Showing 9001 words to 12000 words out of 48145 words
nasu Rabilu Musa d'an Ibro, Allah ya gafarta masa" Kai tsaye yace"Saboda nasan yaya nake shiyasa nake takatsatsan da kallon abunda zai tada min da hankali" Murmushi Bash yayi yace"To wallahi gwara ma ka kadaina takurawa kanka ka tsaya ka mori k'urociyar ka, kallo ne kawai fa, ba aikatawa kayi ba balle kace kana da zunubi" Hakeem yace"Na lura k'aranci ilimin addini yana damun ka Bashir, mu bar wannan maganar, kada rayuka su b'aci don yanzu zan maka abunda bakai zato ba,, kai ma addu'a nake ma kullum Allah yasa ka gane, in sha'awa na damun ka in ka koma gida kayi aure kawai shine mafuta, domin a halin da kake ciki zaka iya fad'awa halaka" Bash yayi shiru yana tab'e baki, Shiko Hakeem driving d'inshi yake fuskarsa a had'e.
*WANENE ABDUL HAKEEM?*
Abdul hakeem Abbas D'ankaka, matashin saurayi ne d'an kimanin shakaru Ashirin da tara, yayi karatun sa na primary socndry a kano inda ya wuce America can yayi degree d'in shi fannin engineering,, sosai yake da brain inda wani company, nan k'asar America suka d'auke shi aiki ya amunce amma da sharad'in sai ya koma gida ya sanar da iyayen sa, bayan haka kuma sam bashi da ra'ayin zama k'asar saboda lalaewar ta,, mutum ne mai tsantseni baza ka gane haka ba sai ka zauna dashi, amma kallo d'aya kayi masa zaka d'auka wayyaye ne, kan holewa ta duniya saboda yana da bud'add'iyar fuska da iya mu'amula, da fara'a da barkwanci ga shi idanunsa a bude so ke ko yaya ya zauna da kai na minti goma zai fahimcin halin ka, wannan yasa mutane suke masa wani bahagon kallo, Ubangijinsa ne kawai yasan waye shi,
Sun had'u da Bash ne a company shima yazo interview, shine suke abota, tunda Bash yazo k'asar yake yawo gurare, yau sai da yaja ra'ayin Hakeem ya bishi haka ta faru. Bash d'an Sakwatto ne, iyayen sa da "yan uwansa duk suna can da zama,sab'anin Abdul Hakeem, da suke Abuja da zama amma asalinsa dan jahar kano ne.
General Abbas d'ankaka tsohon soja ne da yayi ritaya shekaru goma da suka wuce,, yana da mace d'aya Hajiya Hasiya suna da " yaya uku rak, biyu maza d'aya mace, Abdul Hakeem ne babba sai Salim sai Salima itace auta yanzu ta gama scondry tana shirin shiga jami'a, Salim kuwa saura shekara d'aya ya had'a HND d'insa , Salim da Salima kamar su d'aya,, suna kama da mahaifiyar su, da ta kasance shuwa fara ce tas sune suka d'ebo kamanin ta, shiko Hakeem Sak mahaifin sa, yana da duhun fata ba sosai ba, kalar fatar shi abun kallo ce, sosai suke girmama shi gami da bashi girmansa, suna gudanar da rayuwar su a tsare babu baragada komai cikin ilimi suke yi
************************
************************
Kwana da yini tayi bata kula Mai koko ba,kamar itace ta doke ta, Mai koko kuwa sai lallab'ata take tana botsarewa, dan kanta ta hak'ura ta daina fushin.... Tsayawa tayi kan Mai koko k'erere tace"Bani kud'in makarantar" ta kalle ta cike da takaici tace"Babu gaisuwa kawai kinzo kin tsaya min aka ina amfanin haka? Wai ke yaushe zakiyi hankali ne"? D'auke kanta tayi tana zumb'ura baki, girgiza kai kurum tayi ta d'auki wani gwangwani da take ajiyar kud'i ta ciro hamsin ta mik'a mata tana fad'in"Gashi ki d'auki goma ki dawo min da canji na" Karb'a tayi da sauri a zuciyar ta tace"Wallahi ko sisi bazan dawo dashi ba, ladan dokan da akai min" Mai koko tace"Allah ya bada me amfani don Allah banda tsokanar yaran mutane" Banza tayi mata ta futa fakam-fakam!! Tun a hanya ta siyi aya jik'akkiya da goro ba, na goma-goma ta kwance d'an kwalin ta ta kulle canjin talatin d'in,,, To yau ranar wanke allo ne domin a sauya rubutu, d'aya bayan d'aya kowa yake biya allon sa, in ya iya sai ya je ya wanke ya kawo wa Malam,, Da k'yar Ladidi ta biya nata Malam nayi mata gyara yace"Gaskiya ki bari sai wani satin sai ki wanke kafin sannan kin iya" hararasa tayi, tace"Ba gashi nan na biya maka, gaskiya ni sai na wanke kamar yadda kowa ya wanke" yace"Ban yarda ba fa" mik'ewa tayi da allon a hannuta taje ta wanke,, kallonta yake cike da mamaki yace"To yau kuwa Wallahi bazan baki alawar ba" Dariya tasa tace"Ka rik'e kayar ka yau ina da kud'in siya, ga gansu ma" tafad'a tana nuna masa inda ta daure, k'wafa kawai malam yake yana kallon ta tana wanke allo tazo ta aje gabansa ta wuce fud'un-fud'un tana fad'in "Kuma dole ai min rubutu". Malam addu'ar shirya kawai yake mata.
Tare suka jero da Alawiyya yanzu sun shirya basa fad'a, Alawiyya tace" Zo muje gidan muyi kallo, jiya babanmu da yaje burni ya siyo mata tv da vidio" Dariya Ladidi tasa ta daddaki kanta, tana fad'in "Da gaske kike "? Alawiyya tace" Wallahi" Ladidi ta rike hannunta suka kama sauri,,, aikuwa suna isa gidan suka tarar an kunna, yara sun cika gidan sai kallo suke, wani film ne singam fasarar Hausa, Ladidi tayi tsalle ta shiga tsakiyar su,, shikkenan guri ya hautsine daga wani yayi motsi zata buge kansa ta ce ya kare mata,, idan aka zo gurin fad'a, sai ta saka ihu! Ta mike tsaye tana gwadawa, inda tsautsayi ta buge na kusa da ita,, tuni kukan yara ya cika babarsu Alawiyya tace"Kai kashe kallon zanyi Wallahi ya daina dadi baka jin komai sai kuka" Ladidi ta rarrafa gurin ta rirrike mata hannu tana magiya kar ta kashe ta daina, da k'yar babarsu Alawiyya ta hak'ura ,, gurin fad'a kazo Ladidi ta kurma ihu!! Ta kalli Iliya dake zaune gefen ta, tace"Iliya don Allah ya sunan afton nan ya iya fad'a wallahi, hehehehe, kaji har wani take ake masa,, *kama b'arawo suburbud'e shi, sa shi a mota oga Singam!!!!* hahahahaha ta kwashe da dariya ta koma ta zauna tana sosa kanta jikin ta sai tsuma! Yake,, aikuwa yaran da suke gurin suka rud'u da fad'in *"Kama b'arawo suburbud'e shi sa shi a mota Oga Singam!!!!!!* babarsu Alawiyya ta dunga dariya tana fad'in "Ladidi sai dai idan baki zo guri ba, ubangiji Allah ya tayar miki da wannan k'uruciyar iya haka".
*COMMENT VOTE AND SHARE*
[9/26, 11:14 AM] 8k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
*🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚*
*🧟♀🧟♀🧟♀K'WADAGA🧟♀🧟♀🧟♀*
*NA*
_BINTA UMAR ABBALE_
~*®BINTUBATULA👄*~
*MARUBUCIYAR*
```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```TSANTSAR BUTULCI```
_*LOODING:*_
_*{LADIDI K'WADAGA🌚}*_
_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_
_______________________
```We are here to educate motivate and entertain aur reades```
_______________________
_*DEDIGATED*_
*TO*
_RAHAMA ALIYU_
_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_
*🅿8*
Sai wajan magariba sannan film din ya k'are, suka futo daga d'akin huuuuuuuu! Sun rud'e da fad'in *"Kama b'arawo suburbud'eshi sa shi a mota Oga Singam!!!!"* Ladidi ce shugabar su, in ta fad'a su fad'a,, haka kowa ya nufi gidan su yana wannan wak'ar da Ladidi ta k'irk'ira gurin kallo, da wak'ar a bakin ta ta shiga gida,, Mai koko ta bita da kallo cikin mamaki tace"Babu sallama sai wak'a Ladidi"! Dariya ta fashe da ita ,tace"Iya kin same"? Mai koko ta girgiza kai cikin mamaki,, "Wallahi wani film muka kalla gidan su Alawiyya me mugun kyau!! Gaskiya afton d'ab bala'i ne, uhmmm! Kin ga yanda yake suburbud'an " yan iska kuwa!? Ta k'yalkyale da dariya tana Sosa kanta ta cigaba da cewa"Iya nake fad'a miki har wani take ake masa,, saboda tsabar jarumta,, na tambayi Iliya ya sunan afton yace bai sani ba,shine na tsara masa wannan wak'ar. *Kama b'arawo suburbud'e shi sa shi a mota Oga Singam!!!"""* ta k'arashe wak'ar tana wata mahaukaciyar dariya, tamkar wata shashasha, Dariya Mai koko tasa tace"Aikam wak'ar tayi dad'i Ladidiya ta Mai koko,, ke dai kina son kallon hindiya" Ladidi ta dunga dariya taji dadin yabon da Mai koko tayi mata tace"Shiyasa ai nake so Kawu ya siya mana kayan kallo wallahi" Iya tace"Ke kin san bazai siya, nice zan siya miki amma sai kin nutsu kin daina shashanci da rashin ji gami da fada da maza" da gudu taje ta rungume ta tana Fad'in"Iya na daina insha Allahu, yaushe zaki siya mana" tace"Ki bari in d'auki a dashi na, zan siya miki amma fa sai naga kin nutsu". Ladidi tayi ta murna Iya tace"Kije ki yi alwala kiyi sallah, sai ki zo kici abunci" ta mike da saurinta sai farin ciki take Mai koko zata siya mata kayan kallo
*******
Zaune yake a cikin wani had'addan bedroom kana ganin tsarin shi kasan na hotel ne, wanda ya had'a abubuwan more rayuwa da jin dad'i kai daga nin tsarin hotel din kasan ba na k'ananun mutane ba, ko a american ma sai wane da wane,, waya ce a hannusa, magana suke da Dady d'insa Yace"Dady ina tafe a wannan satin insha Allahu" daga d'ayan b'angaran G.Abbas yace"Wace rana zaka zo kason ina son zuwa in duba gidan gona ta a Kano ko" Dariya Hakeem yasa yace"Dady har ka samu guri ka fara aiki bani da labari" ?Dady yace"Sai kazo zaka gani, guri mai kyau can wani k'auye ne,, k'aramar hukumar Ungwago,, gonaki hud'u na had'a a gurin, babu abunda ban dasa ba,, ga gurin kiwo da gurin hutawa, gurin ya tsaru sosai" "Kai Dady har ka kwad'atamin son zuwa wallahi, insha Allahu mun gama komai anan, sun bamu izanin tafiya, inan tafe ranar Monday" Dady yace"Sai ka zo,, ai tuni su Salim suka je suka ga guri" b'ata fuska yayi yace"Dady kayi min laifi" Dariya yasa, Hakkim ya cigaba da cewa"Nine ya kamata na fara zuwa na gani na sa albarka" Dady yace"Kai dasu duk d'aya ne, kasan don baka gari ne". "Na sani Dady ai in nazo can zan gudu inje in huta" Dady yace"Zakaji dadin hutawa kuwa domin gurin yayi". Hakkim yayi ta sa Albarka Dady yana amsawa da amin, sukayi sallama cikin so da kaunar juna Wanda Allah ya kimsa tsakanin iyaye da "yayansu.
******
D'alha ne ya shigo gida a gajiye,, Iya da Ladidi na zaune tsakar gida kan wata tabarma Duk ta zare ta zama saura, kibiya ce a hannun Iya tana tsefewa Ladidi kai sai mita take kan kwarkwatar dake kanta wacce tak'i jin magani Babban abun takaicin ma shine duk rabin kan ya cire wani guri da gashi wani guri babu,, ga uban amo sani da k'wan kwarkwata abun k'yank'yami,, tace"Wannan kan naki gwara kawai a aske shi kowa ya huta, ni kam ban tab'a ganin kwarkwata me naci ba,kamar taki" Zumb'ura baki tayi tana k'okarin fuzge kanta tana fad'in"Ita bata yarda ba aske mata kai,, cikin wannan halin D'alha ya same su,, ya zauna gefen Iya yana mai da nuffashi,, Iya tace"Sannu da alama ka shawo rana, Allah yasa nagama abunci" Girgiza kai kurum yake, yace"Wallahi kuwa, Iya talaka shine babban abun tausayi a duniyar nan,, raza zafi haka zaka futa nema wataran ma ka futa baka samo ba" tace"Sai hakuri ai, Allah dai ya bamu rabo me amfani" Ameen yace" mik'ewa tayi tana fad'in"Bari in kawo maka ruwa da abunci""" Kallon Ladidi yake cike da takaici yace"Don ubanki babu sannu da zuwa ko, kin iya zuwa ki karb'i kud'in makatanta babu fashi""" Hannunta ta d'ora kanta ta soso ta soso ta ciro kwarkwarta har guda biyu ta ajiye kasa ta sanya farce ta kashe, abunta,, yace"Ba magana nake miki ba"" kallonsa tayi babu tsoro tace"Kawu Sannu da zuwa " Tsaki yaja yana fad'in"Kazamiyar banza kawai" Iya ta zauna tana aje masa langa, me d'auke da Dambu na tsaki yaji gyad'a da alayyawu tace" Kayi mata addu'a mana k'uruciya ce" Kofin ruwa ya d'auka ya kai bakinsa sai da ya sha sosai ya aje yace"Iya nagaji da ganin wannan k'azantar ta kwarkwata, yanzu ina futa zan siyo reza ayi mata k'wal kwabo idan kwarkwartar taga babu gashi, tayi nata guri". Tace"Wallahi nima shawarar da na yanke kenan" Ladidi ta mike da gudu ta shiga d'aki tana rusa kuka,, D'alha yace"Kyayi kya gama askin shine mafuta... Ya cigaba da cin abuncin sa.
Sai da ya cinye Tass yayi hamdala ga Allah, mik'ewa yayi ya wanko hannunsa ya dawo ya zauna yana fad'in "Iya kin San wani abu kuwa" ?
"A'a sai ka fad'a" yace"Yanzu da zan dawo dake ta sabon titi na biyo. Wallahi gonarmu da ta Jatau da ta Malam Manu me mutuwa, wani me kud'i ya siya ya had'a guri guda ana ta aiki a gurin sosai gurin yayi kyau , yanda naji masu aikin gurin suna fada wai gidan gona za'ayi mishi gorin hutawa da gurin kiwo gurin noman kayan marmari, kin San b'angaran Manu biyu ne akwai gurin da yake noma kayan marmari goba d'ata Lemo da sauransu,, to naga an kewaye gurin da wani k'arfe za'a cigaba da aiki ,nace"Allah ya huttashe dani na shiga in dunga sarowa cikin sauk'i". Iya tace"Alhamdulilahi, aikuwa ka huta wallahi"'" ammafa ni lamarin masu kud'in nan na bani mamaki, haka kurum saboda kudi na cizon su sai su k'irk'iri abunda bai dace ba, a maimakon su raba kud'in ga mabuk'ata"
*COMMENT VOTE AND SHARE*
[9/27, 10:30 AM] 8k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
*🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚*
*🧟♀🧟♀🧟♀K'WADAGA🧟♀🧟♀🧟♀*
*NA*
_BINTA UMAR ABBALE_
~*®BINTUBATULA👄*~
*MARUBUCIYAR*
```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```TSANTSAR BUTULCI```
_*LOODING:*_
_*{LADIDI K'WADAGA🌚}*_
_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_
_______________________
```We are here to educate motivate and entertain aur reades```
_______________________
_*DEDIGATED*_
*TO*
_RAHAMA ALIYU_
_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_
*🅿9*
Kawu D'alha yace"A'a Iya ba duka masu kud'in suke da Wannan halin ba, wallahi akwai masu kirki da taimakon jama'a" "Gaskiyar ka,, akwai sosoi" Mai koko tafad'a haka dai suka cigaba da hira kafin aka kira sallahr magariba D'alha ya nufi massalaci, Ladidi take tai wa magana tayi mata banza sai shek'ar kuka take,, itama sai ta k'yaleta kawai ta dauro Alwala domin yin sallah.
*********
Monday, 12:00pm jirgin su Abdul Hakkim ya sauka,, Dady da Salim da Salima sai ware ido suke suna jiran suga futowar sa,, A hankali ya dunga saukowa, kana kallonsa kasan yana cikin farin ciki,k'ayataccan murmushi ne d'auke a kyakykyawar fuskarsa mai cike da kyau da kwarjini gami da nutsuwa,, yana sanye da suit Wanda sukayi masa bala'in kyau, k'afar shi sanye da rufaffan takalmi blck sai shaining yake,, kunnen shi mak'ale da eir pix,, hannunsa guda k'atuwar wayar sa ce, d'ayan kuma trolly d'insa ce yana jan ta, Salima ta rugu da gudu, tun kafin ta k'araso ya maida wayar aljuhu, ya bude hannunwan sa,, rungume juna sukayi, dariya take tana yi masa barka da zuwa,, da murmushi a fuskarsa yake amsawa yana d'an dukan bayanta, Salim ya k'araso gurin cikin farin ciki yace"Broth barka sannu da zuwa, trolly din ya k'arba daga hannunsa, Hakkim ya dafa kansa yana fad'in"Broth na dawo lafiya ammafa na zo da sabuwar reza sai na aske wannan gashin naka da yayi tozo a tsakiyar ka,, bakaji broth na hana ka irin wannan aski na "yan iska"" Salim yasa dariya yana fad'in"Humm Babban yaya kaima fa irin sa ne a kanka" Dokan kansa yayi yace"A'ina ya zama ina naka,, nawa daban naka daban" 'yar dariya Salim yasa yana Sosa kai, haka suka k'arasa bakin mota inda Dady yake tsaye yana sakin wani kyatattacen murmushi ganin yadda iyalinsa suke so da kaunar junan su,, rungume juna sukayi Hakkim yace"Dady na same ku lafiya"? "Lafiya alhamdullahi sai dai munyi kewar ka, da sa idon ka" Dariya yasa yace"Gani na dawo zan d'ora inda na tsaya mutukar naga ba dai-dai ba""" Dady yace"Ai naga alama gashinan har kafara wa Salim k'orafi" dariya sukayi gaba d'anyan su, suka bude mota suka shiga,, Direba yaja suka tafi.
********
Kwanuka da kofuna ne a jere, tun daga cikin gidan har zuwa soro, kowa naso layi yazo kanshi, har da maza a tsatstsaye a waje suna jira a mik'o musu, yawancin su masu wuce wa ne,, shine take d'aura musu a Leda,, duk wannan aikin ita kad'ai takeyi tayi-tayi da Ladidi ta futo ta taya ta tak'i dake yau alhamis babu makaranta, tana cikin daki tana jin haushi, saboda ko yau da safe sai da Kawunta ya kara maganar aske mata gashi, shine take gaba da Mai koko tak'i kula ta,, hayaniyar yara ce tayi yawa kowa yana ganin kamar za'ayi masa zure,,, da sauri ta bankad'a labule ta futo, fud'um-fud'um, kai tsaye hanyar futa ta nufa,, Sam Iya ba taga futuwar ta ba dake ta juya baya,, tana zuwa inda jerin kwanunkan suke, sai ta fara d'ebo na k'arshe tana mai dasu gaba, na gaba ta dawo dasu baya,, ta hargitsa layi,, Iliya yana tsaye yaga kofunsa ya dawo baya yace"Ke Ladidi mayar min dashi inda yake sai da kika ga an kusa zuwa kaina zaki hargitsa layi" kai tsaye tace"Bazan mayar ba" ruk'e k'ugu tayi tana kallonsa,, a zuciye ya nufi inda kofunsa yake yaje ya dawo dashi inda yake,, aikuwa bai gama ajiye shi ba,, ta d'auka tayi wurgi dashi waje,, takaici yasa Iliya kai mata duka, itama ta kai masa,, kafin kace kwabo fad'a ya rincab'e a tsakaninsu,, wata yarinya ce ta futo hannunta d'auke da kwano Wanda yake cike da koko sai turiri yake,an sallame ta,, babu zato Ladidi ta ingiji ta kokon ya kife a jikinta, yarinyar ta kurma ihu!!!"Wayyo Allah na""" Iya ta saki ludayin hannunta da sauri ta nufi soro,, Me zata gani, Ladidi da Iliya ne suke kokawa katitir! Duk da Iliya yake namiji wanda ya girmi Ladidi da shekaru kusan biyar, ya kasa yin galaba a kanta, duka take kai masa ta ko ina tana k'okarin tad'o k'afarsa da tata k'afar, in ka kalleta a lokaci sai ka rantse da Allah ba Ita bace, duk kamaninta sun sauya,sai naushi take kai masa tana cakumar sa,, Mai koko ta rasa gurin wanda zata nufa,, ga Aminoni tana Ihu!!! Koko ya k'ona ta,, ga Ladidiya can tana d'aban albarka.
*COMMENT VOTE AND SHARE*
[9/27, 5:17 PM] 8k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
*🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚*
*🧟♀🧟♀🧟♀K'WADAGA🧟♀🧟♀🧟♀*
*NA*
_BINTA UMAR ABBALE_
~*®BINTUBATULA👄*~
*MARUBUCIYAR*
```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```TSANTSAR BUTULCI```
_*LOODING:*_
_*{LADIDI K'WADAGA🌚}*_
_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_
_______________________
```We are here to educate motivate and entertain aur reades```
_______________________
_*DEDIGATED*_
*TO*
_RAHAMA ALIYU_
_ALHERIN ALLAH YAZO INDA KIKE_
*NANA AISHATU KADUNA*
_Hak'ika ina jin dadin comment dinki ubangiji Allah ya bar kauna,Aishatu inai miku fatan alkairi a rayuwar ki🥰_
_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_
*🅿10*
Da k'yar Iya ta taimaka wa Aminoni ta cire rigarta ta goge mata jikinta tana ta faman yi mata sannu, ita ko sai