Showing 36001 words to 39000 words out of 48145 words

Chapter 13 - LADIDI KWADAGA

Start ads

24 Aug 2025

75

Middle Ads

*{LADIDI K'WADAGA🌚}*




_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_

_______________________
```We are here to educate motivate and entertain our reades```
_______________________


*30/October/2019*

________________________

*JAN KUNNE⚠*

_*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_





*DEDIGATED*
*TO*
*RAHAMA ALIYU*
~*ABUJA*~





_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_




*🅿31*





General yace." Dole ki dinga saka ido a kanta saboda amana aka bamu har sanda zata gama shan magani ta koma gurin iyayen ta." Hjy Asiya tace." Insha Allahu zan kula wallahi yanzu ma ban San ta futa ba." Nan kusa cigaba da hirar da ta shafe su, Ladidi kuwa nacan tana kallon tv yayin da Salima take kwance kan kujera tana chat babu ruwanta da wani kallo tunda bai dame ta ba.

Goma shaura general ya kalli ladidi yace." Aminatu ya kamata ki kwanta haka saboda gobe ki tashi da wuri zamu je kiga dector ko."? Zumb'ura baki tayi tace." Sai na gama kallona." Salima ta kalli tv din tace." Film din nan fa da saura Dan sai kin kai kusan sha d'aya da rabi na dare a zaune a gurin nan sannan zai kare." General ya mik'e yana fadin "Rabu da ita Salima ta gama kallonta ke dai ki bar dakin a bude kar ki rufe kofa." Yana gama maganar shi ya wuce bedroom Hjy Asiya ta bishi, to Salima ma minti ashirin ta kara ta mike ta shiga bedroom domin kwanciya, aka bar Ladidi ita kadai a parlor.... Sha d'aya saura Yusuf da Salim suka shigo, cike da mamaki suke kallonta, ganin irin kallon da suke matane ya bata haushi tace." Meye! Kuka zuba min ido." Shiru sukayi kawai domin suna iya magana ta sanya ihu ransu ne zai b'aci in Dady ya ji, wani daki suka shige dukaninsu suna mamakin rashin kunyar yarinyar gami da k'arfin halinta

Sha daya da kwata ya shigo shima ya gaji mutuka bacci kawai yake so yayi, yana shiga parlor yaga Ladidi tsaye gaban Tv tana dariya kamar mahaukaciya tv ya kalla da sauri sai yaga jarumi Akshey kumar yana dukan boss da alama film din yazo k'arshe. Ladidi sai ihu! Take tana fad'in"Yawwa! Kashe shi! Hege! Mugu dama bashi da wani amfani"!! Takaici ya hana shi cewa komai kawai ya nufi gaban tv romt ya d'auka ya kashe TV ya zare wayoyin daga jikin soket din. A zabure!!! Ta kalle shi! Sai kuma ta ja da baya ganin Hakkim din ne. Bude baki tayi zata yi magana yace." Wuce! Kije ki kwanta mahaukaciya kawai." Ladidi takaici kamar ta Dora hannu aka gashi ana fad'an k'arshe wannan Dan rainin hankali yazo ya kashe TV kamar zata yi kuka tace" ka kunna min in karasa gani,."

A fusace! Yace." An ki a kunna miki Dan uwarki ibilishi dak'ikiya wacce bata sa komai a gaba ba sai dakikanci da jahilici." Tunda take a rayuwa babu Wanda ya tab'a yi mata zagin cin mutum fi irin na yau. Ta fara sanin ciwon kanta tana a matsayin shekaru goma sha uku.yanzu idonta ya ciko da kwallah sosai. Tsawa! Ya buga mata akaro na uku yace." Kin bar nan gurin ko kuwa sai nayi kulikulin kubura dake yanzu." Da gudu ta shige dakin da Salima take tana wani irin kukan taki. Shiko wani sanyi yaji cikin zuciyarsa ganin ya sata kuka dama abunda yake so kenan, duk irin b'acin ran da ya kunsa daga gurin Dadyn sa, sai ya fanshe a kanta, d'akinsa ya nufa zuciyarsa babu dad'i.


Misalin k'arfe bakwai da rabi kowa ya hallara a parlor ana shirin karyawa, ya futo cikin shiru fuskar nan a had'e General ya kalle shi tare da fadin "yawwa dama yanzu nake cewa Salim ya shiga ya kira min kai mu tafi hospital din nan da wuri."

Zama yayi kujerar daining yace." Dady wane irin hospital ? Ni da zan wuce Abuja yanzu."

Wani irin kallo general din yayi masa yace." Yanda muka zo tare to haka zamu koma. tare babu inda zakaje." Ganin Dady din fuskarsa babu wasa yasa ya kwantar da murya cikin laluma yace." Dady kasan sati biyu zanyi in koma America kaga yau nayi kwana Tara da zuwa, ya zama dole yanzu inje in fara shirye-shiryen tafiya ko."


Shiru general din yayi masa ya cigaba da karyar warshi hankali kwance. Hjiy Asiya ta kalle shi tare da fadin "ko a had'a maka breakfast din ne." Gyad'a kansa yayi.
Had'a masa tayi ta tura masa gabansa, tsatstsakura yayi a je fork din, ya cigaba da kurb'ar tea din ranshi babu dad'i.


Salima da Ladidi ne suka futo tare sun shirya tsaf!! Ladidi an sha kwalliyar fuska leb'anta jazur da Jan janbaki babu yanda Salima bata yi da ita ba kan kar ta sanya sai da ta saka, ta zabga jar hoda fuskarta tayi fururu!! Kauda kansa yayi yana Jan tsaki! Salim ya sunkuyar da kansa yana kunshe dariya. General yace. " Aminatu wannan kwalliyar fa." Washe baki tayi tace." Yanzu nayi tayi kyau ko." Yace." Kinyi kyau mutuka amma ke Salima gyara mata hodar fuskar tata zata fi kyau." Salima ta fara goge mata fuskar nuna wa tayi bata so don sai kauda fuskarta take. Hjy Asiya tace." Rabu da ita kawai tunda bata so." Suna zama kan kujearar daining din ya mik'e hannunsa rike da cup din tea ya wuce can parlor had'e da zama kan kujera yana ya mutse fuskarsa kamar Wanda yaga kashi.



gurguje Salima ta had'a musu breakfast suka karya General ya mik'e yana duba agogon hannusa yace." Ku tashi mu tafi. Salima da Ladidi suka mik'e da sauri suka futa waje Salim ya mik'e Yana fadin "Dady bari inzo inyi draving d'inku tunda big broth zai tafi.. General ya kalli Yusuf da ya futo daga daki cikin shiri yace." Kai yau zaka koma ne."? Yusuf yace." Eh Dady." Gyda kai kurrum general yayi yace." Wato ya sauya maka ra'ayi kenan.". Murmushi yayi tare da fadin "ba haka bane Dady" wuce wa yayi yana fadin" Nayi karya kenan, Ku sauka lafiya." Yana gama maganar shi ya futa Salim ya rufa masa baya. Hajy Asiya nayi masa adawo lafiya.







*30/October/2019*
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

*🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚*
*🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀*




~*NA*~
_BINTA UMAR ABBALE_
*BINTUBATULA👄*



*MARUBUCIYAR*

```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```TSANTSAR BUTULCI```

*LOADING:*
*{LADIDI K'WADAGA🌚}*




_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_

_______________________
```We are here to educate motivate and entertain our reades```
_______________________




*JAN KUNNE⚠*

_*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_



________________________
*1/NOVEMBER/2019*
^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^



*DEDIGATED*
*TO*
*RAHIMA ALIYU*
~*ABUJA*~





_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_





*🅿32*





Wannan karon Ladidi ba tayi hauka a hospital ba tsaf ta tsaya dector ya duba ta sosai yayi mata wankin kunne kamar yanda ya fad'a jiya, nan sukayi sallama da general, cikin mutum ci da mutuntawa suka dawo gida, lokacin Hakkim da Yusuf sun Dade da barin garin, general yace." Gwara da ya tafi domin ina ganin zaman sa a gidan zai iya sanya wa Aminatu ta gudu kamar yanda ta fara yunk'uri guduwa da farko."

Ita dai Hjy Asiya lallaba Ladidi kawai take kamar yanda mijinta ya umarce ta, bayan sallahr la'asar ne Mai koko ta iso gidan cikin walwala da sakin fuska Hjy Asiya ta karb'e ta lokacin general ya shiga cikin gari domin gaisawa da tsoffin abokansa,

Ladidi ta dinga ihu!! Tana murna ta rungume mai koko tana fad'in"Iya kin ganni ko dubi kayan jikina Iya wallahi ina son zama da mutanan suna da kirki, don Allah ki barni a gurin su."

Mai koko tace" Ai kya bari mu gaisa tukkuna kafin ki fara yi min wannan sangar ta taki ko." Ladidi ta zauna kusa da ita sai washe baki take ta fara gaishe ta.

Mai koko ta amsa fuska a sake tace"Dole ne ki so zaman gidan nan tunda kin samu tv da vedio amma ni kam babu Wanda zan iya barwa ke Ladidi ."

Ladidi ta b'ata fuskarta kamar ta kurma ihu!! Hjy Asiya tace" Tunda tana son zama damu Iya muna Neman alfarma ki bamu ita don Allah mu tafi da ita can abuja mana."


Mai koko ta bude baki cike da mamaki tace." Habuja fa kika ce Hjy? Kina nufin in baku Ladidi Ku tafi da ita yaron ku ya k'arasa ta, shi da naga bashi da imani, ba da ban Allah ya kiyaye ba da tuni ya kurmantar da ita, Hjy kuyi hakuri bazan iya ba." Ta k'arashe maganar ta tsakanin ta da Allah.
Girgiza Kai Mai koko tayi alamun bata amunce ba, Hjy Asiya ta kalli Salima dake zaune kan kujera da waya a hannu tace"Salima kawo wa Iya ruwa da abunci."

Da sauri Mai koko tace"Alhamdullahi Hjy a koshe nake wallahi." Hjy tace"A'a Iya dole ki ci wani abun kam ai ko ruwa kyasha." Shiru mai koko tayi tana addu'ar kar Allah yasa Ladidi ta tubure mata kan abunda ta fad'a, jiya ma kwana sukayi suna Abu guda ita da Dalha domin ya fad'a mata yanda suka yi da General, tace masa bata amince ba, ko da wasa kar ya kuskura ya amsa masa.

Ganin take taken Ladidi ne yasa Mai koko mik'ewa tana niyyar tafiya Ladidi tak'i kallon inda take sai zumb'ura baki take."

Mai koko ta rik'e hab'arta cike da takaici take fadin". 'Yar nan kar dai da gaske take." Bata da me bata amsa, don haka sai ta nufi hanya futa Hjy Asiya ta mik'e da sauri tayi mata rakiya har waje.


Salima ta kalli Ladidi a tsanake tace"Idan fa kina so ki shiga birni dole ne duk wannan shashanci ki daina ki nutsu ki daina k'auyanci da rawar kai shima na tabbatar da cewa rashin kamun kan da kike yi ne yasa bakwa shiri da big brother, idan kika kama kanki zaki ga kowa yana son yin mu'amula dake."


Ladidi ta kalleta a nutse tace"kina nufin idan na daina magana yayan ki zai dai na hantara gami da ce min aljana." ? Salima tace"K'warai kuwa Big brother ya tsani k'azanta da rashin kamun kai, ki nutsu zaki ga ya daina hantarar ki." Shiru Ladidi tayi tana sak'e-sak'e cikin zuciyarta.


*******

Yau kwanan Ladidi biyar a gidan gona kullum ta wanke goma ta tsoma biyar ta ci abunda ranta yake so ta sha abunda ranta yake so, dodon ta baya gidan shiyasa take sakewa tayi kallonta son ranta, duk sai a tashi a barta a parlor ita kadai.domin kar ranta ya b'aci yasa general yake k'yaleta, ta more saboda ya fuskanci yarinyar dole sai da siyasa.

Yau ne Ladidi ta gama shanye magungunan ta kuma Alhmdullahi jin ta ya dawo rad'au! DOMIN har har yaso yafi da. A yau ne kuma Mai koko ta dira a gidan da niyyar tafiya da ita.







*BINTA U ABBALE*
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

*🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚*
*🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀*




~*NA*~
_BINTA UMAR ABBALE_
*BINTUBATULA👄*



*MARUBUCIYAR*

```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```TSANTSAR BUTULCI```

*LOADING:*
*{LADIDI K'WADAGA🌚}*




_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_

_______________________
```We are here to educate motivate and entertain our reades```
_______________________




*JAN KUNNE⚠*

_*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_





^^^^^^^^°^^^^^^^^^^^^
*3/November/2019*
^^^°^^^^^^^^^^^^^^^^^




*DEDIGATED*
*TO*
*RAHIMA ALIYU*
~*ABUJA*~





_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_








*WANNAN PEGE D'IN NAKA NE ABUE SALEH ZAMANI WRITARS, ALLAH YA K'ARA MAKA HIKIMA DA AZANCI*





*33*





General yana ganin Mai koko yasan da abunda tazo, shi tun jiya sun gama magana da D'alha ya yardar masa ya tafi da Ladidi abuja, domin yana kwad'ayin tayi karatu kuma ta nutsu tabbas hankalin sa ya kwanta da mutumin yasan bazai cuce shi na.

Sosai general ya karb'i mai koko fuska a sake yake gaishe ta ta amsa babu yabu babu fallasa tace"Naga kun shirya dama ina addu'ar Allah yasa na tadda daku domin tun jiya jikina yake bani da akwai wata a k'asa."

General yace." Hak'ika Iya kina da gaskiya kuma maganar cewa za'a b'oye miki sam! bata taso ba, jiya mun Dade da D'alha a waje muna tattsunar maganar . Nan duk ya kwashe komai ya fada mata.

Mai koko tace" Kun munafur ce ni Alhaji, ina ganin mutumncin ka, Wallahi wato dama da biyu kace dole sai ta zauna a gidan ka ko domin Ku cusa mata k'in zama cikinmu ai babu komai, Alhaji ga amanar Ladidi nan a hannuku marainiya ce,duk Wanda ya cuceta shi da Allah."
Ta k'arashe maganar muryar ta na rawa.

General bai ji dadin kalaman da Mai koko tayi amfani dasu ba gurin fada masa magana amma domin a zauna lafiya yasa ya dinga lallab'ata hade da rarrashin ta, cewar ta kwantar da hankalinta yayi mata alk'awarin duk wata zai dinga sanyawa ana kawo ta suna gaisawa.

Ba tace komai ba ta mik'e ta fuce daga parlor zuciyar ta babu dad'i, Hjy Asiya ta biyo bayan ta tana yi mata magana mai koko ko juyo wa ba tayi ba, babban abunda ya bata shaushi ganin yanda Ladidi taki kallon inda take balle ma tayi mata magana.


Tana komawa gida ta Tarar da D'alha ya futo zai tafi gurin sana'ar sa, nan ta rufe shi da fada tana share hawaye tana fadin"me yarinyar nan ta tsare maka ne ? Ka dauke ta ka bada ita hannun mutanan da baka sani ba."
D'alha ya tsaya yana fahimtar da ita, kin sauraron sa tayi ta shige cikin gidan ranta a bace.!

Futa yayi kawai yasan duk maganar da zai fada mata yanzu ba sauraransa zata yi ba, dole ya bari ta huce tukkuna sai yayi mata bayani yadda zata fuskarta.


*******
*LADIDI A ABUJA*


Tunda suka isa birnin tarraya take kalle-kalle cike da k'auyanci gine-gine take kallo iri-iri Salima ta tab'o da hannunta tace"Salima kuma wannan dogwayen gine-ginen basa fad'owa kan mutane." Salima tayi murmushi tare da fad'in"Amanatu kenan, duk haka ginin garin yake, babu kuma Wanda zai fad'o." Ladidi tayi shiru cikin motar zuciyar ta fara zugata da tasani bata biyo su ba tabi Iya wata kila ma zasu siyar da ita ne, hawaye ta fara sharewa cike da tausayin kanta, Salima tace"Kuka kike Amina." Fuskarta ta b'oye tsakanin k'afafun ta,General ya juyo da sauri tare da fadin"Kukan me takeyi Salima." Tace" Wallahi ban sani ba Dady." Salim ne yasa dariya tare da fadin "ko ta tuno gida ne"? Hjy Asiya tace" Salim kar ka kara yi mata dariya " gumtse bakinsa yayi yace." Toum, Hjy ASIYA ya juyo tana rarrashinta da kyar tayi shiru, suka Isa gida.

Ganin mai gadi na bude wani wangameman get yasa Ladidi ta tsorata ganin doguwar kanta kewaye da kayoyi lokaci guda zuciyarta ya fara sak'a cewar in tayi sha'awar futa wasa ta ina za ta futa, bata k'ara tsinkewa da al'amarin na sai da taga wasu manya-manyan sojoji guda uku ko wanne hannunsa rike da budinga sun taso daga gurin zaman su, suna wa General barka da zuwa.

B'uya tayi bayan Hjy Asiya tana zare idonta, nan Salima taja hannunta suka shige ciki.

Tunda suka shiga parlor take bin ko ina da kallo gaskiya haduwa lparlor ya kai ya kawo wasu tafka-tafkan hotona ne kafe a hango uku general ne da iyalinsa, sai kuma nashi shi kadai yana sanye da kayan sojoji

Jikinta yayi sanyi ta kalli Salima tare da fadin"Dama Baba soja ne."? Salima tace" Eh amma ritaya shekaru biyar da suka wuce. " shiru tayi tana kara bin parlor da kallo can ta hango wani tafkeken hoton Hakkim jikin bango Yana sanye da wasu suit Wanda suka yi masa mugun kyau dariya yake yi lokacin da aka dauki hoton tsantsar kyawun shi gami da haibar shi ya sun futo da alama ma hoton na anan aka dauke shi ba, kamar a k'asar waje ne................








*BINTA U ABBALE*
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

*🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚*
*🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀*




~*NA*~
_BINTA UMAR ABBALE_
*BINTUBATULA👄*



*MARUBUCIYAR*

```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```TSANTSAR BUTULCI```

*LOADING:*
*{LADIDI K'WADAGA🌚}*




_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_

_______________________
```We are here to educate motivate and entertain our reades```
_______________________




*JAN KUNNE⚠*

_*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_





^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^
*5/November/2019*
^^^°^^^^^^^^^^^^^^^^^^





*DEDIGATED*
*TO*
*RAHIMA ALIYU*
~*ABUJA*~





_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_






*🅿34*




Jikinta a sanyaye ta zauna kusa da Salima, a lokacin idan ka ganta baza ka tab'a cewa Ladidi ta Mai koko bace saboda yanda ta koma kalar tausayi duk babu wannan rawar kan da ta saba.
General da Hjy Asiya suka shigo palo bakin su dauke da sallama, mai aikin gidan ce ta futo daga kicin da sauri tana yi musu barka da zuwa. Hjy Asiya ce kawai ta saurare ta tuni general ya hau sama, jikinshi duk babu dad'i wanka kawai yake son ya yi.

Baito mai aiki ta kalli Ladidi tana washe bakinta tace"Hjy bak'uwa muka samu ne." ? Hjy Asiya dake kokarin hawa sama tace"E gatanan bak'uwa ce kuma 'yar gida."

Baito tace"Masha Allah yarinya kyakyawa da ita gata 'yar Fulani, ya sunan ki."?
Baki na rawa tace." Sunana Ladidi." Salima tace"Daga

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login