Showing 15001 words to 18000 words out of 48145 words
tana tsalle, kamar zata kai masa duka take fad'in "Sakar min hannuna ni ba " yar iska bace". Hakkim ya buge mata baki da d'aya hannun nasa, kafin kace kwabo jini ya fara zuba, ihu! ta kurma wanda yasa su Yusuf suka runtumo da gudu gurin. Hakkim na tsaye hannunsa tam! da na Ladidi sai buge-buge take tana kwanciya a k'asa dole sai ta k'wace daga hannunsa, wawan hauri ya kai mata da k'afar shi guda, ta k'ara k'wala k'ara tana kuza masa ashariya! Yusuf ya k'araso gurin, hankali a tashe yake fad'in"Wai meye yake faruwa ne? wannan yarinyar fa, daga ina".? Bak'in ciki da b'acin ya hana shi cewa uffan,sai cije baki yake yana dukanta da k'afar sa, Salima ta k'araso gurin jikinta a sanyaye take fad'in"Broth waye ya b'ata maka jiki da wannan k'azantar " Yusuf ya Kai dubansa gurin shi sam bai lura ba, hankalin sa na kan Ladidi, har hanzu hannuta na rike a nashi yana dukanta da k'afafunsa ita kuma bakin ta bai bar zaginsa ba, tana deb'o k'asar gurin tana watsa masa a jiki. Yusuf ya fara k'okarin kwace daga hannunsa, ya fuzge da k'arfin yayi wani mugun boll da ita ta gangara can gurin k'ofar futa kanta ya bugu da wani dutse, da sauri ta mike tamkar ba ita akai wa wannan dukan ba, wani mugun tsalle tayi sai gata a gabansa, dama ya tsammaci zuwan ta, k'afar sa ya sanya ya tad'eta! Ta fad'in a gurin a sume!! Yusuf ya saka salati yana fad'in"Shikkenan kaga ka kashe yarinyar mutane ko, innalilahi wa'inna ilahi raji'un"!! Salima ta fashe da kuka tayi kan Ladidi tana tattab'a jikinta, Yusuf ya futa daga gurin da sauri, gabansa sai fad'uwa yake, ashe k'addara ce ta kawo shi, shi ko Hakkim ko a jikinsa, karkad'e rigar sa yayi cike da bak'in ciki da b'acin rai! Yake k'okarin barin gurin,Salima ta rik'e hannunsa tana kuka take fad'in"Broth ina zakaje LA tsaya ka duba wannan yarinyar ko suma tayi don girman Allah, ni kam Wallahi da nasan haka zata faru da ban biyo ka ba" . Fuzge hannunsa yayi cikin b'acin rai! Yace"Yanzu ma kina iya komawa gida babu Wanda ya rike miki k'afafu ga hanya nan" yana gama fad'in maganar shi ya futa daga gurin. Karo suka ci da Yusuf ya tawo da sauri hannunsa rike da robar ruwa na faro, ko kallonsa bai yi ba yayi fucewar sa.
*COMMENT VOTE AND SHARE*
[9/30, 10:08 AM] 8k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
*🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚*
*🧟♀🧟♀🧟♀K'WADAGA🧟♀🧟♀🧟♀*
*NA*
_BINTA UMAR ABBALE_
~*®BINTUBATULA👄*~
*MARUBUCIYAR*
```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```TSANTSAR BUTULCI```
_*LOODING:*_
_*{LADIDI K'WADAGA🌚}*_
_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_
_______________________
```We are here to educate motivate and entertain aur reades```
_______________________
_Alhmdullahi jiki yayi sauk'i_
*Gaskiya naji dad'i sosai da kularwar ku akaina nagode masu kirana a waya kuna yimin ya jiki da fatan samu lafiya,masu min sannu ta pravite wanda na sani da wanda ban sani ba nagode sosai da sosai ina muku fatan alkairi*
*Jan kunne⚠*
_Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin book d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ ki siyar min da littafi ba da sanina ba, Wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan haka, hattara dai!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje yaci gumin sa, kane mi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka_
*DEDIGATED*
*TO*
*RAHAMA ALIYU*
_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_
*🅿13*
Cikin sauri Yusuf ya k'araso gurin da Ladidi take kwance, ya bud'e ruwan,ya fara zuba mata a fuskar ta furgice! ta mik'e zaune ta k'wala k'ara! Waige-waige take tana neman Hakkim a gurin, Salima ta rik'e hannunta tana son tayi mata magana. Fuzge hannunta tayi da sauri ta mik'e tsaye tana fad'in" Yana ina."? Duk suka mik'e suna kallonta, Yusuf yace." Ke yarinya me ya shigo dake gurin nan?,da har kika jawo wa kanki suma." Banza kallo tayi masa ta murgud'a bakinta, bata ce masa komai ba, ta bar gurin bagazan-bagazan! kallo suka bita dashi, Yusuf ya kalli Salima yace." Anya kuwa yarinyar nan me lafiya ce"? Salima ta k'unshe dariya tace." Lafiyan ta lau. Kamar ka manta da a k'auye kake dole kaga haka." Yusuf ya girgiza kai yace." Ni abunda ya bani mamaki da ita shine yadda ta shigo gurin nan wallahi". "Gaskiya nima nayi mamaki." Salima tafad'a yayin da suke k'okarin futa dafa gurin.
********
Ta inda ta shiga gurin tanan ta haura ta futa Hakkim na kallonta tun futowar ta har lokacin da take haure katangar yana gani, zuciyar sa yana mamakin ibilicin yarinyar, yau d'in nan zai sanya a kewaye katangar gurin, da waya mai k'ayoyi, duk saboda ita dole kuma a zuba masu gadi a gurin. tuni ya cire kayan da ta b'ata masa ya watsar dasu harabar gurin, domin mugun k'yamk'yami ne dashi, idan ya tuno halittar yarinyar sai yaji zuciyarsa tana wani irin tashi! sosai zuciyar sa take masa zafi, tunda yake a rayuwarsa babu wanda ya tab'ai masa irin abunda yarinyar tayi masa dole ne ya d'auki mataki akanta mutukar ya kara ganin k'afarta a gidan, karya ta zaiyi kawai kowa ya huta. Su Yusuf suka k'araso gurinshi ya sha kunnu domin baya son ma yayi masa maganar, Simi-simi Salima ta shiga ciki, Yusuf ya samu kujera ya zauna yana kallon Hakkim d'in, da yake k'ara yin kicin-kicin da fuska, yace." Zauna zamuyi magana da kai". A fusace! Ya juyo yana fad'in"Ubana ne kai zaka bani umarni". Yusuf ya kalleshi , da alama zuciyar sa har yanzu batayi sanyi ba. Yace." A'a ba ubanka bane". "To ka fad'i duk abunda zaka fad'a kunne na yana ji". Ya k'arashe maganar yana juya masa baya. Yusuf ya mik'e ya k'arasa inda yake, kafad'arsa ya dafa cikin taushin murya yace." Aboki wai me ya faru tsakanin ka da yarinyar nan? Wallahi hankalina ya tashi sosai domin ta dad'e kafin ta farfad'o,haka kurum daga zuwanmu guri zakayi kisan kai saboda zafin zuciya". Hakkim ya juyo yana fuskantar sa, cikin kaushin murya ya fara fad'a masa abunda ya faru. Yusuf ya sauke ajiyar zuciya yace." Gaskiya kam yarinyar ba tayi maka dai-dai ba,amma kai ma bai kamata kayi mata irin wannan dukan ba,saboda yadda na lura da ita kamar irin yaran nan masu lalurar k'wak'walwa kasan k'auye ko d'ansu na cuta basa mai da hankali sai abu yayi tsanani, sannan zaka gansu sun nufi asibiti hankali a tashe." Zuciyarsa ce fara sanyi ya zauna kan kujera guda Yusuf ma ya zauna kusa dashi, yace." Ka bari kawai Yaro wallahi zuciyata a lokacin ji nake tamkar na kashe ta na huta da b'akin ciki." "Kayi hakuri don Allah ka rage zafin zuciya." Yusuf yafad'a yana dukan kafad'unsa.
Salima ya k'walawa kira, tana can ta shagala da kallon yadda aka tsara falo da kayan jin dad'i da more rayuwa, har ta kunna kallo tanayi taji kiran big broth amsawa tayi ta mik'e da sauri, tana zuwa yace." Ki shiga kchin kiyi mana abunci." "Angama big broth" tafad'a cike da bin umarni, kai tsaye kichin d'in ta nufa, gashinan komai akwai na amfani nan take ta fara aikinta.
**********
To can gidan su Ladidiya kuwa Mai koko ta saddak'ar ta fawwala wa Allah cewar Ladidi ta mutu cikin rijiyar don haka mutane sun cika gidan ana yi mata ta'aziyya, Jama'a sun kewaye ta, tana zaune da carbi a hannu ga idonta yayi jajazur! taci kuka ta k'oshi, D'alha na waje da mutane zazzaune kan tabarma, sam yak'i yadda cewar Ladidiya ta mutu cikin rijiya k'wak'walwar sa tafi tunanin yarinyar tana can gurin gantalin ta, shiyasa ya kasa zaune ya kasa tsaye sai zurga-zurga yake a gurin. Duk Wanda yazo gurin sai ya hau yi masa gaisuwa, ko kallon su baya yi
*********
Tafiya take fakam-fakam!! sak'e-sak'e kawai take a zuciyarta da tunanin d'aukar fansa kan, d'an burni,sunan da ta sama sa kenan, wallahi bai dake ta a banza,sai ta rama duk hanyar da zata bi ta sani, leb'anta ta tab'a da hannunta, cire hannuta tayi tana girgiza kai! a fili tace."Wallahi he na rama idan ubanka ne shugaban k'asa he na rama, nima sai na fasa maka baki,hummm!! Zaka san ka tab'o Ladidi jikar Mai koko, bana barin takwana kuma bana manta ranar d'aukar fansa." Da tafiyar ta ya gane i tace jiki na rawa ya k'wala mata kira,"Ladidi" da sauri ta juyo tana waigen idan taji ana kiranta. Kakanta ne D'an fulani, yake tawo wa inda take, yana can gurin kiwo labari ya same shi na mutuwar ta,shine ya tawo cikin tashin hankali! Abun mamaki kuma sai gashi ya ganta a hanya, yana k'arasowa inda take ya damk'i hannuta, bai ce mata komai ba suka fara tafiya, zub'uro baki tayi tace." Ni ka sake ni ka rik'e min hannu da k'arfi ai gida zani ba wani guri ba." D'an Fulani yayi mata shiru, shi dai k'okarin shi kawai yaga ya danganata da gida,hankalin kowa ya kwanta. Tun daga nesa jama'ar dake gurin suka hango tawowar su, sai aka fara kallon-kallo tsakanin su, da suka tabbatar da cewar itace sai kowa ya fara zura silafas d'insa yana guduwa, D'alha ya juya yaga wayam! babu kowa a gurin, girgiza kai kurum yayi yana jin wani d'aci cikin zuciyarsa wato Ladidi ta zama abun tsoro kenan? D'an Fulani ya d'amk'ata a hannunsa yana fad'in"Gatanan can wajejan titi na gano ta tana tafiya ita kad'ai." D'alha ya sauke ajiyar zuciya yace."Alhamdullahi, dama ni jiki na bani yarinyar nan tana raye,amma jama'ar gari suna ta fad'in ta mutu a cikin ruwa,Allah nagode maka daka bayyana mana ita ko hankalin Mai koko ya kwanta." Sai sanan Ladidi ta tuna da abunda ya faru d'azu tsakaninta da Mai koko, dariya ta kece dashi,hahahaha! D'alha ya gaura mata mari! Yana fad'in"Rufe miki don buhun ubanki, shashasha, shakatafe, naga ranar da zakiyi hankali dai" D'an Fulani kuwa a'lamarin Ladidi ya fara bashi tsoro,don haka yace."D'alha mu shiga cikin gidan sai mu San abun yi." Kai tsaye cikin gidan suka shiga.
*Tofaa ko ya zata kasance idan jama'ar gidan sukaga Ladidi Wanda suka dauka ta mutu cikin rijiya,ko yaya Mai koko zatayi in taga Ladidi? To Ku cigaba da bina dai cikin labarin domin in warware muku*
*COMMENT VOTE AND SHARE*
[10/2, 5:54 AM] 8k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
*🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚*
*🧟♀🧟♀🧟♀K'WADAGA🧟♀🧟♀🧟♀*
~*NA*~
_BINTA UMAR ABBALE_
*BINTUBATULA👄*
*MARUBUCIYAR*
```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```TSANTSAR BUTULCI```
*LOADING:*
*{LADIDI K'WADAGA🌚}*
_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_
_______________________
```We are here to educate motivate and entertain our reades```
_______________________
*ALHAMDULLAHI*
*HAUWA S ZARI'A*
_Maman Usuwan_
*Ina taya ki murnar kammala littafin ki HAKA ALLAH YA NUFA _KADDARA TACE_ ALLAH YA KARA BASIRA YASA SAKON KI YA ISA INDA KIKE SO*
____________________
*JAN KUNNE⚠*
_*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_
*DEDIGATED*
*TO*
*RAHAMA ALIYU*
~*ABUJA*~
_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*
*🅿14*
Suna k'okarin shiga da ita cikin gidan tana turjewa D'alha ya kwad'e mata k'eya yana fad'in "Zaki wuce muje ko kuwa,? Kin tayar wa da mutane hankali, gidan buhun ubanki zaki je ne" Ihu! Ta kurma, wanda yasa Mai koko da sauran jama'ar gidan mik'ewa tsaye da sauri sukayo waje suna salati! Kafin su rufe bakinsu, sai ga Ladidi an shigo da ita tana turjewa! Mai koko ta bude baki zatayi magana D'alha ya katse ta hanyar cewa." Don Allah kar Ku tsorata da ganin ta, dama na fada muku tana raye bata mutu ba, ga shi a can bakin titi d'an Fulani ya gano ta,wanda shima labari ne ya riske har inda yake kiwo cewar ta mutu." Mai koko ta k'araso gurin da jiki a sanyaye zuwa yanzu itama ta fara tsorata da al'amarin Ladidi, da muryar ta wacce tasha kuka ta gaji tace. " Ladidiya dama baki fad'a rijiya ba, me yasa kika yi min haka Ladidi"? Turo baki tayi tace." Nifa ban fad'a rijiya ba, kinga gurin dana b'uyar miki fa" Mai koko tabi hannuta da kallo, cike da mamaki da al'ajabi Matan da suke tsatstsaye a gurin, duk suka tsure sai zare ido suke burin su kawai su bar gidan, Mai koko tace." Me yasa to duk aka duba ba a ganki ba"? Shiru tayi mata, D'alha ya dubi matan dake tsatstsaye, yace." Ko wacce tana iya tafiya" aikuwa kafin kace kwabo duk sun zura takalman su, suna bangazar juna suka futa daga gidan, ko wacce cikin ta ya d'uri ruwa. D'an Fulani yace." Ku zauna zamuyi magana ta fahimta" Mai koko taja hannun Ladidi suka zauna kan tabarma. D'alha suka zauna gan benci, D'an Fulani ya kalli Mai koko a nutse yace." Al'amarin yarinyar nan ya soma bani tsoro saboda haka na yanke wata shawara." Mai koko tace." Ai kana da iko akanta tunda kai ka haifi mahaifiyar ta." Yace." NA yanke shawarar cewa gobe insha Allahu zan kawo malamin ruk'iya zai yi mata idan da makarai a jikinta sai a sulhun ta dasu"
Shiru tayi na minti biyu, ta d'ago kai tana kallonsa, tace." Ba wai nak'i taka bane, gaskiya ka janye maganar ruk'iyar nan,domin su wad'annan mutane ba a haka dasu, idan kuma basu suka rab'e ta b,kaga sai a jawo mata su da hujja, abar maganar ruk'iya mu cigaba da yi mata addu'a" Dan Fulani da D'alha suka kalli juna, girgiza kai kurum D'alha yake yasan dama Mai koko baza ta yarda ba, shi ko D'an Fulani saboda tsabar haushi da takaici bai sake cewa komai ba. Ya mik'e yana musu sallama, sama-sama Mai koko ta amsa masa, D'alha ya mik'e domin ya raka shi. Mai koko ta dinga rarrashin Ladidi, da lallab'ata tamkar ba wacce tayi mata laifi ba, tace." Tashi ga ruwan zafi can muje kiyi Wanka ko"? Mak'ale kafad'a tayi. Tace." Akwai miyar kifi nan a fulas na aje miki sai ki siyo buredi" Mik'ewa tayi zaune tana Sosa kai tace." Amma ni zanyi wanka na gaskiya" tace." E amma zan cud'a miki baya." Mik'ewa tayi tana tube kayan jikinta ita kuma ta nufi kicin din, bakin rijiya ta tsuguna tana wasa da ruwan Wanka, Mai koko ta k'araso da abun sabulu a hannuta tace."Ladidi waye ya fasa miki leb'e haka? Ko garin tsalle-tsallen ki ne"? Hannuta tasa ta shafo gurin, girgiza kai tayi tace." Wani d'an burni ne, kawai babu abunda nayi masa don zalin ci." "A'a Ladidi nasan halin ki fa"? Iya tafad'a tana murza sabulu jikin soso. " Kawai don na shiga gonarmu shine ya doke ni" "Wace gona kuke da ita Ladidi'? Iya. Ta fada cike da mamaki! " Ranan da zamu wuce Kawu ya nuna min gonar tun kafin a gina gurin yace."Tasu ce da babana." "To yanzu na gane inda kika dosa" Iya tafad'a tana durzar jikinta da soso, ta cigaba da cewa " Ladidi kin cika futuna me ya kai ki gurin nan, yanzu bs gonar su bace, domin sun siyar da ita dalilin haihuwar ki, ranar bakiji Kawun ki yana fad'in wani mai kud'i ya siya har da tasu Malam Tanimu da Manu ba" girgiza kai tayi tace." Ni babu ruwana ko sun siyar ko basu siyar ba, in naga dama zanje ne" Mai koko tace." To sai ki kiyaye domin mutanan burni ba dai-dai suke da na k'auye ba." Zumb'ura baki tayi tace." Aiko sai na rama abunda yayi min ko shugaban k'asa ne ya haife shi." Mai koko dai shiru tayi domin bata so ta tsanan ta mata kar ta sake guduwa.
Kawu D'alha kuwa akwai abunda ya k'udura a ransa kan Ladidi. Sai da ya tabbatar da sunyi bacci sannan ya shigo gidan, kai tsaye dakin Mai koko ya nufa, dama duk ranar da tayi ibilincin ta. To in ta kwanta bacci bata motsawa sai gari ya waye, Mai koko ma bacci take sosai ansha fargaba an gaji, reza ya futo da ita daga cikin aljinunsa ya kwance d'aurin d'ankwalin Ladidi a nutse a shafa sabulu da ruwa ya soma yi mata aski babu abunda ya dame shi. Har D'alha ya gama aske mata kai bata motsa ba, ya mayar mata da dankwalin ta ya daure mata kanta kamar yanda tayi, ya sunkuya ya tattare gashin da zube k'asa ya zuba cikin leda shara ya zuba yasa omo ya wanke hannunsa tass!!! . Ladidi bacci tayi sosai da sosai sam bata san inda kanta yake ba, sai wajan shiga da rabi na safe ta tashi lokacin Mai koko ta Dade da tashi tana can tana hidimar huta huta domin ta d'ora ruwan kuka. D'ankwalin ta take laluba kan shinfid'ar ta d'auka zata d'aura akanta tana tab'awa taji sumul tamkar gwiwa hannuwa biyu tasa tana shafawa, Ihu!! Ta kurma tana fad'in "Wayyo!! Mai koko wani ya aske min kai na" Mai koko ta aje icen dake hannunta da sauri ta nufi dakin. Tana shiga taga Ladidi ta d'ora hannu aka tana kurma ihu! Ga kanta sumul! Babu k'wallin gashi ko d'aya, cikin mamaki tace."Ladidi waye yayi miki k'wal kwabo hak..... Kafin ta k'arasa muryar D'alha ta katse ta inda yake cewa." Iya nine nayi mata aski saboda in cika rantsuwa bayan haka kuma da wahalar da ta bamu jiya, shiyasa na yanke wannan hukuncin a kanta."
*COMMENT VOTE AND SHARE*
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
*🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚*
*🧟♀🧟♀🧟♀K'WADAGA🧟♀🧟♀🧟♀*
~*NA*~
_BINTA UMAR ABBALE_
*BINTUBATULA👄*
*MARUBUCIYAR*
```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```TSANTSAR BUTULCI```
*LOADING:*
*{LADIDI K'WADAGA🌚}*
_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_
_______________________
```We are here to educate motivate and entertain our reades```
_______________________
*JAN KUNNE⚠*
_*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_
*DEDIGATED*
*TO*
*RAHAMA ALIYU*
~*ABUJA*~
_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_
*🅿15*
Mai koko tace." To kinji inda maganar take, don haka sai kiyi hak'uri kinji da kunnen ki,wanda ya aske miki kanki." D'alha ya kalle ta cikin taikaci ya buga mata tsawa tare da fad'in."Rufe min baki ko inzo k'ara