Showing 6001 words to 9000 words out of 48145 words

Chapter 3 - LADIDI KWADAGA

Start ads

24 Aug 2025

59

Middle Ads

hannu aiki za'ayi mata,, Dan Fulani na kuka da rokon Allah ya sanya hannu Labaran ma ya sanya, to tun kafin a shiga da ita ta rasu,ganin cikin na motsi yasa suka shiga da ita cikin gaggawa aka Ciro yarinya mace, mai kama da uwarta.


Cikin halin damuwa nurse ta futo ta sanar dasu halin da ake ciki, sosai suka shiga rud'u da tashin hankali daga bisani suka hak'ura suka barwa Allah, suka karb'i gawar Amina suka tafi domin yi mata suttura, mai koko na rungume da jaririya tana kukan zuciya.



*****************

Mai koko ta d'auki son duniya ta Dora shi kan Amina da taci sunan mahaifiyar ta, dama kafin su baro asibitin sun duba ta sosai ko itama tana d'auke da ciwon sikila, Allah mai yadda ya so yarinya lafiyanta Lou sai dai k'ankanta, amma inda ans bata madara me kyau zata murmure.

Malam Labaran bai yi shawara da kowa ba yaje ya sanya gonar shi a kasuwa nan take aka samu mai siya kasan cewar gonar tana da kyau kuma tana da fuska akayi ciniki aka bashi kudinsa, ya nufi asibitin cikin gari duk abubun buk'ata ya siyowa Amina ya siyo mata madara masu kyau, da kaya niki-niki ya shigo gidan, Hurera tai yi mamaki sosai nan ya zauna ya warware mata komai, tace"Malam da kayi shawara dani da baza ka siyar da gonar ka ba" yace"Saboda haka shine mafuta asurinmu ya rufu, Kinga madarar nan tana da tsada idan ba haka ba bamu da kud'in siya, kuma ko d'aukar me shayarwa mukayi dole mu biyata, tace"Hakane kuma to Allah ya rufa mana Asiri,, nan Hurera ta kara k'aimi gurin Sana'a har ta kafu da sanar Koko da safe,, shi kuma D'alha yake sana'ar sai da D'ata goba da mangwaro asirinsu na rufuwa,, Dake ranar lahadi aka haifi Amina yasa Mai koko take ce mata Ladidi shikkenan mutane suka rike suma suke kiranta da Ladidiya,, shekararta uku a duniya Allah ya amshi ran Malam Labaran ciwon kai tafarar daya,, Mai koko nauyi ya kara yi mata yawa, dake jaruma ce, sam bata karaya ba, ta cigaba da neman kud'inta, da kanta ta kai Ladidi makarantar allo tun tana da shekaru hudu,, tana zuwa cikin yara zaka ji gurin ya kaure da kuka Ladidi Duk ta doke su, har wad'anda suka girme ta dokansu take,,Malami ya doke ta tayi masa Allah ya Isa,aikuwa ya dawo wa da mai koko ita yace"Tana hana su karatu in taje dokan yara kawai takeyi ta hanasu karatu gashi in an doke ta tayi Allah ya Isa shi kam bazai iya ba" Mai koko tace"Kaje ai ba kai kadai bane me makaranta na kai ta wata, sai da akayi wata shida tukkuna sannan ta kaita wata makarantar nan ma bata canza zani ba,, tana zuwa makarantar karatun yara ya lalace domin duk gurinta suke komawa suyi ta wasa duk tsawan da malam zai musu basa jinsa. Nan ya fahimci zuwan Ladidi ne jawo haka, tunda da yana iya tankwara su, aikuwa sai ya ware ta a cikinsu in tayi futina yaci ubanta, ita kuma ta zage shi, gashi duk dukan da za'ai mata bata kuka sai dai idonta yayi ja, malam da yaga ba zai iya ba ya tattarata ya mayarwa da mai koko ita,, abunda ta fadawa malamin farko haka ta fada masa,, shekara guda bata zuwa makaranta, sai wasa da yawo kusfa-kusfa D'alha bai tab'a Ankara ba, dake da wuri yake futa baya dawowa sai gab da magariba, ya dawo ya wuce ta makarantar Allo yaga an tashi yana ta daga kai yaga ta inda Ladidi zata b'ullo bai ganta ba, sai yayi tunanin ko ta tafi gida, yana tafiya ya hangota kan katangar wani gida ta mike tsaye tana ta tafiya tana k'yalkyala dariya kanta babu d'ankwali, sai diddigagen gashinta da kwarkwata ta cinye rabi ta bar rabi, duk k'wanta nan burjik!! Kira ya kwala mata"Ladidi"!! Da sauri ta juyo jin muryar Kawunta ta hantsilo k'asa ko a jikinta ta mike da gudu tayi gida,,, girgiza kai yayi ya bi bayan ta.

Sosai ya dunga fad'a Mai koko tace"Ai sai ka d'auke ta ta kaita da kanka ko wace makaranta aka kai ta sai su koro ta saboda tsabar bakin ciki sun tsani marainiyar Allah" Yace"Halin ta ne ya jamata zan kai ta, wata makatanar da kaina Wallahi da kaina zan dunga hukunta ta" Shiru mai koko tayi masa ya gaji ya shiru, ita ko Ladidi na bayan ta tana zumb'ura baki gami harare-harare ta tsane shi tunda kullum cikin takura mata yake. Washe gari da safe D'alha ya sa ta a gaba suka nufi makaranta ya damk'a ta a hannun Malam yace"Gatanan yayi mata hukunci in tayi laifi, kuma ya kula da karatun ta."






*COMMENT VOTE AND SHARE*
[9/24, 10:29 PM] 8k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

*🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚*
*🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀*




*NA*
_BINTA UMAR ABBALE_
~*®BINTUBATULA👄*~



*MARUBUCIYAR*

```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```TSANTSAR BUTULCI```

_*LOODING:*_
_*{LADIDI K'WADAGA🌚}*_




_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_

_______________________
```We are here to educate motivate and entertain aur reades```
_______________________



_*DEDIGATED*_
*TO*
_RAHAMA ALIYU_




_*KU SONI TA ZARCE💝💝💝 NIMA NA NASO KU TA ZARCE❣❣❣IN HAR KUKA KUFCE! 😡😡A KANKU NI ZAUCE! 🤢 IN KUNJI😍😍*_
😃😃😃😃😄😄😄😃

I will always saying thank you to my people love you so much,, muna tare insha Allah😘




*🅿6*




D'alha ya kama hanya yai tafiyar sa, gurin sana'ar sa, tunda malam yayi mata gurin zama cikin yara take ta faman zabga masa harara sosai yayi mamakin yarinyar ko da yake dama yana da labarin ta sosai,, sai ya d'auke kansa kawai yayi kamar bai ganta ba,, ya cigaba da koyar da yara, yarinyar dake kusa da ita ta zura hannu ta mintsina yarinyar ta fashe da kuka, Sai tayi saurin cire hannunta tana kallonsa yana kallonta,, ya gane itace yarinyar ya kira da hannunsa, gurin zama yayi mata,, Ladidi taji haushin haka, tayi shiru tana zumb'ura baki, lokacin tashi nayi yayi musu addu'a duk suka mike sai ta d'auki takalmi wata ta b'oye, to yaga lokacin da ta d'auka, murmushi yayi ya kira yarinyar ganin tana kuka, Ladidi ya kira, taje tai masa k'erere aka yace"Bata takalmin ta" Zumb'ura baki tayi tace"Baya gurina fa" "Naga fa sanda kika d'auka kika b'oye bata kinji ko,, ni nasan kyautar da zanyi miki" Shiru tayi yace"Zan baki alawa" Aikuwa sai ta futo da takalmi da ta b'oye kasan zaninta ta jefawa yarinyar, da sauri ta d'auka ta sa, ta kalle shi, kai tsaye tace"Bani alawar" yace"Dama ba karatu kika zo ba" ? Daga kai tayi" yayi murmushi yace"To don Allah kiyi karatu ki nutsu kinga Kawun ki ya kawo ki kiyi karatu nayi miki alk'awarin bazan Doke ki ba kamar yarda ya fad'a" baki ta tura tace"Ko ka dake ni ba zafi zanji ba" dariya yasa yace"Nasan da haka ai,, shiyasa ma bazan tayar da hankalina ba". "Ni dai bani alawa ta" fad'a tana Sosa kanta,, Hannu ya zura cikin aljihun sa ya ciro Alawa guda biyu yace"Kullum nayi miki alk'awari zan dunga baki mutuk'ar zakiyi karatu in kin zo makaranta kuma zaki nuttsu ki daina tsokanar "yan uwan ki" Karb'ar Alawar tayi tayi tafiyar ta, ta barshi da baki a sake, girgiza kai yayi ya d'auki allon nata yana dubawa, duk girman ta, tana Alam tarakaifa. Wanda basu kai shekara goma ba ma sun shiga sabbi,, ita tana zaune, haka kawai yake tausayin yarinyar, yana fa yara guda biyar duk kamarta shiyasa in yaga yara na k'uruciya yake musu addu'ar shiriya Wannan shine silar zaman Ladidi a makaranta ko tayi nufin tsokona ko gudun makaranta sai ta fasa saboda alk'awarin alawar da Malam Salihu yayi mata, shi kuma kullum baya fashi, ana tashe zai bata,, gashi Yanzu tayi nisa a karatu ta kusa izu d'aya. Babu laifi tana gane wa.

*WANNAN SHINE TOSHEN LABARI*



Da Asubah D'alha ya futo da niyar zuwa massalaci, da cocilan a hannunsa yana haskawa, sai ya ga Mai koko na k'okarin saukowa daga bainci da alama itama tashin ta kenan, Cikin mamaki ya tsaya yana kallonta yace"Iya me kike anan"? Shiru tayi masa ta mike tana Sosa jikinta, yace"Da alama nan kika kwana meye dalili"? Cikin b'acin rai tace"Wannan ja'irar yarinyar ce ta rufe min k'ofa jiya babu yadda banyi ba ta bude min amma tak'i"D'alha mamaki sosai yake yace"Tak'i bude miki k'ofa me makon ki min magana shine zaki kwanta a soro cikin sauro Iya sai kinje zazzab'in cizon sauro ya kama ki"? K'okarin shiga cikin gidan take tana fad'in"Kai dai magana ta wuce, ai kayi tafiyar ka" Gyad'a kai kawai yayi ya wuce yana mamakin son da Iya takewa Ladidi wannan son shi a ganinshi cutar wa ne, domin shi yake k'ara lalata yarinyar. Har yaje massalaci yan sak'e-sak'en hukuncin da zai d'auka kan Ladidi domin ko me Iya zatayi sai ya doke ta ya rantse. Bayan an idar da sallah sun futo,, Halliru mai Fura ya tsaida shi suka gaisa,gani yayi Halliru na sha masa kunu yace"Malam Halliru lafiya ko" ? Halliru ya sauke ajiyar zuciya yana fad'in"Idan kaji kira daga mai gari kar kayi mamaki" Cikin mamaki D'alha yace"Me ya faru" Rai a b'ace Halliru ya kwashe duk abunda ya faru ya fad'a masa,, innalillahi wa'innailahi raji'un shine abunda D'alha yake ta Nanatawa yace"Don girman Allah Halliru kayi hak'uri wallahi in banda ka fada min ban san abunda yake faruwa ba, itama Iya ina tabbatar maka da cewar bata sani ba kayi hakuri don Allah kar ta kaimu ga zuwa gurin mai gari, wannan tonan asiri ne"


Halliru ya sha kunu yace"Inyi hakuri kamar yaya? Kana nufin in zauna bani da abinyi kome? Na fada maka fa yarinyar nan duk jarina ta rusa kaje ka tambayi Mutari me nama zai fada maka komai" D'alha ya kwantar da murya yana fad'in "Duk baza ta kaimu ga haka ba,, yanzu ya kake so ayi" ? Kai tsaye D'alha yace"Kawai mu raba asara Ku bani dubu biyar ni nayi muku lamani" D'alha ya tsaya yana tunani daga bisani yace"Shikkenan insha Allahu zamu San abun yi ka kwantar da hankalin ka"

Halliru ya saki fuska yana fad'in "Shikkenan sai na jika"
Sallama sukayi kowa ya kama hanyar gida.

Lokacin da ya isa gida, Mai koko na tsaye gaban wata k'atuwar tukunya da duguwar muciya a hannunta tana ta aikin motsa koko ga kwanuka har an fara layi,, kai tsaye d'akin ta ya nufa, sam bata yi tsammanin dokan Ladidi zai yi ba,, sai ihun ta kawai ta ji da sauri ta jingine muciyar ta shiga dakin da sauri,, tana fad'in "Au!! Dama dokan ta ka shigo kayi ko D'alha? Can na hango Ladidi k'arshen gadon k'arfen Mai koko sai ihu!! Take kurmawa babu ko k'wallon hawaye, D'alha ya zage k'arfi yana ta labta mata bulala,ya ki cewa komai,, Tace" Shikkenan kashe ta tabi iyayen ta, tunda kak'i ka saurare ni" yana haki! Yace"Da kin san abunda yarinyar nan tayi to da kin bani gudumawar abun duka" Cikin fushi tace"Kome tayi bazan bada abun duka a illata ta ba, ni dai nace ka daina dukanta in dai ni na haife ka" D'alha ya yar da abun dukan yana haki! Cikin b'acin rai yake warware mata abunda ya faru, sosai itama ta jinjina al'amarin, amma don k'arin abun haushi sai cewa tayi"Yo ai da ka k'yale shi yaje ya fad'uwa mai gari sai me, dan yaje, dubu biyar dai insha Allahu za'a bashi, ai k'imar mutum tafi kudi shi kud'i suka dama da zai zugo ka kazo kana dukan marainiyar Allah"
D'alha yace"Ko yau ta k'ara sai na doke ta, in ta kama ma in sa ta a mari sai in daure mata k'afafu sai inga k'afafun yawo"
"Tunda kai ai haka akayi maka sai ka daure ta magani" Mai koko tafad'a cikin takaici,futa yayi a fusace! Ta mai. da hankalin ta kan Ladidi dake ta faman sosar jikinta wani gurin har ya kwailaye, amma saboda dauriya da kafiya gami da jarumta ko kwalla babu a idonta k'ema gadas, sai da sunyi jajazuri! Tace"Kin kyauta kinji ko, aini kam bazan miki baki ba sai dai i n nema miki shiriya a gurin Allah idan kuma wani, shad'ainin ne yake sanya ki wannan Ibilicin to sai yayi magana mu sulhunta dashi, Allah ya bashi hakuri" tana gama maganar ta ta futa daga dakin domin ta fara jin hayaniyar yara a tsakar gida.


Ladidi ta jima kan gado Tana Sosa jikinta dole fatar ta kwaile mussaman cinyar ta duk tayi rud'u-rud'u da duka, saukowa tayi daga kan gadon ta d'auki zaninta ta daura. fuskarta a murtuke ta d'auki dakkaken gawayi wanda suke goge bakinsu dashi, ta futa tsakar gida,, can bakin rijiya ta nufa ta d'auki buta ta zub ruwa nan bakin rijiyar ta tub'e wandon ta tayi futsari, ta fara durzar bakinta da gawayi, ranta a mugun b'ace, duk yaran da suke mata magana tana jinsu tayi musu banza.

Al'wala ta d'aura ta shige d'aki, Ladidi duk k'injin ta tana sallah in lokacin ta yayi.Ko kwantawa tayi ta manta ba tayi ba, to lokacin ta nayi zata rama haka takeyi tasan lokotan ko wace sallahr farillah.


***************
***************

*FLORIDA*

Ta k'asar America,, had'and'un samari na gani zaune gurin shak'awa,, tsakiyar su lemu ka ne, masu sanyi da wani irin cin-cin wanda yaji madara da kayan had'i, suna ci suna hirarsu irin ta abokai, gefe guda kuma turawa ne suke ta sha'anin su, kai harda bak'ar fata ma, "yan k'asashe daban-daban kowa sai cin karansa yake babu mai damuwa da kowa, da yawa daga cikin su babu kayan arziki ajikin su, daga su sai wani tsinkakken wando wanda ya shige musu matse-matsi da tsinkakkiyar briziyya Wanda bata gama rufe musu nonowa ba duk gasu nan a waje, da gudu suke tsalle suna fadawa cikin ruwa suna dariya. Hakeem ya d'aga kansa yana kallon su,, fuskar sa a had'e yace" Dube su don Allah banzaye dasu sai nuna tsaraicin su suke, ashe dama abunda ya sa ka dame ni kenan kana so kazo ka kalli tsaraici, abunda Allah ya hana, haka kawai ina zamana cikin rufin asiri ka takura min sai nazo mun futa d'an iska kawai" Dariya Bash yasa yace"Kai don Allah fad'i gaskiya dai Yanzu ganinsu bai d'ebe maka kewa ba?, nifa wallahi dama da biyu nazo gurin nan,, so nake kafin mu koma in bawa idona hakkin sa" Cikin taikaici Hakeem yace"Kai wannan ya dama Wallahi nifa in ga mace cikin hijabi yafi min mutumci nama fi jin sha'awar ta akan in ga tsaraicin ta, don Allah tashi mu bar gurin nan" Ya fad'a yana mik'ewa tsaya,, mik'ewa Bash yayi yana fad'in"Ka dai fad'i gaskiya malam wa zaka nunawa ustazanci" banza yayi masa ya fara tafiya, wata beb ce ta futo daga cikin ruwa da gudu, daga ita sai d'an mitsitsin wando babu ko brziyya ta d'anshi, babu zato suka fad'i k'asa.









*COMMENT VOTE AND SHARE*
[9/25, 5:40 PM] 8k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

*🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚*
*🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀*




*NA*
_BINTA UMAR ABBALE_
~*®BINTUBATULA👄*~



*MARUBUCIYAR*

```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```TSANTSAR BUTULCI```

_*LOODING:*_
_*{LADIDI K'WADAGA🌚}*_




_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_

_______________________
```We are here to educate motivate and entertain aur reades```
_______________________



_*DEDIGATED*_
*TO*
_RAHAMA ALIYU_



_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_



*🅿7*




A mutuk'ar fusace ya hankad'e ta ta fad'i k'asa ya mik'e tsaye da sauri, cikin zafin zuciya! Ya damk'o wuyanta ya dunga rafka mata marika, lafiyyayu. Da sauri Bash ya k'araso gurin gami da fuzge yarinyar daga hannun shi yace"Lafiyan ka kuwa hana Hakeem, wannan wane irin zafin zuciya ne, ai tunda ka kawo kanka gurin nan kasan haka zata faru"' Cikin b'acin rai yace" Dallah Malam rufe min baki,kai me yasa ba tai maka ba sai ni? Saboda ni ta raina,ko an fad'a mata cewar d'an iska ne ni, kamar ka, da zata zo ta rungume ni" Yarinyar tana tsaye hannunta dafe da kuncin ta, sosai taji zafin marin da yayi mata, idanun ta sunyi ja sosai,, tace"Don nazo in jiyar da kai dad'i shine ka wulak'anta ni, a idon mutane,, kasan ni ko wacece kuwa"? Banzan kallo yayi mata yace"Rufe min baki ko in zo in k'ara miki wani, ko ke wacece bai dame ni, ke kika shiga gona ta, meye ruwan ki dani zaki zo ki samin najasa a jiki" Cikin takaici tace"K'arya kake kace bakasan mace ba, wannan idon naka da yake a bude, saboda kayi min yasa yana kusance ka" Cike da takaici ya kalle ta sama da k'asa yace"To ni bakiyi min ba, shashashar banza kawai baki da Abunda zaki rud'e ni dashi, ko kina musulma d'iyar Hausa Fulani kina aikata ashararan ci, ina jiran hukuncin da zakiyi,, Sunana Abdul Hakeem Abbas D'an kaka" Ya zura hannunsa cikin wandon jins d'insa ya ciro wani k'aramin kati ya wurga mata, yace"Wannan katin shi zai nuna miki duk inda nake, ina sauraron ki" yana gama fad'in haka ya bar gurin a fusace! Bash ya kalle ta, tana tsiyayar da hawayen bak'in ciki, girgiza Kai yayi baice komai ba ya wuce, cikin zuciyar sa yake fad'in "Baki san wanene Hakeem ba shiyasa kika aikata masa haka, ya san halin mutumin shi, da tsantse ni, baya son abunda zai had'a shi da wata mace mutuk'ar ba halalin sa bace.

Cikin mota ya tadda shi yayi cikin-kicin da fuska,, sai kad'a k'afa yake, yana zama cikin motar ya balbaleshi da masifa,, Bash yace"Wai Ubana ne kai da zaka dunga min masifa nafa gaji wallahi abu ya ruga ya faru sai magana ta wuce", "Ank'i a daina maganar ai kaine babban me laifi a gurina haka kawai ka takura min lallai sai naje gurin,, Bash yace" Da nasan abunda zai faru da ban gayyace ka ba, nasan yau yini zakayi kana tsine min" Tsaki! Yaja yace"Daga yau in zaka je yawon ka kar ka k'ara takura ni dole sai naje,, kaje kayi tayi kai tunda baza ka fasa ba" Bash yasa dariya yana fad'in"Angama ogana, wai ni don Allah in tambaye ka mana"? Ajiyar zuciya ya sauke yace"Ina jinka" . "Me yasa kullum kake takurawa kanka ne? Kace kallon mace ma baka so kayi inaso ka sani wannan tsantsenin naka ba shine zai tsare ka daga Abunda kake gudu ba, na lura fa kallon India film American film baka cika yi ba,, kafi kallon Hausa film mussaman na " yan k'auye

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login