Showing 42001 words to 45000 words out of 48145 words

Chapter 15 - LADIDI KWADAGA

Start ads

24 Aug 2025

73

Middle Ads

har Momyn ta Hjy Asiya..... General ya fara tofa mata dukanin addu'ar da tazo bakin sa. Ya kai
Kusan 30minutes tsugune gaban Ladidi yana tofe jikinta da addu'a, sannan ta bude idon ta, gami da yin wata irin mik'a! Ta mike zaune zumbur!
Kuka ta fashe dashi tana waige-waige a gurin. Su din dai ta gani a tsaitsaye sun zuba mata ido.
Take kukan ta ya kara k'arfi tana nuna kafarta duk bakinta yayi mata nauyi so take tayi magana amma ta kasa.

General ya fahimci ta dawo dai-dai sai ya fara kokarin daukar ta cike da tausayin ta, domin ya lura aljanun da suke kanta manya ne sosai Dole ta kasa motsa jikinta.

Jiki babu k'wari su Hjy da Salima suka bi bayan general Wanda ke rungume da Ladidi a jikinsa ya nufi cikin gidan da ita.

Hjy da Salima Dan babu yanda zasu yi da sun hana general shigar musu da Ladidi gida saboda tsaro , Salima tsoron mutum me aljanu take.


Kan kujera ya aje ta ya kara k'arfin AC ya kalli Hjy Asiya tare da fad'in ki hada mata ruwan ka tayi sai taci abunci."

Hajiya Asiya ta wuce kicin jikinta duk babu k'wari, ita kuwa Salima zama tayi ta k'urawa Ladidi ido babu abunda take tsoro da fargaba sai dare domin tasan Dady zai ce Dole sai ta kwana d'aki daya da Ladidi.


Kamar me k koyon magana tace"Zan sha ruwa."
General da kansa ya nufi furji ya dauko mata ruwan gora mai sanyi bayan ya bude murfin ya mik'a mata.
Tunda ta kafa kanta kan robar ruwan bata d'ago ba sai da ta shanye shi tas! Sannan ta jefar da robar hade da yin wata shegiyar gyasa lumshe idonta ta fara yi, tuni ta b'ingire a gurin nannayaun bacci yayi gaba da ita.

General ya saki ajiyar zuciya ganin bacci ya dauke Ladidi ya mike yana niyyar barin gurun, da sauri! Salima ta mike hade da rike rigar shi ta baya tana tafiya tana waiwayen Ladidi.
General ya juyo yana kallonta da murmushi a fuskar sa yace." Na lura dake da Momy taki tsoron Aminta kuke yi tun d'azu naga sai zare ido kuke yi."
Salima tace."Wallahi Dady da gaske tsoran ta nake ji, yanzu haka jikina a jike yake ban San sanda futsarin tsoro ya kuffe min ba." Dariya general yasa yace." Ho Salima sarki tsoro ki daina jin tsoron Aljan babu abunda ya Isa yayi miki Wanda Allah bai miki shi ba, ke kike da makamai a hannun ki, kina fara karatun ayatul kursiyo sai gudu." Salima tace"Duk da haka dai Dady wallahi tsoro nake ji, mu kam Big broth ya jawo mana, Dady kana jin abunda fa aljanun suke cewa zasu masa, wai sai sun dauki fansar abunda yayi mata."
Murmushi general yayi a lokacin da suke taka steps yace." Duk abunda suka yi masa shi ya jawo kanshi babu ruwana. " cikin Salima ya karta!!! Cike da tsoro tace"Please Dady ka basu hakuri don Allah kar su tab'a mana bro." Salima iya Gaskiyar ta take magana. General kam dariya yake mata sosai har suka hau sama, ko wanne ya shige dakin shi.

Hajiya Asiya na futowa daga kicin taga parlor babu kowa Sai Ladidi a kwance kan 3sitar wata irin fad'uwar gaba taji, da sauri ta fara hawa step ta waiwayen Ladidi dake kwance

General ta samu zai shiga bathroom tace"Yallab'ai gashi ruwa har yayi zafi kuma naga tana bacci a k'asa. " Yana kokarin shiga toilet din yace." Ai bacci shine samun nutsuwar ta, ki k'yaleta tayi kar Wanda ya tashe ta, sai ta tashi Dan kanta. "

Hajiya Asiya ta zauna bakin gado tana al'ajabin wannan Abu.


******

Hakkim kam ya manta da wata Ladidi don Ku da suka gama waya da Dadyn sha. Ya fada masa tayi dogon suma bai damu ba, shi tunda ya bar k'asar shikkenan, suje su k'arata su da suka daukota.

Wasu had'andun gidaje ne company da suke wa aiki ya raba musu kyauta, plate uku ne shi d'aya Salmanu d'aya Bash d'aya, gidane me girman gaske babu abunda babu na more rayuwa swimming shi kanshi uku ne da gurin motsa jiki uku gurin wassanin yara iri-iri a gurin. Yanda company ya basu gurin zasu iya yin aure su tare da iyalinsu zaman america har a bada su da iyalinsu.
Tofa Bash tun da suka je ya samu sake wa ya fara sha'anin shi da 'yan mata kala-kala, shi kuwa Salmanu baya Neman mata amma fa shaye-shaye babu irin Wanda baya yayi, Bash kullum da daddare yana night club, sai dare ya raba yake dawo wa gida, wataran Salmanu yana binsa yaje yayi kallo ya dawo gida a buge.

Hakkim ya rasa yanda zaiyi musu kullum Cikin yi musu masifa yake sai dai suyi masa dariya kawai suna fadin "Har yanzu kanshi a tukunya yake bai san yaya duniya take ciki ba.

Tunda suka Isa garin na america yau kwanaki takwas kenan wayoyin sa suke kashe, yau ta kama Sunday babu aiki duk suna gida yace bari ya kunna wayar tasa, dama saboda fad'an Dadyn d'insa ya kashe wayar ya San dai yanzu ya huce fushin sa.




*24/11/2019*




*BINTA U ABBALE*
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

*🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚*
*πŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€K'WADAGAπŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€*



~*NA*~
_BINTA UMAR ABBALE_




*ZAMANI WRITES*
*ASSOCIATION🀝🏻*
___________________
```We are here to educate motivate and entertain our readas```
____________________





*DEDIGATED*
*TO*
*RAHIMA ALIYU*
*ABUJA*




*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*





*πŸ…Ώ40*





Ko da General yaga kiran wayar Hakkim kin dauka yayi. Hajiya Asiya ta shigo ta same shi zaune ga waya nayi tace"Dady kana ganin kiran waya fa." Yace." Ki dauka in zaki dauka yaron ki ne sai Yau ya ga damar tunawa damu. " Hajiya Asiya ta dauki wayar tana fad'in "Ni kam zan dauka mu gaisa dashi." Hararata general yayi tare da fadin" Ke akan 'yaya bakya jin kunya ai." Dariya tayi ta d'aga wayar, b'angaran hakkim kuwa jin muryar Maman shi sai ya saki fuska cikin shagwaba yace." Mama Duk kun manta dani ko? Sai da na gaji don kaina na kira wayarku babu Wanda ya kirani yaji ya na sauka lafiya." Hjy Asiya tayi 'yar dariya tare da fad'in"Nasan kana cikin koshin lafiya my son, duk laifin ka ne, kaje ka sumar da yarinyar mutane ka gudu yanzu inda bata dawo nutsuwar ta ba me zaka ce umm? Don Allah ka rage zafin zuciya myson." Yace." Momy daga taimako sai ace na sumar da ita, ni wallahi da zaku bi tawa da Ku mai da yarinyar nan domin Zata jawo muku masifa." Hjy ta kalli gen dake kallon TV tana jin tsoron kar yaji abunda hakkim din yake cewa, da sauri ta katseshi ta hanyar fadin"Kai ka fiye Abu myson babu wani Abu insha Allah." Yace." Shikkenan tom ni dai babu ruwana inanan." Dariya Momy tayi tana tambayar sa aikinsa yace." Alhmdullahi Momy komai ya kammala muna aiki har sun bamu gurin zama. " Momy tace"Tom Allah ya taimaka yayi jagora ." yace." Dady ne."? Gashinan zaune." Yace." Yawwa bashi wayar mu gaisa. " general ta mik'awa wayar ya karba a nutse suka gaisa dashi ya tambaye shi aiki kamar yanda Momyn shi ta tambaye nan yayi masa fatan alkairi sannan suka yi sallama.

****
*K'auyan d'an kunkuru*

Tunda Ladidi tq bar K'auyan Dan kunkuru hankulan jama'ar garin ya kwanta kowa ya sake yana rayuwar su nan suka k'ara tabbatar wa da cewar Ladidi annoba Ce a garin, wasu kuwa fad'i suke ai Mai koko ta tura Ladidi birni domin tayi iskanci ne wasu kuwa saboda jahilci cewa suke yi ai Mai koko da D'alha sun siyar da Ladidi saboda su hutawa da masifa kowa da abunda yake cewa. D'alha ya samu aiki a cikin birni sai ya daina sana'ar sai da d'ata da gobe yana zuwa cikin gari yayi sati d'aya biyu uku ya dawo gida, Mai koko kuwa har yanzu tanan tana sana'ar kokon ta, tayi kewar Ladidi ta gaji wani lokacin in ta tuna da ita har hawaye take yi tana tunanin ko a wane hali take ciki oho, gashi D'alha baya zama amma tayi alk'awarin wannan dawowar in yayi dole zata turasashi ya kai ta inda Ladidi take ta ganta.


****

Yau watan Ladidi biyar a abuja za kuso kiga yanda ta sanja tayi wata kiba mai ban sha'awa farar fatar ta ta murje, duk wannan ramar babu ita sumar kanta ta futo sosai domin har tafi ta da, sai dai ko da wasa bata bari a tab'a mata kanta da sunan kitso duk ranar da akayi tsautsayin tab'a kan kuwa aljanunta sai sun buge ta yini suke yi Abu d'aya dole sai an kira malamin dake tsaye a kanta yazo yayi mata addu'oi sannan suke gusawa ta kwana tana bacci sai don kanta ta tashi.
[11/28, 9:34 AM] BintuUmarAbbale Shiyasa suke taka tsantsan da abunda zai bata mata rai indai tace bata son Abu to Dady zaiyi ta fada kar ayi mata shi, lokacin general ya sanya Yusuf dake gari ya nemo mata makaranta mai tsada akayi komai da komai general da kanshi yake kai ta ya dauko ta duk da cewa akawai direbobin sa kusan uku, shi dai bukatar sa Aminatu ta samu nutsuwa, cikin ikon Allah da taimakon Liman Ladidi ta samu ta nutsu ta daina shirme da shiririta yanzu kallo ma bai dame ta ba kullum in ta dawo daga makaranta suna tare sa Salima tana nuna mata abunda bata gane ba.
Yusuf dake shirin kai kud'in aure yaji duk duniya babu yarinyar da yake so kamar Ladidi yana mamakin asitaccan kyawun ta don a k'auye ta ke ne shiyasa komai ya b'uya, sai ya zamana bashi da gidan zuwa sai gidan su Hakkim yana fakewa da cewa yazo gaishe da General ne, nan kuwa Ladidi yake karewa kallo dukaninsu basu gane ba, lokacin suka yi wata irin sha kuwa da Ladidi itama in bata ganshi ba ta dinga cigiyar sa kenan..... Yusuf ba kullum suke waya da Hakkim sai jefi-jefi domin wani lokacin shi hakkim din bashi da time kullum suna aiki yafi samun sakewa Duk weak end sai su sha hirarsu a waya yayi ta tsokanar sa cewar ina bagidajiyar budurwar sa, shi kam Yusuf dariya yake yana fadin "Na wuce babinta yanzu na sanja wata zukekiya zan turo maka hotonta ma ka gani." Hakkim mamaki yake sosai yace."Yanzu duk irin son da kake wa Naja'atu ka daina kalli ka cika mayaudari." Yusuf dariya yayi yace." Na samu wata wacce ta fita komai da komai akan me bazan rabu da ita ba." Tsiya Hakkim yake masa yace ." ka turo min inga hoton yarinyar da ta rusa gwamantin Hafsa a zuciyar ka." Yusuf Yace. " zan turo maka amma ba yanzu ba." Haka suka yi sallama cike da barkwanci da kaunar juna.







*28/11/2019*





*BINTA U ABBALE*
*🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚*
*πŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€K'WADAGAπŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€*



~*NA*~
_BINTA UMAR ABBALE_




*ZAMANI WRITES*
*ASSOCIATION🀝🏻*
___________________
```We are here to educate motivate and entertain our readas```
____________________





*DEDIGATED*
*TO*
*RAHIMA ALIYU*
*ABUJA*




```BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM ```





*πŸ…Ώ41*





A takaice dai sai da Hakkim yayi shekara guda sannan ya dauki Hutu ya fara shirye-shiryen zuwa gida Lokacin ya kara wani kyau da waye wa.... Ya fara soyayya da wata Aboki yar aikinsa 'yar Ghana Sarah kenan tun da taga Hakkim ta kwallafawa ranta shi. Tun Yana share ta har dai yaji ta kwanta masa da ya fuskanci tana da nutsuwa da kamun Kai sam bata iya shirme irin na 'yan matan ZAMANI ba. Yaji zai iya auranta ko don kyawawan haleyen ta. Ganin ya dauki Hutu yasa Sarah itama ta dauki Hutu a rana daya suka tafi filin jirgi sukayi sallama da juna kowa ya nufi kasarshi cike da kewar juna.


Labarin zuwan Hakkim gidan yayi mugun d'agawa Ladidi hankali domin mata mance dashi ba s gidan sosai yanzu ta tsani abunda zai sake hada ta dashi ko da can ma rashin hankali ne amma yanzu ji take bata da babban makiyi kamar shi.... Duk taki sakewa a gidan Sai nukufurci take yi, Cikin su babu Wanda ya fahimci abunda take wa fushi Hjy Asiya dai hankakin ta ya tashi tana jin tsoron kar aljanu su buge ta domin duk ranar da ta tashi da fushi da nukufurci yini take tana tayar da aljanu sai an dauki malamin ta sannan suke gusawa, sai ta samu mijinta tayi masa maganar.


General yace." Na fiki damuwa da zuwan Abdul saboda nasan abunda zuwansa zai haifar tunda kina gani tunda aka fara zancan zai zo take fushi ki duba ki gani tafi wata biyar iskar ta bata tashi ba, nasan idan ba'ayi wasa ba zuwan sa zai haifar da matsala."


Hjiy Asiya cikinta ya d'uri ruwa domin tana masifar jin tsoron iskokin Ladidi kala-kala suke hawa suke sauka kuma ko wanne idan yazo da budirin sa yake zuwa domin akwai ranar da ta fara tun k'arfe goma na safe basu sake ta ba sai goma na dare akwai wani Wanda ya hau yace a cikin daran nan aje a samo masa k'adangare mai kala hudu har da fad'ar irin kalolin kamar haka
*1 bulu*
*2 shanshanbale*
*2Yalo*
*3 Orange*

Take Hjy Asiya ta fahimci ko wane k'adangare yake nufi guduwa tayi d'akinta ta bar general yana ar tabu dasu... Cikin daran ya kira Malamin dake mata tofi yazo sannan fa suka gusa tayi ta bacci kamar mattaciya ta tashi a jeme duk tayi rama abun tausayi.


General yana bala'in tausayawa rayuwar yarinyar marainiyar gaba da baya tarin almutsutsai sunyi kaka gida a jikinta fatan shi ma Allah yasa su barta tayi aure.


Kwantar mata da hankali yayi yace." Duk wani Abu da kika San zata gani hankalin ta ya tashi sai ki guje shi kuma shima Hakkim din ki ja masa kunne sosai ni kaina sai na gargade shi kan yarinyar babu ruwan shi da ita." Hjy Asiya ta mike jikinta duk babu kuzari Salima kuwa tafi kowa rud'ewa a gidan.

****

Shi Hakkim da ake abun domun shi Sam ya manta da wata Ladidi soyayyar Sarah ta mantar dashi wata 'ya mace don haka da kuzarin sa ya sauka a k'asar tashi ta gado, fuskarsa cike da fara'a ya rungume Dan uwansa Salim da yazo daukar shi. B'ata fuska yayi yace." Bro me ya hana Dady zuwa daukana ne kamar yanda ya saba."? Salim yace." Wallahi kwana biyu yayi zazzab'i shine fa jikin NASA bai yi kwari ba har yanzu... Suna kokarin shiga mota Hakkim din yace." Shine ni saboda an raina ni aka ki fada min." Salim na driving yace." Am sorry bro laifina ne."! Kafadar sa ya buga yace." Zan hukunta ka kuwa." Salim yasa dariya yana bashi hakuri yace." Bro ka kara girma da kyau ba kamata yayi ka kawo mana big aunt. "!!! Hakkim yayi murmushi hade da fadin" kar ka damu tanan zuwa insha Allah." Salim yace."Alhmdullahi dama dady yana ta so yaga baby's a gaban shi." Cikin barkwanci Hakkim din yace. "Kai ka fara kawo masa baby's din mana." Salim yace." UmUm!!! Ai Kaine babbana." Dariya suka sa a tare cike da nishadi to a haka suka isa gida Cikin farin ciki da kaunar junan su irin na 'yan uwanta ka.







*5/12/2018*





*BintuUm@rAbb@le*
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

*🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚*
*πŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€K'WADAGAπŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€*



~*NA*~
_BINTA UMAR ABBALE_




*ZAMANI WRITES*
*ASSOCIATION🀝🏻*
___________________
```We are here to educate motivate and entertain our readas```
____________________





*DEDIGATED*
*TO*
*RAHIMA ALIYU*
*ABUJA*




```BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM ```





*πŸ…Ώ42*






Hajiya Asiya ta tari Hakkim cikin kulawa da 'kauna irin ta uwa da d'anta, a parlor suka zauna ta cika gaban shi da kayan ciye-ciye birjik yace." Momy wannan delicious din duk ni kad'ai lallai kinyi kewa ta da yawa."

Cikin jin dad'i tace"Dole my son nayi kewar ka sosai shekara guda ai dole in tar'be ka da muhimanci."

Dariya yayi yace." Momy nazo miki da labari mai dad'i fa." Tace"Masha Allah gama cin abincin ka bani na sha." Murmushi yayi ya fara cin abincin sa cikin nutsuwa.


Salim yace." Momy ni kin manta dani kenan." ? Tace" Ka bari tukkuna ya kammala sai kaci sauran." Cikin shagwa'ba yace." Momy ni bazan fi sauran ba sai kace wani al'majiri." Dariya suka yi masa dukanin su.


Hakkim ya kammala cin abuncin ya dauki tissue ya goge bakinsa ya kalli Momyn sa yace." Wai ina dady ne."? Tace"Yanzu zai shigo yaje d'auko Aminatu a makaranta. " Cike da mamaki yace." Momy wacece Amina da har dady zai je d'auko ta a makaranta."?


Ganin yanda ya 'bata fuska yasa Momy gyara Fuskar ya tace"Ladidi nake nufi ba ka dawo gidan ba tom babu ruwan Ka da ita don ba cikkakiyar lafiya ne da ita ba, don Allah kar ka shiga harkan ta."


Jin ta ambaci sunan yarinyar da ya tsana duk duniya yace." Momy har yanzu baku maida yarinyar gida ba."? Tace"Wane gida kuma? Karma ka sake Dadyn Ku yaji wannan maganar daga bakin ka zai 'bata maka rai! Nima kaina abun sai ya shafe ni."


Babu walwala a tare dashi yace." Momy kan yarinyar nan wallahi zan iya koma wa inda na futo nifa kallonta bana son yi wallahi."

Salim yace." Aikuwa zaku yi fad'a da Yusuf domin budurwar sace Wallahi ka iya bakin ka." Hakkim ya kawo hannu ya gwa'be bakin Salim d'in ya goce da sauri yana dariya.


Tsaki yaja cikin 'bacin rai yace." Yusuf bai da hankali wallahi ko meye abun so jikin 'kanjamammiyar irin wannan mtssss." Salim Yace. " sanin da kayi mata a da kenan, amma Yanzu indan ka ganta zaka sha mamaki."


Mi'kewa yayi yana fad'in"Momy ni zan je in kwanta in huta zuwa anjima." Tace"To my son sai ka futo." 'Kokarin futa yake yi General ya shigo parlor Ladidi na bayan sa tana sanye da kayan makaranta.


Baya ya matsa yana fadin "Dady barka da shigowa." Hannu general din ya mik'a masa suka yi musabaha kana yace." Dady na same Ku lafiya."? General yace." Lafiya Lou Alhmdullahi ya aiki? Ka samu lafiya kaje ka samu guri kayi Uwar 'kiba mu kuma nan ka barmu da zan can Ka."

Dariya yasa yana Sosa kansa yace."Dady ban in na kira wayar ka baka d'auka ."

General d'in yace." Kai kasan dalilina ai kuma ka kiyaye babu ruwan ka da yarinyar mutane." Yafadi maganar babu alamun wasa a tare dashi.

Yace." Dady ka kwantar da hankalin ka ni da wuri zan koma ma." Ciki general d'in ya shiga yana fad'in"Wannan kuma Matsalar ka ce ni dai na fad'a maka."

Ladidi ta 'kura masa ido kurr!

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login