Showing 30001 words to 33000 words out of 81013 words

Chapter 11 - SARAUNIYA JIDDA CMPLT

Start ads

09 Aug 2025

220

Middle Ads

suke da ita,

shiyasa taji duk zaman parts dinsu ya isheta,sallama tayi musu tayi gaba.

Koda ta isa part dinsu ta iske prince har yyi wanka yana daure da towel iya kugunsa,

Dasauri takarasa tayi hugging dinsa ta baya tareda kwantawa bayansa cikin kissa tafara magna mae prince.....

Wanka xakayi baka fadamun ba,naxo natayaka ko...

My prince ashe prof.yanada mata da yarinya dasuka bata baka taba fadamun ba,

Prince bae cemata komae ba,duk da tana makale a bayansa,

Taciga ba dacewa amma fa nasanta a india ashe can take karatu?
Sae dae bata da kunya,har gida fa ta iskeni tacimun face,

Dasauri yajuyuta suna fuskantar juna yace dama kinsanta ne da hartasan gdana na india?

Tamayar masa da aah,nan takwashe karya da gskyar abinda yafaru last week da jidda taxo gdanta.

Shiru yyi na dan lokaci,ashe ranar da jidda ta haskashi a mota gdansa ta xo daman๐Ÿค”

Tsadadden murmushin nan nasa yyi sannan yace don't worry my sweety,xanyi maganinta cikin gdan nan,

Bakinta ya lalubu kamar jira take ta cafke nasa,nan fa tsayuwa tagagaresu,suka zube saman gado,
Ina ganin haka na baromusu dakin.

Sae yamma likis sannan prince yaje part din umminsa,ita ma tasharesa tayi fushi dakyar yashawo kanta,

Nan takara cemasa yanxu angano yarinyar nan ae yakamata ace da aka gama meeting kaxo kazauna da kanwarka,

Har najib yazo sunyi fira yanata tambayarta karatunta gwanin burgewa,
tana maganar ne cikin fushi,

Da har yyi shirun nan nasa kamar bazaiyi magna ba,sae kuma yace to ae ummina sae ki turata da deejah part dina mu gaesa da kyau din,

Kaniyarka,nace kaniyarka,shashan banxa da wofi,shi najib din mekafisa ne iye?
Da harya yatako xuwa inda take don su xanta da yar uwarsa,

Dafe kae prince yyi sannan yace am so sorry ummina,bantafi bane don bacin ranki,sae don nagaji ne kawae,
Wanka fa nayi,sae na kwanta sleep .

Yanxu tana ina ne?
Ummin tace tana gdansu fidoh,

Yace shikenan intadawo sae mugaesa ko?
,don Allah ummina banson wannan fushin naki,

Sae lokacin tayimasa daria tace son banason wannan halin naka ne,yacena daena insha Allah.

****************

1week kenan da xuwan Jidda gombe,anbata bayi hudu masu kula da ita,sannan duk inda tayi deejah namakale da ita,

Ga kuma fidoh taxama kawarta kullum sae taxo sunfita shakatawa,

Kullum sae sunyi waya da auta da aysher,

Salman dintama kullum sae sunraba dare suna soyewa don sun fadamasa komae akan ita yar gwambe ce dama bacewatayi aka riketa amma basu fadamasa labarin MUGU ba,


Yau takama Tuesday jidda ce keta safa da marwa don salman hakurinsa yakare,yau yacemata yana hanyar gwambe don xuwa ganinta.

Tarasa yanda xata fadawa ummin,sae kawae tayanke shawarar kaesa gdansu fidorh asirinta a rufe,

Haka kuwa akayi,takira fidorh tafadamata komae daman tasan labarin salman din ,so batasha wahala ba wurin yimata bayanin xuwansa.


2:30pm
Jidda ce cikin shiga na alfarma tana sanye da wani tsadadden swis less,blue and black colour dinkin yahau jikinta bodyn yafitu masha Allah,

Simple make up ne saman fuskanta,bakin sae kyalli yake gwanin ban sha'awa,
Sarkanta na gold tasanya da abun hannu da zobensu,nan fa suka fara daukan ido,

Alkyabbanta ta dora akae tafitu,bakaramin haskawa tayi ba tayi kyau,tayi kyau harta gaji.

Dakin ummi tanufa ta ikseta kwance saman gadonta bayi nata mata tausa suna ganinta suka bar wurin,

Tashi ummi tayi taga kishingeden datake, takamu hannun Jidda tace masha Allah daughter kinyi kyau,sae ina kuma?

Murmushi jidda tayi sannan tace wurin fidorh xanje,
Murmushi ummin tayi tace to kibiya kigaesheda mae martaba kafin kitafi,yana part dinsa bae kaega fita fada ba.

Daxun naje gaeshesa yake tambayana ke,

Jidda ta amsa da insha Allah yanxu xantafi,sae na wuce din,sannan ta juya tabar dakin.

Harta fita ummi nabin bayanta da murmushi a fuskanta tana son jidda sosae har cikin ranta kamar ita tahaifeta.

Jidda bata tsaya ko inaba sae part din mae martaba,tun a hanya fidorh,Da salman ke kiranta don harya iso,
Yana gdansu fidorh din.

Tana yin sallama tashiga cikin palon,taji wani sallaman bayanta cikin wani cool voice mae ratsa zuciya,

Dasauri jidda ta juya yana sanye cikin riga da wando,farar t-shirt d bakin wando hannunsa zobe cikin aljihu yyinda kanshin turarensa na SI ya mamaye palon.

kamar koda yaushe idanunsa a lumshe suke,
sumar kansa luf-luf takwanta saman kansa sae sheki yakeyi da kyalli,

Ko inda take bai kalla ba,Wuri yasamu ya zauna can nesa da ita saman kujera,

yafiddo wayansa yana danne-danne,dan karamin pink din bakinsa jidda ta tsurama ido,daga bisani tadauke kae daga kallonsa hade da tabe baki.

Don tun randa akayi meeting bata kara ganinsa ba sae yau,

10mns kenan dazuwansu amma bawanda yacemawani kala,

Gashi wayan jidda sae kiranta salman yake,still mae martaba haryanxu bai fituba harlokacin

kiran salman ne still yakara shigowa , takalla kofufin taga babu alamun fituwar wani haryanxu,

sae tayi picking call din tareda gadin am so sorry my luv๐Ÿ’•

Insha Allah ganin xuwa ba ddewa ba,
Nakagara nima nayi toxali da face din nan naka my handsome....

Tunda tafara mgna prince yadago kansa ya zubamata tsadaddun idanuwan nan nasa
.....


Anty Fyn...๐Ÿ˜Š
[5/27, 5:46 PM] Anty Fyn๐Ÿ˜˜: [5/23, 9:43 PM] Anty Fyn๐Ÿ˜˜: S๐Ÿ…ฐR๐Ÿ…ฐUNIY๐Ÿ…ฐ JIDD๐Ÿ…ฐ


NA


ANTY FYN๐Ÿ˜˜

Ina kuke members of dis grps
Khaleesat haydar novels,
Rufaida omar fans,
Billy giro novel room
Shukrah novels
P.M.L writers and oll novel groups...& oll writers groups

Anty fyn na Mika jinjina tareda kyakykyawar gaesuwa a gareku..๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜Š๐Ÿ˜Š๐Ÿ˜Š๐Ÿ‘


Page 66-67


Kadaure kasha wani abu mae sanyi kaji my.....banason kadamu kanka sahibi.

Yanxu xantaho harsae kagaji da ganina sorry...datse kiran tayi jin kamar alamun tafiya...

Dasauri tadaga kanta caraf suka hada ido,waremata wadannan manyan idanuwan nasa yyi masu rikita mae kallonsu,

Wani irin kallo yake bintashi wanda takasa fassara ma'anarsa,kaga kuma wani mugun kwarjini dayamata duk jikinta rawa kawae yake,

Girgiza kae yyi irin naxamu hade, tareda watsamata wata muguwar hararar da saeda hanjin cikinta yakada.

Yadauke kansa daga kallonta kamar dama dole akasashi kallonta.

Yan gungune jidda tayi tareda tabe baki,juyuwa yakarayi taredayin alamun xai mike tsaye dasauri jidda tarigashi mikewa tadoshi kofa,

Sallamar mae martaba ne yasa jidda saurin dawowa kamar daman lokacin tashigo hada wani sakeyin sallama,

Mae maetaba ne ya amsa mata sallaman cikin fara'a atare suka zube har kasa ita da prince suka gaeshesa,

Kallonsu yyi cikin tsanin murna yace kuntashi lfya son &daughter?

Gabaki daya suka amsa da lfyalo Alhmdllh,

Sarki yace masha Allah,ya kalli jidda yace my daughter dafatan kinajin ddin zama damu?

Jidda tayi murmushi tareda yin kasa dakae tace inajin farinciki marar misaltuwa kasancewata ina taredaku daddy,

Babu abinda xance sae dae kara godiya ga mahalicci daya sadani daku da rayuwarku.

Murmushi jin ddi mae martaba yyi,sanna yace gud my daughter.

Yaushe xakuyi resuming skul din ne?
Jidda tace nan da 3weeks ne daddy.

Girgiza kae yyi yace Allah ya kaemu lfya,
Sannan yacigaba da cewa kinsan yaushe ne date din birthday dinki?

Cikin zakuwar son jin ranar jidda tagyada kae,tareda fadin bansaniba daddy amma na dde ina son insan ranar,

Sarki yyi murmushi yamaeda kallonsa ga prince da yyi shiru idanunsa a lumshe kamar baesan mesuke mgna akae ba,

Hannunsa yariko ahankali yabude idanunsa sosae yana kallonsu donshi har ransa yafara baci sae wani tambaye tambaye mae martaba kema jidda kamar wata yar gold.

Yaushe ne birthday din kanwar ka jidda?
mae martaba ya katsesa da tambayar.

Prince ji yyi kamar ya kurma ihu,wae ma shi ake tambaya birthday din yarinyar nan sale-salen taraenasa kawae ,a hankali ya furta bansaniba abba,

Bata rae sarki yyi sannan yace kana nufin harka manta lokacin da marganyiyah ke maku celebrating birthday kaeda jidda?

Shiru yyi irin na abun tunani,sannan yace oh!next week ne on 3rd june,

Sarki yace yawwa koda naji,yaushe kae xaka kuma aekin ne?

Prince yace hutun 1month nadauko,
Sarki yace gud,next week sae kushirya kuyi celebrating birthday dinku a nan cikin gda tunda rana daya ne,

Daram-daram kirjin jidda ke bugawa wae ma rana daya suke birthday da wannan dan raenin wayon,amma bahaka taso ba.

Prince kuwa tsadadden murmushin nan nasa yyi dake kara masa kyau,yace insha Allah abba haka xa'ayi.

Jidda ma murmushin taka kalo,tace Allah ya kaemu daddy,

Sarki ya amsa da amin,sannan yasa musu albarka!

Mikewa jidda tayi tayimusu sallama tayi gaba inda tabar mae maetaba da prince suna xantawa irin na da da ubansa.

Jidda bata tsaya ko ina ba sae gdansu fidorh inda straight palon baki tawuce,

Kwance ta iskesa saman kujera ya rufe fuskansa da hularsa,

Sanya yake cikin wani hadden blue din yadi tazarce anyimasa aekin da dark blue.
Yyinda kamshin turarensa ya game palon gwanin ddin shaka,

Sumar kansa ta tsurama ido gatanan baka wulik dukda yyi aski amma akwae dan suma mae kyau saman kan,

Bude hulan yyi kyakykyawar fuskansa ta bayyanah,murmushi mae sanyaye rae yasakar mata,tareda zubamata ido kamar yau yafara ganinta.

Cooldud....jidda tafurta cikin dariar jin ddin ganinsa,

rufe fuskanta tayi da tafin hannunta ganin irin kallon da salman kemata.

Marae -rae ce murya yyi yace haba jiddana yaxaki rufemun kyakykyawar fuskan nan,dake sanyani natsuwa,

Cikin shagwaba jidda tace tu kadaena kallona mana ko,..anajin kunyarka fa๐Ÿ˜Ž

Murmushi mae sauti yasaki,sannan yace tubanake gimbiya Jidda ,

Turu baki jidda takarayi tace banason wannan sunan fa๐Ÿ˜Ž

Saukowa yyi daga saman kujerar dayake ya zube kasa,yafara yimata gyara kimtsi,tubanake SARAUNIYA JIDDA.

Batasan lokacin da daria ta kufce mata ba hada kyakyatawa,
Yanda salman ke sunkuyama tane kebata daria.

Kashe mata ido yyi๐Ÿ˜‰

Yace daria namaki kyau jiddanah don Allah inmunyi aure kirinkamun daria kullum.

Kasa dakae jidda tayi cike dajin kunyar furucin auren da salman yyi,

Tsinkayo muryasa takarayi yace kinada kyau jiddana,nakagara na damkeki jiddanah,

Yakamata a kaeni wurin mae martaba ko yabani daman turuwa,

Zaro eyes jidda tayi tareda girgiza kae tace bayanzuba.

Kallonta salman yyi na yan seconds, yace jiddana bakya tausayina ko jiddana?

Jidda tace bahaka bane my...
kawae dae inajin nauyi ne,kaga ko 2weeks banyi ba,
amma insha Allah nanda yan kwanaki kadan sae namaka jagora har wurinsa,time din nakara sakin jiki dasu.

Cike da gamsuwa Salman yace shikenan Allah ya kaimu time din...

Jidda ta amsa da amin nan fa sukacigaba da firarsu irin na masoyan da kamar su cinye junansu.



Prine kwance saman gadonsa idanunsa a rufe tun dasowarsa gurin mae martaba,

Shidae a iya saninsa yarinyar nan mgna baetaba hadasu ba amma meyasa takesan kawomasa raeni,

A gabansa take waya da saurayi,
Sannan suna zaune a dakin mae martaba ko kunya bataji,
Ga kuma rashin gaesuwar dataki yimasa kiri-kiri taki gaeshesa,

Tsadadden murumushin nan sa yasaki mae sauti hangowa yyi lokacin datayimasa gungunae,taga kamar zai mike dasauri hartakae kofa,

Kenan dama rashin kunyar tasamun wuri ce tunda tana tsoronsa,

Dasauri yamike tunawa yyi da fitar datakesonyi ta hadu da boyfriend dinta,

Cikin ransa yace kadafa barikin indian ne xataxo tayi musu a masarauta,ta zubda musu mutunci,
mikewa yyi fuskansa a hade ya fitu daga part dinsa,

A hanya yagamu da dr.maryam amma ganin yanda face dinsa yake a hade kuma ko inda take bae kallaba yasa itama batacemasa kala ba ta wuce ya wuce.

Jidda ce ita da fidorh sukarako salman inda yana gab dashiga mota cikin parking space din gdan najib nacinno kan motarsa wurin.
dole yatsaya suka gaesa cike da girmamawa,sannan jidda tarakasa har bakin gate tana daga masa hannu,sunyi dashi next week xai dawo ranar birthday dinta.

Harsaeda yabacemata sannan ta tsallaka xuwa kofar gdansu caraf suk hada ido dashi,

Fituwarsa kenan daga gdan,yaga tanayima salman bye,bye.duk da bae lura danacikin motar ba,

Fuskansa kamar an aekomasa da sakon mutuwa,

Gabanta na dukan tara-tara tanufi tagefensa xata wuce yadamko wuyanta tuni tasaki ledar da salman yakawomata,

Kara hade rae yyi dasauri tadaena kallonsa sabida yanda idanunsa suka canxa ga jijiyoyin kansa sun firfitu,

Fizgarta yyi dakarfi suka nufi cikin gdan sabida kar yyi mgna a waje bayi su sami abin yadawa.

Kiiiiiii yake janta har arean part dinsa sannan ya bankadata ta fadi kasa,
Bakaramin tsorata jidda tayi ba ko ina jikinta rawa yake!

Cikin kakkausar murya yafara mgna 4rom where you are?

Wata uwar tsawa yadaka mata I said 4rm where you are?

Keda ubanwa ye nagani yanxu?

So listen very careful kiji wornin din xan miki dama iskanci nasan kinsaba tun a india na shaida,

amma abinda nakeson kisani shine,nan gdan ba gdan yan bariki bane idan barikinki xakiyi sae ki hada kayanki kibar gdan,

Kuma ki aje maetarki har sae kin kuma india sannan kyacigaba ,

Amma billahil azim,kinji narantse nakara ganin kafarki a waje,bare kuma naganki da wani saena babballaki,
sae na lafira yafiki jin ddi,
Idiot kawae,
Yana kaewa nan yyi gaba batareda jiran me jidda xatace ba.

Inda yawurgar da Ita nan take kwance kasa,baki bude cike da mamakin irin wannan masifar har lokacin jikinta bai daena rawa ba,

Gakuma tsanin takaeci dayarufeta yasa ma takasa tunin komae Allah ya isa kawae take iya furtawa tareda fadin sae an fitadin,
Watsastste kawae, tafashe da kuka a wurin.

Prince ko bae zame ko ina ba sae part din mae martaba,

Nan yasamu umminsa ma na wurin,

Gaeshesu yakarayi cike da girmamawa,sannan yyi shiru,

Mae martaba ne yakallesa yace son nasan da magana so go ahead inajinka.

Kasa dakae prince yyi sannan yacedama wannan yarinyar ce naganta dawani saurayi a kofar gdan abban najib,

So kuma ni banyarda da tarbiyan yaron ba shiyasa naxo don nashaidamaka ko xata fitar da miji ne idan aure take ra'ayi,sabida gudun yaudara..


Dariar nan irinta manya mae martaba yyi sannan yace son ae wannan ba matsala bane dama abinda ke raena kenan,

Prince yasaki wani makirin murmushi,Cikin jin ddin tiggun dayahada yace eh!to ae hakan nada kyau allah yaja da ran sarki,

Murmushi irin na manya mae martaba yakarayi sannan yace ae shikadae ne abinda xanyima wannan yarinyar,

Ko mahaifinta yadawo zaiga tabbas duk daya nadaukeku shiayasa nayanke aurar da ita gareka,

Dasauri prince yace na'am,mae martaba yace of course ,

Nabaka auren hauwau jidda, amatsayin matarka ta biyu.....sae ka hado sadaki!

Dif-dif prince yaji kamar numfashinsa xai dauke idanunsa yakara budewa sosae yaga ba mafarki yake ba,
tuni zufa tafara ketomasa yyinda idanunsa suka
canxa launi lokaci guda..........


Anty Fyn...๐Ÿ˜Š
[5/27, 5:47 PM] Anty Fyn๐Ÿ˜˜: S๐Ÿ…ฐR๐Ÿ…ฐUNIY๐Ÿ…ฐ JIDD๐Ÿ…ฐ

NA


ANTY FYN๐Ÿ˜˜



Wannan page din naku ne,ina kuke yan grp din Anty Fyn Special novels,su mtukur,mani house,my cwt kanwa(teemer luv๐Ÿ˜˜),Cwt fancy,faty bauchi,aahmila,anty fatee,.mrs galadima,mmn yusrah,matar soja,alfa fateema,smart luv,oluwashina, and rest..of grp members anty fyn namika jinjina a gareku thnx a lot 4 r ur support ...Allah ybar kauna๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜



Page 68-70


Shiru yyi yama kasa mgna har saeda mae martaba yakatse shirun da cewa son yakayi shiru?

Umminsa ce ta amsa da godiya yake ranka ya dade kunya yakeji,

Dasauri yadago idonsa dasuka kuma launin jajjawur yana kallon mahaifan nasa,

Cikin sarkewar murya yafara mgna don Allah abba,kayi hakuri kabarta tazabi wanda takeso,

Kallonsa mae martaba yyi na yan dakiku sannan yace wannan ba matsala bane dukanku gata ne xanmuku so bana bukatar shawaran kowa daga cikinku,

Kasa dakae prince yyi dayakejin kamar zai rabe biyu,yace abba kayi hakuri amma bana ra'ayin mata biyu,

Wlh dayan ma dakyar nake kula da ita,da ana rabi tu nida rabi ma xanyi,

Wata irin tsawa mae martaba yadaka masa yace ni kke cema baka iya rike mata biyu?

Yar kanen nawa ne daxan hadaku aure kke mun wannan furucin kamar xan nahadaka aure da kafira?

So get out of my side! aure dae babu fashi idan nadauramaka ka kasheta ka huta,

Sae in tabbatar da cewa baka iya zama da mace biyu na batamaka tsari,

Cikin tsanin tashin hankali prince yake bin mahaifan nasa da ido ga bakinsa yyi nauyi,

Cikin rawar murya yace don Allah abba kayi hakuri,banyi wannan furucin ba don bacin ranku,

Cikin zafin nama mae martaba yakatsesa da i said get out of my sight !
mutumen banxa mutumen wofi kawae๐Ÿ˜ก

Mikewa prince yabar wurin tafiya yake kamar xai fadi,idanunsa sun kan-kance dayasan haka xata faru da bae jeba,

dakyar yakae kansa part dinsa,bayi nagaidasa amma ko kallon inda suke bayayi,
Koda ya isa xubewa yyi saman gado zuciyarsa kamar xatafitu.

Gawani tsanin tashin hankali, daya keji a ran sa,tunda yake da mae martaba baeta yimasa fada ba,amma yau sabida wata banxa har tsawa yake masa kamar bashine na gaban goshi ba.

Haka dae yyi ta sake-sake don dole yaje yakara bashi hakuri sannan yafadamasa ya amince,
Wata irin tsanar jidda ce tadaso a zuciyarsa koganinta bayasonyi ma yakeji a ransa bare kuma aure,

Kiran sallah magriba ne yadashi daga kwancen dayake mikewa yyi yaufi toilet don yin alwala.


Jidda kuwa tunda yabarta nan,ta dde tana kuka sannan taja jiki tanufi part din ummi,tayi sa'a bakowa a babban palonta,sae bayi masu yin mooping din maraice,

Dasauri tawuce dakinta tafada wanka,nan ma ta dde tana nanata bakaken magan ganun da prince yagayamata,

Cikin kunar rae tafitu
Tashirya cikin kayan baccinta sallah ta gabatar,sannan tahaye gadonta don abinci batajin xata iyaci yanda takeji a ranta.

Wayar auta ce tadawo da ita daga dunuyar tunanin da tafada,
Cikin rashin kuzari tadauko wayar tareda yin pickin call din.

Hello ,besty dafatan ansakomana yayahnmu da wuri,
Murmushi jidda tayi don anbatar salman da auta tayi hartaji sanyi cikin ranta,

Tunawa tayi ko kiransa batayi ba bare taji ya hanya?
Ina yake yanxu

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login