Showing 33001 words to 36000 words out of 48145 words

Chapter 12 - LADIDI KWADAGA

Start ads

24 Aug 2025

68

Middle Ads

Dady Hjy Asiya itama tasa dariyar tana ta yasu.

Yana zaune gurin hutarwar ya hangi futowar su, tun daga nesa yake k'arewa yarinyar kallo zuciyarsa na sak'a masa abubuwa da yawa a kanta, sosai yake jin zafin abunda tayi mishi farkon zuwan shi gidan. Yana jin wani irin haushin ta gami da k'yamarta domin shi ramar ta ma tsoro take bashi yarinya sai kace muciya sai kai da uban ido kwala-kwala jiki duk jijiya. Saurin d'auke kansa yayi da yaga Dady ya d'ago kansa yana dube-dube aikuwa karaf ya hango shi zaune. Daga murya yayi tare da kiran sunan shi. Ya amsa cike da ladabi ya taso. Ladidi na tsaye hannuta rike da murfin mota ta dinga banka masa harara tana ya mutse fuska duk cikin'yayan General shi kadai ta tsana tunda baya kaunar ta.

Cike da bada umarni General yace." Ka shiga ka tuk'a mu zamu shiga kasuwa yanzu." Sunkyar da kansa kasa yayi yana sosa kai kamar munafuki yace." Dady da ina so in koma abuja ne yanzu shirin da nake kenan wallahi." Wani kallo General din yayi masa yace." Ka koma abuja kayi me."? Kansa ya Sosa yana shirin kirkiro k'aryar da za shirga. General din yace." Kaga Malam bama son rashin abunyi kawai ka shiga mota kamar yanda nace.ai na gano abunda zai sanya ka koma abuja yau din." Cike da takaici Hakkim ya bud'e kofar mota mazaunin dravar ya shiga yana jin wani kunci da takaici a zuciyarsa Wato shi ya zama dravar kenan ? Shi da yazo Hutu an mai she shi dravar saboda tsabar bashi da galihu dravar ma na kucakar yarinya 'yar k'auye me kwarkwata gami da karzuwa, ya zame masa dole ya bar garin nan.domin ya fuskanci Dady ya shirya tsaf! Gurin ganin ya kuntata masa.

Suka hau titi sosai sai gudu yake Ladidi ta tsira da k'arfi tace." Baba kace dashi ya daina gudu nan da yake tsoro nake wallahi."

General yayi saurin kallon Hakkim yace." Ka kula mana ka rage gudu sai shilla mu kake kamar zamu tashi sama."


Hakkim bai san sanda ya daki kan motar ba saboda tsabar takaici wato yanzu Dady shima umarni Yarinyar take bashi. General yace." Kai meye haka kuma? Kai da aka ce ka rage gudu zaka daki kan mota ."


Hankalinsa ya dawo cikin wayancewa ya Sosa kansa bai ce komai ba ya rage gudun da yake yi. Shi ko General ya juya ya cigaba da hirarasa dasu Ladidi wacce Salima take ta zolayarta ita kuma sai zantuka take mata irin na shashanci.

A hankali yace." Dady mun futo cikin gari wace kasuwa zamu shiga ne." ?

General yace. " anya kuwa zamu shiga kasuwa yanzu dubi lokaci 1:00 na rana muje Sahad stor kawai duk abunda ake bukata za'a samu."

Bai ce komai ba ya juya kan motar zuwa Shahad Sto zuciyarsa na masa zafi DOMIN ya fuskanci Ladidi za'ayiwa siyayya.



Parking yayi inda aka tanada suka futo shi kuma ya gyara zama cikin motar bashi da niyyar futowa.General yace." Ka futo mu shiga tare mana." Girgiza kansa yayi tare da fad'in "Dady Ku shiga kawai bana bukatar komai."


General yace." Sai ka futo fa domin ni banga amfanin zamanka cikin motar ba."


Hakkim bai iya musu ba bare ga mahaifinsa sai ya bude mota ya futo kawai yana jin taikacin takura sa da Dady yayi abunda ba halinsa ba.


Suna shiga ya samu kujera ya zaune fuskar nan a murtuke,wayarsa ya Ciro yana latsawa . Dady suka wuce ciki shida su Salima.Ladidi sai K'auyan ci take zubawa sosai jama'ar da suke ciki suka dinga kallonta kamar sun samu TV Dady sunyi gaba shi da Sallma bai San ta tsaya a baya ba, tana hauka ganin wani takalmi me mugun tsini da jakarsa cikin wani glass sai d'aukar ido yake kokari kawai take ta bude glass din ta Ciro takalmin fad'i take." Yeeeeeh kan uban can kunga wani hegen takalmi kamar jirgin sama wallahi sai na d'auko hi." Hannunwanta biyu ta sanya tana k'okarin zuge glass din sai wata mahaukaciyar dariya take. Aikuwa kan kice kwabo jama'a sun fara Ciro wayoyinsu suna mata video suna dariya, wata mata tazo ta riketa tana fadin "Ki tsaya mana a zo a bude miki." Bangaje ta tayi ta fad'i a gurin.daya daga cikin ma'aikatan gurin ya k'araso da sauri yana mata magana, ko kallonsa ba tayi ba ta cigaba da abunda takeyi.


Cikin zafin rai ya k'araso gurin ya juyo da ita a zafafe ya shimfid'a mata wani bahagon mari! Ji kake Tass! Tass! Har sau biyu.
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

*🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚*
*🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀*




~*NA*~
_BINTA UMAR ABBALE_
*BINTUBATULA👄*



*MARUBUCIYAR*

```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```TSANTSAR BUTULCI```

*LOADING:*
*{LADIDI K'WADAGA🌚}*




_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_

_______________________
```We are here to educate motivate and entertain our reades```
_______________________




*JAN KUNNE⚠*

_*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_





*DEDIGATED*
*TO*
*RAHIMA ALIYU*
~*ABUJA*~





_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_






*23/October/2019*






*29*








Wani uban ihu! Ta kurma Wanda ya jawo hankalin mutane da dama dake cikin gurin ciki kuwa harda General da Salima dake can b'ngaran kayan tea Salima na had'awa, da sauri General ya aje kwalin Milo dake hannunsa domun ya fahimci Ladidi ce take kurma ihu!! Yana zuwa yaga dandazon mutane sun kewaye ta, ga Hakkim a tsaye a kanta yana zazzaga mata masifa tare da zaginta da fada mata munanan maganganu.

Cike da b'acin rai ya k'arasa gurin yace." Wai me yake faruwa ne? Take wani ma'aikacin gurin ya fara fad'a masa duk abunda ya faru, ya kalli Hakkim ransa a b'ace yace" kan ta aikata haka ka dake ta.? Shiru yayi yana kauda kansa yaso Dady bai zo gurin ba ya wulakanta ta cikin jama'a. Genaral ya kalli jama'ar gurin yace" kowa ya tafiyar sa" aikuwa suka watse daga gurin. Ya kalli ma'aikacin dake tsaye a gurin yace." Ka ciro mata takalmin da jakar tunda tana so." Yace." Angama Alhaji." Hakkim tsantsar takaici da b'acin rai yasa ya bar gurin a fusace! Dady ya bishi da kallo yana girgiza kansa. Ladidi ya kalla dake zaune a kasan gurin hannunta dafe da kuncinta sai zumb'ure-zumb'uran baki take yace."gashi nan za'a d'auko miki takalmi ai kina so ko"? Daga kanta tayi ta mik'e tsaye tana buge jikinta General yace." Duk abunda kika gani kina so anan ki fad'a a d'auko miki kar ki kara saka hannu saboda kar kiyi musu b'arna" d'aga kanta tayi, zuwa yanzu itama ta fahimci wautar da ta. tafka, Bayansu ta bi simi-simi duk jikinta yayi sanyi da ganin yanda jama'a suke kallonta wasu na ta b'oye dariyar su wasu kuwa tana kallonsu suna bude wayoyinsu tasan abunda tayi suke dubawa suna dariya kunya duk ta ishe ta taji takaicin zagin da Hakkim yayi mata cikin mutane.

Salima ce ta dinga zab'ar mata kaya masu kyau da dogayen riguna gami da undis kayan kwalliya mayafai masu kyau da tsada, tsaf suka kammala Dady ya biya kudi Salima ta fara yunk'urin d'aukar kayan General ya dakatar da ita tare da fad'in" ta kira Abudul a waje." Jiki a sanyaye ta tafi yana zaune cikin mota tace Broth Dady na kiran ka" fuskarsa a murtuke yace." Me zanyi masa dallah Malama kauce ki bani guri" da sauri Salima ta bar gurin, tana komawa tace" Dady gashinan" wani ma'aikacin gurin ya k'araso tare da fadin " Alhaji wannan aikin mu ne" ya fara d'aukar kayan yana futa dasu wajan mota suka biyo bayansa Boot ya bud'e masa yana zubawa General ya kalli Hakkim dake faman d'auke kansa yace." Kaje ka taya shi d'ebo kayan mana"

Wani iri yaji a zuciyarsa wai me Dady yake nufi ne? Shi ko General yana sane yake masa haka domin ya k'untata masa ne. A hankali ya futo daga motar ya shiga ciki, su kuma suka shiga motar Hakkim ya dinga futo da kayan yana zubawa a boot zuciyarsa na masa zafi da rad'adi. Sai da sukayi saura sannan ya bar masa ya k'arasa General ya futo da kudi ya bashi, yayi ta godiya ya tafi.
Motar ya shiga ya kunna suka bar gurin, General da 'yayansa hira suke sosai babu me saka sunan Hakkim a ciki to shima nashi b'angaran yaji dadin haka, sauri-sauri yake suje gida ko ya daina ganin mummunar fuskar yarinyar duk sanda zasu hada ido da ita ta mirror mugun kallone yake raba su da ita.

Suna Isa gida ana kiran sallahr la'asar da sauri ya futo daga motar domin baya so ma wata magana ta had'a shi da Dady din don kar yace ya d'ibi kayan ya shiga dasu ciki.

Yana shiga parlor dircat bedroom d'insa ya shiga babu wanda ya kula a cikinsu Salim ne yake masa magana da cewar "broth kun dawo kenan"? Uffan be ce masa ba ya wuce ciki." Hjy Asiya tace" butsu kenan mybe sun tafka rigimar shida Dady shiyasa ya shigo yana bugun iska" Yusuf yace." Aikuwa kuma nasan duk akan Ladidiya ne" Salim yace." Aikuwa na lura yarinyar ta shiga ran Dady wallahi ". Hjy Asiya tace." Ni kaina yarinyar tana bani tausayi sosai na lura shima Dadyn Ku tausayin ta yake ji kasan shi da tausayin tsiya" Yusuf yace "hakane Mama." General na shigowa ya umarci su Yusuf da Salim suje su kwaso kaya cikin mota, suka mike domun cika umarni, daining ya nufa yana fad'in" Zo ki had'a mana abunci mu kwaso yunwa sosai." Hjy Asiya ta mike tana fad'in "ai naga alama gashi wancan sarkin zuciyar ya shigo a fusace kamar zai duke mu." K'wafa general yayi yace." Rabu dashi kinji! Na rasa me ke damun Hakkim wallahi zafin zuciyarsa yayi yawa, Aminatu ya samu Sahad sto ya k'ara duka jama'a suka taro a Kansu." Hjy Asiya ta saka salati tana fad'in " Me tayi masa kuma"? Girgiza kai yayi yace." Ta nuna tana son takalmi to kinsan halin mutuniyar taki da k'auyanci tana k'okarin yi musu barna shine ya yanke wannan hukunci a kanta." Hjy Asiya ta kalli LADIDI dake tsaye tana kumbura kamar zata fashe tace." Zo Amina ke Salima Zo Ku ci abunci." Suka k'araso gurin tare da zama kan kujera. Nan ta hadawa kowa nashi cikin hikima take wa Ladidi Fad'a sosai jikinta yayi sanyi da abunda ta aikata Hjiy Asiya ta kalli Salima tace." Ki nuna mata yadda zata yi amfani da komai ki dinga koya mata abubuwa burni ta fara girma kinga ko zaki girme ta da k'adab ne ki dauketa a matsayin k'anwar ki". Salima tace." Insha Allah Mama na dauki alk'awarin yin haka, sai naji ina ma kakarta zata barma na ita." General yace." Ba ke kadai kike wannan tunanin ba Salima."

Haka dai suka ci abunci suna hira , bayan sun gama General ya mike ya shiga bedroom domin yin wanka da sallar la'asar Salima da Ladidi suma suka shiga cikin wani bedroom Sukayi Wanka tare da Sallah nan Salima ta baje kayan tana nunawa Ladidi yanda ake amfani da komai.

Magariba kowa ya shiga domin yin sallah Ladidi ta futo parlor taga babu kowa da sauri ta nufi kofar futa, harabar gurin shiru duhu ya fara kawo wa masu gadi duk sun juya baya suna sallah tazo ta bud'e k'aramar k'ofa ta futa, ko ina zata oho!!!!














*BINTA U ABBALE*
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

*🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚*
*🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀*




~*NA*~
_BINTA UMAR ABBALE_
*BINTUBATULA👄*



*MARUBUCIYAR*

```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```TSANTSAR BUTULCI```

*LOADING:*
*{LADIDI K'WADAGA🌚}*




_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_

_______________________
```We are here to educate motivate and entertain our reades```
_______________________




*JAN KUNNE⚠*

_*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_





*DEDIGATED*
*TO*
*RAHIMA ALIYU*
~*ABUJA*~





*26/October/2019*





_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_












*🅿30*






Waige-wage take yi babu kowa a layin tsitt!! Kawai ta sai ci hanyar zuwa gidan su tana yi tana waiwayen bayan ta, Hakkim ya futo daga wani massalaci dake bayan layin ya hango ta tana tafiya kamar wata mahaukaciya, bayan ta ya bi da sauri domin ya tsorata mutuk'a yana jin tsoran kar ta gudu Dady ya sirfa masa bala'i yasan cewa zai yi shine ya kore ta, jin ana bin ta a baya yasa ta wai wayo da sauri suka hada ido da Hakkim din a guje!!! Ta falle, siket din jikinta na harde ta, shima gudun ya sanya da k'arfi yana tattare hannun rigar shi saboda ya lura sai yayi da gaske domin yasan halin taurin kan yarinyar.

Garin waiwaye taji tun tub'e da wani k'aton dutse ta fad'i a gurin tare da rik'e k'afar ta guda tana kurma ihu!!! Ya k'arasa gurin yana watsa mata wani banza kallo. Cikin wata razananniyar tsawa! Yace." Don ubanki ina zakije? Kurrr!!! Tayi masa da ido tana cije bakinta. Ya k'ara buga mata tsawa a karo na biyu tare da fadin "ba magana nake dake ba ne shashasha mahaukaciya kawai." Da sauri ta mike tsaye tare da fad'in." Kaine mahaukaci bani ba." Cike da mamaki yake kallonta. K'irjinsa ya nuna da hannunsa yace." Ni." Gyad'a kanta tayi babu tsoro a idonta. Wani bahagon mari ya kwarfa mata a fusace! Yace." Wuce muje gida ko yanzu in karasa toshe miki d'aya kunnen naki." Ido jazur tace." Ank'i a wuce din."

Janta ya fara yi a k'asa ita kuma tana d'ebo k'asar gurin tana watsa masa a jiki tana zaginsa." Hakkim yaji kamar zuciyarsa zatayi bundiga wai wannan yarinyar wace irin ibilishiya CE ne? Yake fada cikin zuciyarsa.


Wayarsa ya Ciro da sauri ya fara Neman numbar Dadyn nasu.General ya dauki wayar da sallama Hakkim din yace." Dady ka futo yanzu ga yarinyar nan a bayan layi na ganta zata gudu." General ya aje wayar da sauri! Ya mik'e Hjy Asiya tace." Wani abun ne ya faru."? Cikin fada yace." Garin yaya kika bari Aminatu ta futa amanar da kika d'auka kenan." ? Hjy Asiya ta mike tsaye da sauri tace." Yarinyar da suke daki ita da Salima Yallab'ai. " futa yayi ba tare da ya tsaya ya saurari sauran zan can ba.
Ita kuma ta nufi dakin Salima hankali a tashe! General yana futa ya hango Hakkim na janta kamar Wanda yake Jan ice ranshi ya b'aci da sauri ya karasa gurin yace." Hakkim mutum fa kake ja a kasa ba dabbah ba." Cike da jin haushi yace." Dady kasan halin kaurin kan yarinyar fa, yanzu ma bakaga yanda take zagina ba. Aikuwa kafin ya rufe bakinsa Ladidi ta dibi kasa ta watsa masa k'asa tare da fadin "Allah ya isa mugu azzalimi sai na rama duk abunda kamin kuma na fasa zama a gidan NAKU." Ta k'arashe maganar muryar ta na karkarwa. Hakkim ya sake ta ta fad'i a gurin aikuwa da sauri ta mike zata zunduma da gudu General yayi saurin rike hannunta tamau!! Sai ta soma lauyewa zata fad'i kasa Hakkim ya kalla dake k'okarin shiga gida yace." Zo ka d'auke ta ka shiga da ita ciki Aminatu fitinar ki tayi yawa." Ya fada cike da kosawa. Kukan da take boyewa ne ya kwace mata,kafin kaga Abu yasa ta kuka zaka dad'e. Sosai take kuka General ya tsuguna yana rarashinta ta tubure ita baza ta koma cikin gidan ba kawai ya barta ta tafi gidansu.


Umarni ya bawa Hakkim ya d'auke ta ya shiga da ita, babu yadda ya iya ya tattare hannun rigar sa ya fara kokari d'aukar ta ta dinga kawo masa duka da ya kushi yana ji ya naga ni ya sab'ata a kafad'a suka nufi cikin gidan. Ladidi ta dunga dukansa bayansa da gwiwar hannunta tana cizo da ya kushi gami da yi masa Allah ya Isa, shi ko duk yana jinta yana jin kamar ya jefar da ita a gurin amma babu halin yin haka tunda umarnin dady ne. Shi kansa General ya ji haushin abunda yarinyar take yana ji kamar ya kaude ta da mari yarinya me baud'ad'an hali in ka taro ta can sai ta baud'e ta tafi wani guri. Lallai yanzu ya soma ganin halinta.


Tsakiyar parlor ya aje ta ya juya ba tare da yace da kowa komai ba ya fuce daga parlor. Hjy Asiya ta k'araso inda Ladidi take tana rarrashinta tare da tambayar ta abunda aka yi mata, kuka kawai take taki cewa komai. General ya kalli Hjy Asiya tare da fad'in" kunna mata kallo ki sanya mata film na fad'a." Aikuwa da sauri ta kunna tv India film ta d'auko ta sanya a DVD film din fassarar Hausa ne na jarumi akshey kumar,,, kafin mintu goma film ya fara d'aukar zafi can na hango ladidi ta warware ta kamar ba itace take kuka da turje-turje ba ta zubawa TV ido tana kallo fuskar ta a sake har ta manta da guduwa gidan mai koko.

Hjy Asiya ta kalli mijin NATA tare da girgiza kanta tace." Anya kuwa yarinyar nan bata da matsala a kwakwalar ta."?

Numfashi ya sauke ya zauna gefan ta yace." Lafiyan ta lau wallahi kin San wasu yaran haka k'uruciyar su take sai sun girma sannan hankali yake zuwa Kansu kuma kin San dama dab'iun mutanan k'auye dana birni ba d'aya suke ba."

Tace." Ko dana ji iya sanina dai babu abunda akayi mata Wanda zai tunzura zuciyarta da har zata ce zata gudu gida, domin shi Hakkim ma tunda ya futa d'azu be shigo parlor ba balle in ce ko shine tunda da shine basa shiri."












*BINTA U ABBALE*
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

*🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚*
*🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀*







~*NA*~
_BINTA UMAR ABBALE_
*BINTUBATULA👄*



*MARUBUCIYAR*

```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```TSANTSAR BUTULCI```

*LOADING:*

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login