! Ko tsoron dare ba tayi, Tara da rabi na dare, haka ta dunga wuce majalisa ta maza babu abunda ya dame ta,, har ta karya kwana zata nufi gida sai ta canza shawara juyawa tayi ta koma da baya, kwanar gidan kallo ta nufa,, tun daga nesa ta gango matasa sun cika rumfar kwanon ga hasken wuta nan tar! Masu gyad'a da daddafan k'wai da saurarnsu sai cini ki suke,, bayan gurin kallon bola ce,, gashi ba wani dogon gini bane wani gurin ma da langa-langa a ka rufe,, a hankali ta hau kan bolar ta daddafa ta d'ane kan k'aramar katangar,, kanta ta zura tana lek'awa, aikuwa taga matasa sun cika gurin suna zaune kan bainci wasu ma basu samu guri ba, suna tsatstsaye sai ihu! Suke da alama film din ya d'auko dad'i, sosai take zura kanta domin taga wane irin film ne da ake ihu!! Wani saurayi ne ya kare mata da tsahon sa, ji take kamar ta sauka ta zabga masa mari,, ihun da sukeyi yana hana aji komai sai wani take take ji babu alamun k'usha-k'usha,, kunne ta kasa sosai lokacin da Taji wannan saurayin yana magana dana kusa dashi "Gaskiya ina son film d'in nan wallahi, Sharukahn ya iya soyayya , nifa lokacin da ya rungume ta, he da na kusa suma dan dad'i wannan film din yayi kyau wallahi" Dariya d'ayan yasa yace" Ya sunan film din ma"? "Khoch-khoch hotaih" Hahahaha Gaskiya film din yayi ko nawa ake ce zan biya domin in kalle hi"
Ihun!! da suka ji ne yasa suka mai da hankalin su kan Tv,, Ladidi tace"Hegu "yan iska ni da nasan ba na fada bane ma bazan zo b.... Maganar ta ta katse lokacin da Allah ya bata ikon hango akwatun tv an hasko Sharukan da kajol suna soyyaya da rungume-rungume! " Kan Uba!! Ta kurma wani uban zagi,, tsaki taja tana k'okarin dura kasa tace"Allah wadaran in tsaya in kalli wannan iskancin, nifa shiyasa na tsani wannan Dan film din gwara Salman kan,, yana da mutum ci,, dura tayi k'asa tana Jan tsaki sai mita take da ta sani bata zo ba, inda ta San ba fim din fada bane,
Shiru gurin duk masu saye da siyarwa dake gurin sun tashi,wasu ma har sun soma futowa daga gurin kallon dana film din yazo karshe, ko a jikinta, ta kama hanyar gida fud'un-fud'un,, kamar daga sama, taji an cafki hannuta, ta juya a fusace! Ilu ne ya ke mata wani kallo yana lashe baki. Hararsa tayi tace"Sakar min hannu ko in ci abu ta kazar ka" Ilu yace"Ni kike zagi takand'a" ? Fuzge hannuta tayi a fusace! Ta tsani ya kira da wannan suna wai takand'a, tace"Uwarka ce takand'a bani ba"

Mari ya kai mata, ta kauce da sauri,, hannuta yaja da k'arfi ya na kokarin kai ta wani lungu ta turje tana zagin sa,, yace"Dama neman ki nake ruwa a jallo Dan uban ki, d'azu kin fasawa k'anwata baki ranan kin zage ni ,to yau zaki gane kuran ki" janta yake tana turjewa, gami da durzar k'asa da kafafun ta, duk k'arfin sa sai da ya sare, ya kama haki!! Tace"Sake ni ni ba "yar iska bace"

Yace"Sai ki gayawa wanda bai sani ba, Dan uwarki daga gidan Uwar ki kike shegiya jiki duk jijiya sai k'arfin tsiya"

"Uwarka ka zaga ba tawa ba" tafad'a a fusace! Yace"Au! Baza kiyi shiru ba" ?

"Sai kayi shiru zanyi, kuma wallahi zaka San ka zagi uwata" "To me zakiyi Takand'a" ? yafad'a yana mata dariya ta k'arfin hali, domin duk ya gaji yau ya kara tabbatar da cewar yarinyar ba ita kadai bace,, shamtar sa tayi yana fad'in "Zaga kuwa abunda zanyi yanzu" kafin ya ank'ara ta kwashe k'afafun sa da hannu daya ta zubar dashi a gurin ta falfala da gudu tana shek'a dariya babu ruwanta da dare.

Ilu ya rike bayansa yana rintse ido sosai bayan sa ya bugu da wani dutse ya Dade a kwance a gurin "yan gidan kallo na ta wuce shi a kwance,, cikin takaici ya mike tsaye yana da ya sanin kula Ladidi gashi ta ji masa ciwo a banza.



Mai koko na tsaye a soro cikin tararrabi, k'arfe goma da rabi na dare, Ladidi ba ta shigo gida ba, ta duba ko ina bata nan,, D'alha ya gama fad'an sa ya futa nema,, da ya d'auka abun wasa ne, sai da yaga an gama Taskar labarai, hankalin sa ya tashi, babu shiri ya bazama neman ta,, duk ya duba inda ya dace babu ita, ya nufo gida cikin gajiya da sarewa, zuciyarsa ta raya masa yaje ya duba gidan kallo, hanya ya kama yana tafiya yana addu'a a zuciyar sa,, da tafiyar ta ya gane ta,, b'uya yayi sai da tazo ta wuce sannan ya futo ya bi bayanta, abunda yasa ya b'uya shine yasan halinta in ta ganshi tana iya guduwa,, tana shiga soron gidan yana shiga,, ya sanya k'arfi ya k'wade mata k'eya d'ankwalinta ya fad'i kasa, ta rusa ihu! Wannan karon Iya bata hanashi dukanta ba, fad'i take " Kara mata ja'irar yarinya gantalalliya ta tayar mana da hankali"

Ladidi ta buga wani uban tsalle ta afka cikin gidan tana kurma ihu!! Kamar Wanda aka kona mata jiki da ruwan zafi,, d'akin Mai koko ta shige ta zura sakata tana ihu! Tun k'arfin ta.















*COMMENT VOTE AND SHARE*
[9/24, 10:59 AM] 8k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

*🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚*
*🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀*




*NA*
_BINTA UMAR ABBALE_
~*®BINTUBATULA👄*~



*MARUBUCIYAR*

```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```TSANTSAR BUTULCI```

_*LOODING:*_
_*{LADIDI K'WADAGA🌚}*_




_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_

_______________________
```We are here to educate motivate and entertain aur reades```
_______________________



_*DEDIGATED*_
*TO*
_RAHAMA ALIYU_




_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_





*🅿5*





D'alha yace"Gashi kinji daga bakinta ko? can na gano ta ita kad'ai kan hanya tana tafiya ko tsoron dare ba tayi" Mai koko tace"Yanzu dai kayi hakuri mubar maganar sai da safe dare yayi" K'wafa yayi cike da takaici ya yar da abun dukan ya shige d'akinsa. Iya ta sassauta murya tana fad'in"Bude min kofa kinji ko,, bazan bari ya doke ki ba" Ladidi najinta tayi mata shiru,, "Na ce dake ya tafi d'akinsa ki bude min kofa nace ko" Banza tayi mata,, Sauraye sai cizon Iya suke babu abunda take so illa ta kwanta don tayi muguwar gajiya, rarrashin Ladidi take ta bude mata kofa,, k'eme-k'eme tak'i budewa, gyara kwanciyar ta tayi ta lumshe idonta bacci na fuzgarta, tana jin surutun da Mai koko take sam bai dame ta ba,, b'acin rai da takaici suka saka zuciyar Mai koko kamar ta buga gashi ko "yar tabarma babu a tsakar gidan ballantana ta shimfud'a ta kwanta,, ga duhu ga sauro ga danshin ruwa, bata so ta daga murya saboda dare kar D'alha yaji soro ta nufa a hankali ta kwanta kan dogon bainci da masu siyan koko suke zama tana addu'a a zuciyar ta, Allah ya shirya mata Ladidi.




*TUSHEN LABARI*


*K'auyan d'an kunkuru* k'auye ne dake cikin jahar kano,, ya had'a da Fulani a ciki amma ba sosai ba,, k'auye ne da yake da albarkar gonaki da filaye gami da manya-manyan bishiyun mangwaro ko ta ina,, Malam Labaran manomi ne wanda yake da gona guda d'aya yake noman d'orawa da gero a ciki,, da Abunda ya dogara kenan dashi yake ci da iyalinsa yake sauran bukatu, yana da mata d'aya da yara biyup
duk maza, matarshi sunanta Furera, mace mai Neman na kanta tunda aka kawo ta gidan Mijinta take sana'oi iri -iri , domin ta dogara da kanta, dansu na fari sunan shi Aminu yana da lalurar sikila sai Dan uwanshi D'alha shi lafiyan sa lau, abunka da k'auye San basu maida hankali gurin ciwon dansu ba, sai dai in ciwon ya motsa masa suyi masa jike-jike su bashi, Cikin hukunci ubangiji ya mike ya cigaba da rayuwa kana kallo Aminu kasan bashi da koshin lafiya tare suke tafiya gona da mahaifin sa,, ko sunje can ma baya iya aikin koma, D'alha ne me karfi,,

Malam Labaran yana da aboki D'an Fulani gurin zuwa kiwo suka hadu dashi,, inda Allah ya had'a jininsu ta kaisu ga had'a yayan su aure Aminu da Amina "yar Dan Fulani itama tana d'auke da irin lalurar Aminu, dake d'an Fulani ma'abocin jin redio ne, ya tab'aji suna fada cewar idan masu irin cutar zasuyi aure su dunga auran jinsu su, nan Labaran ya amunce, ya kuma Sanar da Aminu da Hurera duk suka amunce suna fatan alkairi,, lokacin yayi aka d'aura aure cikin aminci Amina ta tare gidan Mijinta Aminu inda gurinsa yake kewaye da langaga sai dai in zata shiga band'aki take futowa babban tsakar gida,, wata hudu da auran su, ciwon Aminu ya tashi kafin ayi wani yunk'uri ya galabaita mutuk'a jikinsa kamar babu jini ya dashe Tass,, wani makocinsu ya basu shawarar zuwa birni domin a duba shi, to suna cikin shirin tafiya ne, Allah ya amshi Abunsa , mutuwar sa ta girgiza mutane mussaman matarsa Amina tayi kuka har ta gaji " yan uwa na tasaunta tayi hakuri,, bayan sadakar uku kowa ya watse akabar mutan gida da kewar Aminu mutumin K'warai kenan, bayan sadakar ar'ba'in ne aka gano cewar Amina na da ciki, aikuwa Mai koko ta dunga kula da ita sosai har lokacin haihuwa yazo,, inda Amina ta fara zubar da jini abunda ba a so kenan ko mai lafiya balle mai sikila, hankali a tashe aka d'auke ta sai asibitin birni *(Murtala muhamad hospital)* ganin tana cikin halin taimako ne yasa suka shiga da ita dakin operation,, suka ce mijinta ya sa

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login