Showing 18001 words to 21000 words out of 48145 words

Chapter 7 - LADIDI KWADAGA

Start ads

24 Aug 2025

67

Middle Ads

fasa miki shi,shashasha kawai!! Gum! tayi da bakin ta dama kukan babu hawaye sai dai ihu! Sai dai kana kallon idonta kasan tana cikin b'acin rai! Yarinya 'yar shekara goma sha biyu ta san d'aukar fansa, abunda take ta raya wa kenan cikin zuciyar ta Kawunta da d'an burni sai ta rama abunda sukayi mata. Mai koko ta kalleta ganin yadda take ta sauke ajiyar zuciya yasa ta sassauta murya tace." Yanzu ke kanki zaki ji dad'i kuma iska zata shiga kanki sosai kinga kin rabu da kwarkwata har abada,domin wani sabon gashi ne zai futo miki." Banza tayi mata. Kawu D'alha ya futa ya barsu a d'akin, Mai koko dai da taga tak'i kulata sai ta futa ta k'yaleta tana addu'ar kat Allah yasa ta b'ullo da wani abun kuma. Aikuwa futowa tayi babu d'ankwali a kanta nufi gidin rijiya, 'yan siyan koko suka bita da kallo, tuni wasu daga cikinsu suka fara futa waje cikin tsoro ganin kan Ladidi a cikin rana sai k'yalli yake, Mai koko tace." Ya kuke futa kuma kowa ya tsaya a sallame shi." Wani Yaro yace." Iya wacece wacan kamar Ladidiya ko." Iya ta kalli inda Yaron yake nunawa Ladidi ta gani da buta a hannu tana durzar bakin ta da dakakkaken gawayi kanta sai k'yalli yake cikin hasken ranar da ya fara futowa, cikin takaici tace." Ladidi ke ko kika futo babu Dan kwali ko kunyar k'awayen ki baza kyaji, ki koma ki dauro dan kwalin ki." Kuskure bakinta tayi tace." Daga yau na bar d'aura d'ankwali wallahi haka zan dinga yawo da kai na, kuma duk yaron da ya tsokane ni, inci Ubansa." Jiki a sanyaye Mai koko ta juya ta cigaba da abunda take cikin zuciyar ta take fad'in"Ba a rabu da bukar ba an haifi Habu,dama ni nasan wata futunar zata k'ara b'ullo da ita."
Tana gama Alwalar ta bar gurin. Wani tsohon buhu ta kwance nan kayan ta na sawa suke ta ciro wata doguwar riga irin ta kanti duk taji jiki dan wani gurin ma d'inkin ya soma zarewa gashi ta tattare sosai ta d'angale mata duk k'waurinta a waje ta saka, ta zura hijabin da take sallah ta tayar da sallah.Bayan ta idar ta tub'e hijab d'in ta aje shi kan gado, haka ta futo babu d'ankwali kai tsaye hanyar futa ta nufa, tunda ta doso gurin suka fara matsawa kowa na k'okarin ya bata hanya kar ta make shi, ball tayi da kofin Alawiyya dake bisa layi, Iya ta juyo da sauri tana fad'in." Kar Ku har gitsa layin fa.' Ladidi ta gani tana k'okarin futa,da sauri tace." Ina zakije a haka sai da nace ki d'aure kanki ke ku kunya ba kya ji." Ko kallonta ba tayi ba ta fuce abunta,girgiza kai kurum tayi ta cigaba da aikin ta tan addu'ar Allah yasa Kawunta na waje ya koro ta, aikuwa D'alha na tsaye da kayan sana'arshi suna gaisawa da mak'ocin su Yahaya,suka had'a ido dashi, sam bata tsorata ba. Ta fara k'okarin wuce shi,tsawa ya buga mata yana fad'in"Koma ki d'auro d'an kwallinki" Ido jazur! Ta koma ta cikin gidan, D'alha yayi sallama da Yahaya ya kama hanya ya tafi, lab'ewa tayi bayan k'yaure sai da ta tabbatar da yayi nisa sannan ta futo, tana ganin Yahaya yana gyara kwatar gidansa, ta galla masa harara, yana sunkuye bai sai abunda take ba, sai saukar Abu yaji a jikinsa, da sauri ya dago yana karkad'ewa sai ga tarkacan da ya kwaso daga kwata suna fad'owa k'asa, bayan rigarsa duk ya b'aci da kwata, waige-waige yake yana neman yaron da yayi masa wannan sha'ani, ido hud'u sukayi da ita, zabura! Yayi ya matsa gefe guda baki na rawa yace." Lad..ladid..katsaye shi tayi ta hanyar fad'in" Jiya har da kai gurin cewa na mutu har kuna shimfid'a tabarma da zama, to ban mutu, kuma duk sai na kashe Ku." Cikin Yahaya ya bada sautin kulululu!! Bakin sa sai motsi yake, zare masa manyan idonta tayi, ganin yanda yake gumi! ne yasa ta k'yalk'ale da dariya "hahahahahaaaa! fyallawa tayi da gudu ta barshi tsaye a gurin,saura kad'an ya saki futsari.
Cikin mutuwar jiki ya zauna kan dakalin gidansa yana sauke ajiyar zuciya,sai zare ido yake.


Babu inda tayiwa tsinke sai gidan gonar su Hakkim, tana isa ta tarar da an kewaye katangar da waya mai fasa k'afafu dan wani gurin ma har da k'ananun k'walabe, b'uya tayi wani gurin tana tunanin ya za'ayi ta shiga gurin. Can taji motsi an bude kofa, lek'awa tayi kad'an , d'an burni ta hango ya futo daga ciki jikinsa sanye da singlet da wando iya gwiwa 3quetar, suna magana da wani me wanki takalmi, tsura masa Ido tayi tana girgiza kai, a fili tace." Wannan girman jikin naka da wannan k'wanjin naka da wannan murd'ewar taka, duk baza su hanani in d'auki fansa akanka ba, hummm! Ko Kaine Singam gurin k'arfi sai na rama fasa min bakina da kayi." Tana kallonshi suka gama magana da me gyaran takalman ya koma ciki ba tare da kulle k'aramar kofar ba. Da sauri ta futo daga gurin b'uyan ta, kamar walkiya tazo ta shige ciki, Mai gadi nacan na fama da redi'o a hannu, wata bukka ta shiga ta b'uya Kansan kujerun hutawar dake ciki, tana kallonshi ya futo daga wani d'aki hannunsa ruk'e da takalma biyu ya kara futa waje, wuf! Ta futo daga farko inda take, ta afka inda taga ya futo, Sam had'uwar falon ba ya gabanta burinta kawai ta d'auki fansa, ba ta tsaya kalle kalle ba ta afka wani d'aki da tagani a bude, tana shiga ta fara zare ido motsin ruwa taji a band'aki, da sauri ta matse jikinta ta b'uya bayan gado. dama kar ku manta Ladidi bata da k'iba siririya ce sosai, Yusuf ya futo daga toilet yana goge jikinsa da towol, sauri sauri ya sanya kayansa. Ya tsaya gaban mirror yana shafa mai ajikinsa, Hakkim ya shigo d'akin hannunsa rike da takalman su an wanke su tas sai kyalli suke, Yusuf yace." Ka dame ni na tashi na shirya gashinan dai na shirya sai kayi sauri kaima." Zube takalman yayi a gefe guda, toilet ya nufa yana fad'in" Yanda kake da nauyin bacci idan ba haka nayi maka ba ai baza ka tashi ba." Yusuf yace.'' Son bacci da nauyin bacci har na kai ka." Shiru yayi masa ya shiga toilet din, shi kuma yana gama abunda yake ya futa farlor, Ladidi duk tana jinsu, tasan Hakkim ne ya shiga band'aki, futowa tayi daga inda take, ta zauna gefan gadon gami da tsurawa kofar band'ankin ido tana dakon futowar sa. Jikinsa d'aure da guntun towol ya futo cin yoyinsa duk a waje domin babu gajeran wando,a jikinsa dama da k'yar towol d'in ya ratsa masa jiki, yana futowa idonsa ya sauka a nata, tana zaune ta d'ora kafa d'aya kan d'aya, kanta sai k'yalli yake, sam! Bai gane ta ba, domin duk hattun ta sun sauya. Da k'arfi! Yace." Auzibillahi minashaid'anirrajim"!!!! Nan take ya fara karantun ayatul kursiyo, har yanzu idonsa na kallonta itama ta k'ura masa ido k'urrrr!!









*COMMENT VOTE AND SHARE*
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

*🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚*
*🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀*




~*NA*~
_BINTA UMAR ABBALE_
*BINTUBATULA👄*



*MARUBUCIYAR*

```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```TSANTSAR BUTULCI```

*LOADING:*
*{LADIDI K'WADAGA🌚}*




_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_

_______________________
```We are here to educate motivate and entertain our reades```
_______________________




*JAN KUNNE⚠*

_*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_





*DEDIGATED*
*TO*
*RAHAMA ALIYU*
~*ABUJA*~





_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_




*🅿16*



Cikin abunda bai fi second guda ba ya ganta a tsaye kan allon gado,kafin yace me ta buga wani tsallen ta sauka kan dressing mirror, tuni kayan shafa suka fara fad'owa k'asa suna fashewa,ta sanya k'afarta guda ta fara ball da sauran suna fad'owa kan 'yan uwansu, d'aya k'afarta tasa ta baya ta daki! mirror d'in ya tarwatse! Dura k'asa tayi ta tsaya gami da rik'e k'ugu! tana kallon sa. Hakkim kuwa jikinsa duk ya jik'e da gumi! Tamkar ba daga wanka ya futo ba, zuwa yanzu yasan mutum yake tare dashi ba aljan ba,saboda lokacin da take ball da kayan shafar sa ya kalli k'afarta,sosai ya tsorata da ibilicin wannan hallitan mace ko namiji domin dai ya kasa gane wani jinsi ne, k'aramin towol d'in dake rataye a wuyansa ya ciro ya goge gumin goshin sa, ya jefar dashi k'asa,rai a b'ace ya durfafi inda take. Tana tsaye turmin danya tana sauraron isowar sa, sam ya manta da kwalaben da ta fasha,kwalba ta caki k'afarsa me mugun tsini kafin kace kwabo jini ya fara zuba yana bin tayal cije baki yayi cikin azaba! Ladidi ta kwashe da dariya "Hahahahaha" tana nuna shi da hannu,d'ago kansa yayi yana kallonta,shan kunu tayi tace." Ni ce wannan yarinyar ta jiya daka doka na fad'a maka dama sai na rama,ko shugaban k'asa ne ubanka. Hehehhaaha." Ta k'arasa maganar tana mahaukaciyar dariya. Cikin tsananin fushi ya cire d'aya k'afar tashi da niyar d'amk'ota, k'afar ta caki! Wata kwalbar turare me tsini! K'ara! ya saki yayi taga-taga zai fad'i, da sauri ya dafe towol d'in jikinsa da yake barazanar fad'uwa k'asa, saboda sanin halin da yake ciki shi kadai ne a jikinsa, gwiwar sa ya sanya a gurin ya sanya hannunwa ya dafe k'asa sai cije baki yake, idonsa ya kad'a yayi ja, jini kuwa duk ya b'ata gurin. Kan gadon ta hau tayi tsaye tana kallonsa, Tace." Naji dad'i na rama abunda kayi min gaba ma sai ka k'ara dukana kaga abunda zanyi maka." Tana gama maganar ta ta dura k'asa, bude kofa tayi ta futa daga d'akin, Salima da Yusuf na tsaye harabar gurin suna jiran futowarsa kawai sai suka ganta ta futo,bagaz-bagan! ta wuce fuuuuu! tamkar zata tashi sama! Cike da tsoro Yusuf ya shiga ciki,Salima kuwa kin shiga tayi,domin ba k"aramin tsorata tayi ba, ita kam da tasan wannan masifar zata gani da bata biyo su, ba k'afafunta sai rawa suke ta nemi guri ta zauna,cikin zuciyarta take cewa gaskiya gurin nan akwai aljanu insha wata k'ila Dady bai sa anyi saukar alk'urani me girma a gidan ba. Cikin jarumta ya mik'e tsaye da sauri ya bi bayanta,yana jin in ya kama yarinyar nan to sai dai idan uwarta ta haifi wata domin har in bai kashe ta ba to sai yayi mata muguwar illah a rayuwarta, wani irin suka da azaba! Tafin k'afafun shi suke yana jin shigar kwalbar jikin jikinshi bai damu ba, bud'e kofa yayi a fusace! Suka ci karo da Yusuf ya shigo a razane! ganin fuskar Hakkim d'in babu rahama ko kad'an, yasa ya duburburce yace." Yaro wai meke faruwa ne,waye ya futa yanzu mace ko namiji? naga yaro ya futa yanzu, ina cikin rud'u fa,anya gurin nan babu aljanu kuwa." Shiru yayi masa cikin k'arfin hali ya nufi kofa da niyyar futa. Yusuf ya bishi da kallo yana kallo yadda yake Jan k'afa ga jini duk ya b'ata gurin, da sauri ya bishi ya dafa kafad'ar shi,yana fad'in." Wai ina zaka ne cikin wannan halin."? A hasale yace." K'yaleni malam." Yusuf yaje ya rufe kofar futa da key ya zura a aljihun sa, yace." Babu inda zakaje sai ka fada min abunda yake faruwa, yanzu fa na futo daga d'akin lafiya Lou amma dubi wani abun al'ajabi. " yace." Zo ka bude min kofa." Yusuf yace." Bazan bude ba wallahi." Wani uban naushi! ya kaiwa kofar da hannuwansa yana fad'in." Yusuf wallahi suma tallahi idan idona ya k'ara ganin yarinyar nan, to ina me tabbatar maka da cewar sai dai uwarta ta haifi wata,wallahi duk shad'aicin ta,sai naci ubanta sai na ragargaza ta, ni zatayi hakaaaaa."!!!!!! Salima na daga waje ta ji ihun Dan uwanta a tsorace ta fara buga kofar tana kuka, Yusuf ya bud'e mata ta shigo yayi saurin mai da kofar ya rufe, cikin mawuyacin hali taganshi tace." Babban yaya waye ya zubar maka da jini? Innalillahi wa inna ilahi raji'un." Sai ta kara rurucewa da kuka. Yusuf ya rasa ma abunyi yace." Yanzu dai muje hospital ayi maka dressing d'in ciwon nan,in yaso ko ma meye sai ya faru, ni wallahi kaina ya kulle ma." Salima tace." Ya Yusuf fada sukayi ne." ? D'aga mata kai yayi ya nufi bedroom domin dauko masa kaya, to duk irin tambayoyin da Salima take masa yak'i tanka mata, yana durkushe sai sakin ajiyar zuciya yake ta b'acin rai! Da cin alwashi kan Ladidi. Wata razananniyar tsawa! ya buga mata tare da fad'in "Tashi ki bani gurin idan na fada miki waye me zakiyi, ne kin dame ni." Salima ta mike da sauri taja gefe cike da tsoro take kallonsa ganin yanda duk hallitunsa suka sauya.







*COMMENT VOTE AND SHARE*
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

*🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚*
*🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀*




~*NA*~
_BINTA UMAR ABBALE_
*BINTUBATULA👄*



*MARUBUCIYAR*

```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```TSANTSAR BUTULCI```

*LOADING:*
*{LADIDI K'WADAGA🌚}*




_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_

_______________________
```We are here to educate motivate and entertain our reades```
_______________________




*JAN KUNNE⚠*

_*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_





*DEDIGATED*
*TO*
*RAHAMA ALIYU*
~*ABUJA*~





_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_




*🅿17*



Yusuf ne ya katse masa tunanin da take. Yace."Ka tashi ka saka muje hospital, ko sai na taimaka maka ne."? Da k'arfi ya fuzge! kayan da ya ke mik'o masa, ya mik'e da kuzari ya fara sanyawa zuciyarsa nayi masa zafi da radadin gami da takaicin abunda Ladidi tayi shuka masa. Yusuf yayi gaba yana fad'in." Bari in matso da mota kusa." Ko kallonsa baiyi ya fara d'ingisawa Salima tabi bayansa simi-simi.

Cikin gari suka futa suka nemi wani pravite hospital, nan akai masa dressing sosai suka had'a masa magunguna masu kyau da tsada, Wanda in yayi amfani dasu insha'Allah zai samu sassauci. Hanyar su ta dawowa suka tsaya suka siyi abubuwan da basu dashi, Salima ta kalli Yusuf a tsorace tace." Ya Yusuf nifa ina jin kwana biyu ko uku zanyi in koma gida wallahi tsoro nake ji." Yusuf ya fashe da dariya har da dukan kan mota yace." Nima ai munyi d'aya dake gaskiya tafiya zamuyi tsakanin jiya da yau mun sha fargaba mu da muka zo Hutu mun b'ige da jinya, ga tashin hankalin wannan yarinyar." Hakkim ya ja tsaki! yace." Wallahi babu inda zaku je,ni kadai na shirya tafiya ta,saboda gulma da munafurci kuka ce dole sai kunzo, mussaman ke." Ya fada yana kallon Salima da ta sunkuyar da kanta ya cigaba da cewa "har da kuka sai kinzo saboda haka dole ku zauna sai sanda naga damar tafiya sannan." Yusuf yace." Ni indai tani ne babu matsala Salima ce abun ji." Aikuwa ta marairaice fuska, Yusuf ya dinga mata dariya yana tsokanar ta da daddare zata ga Ladidi a kusa da ita tazo taya ta kwana aikuwa duk ta gigice. da wannan suka Isa, Hakkim ya futo daga mota yana kalle-kalle wai ko zai ga Ladidi,duk suka shige suka barshi a gurin, daga bisani ya bi bayansu yana d'in gisa k'afafu.



*********

Ladidi kuwa tunda ta samu ta d'auki fansar abunda Dan burni yayi mata sai kawai ta manta dashi da al'amuran shi ta cigaba da sabgarta.

Tafe take fakam-fakam da allo a hannunta ta cire d'ankwalin ta taci Uwar d'ammara dashi, tana sane ta cire ko wani zai tsokane ta ta samu na duka, bayan haka kuma tana so ta b'akantawa Kawun ta D'alha rai tunda ta lura baya so ya ga tana yawo babu d'ankwali, shi kanshi hijab dinta na hannuta, karo suka ci da Iliya dai-dai wani lungu,

Tun daga nesa yake k'unshe dariya, har ya k'araso daf da ita, taki kaucewa tamkar zasu bangaji juna, Iliya ya sha kunu ya d'an kauce mata tazo ta wuce, shima kamar zai wuce sai ya tsaya ya mik'a hannusa ya daki! kanta sosai yace.' Woooo k'waryar malo dama a namiji aka hallice ki domin kin fi kyau da maza!yana gama fad'ar haka ya runtuma da gudu yana dariya, aikuwa a sittin! Ta bishi da wani irin mugun gudu kamar zata tashi sama, yana gudu yana waiwayen ta,ganin ta kusa cimma sa yasa ya kara k'aimi!wani irin tsalle me had'e da gudu ta buga sai gata a gabansa,ba tayi wata-wata ba ta zura k'afarta k'arkashin tasa ta tad'o shi ya fad'i wanwar a gurin, ya yunk'ura zai mik'e, da sauri ta d'ebi k'asar gurin ta watsa masa a fuska, aikuwa ya saka ihu! Yana rintse idonsa, kamar walkiya ta bar gurin. Iliya ya dinga lalube yana ihu gami da mutsika idanunwansa k'asa sai gurin-gurin take masa a ciki ruwa ne kawai yake shatata da k'yar ya mike ya fara tafiya, aikuwa ya jishi cikin kwata tsumbul, yayi zaman 'yan bori, ya dinga salati yana neman d'auki.


*********
Yau kwanan so biyar a garin d'an kunkuru Hakkim ya warke tsaf, kullum cikin zuba ido yake yaga ko Ladidi zata kara dawo wa, shiru safe da yamma sai sun futa ganin gari cikin mota, ya dinga kalle-kalle kenan ko zai ganta babu alamunta, cikin zuciyarsa shi kadai yasan irin tanadin da yayi mata, Labarin abunda ya faru kuwa har su Dady sun sani domin Salima ta fada musu komai, Dady ya kira shi a waya tare masa fad'a kan ya kula kar ya k'ara dukan yarinyar kowa a garin shi kam baya son tashin hankali, amma ya Dade da sanin halin dashi mafad'aci ne sosai idan aka tab'o shi, tun yana yaro haka yake,amma fa in baka tab'o shi ba zaka jima dashi kuna mu'amula domin yana da saukin kai. Duk wannan gargad'in da Dady yayi masa yaji ne kawai amma yanda yaci alwashi kan yarinyar yana gani in bai dauki fansa a kanta ba ma kamar ya aikata zunubi ne.



**********
Yau Juma'a tun sassafe Mai

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login