Showing 45001 words to 48000 words out of 48145 words
Tana mamakin irin Uwar 'kibar da yayi ya 'kara haske abunshi.
Had'a ido suka yi shi da ita, yaji gabansa ya fad'i! Ta maza yayi ya maze yana danne zuciyar sa yace." Kauce ki bani hanya." Harara ta watsa masa kana ta matsa daga bakin 'kofar.
Futa yayi niyyar yi ya sanya 'kafarshi dake cikin takalmi sahu ciki ya take mata 'kafa cike da mugunta.!
Aiko tsigar jikinta ta fara mi'kewa ta fara jin wani irin jiri 'kara ta 'kwala!! Ta zube a gurin tana fuzge-fuzge! Ihun 'karar ta ne ya dawo da shi parlor sai ya tadda ita a kwance 'kasan tayel su General sun rufu a kanta suna yi mata tofi ita kuma sai fuzge-fuzge take wata irin kumfa na futowa daga bakinsa.
Dariya abun ya bashi amma ya dake ya 'karaso gurin yana le'kenta aikuwa ta zaburo! Da sauri tayo kansa.! Cikin jarumta ya tsaya a gurin Hajiya Asiya cikin tsoro take fad'in"Ka futa da sauri! Maza! Ka futa Kaine basa son su gani." Cike da mamaki! Yace." Momy su waye."?
*10/12/2019*
*BintuUm@rAbb@le*
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
*πππLADIDIπππ*
*π§ββπ§ββπ§ββK'WADAGAπ§ββπ§ββπ§ββ*
~*NA*~
_BINTA UMAR ABBALE_
*ZAMANI WRITES*
*ASSOCIATIONπ€π»*
___________________
```We are here to educate motivate and entertain our readas```
____________________
*DEDIGATED*
*TO*
*RAHIMA ALIYU*
*ABUJA*
```BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM ```
*π
Ώ43*
Kafin ya rufe bakinsa Ladidi tayi wani yun'kuri inda ta buge General da yake tsaye a kanta yana tofa mata addu'a duk da tazo bakinsa, kan Hakkim tayi gadan-gadan!
Ganin da gaske take tayo kansa zata d'afe jikinsa da sauri ya buga tsalle yayi gefe guda cike da al'ajabi abunda yake faruwa tabbas Yarinyar aljanu take yi domin dai duk lafiyayan mutum ba zai dinga wannan buge-bugen ba.
General yaje ya dauki wayarsa da sauri! Ya kira wayar Malam yace." Maza yazo babu Lafiya to da yake gidan malam din babu nisa dasu minti goma ya shigo cikin parlor yasan tunda aka kirashi abun ya ci tura, kan Ladidi yayi dake kwance tsakiyar parlor tana wani irin matagugu kumfa na futa daga bakinta ga idonta duk ya jirkice gashin kanta ya ya mutse! Duk me imani a lokacin sai ya tausaya mata, Hakkim dake tsaye bakin 'kofa yaji ta bashi tausayi babu shakka aljanu iri-iri ne akwai masu taimako akwai kuma mugwaye ya lura wadanda suke kan Yarinyar mugwaye ne sosai ta bashi tausayi ganin yanda duk hallitun ta suka jirkice
Malam na rike hannun ta guda ta nitsu ta daina abunda take yi. Addu'a ya fara tofa mata a jikinta da fuskarta tsawon minti ashirin suka ji wata irin murya na magana.
"Ka bari! Bama so kana takura mana damu da jaririyar muuuuu."! Malam yayi gyaran murya ya fara magana kamar haka.
"Kunce bakwa so ayi muku addu'a kuma kun'ki ku rabuda yarinyar nan ta samu Lafiya yanzu me ya kawo Ku ko kuma kun manta da al'kawarin da kuka daukar min na cewar zaku k'yale Yarinyar nan tayi rayuwar ta kamar yanda kowa yake yi."
Cikin sha'kakkiyar murya suka ji ance "Mu ba laifin mu bane ga mai laifi can."! Duk suka juya suna kallo Hakkim dake tsaye bakin 'kofa yana cike da mamaki ana magana da Aljani a cikin gidansu lallai dady ya dauko wa kanshi masifa.
Malam yace." Dole kuyi hakuri dashi tunda yayanta ne kuma Dan gida ne don dai baya gari ne kwana biyu Idan kuma kunki hak'ura tom ni zan 'kona Ku komai yawan Ku baku fi k'arfin ayar Allah ba."
Wani irin siririn kuka suka ji ladidi tana yi tana sha'kewa sannan suka ji wata irin murya ba irin ta d'azu ba tana magana kamar haka
"Kada ko 'kona mu domin mune garkuwa a jikinta mu musulmi ne kuma muna tsare ta daga sharrin jinshi mu masu cutarwa muna so kujawa Jariri kunne ya futa daga sabgarmu da ta jariryarmu domin kullum muna kusa da ita muna bibiyar lamuranta shiga hankalin sa damu babu ruwan sa damu."!!!
Malam yace." Kuma babu ruwan Ku dashi kuma kar Wanda ya sake ya ya kulla masa wani sharrin a cikin wallahi sai na 'kone shi kurmus!
Shiru na tsawon minti biyar babu Wanda yace komai Ladidi suka gani ta fad'i a gurin rigib! Bacci mai nauyi ya dauke ta! Malam ya mike tsaye yana kallon general da yake kallon Ladidi cike da tsananin kauna da tausayin ta, hak'ika da yana da yanda zai yi da ya cire mata wad'annan kafuran aljanun da suka dame ta suke wahalar da ita gami da hanata sakewa sosai yake tausayawa Yarinyar a rayuwar sa.
Malam yace." Yana da kyau Ku kula kuma ku kiyaye abunda zai bata mata rai mussaman kai." Yafad'a yana kallon Hakkim dake tsaye bakin kofa yana mamakin al'amarin.
Ya cigaba da cewa"Kaji 'korafin su akanka yake don haka ka kiyaye abunda zai sa su kusanto jikin yarinyar har ta kaisu ga bata wahala irin wannan domin ni daku Duk mun san cewa Jinnu ba karya bane kuma wadanda suke jikin yarinyar manya ne yana da kyau a kiyaye 'bata mata rai ko kuma ayi mata abunda bata so insha Allah ni nayi alk'awarin duk sai na rabata da mugwayen cikinsu da izinin Allah."
General yace." Insha Allah za'a kiyaye kuma dama ta kwana biyu basu matsoba wannan ma tsautsayi ubangiji Allah yayi mana tsari dafa sharrin su."
Malam yace." Ameen yana kokarin tafiya ne general ya Ciro kudi masu yawa ya bashi da kyar ya karba yana fadin"Shi ba don kudi yake taimakon yarinyar ba kwai yanayi ne don Allah. General din yace." Shima ya sani kyauta akwai ya bashi, cike da girmama juna suka yi sallama.
Sosai general yayi wa Hakkim fada kan ya futa daga sabgar Ladidi ko don gudun abunda ka iya zuwa ya dawo, to shima Hakkim din nashi 'bangaran ya fahimci komai kuma yanzu ya gane cewar duk abunda Ladidi take yi ba yin kanta bane junnu ke sata yayi alk'awarin futa sabgar ta har abada tunda dai shi dady din yaji ya gani zai riketa a haka Shikkenan Allah ya taya shi rik'o.
Ladidi bata farka daga bacci ba sai kusan daf da magariba sannan ta farka jikinta duk ya mutu ko ina nayi mata tsami tunda taji ta farka da mugun ciwon kai tasan tayi iska!!! Tana share hawaye ta mike ya shige d'akinta Wanda aka mallaka mata a gidan, zama tayi gefan gado tana kuka domin itama har ga Allah ta tsani wannam abunda take yi don dai babu yanda zata yi ne addu'a take cikin ranta Akan Allah ya yaye mata.
Ko da Hjy Asiya ta futo daga daki taga babu ladidi a parlor nan ta fahimci ta farka daga bacci kicin ta shihe kawai tana girgiza kanta gefe guda Kuma tana tausayawa yarinyar da irin tata kaddarar.
Ladidi kuwa ruwa ta hada mai zafi tayi wanka duk Dan taji dadin jikinta ta fito daure da alwala ta shirya tsaf ta futo parlor lokacin babu kowa sai ta zauna kan kujera tana jiran kira sallah magariba
Salim ne ya shigo parlor ya ganta ita kadai yace"Menna 'yan mata ta gidan Yusuf bada kanki a sare."
Hararasa tayi ta dauke kanta shi kuma yasa dariya yana fadi'n komai abunki Yusuf zaki aura." Ita dai shiru tayi masa shi kuma ya shigeta yana cigaba da tsokanar ta har Hjy Asiya ta futo daga kicin. Tace"Sarki tsokana kazo zaka dame ta ko."?
Yace." Shigowa ta. kenan wallahi Mama yau ina Salima take ne tun safe ban ganta ba." Hjy Asiya tace"Ta yini gidansu kawarta amma dai yanzu tace min tana kan hanya."
Hakkim ne ya shigo parlor yana sanye da JS a jikinsa sunyi masa kyau sosai ya taje Lafiya yar suman kansa Salim yace"Yauwa broh zo ka bani tsaraba ta da kayi min alk'awari." Hararasa Hakkim Yayi har ya 'karaso tsakiyar parlor ganin Ladidi a zaune sai juya daining ya nufa yana ya mutse fuska.
*16/12/2019*
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
*πππLADIDIπππ*
*π§ββπ§ββπ§ββK'WADAGAπ§ββπ§ββπ§ββ*
~*NA*~
_BINTA UMAR ABBALE_
*ZAMANI WRITES*
*ASSOCIATIONπ€π»*
___________________
```We are here to educate motivate and entertain our readas```
____________________
*DEDIGATED*
*TO*
*RAHIMA ALIYU*
*ABUJA*
```BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM ```
*π
Ώ44*
Zama yayi kan kujerar daining Hjy Asiya ta futo daga kicin ta ganshi fuska ta saki a nutse tace "Dama yanzu nake shirin aikawa a kira ka domin d'azu naga ba wani abincin kirki kaci ba."
Murmushi yayi a hankali yace."Ni kam na koshi mama kar ki ce sai naci wani abunci yanzu cikina zai fashe." A shagwabe ya fad'i maganar.
Ladidi dake zaune a can parlor tana jinsu tab'e bakinta tayi tana mamakin sa gotai gotai dashi yana shagwaba a ganinta shirme ne.
Hajiya Asiya tace"To Shikkenan bazan matsaba maka ba ai cikin Kane yanzu dai bani labarin domin dai tun d'azu nake tsumayin ka."
Hakkim ya lumshe idonsa da ya tuno da Sarah yace." Mama nayi budurwa fa kuma insha Allah ita zan aura domin na yaba da d'abi'unta."
General ne ya karaso gurin Hajiya Asiya tace"Yawwa ga dady nan ayi maganar dashi amma dai gaskiya naji dadin wannan al'amari.'
General yaji duk abunda suke tattaunawa amma bai ce musu komai ba cin abincin sa kurrum yake.
Hajiya Asiya tace"Dady kanajin mu fa da Hakkim ka'ki cewa komai." A nutse yace." Allah ya sanya alkairi Abdul girma yazo." Dariya hakkim yayi yace."Dady da wuri fa nake so ayi komai a gama."
General yace." Ai babu matsala ni Zan sanya ayi min bunkice kan Yarinyar Allah ya kaimu lokacin."
Hakkim yaji dadin hadin kan da ya samu gurin mahaifin nasa ya San kuma ko da yayi bunkice ya samu labarin cewar Sarah tubabbiya ce bazai hana auran ba sanin halin dady nasa Yana da saukin kai da bawa kowa damar za'bar abunda yake so.
******
Yau kwanan Hakkim uku da dawowa kuma tun ranar da abun ya faru bai kara shiga harkar Ladidi ba wani sa'in ko parlor ya shigo ya tadda ita a zaune a futa yake yi saboda Sam baya bukatar abunda zai hadashi da ita, To itama Ladidin nata 'bangaran hakane kwata-kwata idan yana guri bata sake wa a gidan shiyasa duk sanda taji motsinsa a parlor bata futowa har sai ya futa.
Yusuf ya dage fa da gaske yake yi shi son Ladidi yake general yasan da maganar haka ma mahaifinsa duk sun San da maganar shi dai general har yanzu bai ce komai ba yana dai kallon yanda Yusuf din yake shige da fuce a gidan da yanda yakewa Ladidi hidima suttura iri-iri wani ma ba na 'kasar bane ga k'atuwar waya ya siya mata.
Hakkim kam kallonsa yake yana mamakin sa da irin ibtila'in da yake so ya d'aukowa kansa yarinyar da take da tawagar aljanu a kanta itace zai aura lallai Yusuf yaci kai.
Shi kam Yusuf ya matsawa dadynsa dole yazo ya nema masa aure gurin general hakanan yazo a lokacin ne kuma general din yace." Ya bari tukkuna zai je ya nemi izini daga gurin iyayenta domin shima ba a bashi damar ya aurar da ita ba, Mahaifin Yusuf yace." To hakan yayi idan ka tashi tafiya sai muje tare." To da wannan suka rufe maganar.
Hakkim yaso ya zuga Yusuf kan ya fasa auran Ladidi a cewar sa tana da girka girkan jinnu watarana yana ji yana gani zasu dame shi. Yusuf Yayi nisa a kaunar Ladidi yace ko bishiyar kuka ce a kanta shi yaji ya gani.
Hakkim dariya yake masa yanayi masa kallon Mara hankali. Tunda mahaifin Yusuf yazo wa da dady wannan maganar yasa kansa cikin damuwa tabbas tsakanin Hakkim da Yusuf a gurunsa daya ne amma idan San samu ne shi kam yafi so Hakkim ya auri Ladidi saboda yanda Allah ya zuba masa kaunarta cikin zuciyarsa dole yayi wani abu akan lamarin.
*18/12/2019*
_BintuUm@rAbb@le_
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
*πππLADIDIπππ*
*π§ββπ§ββπ§ββK'WADAGAπ§ββπ§ββπ§ββ*
~*NA*~
_BINTA UMAR ABBALE_
*ZAMANI WRITES*
*ASSOCIATIONπ€π»*
___________________
```We are here to educate motivate and entertain our readas```
____________________
*DEDIGATED*
*TO*
*RAHIMA ALIYU*
*ABUJA*
```BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM ```
*π
Ώ45*
Salima da Ladidi ne zaune a parlor suna hira lokacin Hjy Asiya tana kicin ita da mai aikinta Hjy Asiya Lemo ta had'a na zob'o tsaf ta kammala ta sanya a frji baito mai aiki ta hau gyara gurin ita kuma ta futo daga kicin din.
Ladidi duk jinta take yi a takure a gurin sakamakon shigowar dodon ta Hakkim Wanda yake magana da Salima.
Ganin zaman da take gurin bashi da amfani yasa ta mike da sauri zata bar gurin. Cikin bada umarni yace." Ki koma kiyi zaman ki ni futa zanyi ban ga dalilin da zai sanya idan kin ganni a guri sai ki ke damun kanki wannan zai nuna wa mutane cewar kamar wani abun nai miki."
Ladidi ta wuce shi kawai ba tare da ta koma ta zauna ba, Salima ya kalla yace." Kin gani ko Yanzu idan dady zai gani zaice nine nake takura mata.
Salima tace"Nima fad'an da nake mata kenan cewar ta dinga sakewa da kowa kai din ma yanzu ka gane bata da lafiya duk abunda take yi"
Hakkim yace." Ni tuntuni dama na fahimci yarinyar tana da matsala ni kam yanzu babu ruwana da ita bare aljanunta su tashi ace nine."
Salima tasa dariya tana fadin"Ni kaina yanzu na daina jin tsoro Wallahi da ne dai nake jin tsuro idan suka tashi."
Ta'be bakinsa yayi ya zauna kan kujera tare da fafine"Je ki kawo min abunci yunwa nake ji." Salima ta mike da sauri ta nufi kicin.
Ladidi kuwa na cikin dakin zugum tayi kan gado tana tuno fuskar Hakkim yanzu take ganin kyawunsa sosai taji zuciyarta na masa wani irin so cikin zuciyarta tace"Allah yasa dady yace ya aure ni da naji dad'i."
Ita kadai take zancan zuci kafin ta kwanta kan bed din tana lumshe ido cike da soyyayr Hakkim din.
****
Daddare bayan sun gama dinnar General ya kallesu a nutse yace." Zamuje kano 'kauyan d'an kunkuru zamu je mu dubo su Mai koko bayan haka kuma zan mu nemi izinin daga gurin waliyyin Aminatu."
Hakkim yace." Dady Allah ya sanya alkairi ni kam bazan samu zuwa ba."
General yace." Dole sai kaje baka da wani uziri da zaka kawo min na yarda dashi."
Sunkuyar da kansa yayi yana sakin dariya,Salima da Salim kam murna suke yi zasu je gidan gona, Ladidi kam babu Wanda ya kaita farin ciki sunkuyar da kanta tayi cikin jin dad'i.
Hakkim ya dinga mamakin ta sau kusan hudu suna hada ido dashi sai tayi saurin kauda kanta tana sakar masa murmushi abun ya daure masa kai sosai daga k'arshe sai ya fara tunanin ko aljanunta ne zasu motsa tashi yayi daga gurin yana tsaki a zuciyarsa yace." Haka kurrum ki dinga dariya kamar wata shashasha, waje ya futa ya zauna kan wata irin kujera ta huta waya ya futo da ita ya kira Rabin ransa Sarah,
Ladidi kuwa haushi taji da ya tashi daga gurin tana jin dadin kallon kyakyawar surarar shi da muryarsa mai dadin sauraro ikon Allah ita kanta mamaki take yi lokaci guda Allah ya Dora mata sonshi da kaunar sa.
****
Washe garin ranar suka shirya tsaf harda Yusuf suka tafi *Kano ta dabo timbin giwa kano ko dame kazo an fika!*
Tun mota Ladidi take murna da dariya Hakkim nayi mata kallon Mara hankali lokaci lokaci yana jan tsaki mussaman Idan yaga irin rawar jikin da Yusuf yake yi a kanta. Shifa dan dady ya matsa masa ne da babu abunda zai sanya ya hada tafiya da Mara hankali sunan da ya sata mata kenan.
Mai koko na zaune a tsakar gida tana sauraron redio kawai Ladidi ta fad'o gidan babu sallama tayi kan Mai koko tana ihu!
Iya ta mike zaune da sauri tana murna da farin ciki sai shafa jikinta take tana mutsika idonta fad'i take "Yau wa nake gani a gabana Ladidi na ce ta zama babbar mace kai Alhmdullahi Allah nagode maka Ashe dai zan sake ganin ki Ladidi ta Mai kok...... Kafin Iya ta rufe bakin ta Ladidi ta fad'i a gurin tana turje-turje! sai burgima take yi a tsakar gida wata farar kumfa na futowa daga bakinta, hakan yayi dai-dai da shigowar su Hakkim gidan general yayi kanta da sauri hat suna buga karo da Mai koko wace take ta faman salati da sallalami! Hakkim Yusuf Hajiya Asiya Salima da salim duk suna tsaye suna kallon ikon Allah.
*22/12/2019*
_BintuUm@rAbb@le_
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note