Showing 45001 words to 48000 words out of 81013 words

Chapter 16 - SARAUNIYA JIDDA CMPLT

Start ads

09 Aug 2025

236

Middle Ads

Su auta ma gobe Friday xasu wuce ita aysher,

Dan tsoki tayi tashiga dialing no.din Dr.salman koda,xai sadata da aminiyar tata,

Koda yyi picking call din sae suka cigaba da soyewarsu tama manta, da auta take nema sai bayan sungama wayan.
murmushin jin ddi tayi sannan ta lumshe ido tana tunanin salman dinta bacci mai ddi ya dauketa cikeda mafarkin salman dinta,


************

WASHE GARI

Tun safe gate din gdan mai martaba yake a bude baki na nesa da kusa,
Yan uwa da abokan arziki keta shigowa cikin manyan-manyan motoci domin halarta daurin aure wanda xa'ayisa karfe 11:30 am.

Bangaren bayin gdan ma suma sunata yin Nasu aekin na bayi masu gyare-gyare nayi masu decoration sunayi,

Side din hjya sa'adiyya kuwa cike yake da yayanta mata da jikokinta dakuma manyan manyan aminanta Sunata shagali,

Uban gayyar kuma kwance yake saman royal chair dinsa Dr.maryam na gefensa tana masa sangarta banxa,

Shikuwa hankali kwance yakeshan coffee dinsa don yau dayake tunanin ransa xai kai karshen baci,

Sae kuma gashi yatashi ransa fes bbu wani damuwa don jiya kusan kwana yyi sallah,

Gashi ya lallashi matarsa ta fahimcesa sam baida interest kan Auren jidda,
Shi a nasa ganin kamar ba aure ne ake shirin yimusu ba,
Kawae xa a bashi a ronta ya koya mata hankali,
Ya horata,
To da irin wannan kalamin nasa yasa dr.maryam tasaki jikinta itama kamar ba itace ake shirin yiwa kishiya ba,

Mikewa Prince yyi yakalli dr.maryam yace my sweety.......

Sae kawae naga dr.maryam tashiga bathroom tahadamasa ruwan wanka tafitu tana ciremasa kaya,
Taja hannunsa xuwa bathroom din.

side din uwar biki na kuma wato ummin prince side dnta yafi kowane cika neman amarya ake mae make up taxo domin yimata make up din daurin aure,

Yakumbu ummin prince takira tace wai yakumbu ya banga yar tawa ba tana daukan ido?
Ni Sam banma sanyata a ido ba duk yau ina tashige me?
.karayin KASA dakai yakumbu tayi Tace Allah ya taimakeki ae gimbiya nacan na bacci tunda nahadamata ruwan wankan turare daxata Shiga tacemun nakulleta ta baya,

Da tafitu daga wankan bacci xata kuma batajin ddin jikintq,

Salati ummin tafarayi sannan Tace mutafi kibudemun dakin jiddan,

Koda suka Shiga dakin Jidda na kwance tayi dai-dai saman gado tana bacci hankalin kwance,

Kiran sunanta ummin tafarayi ,a hankali Jidda tafarq bude idanuntq har tabudesu duka,
Tasaukesu kan ummin Prince,

Saukowa tayi daga saman gadon taxo gaban ummin ta tagaisheta amsawa ummin tayi tana mai murmushi,

Tace my daughter maza,a tashi ayi wanka ga mai make up nan Tana jiranki,
Ae amarya bata baccn safe,

Yakumbu tahadamata ruwan wanka taje ta watsa ruwan tafitu,

Nan fa mai make up tafara aikinta...

Wata army green din doguwan Riga mai wasu irin stones tareda head dinta colourn pitch aka mikowa jidda tasanya,

Nan fa takara haskawa kamar walkiya gabaki daya daga ita har rigan daukan ido suke,

Ita dakanta mai make up din ido tazuvawa jidda cikin ranta tanajin-jina irin tsananin kyawun Jidda,

Wani farin net tasanyawa Jidda akai wanda yasauko har yarufemata fuska,sannan tafara yimata wankan turare,Har saida jiddan tace mata ya isa hakanan,

Ita kanta jiddan data kalli kanta a mirrow,sae dataga kamar ba ita ba,
Itakanata tasan tayi kyau murmushinta mai kyau tayi.

Fidoh ce tashigo dakin dasauri cikin shigarta na alfarma ganin Jidda yasa tasaki daria fariciki tareda fadin wooooooow😘😘😘

Amaryan yayanmu kinganki kuwq?
Shiyasa Prince yKe ta wulakanci ashe don yasan abinda yataka,yasan yanada tsadaddan baby a gefe,

Yyye net din fidor tayi tafiddo wani dan karamin kit tabude sai ga dankareriyar sarkan diamond ta bayanna sai wal_wal take,

Cikin hanzari fidorh tashiga sanyamata har abin hannu,

Wayanta tafiddo tafara yimata wasu hot pics sannan tasunkuya dai-dai kunneta Tace albishiinki,har an daura aurenku,

Wata irin faduwar gaba Jidda taji wadda bata taba yin irintaba nAn da nan idonta yacika da kwalla dukda bata dauki auren serious ba amma taji idanunta sun kawo ruwa dawani irin tashin hankali maran misaltuwa inama ita da salman dinta ne,

Wata xuciyan ne tabata amsa da Dalla kada kidaMu kanki bikinki da salman ae nan gaba kadan ne,

kuma sai yafi wannan kyau d kayatarwa,ajiyar zuciya tasaki mai karfi wanda har fidoh ta tambaya da lfya?


Hannunta fidoh takama suka nufi down stairs nan fa wurin yadauki guda isowarsu cikin Palon yyi dai-dai da shigowan angwaye.

Babu abinda ummin prince ke fadi tace Alhmdllh ganin irin kyawun d Jidda tayi,ga kuma mafi soyuwa acikin yayan nata wato prince kana kallonsu kasan sun dace da juna,

Pictures Ake ta dauka masu video nayi,
Babu abinda jidda keyi sai innalillahi wa inna ilahi raji'un sakamakon wta irin faduwar gaba datakeyi ,
Mai da kallonta tayi ga prince Wanda yasha wata danyar shadda fara tas mai daukan ido tasha wani mugun aiki Wanda akayi da coffee din zare,dinkin yar ciki da babban riga,

Hular Kansa ma coffee CE,kafarsa nasanye cikin coffee din cover shoe,

Hannunsa na dama yana sanye da agogonsa na diamond mai dan karen kyau, gakuma zobensa na azurfa dayakara kayatar da hannun yana sanye a karamin Dan yatsansa,

A takaice prince ya wanku iya karshe,yyi kyau har yagaji,komae NASA abin kallo ne babu abinda yake sai tsadadden murmushin nan NASA da triple dimple dinsa ke loba wa gwanin ban sha"awa .

shiyasa jidda tashagala da kallonsa bata taba karemasa kallo kamar yau ba,

Kuma bata taba ganin wanda shigan hausaaa yyi ma kyau ba kamar Prince,

Wata zuciyan ne ta ce kyan banxa,ji bakaken magan ganun dayake fada miki,
Nan da nan takauda kae daga kallonsa,
Jitayi wata kanwar ummin prince wadda ake kira da Anty jummai tanafadin a jawo ango ayimasa pics da amaryansa,

Najib ne yajawo hannun prince har Inda Jidda take xaune jin hannun prince cikin nata yasa hantar Cikinta kadawa,

Anty jummai CE taxo gaban Jidda tayane Dan net din d aka rufemata fuska dashi,

Fitsari ne kawai jidda bata saki ba,ganin idanunwan dubban jama'a akanta,
prince kansa ido yaxubamata har ga Allah inyace yarinyar batayi kyau ba yyi karya sai dai Sam bata cikin yan kayansa yadauke idonsa dasauri,

Ihu yaji ansanya
Abinda bai saniba Shine tunda yafara kallon Jidda ake daukansa pics tako ina,

Tsadadden murmushin nan Sa yyi cikeda yan bariki yasunkuya dai-dae ku nnen Jidda yace smile mana...my Cwt gal..😉

Yyi maganar ne yanda Anty jummai dake gefe xatajisa,
aekuwa saidataji,
Har tayi kokarin kaimasa duka yakauce yana murmushi,
Sunsha pics inda daganan suka nufi side din mai martaba,da na hjya sa'adiyya ,

Ranar farida ta raina kanta ganin karshen kyau da jidda tayi,da yanda taga prince yana nunawa duniya bilhakki yanason jidda,gakuma kowa na gdan nasanta shiyasa tayi lakwas sau biyu kadae tashiga pics din ma,

Bare kuma dr.maryam kasa tsayawa tayi wurin tanufi side dinsu taita kuka.
don ba karya duk Wanda yaga prince da jidda yasan sun matukar dace wa dujuna,


Babu abind ke damun jidda kamar yNda taga a na daukansu pictures tasan dole sushiga duniya addu'a tayi Allah yasa salman d mutanenta kada suga pictures din nan,har Auren ya mutu,

Anci ansha an gwangwaje biki yyi biki taro yatashi lfya,

Bayan sallahn isha'i Jidda CE saman sallahya tana tasbihi dakuma Neman tsari daga sharrin makiya,sannan taroki Allah yasa auren kada yadade yyi sati daya,sannan kuma tanemi Allah ya kaisu lfya yabasu sa'an karatu yadake yau 12:15am jirginsu xai tashi xuwa india..

Shafa adduan tayi,sannan tajawo wayanta no din auta takira taji switch off takira ta aysher itama tajita a rufe amma fa tasan yanxu sun isa,
Ko ya akayi no.dinsu baya,shiga oho!

Yayh Saef takira sun DDE suna fira amma ko kadan bata fadamasa an daura mata aure ba,

Yace mata dai zaixo har India akwai maganar dayakeso suyi yafison sai face to face sannan,

Hakasukayi sallama batareda tayi tunanin ko wace mgana yakeson suyi ba.

Dr.salman dinta takira suyi wayar bankwana ganin har 10:01pm kada a fara nemanta,

Shima sun kwashi kusan awa daya suna waya tana narke masaa dakyar sukayi sallama badon sunso ba,

Tana gamawa wata baiwa tayi sallama tareda Neman izinin shigowa,
Jidda ta ba izini,
Zubewa tayi ta kwashi gaisuwa sannan Tace ummin prince na nemanta yanxu,

Ganin nan xuwa jidda ta furta tareda mikewa tasanya far in hijab dinta mai adon golden kalan na larabawa tafita down stairs dr.maryam ta iske xaune gefen ummin prince kanta a kasa gakuma wasu mutane a Palon wadanda bata gane fuskokinsu ba,

Xaunawa jidda tayi dayan side din ummin nan fa aka Shiga yimusu NASi ha,sosae duk akan su xauna lfya suyi biyayyah ga mijinsu suyi hakuri da junansu da dai sauransu..

Kiran fidorh ummin prince tayi tace mata taja jidda sutafi sama tasake wanka,

Bayan tafitu wankan ne fidorh tamikamata wani tsadadden material Milk colour maran nauyi sai dae kana ganinsa kasan bakarin material bane,

Dinki Riga da siket me,dinki yaxauna ji kinta das-das kwalliya sosae fidor taxauna ta tsara saman kyakyawan fuskan nan,
Cikin kan-kanannlokaci jidda ta fitu kamar mai shirin gasan, kyau,

Alkyabba mai Dan Karen kyau fidorh ta dorawa jidda sannan tafara aikin wato yi mata wankan turare,

Fituwa sukayi lokacin karfe 11;20pm na dare,suna sauka down stairs ummin prince Tace masha Allah ,masha Allah my daughter,

Hannunta takama suka nufi side din prince domin kaita dakinta tagani kafinsu tafi,

Fadin tsarin da kyawun Palo biyu da bedroom ukku da kitchen din jidda bata lokaci ne,mai karatu yahangp yanda ummin ummin prince xata kayatar da Gdan jidda yasan dole naira tayi kuka,

A gurguje suka fitu daga side din dakyar jidda Iya yiwa ummin prince godiya,

Amma cikin ranta tunanintake irin wannan GDA dakayan cikinsa duk NATA ne amma a matsayin matar prince?

So basusan baxaman aure xa suyi ba,
Sun dage sai wahala suke musu Karo nafarko Dataji tausayin iyayen nasu dakuma irin kulawar da ummin prince ke bata,

Shigowarsu Palon mai martaba ne yamaidota data duniyar tunanin data afka

Mai martaba na hakimce saman saman kujera hjya sa'adiyya na gefensa,
prince da dr.maryam na xaune saman carpet din dakin kansu nakasa,

Saman Kujera ummin prince taxauna daga bangaren daman mai martaba,

Wuri jidda tasamu itama tazauna a kASA ta Sadda kanta kasa kamqr yqnda su prince sukayi,

Sallama Mae martaba yyi kowa da kowa ya amasa ,sanan yafara yimusu nasiha da nuna musu darajar aure,
Da darajarsa yaja hankalin su jidda kan biyayyah gamiji,
sannan yaja hankalin prince daya rike nauyin dayahau Kansa,yyi adalci tsakaninsu ,yaji tsoron Allah kada yaxalunci ko daya daga cikinsu ko y fifita daya akan daya hakan bakaramin bala'i bane,
Hakayyi ta yimusu wa'azi mai ratsa zuciya tuni jidda tfashe da kuka tasan ko daya baxata Iya ba,baxta iya yima prince ko daya daga cikin hakkin daya rataya akanta ba,shikenan kuma mala'iku xasu dunga tsinemata albarka ita tashiga ukku,

Dakyar Ummin ta lallsheta tayi shiru, inda aka fara fitu dakayansu anasanysu Mota,

sannan suma suka shiga Motocinsu hada ummin prince cikin masu rakiya,
Prince da Dr.maryam motansu daya,ummin Prince da jidda da deejah motansu daya,
Hjya sa'adiyya da farida,da babbar yayah suma cikin Mota daya ,sauran yan GDA su fidorh najib suma duk suna cikin nasu motocin,

Suna cikin tafiya ne ummin Prince Tace my daughter akwai wasu magunguna na nan cikin karamin kit dinki Akwai bayanin yanda xakiyi amfani dasu,a wani littafi shima yana nan ciki ,

Kidaure kiyi amfani dashi kinji,
Haka ummin prince tayita kwatantawa jidda har suka iso airport din.

Batareda da bata lokaci ba Prince, Dr.maryam,farida sai kuma amarya jidda😉😜
Suka shige Jirgi anatata daga musu hannu kuka yaci karfin jidda tashige dasauri...😥😢😭

INDIA.....😉


Anty Fyn....😊
[29/07, 20:39] ‪+234 814 610 5988‬: S🅰R🅰UNIY🅰 JIDD🅰

NA


ANTY FYN😘



Dedicated to khadeejah sidi&Billy giro😊


Page 81


Jiki a sanyaye ummin prince takama hannun deejah daketa kuka suka nufi mota.

Cikin jirgi kuwa tunda jidda tashiga take aikin kuka,ganin babu mai lallashinta yasa tayi shiru don kanta.

Dama Dan nesa dasu prince tazauna,dagowa tayi takallesu taga Dr.maryam tayi matashi da cinyar prince sai wani shafa fuskansa take shikuka yana kokarin cije mata hannun ,

Sai murmushi yake,Dan karamin tsoki taja ahankali tafurta da yan iska kawae,

Wani malalacin murmushi tayi da ita,kadae tasan ma'anarsa tagyara xama tareda lumshe ido,

Ba a dau lokaci ba bacci Mae nauyi ya dauketa,


4:30pm

Jirginsu yasauka a new York, fituwa mutanen suka farayi daya-bayan daya,

Farida na hango tana fituwa gakuma su Prince a bayanta hannunsa namakale da na Dr.maryam data dan kwantq saman kirjinsa haka sukaita safkuwa har suka zo KASA,

Ido nake rabawa naga ta inda jidda xata bullu amma shiru-shiru sai safkuwa ake banganta ba,

A hankali take saukowa cikin takon kasaita da nuna ta isa,

Hango aminan NATA tayi da zuwansu kenan,yasa tafara sauri kamar ba ita ke yanga ba,

Daga karshe kuma tasanyq gudu auta da aysher dake tsaye suma suka ruga fadi suke oyoyo,oyoyo....

Da gudu jidda takaraso sukayi wani irin hugging juna su duka ukkun suna shewar murna,

Hakan dasukayi yasa hankalin mutane dayawa yadawo kansu,

Motoci guda goma Jere sukaxo tarban prince,
Prince da tun fituwar jidda jirgi yake kallonta dayanda tafara tfya ahankali,dakuma sanda tafara gudu,

Cikin tsanin bacin rae yasaki hannun Dr.maryam yanufi inda su jidda suke tsaye,
Jidda da aminanta harda farida dataxo gaisawa da auta, fira tabarke tsakaninsu suna maida yanda akayi suna daria cikeda tsanin farincikin ganin junansu,

Ko kallon inda su prince jidda batayi ba bare tasan yanatahuwa,suka nufi Mota domin Barin wurin,

Ansar car key din jidda tayi dga hannun aysher tabude marfin Mota kenan tana niyyar Sanya kae taji wani mugun duka a tsakiyar bayanta saida tayi yar kara,

A harzuke ta juyu sukayi 4eyes dashi idanunsa sunkuma kalan jajjawur sun kankace,

Tuni hantar cikinta yakada tasauke idonta kasa dasauri nuni yamata da wata bakar range rover koba a fadamata ba tasan abinda yake nufi sakin car key din hannunta tayi,

Tayi tsaye kikam bata,da alamun ko motsawa ganin yafara nufu inda take ne yasa ta arce da nakare, tanufi motan dagudu sosojojin dake wurin tsaye ne suka budemata kofa tashige,tana gungunai,

Juyawa tayi taga Dr.maryam natayin yar dariar jin did,
Ranta ne yakara baci ganin dariar da dr.maryam keyi mata,

A kufule ta furta duk xaku ci ubanku daga ke harshi duk wanda yaci tuwu dani mai ya sha...

Wani Mugun kallo prince Ya watsawa su auta da aysher Wanda yasa auta shigewa Mota dasauri,

Juyawa yyi yaga inda farida tayi, amma baiganta ba,
Ae tun yana fara yiwa jidda nuni da hannu farida tabi tabayansa ta sheka da gudu kafin a xo kanta,

Cikin takunsa na kasaita yafara tafiya fuskan nan tamau kamar baisan meye daria ba bare kuma smilling yanufi motar xai shiga,

Cikin karairaya dr.maryam tanufu inda yake Amma run kafin takaraso ya tsaidata da hannu cikin muryan nan tasa mai tsoratarwa yace maza kishiga mota kema kitafi gda banson sakarci,

Wata irin kunya takama dr.maryam har tana tun-tunbe wurin sauri cikin ranta tana jinjina kai irin wannan yarfi da prince yamata kamar ta suma don takaci,batasan ranar daxai canxa ba,

Duk yanda KKE da Prince rana daya sai ya yarfa mutum gaban bainar jama',dakyar ta isa bakin motar tashiga dasauri.

Jidda dake cikin mota kuwa dukda ranta yake a bace ganin cin fuskan da prince yyi wa dr.maryam yasata kwashewa da daria hada rike ciki,

A fili ta furta idiot kawai,jin karan bude mota ne yasatayin shiru dasauri prince ne aka budewa mota yashigo baya inda jidda take.

Driver yyi wa mota key sukahada convey suka halba saman titi,

Tunda yashigo motan aka kirasa waya cikin harshen larabci yake maganar shiyasa jidda dake kallon gefe batajin abinda yake fada don bawani gane larabci take ba,

Dan juyuwa jidda tayi taga yanda yake mgna yana yatsina fuska kamar dole yake mgnar,
Gashi sai wani cika yake yana batsewa batasan lokacinda daria ta kwace mata ba,

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login